Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da sauri tana tsane jikin ta.


Boooomm taji ta bugu da mutum inda wayar dake hannun sa ta faɗi ƙasa.


Da sauri ta sunkuya ta ɗago masa wayar tana faɗin "Sor.."


Maganar ta ce ta carke lokacin da idanun ta suka sauƙa cikin nashi.


Amsar wayar yayi yace "It's alright" ya faɗa yana wucewa.


Daskare wa tayi anan wurin ba tare da ta iya motsa koh da ƴar yatsar ta bace................





*Yawan Comment, yawan typing*





*MHIZZ JIDDHERR............✍🏽*
[8/30, 9:32 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D*
```[The Abandoned Prince]```





*NA*
*JIDDAH BINT MUHAMMAD*





*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*





*016...*




...............Manƴan idanun ta da ta waro tun sadda ta haɗa idanu dashi ne ta kasa ƙiftawa har yanzu, sannan kuma ta kasa motsa koh da ƴar yatsar ta ne, haka nan ta tsaya in shock kamar wacce tayi sumar tsaye.



Tabbas shine, ta gane shi kallo ɗaya tayi masa ta gane kamannin sa, like a flash haka fuskar sa da kamannin sa suka faɗo mata cikin kwakwalwa.



"DEENAH!, DEENAH!!" cewar Anty Khadija tana girgiza ta.



A firgice ta ɗago tana kallon ta.


"Meke damun ki, bakije kin wanke bane?."



Dube-dube DEENAH ta fara ganin ya bar wurin bata gansa bane yasa ta nufar hanƴar cikin hall ɗin da gudu.



"DEENAH Stop" cewar Anty Khadija tana mara mata baya.



Tsaye DEENAH da takejin zuciyar ta kamar zata faso waje tayi a tsakiyar hall ɗin tana dube-dube, duk wanda ta gani da farin kaya kuwa sai taje ta duba fuskar sa taga koh shine.



Haka nan tayi ta yawo a cikin hall ɗin tana lelleƙa fuskar mutane cike da kiɗima, yayin da mamaki ke cike a fuskar kowa ganin yadda ta gigice ta daburce kamar wata zautacciya, nan duk kallo ya dawo kanta kuma.



Anty Khadija ce ta kamo ta tace "DEENAH miye hakan kike yi, bakiga kowa na kallon ki bane?."


"I saw him, i just saw him now" ta faɗa tana cigaba da bin mazan wurin tana leƙa fuskokin su.



Haka nan tayi ta zagaye hall ɗin baki ɗaya but bata ga ZEEYAD ba, batasan inda ya shiga ba.



Ficewa tayi daga cikin hall ɗin da gudun ta inda kowa ya bi ta da kallo Anty Khadija na mara mata baya.


Tsaye tayi ta sama stairs ɗin tana jejjefa idanun ta koh Allah zai sa ta ganshi a cikin mutanen nan.


Bata gan shi ba hakan yasa ta sauƙa zuwa hawa na uku tana duba shi bata gansa ba har ta fice zuwa waje.



Nan ma dube-dube ta fara tana waige-waigen neman sa, kamar a mafarki ta gansa yana shirin shiga motar sa da aka buɗe masa waya kare a kunnen sa.



Bata tsaya yin wata-wata ba kuma ta nufe shi cikin gudu tana kuka tare da ihun "Stop" kamar wata zautacciya.



Kafin ta isa motocin suka bar cikin hotel ɗin, DEENAH zubewa tayi tare da rushewa da kuka mai tsuma zuciya, sai a lokacin Anty Khadija tayi nasarar fitowa daga ciki ta same ta tana kuka kamar zata shiɗe.


"DEENAH, DEENAH mai ya sameki?."


DEENAH bata iya kula ta ba sai ma kuka da take tayi tana faɗin "I saw him."



"DEENAH, waye ne, waye kika gani?."


"He is the one, i saw him."


Ƙarasowa ƙawayen Anty Khadija sukayi wurin suna tambayar abinda ya faru.



"Khadija mai ya sameta?."



"Nima bansani ba, abinda nake tambayar ta kenan bata bani amsa ba" ta faɗa ita ɗin ma kamar zatayi kuka tana rungumo DEENAH jikin ta.



