You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
ka yanzu, just don't try to mess up with me, uhm?" ya faɗa yana kallon Sooraj ɗin da kamar ya tashi sama sabida haushi.
"Har kai wanene da zaka ce zaka tsare ni da maganganu...?."
"Oh come on, i told you not to try to messed up with me didn't i?."
"Mai zaka iya yi?" ya faɗa cikin aika masa da mugun kallo.
Kallon sa ZEEYAD keyi kafin kuma cikin ɗagun murya yace "Guards!."
Duk fitowa sukayi daga spot ɗin da kowanne ke tsaye suna iyowa wurin da ZEEYAD da Sooraj ke tsaya, cikin girmamawa da duƙar da kai suka ce "Yes the great Prince."
Ba tare da ya kalle su ba yace "Lock him up in the dark room for 3hours."
"Yes Prince" suka amsa cikin girmamawa suna iyowa kan Sooraj da niyyar kama shi, tsawar da ya daka musu ne ya sanƴa su dakatawa duk suna kallon sa kafin ya kalli ZEEYAD cikin hura hanci da huci yace "Ni zaka wulaƙanta, how dare you?."
Ɗan ta6e baki ZEEYAD yayi yace "I warned you, didn't i?."
"I will make sure kayi nadamar abinnan da kayi" ya faɗa yana nuna ZEEYAD ɗin da yatsa.
"Take him away" ya faɗa.
Duk iyowa kansa sukayi tare da kama shi sukayi gaba dashi kamar yadda ZEEYAD yace musu.
Muguwar kallo mai cike da ma'anoni iri-iri kawai yake aikawa ZEEYAD yanajin zuciyar sa kamar ta tarwatse tsabar ƙunar da takeyi masa.
Barin wurin ZEEYAD yana kimtsa iriyar rayuwar da zai bi kowanne daga cikin fadar tasu dashi, ba zai ta6a samun salama ba har sai yaga kowannen su ya ɗanɗana ƙuɗar sa fiye da yadda sukayi masa, one after the other zaiyi maganin su.
Da wannan tunanin ya isa ga part ɗinshi da tafi na kowane ɗa a cikin masarautar girma da haɗuwa.
Da kallo yabi bayi matan dake ta aikace suna kai komo dashi, kafin kuma cikin 6acin rai yace "I want to be alone."
Sum-sum kowacce ta fice da kayan aikacen ta yana sake tsuke fuska ya haura sama, sam baiga dalilin da zai sanƴa ana barin masa bayi mata sukayi masa aiki ba, hatta ruwan wanka da kanshi wankan ma wai masu yi masa daban aka ware tsabar ance musu shi ɗin shege ne, sai da ya yiwa abin tufkar hanci kafin su daina shigo masa ɗaki, iyakan su cikin falo da sauran ɗakunan dake cikin part ɗin ba dai su taka zuwa ɗakin kwanan shi ba.
Ɗakin motsa jikin sa ya nufa wanda ke ƙawace da ababen Exercise kala daban-daban na bada ƙarfi.
Ƴar ƙaramar rug ɗin hannun sa ya ajiye kan couch, kafin ya nufi ɗaya daga cikin *DECLINE BENCH PRESS* ɗin dake jere cikin instrument ɗin motsa jikin ya kwanta, kafin kuma ya ɗaga ƙarfen ya fara aiki da ita cikin kwarewa.
Ya kai almost 30mins yana yi inda Knocking ɗin da yaji a bakin ƙofa ya sanƴa shi saurarawa.
Knocking aka sake yi a karo na biyu hakan ya sanƴa shi faɗin "The door is opened" ya faɗa yana cigaba da aikin shi.
Rufe bakin sa keda wuya aka turo ƙofar aka shigo cikin sallama.
Sadeeq ne da wata kyakkyawar budurwa a bayan shi hannun ta riƙe da tray sai sambaɗa murmushi take.
Wuri Sadeeq ya samu ya zauna kafin ita kuma ta ajiye tray ɗin akan table tana maida duban ta gun ZEEYAD, murmushi take dan kuwa ba ƙaramin burge ta yake idan ta ganshi ya fito fili yin jogging ba.
"Hey" cewar Sadeeq yana duba agogon hannun sa.
Dakatawa ZEEYAD yayi yana ajiye ƙarfen kafin kuma ya ɗago zaune, ganin ta ne ya sanƴa shi saurin gimtse fuskar sa yana kallon Sadeeq.
