Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bai bata kud'i ba, d'an tab'a table d'in yayi yace "y'ar uwa tunanin mey kikeyi, you are too young for that", sai a lokacin ta d'ago ta kalleshi da murmushinshi mai kyau a fuskanshi, ajiyar zuciya tayi tace "Ba tunani nakeyi ba", tsareta yayi da ido yace "okay tell me what we just said", shiru tayi ta d'auke kanta, murmushi yayi yace "you see you can't say, ki dena its not good for you at such a tender age", batace mishi komai ba itadai, dan tama manta da sunanshi ko jiya da ya fad'a musu, alama yayiwa waiter yaxo, ce mishi yayi ya bashi bill d'insu, shi ya biya musu duka kud'in abunda sukaci, duk da suna ya bari bai sauraresu ba, Samantha ce ta mik'e tace "okay Mr Shaheed, we got class now, hope to see you ltr, and thank you for all" murmushi yayi mata kawai yana kallon Batuul dake Zaune, ciwon cikinta na dad'a k'aruwa, a hankali ta mik'e tana kallonshi taga shima ita yake kallo suka had'a ido, maza tayi ta d'auke idonta tace mishi "mun gode" murmushin sa na nan fuskanshi har lkcn yace "its okay", daga haka suka mishi Sallama suka wuce, bayansu yabi da kallo har sai da ya dena kallonsu ya juya tareda murmushi, suna tafiya Samantha tace "He is such a gentle man, am already crushing babes", Aisha kawai ta biye mata Batuul kam shiru tayi tana jin abinda ke damunta har suka isa class






