Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

naka?, maiyasa zata yimin haka?."

"Well DEENAH maybe she has a reason behind it..."

"Wane irin dalili ne hakan, koma menene dalilin ta baikamata tayi masa hakan ba, he doesn't deserved that, she humiliated him after all the love and care he had shown me, ba zan manta lokacin da ya durƙushe kan guiwowin ba sa pleading her akan kada ta raba shi da DEENAH but she turned a deaf ear ta wulaƙanta shi, sam bai cancanci hakan ba, menene laifin sa?."

Shiru Jafar yayi yana mai jin tausayin ƙanwar tasa ganin yadda take ta kuka, baisan wane irin kuka zata yi ba bayan ta gano cewar ba zata kuma haɗuwa da shi ba maybe yace har abada, he is very sad da abinda Umma tayi gashi kwata-kwata yanzu he can't get through ZEEYAD, hakan na nufin yayi nesa dasu sannan ba zai sake dawowa Nigeria ba, da wannan tunanin ya bar cikin ɗakin tare da ficewa daga gidan ma baki ɗaya.

DEENAH kuwa wuni tayi a ɗaki ranar koh abinci bata fito taci ba, sosai takejin haushi da zafin abinda Umma tayi, dah Umma tasan irin son da take yiwa ZEEYAD dah bata fara yi masa hakan ba, tasan yanzu ita da farin ciki kuma wataƙil sai a lahira, sabida Umma zata sake jefa ta halin da yafi na baya da tayi, sosai take kuma jin haushin kanta na kasa tuna ZEEYAD da tayi a wannan lokacin, after irin wahalar da ya sha a kanta, what if dagaske ta rasa shi har abada kenan, toh tabbas itama zasu rasa ta ne.



************************


__________Tsaye take ta a gaban wani ƙaton tekun, wurin shiru yake bakajin ƙarar komai sai na iskar dake kaɗawa dama kuma ruwan tekun ɗin dake kai komo yawa zai haɗiyo mutum, tana sanƴe da farar gown ɗin da ya kai mata har ƙasa kanta ɗaure da farar ɗankwali, ta juya baya.

A hankali yake takowa wurin ta staring at her back.

Juyowa tayi suna haɗa idanu kafin kuma ta sakar masa wani irin murmushi tana cigaba da kallon sa.

"DEENAH?" ya furta.

Hannu ta miƙa masa alamun yazo gare ta, babu musu yayi saurin ƙarasawa yana shirin kama hannun nata.

Wata budurwa ce wacce baiga fuskar ta ba tayi saurin shigewa tsakiyar su, kafin ta juya ga DEENAH tana tunkuɗa ta cikin ƙaton tekun ɗin.
"DEENAH!" ya furta da ƙarfi, a daidai lokacin ne kuma ya farka daga mafarkin da yake yi ɗin.
Dafe kansa yayi da hannayen sa yana jin yadda zuciyar sa ke mugun gudu, idan da wannan sau huɗu kenan yana yin thesame mafarki da DEENAH, wanda ya rasa gane mai hakan ke nufi, addu'a yayi sosai yana mai ɗago da kansa.
Idanun sa ne suka sauƙa kan wata Baƙar kuliya mai wani irin manƴan Hazel eyes staring at him in the dark.

Koh kaɗan bai wani ji koh da ɗar bane a cikin zuciyar shi sai ma idanun kuliyar da yake kallo shima.
"So it's you again, it's been long since i saw you" ya faɗa.

Wani irin kuka mai ban tsoro kuliyar tayi kafin kuma tayi saurin sauƙa daga kan gadon tana ficewa da gudu ta window ɗin ɗakin.

Da kallo yabi inda tabi kafin kuma ya miƙe tare da zuwa ya tsaya ta window ɗin.
"I know you're evil, but whatsoever you may be i would make sure i get you one day."





