Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gidane naganka a side ďinshi, ce mishi yayi "No Ammah na ciki, daga wajenta nake, yace "okay let me get to her", k'ofan falon Abui ya buďe, yana saka k'afa Batuul dake ciki taji gaba ďaya ta zama restless, bugun zuciyan ta ya fara, a hankali ta rik'a tauna abincin dake bakinta, k'ofar ďakin da suke ya tura ya shigo, cak komai ya tsayawa Batuul dan batayi expecting ďinshi ba at this time, k'anshin turarenshi ya cika ko ina na ďakin, da sallama ya k'araso ďakin yana kare ma mutanan ciki kallo snn ya zauna a gefen gado, Gaisheda Ammah dake ta binsa da kallo yayi ta amsa tana masa sannu da xuwa, sannan ya gaida Aunty Amna da ta dage sae tsokananshi take, Farida ce ta gaisheshi ba tare da ta kallesa ba, ba yabo ba fallasa ya amsa mata, sau ďaya ya kalli inda Batuul take ya ďauke kanshi, ita dai bata ce mishi komai ba gashi nan dab da ita ya zauna, xame hannunta tayi daga plate ďin ta cewa Farida ta k'oshi, Abuturrab na kallon Ammah yace "Ammah béri manyin, (Ammah inason abinci) banyi breakfast ba yau throughout bare inci lunch ga yamma tayi", Aunty Amna ce tace "wannan duk ďokin zama angon ne ya hanaka cin abinci" tana dariya tayi maganar, bai ce mata komai ba sae murmushin da yyi dan ya saba da tsokanar Aunty Amna, shi bai tab'a haďuwa da Aunty ďinshi mai tsokana kamar ita ba, Ammah ce ta dubi inda su Farida ke cin abinci ta lura da Batuul bata cin abincin, tambayanta tayi "bitti ya akayine bakya cin abincin", murmushi Batuul ta k'irk'ira tace "Na k'oshi Ammah", ce mata tayi "Bitti ďauko wa Abu abincinshi a palo, yana nan na shirya akan tray xa ki gani", a sanyaye ta mik'e tare da cewa toh, inda ta ajiye ďankwalinta ta duba zata ďauka taga akai ya zauna, bata ce mishi komai ba tayi hanyan palo, binta yayi da kallo har ta b'ace sannan ya ďauke idonshi tare da tabe baki a ranshi yace batason rufe kanta, dan yasha ganin gashinta on several occasion, mik'ewa Ammah da Aunty Amna sukayi suka fita dan sun gama abinda zasuyi, turowa kawai zasuyi a zo a ďauki kayan, inda Farida take zaune ya duba yaga tana ta faman dambe da k'ashi, ďauke kanshi yyi daga kallonta tare da jan tsaki, can ya sake dubanta gnin bata ma san yana yi ba sae fama da k'ashin take bayan ga nama me yawa a plate din yasa ya xabga mata harara yace "ke in baza ki ci abinci nan ba tashi ki fita, kin zauna kina ta kokuwa da k'ashi ko ina zaki kai na cikin plate ďin" zumb'uro baki tayi tareda kinkiman plate ďin abincinta tayi waje a ranta tana faďin "ohh masifaffe, mutum ran aurenshi ma sai yayi masifa ko ina ruwanshi da k'ashin da nake ci oho", ta fice abinta ya bi ta da harara.