"Kinga mutane sun fara taruwa, mu tada ta mu bar nan wurin" cewar ɗaya daga cikin su.



Duk kama ta sukayi da niyyar tayar da ita tsaye sai dai taƙi ta bari.



"Leave me alone" ta faɗa cikin kuka.



"DEENAH, ki tashi haka nan, gida kikeson tafiya koh?" faɗin Anty Khadija.


"He is gone, i have lost him again."



"Waye kike magana wai akai?."



Da sauri ta ɗago ta kalli Anty Khadija tace "Anty Khadija, kinsan shi koh, wannan ɗinnan da kikayi min maganar sa, kinsan inda yake koh?."



"Waye, wa kenan?."


"Balarabe" ta faɗa.


"Balarabe, wane balarabe kuma DEENAH?."



"Na ganshi, na ganshi kafin na ƙaraso wurin sa kuma motocin sa sunja sun tafi, Wayyo Allah na, na shiga uku" ta faɗa cikin shesheƙa.



"DEENAH ni ban gane wanda kike magana a kai ba, waye ne shi kwatanta min shi."



"W..wani...wani ne balarabe ne, ya sanƴa farin kaya, na ganshi da zanje wanke jiki na kafin na dawo kuma ya tafi, ya tafi Anty Khadija shikenan kuma na sake rasa shi, dan Allah ku nemo min shi."



"Toh wai kodai ZEEDAN take nufi?" cewar Aisha.



"ZEEDAN kuma, a'ina zata san shi."



"Toh naga shi kaɗai ne Balarabe anan da ya sanƴa farar shadda."


"Tabbas shine" cewar Anty Khadija.


"Kina da tabbacin shine?."



"Na ga lokacin da ya fito daga corridor ɗin da DEENAH ta shiga, koh da naje na tadda ta kamar bata cikin hankalin ta seems like ta san shi kenan."


"How sure are you?."



"Ina Aisha, shiga mana page ɗinsa a instagram muga koh shi take nufi" cewar Anty Khadija.



Aisha wayar ta ta ciro tare da kunna data ta shiga instagram ɗinta.



Ƴan danne-danne tayi kafin ta miƙowa Anty Khadija wayar.



Nuna mata tayi tace "shine wannan?."



Da sauri ta amshi wayar ta shiga kallon hotunan nasa idanun ta na manƴa.



"Shi..sh..shine, shine Anty Khadija wallahi na gane shi, ba zan ta6a manta fuskar sa ba, dan Allah ku kai ni wurin shi" ta faɗa tana kallon Anty Khadija.



Kar6ar wayar Anty Khadija tayi tana maidawa Aisha abin ta nan tace "Babbar magana."



"We should locate him" cewar Aisha.



"And how do you think that is possible?, the guy is Famous he can't easily be found or seen, dan mungan shi a auren nan doesn't mean zamu iya kuma ganin sa cikin sauƙi" faɗin Anty Khadija.



"Anty Khadija ya sanni, dan Allah ku kai ni wurin sa."



"Kinga DEENAH tashi mu tafi gida."



"Dan Allah..."



"Tashi mu tafi, idan munje gida zamu nemo mafitar inda zamu samo sa cikin sauƙi" ta faɗa tana ɗaga ta tsaye.



Ficewa sukayi zuwa bakin titi, nan Anty Khadija tace "Dan Allah wata ta ɗaukomin jaka na a table ɗinda ZEEDAN ya zauna na mance shi."



Biyu daga cikin su ne suka koma suka ɗauko mata jakar kafin su tari Taxi suka shige, inda su kuma ƙawayen suka koma wurin party...........




************************




............"Toh da kuka ganshi ɗin kuma mai ya hana ku tsaida shi?" faɗin Mami.



"Mami ita ce ta ganshi, kafin kuma ta isa gareshi ya riga da ya fice, infact a table ɗaya muka zauna dashi."



Ɗagowa tayi ta kalli Anty Khadija, nan ta girgiza masa kai "Kwarai kuwa shine wanda nake faɗamiki ki ɗago ki kallesa amma kika ƙi sakin jikin ki, ashe ma shi ɗin is someone very important to you."



"Mami dan Allah ku nemo min shi idan ban basa haƙuri ba ba zan ta6a samun nutsuwa da kwanciyar hankali ba, dan Allah ku nemo min shi tunda yana cikin garin nan."