*Yawan Comment, Yawan Typing*






*MHIZZ JIDDHERR.................✍🏽*
[7/31, 12:45 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D*
```[The Abandoned Prince]```



*NA*
*JIDDAH BINT MUHAMMAD*





*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*





*033...*




*A NEW LIFE*




____________Kwance take kan bed ɗinta da duƙunƙune kanta cikin pillow.

Buɗe ƙofar ɗakin Umma tayi ta shigo, ganin har yanzu DEENAH ɗin na yadda ta barta yasa ta fara magana cikin takaici da baƙin cikin halin da ta 6ullo dashi ƴan kwanakin nan "MADEENAH watau dai ba zaki bar wannan kukan na dalilin banza da wofin da kika tsirowa kanki ba koh, shikenan ke kullum bakida aiki sai rufe kanki a ɗaki kiyi ta kuka, ai yaci ace koh ciki ɗaya aka haifo ki da yaron nan kin manta dashi yanzu, toh ki sani ba zan kuma lamintar hakan daga gareki ba, zaki tashi ne tukun ki wuce kizo kici abinci koh sai ranki yayi mugun 6aci yanzun?."

DEENAH da ta ƙara volume ɗin kukan ta, ɗagowa tayi tana wurgi da pillow ɗin kafin kuma ta tashi tana faɗawa cikin bathroom ta rufo ƙofar da ƙarfi.

Da kallo Umma ta bi ta kafin kuma ta ƙarasa bakin ƙofar bathroom ɗin tace "Idan kin gama kukan naki marar dalili ki fito yanzun nan ina jiran ki, idan kuma kika kuskura kika sa raina ya 6aci baki fito dawuri ba ni dake ne a gidan nan" tana faɗin haka ta juya ta fice daga cikin ɗakin.

Kuka mai ƙarfi DEENAH dake cikin banɗaki ta sanƴa, sai da tayi mai isarta kafin ta wanke fuskar ta da duk ya kumbura tsabar kuka ta fito.

Cikin falon ta fito ta zauna ba tare da ta tankawa Umma dake binta da kallon takaici ba.

"Zaki zo ki ɗau abincin kici ne kokuwa?."

Tashi tayi daga inda take zaune ta sauƙo inda Umma take tare da ɗaukar plate ɗin abincin tana niyar barin wurin.

"Ina zaki?, dawo nan ki zauna kici."

Dawowa tayi ta zauna tana ƙoƙarin haɗiye kukan dake son ku6uce mata tare da buɗe plate ɗin ta hau cin abincin.

Tusawa kawai takeyi ba wai dan tanajin daɗin sa ba, yayin da hawaye ke gangaro mata kan ƙunci.

Bai fi cokali huɗu tayi ba taji amai na ƙoƙarin zuwan mata, dan haka ajiye cokalin tayi tana kya6e fuska inda dakyar ta iya haɗiye na cikin bakin ta.

"Ba dai ki cemin har kin ƙoshi ba."

"Umma dan Allah kiyi haƙuri wallahi bana jin cin abincin" ta faɗa cikin kuka.

"Aa ba dai a gidan nan ba kam, banga dalilin da zai sa kice bakya jin ƴunwa ba bayan lafiyar ki ƙalau, maza ki buɗe baki kici abincin nan yanzu."

Hannu ta kai ta ɗau cokalin tana sake ɗebo abincin ta kai bakin ta.

Bata kai ga haɗiye wa ba, taji amai na zuwa mata ba tare da wani 6ata lokaci ba kuwa ta shiga kwararo shi anan yawa ƴan hanjin cikin ta zasu zazzago duka.

A ruɗe Umma ta iyo kanta tana kama ta, tare da jero mata sannu yawa zata ari baki, kafin kuma ta kama ta suyi cikin ɗaki, bathroom ta kaita ta wanke mata bakin ta kafin kuma ta fito dan barin ta tayi wanka.

DEENAH idanu ta ƙurawa cikin mirror ɗin banɗakin tana kallo da idanun ta da sukayi luhu-luhu tsabar kuka wanda gani ɗaya zakayi mata kasan ba isasshiyar lafiya gare ta ba.

Wanka tayi ta fito kafin ta shirya cikin wasu irin Baggy ɗin riga da wando tana komawa kan bed ta kwanta tare da rufo bargo har izuwa kanta.