Bayan few minutes Batuul ta shigo ďakin kinkime da babban tray, saura kaďan ta sake tray ďin don wani irin faďuwa gabanta yayi ganin shi kaďai ne a ďakin, kanshi ya ďago ya ganta tsaye, ďauke kai yayi yaci gaba da abinda yakeyi a wayarsa, ganin ta fara gajiya da tsayuwan ne ya sata k'arasawa jiki a sanyaye ta shigo, a gabanshi ta sunkuya ta ajiye tray ďin , shi kuma gashin kanta da tayi parking in a messy bun yake kallo, yadda sukayi curls wasu na lilo ya zubawa ido, ďagowa tayi daga tsugunnen ta mik'e tsaye, tsayawa tayi a kanshi tana so tace yana zaune a kan ďankwalinta zata ďauka amma ta kasa bude baki, binta yayi da kallo yace "wa zai zuba min abincin kin wani ajiye kin nemi waje kin tsaya kina kallona, C'mon sense din ki bae baki cewar ba dungure min abincin xaki yi ki mike ba", bata kulashi ba sae wani hade rae da tayi ta tsuguna ta ďauki plate da serving spoon kanta a kasa tace mishi "mey zan zuba maka", ba tare da ya kalleta ba a takaice yace "anything", gima ta zuba mishi a plate ďin, daga gefe ta saka mishi scrambled potato mai cheese sai kémoniye a wani saucer, kallonta kawae yake har ta dago kai tana kallonsa tace " Ya isa?" Bae tanka ta ba sae sunkuyawa da yayi ya ďauki abincin ya fara ci a hnkli, ďagowa yayi da kanshi ya ganta tsaye tana fidgeting yatsunta kamar zatayi magana, kallonta shima ya tsaya yi sae dae fuskarsa a daure, sunkuyar da kanta tayi da sauri, shi kam bae fasa kallonta ba sae a nn ya kuma lura da yarintar ta, k'aramace ssae ya faďa a ranshi, a fili kuma cikin dakewar murya yace mata "get me a bottle of water", ba musu taje ďauko mishi ya bita da kallo har ta bude fridge ta dauko ruwan, kan ta juyo ya maxa ya sunkuyar da kansa, ta karaso ta mik'a mishi, hannu yasa zai karb'a taji hannunshi cikin nata, maza tayi ta sake ruwan ya faďi a k'asa, kallonta yayi tare da jan ďan k'aramin tsaki ya ďauki ruwanshi, ganin ta kasa mishi maganan ďankwalinta ne ya sata kawai ta fita haka, juyawan da tayi zata bar wajen kawai ta bige tumbler dake wajen , a take suka tarwatse a wajen, ba karamin rikicewa tayi ba ta daga k'afa da sauri zata matsa daga wajen ta tak'a ďaya daga cikin broken glass ďin, wani k'ara ta saki ta tsuguna a wajen, wani mugun kallo yake jefa mata kmr xae maketa, ita ko duk ta tsorata ta saka kuka, ganin jini a kafar ne ya sashi ajiye abincin hannunsa a gefe da sauri ya mike, tunawa da yayi lokacin da yake k'arami suna London, Aunty na koya mishi homework ďinshi ya ďauki blade ya yanke hannunshi dashi, rudewa tayi sosai har idonta sai da yacika da hawaye tayi mishi treating hannun, har sai da ya warke tukunna ta fara barinshi yana yin abu da kanshi, karasawa yyi inda take ya tsugunna dab da ita har tana iya jiyo numfashinshi a fuskanta, ga k'anshin turarenshi ita yayi mata yawa, hannunshi yasa zai janyo k'afarta tayi maza ta janye, tsaki yayi tare da janyo k'afan yana dubawa, glass ďin da ya mak'ale a k'afan ya sa hannu ya cire, wani ihu tasa tare da k'ank'ame shi, shiru yayi yaji yadda heartbeat ďinta ke bugawa da k'arfe, idonta ta buďe da taji zafin ya ďanyin sauk'i, da sauri ta sakeshi ta matsa baya ganinta kwance a jikinshi, tashi yayi ya koma gefen gadon ya zauna, yunk'urin tashi tayi itama zata tafi ta kasa, wani k'ara ta sake sawa, tasowa yayi ya dawo gabanta ya mik'a mata hannun alamun ta rik'e ya mik'ar da ita, nok'e hannayenta tayi, haushi ne ya sashi sunkuyowa ya ďauketa cak sae jin ta tayi jikinsa, ta wara ido ganin abinda yayi, k'ok'arin sauk'a ta farayi daga hannunshi, hade rae yyi ssae ya xuba mata idonshi masu kama da na masu jin bacci, hawaye ne makale idonta suna shirin