Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

you saying ZEEYAD."

"I know ranka zai 6aci sabida nayimaka ƙarya tun farko that i have been fooling you all this while, the truth is that...." shiru yayi bai iya ƙarasawa ba yana kallon Daddy ɗin.


"Come on tell me, menene baka faɗamin ba game da rayuwar ka?."

"Actually Dad, my Father is alive, sannan kuma ina da family, ban rasa family na a hatsari kamar yadda na faɗamaka a farko ba, sabida gudun kada kace na koma garesu."

"What, you have a Family?."

Kai ya jinjina masa nan yace "Come on let's sit and discuss this" ya faɗa yana samun wuri ya zauna.

Zama ZEEYAD ma yayi kafin Daddy yace "Tell me everything about your life ZEEYAD."


Shiru ZEEYAD yayi na ƴan mintina kansa a ƙasa yace "The truth is that, i wasn't a begger but...but an Abandoned Prince" ya faɗa kansa a ƙasa zuciyar sa na zafi.

Shiru Daddy yayi yana duban sa cike da mamaki, dan kuwa sam bai fahimci inda zancen ZEEYAD ɗin ya dosa ba "An Abandoned Prince?, bangane ba, can you explain further?."

Ɗagowa ZEEYAD yayi ya kallesa kafin yace "I mean am a Prince, but my Dad abandoned me when i was 10."

"Kana nufin kace min kai ɗan Sarki ne?" cewar Daddy cike da mamaki yana kallon sa.

Kai ZEEYAD ya jinjina masa, nan Daddy ya sake cewa "But..how could you be a Prince i mean bakayi kama da ɗan sarki ba."

"That is because i was Abandoned after my Mom's death, my own Father Abandoned me, he treated me like an outsider."

"ZEEYAD tell me more about yourself."

Shiru ZEEYAD yayi na ƴan mintina dan kuwa sam bayason tuno irin rayuwar wahalar da yayi a baya, bayason tuno da kowa daga cikin family ɗinsa hakan na matuƙar ƙona masa zuciya tare da ƙara tsanar su a cikin zuciyar sa, babu abinda zai sanƴa shi komawa ƙasar sa a yanzu face saboda Family ɗinsa dake chan wato Family ɗin abokin sa Sadeeq, dan kuwa Family ɗinsa maƙiyan sa ya ɗauke su ba ƴan uwa ba, sai dai dukda haka ba yanzu yakeson komawa ba tukun har sai yayi gagarumar shirin da koh kallon banza mutum bai isa yayi masa a bayan sa ba, so yake yayi proving ɗinsu wrong kan cewar ba zai ta6a samun cigaba a rayuwar sa ba, sai dai yanzu baya cikin nutsuwar da zai tinkare su har sai MADEENAHn sa ta samu lafiya ta hakan ne kaɗai zai sami kwanciyar hankalin aiwatar da abinda yayi niyya.

Ɗago da jajayen idanun sa yayi kafin kuma ya miƙe tsaye tare da zuba hannayen sa cikin aljihu, juyawa Daddy baya yayi kafin kuma yace "20 Years Ago, A Heir was born to the King of Egypt(Cairo), bayan jiran da yayi shekaru goma Allah bai basa haihuwa ba, One fateful day, my Mom got pregnant to me, and after nine good months....i was Born."


*20 YEARS BACK*


"""""""""Cike da matuƙar girmamawa suka zube gaban mai Martaba "Your Highness, an turo mana cewar mu faɗa maka cewa naƙuda ya kama Sarauniya LATEEFAT dama kuma Sarauniya Hafeezah, zaka iya zuwa dan ganin wacce zata riga haifa maka magaji a cikin su kamar yadda al'adar wannan MASARAUTA ta tanadar."

Cike da kiɗima mai Martaba ya fice daga ƙatuwar faffaɗar Fadar tasa izuwa babban asibitin Masarautar dan shaida wa idanun sa wacce zata riga haihuwa tsakanin matan nasa biyu wato Hafeezah dama kuma Lateefat.

Isar sa asibitin bai zarce koh ina ba sai ɗakin haihuwar, inda mata biyu ke kwance koh wacce akan gado daban, inda kuma wasu dattijai mata uku ke kan kowacce daga cikin su dan kar6ar haihuwar ta.