"Haba mana MADEENAH ki kwantar da hankalin ki haka nan, insha Allah za'a nemo sa da izinin Allah indai yana cikin garin nan, na kira yayanki Jafar yana hanƴar sa ta zuwa, insha Allah damuwar ki ta kusa zuwa ƙarshe, kiyi haƙuri."



Sautin kukan ta ne kawai ya cika falon inda su kuma ke ta rarrashin ta cikin son kwantar mata da hankali, sai dai koh kaɗan taƙi saurarawa.




Bayan kamar 20mins Jafar ya shigo falon bakin sa ɗauke da sallama.



Da gudu taje tana faɗawa jikin sa tana sake ƙara volume ɗin kukan ta.


Bayan ta ya hau bubbugawa cikin rarrashi amma kamar sake zuga ta yake.


Ɗagowa tayi cikin kuka tace "Yaya na gan shi wallahi na gan shi yaya."



"Wanene?" ya tambaya.



"Balarabe, wallahi na ga balarabe yaya."



Idanu ya zaro cike da mamaki yace "Balarabe kuma DEENAH?."



Saurin jinjina masa kai tayi tana cigaba da kuka.



"Jafar ƙaraso mana" cewar Mami.



Hannun DEENAH ya janƴo suna samun wuri su zauna.



Gaida Mami yayi cike da girmamawa kafin tace "Sannu Jafar, sai yanzu kake ƙarasowa?."



"Wallahi Mami ina chan wurin aiki ne."



"Toh masha Allah hakan yayi kyau sosai, ka dai ji abinda ƙanwar taka ke faɗa koh?."



"Abin da mamaki, tayaya kuma zaki ga balarabe?."



"Wallahi shi na gani yaya, gashi nan ka tambayi Anty Khadija ma ai har hoton sa ta nuna min."



"Wai dagaske?" ya faɗa yana kallon Anty Khadija.



"Haka dai tace wai shine, but kai ka san shi ai koh?."



Saurin jinjina mata kai yayi nan tace "Toh bari na dubo hoton sa ka gani."



Latsa wayar ta ta shiga yi, nan ta nemo hoton sa tana miƙawa Jafar wayar tace "Shi ne?."



Amsar wayar Jafar yayi ya shiga kallon hoton, sosai ya kalla kafin kuma ya ɗago ya kalli DEENAH yace "DEENAH wannan ne kike cewa shine balarabe?."



Kar6ar wayar yayi tana kallo nan tayi saurin jinjina masa kai tace "Eh yaya shi ne, ba ga shi nan kana gani ba."



"Come on DEENAH, wannan sam ba balarabe bane koh kama ma basuyi ba."



Sake duba hoton tayi tana girgiza kai tace "Yaya ka sake dubawa da kyau wallahi shi ne."



Amsar wayar yayi yana miƙawa Anty Khadija yace "Inaga she is just eager to see him shiyasa take ɗauka kamar shi ne, but sincerely speaking wannan ba shi bane."



Kallon Jafar kawai ta tsaya yi tana mamakin kalaman sa na cewa ba balarabe bane ta gani.



"Yaya" ta faɗa.



"DEENAH yakamata ace kin dawo cikin nutsuwar ki haka nan, this is not balarabe koh kama basuyi ba, how kike tunanin a homeless person like him can be so rich and Famous like this in just shekaru goma."



"Shekaru goma is not a just yaya, maiyasa wai dukkanin ku kuka kasa fahimta ta ne, i told you wannan balarabe ne na gani amma dukkanin ku kuna ɗaukar lamari na wasa, bakusan abinda nakeji a cikin zuciya ta ba, sai dai kawai kuyi ta bani haƙuri, i know i saw him but you doesn't seem to believe me har kana cemin ba shi bane bayan kasan shi, he is your friend back then."



"DEENAH listen to me..."


"No i won't listen, dukkanin ku babu wanda ya damu da damuwata dama kuma halin da nake ciki kullum, tunda babu wanda zai nemo min shi a cikin ku, then ni zan nemo shi da kaina" ta faɗa tana barin cikin falo ɗin ta fice waje.



"DEENAH" duk suka kira ta suna tashi su mara mata baya.



Riƙo ta Jafar yayi yace "DEENAH ki kwantar da hankalin ki, ina dai kince wannan balarabe ne koh?."