zubowa, ce mata yayi "stay still, ciwo kikaji bazaki iya tafiya ba, am helping, ki tsaya in gama or ki sha mari ynxun nn, ina wasa da ke ne" yana hararanta ya kare mgnr, shiru tayi ta dena k'ok'arin sauk'an da take sae dae ba karamin faduwa gabanta yake ba, toilet ďin ďakin ya shiga da ita ya ajiyeta a bakin bathtub, shower ya janyo ya kunna ruwa yana zubawa a wajen tare da sa hannu yana wanke jinin da ya fara bushewa a wajen, rintse ido tayi ta dafa sa sabida zafin da wajen keyi, sai da ya gama ya sake ďaukanta cak ya fito da ita ďakin, a kan kujera ya kwantar da ita , ďakin Abui ya shiga ya ďauko first aid kit, dab da k'afanta ya zauna ya kamo k'afan ya shiga gogewa da spirit da cotton wool, ido ta rintse tsabar azaba ta rik'e hannunshi da sauri, sae kuma ta sake kuka, hannunta da ta rik'eshi dashi yabi da ido, ďauke hannun yayi daga jikinshi yaci gaba da abinda yakeyi, zafin ne yayi yawa tace mishi "Yaa Abu dan Allah ya isa haka, akwai zafi", dubanta yayi yaga hawaye take ssae ,ce mata yayi "clean your face and close your eyes, it wont hurt, beside raki ne yyi maki yawa", hakan tayi ta rik'e mishi riga har sai da ya gama dressing ciwon , tashi yayi daga wajen ya gyara mata k'afan ta kwanta comfortably, juyawa yayi zai fita tace mishi "Yaa Abu don Allah ka kira min farida", tsayawa yayi cak ba tare da ya juyo ba jin ta k'ira sunanshi sai da yaji abinda take buk'ata, ba tare da ya juyo ba yace "Anki" fita zaiyi daga ďakin kenan Farida ta shigo tana ihun "Batuul mey kika tsaya yi tun ďazu ina jiranki kizo kiga kayan da akayi mana, its f**ki....." bata k'arasa ba tayi maza ta rik'e baki ganin Yaa Abu a tsaye, dariya ne kawae Batuul bata yi ba ganin yadda ta haďiye maganan, a sanyaye ta k'arasa wajen Batuul tace "mey ya sameki, ya akayi kika ji ciwo har haka daga fitana" "Shut ur filthy mouth nd clean up this mess kafin in dawo" yana kai wa nn ya sa kai ya fita, da harara ta bisa snn ta dube Batuul tace "shi ya ji miki ciwon ko, ai nasani, kuma in yaga mutum yaji ciwo yafi kowa damuwa, garin yaya", kai Batuhl ta girgiza tace mata "Ba shine fa ya ji min ciwo ba, nice na fasa tumbler da na ajiye, dama ance everybody will b d first victim of his own corruption, gashi nan ni ya fara ji wa ciwo", tausaya mata Farida tayi tace "sannu", tambayanta Batuul tayi "mey kike faďa ne da kika shigo har da su f**king" ta k'arashe maganan tana mata dariya, "kayanmu ne na dinner, yayi kyau sosai, both d material and d style sunyi kyau sosai, sai ma mun saka tukunna", ce mata tayi "Dinner sai ku, ni yanxu ina naga k'afan zuwa dinner" a ranta kuwa hamdala tayi ta samu rusheshen excuse da xata bada dan dama bata son zuwa, a hnkli Farida tace "toh nima bazanje ba tunda bazaki ba", ido Batuul ta wara ta buďe baki tace "kinsan mey kike faďa , dan bazanje ba kema bazaki ba, ai sai in sa Ammah ta turaki dole, bare da ita ma za a ai dole kije", dariya Farida tasa tace "I wont miss it for the world wasa ma nakeyi, zanje kema kuma zakije yarinya", kamin ta bata amsa Ammah ta shigo ďakin, ganin Batuul a kwance yasata hanzarin k'arasowa inda suke, tambayanta ta shiga yi yadda akayi taji ciwo, faďa mata gaba ďaya, sai da ta gama tace mata "Toh yanxu ina Abutturab ďin, shine dan bak'in hali ya fita ya barki ke kaďai Kuma bai zo ya sanar dani kinji ciwo ba", "yanxun nan ya fita Ammah", Batuul ta faďa mata, taimaka mata sukayi ta tashi, har toilet sukaje da Farida tayi alwala ta fito, kaďan kaďan take ďingisawa, side ďin Ammah suka koma sukayi sallah suka fara shirin zuwa dinner dan Ammah tace babu abinda zai hanata zuwa, har da dan hawayenta don ba hka ta so ba.
