Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ever stop me from having you as mine, am sending your dear wife inda ba zaka ta6a ganin ta ba, you will live with me a matsayin ita, and we will live a life full of love and care" ta faɗa cikin yin hajijiya tana dariya.

Tsagaitawa tayi kafin ta kuma takowa inda DEENAH ke kwance, hannu ta sanƴa a jikin ta tare da karanto wasu irin makaran tsafi take kuma komai nata ya koma irin na DEENAH, kai kace DEENAH ɗin aka raba biyu.

Murmushi tayi tare da miƙewa tsaye tana kallon DEENAH ɗin kafin kuma ta shiga karanto wasu irin makaran tsafi cike da yaren da ba zaka san koh na menene ba, take wata tsohuwa gijib ta bayyana, kallon Naseeba tayi tare da faɗin "Burin ki ya cika, and now the girl is mine, kin cika alƙawari bani ita akan lokaci kamar yadda kika faɗa" ta faɗa cikin jinjina kai tana kallon DEENAH.

Murmushi Naseeba tayi kafin tace "Take her, take her far awayyy from here, take her to inda babu wani mahaluƙi da zai iya gano ta, yadda zanji daɗin rayuwa da wanda na ɗau shekaru ina begen sa."

Dariya tsohuwar tayi tace "Ofcourse tunda kikayi min abinda nakeso dole nayi abinda kema kika ce, zan ɗauke ta na kaita inda babu wani ɗan adam da ya ta6a taka ƙafafun sa zuwa wurin, ita ɗin sadaukar wa ce garemu dan haka zan ɗauke ta nayi nisa da ita inda duk neman da za'a yi mata cikin duniyar ba za'a gano inda take ba, sai dai kema ki kiyaye sharuɗan da na gindaya miki indai kikayi hakan toh tabbas komai zai tafi dai-dai yadda kowannen mu yaso."

Alamu tayi mata da hannu tana faɗin "Take her tun kafin ya dawo cikin gidan nan."

Murmushi tsohuwar tayi tare da jinjina kai tana kallon DEENAH, wasu surutan ta tayi tana nuna DEENAH da sandar hannun ta take kuma dukkanin su suka 6ace ya saura sabuwar DEENAH wato Naseeba.

Wata iriyar ajiyar zuciya ta sauƙe cike da relief zuciyar ta fal farin cikin burin ta ya cika.

Zubewa tayi kan couch ɗin ɗakin tana sake bin jikin ta da ya zama DEENAH sak da kallo, murmushi tayi tare da faɗin "I can't believe this."

Miƙewa tayi ta koma cikin ɗaki, tare da tsayawa a gaban mirror tana ƙarewa kanta kallo, sake gyara ɗaurin kanta tayi kafin ta sake yiwa fuskar ta kwalliya ɗan kaɗan inda ta fito tare da yin kyau sosai da sosai.

"Uhm what a great day for me" ta faɗa cikin murmushi tana faɗawa kan bed ɗin ɗakin.


*********************

__________ZEEYAD bai tashi dawowa part ɗin nasa ba sai da akayi sallahr la'asar kai tsaye ya wuce cikin part ɗin nasa.

Haurawa sama yayi tare da tura ƙofar falon bakin sa ɗauke da sallama.

Lumshe idanu yayi sakamakon ƙamshin turaren da ya bugo sa, idda shigewa yayi yana rufo ƙofar falon.

Ganin baiji motsin DEENAH bane ya sanƴa shi nufar ɗaki, sai dai wayam yaga bata nan.

Shiru ya zauna dan koh a tunanin sa tana toilet ne, sai dai jin shiru ya sanƴa shi miƙewa yana yin bakin toilet ɗin tare da kwankwasawa a hankali yace "DEENAH?."

Jin shiru ya sanƴa shi sake faɗin "Are you in there?."

Tura ƙofar toilet ɗin yayi ya shige inda ya duba kowane lungu da saƙon ciki yaga bata nan, fitowa yayi wondering koh ina ta shige.

