Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rigar bacci, kafin ta nufi bathroom ta ɗauro alwala ta fito tare da nufar Bed ta kwanta bayan ta tofe jikin ta da addu'a.

Shima ZEEYAD canza kayan sa yayi izuwa brown Jallabiya ya ɗauro alwala kafin ya kashe musu hasken ɗakin, ƙarasowa yayi ya rage musu hasken side lamps ɗin kafin ya haye kan bed ɗin yana janƴo ta jikin sa.

Hannun ta ɗaura kan nasa dake manne a cikin ta a haka har bacci ya ɗauke ta.

Cikin bacci yaji kamar ana hura masa iska mai tsananin zafi koh wanda ake kwarawa dukkanin jikin sa ruwan zafi.

Tun yana iya daurewa har ya kasa ya shiga buɗe idanun sa da sukayi tsananin kaɗawa yayin da zuciyar sa keyi masa zafi da wani irin raɗaɗi haɗi da bugu tamkar zai faso ƙirjin sa ya fito.

Buɗe idanun sa ke da wuya yaga shigewar wani irin baƙin hayaƙi cikin jikin sa.

Runtse idanu yayi sakamakon wani irin zafi da zugi dake ta ƙara sukar zuciyar sa haɗi da fatar jikin sa.

Ƙame jikin sa da ya fara rawar sanƴi yayi yana jin kamar wanda ake yayyanka tsokokin jikin sa a haka har ya faɗi ƙasa dafe da saitin zuciyar sa, daga nan kuma duhu mai tsananin gaske ya mamaye masa idanu.

Alarm ɗin ƙarfe ukun da ta saita a wayar ta ne ya shiga ringing, idanu ta buɗe tana janƴo wayar daga kan bedside drawer tare da kashe alarm ɗin, zaune ta miƙe ta shiga karanto addu'ar tashi daga bacci kafin ta kunna bedside lamp tana maida duban ta gefen da yake kwanciya, wayam ta gani dan haka maida duban ta tayi ga inda suke sallah nan ma dai bata gansa zaune ba.

Miƙewa tayi ta sauƙo daga kan bed ɗin ta shiga takawa zuwa bakin ƙofa, jin ƙofar tayi a rufe alamun dai ba'a fita daga ɗakin ba.

Wutar ɗakin ta kunna take ɗakin ya gaurayu da haske, bathroom da nufa tare da buɗewa ta shige sai dai tayi dube-duben ta bata ga kowa a ciki ba, tsoro ne ya fara kama ta, toh ina yayi?, shine tambayar da ta yiwa kanta.

Takowa tayi da niyyar zuwa ta duba closet room taji tayi tuntu6e da abu take ta faɗi ƙasa dan sam bata lura dashi ba, ƙara ta ɗan saki sakamakon goshin ta da ya ɗan bugu kafin tayi saurin maida duban ta kan abinda tayi tuntu6e dashi ɗin.

ZEEYAD ta gani kwance, ba tare da ta kawo komai ranta ba ta rarrafa zuwa inda yake hannayen ta ta ɗaura kan ƙirjin sa ta shiga girgiza shi tana kiran sunan sa akan ya tashi suyi sallar Nafila.

Gani tayi koh motsawa baiyi ba "Abyad?" ta sake kira a hankali.

"Abyad ka tashi mana" ta faɗa tana sake jijjiga shi.

Ji tayi kodai wasa yakeyi mata ne tashi tayi ta ɗauko ruwan gora kafin ta shiga yayyafa masa, nanma gani tayi koh gezau baiyi ba.

Dropping ruwar gorar tayi yana faɗi ƙasa kafin ta durƙusa da sauri tana manna kanta da ƙirjin sa tare da saurarar bugun zuciyar sa.

A razane ta ɗago zuciyar ta na dukan tara-tara, sake maida kanta tayi dan koh tana tunanin bataji bane mai kyau, nan ɗinma dai thesame thing ta sake ji.

Ɗagowa tayi da sauri idanun ta na tara hawaye ta shiga lalumar jikin sa, hannun sa ta ɗaga tana saurarar pulse ɗinsa, sakin hannun tayi da sauri tana ja da baya kafin kuma ta shiga girgiza kanta cikin kukan dake zuwan mata ta shiga faɗin "No... no... this... this can't be... you can't be dea.." bata ƙarasar ba ta sake rarrafawa da sauri tana komawa wurin nasa tare da ɗago da kansa tana rungume shi a ƙirjin ta, fuskar sa ta shiga kallo kafin tace "I know you're kidding me, i know you're not dead, maybe... maybe you're sick... yes i know you must be sick that is why you're unconcious" ta faɗa cikin tatta6a fuskar sa zuwa wuyar sa da yake sanƴi babu alamun zazza6i.