💖💝BATUUL💖💝






22





By phartiemarhk





Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*





Shiri suka hau yi bayan sunyi isha da magariba, ďakin Ammah suka zauna suna dudduba kayan, lace ne purple mai ďan ratsi ratsin grey mai kyau, ďinkin ya amshsu soaai, iri ďaya akayi musu, sai da suka gama Ammah ta dubi Batuul "Bitti kunyi kyau, amma babu sark'a da ďan kunnefa, ke Farida ya baki bata ba, sai ki saka keh kaďai", hararan Batuul Farida tayi sannan tacewa Ammah "Ammah kiga jewellery box ďin mafa a gabanta yake, nace ta zab'i wanda zata saka tak'i wai baza ta saka ba", Ammah cewa tayi "A ah Batuul bazai yiwu ba, ina aka tab'a gaye babu ďankunne", mik'ewa tayi ta buďe closet ďinta ta fiddo wani ďan akwati k'arami mai kyau kmar chest box na katako, sai da ta zauna ta buďeshi ta fiddo wasu set ďin y'an kunne da sark'a masu kyau da abun hannu da zobe na azurfa harda agogonshi ta mik'awa Batuul, "ungo maza saka wannan", a kunyace Batuul ta karb'a ta saka, kamar wasu diamond ta saka haka ya dinga haske sabida tsabar kyan da yayi, sai da ta saka Ammah ta dubeta tace "Masha Allah ko kefa", wasu matane suka shigo dukkansu sunyi shiga ta alfarma cikin kayansu masu kyau, harda Aunty Amna a cikinsu, zuwa tayi kusa da Ammah sannan tace mata "Ammah motocin sunxo sunce a shirya a fito, tace toh sai kije ku fara tafiya, ni Sadiq ne zai kaini ku tafi tukunna", Farida ce ta fara fita, motan farko tabi, Batuul dake ďingisawa kamin taje motocin sun k'are, dawowa tayi tacewa Ammah babu motocin suntafi, a ranta tana murna Allah yasa babu wanda zai dawo, "ba damuwa, bari in Sadiq yazo sai mu tafi tare", tace "toh", ta hau gado ta kwanta, Takwas da kwata Sadiq ya k'ira Ammah uace mata ya iso, yana jiranta, wasu y'an matane sunsha kyau suma zasu wajen dinner suka ce mishi, tafiya zaiyi yace ehh amma Ammah yazo ďauka, suka ce mishi tunda ita kaďai ce bari su shiga dan har yanxu motocin suke jira su dawo, gaba ďaya bayan sunyi occupying saura seat ďin gaba kawai, tare da Batuul Ammah suka sauk'o, rik'e da hannunta a hankali suka taho sabida ciwon da taji, sai da suka zo Ammah taga mota a cike, ce mishi tayi "Sadiq ya akayi haka, ina Batuul ďin zata zauna", "Ammah bansan da Batuul ba shiyasa na ďaukesu", "Shikenan kuje da Batuul ďin , bari in k'ira Alai yazo in ya sauk'e mutanen da ya kai ya dawo ya ďaukeni, Bitti shiga kuje", Batuul dai na tsaye tana ta addu'an Allah yasa ma kar a samu space ďin, cewa Ammah tayi "a ah Amma, ke ki fara tafita ni sai a sa driver ya kaini ko Ahmad ne sai in k'ira ya kaini", bata rufe bakinta ba Ammah ta hango Abutturab yana tahowa, cikin tafiyarsa ta kasaita ya nufo inda suke yana gyara hulan kanshi, k'amshin turarenshi gaba ďaya ya baza wajen, baima lura dasu a wajen ba, sai da ya k'araso yaji muryan Ammah ya ďago ya dubi inda suke, ce mishi tayi "yawwa