Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Hafeezah bata ƙaunar ta da kai, hakan ya sanƴa ta tilasta maka wurin auren ƴar aminiyar ta."

A hankali YAZEED ya jinjina masa kai.

"Tell me, mai tace zatayi maka muddin baka auri ƴar wurin aminiyar tata ba?."

Shiru YAZEED yayi ya kasa basa amsa, ajiyar zuciya mai Martaba ya sauƙe yana mai mamakin hali irin na Hafeezah, koh ba'a ce dashi komai ba yasan ta tilastawa ɗan nata tare da ɗaukan masa alwashin wani abu muddin baiyi abinda tace ba.

A hankali ya furta "Alright, you will Marry them all, ka cika alƙawarin ka na ganin cewa ka kwatanta adalci a tsakanin nasu, yin hakan zai sanƴa Allah ya taimake ka ya kuma kawo maka sassauci a rayuwa, kayi ƙoƙarin ganin ka rabu da mahaifiyar ka lafiya wurin yin abunda ta umurce ka muddin ba wai ya sa6awa doka da addini bane."

Kai ya jinjina cikin raunanniyar muryar sa yace "Insha Allah Abhi."

"Kaje ka kira wo ɗan uwanka, da akwai abubuwan da nakeson tattaunawa daku yanzu."

Miƙewa YAZEED yayi daga zaunen da yake cikin girmamawa ya amsa mai Martaba kafin ya fice daga fadar.


**************************


*WASHE GARI*


_______Zaune DEENAH take jugum, tunda taji labarin dangin ZEEYAD na hanƴar zuwa tambayar hand in marriage ɗinta take jin abin kamar almara, she can't believe, dah ace shi ya faɗa musu ba Grandma ba dah ba zata ta6a yarda ba, mamaki take why yake cikin eager ɗin mallakar ta da wuri haka.

Shigowar Jafar ɗakin ya sanƴa ta ɗagowa tana kallon sa har ya ƙaraso kusa da ita ya zauna.

Murmushi yayi mata kafin yace "I thought zan zo na same ki cikin farin ciki, coz mafarkin ki ya kusa zama gaskiya, atlast ZEEYAD is gonna be your Husband, no more cries, no more being depressed, no more over-thinking, sai kice Alhamdulillah."

Rungume sa tayi hawaye na biyo mata ƙunci, sosai takejin ta fara kewar su tun yanzun, sam batason yin nesa da family ɗinta, yanzu kuma fah tafiya zatayi kenan zuwa gidan zaman ta na kanta wanda ita ma zata tara nata future Family ɗin, sosai takejin wani irin kewa na dabaibaye mata zuciya.

Ɗan dariya Jafar yayi yace "Toh tun ma basu ƙaraso anyi maganar ba kike kuka, ranar da zasu tafi dake kuma fah ya zakiyi?."

"Ba sai na fasa bin su ba" ta faɗa cikin muryar shagwa6a.

"Well ai kuma bamu isa mu hana su tafiya dake ba, coz kin riga kin zamto ɗaya daga cikin family ɗinsu."

"Nidai ku kaɗai ne Family ɗina" ta faɗa cikin ɗagowa tana share hawayen ta.

Dariya yayi kafin yace "Yeah koh kin tafi ɗin we will still be family forever."

Murmushi tayi tace "Koh wane sati sai nazo na ganku na tafi."

Idanu ya waro kafin yace "Ai koh gari ɗaya muke ba zaki dinga zuwa bayan sati ba bale kuma chan Egypt."

Baki ta turo tana ƙunƙunai ƙasa-ƙasa.

Wayar sa ya ciro cikin aljihun sa kafin ya shiga ta whatsapp nasa ya binciko wani number ya shiga, hotunan kayan ɗaki da falo aka turo masa masu kyawun gaske da tsada, miƙa mata wayar yayi yace "Ki za6i wanda yayi miki anan."

Amsar wayar tayi ta shiga duddubawa, ɗagowa tayi ta kallesa tace "Wadannan kayan ɗakin sai kace wata ƴar gwamna, basuyi tsada ba kuwa?."