Muryar ta yaji daga cikin ɗakin closet tana faɗin "Abyad kazo ka taimaka min na anan."

"Ohh" ya faɗa a hankali yana ƙarasawa bakin ƙofar kafin yaja ya tsaya yana faɗin "Should i come in?."

"Yes come in" ta faɗa.

Tura ƙofar yayi ya shiga inda ya ganta tsaye ɗaure da towel ɗin da kaɗan ya wuce mazaunan ta.

Juyowa tayi tana kallon sa cikin murmushi, murmushin shima ya saki cike da mamakin ta ba tare da ya iya ɗauke idanun sa daga kanta ba.

Ƙarasowa tayi inda yake tsaye hannun ta ɗauke da doguwar rigar kanti take faɗin "Zip ɗin ya cize, will you please help me ka gyara min shi."

"Sure" ya faɗa yana amsar rigar daga hannun ta, nan yace "By the way, when did you loose your hair" ya faɗa yana kallon gashin kanta dake a tsafe.

Hannu ta kai ta ta6a gashin tare da faɗin "My hair?, ɗazun nan ne bayan ka fita."

Gyara mata Zip ɗin rigar da ya cize yayi yana miƙa mata, amsa tayi cikin murmushi tana kallon sa haɗi da furta "Thank you."

Folding hannu yayi a ƙirji yana kallon ta, nan kuwa ta fara shirin warware towel ɗin jikin ta ba tare da ta kore sa ba, ɗan waro idanu yayi kafin yace "Are you being real?."

"What?" ta faɗa.

Murmushi yayi tare da jawo ta jikin sa yace "I thought zaki kore ni ne."

Murmusawa tayi kafin tace "No why zan kore ka, you're my Husband aren't you, and dukkanin wani abu dangane dani is all yours" ta faɗa cikin shafo lallausar gashin gefen fuskar sa.

Haɗe hancin su yayi guri ɗaya yace "I thought you will wait har sai Grandma ta kawomin ke da kanta, but i can see you're so eager to get this done."

Murmushi tayi tana sake shigewa jikin sa tace "Let's do it now" ta faɗa cikin riko gaban rigar sa.

Shi dai ZEEYAD sosai ya cika da mamakin DEENAH ɗin ganin canzawar ta lokaci guda haka, riƙe hannun ta yayi daga 6alla buttons ɗin rigar sa da take kafin ya kalleta yace "This will be more interesting at night" ya faɗa yana maida su ya rufe, kafin ya ɗan ja hancin ta yace "I will see you tonight, i know Grandma zata iya aikowa any moment from yanzu azo a tafi dake, and nima inason zuwa ganin YAZEED, so make sure you're well prepared tonight" ya faɗa cikin bata peck a gefen kumatu kafin kuma ya fice daga cikin ɗakin ma gabaɗaya.

Da wani irin kallon mugun haushi ta bishi, nan kuma tace "Anyways then, i will wait for you tonight Darling, koh da nan da zuwa gobe kace i will wait, muddin i can have you then banida wata matsala" ta faɗa tana sanƴa kayan jikin ta tare da fitowa cikin ɗakin.


*********************


__________Grandma da kanta ta kawowa ZEEYAD amaryar sa har kan bed ɗinsa.

Sosai ta sanƴawa DEENAH albarka kafin kuma tace "Ni zan barki haka nan, duk wani abinda yayi miki wanda bakiji daɗin sa ba ki kawomin ƙarar shi nikuma zanyi maganin sa kinji koh?."

Kai ta jinjina wa Grandma ɗin kafin kuma tace "Ni na barki cikin farin ciki ƴar nan, Allah ya dauwamar da farin ciki cikin rayuwar auren ku" tana faɗin haka ta fice daga ɗakin tana rufo ƙofa.

Fitar ta keda wuya fake DEENAH ta buɗe fuskar ta dake cikin mayafi tana bin ƙofar da kallo tare da sakin wani irin shu'umin murmushi.

