Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

haka?" cewar Kiki tana kallon Sarauniya Naseeba da mamaki ya gama shanƴe ta ta kasa koh da ƙifta idanun ta ne daga bin inda suka bi da kallo.

"Ban fah gane ba, he became so mad and angry da ganin hawaye kan fuskar yarinƴar nan, meke faruwa ne?" faɗin Kiki ɗin cikin nazari.

Barin fadar Sarauniya Naseeba tayi inda Kiki ɗin tayi saurin mara mata baya.

JALILAH ji tayi jikin ta yayi sanƴi, zuciyar ta fal cike da tunanin abinda ya faru anan.

Sadeeq kuwa jan jikin sa shima yayi ya bar cikin fadar, he can't believe wauta irin na ZEEYAD da DEENAH, yanzu dole zuƙatan mutane dayawa ya cika da zargi kala-kala.


*****************

______"It's alright DEENAH, stop crying please" ya faɗa idanun sa kan fuskar ta da ta kasa barin kukan har yanzu.

"Just...just ka kaini wurin Umma ta, where is she?."

"I guess tana tare da Grandma a part ɗinta."

"Take me to her, i don't wanna stay here any longer" ta faɗa cikin goge hawayen fuskar tata.

Kallon ta kawai ZEEYAD yake cike da tausaya mata, yasan halin Sarauniya Hafeezah zatayi fiye da abinda tayi wa DEENAH a yanzun, but ta wani 6angaren kuma zuciyar sa cike take da haushin YAZEED da ya bari mahaifiyar sa ta ciwa DEENAH mutunci a gaban ɗumbin jama'a.

Cupping fuskar ta yayi yana share mata hawayen yace "Stop crying DEENAH."

Cire hannun nasa tayi daga riƙon fuskar ta da yayi tana faɗin "Ka kaini wurin Umma ta."

"Listen am sorry for not been around lokacin da ake ci miki zarafin nan."

Kallon sa tayi tace "Koh kana nan ɗinma what can you do, is she not your Mom?, you can't do anything."

Kallon ta yake yadda take maganar cikin kuka tana share hawayen ta.
Ɗan murmusawa yayi kafin yace "No she isn't my Mom."

Tsagaitawa tayi da goge hawayen nata tana kallon sa.

"She is YAZEED's Mom and my Stepmom" ya sake faɗa.

"Where...where is your Mom then?."

Shiru yayi yana kallon ta kafin ya ɗan kauda fuskar sa yana cize lips nasa.

"Tell me" ta sake faɗa tana kallon sa.

"I only have my Grandma and... Dad maybe."

Ji tayi jikin ta yayi bala'in sanƴi, cikin calm voice tace "Am so sorry for your lost..."

"Don't be sorry please, nobody is meant to stay in this world permanently, just pray for her."

Kai ta jinjina masa tace "Allah yasa tana makoma mai kyau."

Kai ya jinjina mata kawai cikin murmushi.

"We should go to your Mom" ya faɗa yana buɗe murfin motar da suke ciki.

Saurin riƙo hannun sa tayi, hakan ya sanƴa shi tsayawa kallon ta, maido ƙofar yayi ya rufe.

Kai ta girgiza masa tace "Tell me more about you, i need to know who you really are, and how you end up being a homeless person back then, and how you turned to be so rich and Famous like this."

Murmushi yayi yana riƙo hannayen ta yace "I will tell you everything, but not now."

"Har sai yaushe then?, we are living tomorrow Morning and you don't want to tell me anything about what you are."

Kallon ta yake cikin murmushi, nan yace "Why do you want to know everything about me?."

"Never mind" kawai ta faɗa tana ƙoƙarin buɗe murfin motar yace "Listen..."

Juyowa tayi tana kallon sa nan yace "I will tell you what you wanna hear."

"Tell me" ta faɗa tana kallon sa.

Kallon cikin idanun ta yayi kafin ya buɗi baki cikin calm muryar sa yace "I love you DEENAH."