Kafaɗu Sadeeq ya ɗaga masa alamun oho kafin kuma ya tashi yana janƴo ƴar ƙaramar towel ya shiga goge jikin sa yana ƙarasowa ya zauna kusa da Sadeeq ba tare da ya kula ta ba.
Murmushin yaƙe ta saki ganin yadda yayi kamar bai ganta ba tace "Ina kwana Akhi?."
Kamar ba zai amsa ba kuma yace "Am good."
Murmushi tayi kafin tace "Kayi haƙuri ban shigo da izinin ka ba, dama breakfast na kawo maka, i made your favorite" ta faɗa tana buɗe tray ɗin ta ciro wani bowl tare da buɗe murfin shi tana miƙa masa.
Da kallo yabi bowl ɗin dashi kafin kuma ya sanƴa hannu ya amsa yace "Thank you."
Murmushi tayi cike da jindaɗin gode mata da yayi tana kallon sa.
Da gefen ido ya kalli Sadeeq dake kusa dashi yana tsuke fuska.
"Na jira ka gama ci sai na tafi da kwanukan ne?" ta faɗa.
Shiru yayi kafin kuma yace "No, thanks."
Tsaye tayi sam bataji daɗi ba kafin kuma tace "Okay, zan dawo anjima na ɗauka."
Kai kawai ya jinjina mata kafin kuma ta fice zuciyar ta fal farin ciki.
Duk da kallo suka bita ficewar ta ya sanƴa shi saurin dire bowl ɗin yana juyowa ya kalli Sadeeq.
Surrender Sadeeq yayi da hannu yace "She saw me coming here sannan ta san guards ba zasu bar ta ta shigo ba hakan ya sanƴa ta roƙo na kan na jira ta mu shigo tare."
"Well then i guess kaima hana ka shigowa zanyi" ya faɗa yana miƙewa tsaye.
"Oh let's pretend baka faɗi hakan ba."
"You know bama good time da Abhi da Akhi ɗinta, and you let her into my place."
"But the girl is decent, bata ɗauko hali irin na family ɗinta ba, maybe you should get married to her sabida seems like she loves you."
Wani irin mugun kallo ZEEYAD ke binsa dashi kafin yace "Get out."
Murmushi Sadeeq yayi yace "Am going to work yanzu, nazo ne na sanar maka da cewa that girl da Mom nata yau zanyi discharge nasu seems like kamar ka san su koh?."
ZEEYAD ji yayi zuciyar sa tayi wani irin bugawa, idanu ya runtse kafin kuma ya samu wuri ya zauna.
Kallon sa kawai Sadeeq keyi ganin yadda mood ɗinsa ya canza nan take.
"Are you alright?" ya faɗa.
Kallon Sadeeq yayi kafin kuma yace "maiyasa zakayi min maganar su?."
"Does that annoy you?" ya faɗa yana kallon sa.
Shiru yayi masa sai wuri ɗaya kawai da ya kafe da idanu yana kallo.
"Am sorry then" cewar Sadeeq.
Ɗagowa yayi ya kallesa kafin ba tare da yace masa komai ba.
Shiru shima Sadeeq yayi yana kallon ZEEYAD ɗin, kafin kuma daga bisani ya numfasa yace "I think i should be going, inada aiki dayawa" ya faɗa yana miƙewa tsaye.
Da kallo ZEEYAD ya bishi har ya kai bakin ƙofa kafin kuma yace "Ta samu lafiya?."
Juyowa Sadeeq yayi yana kallon sa, kafin kuma yace "No, da ɗan saura but ta tuna wasu abubuwan kuma ta fara magana, idan ta cigaba da shan magunguna kuma ta koma inda ta fito zata iya tuna komai da komai."
Kai kawai ZEEYAD ya jinjina yace "Okay."
"Are you coming or something?" cewar Sadeeq.
Kai ya girgiza masa alamun A'a.
"Okay then, see you" ya faɗa yana buɗe ƙofar ya fice.
Idanu ya runtse yana komawa ya jingina da kujerar da yake kai.
