Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Aljihu, ďayan ne ya koma daga gefen Abutturab yace mishi "ai gaskiya ka faďa, mu yara ne sosai ma, kai da zaka zama ango next few weeks ai kam ka zama babba", harara Abutturab ya jefa mishi yace " kuyi mana kuma auren, kun zauna kuna abun yara har ana yin sallama bakwa ji", Massa ne ya dubi wanda ke gefen Abutturab yace mishi "Abba faďa mishi ai jira muke manya su fara yi sai mu bisu a baya", dariya ma suka bashi yace "Ku kuka sani, mu munyi gaba", haka suka ci gaba da hira suna tsokananshi, sai 10:30 ya tuna da su Farida, mik'ewa yayi cikin hanzari yace "shit", binshi sukayi da ido suna so ya gaya musu abunda ya faru, kallonsu yayi yaga duk shi suke kallo , ce musu yayi "wlhy su Farida na kai wajen prom kuma nace by ten ya kamata in je na manta", Massa ne yayi maza yace "yawwa i wanted to ask you that girl, k'awar Farida ce ko, she is damn pretty, she is so densed, she is ....." , bai k'arasa ba Abutturab yace mishi "Hey meye hakan, k'awar Farida ce fa, yarinya ce fa kake cewa she is so densed, yarinyar da bata fi sixteen yrs ba", da ido suka bishi ganin bai tab'a shiga maganan y'an matansu ba, fita yayi daga ďakin bai ce musu komai ba






A Tulip bistro yaje yayi parking, wayanshi ya ďauko yayi dialing number Farida ba a ďauka ba, sai da ya k'ira wajen sau goma ba a ďauka ba, buďe k'ofan motan yayi ya fita daga ciki ya shiga cikin hall ďin, fuska a tamke ya shiga hall ďin ya tarar ana ta hayaniya, Farida ya hango a kan stage ita da wasu friends ďinsu suna zazzaune a zagaye sunyi round suna playing truth or dare, rasa ya zai yi ya k'irata yayi dan ko yayi ihu ma baza taji ba, Batuul ya hango daga gefe ta zaune ita kaďai a kan kujera da awards a kan table ďin da take tana danna waya, deciding yayi kawai yaje yayi mata magana ta k'ira Farida su tafi, inda take ya k'arasa ya sunkuyo daidai kunnenta zai yi mata magana dan yasan ba lallai taji ba in ya tsaya yi mata maganan kuma bayason su b'ata mishi lokaci,k'anshin turaren da taji ne ya sata saurin ďagowa , heart beat ďinta ya k'aru, waigowa tayi da sauri suka kusa cin karo, zata mik'e ya sa hannu ya maida ta, tsayawa tayi tana kallonshi a tsorace, shima fuskanta ya tsaya kallo yadda lights ďin ke haska stones ďin jikinta sai ya k'ara mata kyau, lkci daya kuma ya hade rae, hannunta ta motsa alamar ya sake mata, sake mata hannunta yayi yace mata "Go and call your friend , ina jiranku a waje", juyawa yayi ya fita daga hall ďin, mik'ewa tayi bayan ya fita jiki a sanyaye ta isa inda Farida take tace mata "Yaa Abu na jiranmu a waje", fita Batuul tayi bayan tayi sallama da mutane ta isa inda motar ke pake, shiga tayi ta zauna daga baya, ta ďago idonta kenan zata ce mishi Farida na fitowa suka haďa ido huďu ta mirror, maza tayi ta ďauke nata tace mishi "tana fitowa" a hankali, Tare da Affan Farida suka fito kamar ka su rabu, sallama sukayi ta shige gaba dan horn ďin da Abu ya danna, direct gida ya wuce dasu, suna shiga gida suka wuce ďakin Ammah suka ga tayi bacci, a hankali suka jawo mata k'ofan suka wuce nasu, kayan jikinsu suka cire sukayi wanka, sukayi sallah isha, bayan sun ďanyi hiran event ďin yau suka kwanta bacci





THREE WEEKS LATER
A firgice Batuul ta tashi daga baccin da take tana ambaton sunan Allah.....
💖💝BATUUL💖💝