Ji tayi zuciyar ta ta wani irin bada sauti da jin abinda ya furta, kallon sa kawai take idanun ta na tara hawaye.

A fusace ta buɗe motar ta fice ta fara tafiya cikin sauri tana goge hawayen fuskar ta.

Buɗe motar yayi shima ya fito da sauri yana mara mata baya tare da kiran sunan ta "MADEENAH?" sai dai taƙi tsayawa sai ma tafiyar tata da take haɗawa da ɗan gudu.

"What, why is he after her, mai kuma sukeyi a cikin motar tunɗazu?" cewar Kiki tana kallon Sarauniya Naseeba da kanta ya gama ƙullewa.

Mugun kallo ta watsawa Kiki kafin tace "Dallah ki rufemin wannan ru6a66en bakin naki, da wanne kikeson naji, i thought koh JALILAH yakeso but...but sai naga kuma kamar he is into this girl wacece itama tukun, kuma daga ina take?."

"Are you sure sonta yake, itace fah yarinƴar da ɗan uwansa ke son gabatarwa matsayin wacce yakeso, does that mean..." shiru tayi tana waro idanu cikin murmushin munafurci.

"Ki lalla6a ki bisu, ki ganemin mai ke tsakanin su."

"Angama ranki ya daɗe" ta faɗa tare da ɗan jawo mayafin kanta yana rufe mata fuska ta fice daga inda suka la6e ɗin.


******************

_________"You have to believe me Okay?, kowa shaida ne, yarinƴar da kakeso is having an affair da wannan yaron da kake ƙira ɗan uwanka, he is cheating on you tare da wacce kakeso."

A fusace ya miƙe tsaye yana nuna mata hanƴa yace "Get out, just move yourself of my sight please, you think zan yarda da dukkanin abinda kika faɗa ne, babu wani abu da zaki sake faɗamin na yarda dashi, waye baisan koh ke wacece a wannan PALACE ɗin ba?, bakida wani aiki sai haɗa husuma da tada ta, just move out please i don't even want to see you face" ya faɗa cikin tsananin fushi yana juya mata baya.

Murmushi Sarauniya Hafeezah ta saki kafin tace "I don't care koh ka yarda koh kada ka yarda wannan damuwar kace, aure ne dai da kai da wannan yarinƴar babu shi dan haka kayi gaggawar cire ta daga cikin ranka, dan kuwa muddin ina raye ba zata ta6a zama matar ka ba."

YAZEED ji yayi kamar ya saki kuka dan jin muryar ta kamar ana gasa masa zuciyar sa yakeji, ya tsane ta gabaɗaya, babu yadda ya iya ne kawai, shiyasa yake ɗaga mata ƙafa a matsayin ta na mahaifiyar sa.

"Mai zai hana ka nemi inda yake yanzun ka tabbatar da abinda nake faɗamaka da idanun ka, sabida ɗaukar ta yayi suka fice daga fadar kamar yadda baiji kunƴar rungumar ta a gaban mutane ba."

Runtse idanu YAZEED yayi yanajin kamar ya shaƙo mahaifiyar tasa koh zaiji sauƙin abinda yakeji cikin zuciyar sa.

"Alright, naji just get out please" ya faɗa ba tare da ya juyo ya kalleta ba.

"Zan fita, sai dai ina mai sake tabbatar maka da cire yarinƴar nan a zuciyar ka would be the best for you" tana faɗin haka ta fice daga ɗakin nasa.

Zuwa yayi ya sanƴa key a ɗakin yana komawa da bakin bed ya zauna tare da dafe kanshi.

Shi ya san munafurci irin na mahaifiyar sa, zata iyayin komai dan ganin ta raba shi da DEENAH tunda har ta nuna bata ƙaunar ta, yasan tunda ZEEYAD yazo ya tafi da DEENAH zai kula da ita sannan ya kwantar mata da hankali, munafurci ne kawai irin na mahaifiyar sa sabida kawai tana son haɗa shi da ɗan uwansa.