Sosai ta shiga halin tunani da ƙuncin rashin sa, a dah tasha ƙaryata kanta cewar bata sonshi but a yanzu ta gane gaskiya, tanason ZEEYAD sannan kuma tun ba yau ba ta kamu da son nasa, and now Umma tazo ta ruguza komai, tana neman kai rayuwar ta ga halaka, a yanzu babu abinda takeji a cikin zuciyar ta sai zafi da ƙunci, sosai zuciyar ta keyi mata raɗaɗi, musamman idan Umma tayi maganar ta mance dashi dan kuwa ya riga da yayi mata nisa, ita kanta tasan indai ZEEYAD ya cika mai zuciya toh kuwa koh da waiwayar ta ba zai sake ba.
Duƙunƙunewa tayi tana cigaba da rera kukan nata da ya zame mata jiki a hankali.


*********************


_________Da dare ganin jikin DEENAH ya rikice ya sanƴa Umma kiran likita yazo ya duba ta har gida, inda akayi mata ƙarin ruwa dama kuma allurai.

Zaune Umma take kusa da ita tana jin yadda take ta rera kukan nata da yaƙi ci yaƙi cinƴewa tunɗazun.

Jafar ne ya kalli Umma yace "Umma inason magana dake?."

Kallon sa Umma tayi tace "Inajin ka."

"Maybe in private" ya faɗa.

Ajiyar zuciya Umma ta sauƙe kafin ta tashi tana ficewa daga ɗakin inda Jafar ma ya mara mata baya.

Kallon ta yayi yace "Umma nasan ni ban isa na ja dake kokuma naga rashin kyautatawar ki akan dukkanin wani hukunci da zaki yanke a matsayin ki ta uwa a gareni ba, sannan kiyi haƙuri ki gafarce ni da maganar da zan faɗa miki yanzu, maganar gaskiya Umma shine sam baki kyautawa ZEEYAD ba haka ma DEENAH, duk da bansan dalilin ki na ganin kin raba alaƙar mu dashi ba amma inason nasan menene dalilin da yasa bakya ƙaunar sa kokuma ya ra6e mu har ma wata alaƙa ta dauru tsakanin sa da DEENAH?."

Kallon sa Umma keyi kafin tace "Ba wai ƙaunar sa bane bana yi, sai dai kamar yadda ka faɗa sam banason wata alaƙa ta ƙullu tsakanin sa da DEENAH."

"Amma Umma maiyasa, Umma he loves DEENAH so very much, sam baiyi deserving abinda kikayi masa ba, Umma ke kanki kinsan yadda yake matuƙar nuna kulawar sa akan DEENAH wanda koh wannan so called saurayin nata Abdul bai nuna mata koh da kwatan hakan bane, Umma ZEEYAD bai guji DEENAH ba bayan rashin lafiyar da ta faɗa a baya, that means he has a good heart sannan a shirye yake da yayi accepting ɗinta duk yadda take, bai ta6a nuna gajiyawar sa na nuna kulawar sa a gareta ba, he was always worried about her na rashin samun lafiyar ta, Umma ZEEYAD has a good heart sannan tsakanin sa da Allah yakeson DEENAH ke kanki kinsan da hakan but maiyasa zaki saka masa da breaking heart nasa wurin raba shi da DEENAH, after all what he did."

"So kana son na ɗauki auren ƴata na baiwa total stranger wanda bansan menene tushen sa da asalin sa ba, bance bashida kirki ba, ofcourse he is kind hearted sai dai barin sa cikin rayuwar mu shine yafi alkhairi a gareshi dan kuwa koh da yana nan ɗin, babu abinda zai sanƴa na ɗau auren DEENAH na basa, bayan ban ta6a sanin kowa nasa ba, hasali ma ba sanin ingantaccen inda ya fito koh wanene shi mukayi ba, bansan ta wace hanƴa ya samu ɗumbin arzikin da yake juyawa ba, bayan daga gani bashida kowa koh wata alaƙa da wannan ƙasar, how comes yaron da na sani yake yawo tamkar almajiri a dah chan turns to be yayi wannan uban kuɗin alhalin bayida wani gata koh mai tsaya masa a ƙasar, and you expect me na ɗau auren DEENAH na basa, daga nan kuma na shiga bakin duniya cewar arziki da kuɗi sun rufemin ido na ɗau ƴata na aura wa wanda bansan asalin sa da tushen sa ba, he had done enough for us, tayaya kake tunanin zan barsa ya cigaba da yiwa DEENAH hidima bayan nasan ba bashi auren ta zanyi ba, yaje shi Allah zai haɗa kowa da rabon sa."