Idan suka tafi does that mean ya rasa ta gabaɗaya kenan?, yayi alƙawarin ba zai sake zuwa kusa da ita ba, sannan yayi alƙawarin ya rabu da ita kenan har abada, dan haka ya zama dole ne ya yaƙi zuciyar sa na ganin ya yaƙice ta, sannan kuma ya rabu da tunanin ta, sunyi rayuwa a baya yakamata ya sanƴa ta cikin past life ɗinsa ya zamto ba zata ta6a dawowa ba, kamar rayuwar ƙuncin da yayi a baya, he needs to forget her ba ma ita kaɗai ba dukkanin family ɗinta, he knows that hakan ba abu mai sauƙi bane a gareshi but he needs to try so very harder na ganin hakan ya faru.
Da wannan tunanin ya tashi ya bar ɗakin gym ɗin izuwa cikin ɗakin kwanan shi.
Wanka yayi ya shirya cikin shigar sa ta alfarma kafin kuma ya fice zuwa part ɗin Grandma dan kuwa nan ne kaɗai zai iya samun sassaucin abinda yakeji a cikin zuciyar sa.
***********************
___________Kwance yake yayi matashi da cinƴar grandma, idanun sa a lumshe yanajin duk wata damuwar sa na gushewa sakamakon tausar da take yi masa cikin gashin kansa.
Grandma ba ƙaramin ƙauna take yiwa jikan nata ba, duk wani abu da zai sanƴa shi farin ciki shi take yi masa, dan kuwa shi kaɗai take gani taji zuciyar ta tayi sanƴi musamman da ya kasance sauran ƴaƴan ta sunyi nesa da ita.
Wata baiwa ce ta ƙaraso inda suke zauna cikin girmamawa tace "Ranki ya daɗe an kammala breakfast ɗin."
Kallon ta Grandma tayi kafin kuma tace "Maiyasa kuka 6ata lokaci dayawa wurin kammala wa, je ki tahowa da Yarima nashi, nasan yana jin ƴunwa."
Amsawa tayi cike da girmamawa kafin kuma ta bar wurin zuwa aikata abinda aka sata.
Ba'a jima ba ta dawo ɗauke da tray ɗin abin karin kumallon ta ajiye.
Ganin tayi tsaye ne ya sanƴa Grandma cewa "Zaki iya tafiya."
"Nagode ranki ya daɗe" ta faɗa tana juyawa ta tafi.
Kallon ZEEYAD Grandma tayi tace "Boy ka tashi kaci abinci kaji."
Tsuke fuska ZEEYAD yayi dan kuwa wani irin bacci mai daɗi ne ya fara fizgar sa nan yace "Grandma bacci nakeji, kuma ba zanci abincin da suka girka ba."
"Toh girkin wa kakeson ci ɗan nan?."
''Naki" ya faɗa.
Murmushi tayi tace "Toh ai shikenan an gama bari na tashi naje na girka maka yanzun nan."
"No Grandma, sai na tashi a bacci tukun, coz am very sleepy."
"A'a fah bakajin ƴunwa ne?."
"No" ya faɗa alamun mai jin bacci.
Hakan yasa ta yin shiru tana cigaba shafa sumar kanshi.
*******************
__________"Umma?" ta faɗa tana kallon Umma dake tattare kaya cikin ƴar ƙaramar jaka.
Ɗagowa Umma tayi tana kallon ta kafin ta bar jakar tazo kusa da DEENAH cikin kulawa tace "Menene?."
Shiru tayi kamar mai son tuna abu kafin kuma tace "Ina zamu je?."
Murmushi Umma tayi kafin kuma tace "Gida zamu koma Auta."
"Gida?, ina ne gidan?."
"Zamu je mu goben nan kinji?."
Kai kawai ta jinjina kafin kuma Umma ta koma ta cigaba da haɗa kayan.
Sadeeq ne ya shigo ɗakin da takardar sallamar bayan sun gaisa da Umma ne ya bata yace "Alhamdulillah, finally za'a koma gida, make sure anyi abiding da rule ɗin da na gindaya, insha Allah zata samu full recovery, sannan kuma zaku dinga zuwa check-up after every 3months, dan ganin lafiyar kwakwalwa ta har izuwa lokacin da zata samu lafiya gabaɗaya."
"Insha Allah Doctor, mungode sosai da sosai, zamu kiyaye duk wata doka da izinin Allah."
Murmushi yayi kafin ya sake yin wasu rubutu a jikin files ɗinta sannna ya fice.