Kamar wacce aka tsikara ta miƙe da sauri tana zuwa ta lalumo wayar sa kafin kuma cikin rawar hannu ta shiga neman numbern Grandma.

Kafa wayar tayi a kunnen ta lokacin da ya shiga ringing, har ya katse bata ɗaga ba, dan haka ta sake dialing sai a karo na uku kafin ta ɗaga kiran, ba tare da DEENAH ta jira cewar ta ba ta shiga faɗin "Grandma... Grandma kizo dan Allah Abyad ba shida lafiya... dan Allah kizo da wuri" tana faɗin haka ta katse wayar da sauri tana komawa wurin sa tare da tallafo kansa tana sake kiran sunan sa "Abyad dan Allah ka tashi, kada kayimin haka you can't be dead now, baikamata ka tafi ka bar ni ba i will be doomed without you Abyad dan Allah ka buɗe idanun ka and talk to me i beg you Abyad please" ta ƙarashe cikin kuka sosai tana shafa fuskar sa.

Bai fi da 5mins ba Grandma ta ƙaraso kafin ta shiga kwankwasa ƙofar tana kiran sunan "DEENAH."

Da sauri DEENAH dake rungume da ZEEYAD ta tashi tana ƙarasawa bakin ƙofar ta buɗe, tare da riƙo Grandma cikin kuka take faɗin "Thank GOD you're here, ina ta tashin shi tunɗazu baya motsi bansan mai ya faru dashi ba."

Hankali tashe Grandma ta ƙarasa inda yake kwance da sauri tana kallon sa a hankali kuma ta shiga kiran sunan sa "Boy" tana shafo fuskar sa.

Cikin kuka DEENAH tace "He isn't waking up tunɗazu nake tashin sa amma baya motsi, am scared kada wani abin ne ya same shi."

"He will be fine insha Allah, i know he will be fine, ɗaukomin waya na kira YAZEED."

Da sauri ta miƙe tana zuwa ta ɗau wayar sa tare da miƙawa Grandma, amsa tayi kafin ta lalumo wayar YAZEED ta shiga buga masa.

Firgigit Sairah da wayar ke riƙe a hannun ta tayi lokacin da ya ɗau vibration, ganin mai kiran ne ya tabbatar mata da cewa aikin su ya tafi according to plan, ta san DEENAH ce mai kiran, murmushin gefen baki ta saki har kiran ya katse bata ɗaga ba.

Wani kiran taga ya sake shigowa shima har ya tsinke bata ɗaga ba, kira na uku taga ya sake shigowa dan haka tayi rejecting call ɗin, har sau uku ana sake kira tana rejecting kafin ta rubuta text message da faɗin _"Stop disturbing Bro"_ murmushi tayi kafin kuma ta danna send button take text ɗin ya tafi.

Goge duk wani call log da text ɗin tayi yadda dai ba za'a gane ta ɗau wayar ba, kafin kuma ta shiga settings tayi disabling ɗin fingerprint ɗinta da ta sanƴa, wayar ta ta ɗauko kafin ta yiwa Sarauniya Hafeezah text da _We did it, everything went according to planned"_ tare da danna send button ya tafi.

Lalla6awa tayi izuwa ɗakin YAZEED dake bacci kamar ma wanda baisan inda kansa yake ba, ta ajiye masa wayar sa tare da ficewa cikin sauri.

Wurin Hafeezah kuwa murmushi ta saki bayan tayi receiving text ɗin Sairah "So now let's see how you become the king, muddin ina raye only YAZEED can be the King no one else, you were my biggest problem but now that i have get ridden of you i feel like the world is my hands" ta ƙarashe cikin dariya ranta fari sol sabida ta gama da ZEEYAD sai dai wanin sa kuma ba shi ba, tunda taji nan da jibi za'a naɗa shi Sarki kamar yadda Abdulhakeem ya sanar da ita hakan ya sanƴa batayi ƙasa a guiwa ba ta aiwatar da shirin ta bayan ta sami wani babban boka da ya kware wurin aikin sa.

Dariya tayi kafin tace "Let's see who you Surprised then your Highness, idan bakayi surprising ɗinsa wurin naɗa sa sarki ba, ni nan nayi surprising ɗinka da gawan ɗanka gobe da safe, so prepared to cry the tears of true remorse your Highness, your dearest son is no more, let's see who you give your throne to then" ta faɗa cikin gimtsewar fuska.