"Kinga kuɗin su ne da kike cewa sunyi tsada?" ya faɗa yana kallon ta.

"Amma ai daga gani zasuyi tsada fah Yaya."

"Babu ruwan ki da wannan just chose wanda yayi captivating mind naki."

Sosai ta shiga kallo kafin kuma ta ɗago tana kallon sa tace "Gaskiya ni ba zan iya za6ar mai kyau ba, ka za6a min da kanka" ta faɗa tana miƙa masa wayar.

Murmushi yayi ya amsa kafin yace "Alright duk wanda kikaje kika gani koh da baiyi miki ba kada ki ba kowa laifi."

"Ai nasan zaka za6a min mai kyau sosai."

"Alright, anjima su Mami zasu zo a fara shirin tar6an baƙin, sai kema ki shirya kafin nan" ya faɗa yana miƙewa tsaye.

"Insha Allah" ta bashi amsa.

Ficewa yayi daga ɗakin kafin ta kwanta flat kan bed ɗin fuskar ta na fuskantar sama.

Sosai takejin ta wani iri duk jikin ta yayi sanƴi.

Ƙarar shigowar text message ne ya sanƴa ta jawo wayar tata tare da buɗe text ɗin nasa tana karantawa.

Murmushi ta saki tana ajiye wayar, kafin ta tashi ta fice daga ɗakin.


**************************


________Sosai Grandma ke shirye-shirye kai kace ranar bikin ne ya gabato.

Kayayyakin da ta haɗawa DEENAH da JALILAH kama daga na sanƴawa, takalma, ƴan kunne dasu awarwaro wadanda duk suka kasance na Gold ne masu matuƙar tsada, da dai dukkanin wasu abubuwan da ake buƙata idan za'a kai tambaya kamar yadda yake a al'adar MASARAUTAR tasu.

Shi dai ZEEYAD da idanu kawai yake bin ta dukkanin wani abu da zatayi dan kuwa ta haɗa kayan ta ta ƙeƙashe tace da ita za'a je tambayar auren DEENAH, tun mai Martaba bai yarda ba har yazo ya yarje duba da yadda ta takura.

Sosai ta gama kintsawa tare da sanƴawa aka fidda dukkanin wadanda yake na DEENAH ne kasancewar mota na jiran ta zasu wuce airport.

"Toh mukam mun wuce Nigeria tambayo auren matar da Boy zai aura, dan haka ku tabbatar kun kula min da gida kada naga wata dameji koh abinda ba shi ne ba, idan kuwa ba haka ba rai zai 6aci dan kuwa ba wani babban aiki bane a wuri na na fatattaki mutum yaje chan yaƙare tunda ba zai yimin abinda raina ke so ba" ta ƙarashe cikin kallon Bayin dake yin hidima a side ɗin nata kasancewar tara su da tayi a layi.

Duk amsa mata sukayi da ba za'a sami wata matsala ba, kafin tayi hanƴar ficewa.

Saurin mara mata baya ZEEYAD yayi yana faɗin "Grandma."

Dakatawa tayi tare da juyowa tana kallon sa tace "A'a kaga kada ka dameni da wasu ƙananun maganganu nasan abinda zaka faɗa bai wuce kace a aura maka DEENAH a taho maka da ita ba, kada ka damu indai hakan kakeso kamar anyi an gama ne, ka sanni da nacin tsiya koh mutum baiyi niyyar abu ba sai na takura shi yayi, sai dai idan banyi niyya ba."

Murmushi yayi yace "Grandma ni ba wannan maganar nakeson yi miki ba, she refused to answer my call since day before yesterday, please idan kinje talk to her ta ɗau kira na."

"Yoh toh dama tayaya zata ɗau kiran ka, kana neman rabo ta da dangin ta, nikam kaga tafiya ta ma ƙarasa sauran maganar a waya, kasan zamuyi ne mu dawo zuwa gobe sabida zuwa tambayo na ɗan uwanka."

Bai tanka mata ba ya mara mata baya har zuwa motar ya buɗe mata ta shiga, sallama suka sakeyi kafin driver yaja motar su wuce.