Ɗaukar file ɗin Umma tayi ta sanƴa a jaka kan kuma ta cigaba da haɗa kayayyakin ta.
Bayan ta kammala ne Nurses ɗin dake kula da DEENAH suka shigo ɗakin dan haka taimaka mata sukayi suka fidda mata kayan waje.
"Tashi muje koh?" cewar Umma.
Shiru DEENAH tayi tana kallon ta nan Umma tace "Ba fah zai zo ba dan haka tashi muje mu, kinji?."
Kya6e baki tayi idanun ta na cikowa da hawaye, hannun ta Umma ta kama suka fice daga cikin ɗakin.
Cikin farfajiyar asibitin suka tsaya jiran Taxi, inda DEENAH duk hankalin ta yayi gaba so take kawai ta sake ganin shi koh zata ji daɗi a ranta, sai dai yau ɗin kamar bai shigo asibitin ba.
Umma ce tace dasu "Ku jira ni anan bara naje shagon chan na dawo."
Da "Toh" suka amsa mata kafin kuma ta wuce.
Ɗaya daga cikin nurses ɗin ce tace "DEENAH, yau fah Doctor YAZEED bai shigo office ba koh kin manta ne yau Thursday baya shigowa?."
Murmushi ɗayar tayi tace "Seems like tayi kewar shi ne?."
"Yeah he is nice, ai kinga dole taji kewar shi."
Cikin kwantar da murya ɗayar tace "Kina tunanin yana sonta ne, kokuma dai kawai a matsayin ƙawar wasar sa ya ɗauke ta?."
"What no, ba sonta yake ba imagine kamar sa kuma ɗan sarki yaso ta, he is just kind to her kamar yadda yake yiwa kowa."
"But, yadda yake sakin jiki da ita suyi hira idan mun fito motsa ƙafa bakya tunanin akwai wata a ƙasa, duba da yadda yake kallon ta?."
"No, he is just being nice kawai."
Hango Umma tafe ya sanƴa ɗayar saurin yin shiru.
Murmushi tayi tace "Thank you girls, gaskiya kunyi matuƙar ƙoƙari sosai akan DEENAH Allah yayi muku albarka."
Murmushi sukayi ɗaya tace "Ai bakomai aikin mu ne, sai dai zamuji kewar DEENAH sosai."
Ɗayar ce tace "Dama ki bamu lambar wayar ki kullum mu dinga gaisawa da DEENAH."
Murmushi Umma tayi kafin tace "Of course zan baku idan kuna so."
Saurin ciro wayar ta ɗayar tayi tana miƙawa Umma tace "Muna so."
Amsa Umma tayi ta sanƴa musu lambar ta na Nigeria kafin ta miƙa musu wayar.
Godiya sukayi mata kafin su tara musu Taxi, duk rungume DEENAH sukayi kafin su buɗe mata motar ta shige.
Hannu sukayi ta ɗaga musu har motar ta 6ace daga ganin su.
**********************
__________Washe gari Ƙarfe bakwai ɗin dare jirgin su Umma ya sauƙa.
Zuciyar Jafar cike take da ɗumbin farin ciki, sabida yau zai ga ƙanwar sa, tun kafin ayi magrib ya tafi jiran su inda achan yayi sallar ma.
Ganin sauƙar jirgin su kuwa kamar an sauƙo masa da farin cikin sa ne.
Hango Umma yayi riƙe da hannun DEENAH suna sauƙowa daga kan matattakalar benin jirgin, idanu ya zuba musu har suka idda sauƙowa suna ƙarasowa, da sauri ya nufe su yana cewa "Umma?."
Wani irin ƙayataccen murmushi Umma ta sakar masa tana buɗa masa hannu.
Da sauri ya rungume ta yanajin wani irin tsantsar farin ciki na dabaibaye shi.
Kallon DEENAH da ta kafe shi da ido tana kallo yayi da alamu dai bata gane shi ba.
Ɗagowa yayi yana sakar mata murmushi ganin sai kallon sa take yi.
"Umma nayi kewar ki."
"Ai baka kaini kewa ba, babban yaya" ta faɗa cikin murmushi tana shafa kanshi.
Murmushin shima yayi yace "DEENAH?."
Murmushi ta sakar masa tana kallon shi.
Riƙo ta Umma tayi kafin kuma tace "Muje gida koh?."