Baki kawai Jafar ya saki yana kallon Umma har ta idda zancen ta nan yace "But...but Umma Allah ya kan sauya rayuwar mutum cikin abinda bai fi daƙiƙa ɗaya ba, dama duk sabida bakisan asalin sa da tushen sa dama kuma yadda akayi yayi arziki bane ya sanƴa ki yanke wannan hukuncin?."

"Kwarai kuwa, koh kai kasan asalin sa da tushen nasa ne, kana aiki ne kawai a ƙarƙashin sa sannan a iya zaman ka dashi ya ta6a buɗar baki ya baka cikakken labarin koh shi wanene?."

Shiru yayi yana nazari kafin kuma ya girgiza kai alamun Aa, sannan yace "Ya dai ta6a cemin shi ɗan ƙasar Egypt ne."

"Egypt?" Umma ta faɗa tana kallon sa.

Kai Jafar ya jinjina nan tace "Who knows if faɗamaka hakan kawai yayi, but koh kaɗan baiyi kama da Balaraben Egypt ba, he must be from Asian countries, koh ma dai menene i have already made up my mind, and i won't go back on my words."

"Amma Umma, think about DEENAH..."

Hannun ta ɗaga masa tace "DEENAH will be fine, am sure kawai tausayin sa dama kuma kyautatawar da yayi mata lokacin da batada lafiya ke damun ta, idan ta ɗanyi kwana biyu yanzu ita ma mantawa zatayi dashi."

"Umma yakamata ace kin fahimci DEENAH, she is inlove with him."

"No she is not, she is still a child, ƙuruciya ce kawai ke damunta, dah zaka yi bincike mai zurfi yanzu zaka gane ba wata soyayya da takeyi masa, just let me deal with her issue."

"Umma you misunderstood DEENAH's feeling, she is actually inlove with him, if not then maiyasa tun bayan dawowar ta hayyacin ta bata kuma sake samun nutsuwa ba, batada wani magana kullum da ya wuce nasa, sannan batada wani aikin yi sai kuka and you called it tausayin sa take, of course akwai tausayin nasa haka kuma akwai soyayyar sa tattare da DEENAH, think about it Umma kina neman jefa rayuwar DEENAH ga halaka ne tun ba'a je koh ina ba ta fara zazza6i imagine kuma mai zai faru nan gaba."

"Enough of this Jafar, babu abinda zai faru, am sure DEENAH will be fine, kayi mata addu'ar samun lafiya kawai."

"Umma ai it's a must nayi mata addu'a, but Umma kinyi kuskuren raba DEENAH da ZEEYAD coz am sure ba zata kuma samun mai sonta kamar sa ba."

"Have you lost your mind koh menene Jafar?, addu'a zakayi mata Allah ya musanƴa mata shi da wanda yafi alkhairi ba wai ka dinga irin maganganun nan ba, it doesn't make sense, and mind you banason sake jin maganar wani ZEEYAD or something similar to that a cikin gidan nan, kayi ƙoƙarin ganin kayi calming ƙanwar ka na ganin ta mance dashi sannan kuma she have to move on,DEENAH ba zata rasa masoyin gaske ba da izinin Allah, banason ka kuma sake yimin wannan maganar, kaji?."

Kai kawai ya jinjina yace "Am sorry, ki gafarce ni idan na 6ata miki rai."

"It's alright, muje mun barta ita kaɗai a ɗaki."

Juyawa sukayi tare da komawa cikin ɗakin.

Kallon DEENAH da har yanzu bata bar kukan nata ba yayi cike da tausayin ta kafin yace "DEENAH, it's okay haka nan kinji, stop crying kada ki jawa kanki wani ciwon."

"Umma...Umma bata sona yanzu."