Abu ka shiryako", yace "ehh Ammah yanxu zan wuce sunata jirana" ce mishi tayi "toh ga Batuul nan ka tafi da ita, bana son barinta ita kaďai a gida ni zamu tafi tare da sadiq", Batuul da kanta ke sunkuye a k'asa tana wasa da abin hannun da Ammah ta bata ďazu tayi saurin ďagowa ta dubeshi jin abinda Ammah tace, ido huďu sukayi ya daka mata harara tare da ďauke idonshi daga dubanta, marairaicewa yyi yace "Ammah sai fa naje hotel mun haďu dasu Massa da sauran friends ďina tukunna mu biya in ďauka Ajiddeh, tabi Sadiq kawae, ke sai mu tafi tare", Ammah tace "ka ji ka. ina ni ina wannan yawon da ka lissafa, gara dai itan, kuje da ita kawae, kuma ai Ajiddeh ba duka motar zata cinye ba da kake cewa zaka ďauko ta, iyaka ta zauna a gaba, Batuul ďin ta zauna a baya", wani irin b'acin rai yaji gaba ďaya ranshi, wai mesa Ammah ke son haďa shine da yarinyar nan ko da yaushe, a tak'aice yace "muje", snn ya juya ya nufi wajen motarsa, Ammah ta cewa Batuul dake tsaye a wajen ta rasa mey ke mata daďi "Bitti kuje kinji", a hankali ta fara ďingisa k'afarta ta isa wajen motar, wani tsaki yaja ganin yadda take tafiya kamar mai tausayin k'asa, sabuwar lambo ce bak'a k'irin mai tint glass, buďe gidan gaba tayi ta zauna , yadda ya fizgi motan ne ya tsorata ta tayi saurin sa hannunta ďaya a jikin k'ofa ďaya a wajen hand brake tana neman wani abinda zata rik'e, jin hannunta tayi kan nashi, da sauri ta janye nata hannun ta dafa gaban motar, sai da suka fita tukunna Ammah ma ta shiga na Sadiq suka fita





Gudu yakeyi akan titi kamar shi ya shimfiďa, tsabar tsoro har wani zazzabi ne taji yana son kamata, sanyi takeji sosai, hannu ta saka ta rage Ac dake aiki a motar, ganin ta rage Ac ne ya sashi juyowa ya dubeta yace "hw dare yhu! inamiki wasa ne zaki tab'a min mota, ko dan kin ganki a ciki" wayanshi ne yayi ringing ya duba yaga mai k'iranshi, bai ďauka ba har ya tsinke, haka ya dinga ringing wayan baya ďauka , daga k'arshe ma ya sata a silent, ita dai bata ce mishi komai ba, tunda abunda ke daminta ma ya isheta, ganin ya juyar da kanshi bai k'ara magana ba ta ďan kwantar da seat ďin motar ta ďanyi relaxing tare da lumshe ido dan kanta ya ďan fara ciwo , a hankali ya juyo ya dubeta yaga yadda ta jingina amma a takure, fuskanta ya kalla, idonshi ya sauk'a kan ďan k'aramin bakinta da aka sa mata purple ombre lipstick, kyabe baki yyi tare da ďauke idonshi daga kallonta yaci gaba da tuk'in shi, can ya sake juyowa ya dubeta, lashes ďinta da suka kwanto fuskarta ya kalla this time around, kamar zatayi magana ta ďan motsa bakinta, bin bakin yayi da ido, buďe idonta tayi taga idonshi akanta, da sauri ta mik'e ta gyara zamanta, shi kuma yyi saurin ďauke idonshi yayi ya mayar kan titi tare da jan tsaki, haushin kanshi yaji da ya tsaya kallonta har ta buďe ido ta ganshi, kuma fa ba wae tayi masa kyau bne, gyara