Maida duban ta tayi ga agogon dake manne a ɗakin taga ƙarfe goma saura.

Miƙewa tayi daga kan bed ɗin tana sauƙa ƙasa kafin ta nufi closet room, bata jima ba ta fito cikin wasu irin tsinannun night wears wanda marabar su da babu kucil ne.

Feshe jiki tayi da turaruka masu daɗin ƙamshi kafin ta koma kan bed tana jawo bargo ta rufe a jikin ta tare da faking baccin ƙarya.

Like after 20mins aka buɗo ƙofar ɗakin, sosai ya haɗe cikin shigar sa ta manƴan kaya sai zuba ƙamshi na musamman yake.

Jinginuwa yayi da bakin ƙofar yana kallon ta cike da mamaki ganin kamar har tayi bacci.

A hankali ya shiga takowa bakin bed ɗin yana durƙushewa kan guiwowin sa tare da ƙure kyakkyawar fuskar ta da kallo.

Sai da ya gama kallon ta tsaf kafin ya miƙe yana shigewa ɗakin closet, bai wani jima ba ya fito cikin ƙananun kaya da 3quater wando tare da yin hanƴar toilet, alwala ya ɗauro ya fito kafin ya tako inda take, a hankali ya shiga buga pillow ɗin da kanta yake kai.

Lamo tayi kamar bata ji ba, har sai da yayi ya gaji ya daina.

Zuwa yayi ya kashe wutar ɗakin inda ya rage saura hasken side lamps, suma rage hasken su yayi.

Hawowa kan bed ɗin yayi yana cuddling ɗinta ta baya tare da manna mata sumbata a neck.

Kame jikin ta tayi wani irin farin ciki na nuƙurƙusar zuciyar ta finally yau burin ta zai cika.

Kwanciya ta gyara tana juyowa facing ɗinsa still idanun ta a lumshe kamar mai baccin gaske.

Hannu ta kai kan faffaɗar ƙirjin sa tana rubbing gently, riƙe hannun nata yayi sabida haka kawai yakejin duk wani ta6a sa da tayi ya kanji wani iri a zuciyar sa.

A hankali cikin muryar bacci ta kira sunan sa "Abyad."

Kallon fuskar ta yayi tare da amsa mata da "Um."

Shiru tayi kamar wata iriyar mai magagin baccin nan tana sake shigewa jikin sa.

Rungume ta shi ɗinma yayi yana mai manna mata kiss a goshi tare da rufa musu bargo.



*********************


_________A razane ya tashi daga mafarkin da yayi ɗin, yana dafe kansa da hannuwa bibbiyu, same mafarkin da yake yi kwanaki akan ana tura DEENAH cikin ruwa ya sake yi wannan karon ma.

Addu'a ya karanto sosai cikin zuciyar sa kafin kuma ya ankara da rigar jikin sa dake a tu6e.

Kallon DEENAH dake shar6ar baccin ta cikin kwanciyar hankali yayi wondering koh itace wacce ta cire masa rigar.

Miƙewa yayi daga kan bed ɗin yana faɗawa toilet, fuskar sa ya wanke kafin kuma ya ɗauro alwala ya fito.

Darduma ya shimfiɗa kan chinese carpet ɗin dake ɗakin kafin ya tada sallah.

Sosai yayi sallahr haɗi da karanto addu'oin neman tsari da sauran su, bai idda ba har sai da yaji ana kiraye-kirayen sallahr Asuba.

Miƙewa yayi ya koma toilet ɗin tare da sake ɗauro wani alwalan yana zuwa inda DEENAH ke kwance tare da buga pillow ɗin da take kai.

A hankali ta ware idanun ta akansa, alamu yayi mata da anyi sallah kafin kuma ya juya ya fice daga ɗakin zuwa masallaci.

Da kallo tabi sa kafin kuma ta wani turo baki tana komawa ta kwanta ta cigaba da baccin ta.

ZEEYAD bai dawo ba har sai ƙarfe bakwai bayan rana ta fito, dawowa ɗakin yayi yadda ya barta haka nan ya same ta still tana bacci.