Tashi yayi ya fice daga ɗakin zuwa neman ZEEYAD ɗin.


******************

_______Duk inda Sadeeq zai zaga neman abokin nasa ya zaga sai dai bai ga koh da mai kama dashi bane, ya kira sa a wayar ma baya ɗagawa.

Shi dai burin sa bai wuce kada ZEEYAD ya kwafsa ya kasa danne kishin da yake wa DEENAH a gaban mutane ba, har a gane da akwai wani abu a tsakanin su.

Part ɗin Grandma ya wuce anan ya tadda ta da Umma da wasu matan suna hirar su basu ma san abin dake faruwa ba.

Ganin sa ya sanƴa Grandma cewa "Mai Martaban ya fito ne?."

Kallon su yayi duka kafin ya girgiza kai yace "A'a, bayajin daɗi dan haka ba zai sami damar fitowa ba."

"Subhanallah, meke damunsa haka?."

"Jinin sa ne ya hau but he is fine now, sabida ya koma bacci ma."

"Toh masha Allah, su Boy ɗin kuma fah?."

Shiru yayi kafin kuma yace "Suna chan duka, dama nazo sanar daku ne cewa ba zai samu damar fitowa ba."

"Toh ai shikenan, gara da ka sanar damu kam, wai mu nan duk shantaƙewa mukayi muna jiran fitowar sa kafin mu koma chan ɗin."

"Bari naje na same su ni" ya faɗa yana ficewa ba tare da ya jirayi cewar su ba.

Da kallo Umma dake jin wani iri ta bisa kafin kuma ta kawar da dukkanin wasu negative thoughts suna cigaba da hira da Grandma dake ta zuba musu surutu.


*********************


_________Tadda ita yayi zaune ta kafe wuri ɗaya da idanu dan haka ƙarasawa yayi yana durƙushewa a gaban ta.

Ɗagowa tayi da idanun ta tana kallon sa kamar yadda shima yake kallon ta, nan tace "You're Playing with my emotions, you love me and yet ka haɗa ni da ɗan uwan ka, kasan ba zaka iya jurar gani na tare dashi ba then maiyasa tun farko ka kawo shawarar amincewa da soyayyar sa, yin hakan tamkar cutar da zuciyar sa ne, sabida shima yana sona, ya kake tunanin zaiji a zuciyar sa bayan ya gano cewa ba shine a zuciya ta ba kuma na amince masa, i can't do this anymore, you've to tell everyone the truth or else am living you forever" ta faɗa tana haɗa kanta da guiwa ta cigaba da shessheƙar kukan ta.

Kallon ta kawai ZEEYAD yake dakyar ya buɗi baki yace "DEENAH please, stop crying, it hurts to see you sad."

A fusace ta ɗago tana kallon sa tace "I won't stop crying, why do you even care?, you're nothing but a pain to my life, i wish ban ta6a haɗuwa da kai, am suffering, can't you see that?, i have waited for you all my life only to see you with another girl kana claiming cewa ita zaka aura, and now kazo ka sake sani gaba cewa kana sona, kai wane irin mayaudari ne?, maiyasa ba zaka so mutum ɗaya ba, kai koh kunƴar ƙarya ma bakayi zaka zo ka wani cemin kana sona, you're a liar, and i hate liars, shigowar ka rayuwa ta bai ƙare ni da komai ba sai ƙunci da baƙin ciki a kullum, stop pretending cewa kana sona, i know baka sona kuma baka ta6a sona ba, indai kana sona da gaske ba zaka ta6a aikata abinda kayi ba, you think ni banida zuciya ne da zaka dinga yimin wasa da hankali?, just stop staring at me and get lost from my sight" ta ƙarashe cikin kauda kanta daga kallon sa.

Shiru yayi yana kallon ta sabida yasan yayi kuskure, sannan baisan ta yadda zai fara bata haƙuri ba, dan kuwa baya tunanin zata fuskance shi ma.