Kallon juna Jafar da Umma sukayi kafin yace "No DEENAH ki bar faɗin haka, kema kinfi kowa shaida yadda Umma ke ƙaunar mu, take kuma iya ƙoƙarin ta na ganin ta faranta mana da dukkanin wani abu da ta mallaka, Umma ba zata ta6a aikata wani abu da zai zamto cutarwa a gareki ba."

"Mai kake nufi, kana nufin Abyad shi ɗin cutar dani zaiyi ne, maiyasa Umma ta kasa ganewa ne, yanada kirki sosai maiyasa zatayi masa abinda ta aikata, bai cancanci hakan ba."

"No DEENAH ki bar faɗin haka, bance ZEEYAD cutarwa ne shi ɗin a gareki ba, but am definitely sure indai har keda shi a destined to be together then babu abinda ya isa ya hana yiwuwar hakan,.just kawai ki kwantar da hankalin ki kici gaba da addu'a kinji?."

Kai ta jinjina masa cikin kuka tana lumshe idanu ba tare da ta kalli Umma dake zaune gefen ta ba.



*************************


__________Tsaye yake gaban mai Martaba dake zaune kan Throne ɗinsa kafin yace "You asked of me."

Murmushi mai Martaba yayi masa yace "Yeah of course, inaso ne mu tattauna da kai."

Yatsine fuskar sa yayi kafin kuma ya dubi manƴan mutanen dake wurin kowanne idanun sa akan su, sannan kuma ya saki fuska yace "Yeah tell me" ya faɗa yana zama a gaban mai Martaba ɗin.

Sosai mai Martaba yaji daɗi nan ya kalli ɗaya daga cikin mutanen dake zaune kan kujera yace "Sarkin yaƙi, i guess lokaci yayi da yakamata a fara koyawa Yarima amfani da takobi."

Wani irin kallo ZEEYAD ya ɗago yana yiwa mahaifin nasa, wani wai amfani da takobi sai kace wanda zai fita yaƙi.

Murmushi sarkin yaƙi yayi yana miƙewa tsaye cike da girmamawa yace "Your wish is my command your Highness, gaskiya ne lokaci yayi da yakamata ace Babban Yarima ya koyi amfani da Takobi koh dan kare kai daga farmakin maƙiya, musamman da ya kasance yana da ƙira da sura irin ta gwarzayen jarumai" ya ƙarashe yana kallon ZEEYAD cikin murmushi.

Kai sarki ya jinjina cike da farin cikin abinda sarkin yaƙi yace "Nan yace kayi gaskiya, aje a fara shirye-shirye zuwa gobe ku fara, Yarima wannan ne dalilin da ya sanƴa ni kiran ka nan dafatan zaka so hakan, sannan zakayi biyayya ga abinda na buƙata."

Miƙewa tsaye ZEEYAD yayi ya kalli sarki yace "Listen Old Man....i mean your Highness i don't want to do this faɗa da makami baya cikin tsarin rayuwa ta."

"Ai kuwa dai yakamata ace ka sanƴa ta a matsayin ka na wanda ya fito daga gidan Sarauta irin wannan" cewar ɗaya daga cikin mutanen wurin wanda shima daga gani babban muƙami yake dashi a fada.

"Wait, i don't understand i guess kakannin mu ne sukayi faɗa da makami a dah, but yanzu duniyar ta cigaba and akwai zaman lafiya, what do i need a sword for?."

"No Son, al'ada ce ta wannan MASARAUTA tamu duk wani yaro a gidan nan toh lallai ya zama dole ne a fara koya masa faɗa da makami tun daga ƙaramin sa, sauran yaran sun daɗe da fara koya kaida YAZEED ne yanzu wadanda za'a fara koyawa wannan karon, am sure you can do it."

Shiru yayi yana kallon mai Martaba ɗin _"Mai wannan mutumin ke nufi ne, ba dai yaƙi zai tura ni ba, i mean koh wuƙa ban iya riƙewa ba talkless of a whole sword, so yake a dawo masa da kaina cikin buhu kenan wataran idan an fita yaƙin"_ ya faɗi hakan a zuciyar sa idanun sa akan mai Martaba ɗin.

"Mai kace Yarima?."

"I..i mean zanyi magana da Grandma tukun, idan ta amince nayi then i will do it."

Murmushi mai Martaba yayi dan kuwa yasan Grandma ɗin tasa batada wani matsala sai ma guiwa da zata sake ƙarfafa masa.