6angaren Grandma kuwa mamaki ne ya cika su ganin abinda YAZEED yayi musu.

DEENAH ce tace "Grandma, ki kira Sadeeq i know he will be here soon."

Kallon ta Grandma tayi kafin tace "Kafin Sadeeq ya iso nan yanzu gari zai iya wayewa, sabida tsakanin gidan su da nan akwai nisa sosai."

"But what do we do Grandma, we've to save him kafin wani abin ya same shi" ta faɗa cikin kuka.

Kallon ZEEYAD da baya motsi Grandma tayi, sosai jikin ta yayi bala'in sanƴi dan kuwa bata tunanin inda akwai rai tattare dashi, ta san maƙiya sunyi nasara akan shi.

Sunkuyar da kai tayi wasu irin hawaye masu zafi suka shiga zubo mata, a hankali itama ta fara sakin shessheƙar kuka ganin angama mata da ɗan jikan nata wanda shi kaɗai ne yanzu gatan ta a duniya.

Cikin rawar murya DEENAH dake kallon ta tace "Grandma, maiyasa kike Kuka, bai fah mutu ba, bashida lafiya ne kawai."

Shiru Grandma tayi mata tana cigaba da kukan ta.

"Grandma?" ta sake faɗa wasu hawayen na sake biyo ƙuncin ta.

Kallon ZEEYAD ɗin take, tayaya ma za'a ce ya mutu, yes ta san Allah ne mai rayawa da kashewa a duk sadda yaso but tayaya za'ayi ace Abyad ɗinta ya mutu?, ta san bai mutu ba wani abin kawai maƙiyan sa sukayi masa.

"Grandma, dan Allah mu kai shi asibiti a duba shi koh wani abin ne ya same shi da baya motsi" ta faɗa cikin kuka tana kallon Grandma.

Goge hawaye Grandma tayi kafin kuma tace "Bari naje waje na kira wadannan masu gadin suzo mu kaisa asibiti" ta faɗa tana miƙewa ta fice daga ɗakin.

Kallon ZEEYAD tayi tace "Insha Allah you will be fine, no harm can come to you."


********************


________Sosai DEENAH ke kuka a gaban gawan ZEEYAD da akayi masa shiru makwancin sa ne kaɗai ya rage a kaisa.

Sosai fadar da ɗau shiru kukan ta kaɗai akeji, YAZEED ne ya faɗo cikin fadar tamkar wanda ake korar sa, turus yaja ya tsaya yana kallon ɗan uwansa dake sanƴe cikin sutura irin ta matattu.

Idon kowa a wannan wurin yayi jaa sosai alamun dai sun sha kuka Except Hafeezah da Sairah da nasu kukan ya kasance na munafurci ne, Grandma kuwa sobbing kawai takeyi yayin da mai Martaba shima ya kasa barin kan gawar ɗan nasa, da ka gansa kasan yana cikin shock da ɗimuwa koh kukan ma ya kasa yi.

Ɗaya daga cikin ministocin ne ya ƙaraso wurin a hankali yace "Yakamata a kai Yarima ZEEYAD makwancin sa haka nan, tunda har anyi sallahr azahar ɗin."

A tsawace DEENAH tace "No... babu wanda zai ta6a shi i know bai mutu ba, ku ɗan dakata zuwa anjima kaɗan ni nasan zai farka amma yanzu kam bai mutu ba" ta faɗa cikin rungume shi.

Shiru kawai mutumin yayi yana ɗan ja da baya cikin sanƴin jiki.

Cire audugar dake hancin sa DEENAH tayi tana jefarwa tare da faɗin "Idan ma yana raye tayaya zamu sani da wannan abin a hancin sa, i know he isn't dead doguwar suma kawai yayi..."

Grandma ce ta katse ta da faɗin "What are you doing DEENAH?, likitoci sun tabbatar mana da cewa Boy baya..."

"They are liars, babu abinda suka iya, ni mijina bai mutu ba, mu ɗan jira zuwa anjima kaɗan zakuga ya tashi."

Shiru Grandma tayi mata tausayin ta na kama ta, ita kanta jurewa kawai takeyi, amma dai abin da duba.

Cikin dashewar murya sarki yace "Azo a kaishi."

Ɗagowa DEENAH tayi tana kallon sa kafin ta shiga nodding kanta tana kare shi daga mutanen dake zuwa da niyyar su ɗauke shi ɗin.