Abuturrab na fitowa ya shiga Duddubawa ko zai ga motar driver amma wayam, da mamaki ya ciro waya ya k'irashi, yana d'agawa yace "I didn't say you should leave, where are you guys", a daburce driver yace "Sir Ma'am insisted we should leave, and am by d office now, av already dropped her", rai a b'ace ya katse k'iran ba tare da ya jira driver ya k'arasa magana ba, he wanted giving her money, kuma inma ta gama lecture ya za ayi tasan anzo d'aukanta, d'an tsaki yaja ya fad'a motarsa, awa biyu sukayi suka fito daga class d'in, gumi sosai takeyi tsabar azaban ciwo amma ta daure dan bataso su Aisha su sani, Aisha ce ta fara yi musu sallama ta wuce yau da yayarta zasu tafi, bayan minti kamar Sha biyar Samantha ma ta wuce, sai lokacin tayi tunanin bata fad'awa driver ya dawo lokacin ya d'auketa ba ya fad'o mata, waje ta nema ta zauna ta kifa kanta kan gwiwa ta fashe da kuka, sunan Aunty kawai take k'ira, ita Yanzu ya zatayi ga ciwon ciki da zai hanata takawa ta tafi da k'afa tunda ba nisa sosai, gashi bata da kud'i bare tayi karambanin hawa Bus ko Taxi tunda ba lallai ma ta gane ba, kuma batada number Yaa Abu bare ta k'irashi tace ta gama lectures azo a d'auketa, to in ma tana da shi iya kiransa xata yi, kuka sosai takeyi kamar wacce ake zanewa, tafi awa d'aya zaune a wajen, kamar daga sama taga mota yaja ya tsaya gabanta, a hankali ta d'ago rinannun idanuwanta dai dai lokacin da ya fito daga motan, tsayawa yyi ya hade rae yana kallonta, sunkuyar da kai tayi ta mike a hnkli tana jan kafa ta xaga xuwa seat din gaba, tana shiga motar shi ma ya shiga ya rufe, ya juya yana kallonta fuskarsa daure sae dae fa har da borin kunyan daxu da safe yace "How dare yhu xan ba driver na order ki sa ya ketare? Kin yi employing driver ne garin nn?" D'ago kai tayi tana kallonsa, sae a snn ya lura da idonta da yyi ja, kana ganinta kasan kuka tayi, d'an kyabe baki yyi ya tada motar ya ja ya nufi gida, jinginar da kanta tayi jikin kujeran motar ta lumshe ido tana jin ynda ciwon cikinta ke karuwa ba kadan ba, yana gama parking a garage ya bude motar ya fita ba tare da ya bi ta kanta ba, da kyar ta bude motar ta fito, bata jira ya kulle motar ba ta nufi cikin gida, bin ta yyi da kallo yana mamakin halinta, komai kuka kmr wata 'yar goye, tsaki yyi ya rufe motar ya nufi cikin gidan shi ma. Bbu kowa falon Batuul ta haura sama da sauri ta shige dakinta ta sa key ta fada kan gado ta cusa kanta cikin pillow ta dinga rusa kuka kamar ranta zae fita, juye juye ta shiga yi ta sauko k'asa ganin kwanciyar ma ya gagareta, kan kace me duk ta fita hayyacinta. Abuturrab kam bedroom dinsa ya shiga, ya nufi toilet yyi wanka, xaune ya samu Ajiddeh dakin da ya fito, ta mike tace "Babe wllh na mance ban gaya maka ba, lotions dina sun kare, gashi akwae wani turare don nake son siya, xan kuma sake kayan make up" wani kallo ya shiga mata yace "Wae ke wace irin mace ce Ajiddeh, how on earth mijin ki xae dawo daga aiki bbu sannu da xuwa, baki bari ya huta ba, baki kawo masa ko ruwa ba ki xo kina masa lissafe lissafen banxa, to bani da kudin siyan komae ynxu" sakin baki Ajiddeh tayi tana kallonsa, sae kuma ta ja tsaki tana hararansa cike da fitina tace "Toh idan ban maka lissafe lissafe ba Aliyu wa xan ma, ko ina da su xan xo ince maka bbu, ubana xan kira ince yyi min bayan kana da halin min" kayansa ya sa ya fice daga dakin ya bar ta nan tsaye, downstairs ya sauka ya kwanta dogon kujera ya lumshe ido, to ita kuma wancan kukan me take a sch, tsaki yyi ya mike xaune ya jinginar da kansa jikin kujera, shi kam kawae wahala aka hadasa da, mikewa yyi ya koma sama ya nufi dakin Batuul, kwance ya sameta kasan dakin tana juye juye tana kuka, tsayawa kallonta yyi da mamaki, shi dae ya shiga uku, karasawa dakin yyi ya durkusa gabanta ya dagota yana kallonta yace "Wae ke kina da hankali kuwa?" Kuka take tana yarfe hannu tana neman kwace kanta daga rikon da yyi mata, jawota yyi jikinsa don xuwa ynxu ta d'aga masa hankali yace "Wae wats wrong with yhu, me ya faru ki gaya min? Talk to me plss, What happen" rufe fuskarta tayi jikinsa tana kuka, ya dago kanta yana kallonta yace "Fateema!" Da kyar tace "Cikina ke man ciwo" yace "Ciki kuma? What did yhu eat at sch" girgixa masa kai tayi ta runtse ido tace "Nothing!" Sae kuma ta fashe da kuka, duk ta rikitasa yace "Wait yana maki haka a gida ne, wani irin magani ake siya maki?" Boye fuskarta tayi jikinsa taki cewa komae sae kuka don ita kadae tasan axaban da take ji, murda kofar dakin aka yi, ae da sauri ya turata ya mike ya koma baya, Ajiddeh ta shigo ta tsaya daga bakin kofar fuskar nan nata daure tana kallonsu, kame kame ya shiga yi yace "Kinga babe wae cikinta ke ciwo kuma taki fadin cause din, nd nd... Wat are we going to do to her then, ko mu tafi clinic?" Ajiddeh ta yatsine fuska tace "Cikinta ke ciwo ko kuma tana Al'ada?" Kallon Ajiddeh ya tsaya yi kafin ya juya ya kalli Batuul da tayi k'asa da kai tana hawaye, Ajiddeh ta watsa mata harara tace "Ko ba jini bane?" Ae Batuul k'asa dagowa tayi, Ajiddeh ta ja tsaki ta fice daga dakin, kallonta Abuturrab ya tsaya yi, [truncated by WhatsApp]
[8/22, 14:47] Umar Dalha: πŸ’–πŸ’BATUULπŸ’–πŸ’