zamanta tayi ta janyo kujeran, ta jingina kanta a glass ďin window tana kallon waje, a k'ofan hotel ďin yaja yayi horn aka buďe mishi ya sa kai ciki, motoci dayawa ya tarar na abokanshi suna jiranshi, duk sun shirya sunyi kyau, sauk'e glass ďin motar yayi tareda fitowa waje, inda suke ya isa, Massa ne ya fara tareshi "Kai fa wulak'ancinka dayawa Aliyu, ya zayi kazo ka bar mutane suna ta jiranka, kainefa da kanka kace babu african time 8 dot muna wajen , ana ta k'iran wayanka ma baka ďauka, har matar taka ma baka ďaukan wayanta tana ta damuna, har na rasa k'aryar da zan shirya mata ma ta yadda daga k'arshe", duk maganan nan da yakeyi Abutturab baice mishi komai ba, idon Massa ne ya faďa kan motar da Abutturab yayi parking , ce mishi yayi "Man ba cutie bace a motan can, mey takeyi a motan ka kuma", ba tare da ya kalleshi ba yace satota nayi zanje in saida ta, ya k'arasa wajen sauran abokan yana mik'a musu hannu, sai da suka gama gaisawa yace musu "kuyi hak'uri na b'ata muku lokaci, something came up, muje ko", kowa motarshi yaje ya buďe ya shiga, photographers na ta ďaukansu hotuna da video, bin Abutturab Massa yayi wajen motanshi yace "na tambayeka ya akayi ka taho da cutie kai da zakaje ďauko matarka ku wuce, ina zaka da ita, a hasale Abuturrab yace "bakaji bane, nace maka saidata zanyi" ya k'arasa wajen motansa, massa yace "Man i aint joking, am damn serious", yaje ya tsaya dab da widown da Batuul ke zaune yace "cutie", da hanzari ta ďago ta dubeshi, ce mata yayi "fito in kaiki a motana, tare zamu tafi", juyawa tayi ta kalli Abu, wani mugun harara da ya kada hanjin cikinta ya sakar mata, lkci daya ya dauke kanshi kamar bai san abinda suke faďa ba, da kyar ta iya bude baki tace " yaa Abu Bari in bi Yaa Massa tunda kaima zakaje....." tana k'ok'arin buďe k'ofa, cikin dakewa yace "come on get back, da kinsan da Massan kika tsaya sai da kika biyoni, kai kuma ka bari in na maidata kaje ka ďaukota ka kaita koma ina zaku, just follown Ammah's instruction" yana kai wa nn ya tada motarshi yaja ya bar sa wajen, tsayawa Massa yayi yabi motar da ido, toh mey Abutturab ďinnan ke nufine akan Batuul, haka rannan a wajen wushe wushe ya hanashi sakat, yau kuma ya hanata binshi, yasan kuma ba sonta yake ba, ina! dama ai babu batun so, kafaďa ya ďaga yayi hanyar motanshi, koma dai menene zaiji bayan bikin, shima convoy ďin motocin da akayi yabi a baya





Allah Allah ta rik'ayi su isa inda zasu ta rabu dashi, gashi ya wani hade rae wane hadarin kaji, ko kwakkwaran motsi ta kasa a motar, mistakenly idan ta kallesa kuma ya xabga mata harara, gate ďin gidansu Ajiddeh ya shiga dan a buďe yake kasancewar ana biki, wasu motocin sun samu sun shigo, wasu kuma na daga waje, parking yayi, y'an mata ne dayawa duk sunsha kwalliya sunyi kyau, wata ce daga cikinsu ta iso inda motan Abu yake, tace "ango muna