Kai Jafar ya jinjina kafin ya ɗebi luggages ɗin su ya kai mota.
Nan duk suka shige kafin ya tada motar ya bar wurin.
******************
_______Horn ya danna a bakin ƙofar gidan nan take mai gadi ya wangale gate ɗin sai ɗaga hannu yake yana washe haƙora cike da farin ciki shima.
A parking space yaje yayi parking motar, tun kafin su buɗe motar suka ga an buɗe, cike da farin ciki Anty Khadija da Amirah suka rungume Umma suna yi mata oyoyo.
Saurin buɗe inda DEENAH take sukayi tana fitowa kafin itama su rungume ta cike da farin cikin ganin ta da sukayi suna ɗagowa.
"DEENAH?" duk suka faɗa suna kallon ta.
Murmushi kawai DEENAH tayi musu tana bin su da kallo.
Mami ma ƙarasowa wurin tayi tana yi musu lale da zuwa.
Duk ciki suka nufa kowanne ka ganshi fuskar nan farin ciki fal a cikin sa.
DEENAH kuwa da kallo take ta bin gidan tana ganin kamar ta san shi.
Bayan sunyi wanka sun huta ne kuma aka gabatar musu da abinci da na sha kala daban-daban, dan kuwa su tun jiya Mami ta turo su Anty Khadija yi musu gyaran gida da sauran abubuwa.
Sosai Umma taji daɗi sai godiya da sanƴa albarka take yi musu, duk haɗuwa sukayi suka fara cin abincin.
Jafar idanun sa na kan DEENAH ganin yadda take ta bin gidan da kallo kamar yau ta fara ganin sa.
A haka suka wuni cikin raha da farin ciki har sai da dare yayi tukun kafin su koma gida.
Umma ɗaki ta kai DEENAH ta taimaka mata tayi shirin bacci kafin itama ta fice zuwa nata ɗakin.
Kwance take idanun ta na akan p.o.p ceiling ɗin ɗakin, zuciyar ta fal tunani, ga kuma rashin sukuni da ta kasa yi tunɗazu, haka tayi ta juye-juye har bacci ya ɗauke ta.
*****************
______Washe gari kuwa makwa6ta ne sukayi ta shigowa gaisuwa dama kuma ƴan wurin aikin su Umma, kowa yana zuwa duba mai jiki, sosai Umma taji daɗin hakan.
Jafar kuwa wurin aiki ya fice after so many attempt da yayi na kiran ZEEYAD dan sanar dashi su DEENAH sun dawo amma wayar tasa bata shiga haka nan ya haƙura ya tafi office ɗin zuciyar sa babu daɗi.
6angaren DEENAH kuwa ɗaki ta dawo dan kuwa ji tayi ba zata iya zama cikin mutanen ba, dan kuwa a takure takejin ta a cikin nasu.
Zama tayi a bakin bed ta shiga ƙarewa ɗakin kallo na kusan 10mins kafin kuma ta kwanta tanajin kewar Ƙawayen ta nurses dama kuma abokin ta Doctor.
*TWO WEEKS AFTER*
________A ƴan kwanakin nan sosai take gane dukkanin abinda ta gani tare da tuna koh menene shi.
Yau ma tsaye take tana bincika closet ɗinta taci karo da school uniform nata.
Tsayawa tayi tana kallon farin kayan kafin kuma ta saki murmushi a hankali tace "School?."
Kafin kuma dukkanin wani abu da tasan tayi a makarantar ya shiga dawo mata cikin kwakwalwa.
"Bodyguard?" ta furta daidai lokacin da ta tuna inda take faɗawa wannan malamin nan nasu cewar shi ɗin bodyguard ɗinta ne.
"Who is he?" ta faɗa sakamakon kasa tuno fuskar sa da tayi.
Maida uniform ɗin tayi kafin kuma ta samu bakin bed ta zauna tana rabka tagumi.
"DEENAH?" taji an faɗa.
Juyowa tayi tana kallon Umma kafin kuma tayi saurin miƙewa tace "Umma waye...waye bodyguard?."
"Bodyguard kuma?" cewar Umma cikin mamaki tana kallon ta.
Kai ta jinjina mata tana kallon Umma ɗin.
"Waye kuma bodyguard?" cewar Umma ɗin.
Shiru DEENAH tayi tana tunanin kafin tace "Ban..banga fuskar shi ba."