"Alright Son, na baka damar kaje kayi shawara da ita ɗin" cewar Mai Martaba.

Kai ZEEYAD ya jinjina kafin yace "Zan iya tafiya?."

Kai mai Martaba ya jinjina, dan haka ba tare da ya jira yi komai ba ya juya ya fara tafiya.

Idanun sa ne suka sauƙa kan Abdulhakeem dake zaune ƙafa ɗaya kan ɗaya yana kallon sa, kauda kai ZEEYAD yayi kawai ya cigaba da tafiya yana barin cikin fadar.

Da kallo Abdulhakeem ya bisa yace _"Oh Poor ZEEYAD, babban Yarima da kansa ace baisan yadda ake sarrafa takobi ba, what a waste"_ ya faɗi hakan a zuciyar shi.


********************


________Fitowar sa da ta gani daga cikin fadar ne ya sanƴa ta saurin mara masa baya, ba tare da yasan tana biye dashi ɗin ba.

Har part ɗin Grandma sukaje tana biye dashi, everything about him burge ta yake, ina ma yace yana sonta yace zai aure ta,da kuwa she will be the most happiest girl on the planet.

Murmushi tayi kafin kuma ta kira sunan sa "Akhi" daidai lokacin da zasu shige cikin falon Grandma ɗin.

Tsayawa yayi yana mai tsuke fuska ba tare da ya juyo ya kalle ta ba.

Ƙarasowa tayi wurin sa tana kallon sa.

Juyowa yayi yana sauƙe idanun sa kan kyakkyawar fuskar ta dake fidda murmushi, tabbas kyakkyawa ce sosai, haka ma halayen ta, but hakan ba zai ruɗe shi ya faɗa tarkon sonta ba.

Kauda idon sa yayi daga kanta yana kai hannu yayi knocking ƙofar falon.

Ba'a jima ba wata baiwa ta buɗe dan haka gaida sa tayi ba tare da ya tanka mata ba ya shige ciki yana tambayar ta inda Grandma ɗinsa take.

"Tana chan ɗakin ta tana karatu" ta basa amsa.

Kai kawai ya jinjina kafin ya nufi hanƴar stairs.

Tsuke baki tayi ganin bai kula ta ba, kafin kuma ta samu wuri ta zauna.

A bakin ƙofar ɗakin Grandma yayi knocking tare da kiran sunan ta.

"Shigo mana Boy" yaji ta faɗa.
Wani irin farin ciki ne ya lullu6e masa zuci dan haka tura ƙofar yayi ya shiga bakin sa ɗauke da sallama.

Zaune ya ganta kan couch hannun ta riƙe da littafin addini tana karantawa.

Zuwa yayi ya zauna kan sofa yana ɗaura kansa kan ƙafafun ta yace "I miss you Grandma."

"Kai ɗan nan kaji tsoron Allah, ba da safen nan ka bar nan wurin ba?."

Murmushi yayi yace "Am serious Grandma, Old Man ne ya kira ni."

"Kul nace ka daina kiran sa hakan koh?."

"Am sorry ina nufin mai Martaba."

"Uhum, i hope kunyi spending good time da juna?."

"No there is nothing good a abinda ya sanƴa sa kira na, he wants me to learn yadda ake faɗa da takobi."

"Masha Allah, abinda na daɗe inason nayi maka magana akai kenan."

Ɗagowa yayi yana kallon ta yace "Seriously?."

Kai ta jinjina masa tace "Kwarai kuwa."

"You mean kinason na koyi yadda ake faɗa da takobi?."

"Sosai ma kuwa, ai shine zai nuna kai ɗin cikakken jarumi ne."

Murmushi yayi yace "All right, zan koya since kema kina so."

Murmushi tayi tana shafa sumar kansa tace "Muje mu na dafa maka favorite ɗinka yau, nasan bakayi breakfast ba."

"Seriously Grandma, i will love to have it."

"Kwarai kuwa, tashi muje" ta faɗa tana ɗaga kansa, kafin su tashi su fice daga ɗakin.

Sauƙowar su ya sanƴa Jalilah dake zaune.saurin miƙewa tsaye tana kallon su cikin murmushi dan kuwa, soyayyar dake tsakanin sa da Grandma ɗinsa ba ƙaramin burge ta yake ba.

Da sauri ta ƙarasa wurin su tana faɗin "Grandma, ina kwana?."