Saurin girgiza masa kai tayi tace "Amma ai kaƙi yarda dani cewa shi ne."



"DEENAH look, zan kai ki wurin balarabe but sai kinyi min alƙawarin zaki daina sanƴa damuwa a cikin ranki, nikuma nayi miki alƙawarin zan kai ki wurin sa zuwa next week."



"What, kasan inda balarabe yake?."



Shiru yayi yana kallon ta kafin kuma yace "Yeah na sani."



"What, kasan inda yake?."



"Yeah."



"Kuma baka ta6a damuwa da ka faɗamin ba" ta faɗa cike da mamaki tana kallon sa.



"Look DEENAH i will Explain everything to you, but you need to calm down, Okay?."



"I should calm down, you want me to calm down after all the pain i had went through for ten years, kasan inda balarabe yake tsawon lokacin nan amma baka damu da cewa ka sanar dani ba bayan kasan irin wahalar da nake sha a kullum, maiyasa zakayi min haka, i thought kai yaya na ne mai sona kuma mai son ganin farin ciki na, ashe ba haka bane ka san abinda zai sanƴa ni farin ciki kasan inda yake but you're keeping me away from him all this long, maiyasa haka yaya" ta faɗa cikin kuka tana ture shi daga jikin ta.



"DEENAH..."


"Don't come near me and leave me alone" ta faɗa tana komawa cikin gidan da gudu cikin kuka.



"Jafar, kasan inda yake?" cewar Mami tana kallon shi.



Kai ya jinjina yace "Eh Mami."



"What, Jafar but why, maiyasa ka 6oye sanin inda yake bayan kasan halin da DEENAH take ciki."



"Sabida hakan shine alkhairi a gareta Mami."



"Bangane ba mai kake nufi?."



"Jafar kana nufin kace ZEEDAN shi ne balarabe?" cewar Anty Hafsat.



"Yeah" ya faɗa kafin kuma yace "I need to go now, zan dawo gobe please take care of DEENAH" yana faɗin haka ya juya tare da zuwa ya shige cikin motar sa ya ja ta ya fice bayan mai gadi ya buɗe masa..............




*************************




.............Sosai take kuka kamar zata shiɗe idanuwan ta baki ɗaya sun kumbura sabida kukan da ta dinga yi cikin dare bata samu isasshen bacci ba.



Ji takeyi Jafar ya cuce ta kuma bayason farin cikin ta tunda har yasan inda balarabe yake tsawon lokacin nan amma bai ta6a faɗa mata ba.




"DEENAH ki fito yayan ki yazo wurin ki."



Ƙin kula ta tayi sai ma cigaba da tayi da kukan ta tana jin haushin Jafar sosai a zuciyar ta.


"DEENAH..."



"Ni banason ganin shi" ta faɗa tana rufe pillow akanta ta kwanta.


Bayan mintina biyar taji yana kiran sunan ta "DEENAH."



"Ka rabu dani" ta faɗa cikin kuka.



"DEENAH am sorry i know ban kyauta miki ba, and it hurts me so bad to see you in pain na rashin ganin balarabe, but i can't endure to see you in more pain bayan kin ganshi."



Ɗagowa tayi tace "He is my cure, ganin sa ba zai sanƴa ni cikin wani baƙin cikin ba, i can't believe kasan inda yake all this while amma kayi shiru baka faɗa wa kowa ba."



"DEENAH ba haka bane, ina guje miki abinda zai faru ne duk sadda kika haɗu da balarabe."



"Babu abinda zai faru, kawai haƙuri nakeson basa bakomai ba, da zaran kuma ya yafemin zan sami kwanciyar hankali, kai ba yayan kwarai bane tunda har kana iya jurar ganin ƙanwar ka cikin tashin hankali."



Sosai bayajin daɗin kalaman dake fitowa daga bakin DEENAH na kiran sa yayan da bai dace ba, bakomai yake nema wa DEENAH ba sai kwanciyar hankali, shi kaɗai yasan abinda zai biyo bayan haɗuwar ta da balarabe.