Zuwa yayi ya sake tada ta akan ta tashi tayi sallah, zaune ta miƙe tana wage baki ba tare da ta koh rufe sa ba, gashin kanta duk ya wani barbaje yawa sabuwar mahaukaciya.

Da mamaki fal ransa ya fice daga ɗakin.

Miƙewa tayi tare da faɗawa Toilet, wanka tayi ta fito kawai kafin ta shirya cikin English wears ɗin doguwar riga iya cinƴa mai hannun vest.

Bata damu da ta gyara kan gadon ba ta fito zuwa falon ƙasa, bayin dake ta gyare-gyare t umurci ɗaya da ta kawo mata breakfast yanzun nan kafin kuma ta koma sama.

Buɗe sauran ɗakunan tayi taga baya ciki hakan ya sanƴa ta nufar gym room ɗinsa anan ta tadda sa yana motsa jiki.

Murmushi tayi tana ƙarasawa gun sa tare da faɗin "Good Morning."

Dakatawa yayi da abinda yakeyi tambayar da ya wullo mata shine "Have you prayed?."

"Yeah of course, sorry kana ta tashi na ban farka dawuri ba, na gaji ne sosai shiyasa."

Shiru yayi bai tanka mata ba, sabida sam bai zaci haka halayen ta suke ba, rashin yin sallah akan lokacin sa.

Ganin kamar ransa a ɗan 6ace ne ya sanƴa ta ƙarasawa inda yake tana rungumo sa ta baya.

Sosai yakejin wani iri idan ta ta6a shi, dan haka zame hannayen ta yayi daga jikin sa yace "I need a Morning coffee to warm me up, can you prepared it right away?."

"What, a coffee?" ta faɗa tana kallon sa.

"But i'm the future Queen, how do you expect me to make some coffee for you after all akwai masu aiki dayawa cikin MASARAUTAR nan, am sure they can make a nice one."

"Don't worry then, i will make it da kaina."

"No you don't have to do that, sabida na sanƴa a haɗo mana breakfast."

Da mamaki yake kallon ta kafin kuma ya fice daga ɗakin zuwa ɗayan ɗakin.

Tarar da bed ɗin yayi scattered kamar yadda ya barsa, juyowa yayi ya kalleta kafin yace "Are you that tired that gado ma ba zaki iya gyarawa ba?."

Rolling idanu tayi kafin tace "I guess we should talk about dalilin da ya sanƴa baka bani haƙƙi na jiya da dare ba, bayan munyi da kai cewa we will have alot of fun."

"I need you to answer my question first, why isn't this room tidy DEENAH?."

Shiru tayi tana kallon sa kafin kuma tace "Sabida ban saba ba, sannan kuma dukkanin abinda nakeso yi min shi akeyi."

Mamaki ne ya cika ZEEYAD ganin yadda take maida magana garangatsai haka, shiru yayi mata yana shigewa closet room, nan ma wasu kayayyakin ya tadda a wawwatse an ciro su ba'a maida su gurbin zaman su ba, koh shi nan wasu bayi basu ta6a tsaftace masa ɗaki ba bale kuma DEENAH.

Sosai ya kai maƙura a 6acin rai sabida ya tsani ƙazanta kwata-kwata a rayuwa.

Tarar sa tayi da faɗin "Don't be mad please, the maids are here zasu tsaftace komai."

Kallon ta yayi yace "Bana buƙatar wasu bayi cikin ɗaki na, don't you ever make the mistake of asking them in" yana faɗin haka ya fice a fusace.

Da kallon mamaki ta bisa, she thought yana mugun son DEENAH and ba zai ta6a yin fushi da ita dawuri haka ba, sai dai koh kaɗan hasashen ta bai zamto gaskiya ba, tun jiya ya kasa ta6a ta, duk kuwa iya ƙoƙarin ta na ganin ta kusance shi cikin dare sai dai bai bari hakan ta faru ba, ta rasa mecece matsalan kodai dama bayason DEENAH ɗin ne?, shine tambayar da tayi wa kanta.