Sunkuyar da kansa yayi yace "I have never loved any girl bayan ke."

Bata kallesa ba haka kuma bata tanka masa ba.

"I never thought zaki zamto wata 6ari na jiki na, you're my first love DEENAH, after all abubuwan da suka sha faruwa a baya ban ta6a manta ki ba daidai da minti ɗaya, i may pretend like am okay, but deep down am suffering from rashin ki a kusa dani DEENAH, and JALILAH i like her because tana da zuciya mai kyau and a kullum Grandma bata da wani zance da ya wuce na ganin ta haɗa ni aure da ita, my Grandma means alot to me so ba zan iya musu akan duk wani abu da ta yanke a gareni ba, i never thought kece yarinƴar da YAZEED yake magana akai kullum, and bayan na gano hakan i thought the best kyautar da zanyi wa ɗan uwa na shine sadaukar da soyayyar da nakeyi miki a gareshi, but i later found out irin kuskuren da na tafka, you're my Happiness DEENAH, you mean everything to me, i just couldn't imagine life without you, you showed me love a lokacin da kowa bayason na ra6e shi, bakiji kyankyami na ba a lokacin da nake yawo a titi, you've a good heart wanda a kullum burin ki bai wuce kiga naci na ƙoshi ban kwana da ƴunwa ba duk kinyi hakan ne ba tare da sanin cikakken koh wanene ni ba, baki damu da zan iya cutar dake koh akasin haka ba, DEENAH... I thought bayan rabuwar mu ta farko dake ba zan sake tunanin ki ba, but things turned out to be the Opposite, you're always on my mind wanda hakan ke sanƴa ni zana hoton ki a duk lokacin da nake zaune bana komai, kuka na yazo ƙarshe ne after 8yrs da rabuwar mu bayan na haɗu da yayan ki Jafar, trust me DEENAH baki ta6a barin zuciya ta ba koh da na minti ɗaya ne...I love you DEENAH, and i promise to always" ya ƙarashe cikin ɗago da jajayen idanun sa yana sauƙe su cikin nata da ta kafe shi dashi tana kallo tunda ya fara magana.

Kallon juna suke for about 1min, DEENAH batasan sadda wani irin light murmushi yayi forming kan fuskar ta ba "You... Really do?" ta faɗa still tana kallon nasa.

"Forever" ya faɗa.

Hannu tasa ta rufe fuskar ta da tafukan hannayen ta, yes yayi gaskiya tabbas kalmar *Inason ki* shi ta daɗe tana biɗa tare da tsumayin ji daga gareshi, ta rasa wace iriyar farin ciki yakamata tayi, jin komai takeyi tamkar a mafarki ba gaske bane ya furta mata kalmar so da bakin shi, sai dai kuma kafin ta kai ga farin ciki, ya zatayi da innocent bawan Allah YAZEED wanda shima ke sonta tamkar ran shi?

Zai sake kula ta kuwa, tunda har mahaifiyar sa ta ɗau alwashin tsine masa muddin yayi hakan, kokuma zata tsaya ne taji daga gareshi kafin ta sakarwa Abyad ɗinta?

Wadannan sune tunanin da suka yi mata ƙawanƴa cikin kwakwalwa, nan kuma tayi saurin kau dasu tana buɗe fuskar ta.

Mamaki ne ya cika ta ganin baya nan, waige-waige ta hau yi koh zata ganshi sai dai babu shi babu alamun sa.

A hankali ta furta "Am i dreaming?."

"No" taji an faɗa saitin kunnen ta.

Saurin juyowa tayi a ɗan firgice tana kallon sa tace "You scared me."

Murmushi yayi ganin yadda ta shagwa6e fuska, wata ƴar doguwar flower mai kyau ya ciro yana nuna mata.

Amsa tayi cikin murmushi tana kallon flower ɗin.
"You like it?" ya faɗa yana kallon ta.