Duban sa ya maida gun ta gefen dama wacce da alamu tafi ɗayar shan wahala sosai sakamakon irin nishin da take.

Da sauri ya tako wurin ta yana kama hannayen ta cikin muryar tausayi ya furta "Lateefat?."

"Your Highness...mu...tuwa zanyi" ta faɗa cike da azabar da take ciki inda kuma gumi duk ya gama wanke mata fuska da jiki.

"Ki bar faɗin haka Lateefat ba zaki mutu ba, zaki haifa mana ɗan mu sannan kuma mu rayu cikin aminci da ƙaunar juna, ba zaki mutu ba" ya faɗa yana sumbatar ta a goshi.

"Your Highness, muna buƙatar ruwan maganin gargajiyar nan dan baiwa Sarauniya Hafeezah dan kuwa da alamu har yanzu haihuwar tata da ɗan saura, gashi kuma ba ƙaramin wahala take sha ba, wannan ruwan maganin shi zai rage mata zafin naƙuda."

"Wanne irin maganin gargajiya kuma, Ina ruwan addu'ar da Liman ya aiko?" cewar mai Martaba da ya ruɗe ganin halin da Lateefat ke ciki.

"Allah ya huci zuciyar ka ranka ya daɗe, amma wannan ruwan Sarauniya Hafeezah ta zubar dashi bayan munyi-munyi akan ta sha amma taƙi."


Cike da zafin zuciya mai Martaba yace "Ku kyale ta, ku cigaba da kula da ita har lokacin haihuwar tata tayi" ya faɗa yana juyawa ga Sarauniya Lateefat.

Bayan doguwar naƙuda dama kuma gwagwarmaya da Sarauniya Lateefat ta sha ne, ta haiho santalelen ɗanta kyakkyawa sosai son kowa ƙin wanda ya rasa, wata iriyar doguwar ajiyar zuciya taja tare da furta "Alhamdulillah."


Murna a wurin mai Martaba ba'a cewa komai, dan haka saurin goge yaron akayi bayan an yanke masa cibi akayi wrapping ɗinsa da towel sannan aka miƙa shi ga mai Martaba dake ta miƙo hannu tunɗazu dan kar6ar ɗan nasa.

Kallon fuskar yaron da yake kama dashi yakeyi ba tare da murmushi ta gushe daga kan fuskar sa ba.

Sumbatar yaron yayi tare da rungume sa yanajin soyayya dama kuma ƙaunar yaron na baibaye duk wani 6argo dama kuma cikin jini haɗi da jijiyoyin jikin shi.

Bakin sa ya kai kunnen yaron tare da yi masa huɗuba da sunan *ZEEYAD* yana sake rungume sa a jikin shi.

Ɗan tallafowa yayi yace "Lateefat, ba na faɗamiki ba, zaki haihu lafiya sannan kuma mu rayu da ɗan mu cikin ƙaunar juna."

Murmushi tayi tana miƙa masa hannu alamun ya bata yaron.

Yaron ya bata kafin ta rungume sa tanajin soyayyar sa sosai a cikin zuciyar ta, Allah ya amsa addu'ar su yau bayan shekaru goma da sukayi basu samu haihuwa ba, babu abinda zasu ce sai dai su ƙara miƙa godiya marar iyaka ga Ubangijin sammai da ƙassai.

Yaron aka amsa kafin mai Martaba ya fice dan zuwa ya sa a sanar da haihuwar mata mafi soyuwa a gareshi cikin matan nasa.

Fitar sa bai wuci da mintina goma ba Sarauniya Hafeezah ta sambaɗo nata kyakkyawan yaron shima.

Inda kuma zuciyar ta ke cike da ɗumbin baƙin cikin riga ta haihuwa da Lateefat tayi.

A haka aka sallami kowacce bayan sun huta.


****************


Duk wani lungu da saƙon wannan MASARAUTA cike take da dumbin jama'a kowane na kai da komowa, kallo ɗaya zakayi musu kaga irin tsantsar farin cikin da suke ciki, sakamakon sadakar kayan abinci haɗi da na sawa da ake tayi musu.

Yayin da kuma kiɗan Drums ke ta tashi ta koh ina, fadar ta cika da ɗumbin jama'a dan taya sarki murnar samun ƴaƴa maza a lokaci guda.


Zaune suke kusa da sarki Inda shi kuma yake tsakiya kan doguwar throne ɗinsa fuskar cike fal da farin ciki.