Cike da mugun haushi ta hau gyara ɗakin duk bata ma wani iya ba ta dai kwa6a shi ne kawai.


*BAYAN SATI BIYU*


_________Sosai suke samun rashin jituwa tsakanin su, Grandma har mamaki abin yake bata, ZEEYAD kuwa koh kaɗan baisan haka halin DEENAH yake ba, though yayi mamakin canzawar ta but baisan abinda ya faru ta canza all of a sudden ba.

Mai Martaba ne ya gayyace su fada yin Dinner tare dashi da dukkan su family ɗin, zaune ZEEYAD yake DEENAH kusa dashi inda dining ɗin ya ɗau shiru sosai.

Hafeezah ce tace "You should contact Naseeba ta dawo daga tafiyar da tayi haka nan, naga dai bata saba daɗewa idan taje gaida iyayen ta ba, tsananin ta tayi kwana uku but yau har sati biyu kenan."

Tari DEENAH ta saki nan ta kai hannu da sauri tana ɗaukar glass ɗin ruwan gaban ta, hannu na rawa ta kafa akai ta fara sha.

Koh gefen da take ZEEYAD bai kalla ba, Hafeezah ce ta kallesa ganin halin koh in kula ɗin da ya nunawa DEENAH, ta6e baki tayi tana kauda kanta daga garesu.

Amaryar YAZEED ce tace "DEENAH, what's wrong shin kun samu wani matsala ne da mai gidan ki, i thought zai nuna damuwar sa ne ganin rabin zuciyar sa na tari."

JALILAH ƙarasowa tayi tana jan kujera ta zauna da alamu dai fitowar ta kenan, kallon ta Hafeezah tayi kafin tace "What took you so long?."

Kanta a ƙasa take faɗin "Am sorry Ummie, na tsaya gyara ne."

"Gyaran mai, ba akwai maids ba?."

"Actually, nafison nayi gyaran ɗaki na da kaina ne."

Ɗago da idanu ZEEYAD yayi tare da ɗan satar kallon ta kafin ya maida kansa ya sadda zuciyar sa na burning tare da wasi-wasin kodai he chose the wrong person ne ya yada right person ɗin.

Satar kallon sa fake DEENAH tayi ta gefen ido yayin da ta ɗau alwashin sai ta cika burin ta yau akan sa.

Shiru kowa yayi hankalin su kan abincin da suke ci, YAZEED ne ya kwaru inda ya fara tari, saurin miƙa masa ruwa JALILAH dake kusa dashi tayi tana ɗan patting bayan shi haɗi da jero masa sannu, harara amaryar ta wulla mata ta gefen ido tana wani irin tsuke fuska.

Tashi YAZEED yayi ya bar dining ɗin yana cigaba da tarin sama-sama.

Kallon amaryar Hafeezah tayi tace "Sairah kibi mijin naki mana ki bashi kulawa mai kyau."

Yatsine fuska tayi kafin tace "Ba kwana na bane yau."

Kallon JALILAH tayi tace "So kike sai nayi miki magana kafin ki tashi ki bishi?."

Da sauri ta miƙe haɗi da faɗin "Am sorry" tana mara masa baya.

Harara Hafeezah ta gallawa Sairah dan kuwa ta lura koh kaɗan bata ɗaukar hannu.

Miƙewa ZEEYAD ma yayi yana yiwa mai Martaba da bai tankawa kowa cikin su ba sai da safe, kafin ya kalli fake DEENAH yace "Let's go."

Tashi tayi kasancewar ta gama cin abincin tana mara masa baya.

Da mugun kallo Hafeezah ta bisu dan kuwa yanzu tunda ta dawo cikin fada dole ne ta ɗaura daga inda ta tsaya.


*************************


_________Rungumo sa tayi ta baya hannayen ta kan faffaɗar ƙirjin ta.

Shiru ZEEYAD yayi bai tanka mata ba, zuciyar sa sosai take cike da doubts akanta.