"No... no... no please, kada ku tafi dashi bai mutu ba, dan Allah ku kyale ni wallahi bai mutu ba, babu ta yadda za'ayi ace ya mutu, let go of me" ta faɗa tana kwacewa daga hannun wadanda suka riƙe ta ɗin tabi bayan su da gudu.

Da sauri YAZEED ya taro ta, fuzge hannun ta tayi daga riƙon da yayi mata cikin 6acin rai kuma take faɗin "Let go of my hand, you're happy now aren't you?, i know kafi kowa murna da mutuwar sa though nasan bai mutu ɗin ba, duk soyayyar nan da kake nuna masa ba na tsakani da Allah bane, ashe kana ɗaya daga cikin maƙiyan sa masu son ganin bayan sa..."

"DEENAH..." Grandma ta katse ta.

Ba tare da DEENAH tayi shiru ba ta cigaba da faɗin "Don't stop me Grandma, you saw it ai, kema kinsan abinda ya aikata, dah ace yayi responding a wannan lokacin then maybe Allah ya taimake mu mu iya ceto rayuwar sa, but what did he do, ya nuna cewa bai damu da ɗan uwansa ba, sannan dukkanin wata soyayya da yaye yi masa was all fake."

"Stop it now" cewar Hafeezah cikin tsawa tana ƙarasowa inda suke kafin ta ɗaura da faɗin "How dare you accused YAZEED of your husband's death, wa ya baki gut ɗin yi masa magana in such a manner?, ki kiyaye harshen ki or else..."

Ba tare da tsoron komai ba tace "Or else what, what will you do, nima kashe ni zakuyi, well then why don't your just go ahead sabida na tabbata nice next target ɗinku, but i will make sure that kun girbi dukkanin wani abinda kuka shuka, ran Abyad ɗina ba zai ta6a tafiya a banza ba, you must all paid a heavy price for his death this is my promise to you, i will make sure you all regret it."

A tsawace Hafeezah tace "Take this mad girl out of my sight, akan mijin ki aka fara mutuwa ne kokuwa?, mijin ki ya mutu ne ba tare da an gano abinda yayi silar mutuwar sa ba, hakan na nufin lokacin sa ne yayi, no one is to be blamed for his death."

"You're all to be blamed, you monsters, you will all regret this i promise."

"Watch your tongue DEENAH, ashe haka kike bakida tarbiyya, Ummie need to be respected..."

Katse Sairah tayi da faɗin "This woman here means nothing to me da har zanyi respecting ɗinta, she is nothing but a devil..."

"DEENAH" Grandma ta kira ta tana zuwa taja hannun ta su fara tafiya.

Dukda haka bakin DEENAH bai rufu ba take faɗin "I know you're all behind this, and i will make sure you all regret it."

"She is totally out of her mind, how dare her" cewar Hafeezah.

YAZEED da jikin sa yayi matuƙar sanƴi kallon tuhuma yayi wa mahaifiyar tasa, bai ce dasu komai ba yaja ƙafar sa ya fice daga fadar, zuciyar sa na matuƙar zafi sosai koh kaɗan maganganun DEENAH basuyi masa zafi ba dukda baisan akan mai take basa laifin mutuwar ZEEYAD ba.

Yana fita yaji an fizgo shi zuwa wani lungu.


Kallon Hafeezah Nazeerah tayi tace "How cruel Hafeezah" tana faɗin haka itama ta bar cikin fadar ƴaƴan ta suka mara mata baya ya saura Hafeezah, JALILAH, Sairah da kuma Rahinah.

Mugun kallo Hafeezah ta watsawa JALILAH da fuskar ta yake sha6e-sha6e da hawaye kafin ta daka mata tsawa da faɗin "Ke kuma mai kikeyi tsaye anan, zaki iya ficewa ki bisu banason shashancin banza."

Da sauri tayi hanƴar ficewa daga fadar.

Ajiyar zuciya Sairah ta sauƙe kafin tace "Wow so finally, nice nan zan zamto matar sarki, i can't wait to see that day."

Murmushi Hafeezah tayi kafin tace "Hakane, but first we will have to get rid of this so called JALILAH sabida ke kaɗai nake buƙata ki kasance mata ga YAZEED."

Murmushi tayi kawai tana ta saƙe-saƙen abinda zatayi cikin ranta.