*************************

_______Sosai gidan ya bazu da ƙamshin girki wanda ya gauraye da ƙamshin turaren wutan da ya gauraye ilahirin gidan baki ɗaya.

Sosai duk sukayi busy wurin shirin kar6ar baƙin, Umma kam ta kasa zaune ta kasa tsaye, tama rasa inda zata sanƴa kanta wai yau ita ce zata aurar da ƴar ta izuwa wata MASARAUTA, MASARAUTA ba ɗaya daga cikin Nigeria ba, sosai zuciyar ta ke cike da farin cikin da ba zata iya kwatantawa ba, bama ita kaɗai dukkanin su mutanen cikin gidan.

Sosai suka kammala komai da shirin su tun kafin su ƙarasowar baƙin.

Mijin Mami kuma mahaifin su Anty Khadija shine wanda zai tsayawa DEENAH a matsayin Uba, dan haka shima tunɗazun ya iso da abokan sa na amana na kusa dashi, suna jiran isowar baƙin.

DEENAH kuwa sosai tasha dark blue ɗin Laffaya mai tsada, batayi wani kwalliya sosai ba, amma kyawun da tayi ba'a cewa komai.

Sosai takejin zuciyar ta ta kasa samun sukuni, wai yau ita za'a zo tambayar auren ta daga wata ƙasar, she can't believe it.

Su Anty Khadija ne ke ta kwantar mata da hankali.

************************

_______Tundaga kwaltar mashigar ungwar tsala-tsalan baƙaƙen motocin wanda aƙalla zasu kai ashirin da biyar koh fiye da haka ne suke ta kunno kai cikin layin gidan su DEENAH ɗin, inda motar Jafar ce a gaba wanda dai da alamu shine keyi musu jagora.

Mutane ne suka tsaya kallon motocin suna mamakin wane mai ragamar mulkin ne wannan haka, basu tashi shiga mamaki ba sai da suka ga an wangale gate ɗin gidan su Jafar wasu daga cikin motocin sun kutsa kai ciki, ga kuma securities kaca-kaca everywhere kamar wanda ruwan su akayi kowanne riƙe da bindiga a hannun sa sun sha baƙaƙen shades.

Anty Khadija da Amirah dake leƙe ta ɗakin DEENAH ne suka buga wani irin tsalle cike da murna suna tafawa.

"Ke wallahi harda sarki da gwamanan garin nan, kutt DEENAH ba ƙaramin goshi kikayi ba, inalillahi" faɗin Amirah cike da tsantsar murnar da take ciki.

"Ke dallah ki sassauta muryar ki kalan kisa su jimu, mu shiga uku yadda suke tare da sojoji ɗinnan" faɗin anty Khadija tana sake leƙa kanta.

"Sun shigo, sun shigo, ku tashi mu fita" ta faɗa tana ɗaukar gyalen ta.

Amirah dake leƙe har yanzu ne tace "Ke ni wallahi nama kasa ganin fuskar baban ZEEYAD ɗin wadannan masu bindigogin sun tare shi, hegu masu ƙatiƙatin kai."

DEENAH dai shiru tayi tana kallon su jikin ta na sake yin sanƴi sosai, hannun ta ma dakyar take iya ɗaga shi.

Muryar Grandma taji a falon su hakan ya sanƴa ta waro idanu tana faɗin "Har da Grandma aka zo."

Su Anty Khadija basu tsaya bata amsa ba, sukayi hanƴar waje da gudu har suna tunkuɗe juna wurin fita.

Dariya suka bawa DEENAH dan haka murmusawa tayi dan kuwa yadda takejin ta ɗinnan bata tunanin zata iya buɗar haƙora tayi dariya.

"Masha Allah, Masha Allah, Ina jikar tawa take ne dukkanin ku na ganku amma ita da yakamata na fara ɗaura idanu akanta ban ganta ba."

"Tana cikin ɗakin, kizo na kai ki" cewar Amirah cike da zumuɗin ganin Balarabiyar tsohuwa a gaban ta sai kallon Grandma ɗin take tayi.