Gefen sa Queen's ɗinne kowacce da nata jaririn a hannu, hankalin su na kan wasannin da ake gabatar wa dan taya su murna.

Sai dai kallo ɗaya zaka yi wa Sarauniya Hafeezah ka gano tsantsar baƙin ciki akan fuskar ta, babu abin dake ƙara mata hakan sai ganin Sarauniya Lateefat dake farin ciki tana murmushi.

_"Kiyi murmushin ki yadda kika so, muddin ina raye wannan murmushin ya kusa zama baƙin ciki a gare ki, i will make sure that i ruin your happy life"_ ta faɗa a zuciyar ta cike da mugun nufi.

Sarauniya Nazeerah kuwa da ta kasance Uwar gida kuma bata samu haihuwa ba, koh a fuska bata nuna alamun baƙin ciki da haihuwar kishiyoyin nata ba, sabida ta san da akwai wata babbar gwarama da ta kusa afkuwa tsakanin wadannan kishiyoyi biyu da suka haifu rana ɗaya, nata dai bai wuci kallo ba, dan kuwa bata ga abinda zai sa tayi baƙin ciki dasu ba, dan koh bakomai ita ya fara sani kafin su, sannan kuma babu abinda ta nema ta rasa a cikin gidan, kama daga kan dukiya, abinci sutura da sauran su, haka kuma baya ƙunsa mata baƙin ciki koh yi mata gori akan rashin haihuwa, dan haka bata ga wani abin tada hankali ba, ita dai nata bai wuci taji daɗin husuma ba.

A gaban ɗumbin mutane aka naɗa Sarauniya Lateefat a matsayin *QUEEN MOTHER* kasancewar ta uwa ga babban yarima kuma ɗan da zai gaji sarki.

Sarki da kansa ya ɗaura mata Diamond Crown a kanta tare da yi mata Tsadaddun kyaututtuka, haka ma kuma ƴan uwa da abokan arziki kowa yaba ta yake da ɗan da ta haifa tare da yi mata kyaututtuka masu kyau da tsada.

Ganin anfi koɗa Sarauniya Lateefat akanta hakan ya sake hura mata wutar tsanar ta dama kuma tsanar jaririn da ta haifa ɗin a cikin zuciyar ta.

Haka aka gama taro mutane suka watse daga fada.

Kallon ta Sarauniya Lateefat tayi daga inda take zaune tana tashi ta ƙarasa wurin ta ganin ta kafe wuri ɗaya da ido ne yasa ta ta6a ta.

Ɗagowa Sarauniya Hafeezah tayi tana kallon ta, murmushi Sarauniya Lateefat tayi tace "Sannu ƴar uwa datafan mun samu kanmu ƙalau, ki bani YAZEED na ɗauke sa" ta faɗa tana kai hannu zata kar6i yaron.

Riƙe ɗan ta tayi gam cike zafin harshe tace "Kada ki nemi ki raina min hankali mana Lateefah, tunɗazun sai yanzu kikaga damar zuwa ɗaukar sa?, tayaya ma zan baki ɗana ki riƙe bayan an tabbatar min da cewar iyayen ki dama kuma kakannin ki riƙaƙƙun mayu ne, ɗana YAZEED yafi ƙarfin duk wani asiri da tsubbu irin naku dake da iyayen ki, na tabbatar da cewa kune wadanda suka jinkirta haihuwa ta har kika riga ni, bayan kuma na riga ki samun ciki."

Sosai Lateefat taji zafin kalaman ta, sai dai kasancewar ita ɗin mai haƙuri ce ta dake tare da yin murmushi tace "Mai kike faɗa ne haka ƴar uwa, ai YAZEED dama kuma ZEEYAD dukkanin su ɗaya suke a wuri na..."

"Ba ɗaya suke ba, kada ki kuskura ki sake haɗa ɗana da wannan ɗan naki, kowa yaje yayi rayuwar sa sannan ya raini ɗan sa, koh da a bayan idona ne na haramta miki ɗaukar ɗana koh zuwa kusada shi, idan kuma baki kiyaye ba wani abin ya faru dashi toh tabbas kece zan baiwa laifi" tana faɗin haka ta miƙe a fusace ta bar cikin fadar inda kuma Sarauniya Lateefat ta bita da kallo.