**********************


________DEENAH ce rungume da Grandma, a yanzu kam kukan zuci kawai take, sosai yanayin ta ya canza, bata iya koh da kwakkwarar motsi ne daga inda take zaune, sosai takejin ta so empty, she can't believe wai ZEEYAD ɗinta ya mutu, sai dai kuma dama Ubangiji maɗaukakin Sarki da kansa yace dukkanin mai rai mamaci ne, zai ɗauki ran wanda yaso a lokacin da babu wanda yayi tsanmani haka kuma ya raya wanda yaso a lokacin da kowa ya cire rai da samun lafiyar sa, ya kan ɗauki ran bawa ba tare da yayi koh da ciwon kai bane, wannan shi ake kira kana naka Allah na nashi, sai dai ita har yanzu tanaji a jikin ta ZEEYAD bai mutu ba, sai dai kuma dole ne tayi haƙuri tunda har zuwa wannan lokacin ba'a zo mata da labarin bai mutu ba, hakan na nufin dagaske ya mutu ɗin kenan, ba zata kuma sake ganin sa ba har duniya ta naɗe, runtse idanu tayi sakamakon wani kukan da yazo mata, gimtsewa tayi kasancewar Grandma ta hana ta yin kukan.

Sosai takejin zazza6i da wani irin hajijiya dukda a zaunen take, ji tayi zuciyar ta na tashi tanajin amai na zuwa mata.

Miƙewa tayi da sauri tana faɗawa toilet ɗin ɗakin Grandma ɗin ta shiga kwaro aman wanda duk ruwa ne ma kasancewar babu abinda ta sanƴa a cikin ta tun safe.

Riƙo ta Grandma da ta biyo ta cikin tashin hankali tayi ta shiga jero mata sannu.

Wanke bakin ta tayi kafin ta riƙo ta su dawo cikin ɗakin.

Ji tayi ba zata iya zama ba dan haka kwanciya tayi tanajin yadda jikin ta ke rufuwa da zafin zazza6i.

Sosai Grand ɗin ta sake shiga wani tashin hankalin kuma, babu abinda take jerowa DEENAH sai sannu cike da damuwa.

********************

_______"What are you saying?."

"I mean he isn't dead, i saw him moving his eyes at the hospital, it was indeed a miracle coz gwaji na farko da nayi masa ya tabbatar min da cewa ya mutu, but by the time da na lura da cewa ya motsa idanun sa na sake running wani test ɗin only to find out that he is still alive."

"You know this kuma ka bari aka kaisa makwancin sa?."

"Yes i know it, but i decided to keep it a secret hakan ya sanƴa ni yi masa allurar da zai sanƴa shi unconcious for 8hrs, so ba zama zamuyi yanzu ba we've to find a way na ganin mun tono sa before he gets suffocated, i thought that yaga wani abu before incident ɗinnan hakan ya sanƴa ni keeping this as a secret har sai munji daga garesa."

"Then what ate we waiting for?, we should get him back now."

"The problem is that masu gadin maƙabartar,ya zamuyi dasu?."

"Leave that to me, kai kuma kaje ka fara shirye-shiryen komai tukun."

"Yes" ya faɗa kafin duk su fice.


**********************


*TWO DAYS LATER*


________Wasu irin zafafan hawaye ne suka shiga zubowa Grandma a ƙunci sakamakon result ɗin DEENAH da ya fito.

Kallon DEENAH dake kwance kan bed hannun ta ɗaure da drip tayi tana sake maida duban ta cikin papern hannun ta.

Kallon ta Umma dake zaune gefen ta tayi tace "Lafiya dai koh, meke damun DEENAH?."

Miƙa mata result ɗin tayi nan ta amsa itama ta shiga karantawa.

Jikin ta ne yayi sanƴi sosai itama tana tausayin DEENAH ɗin dama kuma tausayin yadda rayuwar ɗan dake cikin ta zai kasance babu mahaifi.

"DEENAH nada juna biyu na tsawon sati biyu" cewar Grandma cikin muryar kuka.