52






By phartiemarhk






Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*





K'arasowa yayi gabanta ya d'agota yana kallon yadda gumi yasa front hair d'inta kwanciya, sae kuma ya hade rae yace "dama haka yake yi miki can gida" jin taki cewa komae ya jawota jikinsa, ya rasa dalilin da yasa tausayinta ke shigansa hka, ko don amanarta Ammah ta basa ne yasa hakan, k'asa yyi da murya yace "Tambayan ki nake, talk to me" sake shigewa tayi jikinshi tana riqe cikinta, kuka ta shiga yi mishi tana ta mutsu mutsu, gaba daya ta rikitashi da kukanta, kokarin tashi takeyi daga jikinshi ganin amai na shirin zuwa mata, ya riketa yana kallon fuskanta da ya gama jikewa da hawaye yace "kina da magani ne" kai ta shiga girgiza mishi, wani karfi taji yazo mata ta janye jikinta daga rikon da yayi mata xata mike ya rikota yace "ina zakije", yana mata mugun kallo dan ranshi ya fara b'aci, bakinta ta toshe tana girgiza mishi kai, ce mata yayi "amai zakiyi", kai ta gyad'a mishi sauran hawayen idonta na k'arasa zubowa, k'arasawa yayi da ita toilet d'in, tun kan su shiga ta shiga kwarara amai nan bakin kofar, har ta gama yana riqe da ita, da k'yar ta samu ta miqe, jiri ne taji yana kwasanta ta sulale k'asa a wajen, binta yayi ya kamota jikinshi tare da miqar da ita, babu abinda takeyi sai hawaye, d'ago kanta yayi yana kallonta yace "are you done", kai ta gyad'a mishi ta maida kanta ta kwanatar jikinshi dan rashin k'arfi, ji takeyi kamar zata fad'i in ba a riqeta ba, gaban sink ya dawo da ita har lokacin tana jikinshi, sai maida numfashi takeyi, tap din sink din ya kunna, ya sata wanke baki da fuskanta, har ta gama. Idonta na rufe, bata ankara ba sai ji taji ya sunkuceta a hannunshi, ta bud'e ido da sauri tana kallonshi, harara ya sakar mata ya wani hade rae, maza tayi ta rintse ido har saida taji ya sauk'e ta kan gado tukunna ta budesu a hankali, bayanshi kawai ta iya gani har ya kai bakin k'ofa, rintse ido tayi hawayen azabar take ji yaci gaba da zubowa, pad d'in da zatayi amfani da ma ita batasan ina zata samu ba tukunna, kuma tunda har tayi amai, ya kusa zuwa kenan, yana fita d'akinshi ya wuce, zaune kan gado ya tadda Ajiddeh, da alama waya ta gama, bai bi ta kanta ba ya wuce ya d'au keyn motan shi yayi hanyan fita, a guje ta diro daga kan gadon ta sha gabanshi tace "yaushe ka dawo ne da har zaka kuma fita Aliyu, kuma ina zakaje da yamman nan hka", bae tanka ta ba ya bi gefenta ya fita, ganin yayi hanyan d'akin Batuul yasa ta k'ara hasala ta sha gabansa tsabar masifa har idonta ya kankance tace "Aliyu ba dai gun wannan yarinyar zaka ba, wannan ai iskanci ne, period dinne takewa iskancin nan kamar yau ta farashi, ko kuma sabon salon karuwancin nata ne hakan", wani mugun kallo ya bita dashi ya sa hannu ya matsar da ita gefe ya ci gaba da tafiyarsa, biyoshi tayi a baya tana ta mishi surutun da baima san mey take fad'a ba, k'ofan d'akin Batuul ya tura ya shiga, tana kwance kan gadon nan inda ya barta, k'arasawa yayi bakin gadon daga tsayen da yake yace "zaki iya tashi?", a hankali ta bud'e lumsassun idonta ta kalleshi, hade rae yyi ya sake nanata mata tambayan, k'ok'arin tashi ta shiga yi, da k'yar ta samu ta mik'e xaune, hijab dinta dake gefe ya mik'o mata ta saka, Ajiddeh dake bakin k'ofa baki ta sake tana kallonshi tana huci, da k'yar Batuul ta mik'e yana kallonta yace "can you walk?", a hankali ta gyad'a masa kai, ita ta fara wucewa gaba yana binta a baya, ja tayi ta tsaya ganin Ajiddeh bakin k'ofa, a d'an tsawace yace "muje mana", a hankali ta juyo idonta yayi raurau tana kallonshi, hannu yasa ya rik'ota, har bakin k'ofar ya isa da ita, wani mugun kallo yayi wa Ajiddeh cikin kakkausar murya yace "give me way", ganin yanayin da yayi magana ya sata tsorata, bata tsaya musu ba ta matsa daga bakin k'ofa, tana yi ma Batuul wani mugun kallo da yasata saurin d'auke kanta, a hankali yake tafiya tana biye dashi har suka isa bakin stair case, ji tayi cikinta yayi wani irin kullewa, ae bata san lkcn da ta sulale ta zube wajen ba tace "Ya salam" ya salam