"Alright, kije ki shirya zan kai ki wurin balarabe, but kada kice ban gargaɗe ki ba, haɗuwar ki da balarabe babu abinda zai haifar miki sai ƙarin damuwa wannan shine abinda nake guje miki, amma tunda kince ganin sa shine kwanciyar hankali dama kuma farin cikin ki, then i will make sure na kai ki kin gan shi kafin ya bar cikin Sokoto gobe, and that Mall da nake aiki a matsayin MANAGER Mall ɗin ZEEYAD ne, sannan kuma that Man da kikayi banging dashi har sau biyu ZEEDAN ne, ZEEDAN and ZEEYAD duk mutum ɗaya ne, you go and get ready i will be waiting for you outside" yana faɗin haka ya fice daga ɗakin




DEENAH ɗimauce wa tayi tsabar farin cikin dake fizgar ta, da sauri ta miƙe taje tayi wanka ta fito.


Kafin ta shirya so very quickly wanda da wanka da shirin bai ɗauke ta good 20mins ba ta fito.



Bata kula kowa a falon ba ta fice da sauri zuwa waje.



Anan taga Jafar a cikin mota nan ta shige kawai tace "Yaya make it fast please,i wanted to see him."



Tada motar kawai Jafar yayi ya jata suka bar cikin gidan.



Tafiya mai nisa sukayi kafin su iso ga wani haɗaɗɗen hotel mai kyau da tsada.



A inda motoci ke parking yayi kafin tayi saurin fitowa tana riga shi.



Tausayin ta kawai Jafar keji dan kuwa shi kaɗai yasan abinda ke ran ZEEYAD game da DEENAH.



Bayan sa tabi kamar zata tashi sama dan daɗi, sai dai gefe guda kuma ji take zuciyar ta kamar zata faso waje dan gudu.



Lifter suka shiga ya kai su har flat ɗin da ɗakin ZEEYAD yake.



Bakin ƙofar wani ɗaki yaja ya tsaya ya kalleta yace "Yana cikin ɗakin nan ki shiga, i will be waiting for you outside" yana faɗin haka ya juya ya tafi ba tare da ya bata damar furta abin dake bakin ta ba.



Da kallo ta bishi har ya shige cikin lifter kafin kuma ta maido da duban ta kan ƙofar zuciyar ta na matuƙar rawa sosai.



Tsoro ne da fargaba suka darsar mata a zuciya lokaci guda, kafin kuma cikin rawar hannu ta murɗa handle ɗin ƙofar a hankali bugun zuciyar ta na ƙaruwa.



A hankali ta shigo idanun ta a ƙasa kamar munafuka, kafin ta fara bin cikin hadaɗɗen falon da kallo cikin ƙasa da idanu.



A hankali ta shiga ɗago da kanta tana ƙarewa falon kallo.



Babu kowa a ciki hakan yasa ta takowa ciki tana rufe ƙofar ta ƙaraso tsakiyar falon.



Kan kujera ta samu ta zauna tana wuwwula idanun ta dan ganin ta inda zai fito.



Shiru ta ɗauki almost twenty mins a zaune sai dai bataji alamun kowa ba, har ta fara tunanin koh baya ciki ne.


A garin kalle-kallen ta ne idanun ta suka faɗa kan wata farar A4paper dake ajiye akan center table ɗin falon inda aka ɗaura remote da Pencil akan sa.



Hannu ta kai zata ɗauka nan taji alamun motsin mutum hakan yasa ta saurin daidaita nutsuwar ta tana gyara zama kanta a ƙasa tayi zuru-zuru da ita, kamar kace kyatt ta fece.



Ta bayan ta yake tsaye yana ƙare mata kallo, fuskar nan tasa a matuƙar ɗaure.



Takowa yayi a hankali yana dafa kujera da take kai ta baya.



"MADEENAH" ya faɗa a hankali cikin daddaɗar husky voice ɗin sa.................






_Nasan da yawan ku nada tambayoyi, toh kada ku damu insha Allah a hankali zan warware muku zare da abawa🤘🏼🤩_




*Yawan Comment yawan typing, kiyi sharing fisabilillah idan kin karanta👏🏽*




*Kada ku manta Babu Posting ranar weekend😂🤘🏼*





*MHIZZ JIDDHERR............✍🏽*
[8/30, 9:32 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D*
```[The Abandoned Prince]```