"DEENAH?" ya kira ta.

"It's been two weeks rabon ki da kiyi waya da ƴan gidan ku, i have been waiting naji kinyi maganar su but you didn't."

Sake sa tayi cikin kame-kame take faɗin "That isn't something to worry about, gobe zan kira su but we should go to bed now."

Juyowa yayi yana kallon ta nan ya sake faɗin "I need an answer to my question, kodai har kin fara enjoying dukiya kin wofantar da Family ɗinki ne?."

"What are you saying, koh kaɗan ba haka bane?."

"Then tell me your reason, listen DEENAH i have a lot of doubts about you, i really doubt if you are my DEENAH, the DEENAH that i know doesn't act this way, but koma dai menene i will find out."

"What are you saying, nice mana nice DEENAH, i can see that kai ne ka canza completely, ka daina nuna min wata kulawa, kullum kana cikin tsangwama ta..."

"Thats because you're not my DEENAH, DEENAH ta doesn't behave the way you do, i know her and i can feel her presence a duk inda nake, but being with you for these days banajin wannan feeling ɗin a jiki na, being with her made me feel like hugging her for the rest of my life na dawwama a jikin ta, but for you i never get that feeling, i feel so empty since the day Grandma ta kawo ki ɗakin nan, i never feel the presence of my DEENAH beside me, zuciya ta is full of doubts akanki, i feel like my DEENAH is somewhere far away from me waiting for my rescue, and dukkanin wani hali da kike yi koh kaɗan ba halayen DEENAH ɗin da na sani bane, you've changed alot" ya faɗa idanun sa da fuskar sa na yin jaa sabida 6acin rai.

Ita dai kallon sa take zuciyar ta na mugun bugu ganin kamar asirin ta na daf da tonuwa.

Kallon ta yayi kafin yace "Whats the name of that your younger brother again?."

Shiru tayi tana wuwwula idanu cike da rashin gaskiya.

"Tell me" ya sake faɗa.

Cikin rawar murya tace "Why are you asking his name, i thought kasan kowa daga cikin dangi na, why then kake sake tambaya ta sunan ƙani na" ta faɗa da niyyar juyawa yayi saurin cafko hannayen ta fuskar sa na fitar da wani irin tsantsar 6acin rai ya sake faɗin "Tell me the name of your younger brother."

Fuzge hannun ta tayi tace "Fine then, why don't you just called them and asked them what the name of my younger brother is, wannan rainin hankali ne kake nunamin."

Sake ruƙo hannun ta yayi yana kallon cikin idanun ta, saurin kauda kai tayi tana ƙoƙarin kwace hannayen ta.

"Look into my eyes DEENAH."

"Mai zan tsinta idan na duba cikin idanun naka, listen am tired of having a quarrel with you always, idanma ka daina sona ne why don't you just tell me."

"But i never loved you, i only love my DEENAH" ya faɗa yana kallon ta.

"This isn't fair, why kake tunanin ni ba DEENAH bace, you think dama yadda halaye na suke kafin muyi aure haka zamu dawwama ba zai canzu ba."

Riƙo kafaɗun ta yayi cike da mugun 6acin rai yake faɗin "You're not my wife, i have been a fool for falling into your traps this time, all you've craved for your whole life is to have me in bed with you, baki san ta wacce hanƴa zaki bi ki cika burin ki ba, sai ta wannan by posessing my wife and had yourself turned into her, wannan ne kaɗai hanƴar da kike dashi na ganin kin cika burin ki akaina, i now get to know who you really are, Naseeba" ya ƙarashe cikin kakkausar murya fuskar sa da idanun sa na canza launi.

A matuƙar kiɗime ta waro manƴan idanun ta tana kallon fuskar sa.

Cikin mugun 6acin rai har maganar tasa na seizing yace "Where is my wife?."

"Answer me" ya faɗa a tsawace yana jijjiga ta.