d'in da ta ambata ne ya sashi juyowa da sauri durkusawa gabanta yyi ya shiga tamabayanta baza ta iya tafiya bane, a wahalce ta gyad'a mishi Kai, hannu yasa ya d'auketa cak, Ajiddeh dake tsaye a bakin k'ofa, a tsorace take kallonsu, sosai zuciyanta yake bugu kamar zai fito, idonta har ya cicciko, har cikin mota ya sakata sannan ya zaga shima ya shiga ya tada suka bar gidan, driving yakeyi lokaci lokaci yake juyowa yaganta tana ta murk'ususu, wayanshi ya d'auka ya sanar da doctorn shi gasu nan zuwa, har suka isa asibitin idonta rufe yake tana hawaye, shi ya taimaka mata ta fito, tana riqe jikinshi suka isa cikin asibitin, direct office d'in consultant d'inshi ya wuce da ita, sai da ta zauna shima ya zauna, bayan sun gaisa ya juya yana kallon Batuul yace "Hello young lady , what's d problem", shiru tayi ta kasa ce mishi komai, Abutturab ne ya kalleta yace "baza ki bud'e baki ki fad'a mishi abinda ke damunki ba", kanta ta kauda gefe, likitan ne da kanshi ya mike yace "its okay, let me examine", tashi yayi ya matsa gaban computer shi sannan yace mata ta taso ta kwanta kan gadon dake office din, a hankali ta mike ta isa kan gadon, kallonsu kawai Abutturab keyi ganin yadda take ta gyara hijabin jikinta bataso a d'age, sai da likitan yayi y'an gwaje gwajenshi sannan ya dawo kujeranshi ya zauna yana kallon Abu yace "Is she married?" Kai kawae Abuturrab ya gyada masa, likitan yace "Alryt! she is having menstrual cramps which is caused by the condition of the reproductive tract, such as the endometriosis, uterine tissue that appears outside the uterus, it also happens because the contradictions in the uterus or womb, which is a muscle, if it contracts too strongly during her menstrual cycle, it can press against nearby vessels. This briefly cuts off the supply of oxygen to the uterus, it's this lack of oxygen that causes the pain or cramping", har saida yayi shiru tukunna Abutturab yace "But can it be avoided or controlled?, I mean the pain", murmushi likitan yayi yace "well yeah it can, the pain usually stops when they get married or even after delivery, so maybe when she delivers as you say she is married and she still encounters d pain, If its a mild menstrual cramp, she should take aspirin or another pain reliever, such as ibuprofen, naproxen or acetaminophen, its for d best relief as soon as bleeding cramps start", kallon inda take kwance yayi yaga idonta na lumshe, sannan ya juyo yana jin sharhin da likitan ke mishi, Kowa da inda kwarewarsa take, ya kalli doctor yace "Doctor but is there any home remedy for it, like first aid treatment", kai likitan ya gyad'a yace, "Heat can also help, placing a hot pad or a hot water bottle on her back or lower tummy, taking a hot water bath may also provide some relief, rest when needed, avoid food that contain caffeine and salt, not use tobacco or drink alcohol, too much sugar also should b avoided and chocolates also, massaging of the lower back and abdomen, women who exercise regularly often have less pain also", ajiyar zuciya Abu yayi, murmushi likitan yayi yace "its normal you should not worry, just that others experience more pain, I will b giving her an aspirin injection now, she will b okay", mik'ewa yayi ya isa inda take kwance ya shiga had'a alluran da zaiyi mata, ji tayi kamar mutum na tsaye a kanta, a hankali ta bud'e idonta, kan Alluran dake hannun likitan idonta ya fad'a, a zabure ta mik'e tana girgiza kai, da murmushi a fuskanshi yace "It won't hurt much young lady" hawaye kawai takeyi tana kallon Abu, tasowa yayi shima ya dawo gaban gadon yana mata wani irin kallo, kuka ta fashe da tace "Yaa Abu allura zaimin, banaso xae daina min da kanshi after somedayz", rik'ota yayi jikinshi yace "shhhh, he said it, it won't, close your eyes", rintse ido tayi, shi ya janye hijabin dake jikinta, k'ank'ameshi tayi idonta rufe har aka tsikara mata alluran, sai da aka gama ya d'agota , drugs likitan yayi musu prescribing daga nan sukayi