*NA*
*JIDDAH BINT MUHAMMAD*






*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*





*017...*






............DEENAH kawai daskare wa tayi zaune zuciyar ta na mugun racing kamar zata faso ƙirjin ta ta fito.



Idanun ta da ta waro kasa ƙifta su tayi sumar tsaye kawai tayi a zauna jikin ta yayi mata nauyi sosai bata iya koda motsa ƴar yatsar ta bane.


Ƙaramar stool ya ɗauka sannan ya zagayo ya ajiye a gaban ta ya zauna.



Idanun ta ta sanƴa cikin nashi tana jin wani irin abu na taso mata a chan ƙasar zuciya.



Kallon ta shima ZEEYAD yake ba tare da dukkanin su sun iya ɗauke idanuwan su daga cikin na juna ba.



Sosai wani irin farin ciki da annashuwa ke taso mata ganin yau ta haɗu da wanda take burin sake sanƴawa a idanun ta tsawon shekaru, ji tayi dukkanin wani ƙunci da baƙin cikin ta ya fara yayewa.



Almost 10mins suna kallon juna babu wanda ya iya janƴe nasa idanun, sai shine ya fara kauda kansa inda DEENAH kuwa kamar wacce aka ɗauko sabuwar halitta aka jefa mata a gaban ta.



Yatsun sa ya kaɗa mata a fuska nan tayi firgigit ta dawo daga duniyar tunanin da ta faɗa.



Cikin rawar murya tace "You..you..."



"What are you doing here?" shine tambayar da ya jefa mata ba tare da ya bari ta ƙarasar da abinda take shirin faɗa ba.



Shiru tayi tana kallon sa kafin daga bisa ni kuma ta buɗi baki tace "I can't believe i can see you again in my life."



Kallon ta yayi yace "DEENAH?."



Kallon sa take jin yadda ya kira sunan nata, nan yace "It's been a long time."



Sunkuyar da kanta tayi ganin irin kallon da yake yi mata, nan ta sake tsinkayo muryar sa yana faɗin "Did you missed me that bad?."



Ɗagowa tayi ta kallesa tace "Ina...inaso ne na baka haƙuri, am sorry for causing you alot of pain back then."



Murmushin da ya tsaya masa kan le6e yayi yace "And how do you expect me to forgive you?."



"You're the worst person i have ever met" ya sake faɗa cikin ɗaurewar fuska.



DEENAH tuni idanun ta sun taru da hawaye "Maiyasa ba zaka yafe min ba?."



"Sabida baki cancanci na yafe miki ba."



"You can't do this to me."



"And shouldn't i, kin manta lokacin da kikayi pointing finger ɗinki on me claiming cewa ni ne nayi miki fyaɗe?" ya faɗa cikin ƙunar rai fuskar sa na canzawa zuwa 6acin rai.



"But it wasn't my fault" ta faɗa cikin kuka.



"It wasn't your fault, kina nufin kicemin that rascal Uncle of yours shine yayi forcing naki or what?."



Magana zata yi nan yace "Tell me, tell me nawa ya baki dan kiyi min sharri?."


"Please just hear me out."



"Ohh na gane, tell me one thing, shin ya saba danne ki ne kullum da yaga asirin sa zai tonu ya baki kuɗi dan ki ɗaura min sharri or what, hun?."



"Mai kake faɗa ne haka?, ni babu wanda ya ta6a yi min fyaɗe, not even my Uncle."



"You're lying, you've to be ashamed of yourself for showing your Ugly face to me after what you've done."



Kuka ta fashe dashi nan yace "So now tell me iya adadin mazan da kikayi tarayya dasu after your Uncle."



Ɗago da manƴan idanun ta tayi tana kallon sa, miƙewa tayi tsaye tana jin yadda zuciyar ta ke matuƙar ƙuna da abinda ya faɗa mata.



"Zargi na kake da yin karuwan ci?" ta faɗa tana kallon sa.