Kai ta jinjina masa cikin murmushi tace "I love it."

Jerawa sukayi tare suka fara tafiya yayin da take jujjuya flower ɗin a hannun ta.

Part ɗin Grandma suka nufa anan suka tadda kowa tsaye, nan duk kallo ya koma kansu.

"Glad you're here, where have you been, tunɗazu ake neman DEENAH zasu tafi" cewar Sadeeq.

DEENAH kallon YAZEED dake tsaye yana kallon ta tayi, kafin tayi saurin sadda kanta ƙasa tanajin babu daɗi sosai a cikin zuciyar ta.

"Inaga mu zamu tafi, tunda gasu nan sun dawo" cewar Umma cikin murmushi tana kallon Grandma.

"Sure dear, ku jira i have something to gift DEENAH" kallon JALILAH dake tsaye tana bin ZEEYAD da DEENAH da kallo tayi kafin tace "JALILAH dear, kije ɗaki na ki ɗauko wannan abin nan, am sorry DEENAH jikin mai Martaba ɗin yau babu daɗi, da kaina zan je har chan Nigeriar taku na taho dake idan an tashi yin baiko."

Murmushin yaƙe kawai DEENAH ta iya yi jikin ta na yin sanƴi.

Ba'a daɗe ba JALILAH ta dawo da wani ƙaton kwali anyi wrapping ɗinsa.

Murmushi Grandma tayi tace "Ki baiwa DEENAH, nata ne, kyauta ce daga gareni ki amsa kinji koh?."

Murmushi DEENAH tayi tana amsar kwalin daga hannun JALILAH tace "Jazakillahu Khair Grandma."

"Kada ki wani ji damuwa ƴar nan, yakamata ku wuce haka nan dare nayi, gashi kuma kunce da safe jirgin naku zai tashi, muje haka nan."

Nan duk suka fice daga part ɗin Grandma ɗin.

Kallon driver ɗin da zai ja motar ZEEYAD yayi yace "I will drive the car."

Babu musu ya miƙa masa key ɗin.

YAZEED so yake yayi wa DEENAH magana sai dai yana tsoron bakin mahaifiyar sa, dan haka kallon Umma yayi yace "Thank you so much for your time Aunt, we really appreciate it."

Murmushi Umma tayi tace "Mune da godiya" tana shigewa motar da aka buɗe mata ɗin.

"Nima zanje" cewar JALILAH.

Kallon ta ZEEYAD yayi yace "Maybe you don't have to."

"A'a ka barta mana taje, ai kaga ka sami abokiyar hira idan ka tashi dawowa koh?."

Murmushin yaƙe kawai yayi yace "Alright."

Buɗe gidan gaban tayi ta shiga, dan haka DEENAH zaga wa tayi ta ɗayan 6angaren tana zama kusa da Umma.

Sosai suka sake yiwa juna sallama, kafin yaja motar ya bar gidan.

**************

__________A cikin ƙatuwar hotel ɗin da suka sauƙa yayi parking motar inda duk suka buɗe suka fice.

Booth ɗin motar ya buɗe DEENAH ta ɗauki tsarabar da Grandma tayi mata, kafin ya maida ya rufe fuskar nan tata a matuƙar tsuke.

"Why are you sad?, i don't like seeing you like this."

Banza tayi dashi ta nufi wurin Umma ta tsaya.

Zuwa yayi cikin murmushi yace "Thank you so much Aunt."

Umma da jikin ta yayi sanƴi sosai ne tace "Listen...am sorry for..." bai bari ta ƙarasar ba yace "Come on Aunt... don't said anything please."

Shiru tayi tana kallon sa, murmushi yayi yana kallon DEENAH yace "Bye."

Ji tayi duk batason tafiyar tasa, dan kuwa batasan yaushe ne zasu sake haɗuwa ba, gimtsa fuska tayi idanun ta na tara hawaye, ganin ya shige motar shi da JALILAH.