mishi sallama suka wuce, shi ya taimaka mata har wajen mota sannan ya zaga ya shiga shima, a wajen wani saida abinci ya tsaida motanshi, juyawa yayi suka had'a ido tayi maza ta janye nata, "I will b right back", ya fad'a mata sannan ya wuce, kafin ya dawo harta yi bacci dan ciwon ya fara saketa, ganin tana bacci yasashi murmushin da baisan dalilinshi ba ya shiga motan, k'ok'arin gyara mata kwanciya yayi, a hankali ta bud'e idon baccinta ta kalleshi, yana kallonta yace "sleep back", gyara kwanciyarta tayi taci gaba da baccinta har suka isa gida, a hankali ya shiga tashinta bayan ya gama parking, lumsassun idanunta ta bud'e, yace mata "we are home", jiki ba k'wari ta sako k'afa waje ta fito, shi ya d'auko ledan magani da abincin da ya siyo ya biyota dashi a baya, d'akinta ta wuce kai tsaye ta fad'a gado taci gaba da baccinta. Ajiddeh kam suna barin gidan dama ta shige dakinta da gudu tana rusa kuka ta dauki wayarta ta shiga kiran layin uwarta, sae da ya kusa katsewa aka d'aga, ta fashe da wani matsanancin kuka daga daya bangaren uwartata a rude ta shiga cewa "subhanallahi, lafiya Ajiddeh me ya faru?" Cikin kuka tace "Wayyo Mumy ni na gaji da wnn wahala da nake yi kan Aliyu, Mumy ina cikin tashin hankali don ga dukkan alama wllh aiki ya lalace gaba daya, sae kin ga abinda yake min ynxu, walakancin yau daban na gobe daban, ga shegiyar da ya dawo tare da ma na rasa yanda xan yi da ita a gidan, yanxu haka fa tare suka fita don iskanci wae tana al'ada ta ishe mu da kuka a gida, sae kin ga walakancin da yayi min da na tambayesa inda xa su, wayyo ni Mumy kar ta kwace min miji ya ji yana sha'awar aurenta don wallahi sae kin ga yanda ta iya girki yarinya" cikin matsanancin kuka ta kare maganar, Mumy tace "Ke dae shashasha ce wllh Ajiddeh, ina ruwan ki da wata yar iska can ke da xa ki turo kudi mu koma gun bawan Allahn can a san abun yi, da yyi niyyar aurenta ae ba ke xae aura ba ita xae aura tunda sun fi kusa can munafukae, kawae dae an hado shi da ita ne don take maki lekan asiri ke kuma wawuya baki gane ba, har xaki wani d'aga hankali ke da xaki saita ma shegiyar xama ta ji xaman gidan ma ya isheta, yarinyar da ba ma wani kyau gareta ba in ban manta ba sae wani dogon hanci kmr tsiya, meye kuma xaki damu kan ki, yana da kamar ki fara doguwa siririya kyakkyawa ga diri, g'ashi har gadon baya, yanxu dae ko kudinsa ya kama ki dauka kawae ki dauke ki turo mu san abun yi, ita kuma shegiyar ki daina d'aga hankali kanta baxa ta dade maki a gida ba nasan abinda xan yi" Ajiddeh na share hawayen idonta tace "Toh shknn Mumy xan turo ko xuwa gobe" nan Momy ta dinga mata hudubar tsiya tana digesting har taji tsayawar motar Abuturrab, ko kan ta fito har Batuul ta shige daki dama, hakan yasa ta nufi stairs, suka kusa cin karo da shi, kallo daya yyi mata ya ga ynda idonta ya kumbura saboda kuka, ya bi gefenta xae wuce ta sha gabansa tana masa kallon raini tace "Wllh yau sae dae ka xaba ko ni ko wancan karuwar a gidan nn, idan ba karuwanci ba don tana jini har sae ta so ka sani tana wani murkushe murkushe kana daukar ta? Ta ina ta xama muharramar ka, to Allah baxa ta kwanan min a gida ba yau, ka je ka biya mata hostel" banda tafasa bbu abinda xuciyarsa ke yi, acting gently yace "Bani hanya in wuce" tana masa matsiyacin kallo tace "Naki sae ka xabi ko ni ko karuwan can" cikin kakkausar murya yace "Xa ki sa na maki abinda ban taba maki ba Ajiddeh" wani shewa ta saki tace "Ka Dade baka yi ba Aliyu, uwar meye baka min ba daga cikin walakancin ka har...." Bata rufe baki ba taji saukan lafiyayyun mari har biyu ya shaketa ya ja tun daga sama har suka sauko k'asa ya jefar da ita yyi wani irin ball da ita, ae daina gani tayi na 'yan dakiku, bin ta yyi yana huci ya kuma fixgota yace "Don kaza kazan ki ke kika koya mata karuwancin?" Cikin tsawa yace "Answer me kar in sumar da ke a nn, kin san matsayin ta a gidan nn kike kiranta da karuwa?" Jefar da ita ya kuma yi ya nufi sama yana huci.
[8/22, 14:48] Umar Dalha: πŸ’–πŸ’BATUULπŸ’–πŸ’