17





By phartiemarhk





Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*








THREE WEEKS LATER

A firgice Batuul ta tashi daga baccin da take tana ambaton sunan Allah(a uzu bikalimatillahi tammat, min sharri ma khalaq, bismillahi llazi la ya dduru ma'as mihi shay'un fil ard wa la fis sama'i wa huwal aliyul azim), zama tayi akan gadonta, gumin da ya tsatsaffo a fuskanta ta sa hannu ta goge, mamakin irin mafarkin da tayi yau tayi, tasan mafarkanta na tsoro basa wuce macizai amma na yau daban ne, mik'ewa tayi tabi hanyan toilet ta shiga, ruwa ta watsa tare alwala ta fito, hijab ďinta ta ďauka ta saka sannan ta shimfiďa abun sallah ta hau ta fara nafilfili, bayan ta idar sosai tayi addu'a Allah ya kare ta daga sharrin abun ji da na gani sannan ta ďauko Quraninta daga kan bedside drawer ta karanta, sai da ta gama karanta suratul Anbiya' da Hajj sannan ta duba agogo taga k'arfe biyar, zama tayi a kan abin sallah ta ci gaba da addu'o inta har aka tada sallah a masallaci ta mik'e tayi raka'ataynil fajr ,tayi sallah asuba, tana idarwa tayi azkars ďinta na safe sannan ta mik'e ta cire dogon hijab ďin dake jikinta ta ninke shi tare da abun sallah ta maidasu inda ta ďaukosu, gadonta ta koma ta kwanta, sai da tayi addu'a dan ta tsorata ďazu sosai sannan ta ja bargon ta rufe jikinta dashi ta kwanta, bata tashi ba sai sha biyu saura, ta mik'e taje tayi wanka ta saka wani riga da skirt k'arami mai kyau bata ďaura ďank kwalin kayan ba sai hula kawaj da ta saka a kanta, k'asa ta sauk'o bayan ta gama shafa mai, babu kowa a gidan, a ranta tace mayb mazan sun tafi ball ko tennis ďinsu na jaraba, Aunty da Yusra kuma na gidan biki, sai da taci abinci sannan ta koma palo ta ďau remote ta canja favorite tashar ta star plus, mik'ewa tayi ta koma sama dubo wayanta, missed calls uku ta gani, ďaya na Aunty biyu na Farida, Aunty ta fara k'ira, tana ďauka tace "Hello Batuul, mun fito kina bacci, ki shirya a kawoki gidan bikin , Farida ma na ta tambayanki", sai da Aunty ta gama tace "Aunty kaina ke ciwo tun da na tashi, bana son zuwa saboda hayaniya", da damu Aunty ta ce mata "kinsha magani Batuul", "eh", tace sannan ta ce mata "ki kula da kanki sai mun dawo, zan k'ira su Janet a waya in faďa musu suna dubaki sannan suka katse wayan", suna gamawa tayi dialing number Farida, Farida na ďauka tace "wane irin bacci kikeyi haka har na k'ira twice bakiyi picking ba", ce mata tayi "wayan fa yana ďaki ni kuma ina k'asa, toh meye ma na k'irana da sassafe , ke da ake hidima a gidanku", "ai hidiman ne ya sani k'iranki, wlhy gidan ya cika da mutane , babu daďi, am coming over to your place", kamin Batuul ta sake magana ta katse wayan,