Grandma da sauri ta mara mata baya tana faɗin "Mai kuma kike jira ƴar nan, maza muje ki kaini."

Tun kafin su ƙaraso Amirah ta fara doka kiran DEENAH, DEENAH jin muryar Grandma ya sanƴa ta saurin jan Laffayan jikin ta yana rufe mata fuska.

Shigowar su ɗakin Grandma da fuskarta fal farin ciki ta ƙaraso kan DEENAH tana faɗin "Masha Allah dake ƴar nan, tun kafin naga fuskar ki na san ba bala'in kyau kikayi ba, ta faɗa tana zama kusa da ita tare da rungumo ta.

Lafewa DEENAH tayi jikin Grandma ɗin tanajin wani irin sanƴi a cikin zuciyar ta.

"Toh dai ni fah ba Boy bace bale ayimin rowar fuska, buɗe kyakkyawar fuskar taki na gani mana ƴar nan."

Ɗagowa DEENAH tayi daga jikin ta tana sake jan mayafin nata.

"Toh ai shikenan, inaga dai so take na buɗe da kaina na gani" cewar Grandma tana tashi tsaye tare da sanƴa hannu ta yaye rufin kan DEENAH ɗin, cupping fuskar ta tayi cike da farin ciki tare da bata kiss a goshi da ƙunci tace "Masha Allah, what a beautiful angel you're, haƙiƙa Boy ɗina ba ƙaramin za6e ya iya ba, Allah yayi wa rayuwar ki albarka ƴar nan."

Murmushi DEENAH tayi tana sadda ƙasa cike da kunƴar Grandma ɗin.

Kallon su Umma Grandma tayi tace "Kuyi haƙuri ku ɗan barmu da jikar tawa, akwai abubuwan da nakeso mu ɗan tattauna da ita ne."

Cikin sakin fuska Mami tace "Ai bakomai, ku wuce muje" ta faɗa tana riƙo Amirah da tunɗazu ta kasa rufe bakin ta suka fice dukkan su.

************************

_________Gaf da Magrib suka gama abinda ya kawo su, inda mai Martaba ya nemi ganin surukar tasa, kan DEENAH a ƙasa Umma na riƙe da ita suka shigo cikin falon baƙin dake cike daf da manƴan mutanen cikin garin Sokoto ɗin, ciki kuwa har da Sarki da Gwamnan wannan garin.

A gaban sa DEENAH ta durƙushe tare da gaida sa cike da girmamawa, murmushi mai Martaba yayi yana kallon ta, a hankali ya furta "masha Allah, she will surely make a great and beautiful Queen" ya ƙarashe cikin dariyar manƴan ta sauran mutanen na taya shi.

Murmushin Farin ciki Umma ta saki tana sadda kai ƙasa

Kyauta mai tsokan gaske mai Martaba yayi mata, after all abubuwan da suka taho dashi, bama shi kaɗai ba hatta mutanen da suka zo tare dashi sai da sukayi wa DEENAH kyauta, a cewar su tunda marainiya ce ita baikamata iyayen ta su kashe kuɗi wurin yi mata duk wani kayan ɗaki da abubuwan da za'a kashe a auren ba. _(Nikuwa dai nace sabida dai kunga mai Martaba ne yasa kuke son nuna gwanin ta, idan yana da wasu ƴaƴan kuyi shisshigin haɗa su da naku sabida kunga random girl kamar DEENAH zata yi aure gidan sarautar wata ƙasar ina ga kuma ƴaƴan ku😁, koh dayake Ayaan yana nan🥲)_

Umma harda hawayen farin ciki tayi, godiya kuwa tayi musu shi yafi cikin maliya, ta rasa inda zata tsunduma ranta tsabar farin ciki, bata ta6a tunanin zata yi witnessing irin wannan rana a rayuwar ta ba, sai yau gashi haihuwar DEENAH is big a blessing ba wa ita kaɗai bama ga dukkanin family ɗinsu.

DEENAH ma kukan take a hankali, albarka duk suka sanƴa mata kafin su fara shirin tafiya.