*YAWAN COMMENT, YAWAN TYPING*








*MHIZZ JIDDHERR.................✍🏽*
[9/5, 9:01 PM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D*
```[The Abandoned Prince]```






*NA*
*JIDDAH BINT MUHAMMAD*






*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*






*052...*




_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_



_________Bayan kwana uku aka sallami DEENAH daga asibiti suka koma gida.

Sosai take samun kulawa daga both gurin Grandma dama kuma Umma, suna dukkanin ƙoƙarin su na ganin sun kasance kusa da ita a kullum tare da bata kyakkyawar kulawa duba da ƙaramin cikin dake jikin ta.

DEENAH kuwa tunda ta gano tana da ciki ta rage yawan damuwa da ƙunci tare da wallafawa Allah komai koh dan lafiyar abin dake cikin ta, dan kuwa dashi ne kaɗai zata dinga tuna ZEEYAD ba zata so wani abu ya sami cikin nata ba shiyasa a kullum take takatsantsan ɗin ganin ta kula mai kyau.

Babu wanda aka sanarwa da DEENAH nada ciki sai mai Martaba kaɗai da ya sani sai kuma Sadeeq dasu Grandma koh dan gudun kada maƙiya su kawo mata farmaki su sanƴa cikin nata a gaba.

Bayan ta gama takaba lokacin cikin nata har ya ɗan fara bayyana Umma ta nemi ta koma da ita, sai dai fur Grandma ta katse ta tsare babu inda za'a je mata da DEENAH, ita kaɗai take gani taji sanƴi a ranta ga kuma cikin ZEEYAD dake jikin ta dan haka babu inda DEENAH zata je tana nan tare da ita.

Ganin yadda Grandma tayi ta kuka ne ya sanƴa Umma haƙura ta bar DEENAH tunda taga ita kanta DEENAH ɗin batason tafiyar, hakan ya sanƴa ta haƙura tare da yarjejeniyar idan cikin DEENAH ya kai watanni bakwai zata zo ta ɗauke ta idan yaso sai ta haihu achan.

Ba dan Grandma taso ba ta yarda da hakan koh dan maƙiyan da yaron zai samu ma.


DEENAH ce zaune a ɗaki rungume da hoton ZEEYAD a ƙirjin ta tana kallo, yayin da hawaye suka wanke fuskar hoton.

Grandma ce ta zame hoton daga rungumar da tayi tana buɗe wani drawer ta sanƴa shi kafin ta zauna gefen DEENAH ɗin tana faɗin "DEENAH, yakamata ace kinyi haƙuri haka nan sannan kuma ki san da cewa kukan ki ba zai ta6a dawo da mijin ki ba, kefa kikayi min alƙawarin kin daina sanƴa damuwa a ranki, koh dai so kike hakan yayi affecting abin dake cikin ki ne?."

Saurin girgiza mata kai DEENAH tayi wasu hawayen na sake biyo mata ƙunci.

"Toh muddin bakyason hakan ya faru then yakamata ace kin bar sanƴawa ranki damuwa haka nan, kinji koh?."

Jinjina kai DEENAH tayi tana share hawayen fuskar ta, murmushi Grandma tayi tace "Koh kefa, toh kiyimin murmushi mana na gani."

Murmushin da ya tsaya mata iya le6e ta ƙaƙaro tayi, nan Grandma tace "Masha Allah, bari na kawo miki abinci kici kisha maganin ki sannan ki koma bacci ki huta, kinji?."

"Toh" kawai ta bata amsa, nan Grandma ta miƙe ta fice daga ɗakin, da kallo DEENAH ta bita kafin ta ɗan miƙe akan bed ɗin tana shafo cikin nata.


**********************


_________Tsaye sukayi akansa yayin da kuma wani Malami ya sanƴa shi gaba da alama dai magani yakeyi masa.

YAZEED ne ya kalli Sadeeq yace "Are you sure wannan malamin ya san aikin sa, it's been a month kenan da yake ta fama but har yanzu babu wani labari, kullum excuses daban-daban yake kawo mana."

Shiru Sadeeq yayi kafin kuma yace "Na fara tantama, but mu sake bashi nan zuwa gobe mu gani, indai bai samo wani kwakkwaran solution ba then sai mu canza wani malamin."

"But a'ina zamu samo shi?, you know bamason kowa ya san da cewa yana raye hakan ya sanƴa mu ɗauko sa nan wurin."

Shiru Sadeeq yayi kafin kuma yace "I guess zan sanarwa da Abhi ɗina, na tabbata zai samo mana solution."

"No, what if kuma ya sanarwa mai Martaba fah?."

"Am sure ba zai faɗa masa ba, zan sanar dashi da dukkanin abinda muka tsara."

Jinjina kai kawai YAZEED yayi dai-dai lokacin da mai maganin ya ɗago ya dube su yace "Ku ɗan sake bani lokaci, aljanin dake cikin jikin sa ba ƙaramin takadiri bane, na tabbatar idan muka cigaba da dagewa da yi masa magani zai farfaɗo da izinin

Please Login or Register in order to submit comment