A Protea hotel dake asokoro suke zaune, vip apartment suka kamawa abokanansu da suka zo ďaurin aure, hira suke ana ta tsokanan ango, bai ce musu komai, kanshi ya dafa ya rik'e da k'arfi dan wani ciwo yake mishi sosai kamar zai rabe, wayanshi ya ďaga ya k'irawo Massa dake cikin sauran abokan nasu, ďagowa Massa yayi yaga mesa yake k'iranshi bayan suna zaune a tare, ganin ya rik'e kanshi ne ya sashi tashi ya isa wajenshi, tambayanshi yayi bayan ya rik'e hannunshi da ya rik'e kan nashi dashi "Aliyu lafiya naga ka rik'e kanka, meke damunka", a hankali yace mishi ka kaini gida kaina na ciwo", tare da mikvewa yayi hanyan k'ofa, binshi Massa yayi a baya yace "toh ai gidanku ma da hayaniya, muje in munga doctor sai mu wuce gidanmu ka kwanta, stress ne yayi maka yawa", sai da suka je bakin k'ofa Abba ya ce ina "ina kuma angon zai tafi, tun ďazu yake b'ata rai yayi shiru yana ta tunani, saura fa kaďan ka k'ara hak'uri mun kawo maka ita", sauran ne suka sa dariya suka ci gaba da shak'iyancinsu, Massa ne ya dubesu yace "am sorry dan Allah zamuje mu dawo, Abba call me if ana needing wani abu", lokacin har Abutturab ya fita shima ya bishi a baya, sai da suka biya Nizamiye hospital aka duba shi aka yi mishi prescribing drugs sannan suka ďau hanyan gida, a hanya Massa yace mishi "Man i told you stress ne ke damunka, these days tunaninka ya cika yawa, mey ke damunka", Abutturab ne yace mishi "kafi kowa sanin auren nan is a compromise, yes i like her but myself being married is just out of it", Massa bai ce mishi komai dan likita yace ya huta sosai so baya son ya dameshi dayawa, concentrating yayi a tuk'inshi har suka isa gida, a parlour chamber Massa ďin ya kwanta a ďaya daga cikin dogayen kujerun, Massa ne ya mik'o mishi maganin yasha ya sake kwanciya, tambayanshi yayi "in faďawa su Ammah baka ji daďi bane ko kuma ya za ayi", hannu ya ďaga mishi alaman a ah sannan yace mishi "yanxu Ammah zata tada hankalinta a kan ďan wannan abun, i will get better before event ďin yau", ya sake juyawa ya kwanta ďaya bangaren nashi, wutan ďakin Massa ya rage mishi yace sannan ya fita





Batuul bata fi minti talatin da waya da Farida ba sai gata a gidan, mik'ewa tayi daga kwancen da take ta ce mata "woh Farida , you can be in planet Mars ke ďinnan, yaushe mukayi waya dake da har zakice min kin iso", dariya Farida tasa tace "toh ai ni ďin kenan", zuwa tayi ta zube a kan kujera tace, "kinga gidanmu kuwa, ba ni akewa aure ba amma nafi masu aure wahala, hatta ďakina ya zama ba nawa ba, gaba ďaya gidan ya zama wani iri, jiya ma sai a wajen Abui na kwana, bazan iya ba, ga y'an Ndjamena nan da sa mutane aiki kamar babu y'an aiki a gidan", dariya maganan ya bawa Batuul tace "Lazy you, toh dama ai hakane if ana biki a gidanku sai kayi hak'uri, baki da k'anne da anyi suna a gidanku tun lokacin zaki gane yadda abun yake, lokacin sunan Aabid fa har cubicle ďin toilet ďina sai da aka fasa, bare naku biki, bikin ma na first child ďin gidanku ai sai hankali", ce mata Farida tayi "as in baza ki gane ba, toh aiken kuma na meye, ni ďaurin auren nan da zasu tafi maiduguri ma ya fi min komai daďi, su tafi gidan ya kima normal", "ai ba matan bane zasu ďaurin aure, maza ne zasuje a ďaura su dawo" inji Batuul, baki ta zumb'uro tace "ni dama auren Yaa Sadiq ne ma da sauk'i, amma Yaa Abu fa, ga matar ma ba shiri nake da ita, tayi ta wani girman mutum babu komai sai tsayi da fari, kina ganin duk tsayin Yaa Abu fa da kaďan ya fita, ni ďazu ma kamar naji Ammah na cewa wai a dawo da boxes ďin lefen da aka kai mata tunda sunce sunyi kaďan, 40 boxes fa wai sai an k'ara musu ya zama sixty, shine Ammah ma tacewa su Aunty Amna da suka kai su dawo dashi", girgiza kai Batuul tayi tace mata "ke dai kullum Yaa Abu, toh yanxu dai zai bar muku gidan", da sauri Farida ta mik'e daga zaunen da take tace "Ai ni daďin da nakeji ma bayan auren da sati ďaya zasu wuce UK, life will be better, babu sa ido", dariya Batuul tayi ta ďan dungure mata kai tace "ni tashi muje muyi alwala muyi sallah"