*10 YEARS LATER*


""""""""" "ZEEYAD!, ZEEYAD!!, ka tsaya mana haka nan ina kiran ka" ta faɗa tana biyo shi cikin fadar da gudu.


Zuwa yayi ya faɗa jikin mai Martaba yana dariya tare da 6oyewa a bayan shi.
"Abhi kaga Ummie ba" ya faɗa yana sake 6uya a bayan nasa yayin da ita kuma ke ƙoƙarin kamo shi.

Dariya Abhi yayi yace "Lateefat?".

Ɗagowa tayi ta kallesa kafin yace "Mai yaro na yayi miki haka kike bin shi, mai kikeson yi masa?."

"Bayajin magana, nace dashi ya tashi yaje wurin kakar sa tana ta tambayar sa kwana biyu ga kuma kewar sa da tayi amma yace shi ba zaije ba yawo zai fita."

"Toh ki bar shi mana, abinda yakeson yi ɗin kenan, kada ki dinga tilasta shi akan abinda baya so, koh kin manta shi ɗin babban mutum ne?."

"Ba wani nan dama ai kai bakason a faɗi laifin sa koh kaɗan, duk abinda yayi sai kace wani shi babban mutum ne, a haka zai mulki mutane idan ba'a horar dashi tun daga ƙarami ba" ta faɗa tana samun wuri ta zauna.

Daura shi ma Martaba yayi akan cinƴar sa ya shiga yi masa wasa cike da ƙaunar da yakeyi masa.


"Abhi, yaushe ne nima zan girma na zama sarki kamar kai?" cewar ZEEYAD.


Murmushi duk sukayi kafin kuma yace "Kafin ka zama sarki sai ka baiwa shekaru 28 da takwas baya, na tabbata zakayi adalci tare da yin mulki cikin gaskiya fiye da yadda nakeyi a yanzu."

Murmushin sa mai ƙara masa kyau yayi yace "Toh Abhi idan na girma ɗin ni zan zama sarki sannan kuma na zama shugaban ku kai da Ummie kenan?."


Dariya sukayi kafin kuma yace "Aa mu iyayen ka ne ba zaka ta6a zama shugaban mu ba."

Haka sukayi ta hirar su cike da so da ƙaunar juna.

*****************

Tsaye yake cikin faffaɗar ƙayatacciyar filin wasar tasu ta ta sha ababen wasan yara kala daban-daban, hannun sa ɗauke da ball yana buga ta yace

"YAZEED, kazo muyi wasa."

Juyowa kyakkyawan yaron da ya kira da YAZEED yayi kafin kuma ya taso daga kan lilon da yake kai cikin murmushi yana ƙarasowa wurin ZEEYAD yace "Ɗan uwa na inason yin wasa da kai, amma Ummie na kullum sai tace wai na daina yin wasa da kai idan ba haka ba, Ummien ka zata cinƴeni" ya faɗa alamun bayajin daɗin hakan.

ZEEYAD ji yayi ransa ya 6aci dan kuwa kullum Sarauniya Hafeezah batada magana sai ta aibanta Ummien shi, jefar da ball ɗin hannun sa yayi tare da juyawa zai bar cikin filin wasan nasu.


Cikin gudu YAZEED ya mara masa baya yace "ZEEYAD ka tsaya, maiyasa kayi fushi, ka fasa yin wasan dani ne?."


Tsayawa yayi ya juyo cikin huci yace "Ba zan sake yin wasa da kai ba, sabida kullum Ummien ka sai tayi ta faɗin magana marasa kyau akan Ummie na, indai har kanaso na cigaba da wasa da kai sai Ummien ka ta gyara halayen ta da kalaman ta tukun" yana faɗin haka ya fice.

Da kallo YAZEED ya bisa yanajin zuciyar sa babu daɗi, ƙafa ya ɗaga zai bi bayan shi nan yaji anyi saurin dafa kafaɗar sa ta baya.

Juyowa yayi yana sauƙe idanun sa kan Ummien sa nan yace "Ummie ba nace ki daina faɗin munanan kalamai akan *QUEEN MOTHER* ba, gashi yanzu kinsa ZEEYAD yayi fushi dani har yace ma ba zai sake wasa dani ba."