Sosai takejin wani irin kishi na taso mata, har yaja motar ya bar wurin.

"Muje" faɗin Umma tana yin gaba, nan ta mara mata baya suka koma apartment ɗinsu.






*Yawan Comment, Yawan Typing*







*MHIZZ JIDDHERR.............✍🏽*
[8/15, 9:45 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D*
```[The Abandoned Prince]```






*NA*
*JIDDAH BINT MUHAMMAD*






*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*






*042...*





_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_






*LOVE IN THE AIR🎈❤‍🔥🤸🏽‍♀️*






__________A gajiya ta tashi sabida isasshen baccin da bata samu ba jiya da dare.

Addu'ar tashi daga bacci ta karanto kafin ta rarrafa ta sauƙa daga kan bed ɗin tana zuwa ta kunna wutar ɗakin.

Bathroom ta faɗa ta iyo alwala ta fito, sallahr Asuba tayi, bayan ta idar ne tayi Adhkar ɗinta tare da ɗaurawa da karatun ƙur'ani.

Miƙewa tayi bayan ta idda kafin ta buɗe ƙofar ɗakin nata ta fice.

Ɗakin Umma taje ganin ta zaune kan sallaya ya sanƴa ta komawa idan ta idar ta dawo.

Ɗakin Jafar ta leƙa nan dai taga shima bai dawo daga masallaci ba.

Falo ta dawo tare da yaye curtains ɗin falon duka ta cire su, kasancewar gidan bai sami isasshen gyara ba kwana2 da sukayi basa nan, hakan ya sanƴa ta yanke shawarar yin sanitation.

Bayan ta cire labulayen ne duka kuma ta nufi toilet ɗin falon dasu, tare da sanƴa su cikin washing machine, fitowa tayi ta hau nannaɗe carpet ɗin falon, ganin yayi nauyi sosai ba zata iya bane ya sanƴa ta bari kawai ta nufi kitchen.

Ƙofar da ya fita ta cikin gida ta buɗe a kitchen ɗin nasu kafin ta hau fidda kayayyakin ciki, har ta gama.

Sai da ta fara gyara store ɗin ta maida komai steady abubuwan da ba'a buƙata ta fiddo su kafin ta hau gyaran kitchen ɗin, wanke fridge ɗin kitchen ɗin tayi ya fita ƙal, kafin ta goge sauran abubuwan da ba za'a iya fiddawa ba, sannan ta wanke ƙasan kitchen ɗin tass ta fice.

Ruwa ta tara a famfo kafin ta hau wanke dukkanin utensils da items ɗin da ta fiddo, tana cikin wankewa ne Umma ta leƙo ta kitchen ɗin tana kallon ta.

Shagwa6e fuska tayi tace "Allah sarki Umma na kitchen ɗin fah bai gama bushewa ba."

Murmushi Umma tayi tana kallon ta tace "Yau kuma da aiki aka tashi, toh sannu Allah yayi miki albarka."

Cike da jindaɗi tace "Aameen Umma na, Umma kije dan Allah kafin nan kitchen ɗin ya bushe."

"Allah ya huci zuciyar ki, kinga tafiya ta ma" ta faɗa tana barin cikin kitchen ɗin.

Aikin ta ta cigaba dayi, har sai kusan ƙarfe taran safe kafin ta kammala.

Izuwa lokacin sosai ƴunwa ya gama nuƙurƙusar ta, dan haka falon ta dawo ta samu har an fidda carpet da kujerun.

Ɗakin Jafar ta sake leƙawa taga baya nan, nan kuma taga babu carpet ɗin ɗakin sa, kafin kuma taje ɗakin Umma, nan ta same ta zaune.

Shigowa tayi tana zama kusada Umma ɗin tace "Umma ina kwana?."

"Kin tashi lafiya, ya gajiyan ki?."

"Alhamdulillah" ta amsa kafin tace "Wa ya fidda kujeru da carpets ɗin?."