Wayan Farida ne yayi k'ara , dubawa tayi taga Ammah ke k'iranta, amsawa tayi tare da cewa "Hello Ammah", katseta tayi tare da cewa "Farida kina inane tun ďazu ina nemanki, ina kika shiga", "muna tare da Batuul ne, gidansu nazo", ce mata tayi "ke da waye kikaje gidansu Batuul ďin", a hankali tace "Baa Alai nasa ya kawoni", "toh yanxu zan turoshi zaizo ya ďaukeki ya kuje gidan Yaa Mera, zaki karb'o min sak'o", inji Ammah, da sauri tace "toh" dan murnan ba a yimata faďan fitan da tayi ba a sani ba, ta katse wayan, juyawa tayi ta dubi Batuul taga tana kallonta tana murmushi, ce mata tayi murmushin mey kike min haka, "ashe Ammah bata sani ba kika fito, da tayi miki faďa sosai ai", murguďa mata baki tayi tace "yanxu ma aikena tayi, ni a gama wannan auren mu huta, ki shirya muje mu karb'o sak'on", Batuul ce ta dube ta tace mata "in shirya muje ina?, ke ni babu inda zan fita yau, kije ki dawo", marairaicewa Farida tayi tace "haba mana, you know i love you, you love me too, muje tare kinji, i will get you pack of twix da Raffaello pls", dariya ma ta bawa Batuul tace "Noooo, dagaske babu inda zan fita, beside Aunty ma bata gida bare in tambayeta", Farida bata cewa Batuul komai ba ta shiga dialing number Aunty da wayan dake hannunta, Aunty na ďaukan wayan tace "Hello Farida ya akayi", cewa Aunty tayi, "Aunty muna tare da Batuul ne Ammah ta k'irani ta aikeni, nace ta rakani wai tace baza taje ba saboda bakya gida, Aunty kiyi hak'uri muje, gidan Yaa Mera ne, bana so in tafi ni kaďai", dariya Farida ta bawa Aunty tace mata "kice nace ta rakaki, wani ihu Farida tasa tace "Nagode Aunty, yanxu zamuje mu dawo, ta katse wayan, tsayawa Batuul tayi tana dubanta, ya zatayi da Farida ne a rayuwa, k'in kulata tayi ta tashi ta hau sama ta ďau wayanta ta bugawa Aunty, tana ďauka tace "Aunty kunyi waya da Farida yanxu ko", Aunty ce tace mata "ehh yanxu ta k'irani, ki rakata Batuul kuje ku dawo", toh kawai Batuul tace ta katse wayan, Farida ce ta biyo ta ďakin tace "zamuje ko Batuul", hararan wasan tabita dashi, tana dariya tazo ta zauna a gefenta tace "ai nasan you cant do without me", suna zaune har Baa Alai yazo yace mata ya iso su fito su tafi, mik'ewa sukayi, k'aramin bak'in gyale kawai Batuul ta ďauka ta yafa akan hulan dake kanta da wayanta, suka fita, Batuul ce ta shiga gba Farida ta zauna daga baya, har cikin gidan ya shigar dasu yayi parking suka fito su biyun, suna fita Batuul ta rik'ewa Farida hannu tace "Farida ya fara", kallonta Farida tayi tace "mene ďin ya fara?", "heart beat ďina mana, its increasing, am telling you ppl, its becoming serious", ce mata Farida tayi "sorry anjima sai mu faďawa Aunty", bata amsa mata ba dan ita kaďai tasan abunda take ji, tafiya sukayi mai ďan nisa tukunna suka isa cikin gidan, har ďakin Yaa mera suka isa, tana ganinsu tayi murmushi tace har kunzo, "wannan ba Batuul ba", da mamaki Batuul tace "ehh nice" dan batasan matar ba, matar ce tace mata "Masha Allah kin girma, tun kina 2yrs rabona dake, mamanki na gidan biki ko", da ehh Batuul ta amsa mata sannan Farida tace "Yaa Ammah ce ta aikomu wai muz...." bata k'arasa ba tace mata "ehh kuje da Ya bawa ta nuna miki inda ake aikin kiga ko sun gama" ta haďa ta da Baiwa ďaya suka tafi, Batuul na zaune tare da Yaa mera tana tambayanta abubuwa har makaranta, tace mata sunyi graduating yanxu university zasu shiga, wayanta take ta dannawa tana sawa a kunne sai ta cire, Batuul ta duba tace mata "Batuul", a hankali ta ďago daga wasan da take da zoben hannunta ta dubi yaa mera tace "na'am", "chamber ďin Massa zakije ki duba min shi inata k'iranshi baya ďauka, intercom ďinshi ma baya ďauka kuma ya shigo ďazu, ki ce mishi ina k'iranshi", bata sa komai a ranta ba ta mik'e tace "ta ina ďakin yake", kwatance tayi mata "tace in kin fita ki mik'e sai kin wuce dorms uku, chamber yana by the left", ta amsa da toh ta fita, a hankali take tafiya har ta isa ďakin, knocking tayi taji ba a buďe ba, a hankali ta tura k'ofan ďakin taga babu haske, sai ďan dim light daga ciki, kai ta sa ta shiga cikin ďakin, k'anshin da taji ne ya sata jin kamar zuciyanta zai faďo dan bugawa, tsayawa tayi a spot ďin da take ta kasa gaba ta kasa baya
💖💝BATUUL💖💝