Cikin murmushi Grandma ta amsa mata da "Kin tashi lafiya ƴar albarka, ya kike?."

"Lafiya ƙalau Grandma, ya ƙarfin jikin ki?."

"Alhamdulillah" ta faɗa tana samun wuri ta zauna.

ZEEYAD ma zama yayi kafin yace "Grandma, kin zauna baki kawomin breakfast ɗin ba."

"Mai kake ci na baka na zuba?, gashi chan a dining Jalilah taimaka ki ɗauko masa."

Da "Toh" ta amsa tana zuwa ta ɗauko kulolin abincin tare da jerewa a gaban shi.

"Toh maza sauƙa kaci" cewar Grandma.
"Grandma, bakiyi serving ɗina ba fah" ya faɗa cikin ɗaga gira ɗaya sama.

"I will serve you" cewar Jalilah tana kallon sa cikin murmushi.

"Grandma please" ya faɗa yana ignoring maganar Jalilah ɗin.

Sosai taji babu daɗi a zuciyar ta, but sam bataji wani haushi sosai ba, dan kuwa bata tunanin akwai abinda zaiyi da zai bata haushi sai ma ya burge ta.

"Jalilah dear,zo ki sanƴa masa abincin kinji?."

Cike da jindaɗi ta jinjina kai tana zuwa ta zauna tare da ɗaukar plate ta shiga serving ɗinshi.

Sosai ya sake tsuke fuska, dan kuwa baiga dalilin da zai sa ace yarinƴar nan ce zatayi serving ɗinsa abinci ba, he wonders ma idan turo ta akayi tayi poisoning abincin sa dan yaci ya mutu "That won't work on me" ya faɗa yana kallon ta.

Ɗagowa tayi suna haɗa ido tace "What?."

Tunawa yayi ashe ba'a zuci yayi maganar ba nan yayi saurin yatsine fuska yana kauda kai ba tare da ya bata amsa ba.
Miƙa masa plate ɗin abincin tayi tace "Here."

Da kallo yabi abincin kan Plate ɗin kafin kuma yace "Ajiye."
Ajiyewa tayi tana komawa gefe ta zauna tana cigaba da kallon shi.

Spoon ya ɗauka yana kallon abincin, yayin da kuma yake kallon ta ta ƙasan ido _"She looks innocent, she can't poisoned someone's food"_ ya faɗi hakan yana ƙoƙarin kai abincin bakin sa sai dai yana tsoro.

_"Yeah, i know what to do, i will asked her to join me, then nan ne zan tabbatar ta sanƴa guba cikin abincin kokuwa."_

Gyaran murya yayi yace "Hey."
Duk kallon sa sukayi itada Grandma nan yace "Would you mind joining me?" ya faɗa yana kallon ta.

Murmushi tayi irin abin ya bata mamaki sosai ɗinnan nan tace "Of course i would love to, amma kaci tukun actually bana jin ƴunwa."

_"That's it"_ ya faɗa yana yi mata wani irin kallo.

Saurin sunkuyar da kai tayi tana murmushi, she can't believe yau ZEEYAD ne ya gayyace ta cin abinci tare dashi, what a great day for her.

"But i insist" ya faɗa cikin 6ata rai.

Kallon sa tayi kafin ta kalli Grandma, nan Grandma tace "Come on Jalilah kizo mana kuci."

Murmushi tayi cike da jin kunƴa kafin kuma ta tashi daga inda take tana zuwa ta zauna gaban abincin tare da ɗaukar cokali ɗaya.

Kallon ZEEYAD dake kallon ta tayi kafin kuma tayi saurin sunkuyar da kai tana kai cokalin ta ɗebi abincin tare da kaiwa bakin ta.

Murmushin ta mai ƙara mata kyau tayi tace "Uhm, abincin yayi daɗi sosai."

_"What?"_ ya faɗa a zuciyar sa yana kallon ta lokacin da ta kai cokali na biyu.

_"She is actually eating"_ ya sake faɗa.

"Boy kaci abincin mana" cewar Grandma.

"Yeah kokuma na cinƴe ba" cewar Jalilah cikin murmushi.

Da kyar ya kai cokali ya ɗebi kaɗan tare da yin bismillah yana kaiwa bakin sa.

Idanu ya lumshe lokacin da yaji wani irin daɗi ya ziyarce shi.

Har dai ya kai cokali na uku yaga babu abinda ya same

Please Login or Register in order to submit comment