Sosai ta tsorata da yanayin shi ganin jikin sa har rawa yake saboda 6acin rai.

Cikin rawar murya tace "I...i...i'm your wi..."

"Lies" ya faɗa a tsawace yana ture ta.

Naseeba ganin asirin ta ya tonu ya gano ta ne ya sanƴa ta waigowa cikin ainihin kamannin ta tana kallon sa da idanun ta da sukayi jazir.

Da kallo ZEEYAD ke binta cike da muguwar 6acin ran da baisan yana da ita ba.

"Yes, i'm not your wife, but inaso ka sani ba zaka sake ganin ta ba har abada."

Zuwa yayi yana cakumo gashin kanta kamar zai raba shi da fatar kanta yace "Tell me, where is my wife, where is DEENAH, what have you done to her?."

Dariya ta saki cike da mugunta dukda kuwa irin riƙon da yayi mata nan tace "She is dead long ago."

Ture ta yayi da ƙarfi dan kuwa baisan ta inda ma zai fara hora ta ba, mai ma zai daka a jikin mace yaji daɗi ya san kuma ya huce haushin shi, babu.

Zubewa yayi akan guiwowin sa, zuciyar sa na mugun rawa haka ma gangar jikin sa, hannu ya sanƴa yana cakume gashin kansa da ƙarfi, he can't believe how foolish he is da har Naseeba ta kasance dashi for good 2weeks har ma suke haɗa shimfiɗa tare ba tare da ya fahimci cewa ba DEENAH bace ba, sosai da sosai yakejin haushin kansa, sosai yakejin rashin gazawar sa na kasa riƙe amanar da aka bashi, DEENAH koh 24hrs bata cika a gidan shi ba ya rasa ta, sakamakon mugun irin dake zagaye dashi, sa'ar sa ɗaya shine bai ta6a kusantar da sunan mu'amalar aure ba duk da kuwa jarabar da tayi ta masa, ba zai iya kwatanta iriyar tashin hankalin da yake ciki ba a yanzu, komai ya sunce masa baisan ta ina zai fara ba, baisan ta ina zai nemo mafita ba, yasan duk inda DEENAH take a yanzu tana cikin mawuyacin hali, ba zai ta6a yafewa kansa ba, sabida dalilin sa ne duk wani abu ke faruwa da DEENAH.

Tsaye Naseeba da takejin zuciyar ta kamar ta fallatso tayi tana kallon sa tace "You want to see your wife, then you must give me abinda nayi longing nake nema daga gareka, only then zan faɗamaka inda matar ka take.

Ɗago da rikitattun jajayen idanun sa yayi yana kallon ta nan yace "I will find my wife wherever she is, babu abinda zaki samu daga gareni."

Dariya ta fashe dashi kafin tace "Seriously?, let's see then how and where you find the love of your life, tabbas tana nan a raye sai dai kafin ka samo ta daga inda take you must pay a higher price, sannan she is deep beneath inda babu wani mahaluƙin da zai iya gano ta komin neman sa, da ita da matacciya duk ɗaya suke a yanzu, da zaran na bada permission ɗin kashe ta toh tabbas babu makawa hakan ne zai faru, so the best abinda zakayi yanzu dan ceto rayuwar matar ka is to give me what i need from you."






_Toh nikam dai takaici ba zai kashe ni ba, na dakata haka nan idan na huce ma cigaba, haka kuma idan naga comment dayawa zan cigaba, dan kuwa kaɗan ya rage ban haɗiyi zuciya ba a page ɗinnan, kuma ku dinga yi Kuna yayyafawa zuciyar ku ruwan sanƴi, dan kuwa ni fanta ta mai sanƴi na sayo ina yi ina kur6a abina😕_







*MHIZZ JIDDHERR....................✍🏽*
[9/1, 10:30 PM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D*
```[The Abandoned Prince]```








*NA*
*JIDDAH BINT MUHAMMAD*






*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*





*050...*





_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar

Please Login or Register in order to submit comment