"Yayan ki ne ya kai wurin wankewa bai dawo ba tukun."

"Allah yasa dai bai manta da nawa ba."

"A'a duka ya kai."

"Yauwa, Umma zan gyara ɗakin naki."

Kallon ta Umma tayi tace "Baki gaji bane, kya bari dai anjima ki ƙarasa koh?."

"A'a Umma indai nace zan bari yanzu anjima ba zan iya ba gara kawai na haɗa nayi su kai ɗaya yanzu na huta."

"Toh shikenan, bari yayan naki ya dawo tukun muyi breakfast."

Da "Toh" kawai ta amsa tana kwanciya, runtse idanu tayi jin bayan ta ya wani riƙe yaushe rabon ta da tayi irin aikin nan ta manta tun kafin ta faɗa rashin lafiya.


Da sauri kuma ta miƙe tana zuwa ta janƴo kwalin da Grandma ta bata ta buɗe dan ganin menene a ciki.

Blue ɗin doguwar rigar gown ce mai kyau iriyar wacce taga JALILAH na sawa da takalmi mai kyau sai kuma bangles a ciki.

"Wow, Umma kinga" ta faɗa tana ƙarasowa kusa da Umma.

Kallon kayan Umma ma take tace "Masha Allah sunyi matuƙar kyau sosai."

Murmushi tayi tace "Aikuwa dai sosai."

Ƙarar motar da taji ne ya tabbatar mata da Jafar ɗin ya dawo dan haka tashi tayi ta fice cikin gudu, dan kuwa ba wai sun samu sun gaisa mai kyau jiya bayan dawowar su bane ba kuma ƙaramin kewar sa taji ba.

Cikin farfajiyar gidan nasu ta fita tana nufar inda yayi parking motar.

Buɗe motar yayi fuskar sa washe da murmushi.

"Oyoyo yayana" ta faɗa tana rungume shi.

Farin ciki ne cike fal a zuciyar Jafar ganin ƙanwar tasa ta dawo ainihin ita babu kuma wata damuwa tattare da ita.

"I miss you lil sis" ya faɗa cikin murmushi yana patting bayan ta.

Ɗagowa tayi cikin murmushi tana kallon sa tace "Yaya mai ka samu ne haka sai wani kyau kake ƙarawa kana sake yin fresh" ta faɗa tana shafa fuskar sa cikin murmushi.

Ɗan sosa kai yayi kafin yace "You wanna know, it's a secret but ke kaɗai zan faɗawa and kada ki sanar da Umma, Promise?."

Kallon sa take cikin murmushi kafin kuma tace "Promise" tana tafa hannayen ta da nashi.

Kumatun ta yaja tare da ɗaura hannayen sa kan kafaɗun ta suka fara tafiya, wayar sa ya ciro ya ɗanyi danne-danne kafin ya miƙa mata.

Amsa tayi fuskar ta ɗauke da murmushi yace "Is she beautiful, do you like her?."

Shiru tayi tana kallon hoton tana sake zooming ɗinsa kafin tace "Uhmm....kamata yayi ace ka nemo matar da tafi ƙanwar ka kyau."

Tsayawa yayi yana kallon ta kafin kuma ya kar6e wayar sa yana faɗin "You mean kin fita kyau?."

Kai ta jinjina masa kafin tace "She is just fair in complexion, but look at her nose" ta faɗa tana ta6a hancin ta.

Sake ƙure hoton yayi da idanu kafin kuma yace "Lies there is no way zaki fita kyau, ."

Nan fah suka hau musu tsakanin su kamar wasu yara, inda yake cewa budurwar sa ta fi DEENAH kyau, ita kuma take cewa tafi budurwar tasa kyau.

"Ok, ok, ok, naji let's bait, indai har dagaske girlfriend naka ta fini kyau zan haɗa cake mai kyau ka kai mata, and indai it turns

Please Login or Register in order to submit comment