Duk tare suka bar gidan da mijin Mamy, Grandma kuwa cewa tayi anan zata kwana tunda sai gobe ne tafiyar tasu, idan yaso sai a biyo a ɗauke ta kawai su wuce.

Rungume DEENAH Umma tayi cike da farin ciki, hawaye kawai take tana sake sanƴa mata albarka a cikin zuciyar ta.

Duk wucewa sukayi tare da yin sallahr Magrib da ake ta kiraye-kiraye, sune basu samu zama ba har sai bayan anyi Isha'i.

Sosai suka ji daɗin zama da Grandma inda ta baje sai labari take basu da wanda aka tambaye ta da wanda ba'a tambaye ta, su Amirah kam dama abin nema ya samu ne, ita ke ta biyewa Grandma ɗin, sauran kuwa nasu dariya ne kawai.

*********************

______Washe gari da sassafe driver yazo ɗaukar Grandma, sai masifa take wai ai yazo da wuri, sai da ta tabbatar ta gama kintsawar ta tsaf kafin su kama, hanƴa bayan sunyi sallama dasu Umma sosai kamar ba zasu rabu ba.

Grandma bata daɗe da tafiya ba Alhaji Lawal mijin Mami ya iso gidan, domin tattauna batun da sukayi jiya da mai Martaba ɗin.

Dan haka dashi da Umma da Mami ne suka wuce falon baƙi dan tattauna komai achan ɗin.

"Alhaji sati biyu fah kace, ai yayi wuri yaushe za'a samu isasshen lokacin komai bayan kasan auren al'adar mu ta Hausa Fulani, da akwai wasu shirye-shiryen da yakamata ayi wa amaryar kafin wannan lokacin, yaushe zamu gama komai cikin sati biyu" faɗin Mami bayan mijin nata ya gama yi musu bayanin yadda sukayi da mai Martaba.

"Toh ya muka iya Hajiya, kin dai ga ba ƙananun mutane bane ba, babu ta yadda za'ayi na iya yi musu jayayya da wannan alfarmar da suke nema, dan hakan ne ya sanƴa shi Sarkin tasowa tundaga ƙasar da yake yazo shi nan, toh ya kike tunanin kuma zance masa A'a, baya ga haka kuma ai ana barin halak dan kunƴa irin ɗawainiyar da suka iyo wanda hatta ni kaina naci moriyar hakan ai kaɗai ya isa mu amince da batun su, yanzu dai ku gama duk wani abu da zakuyi cikin sati biyun nan, nasan idan kuka haɗa ƴan dabarun ku na mata komai zai daidaita."

Ajiyar zuciya ta sauƙe tace "Toh shikenan, Allah ya nuna mana ranar da cikin rai da ƙoshin lafiya da alkhairi."

"Shine kawai addu'ar da yakamata muyi dama, yanzu kije ku sanar wa da ita yarinƴa tasan abinda ake ciki, nasan suma ba zasu rasa shirye-shiryen su na kyalkyali banzan ƴan matan zamani ba."

Dariya duk sukayi kafin Umma da duk jikin ta yayi sanƴi tace "Aikuwa dai kam."

"Masha Allah, ni bari na wuce wurin aiki dama nazo ne na sanar daku yadda mukayi dasu, idan da akwai wasu abubuwan da kuke da buƙata sai ayi gaggawar sanar dani."

"Insha Allah" duk suka amsa suna miƙewa tsaye, inda shi ya fice su kuma suka dawo cikin ƙaramin falo.