Cike da muguwar zuciya irin tata tace "Ka kwantar da hankalin ka ɗana, rashin yin wasa dashi shine alkhairi a gareka, idan ba haka ba tabbas Ummien sa sai..."

"Ƙarya kike Ummie, Ummien ZEEYAD mutuniyar kirki ce, kece kike 6ata mata suna a wurin mutane, amma ni kullum idan naje wurin ta ƙara sona takeyi, tana yi min abinda koh ke bakya yi min, kuma tana bani dukkanin abinda nakeso, kuma batayi min tsawa da faɗa koh ta dake ni kamar yadda kikeyi min ba, ni ba ke bace Ummie na daga yau, Ummien ZEEYAD ita ce Ummie ta" yana faɗin haka ya bar wurin da gudu yana bin hanƴar da ZEEYAD yabi.

Sosai zuciyar ta ke mugun tafarfasa akan kalaman ɗan nata
"No this can't be, i can't let her take my only son away from me, ta kar6e komai daga gare ni, tanayin nasara akan komai idan tasa gaba, so i guess lokaci yayi yanzu da zaki bar duniyar Lateefat, dan kuwa ganin mutuwa ta ya fiye min ganin ki a cikin gidan nan, i will make sure you die a painful death" ta faɗa cikin fidda zazzafar huci tana barin wurin.



********************


*3 MONTHS LATER*



""""""Kwance take akan Gadon asibitin wanda da alamu bata ma san su waye ke kanta ba.


Mai Martaba ne zaune ZEEYAD akan ƙafafun sa, dama kuma wasu dattijai wadanda ba zasu wuce iyayen Lateefat ba, kowannen su fuskar sa ɗauke da damuwa.

"Abhi, yaushe Ummie na zata tashi?."

"Soon insha Allah, ka bar damuwa kaji?."


"Abhi naji ance duk wanda hantar sa da ƙodar sa ta lalace basa sake yin rayuwa mai nisa zasu mutu, hakane?."

Shiru Abhi yayi kafin kuma yace "Aa ZEEYAD, ba haka bane, waye ya faɗa maka hakan?."


"A makaranta ne Malamin mu ya faɗi hakan."

"Aa wasa yakeyi muku amma babu wani mutuwa da akeyi kuma ana samun sauƙi."

Shiru yayi kawai tare da ƙure Ummien tasa da idanun da suka tara hawaye yana kallo.