53






By phartiemarhk






Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*





D'akinshi ya shiga bayan ya kwashe ledojin da ya zubar corridor tun lokacin da Ajiddeh ta fara mishi shirmenta, babu abinda yake buk'ata irin ya watsa ruwa a lokacin, toilet ya wuce ya sakarwa kanshi hot shower, har saida yaji ya fara komawa daidai sannan ya fito daga cikin cubicle d'in wankan, alwala yayi a sink sannan ya fito cikin toilet d'in, gaban vanity table ya tsaya ya shafa mai sannan ya fesa turarukanshi masu k'anshi, closet d'inshi ya bud'e ya ciro farar jallabiya cikin jerin jallabiyoyin dake a ciki, xirawa yayi har xai fita idonshi ya fad'a kan ledojin dake ajiye a k'asan d'akin, d'an tsaki yaja ya kwashi wasu daga ciki ya fice waje, d'akin Batuul ya wuce kai tsaye ya tura k'ofan ya shiga, tana kwance kan gado ta kifa cikinta, rabin k'afanta duk ya sauk'o daga kan gadon, d'an tsaki yaja ganin bacci takeyi ya ajiye ledojin dake hannunshi ya fita, makulli ya sa ma kofar dakin ya rufe, snn ya sauk'o kasa don tafiya masallaci, bai tarar da Ajiddeh a palon ba ya fice masallaci, sai da akayi isha sannan ya shigo gidan, wutan palon ya kashe ya haura sama, har lokacin Batuul na bacci, a hankali ya d'an tab'a ta alamun ta tashi, a hankali ta bud'e idonta daga nannauyan baccin da take yi, ganinshi a tsaye yasa tayi maza ta mike zaune, had'e rai yayi yace "tashi kici abinci kisha maganinki", baki ta bud'e zatace mishi ita bata jin yunwa, wani kallo da ya bita dashine ya sata zumb'uro baki ta miqe a hankali, yana tsaye ta shiga toilet tayi brush ta fito, kamar zatayi kuka lokacin da ta fito daga toilet d'in dan har ta fara bleeding kuma bata san inda xata samu pad ba, har lokacin da hijab a jikinta, kan gadon ta koma ta zauna a d'arare, tana tsoron b'ata bedspread d'in, "Ni zan tashi in kawo miki abincin", ya tambayeta yana jifanta da wani irin kallo, jiki a sanyaye ta mik'e zata sauk'o daga kan gadon ta take dogon hijabin dake jikinta, fad'uwa tayi k'asa ji kake tim, y'ar k'ara ta saki da yasa Abu saurin k'arasowa wajenta, d'agota yayi yana kallon idonta da ya cicciko yace " c'mon kin cire hijabin nan ko sai na b'ata miki rai yanxun nan, yhu are bothering me fa a gidan nan", raurau tayi da idonta tana tsoron ta cire hijabin dake jikinta ko tayi staining kayanta, ganin ta tsaya taqi yin abunda ya sata ya sa ya d'age hijab d'in da take qin cirewan, y'ar k'ara ta saki ta d'urk'ushe a wajen, binta yayi ya kamota yace "ina miki wasa ko", kai ta shiga girgiza mishi tana hawaye, yace "Au kuka ma kika sami daman yi?", sulalewa ta shiga yi daga rik'on da yayi mata zatayi k'asa, ya wani fixgota yana mata mugun kallo yace, "I will slap you right now, meke damunki?", shiru tayi ta kasa mishi magana, tsaki yayi ya turata "tashi ki d'auki abincin nan" ya fad'a mata a tsawace, jiki a sanyaye ta tashi ta isa inda ledojin

1 Comments On BATUUL
avatar
hafsat-9-3

12 months ago

Reply

Nice book

Please Login or Register in order to submit comment