Tunda aka sanar da DEENAH auren nasu sati biyu aka sanƴa ta sake shiga damuwa, babu abinda take sai sharce hawaye a 6oye dan kuwa wani irin kewar mahafiyar ta da ɗan uwanta ne suka lullu6e mata zuci, she can't believe zata koma cikin wasu family ɗin ta barsu, sam batason kan family ɗinsu ya wargazu, su biyu kaɗai Umma ta mallaka Jafar namiji ne ba zama yake a gida ba musamman ma da ya kasance yana da aikin yi, zai sauran saura Umma kaɗai babu mai ɗebe mata kewa koh taya ta hira idan ta dawo daga wurin aikin ta ita ma, sosai gidan zaiyi mata babu daɗi ita kaɗai, ta san abinda Umma keji a yanzu yafi wanda takeji a cikin zuciyar ta, bata ƙi ta dawwama tare da Ummar tata har abada ba, sam ba zata iya jurar ganin ta cikin halin kewa ba, tasan sosai hakan zaiyi affecting ɗinta, dah kamar tana da wasu ƙannen ne ma da sauƙi, but duk tausayin Umma ya cika mata zuciya, rayuwar Family ɗinsu zai zamto babu daɗi ba kamar ta dah ba, shima Jafar yanayin aure shikenan kafin Umma ta sanƴa sa a ido tasan zai ɗan dinga jan lokaci dukda tasan yayan nata ba zai ta6a wofantar da mahaifiyar su ba, but tanajin babu daɗi sosai da sosai cikin zuciyar ta, babu abinda take sai kallon Umma da ta lura jikin ta a matuƙar sanƴaye yake, dariya da murmushin da take kawai ta yaƙe ce, but da akwai damuwa cikin zuciyar ta.

Tashi tayi ta bar musu falon ba tare da tabi ta kan kayan alatun da suke dubawa ba, wanda mai Martaba da Grandma suka kawo mata.

Ɗakin ta ta koma ta sha kuka sosai kamar babu gobe, sai da tayi mai isarta kafin ta janƴo wayar ta.

Missed calls ɗinsa ta gani dan haka dialing number ɗin tayi, ringing biyu yayi ya katse kiran tare da kiran ta.

Ɗagawa tayi tana kaiwa kunne tare da yin sallama.

"Habibty" ya faɗa cikin sanƴin muryar sa.

"I want to discuss something important with you please" ta faɗa cikin muryar sabon kukan dake zuwan mata.

"Babe are you Okay, what's wrong with you, wa ya ta6a ki?" ya faɗa cikin ɗan ruɗewa da jin kamar kuka take.

Kai take girgiza masa kamar wanda yake gaban ta tace "Dan Allah kada ka raba ni da Umma ta da Yaya Jafar" ta faɗa cikin shessheƙa.

"Babe ba zan raba ki dasu ba, what made you think of that?."

"Banason yin nesa dasu, tun yanzu nakejin kewar su, banason nayi nesa dasu."

Huci ya fesar yace "Babe..."

"Please i beg you kada kacemin a'a."

"Listen please Baby, ki kwantar da hankalin ki and stop crying ba zan ta6a raba ki dasu ba, they are your family."

"But you're taking me far away from them."

Cikin kwantar da murya da rarrashi yace "Baby, ki kwantar da hankalin if that is the case then zaki dinga zuwa gida ganin su, are you Okay with that."

Kai ta jinjina masa kafin tace "Kullum koh?."

Ɗan waro idanu yayi yana sosa goshi kafin a hankali yace "Yeah, koh da after every 1hour kikeso, please stop crying, Okay?."

"Yes" ta faɗa tana goge hawayen ta.

Murmushi yayi yace "Thats my baby."

Murmushi tayi tana sadda kai ƙasa.

A haka suka cigaba da hira cike da soyayya da ƙaunar junan su.