*Yawan Comment, Yawan Typing*





_*Zan iya cewa sai mun haɗu bayan sallah daga nan?😉*_






*MHIZZ JIDDHERR............✍🏽*
[8/30, 9:32 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D*
```[The Abandoned Prince]```





*NA*
*JIDDAH BINT MUHAMMAD*





*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*





*Ina yiwa ɗaukacin Al'ummar musulmai, sannan kuma masu bibiyar littafin ZEEYAD barka da sallah, Allah Ubangiji ya maimaita mana na shekaru aru-aru masu zuwa cikin rai da ƙoshin lafiya, dafatan dai baku manta da barka da sallah ta ba, dan kuwa har yanzu ban gama nawa sallahn ba😌, zan ajiye account number na, dafatan dai ba zaku sace min guiwa ba wurin ƙin turomin nawa goron sallahr, Yauwa sannan kuma ZEEYAD yace na sanar da masoyan sa cewa kowacce ta ajiye nata account number ɗin nan da kafin a gama bada labarin sa kowacce zata ji alert ɗin miliyan ɗaya cikin account ɗin ta, yayi hakan ne dan soyayyar da kuke nuna masa da DEENAHr sa, wadanda suke jin haushin DEENAH kuma irin su Lateefat da Fatima bet masu ƙaton kai yace na sanar daku cewa babu ku, babu miliyan ɗaɗɗayan da zai raba, dan kuwa ni kaina miliyan ɗari ya bani kuji, shiyasa kuka jini shiru, ina chan ina tawa budirin cikin walwala da arziƙi😂🤘🏼*




*026...*





*_Ayi haƙuri idan anga kura-kurai a ciki, banyi editing ba_*🥲




*TWO WEEKS AFTER*




""""""""Yau tsawon watanni uku da sati biyu kenan Sarauniya Lateefat na kwance bata da lafiya.

Sosai little ZEEYAD yayi kewar rashin jin mahaifiyar tasa a kusa dashi.

Yau ma zaune yake kusa da mahaifiyar tasa yana kallon ta.

Murmushi ta sakar masa tana miƙo masa hannu yazo gareta.

Tashi yayi daga inda yake zaune yaje kusa da ita, kafin kuma ta rungumo sa jikin ta, tana jin wani irin ƙaunar sa har cikin jinin jikin ta.

Sosai takejin a ranta mutuwa zata yi ba zata kuma ƙara wasu tsawon kwanaki ba zata koma ga mahaliccin ta, zata bar mutanen da tafi so da ƙauna a duniya, Iyayen ta, mijin ta dama kuma ɗa ƙwalli ɗaya da ta haifa wanda shi ne farin cikin ta a kullum, batasan ya rayuwar ZEEYAD zata kasance na rashin ta ba, sosai take tausayin ɗan nata, sai dai kuma idan ta tuna da irin ƙaunar da mahaifin sa keyi masa sai taji zuciyar ta tayi sanƴi dan kuwa ta san zai kula da ZEEYAD ɗinta sosai.

"Ka bar kuka haka nan yaro na, maza fah basa kuka musamman ma kai da kake jarumi, wanda zai mulki mutane nan gaba, Jarumai basa kuka" ta faɗa cikin muryar ta dake fita da kyar tana shafa kwantacciyar sumar kansa.

"Ummie wai dagaske ne mutuwa zakiyi ki bar ni?" ya faɗa yana ɗagowa ya kalle ta.

Murmushi ta ƙaƙaro tayi tace "A'a wannan ba gaskiya bane, wanene ya faɗa maka hakan?, ba zan mutu ba har sai naga ka girma ka zama sarki."

Maida kansa yayi ya kwanta a jikin ta tare da rungume ta yace "Ummie ni banaso ki mutu koh na girma ɗin."

Kansa kawai take shafawa kafin ta maida duban ta ga wata dattijuwar mata dake tsaye akan su tana kallon su tace "Ummie na, kin tahomin da ajiyar nan kuwa?."

Kai kawai matar ta girgiza kafin kuma ta sanƴa hannu cikin jakar dake rataye a kafaɗar ta ta ciro wata sarƙa tana miƙa mata.

Amsa tayi tana kallo kafin ta kalli ZEEYAD tace "Ba yanzu nayi niyyar baka wannan sarƙar ba, na fiso sai ranar da za'a naɗa ka sarki na baka kyautar ta, sai dai kuma hakan ba zai ta6a yiwuwa ba dan kuwa bana tunanin zan kai wannan lokacin, zan baka ita ne sabida idan na tafi ka ringa tunawa dani, ka ɗauka cewa kullum ina tare da kai ɗana, idan na tafi kada kayi kukan rashi na kokuma kaji kewa ta, ba zan ta6a jin daɗin hakan ba, nasan mahaifin ka zai kula da kai yadda yakamata sannan kuma ba zai bar ka kayi kukan rashi na ba, kawo wuyar ka na sanƴa maka sarƙar" ta faɗa tana ɗaga sarƙar ta sanƴa masa a wuya.

A daidai lokacin kuma mai Martaba ya shigo dama kuma sauran Sarauniyoyin.

ZEEYAD ne yayi wurin sa da sauri yana kamo hannun sa yace "Abhi, ba kunce min Ummie na ba zata mutu ba, maiyasa toh take magana kamar wacce zata yi nisa damu?."