"Toh fito kizo kici abinci ki sha maganin ki."
Kai ta jinjinawa Umma tace "Toh."
Ficewa Umma tayi kafin ita ma ta tashi tabi bayan ta.
********************
_________A ƴan kwanakin nan ji yayi ya mance da wata DEENAH koh family ɗinta, sabida Grandma ɗinsa ta zame masa komai haka kuma bata ta6a barin sa cikin ƙunci da 6acin rai.
Zaune yake a wani ƙayataccen wuri wanda kai tsaye za'a iya kiran sa wurin hutu, babu abinda kakeji sai kukan tsuntsaye da shawagin su, gaban sa kuwa system ɗinsa ce sai kuma mug ɗin coffee a hannun sa yana sipping a hankali fuskar sa manne da baƙar shade.
YAZEED ne ya ƙaraso wurin ya zauna fuskar nan tasa a cunkushe babu walwala.
Ɗagowa ZEEYAD yayi yana kallon sa, ganin kamar da damuwa a ransa yasa shi faɗin "Meke damunka?."
Kallon ZEEYAD yayi yace "Bakomai."
"Are you sure, ina faɗamaka damuwa ta fah, remember?."
"Yaushe ka ta6a faɗamin, you never tell me anything about your life."
Murmushi ZEEYAD yayi yace "Actually baka ta6a tambaya ba."
Kallon sa yayi kafin yace "Okay, that girl da nake faɗamaka."
"What girl, the one you're inlove with?."
"Yeah ita."
"What's wrong with her, did she betrayed you or something?."
"No tayaya zata fara yaudara ta bayan ba soyayya muke ba?."
"What happened then?."
Shiru yayi yana tsuke fuska kafin yace "I lost her, i mean ta tafi ba tare da na san inda take da zama ba."
"Kamar ya?" cewar ZEEYAD yana gyara zaman shi.
"The girl is a patient and..."
"And you fell inlove with her?" cewar ZEEYAD cikin katse shi.
Kallon ZEEYAD yayi kafin yace "Actually yes, and an riga anyi discharge nasu almost 3weeks kenan, am so bothered you know, i don't even know where to find her."
"You fell inlove with your patient?."
"Yeah, menene a ciki, she is not my patient though, kawai ina ganin ta ne and i fell inlove with her at first sight."
Murmushi mai sauti ZEEYAD yayi dan kuwa shi abin ma dariya ta bashi ganin yadda YAZEED ɗin keyi.
"What's funny bro?, actually this isn't funny you know, i really love her am so disturbed da rashin ganin ta."
Tattare dukan nutsuwar sa ZEEYAD yayi ganin dai YAZEED ɗin is serious.
"Why don't you just find her then?."
"Where, daga ina zan fara, i don't know anything about her."
"Ba kasan Doctor ɗin da ya kar6e ta ba?."
Shiru yayi kafin kuma cike da jindaɗi yace "Yo, Exactly guy, why didn't i think of that?" kafin kuma ya tashi yana buga kafaɗun ZEEYAD yace "See you in a while" ya bar wurin da sauri ba tare da ya sake bi ta kan ZEEYAD ɗin ba.
Da kallo ZEEYAD ya bishi kafin kuma ya saki murmushi yana maida duban sa kan aikin da yakeyi.
****************
_________"Umma!, Umma!!" ta ƙira da ƙarfi a karo na biyu.
Da sauri Umma dake zaune a falo ta itada Jafar ta shigo cikin ɗakin DEENAH ɗin.
Tsaye ta same ta ta kafe wuri ɗaya da idanu tana kallo yayin da hawaye suka wanke mata fuska.
"Lafiya, menene?" cewar Umma tana ƙarasawa wurin ta tare da riƙo ta.
Saurin kwace hannun ta tayi daga cikin na Umma kafin tace "Umma ina yake?."
Cikin rashin fahimta Umma ta kalle ta tace "Bangane ba, wa kenan?."
"Kin fi kowa sanin wanda nake tambaya."
"Meke damunki ne DEENAH?, talk softly mana."
"You want me to talk softly then tell me where he is" ta faɗa tana kallon Umma ɗin.
"DEENAH lafiyan ki kuwa, wa kike magana ne a kansa."
"Balarabe mana" ta faɗa idanun ta na cigaba da tsiyayar da hawaye.