***********************

*RANAR ƊAURIN AURE*




*Yawan Comment, Yawan Typing*





*MHIZZ JIDDHERR..............✍🏽*
[8/25, 11:33 PM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D*
```[The Abandoned Prince]```





*NA*
*JIDDAH BINT MUHAMMAD*





*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*







*047...*




_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_



*Wannan shafin kacokan naku ne ZEEYAD FANS CLUB😍🤗, bama ku kaɗai ba dama duk sauran mabiyan littafin ZEEYAD, alkhairin Allah ya isar muku aduk inda kuke, haƙiƙa addu'a da sharhin da kukeyi min a kullum shine sanadiyyar ƙarin ƙarfin guiwa ta, Allah ya biya muku dukkanin buƙatun ku na alkhairi🤲🏽🥹❤️*



_________Dandazon Mutane ne cike maƙil a babban Masallacin gidan sarkin Sokoto, duk inda ka waiga manƴa-manƴan motoci kawai kake gani kai kace auren ƴar gidan gwamna koh sarkin ake ɗaurawa sabida irin manƴan mutanen da suka halarci ɗaurin auren.

Ana idar da sallahr Jumma'ah, aka nemi awallin kowane ɗaya daga cikin su, inda Dadyn Khairat ya kasance awwalin ZEEYAD, Abban su Amirah kuma na DEENAH.

Cikin ƙanƙanin lokaci aka ɗaura auren *ZEEYAD IBN ABBAS* da kuma amaryar sa *MADEENAH ABDULSALAM* akan sadaki dubu Hamsin kacal kamar yadda Abban su Khadija ya buƙata sabida aure da sadaki kaɗan yafi albarka.

Wata iriyar nannauyar ajiyar zuciya ZEEYAD dake sanƴe cikin shigar fararen kaya irin tasu ta larabawa ya ɗaura brown alkyabba mai matuƙar kyau da tsada akan sa, yanajin wani irin farin ciki da annashuwa na ratsa kowacce saƙo na jinin jikin sa, yana mai nana ta kalmar Alhamdulillah tare da sake miƙa dubbun godiyar sa ga Allah na cika masa burin sa da yayi a cikin zuciyar sa.

Dafa kafaɗun shi Sadeeq dake kusa dashi yayi shima cike da tsantsar murna a hankali yace "Finally, Congratulations bro."

Murmushi ZEEYAD ya saki tare da jinjina masa kai dan kuwa baya tunanin zai iya buɗar baki magana sabida irin farin cikin da yake ciki.

Albarka manƴan wurin suka sanƴa masa da amaryar tasa tare da sanƴawa rayuwar auren su albarka, mai Martaba kam dama bai zo dan kuwa zai tsaya ne a wurin ɗaurin auren YAZEED dan nuna masa ƙauna da kulawa shima.

Mutane ne suka fara fitowa bayan an ɗaura auren, Jafar ne ya ƙaraso gun ZEEYAD tare da rungume sa a hankali yake faɗin "I know you're a good Man with a kind heart, and i know ba zakayi abinda bai dace ba, i trust you completely banida wani tantama akanka, i know DEENAH tayi dacen miji, please take a very good care of my sister fiye da yadda ka nuna mata a dah, don't let her shed tears da sunan kewar mu, ita ɗin amana ce a gareka and i do hope ka riƙe amanar ta da kyau" ya faɗa yana ɗagowa cikin sanƴin jiki dan kuwa sosai yakejin zaiyi kewar ƴar ƙanwar tasa, she means alot to him and gashi yau zatayi nesa dashi zuwa wani wurin, wanda bai kuma sanin taƙaitaccen ranar sake haɗuwar su ba, ji yake tamkar su koma rayuwar su ta dah lokacin da suke ƙanana, baisan yadda zai iya misalta yadda yakejin kewarta cikin zuciyar sa ba.

Murmushi ZEEYAD yayi cikin sanƴi da tausayin Jafar ɗin ya dafa kafaɗun sa yace "I promise to take good care of her fiye da yadda zan baiwa kaina kulawa, trust me."

"I trust you" ya faɗa kafin ya ɗaura da faɗin "We should get going, don't you wanna see your Bride?."

"Ofcourse he does, he is very eager ma kuwa" faɗin Sadeeq cikin ɗan dariya.

Duk jerawa sukayi suka fito kamar wasu ƙuda haka securities da fadawa suka mara musu baya har izuwa motocin su, kafin su jera duka zuwa gidan su amarya.


*************************


_________Sosai ta haɗe cikin tsadaddiyar doguwar farar wedding gown da yake ja mata har ƙasa, kyawu irin wanda DEENAH tayi a wannan rana ba zai kwatantu ba, duk da kuwa fuskar ta a matuƙar tsuke take babu walwala kamar yadda zakaga wasu amaren amma hakan bai hana irin kyawun da tayi fitowa

Please Login or Register in order to submit comment