Shafa kansa mai Martaba yayi kawai ba tare da ya iya ce masa komai ba.

Wani irin tari ne sukaji ya sarƙe Sarauniya Lateefat, dan haka duk kanta sukayi a ruɗe suna kiran sunan ta, kafin kuma wasu su fita kiran likita.

Da kallo ZEEYAD ke bin su, kafin kuma ya tsinkayo muryar mai Martaba na cewa "Hafeezah kuyi waje da Yarima ZEEYAD."

A firgice Hafeezah da ta faɗa duniyar tunanin ta cike da jindaɗin plan ɗinta yayi working ta ɗago kafin kuma ta kama hannun ZEEYAD da niyyar suyi waje.

Tirjewa ya fara yana kiran Ummien sa, hakan ne yasa kuma cike da mugun haushi da mugun ta ta fizgo sa tayi waje dashi tana tsinka masa mari.

Idanu ta zaro ganin ga dogarai nan birjik sai dai baƙar zuciyar ta ta rufe mata ido bata gansu ba, yanzu ganin da sukayi ta tsinkawa ZEEYAD mari tasan tabbas sai sun sanarwa da mai Martaba, daga nan kuma kashin ta ya bushe.

Cike da muguwar makirci irin nata ta fashe da kukan ƙarya tana faɗin "Ohh ni Hafeezah yau da wanne zanji ne, da mutuwar Lateefat koh da taurin kai irin naka?, naji zafin mutuwar Lateefat sosai hakan yasa idanu na suka rufe na mari wannan kyakkyawar fuskar taka, ka gafarce ni ya kai Babban Yarima" ta ƙarashe cikin haɗa hannayen tana kuka.

ZEEYAD sosai ransa ya 6aci dan kuwa yasan Hafeezah bata wani damu da Ummien sa ba, yasan duk makirci ne irin nata.

Mai Martaba suka hango ya fito idanun sa sunyi jaa sosai, ba tare da yabi ta kan kowa ba yayi wucewar sa hakan yasa dogaran sa mara masa baya da sauri.


Wani irin farin ciki da annashuwa ne suka cika wa Hafeezah rai, ji take kamar ta zuba ruwa a ƙasa tasha dan daɗi, ta riga da ta gama da Lateefat, saura kuma ɗan da ta haifa, dan kuwa taci alwashin indai da ranta ba zata ta6a barin ZEEYAD ya zamto Sarki ba, tayi alƙawarin sai taga bayan shi kamar yadda taga ta Uwar sa.

Harara ta zabga masa kafin kuma ta wuce fuu kamar zata tashi sama.

ZEEYAD ne ya koma ɗakin, nan ya tarar da duk kuka sukeyi ga Ummien sa kuma kwance da farar kyalle an rufa mata shi.

Raku6ewa yayi a jikin ƙofar hawayen baƙin ciki na zubo masa.

Tuno da cewar Jarumai basa kuka yasa shi saurin goge hawayen fuskar sa, tare da yin dukkanin ƙoƙarin sa na ganin baiyi kukan ba.

Hannayen sa ya kai kan sarƙar wuyar tasa yana shafa ta.


*********************


Yau sati ɗaya kenan da mutuwar Sarauniya Lateefat, duk inda ka zaga a cikin MASARAUTA zaka fahimci kowa jikin sa yayi sanƴi da wannan mutuwa.


Mai Martaba kuwa ya daina kula kowa sai ZEEYAD, ya daina fitowa fada kullum yana cikin ɗakin sa gaban hoton marigayiyar matar sa.

Hakan kuwa ba ƙaramin ƙonawa Sarauniya Hafeezah rai yake ba, hakan ya sanƴa ta tashi tsaye na ganin ta raba tsakanin uba da ɗansa, dan kuwa tabi duk wata hanƴa na ganin an kashe mata ZEEYAD amma hakan yaci tura.


Ɗago da jajayen idanun sa yayi yana kallon Daddy yace "1 year after my Mom's death, i started facing some kind of hatred from my family, they despised me, they don't want me close to them, basa son nayi wasa da ƴaƴan su, sun raba ni da ƴan uwa na, sun raba ni da YAZEED, shine kaɗai wanda yake nuna min ƙauna a cikin ƴan uwa na, but later on, his Mom took him far away from me, sun canzawa duk wani yaro dake gidan makaranta except me, and since from that day da suka raba YAZEED dani, i never set my eyes on him again, koh da hutu ba'a barin sa yazo duk dan kada mu ga juna dashi, but duk wannan ba damuwa ta bace, babbar damuwa ta shine yadda mutumin da yafi kowa ƙaunata yazo ya canza zuwa wanda yafi kowa tsana ta a wannan gidan, shi ya sanƴa aka cire ni a makaranta mai tsada aka maida ni ta ƴaƴan talakawa, ya sanƴa an kwace dukkanin wani abu da zai sa a danganta ni da ɗan sarki dashi, sannan kuma yasa aka ɗauke ni daga cikin gida aka maida ni yin rayuwa cikin arear bayi mata, cikin wani ɗaki da koh da dabbobin da ake kiwon su a cikin gidan sun fi ni walwala da jindaɗi, hatta bayin dake cikin Masarautar babu wanda yake da irin ƙasƙantacciyar ɗaki

Please Login or Register in order to submit comment