Umma ji tayi gaban ta ya faɗi da jin abinda DEENAH ta faɗa.
"Balarabe, he is nothing a cikin rayuwar ki."
"Of course he is..."
"Then tell me amfanin da yake dashi cikin rayuwar ki?, he left you Okay."
"No he didn't left me, kece kika tursasa masa ya bar ni, i remember everything, how could you do this to me?" ta faɗa tana kallon Umma ɗin.
"Alhamdulillah da kika tuna komai, inaga mu bar maganar yaron nan yanzu, we should all be happy by now come on" ta faɗa tana riƙo hannun DEENAH.
Sake fuzge hannun ta tayi tace "Well then ai baki za6i ayi murnar ba yau, coz i would never be at peace from now on, kin raba ni dashi, i remember lokacin da kika kore shi a asibitin nan, i remember everything, ban ta6a tunanin zaki aikata hakan ba, how could you be so selfish, dan bakya son shi ba hakan ke nufin zaki kore shi daga cikin rayuwa ta ba, because i need him."
"You need him, ni kike wa magana cikin tsawa because of a random guy?."
Shiru DEENAH tayi bata ce komai ba, tanajin zuciyar ta na matuƙar suya kamar ta fito waje.
"You listen to me carefully, of course nice wacce na tilasta masa ficewa daga rayuwar ki, sabida banason alaƙar ki dashi, already zuwa yanzu nasan yayi moving on da life nasa you should also try and do so, and besides maiyasa bakya son rabuwa dashi tunda ba wai soyayya kuke ba, kodai kina son shi ne?."
Ɗagowa tayi tana kallon Umma ba tare da ta iya cewa komai ba.
"Answer me, son sa kike komiye?."
Maida duban ta tayi gun Jafar dake tsaye bakin ƙofa yana kallon su ba tare da ta bawa Umma amsa ba.
"Well i guess ba sonsa kike ba koh?, then ina buƙatar ki cire shi daga cikin rayuwar ki, koh da da wasa bana buƙatar jin sunan sa daga bakin ki, sabida ya riga da yayi miki nisa and am definitely sure idan shi mai zuciya ne ba zai ta6a dawowa ba, sabida na riga da na yanke alaƙar dake tsakanin ku, dan haka ki kwantar da hankalin ki sabida hakan ba zai sanƴa shi sake dawowa cikin rayuwar ki ba, haka ma hawayen da zaki zubar so i need you to give it a rest, no more tunanin da babu gaira babu dalili, yin hakan tamkar tsokano fushi na ne" tana gama faɗin haka ta fice daga cikin ɗakin ba tare da ta tankawa Jafar dake tsaye yana kallon su ba.
Duk da kallo suka bita kafin ya idda shigowa cikin ɗakin, rungume shi tayi tana sakin kuka sosai inda shi kuma ya hau rarrashin ta.
"Maiyasa Umma zatayi haka, maiyasa batason alaƙar mu dashi, maiyasa ba zata dubi halin da na shiga dama kuma wahalar da yayi akaina ba, Yaya yana sona koh ba haka ba?" ta faɗa tana ɗagowa ta kalle shi.
Kai ya jinjina mata alamun eh kafin yace "He was ready to sacrifice anything da ya mallaka akanki, actually balarabe yana matuƙar ƙaunar ki, he never rest tsawon watannin da kika ɗauka a asibiti, he just can't imagine life without you, yana sonki DEENAH hakan ya sanƴa shi karya dokar da Umma ta gindaya na kada wanda ya biyo ta a cikin mu har sai kin samu lafiya,but shi ya gaza yin hakan sabida kawai yanason ganin ki and ready to face and endure duk wani abu da Umma zata faɗa masa, but it turned out to be that Umma da kanta ta kore shi, not wondering irin halin da zaki shiga bayan hakan, ita dai burin ta shine taga ya bar cikin rayuwar mu ba tare da ma ta lura da cewar a ƙarƙashin sa nake aiki ba, and abin baƙin cikin shine ya saida company ɗinsa na nan Sokoto, that means kenan ba zai kuma dawowa ba DEENAH, i think he is out of our lives forever DEENAH."
Kuka sosai DEENAH ta fashe dashi tana komawa kan bed ta zauna "Maiyasa Umma zatayi haka, shikenan yayi laifi dan ya soni kenan, ina laifin wanda yaso
Book Chapters
Chapter 28
Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60