ta jira har amarya ta gaji da jira", a takaice yace "Ae gashi nazo ďaukanta, kuyi mata magana, ko kuma bari in k'irata ta fito", harara tabi Batuul da ganinta a gaban Motan Abutturab, sae kuma tayi dariya tace "No bari inje in fito da ita dan nima yanxun daga wajenta nake", ta juya ta tafi, Massa ne ya fito yacewa sauran y'an matan suzo su shiga motocin kamin amaryar ta fito, a hankali take takowa, tun daga nesa ake ganin kyan da tayi, kayanta sai walwali suke saboda hasken dake wajen, tana k'arasowa wajen motan ta tsaya tabi abinda take kallo cikin motan da ido, buďewa yayi ya fito tare da cewa Batuul "get back" a hnkli ta buďe k'ofan motar tayi ta fito, wani irin Kallo Ajiddeh tabi Batuul dashi baki bude, Batuul bata ma san tanayi ba ta buďe gidan baya ta shige, zagayowa yayi ta gabanta yace "wifey" yana kallonta tare da buďe mata k'ofan, wani irin kallo ta sakar mishi tace "Aliyu mey haka?, wane sabon wulak'anci ne kuma wannan, ya zaka zo ďaukana zamu tafi dinner sai kazo da wata, motan nan fa musamman mukayi order saboda in shiga ranan nan shine ka ďauko wata a ciki", shiru yyi yana kallonta sanin gskya ta fada, hannunta ya kamo ya wara mata manyan idonsa yace "c'mon its your happy day, meye dan wata ta shiga, Batuul cefa ba kowa ba, my cousin sis bbu motar da xata shiga ne shi sa Ammah tace in daukota nima ba a son raina ba coz ke naso ki fara shiga motar", a fusace tace "ai nasha faďa maka ni bana son yarinyar nan, wlhy hankalina baya kwanciya duk inda na ganta, kuma ya xaka yrda ta biyoka bayan ga motoci da drivers a gida", Iska ya furzar daga bakinshi a fusace yace mata "get in, in kuma baxa ki shiga ba ki koma gida" yana kai wa nn ya zaga mazauninshi ya zauna, sai da taga dama tana cika tana batsewa sannan ta shige motan, yana fita sauran motocin suka bi bayanshi , a conference hall akayi dinner, suna shiga mutane duk sun hallara, shi da kanshi ya fito ya buďe mata k'ofa ta fito tana ta b'ata rai tana cin magani, Aunty Amna ta fito ta samesu tace k'annen ango ne zasu shigo da amarya, tsayawa Ajiddeh tayi tana jiran taga su waye k'annen Aliyun da zasu shigo da ita, a hankali Batuul ta fara ďingisa k'afarta zata shiga hall ďin, Aunty Amna ce ta tsaida ita, Batuul tsaya ku shiga da amarya, Farida na fitowa, tana gama rufe bakinta Farida ta fito, su suka tsaya a gaban amarya kaďan , Batuul a hannun hagu, Farida daga hannun dama, sai Abutturab daga gefen Farida, kiďa ne ke tashi a hall ďin kowa yy kyau ssae, sae da suka shigo hall din Batuul tayi tuntub'e don dama ďingisa kafan takeyi, kan ta kai kasa Abutturab yayi maza ya rik'ota, shiru hall ďin yayi kowa idonshi da hankalinshi yayi kansu duk da basu karaso ciki ba gaba daya don da yawa sunyi

1 Comments On BATUUL
avatar
hafsat-9-3

12 months ago

Reply

Nice book

Please Login or Register in order to submit comment