Ɗan ta6e baki yayi shima yana tashi tsaye yace "Ba zargi bane, ya kike tunanin dama rayuwar yarinƴar da Uncle ɗinta ya lalata tun tana ƙarama zai kasance bayan ta girma?."



"Stop it" ta faɗa cikin kuka.



Ɗan murmusawa yayi yace "It hurts right?, abin akwai ciwo idan an ɗaurawa mutum laifin yin fasiƙanci doesn't it?."



Juyawa tayi da niyyar tafiya dan kuwa ba zata iya jurar irin maganganun da yake faɗa mata.



Tsinkayo muryar sa tayi yana faɗin "Tell me iya adadin kuɗin da kike chajar customers ɗinki a dare ɗaya, nikuma zan biya ki dukkanin kuɗin ki bar bada kanki haka nan."



Juyowa tayi tana kallon sa fuskar nan nata sha6e-sha6e da hawaye.



"You want to walk away bayan baki roƙe ni yafiya ba."



"But you said you won't forgive me."



Idanu ya ɗan waro yace "Really, did i?, i thought you will keep begging me, holding my feet and asking for forgiveness."



Ƙarasowa gaban sa tayi tace "Am sorry please forgive me for hurting and ruining your life."



"Not like that, you need to hold my feet and beg" ya faɗa yana kallon cikin idanun ta.



Shiru tayi tana kallon cikin idanun sa kafin tace "Okay then, If that would make you to forgive me then, i would do it" ta faɗa tana shirin durƙusawa ta kai hannuwan ta ƙafafuwan sa.



Saurin riƙo ta yayi ransa a 6ace ya miƙar da ita yana kallon ta.



"Have you lost your mind?" ya faɗa yana kallon ta.



"Idan nayi hakan zaka yafe min, won't you?."



"Na ɗauka ba zakiyi hakan ba, Maybe you should give me a hug instead" ya faɗa yana jawo ta jikin sa ya rungume ta.



DEENAH numfashin ta ne ya kusa ɗaukewa jin ta a cikin jikin shi, sosai ta tsorata tayi sumar tsaye almost one minute suka ɗauka a hakan, muryar sa ta tsinkayo yana faɗin "So zargi na akan ki ya tabbata gaskiya, you really enjoyed hugging men don't you?."



Saurin kwacewa tayi tana ja da baya hawaye na bin fuskar ta.



"Don't pretend to be innocent, that's exactly what you're."


"What am i?."


Shiru yayi yana kallon ta kafin yace "What you are, you're asking me what you're?, idan na kira ki da wannan sunan then you will be shattered."


"Are you trying to call me a Prostitute?."


Idanu ya waro yace "I didn't said that, kece kika faɗi hakan da bakin ki."


"That is exactly what you mean, isn't it?."


Kafaɗu ya ɗaga yace "Duk yadda kika ɗauka."



"Alright then, thank you, that won't hurt me sabida nasan kanaso ka rama abinda nayimaka ne wurin cusa min baƙin ciki shiyasa ka faɗamin haka, toh ka sani hakan ba zai dame ni ba sabida nasan ba hakan nake, but you..... it's been ten years now but har yanzu abin na damun ka."



"What do you mean?" ya faɗa yana sake tamƙe fuska.



"What i mean is duk abinda zuciyar ka ta baka shi nake nufi."



"You called me a Prostitute kai kuma duk abinda zuciyar ka ta baka then haka kake" ta sake faɗa.



"Dan haka tsakani na da kai kuma yanzu babu wata yafiya da zan nema, sabida ka rama abinda nayi maka, a yanzu ma ba zaka sake gani na ba bale kuma na sake yi maka wani laifin da zai sanƴa ka riƙe ni a zuciya, duk zafi da ciwon da kake ji a zuciyar ka bai kai kwatankwacin wanda naji a shekaru goman nan ba, kullum buri na bai wuce Allah ya sake nuna min kai na baka haƙuri ba i have suffered and went through alot all because of what i have done to you as a little girl forced by her Uncle, amma baka ga hakan ba ka riƙe ni a zuciyar ka all these years da gaba, i am so mad na ganin na haɗu da kai, and now here you're i thought

Please Login or Register in order to submit comment