18





By phartiemarhk





Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*






Tsayawa tayi tana juye juye in zata bi, kawai deciding tayi da ta fara sallama ko zai jiyota inma a ciki yake, sallama tayi ta yi taji ba ba a amsa ba, lalube ta fara ko zata switch ďin ďakin har ta gama lalubenta bata ga komai ba, deciding tayi toh ta k'ira sunanshi ko zai amsa, "Massa" ,shiru tayi tana jira taji ko za a amsa amma taji shiru, sau uku tana k'iran sunan taji ba a amsa ba kawai ta juya zata fita ta ga kamar mutum na kwance a kan seater, k'arasawa tayi wajen seater ta tsaya ta tabbatar mutum ne kwance a kai, broad figure ďinshi na kwance peacefully amma bata ganin fuskanahi dan ya juya mata baya, sake k'iran sunan tayi taji bai amsa ba, deciding tayi ta tab'a shi tunda baccin nashi ya kai har haka nauyi, hannu ta sa a goshinshi taji wani ďumi da laushi, maza tayi zata ďauke hannunta taji wani hannu mai laushi da faďi a kan nata, wani abu ne taji gaba ďaya yabi jikinta ga heartbeat ďin ya fara aikin nashi kamar mai shirin fitowa, idonta ya cika da hawaye tab saura k'iris ya zubo, tsayawa tayi still a wajen ta kasa ko da k'wak'waren numfashi, juyowa yayi ya jawota ta kusa faďawa kanshi tayi hanzari ta dafa kujerar, wayanshi ya ďauko daga gefenshi, flash light ya kunna ya haska yaga ko wacece, idonta ta rintse da ya haska flash light ďin a fuskanta, hawayen da ya taru a idon ne ya silalo ta ido ďaya, tsayawa yayi yana kallon cute face ďinta , k'aramin lips ďinta idonshi ya sauk'a akai, yadda hawayen ya gangaro har kan cute lips ďin yabi da ido, ita dai tana tsaye ta kasa motsi, idon ma bata buďe shi ba dan bata san ma ko waye bane, tashi yayi daga kwancen da yake ya zauna har lokacin bai sake mata hannu ba, sai da ya zauna ya fara mamakin, ya akayi tazo gidannan, kuma mey ma ya kawota har ďakin nan, k'ara janyo hannunta yayi , a lokacin ta buďe idonta, wara idon tayi ganin wanda ke rik'e da hannunta a gabanta, ihu ta buďe baki zata kurma yayi maza ya toshe bakinta, ce mata yayi "shut up, and tell me y you are here" tare da fixgo ta ta k'arasa gabanshi, sai da yaga kyarman da jikinta keyi ya ragu sannan ya sake mata baki da hannu, mik'ewa yayi ya isa wani waje ya kunna wutan ďakin, gaba ďayanta ya duba tun daga kai har k'asa sannan ya koma ya zauna a kujerar da ya tashi, tambayanta ya sakeyi, "mey kike yi a ďakin nan har kika zo kina tab'a ni", kasa magana tayi dan gaba ďaya ta tsorata da ganinshi, tsawa ya daka mata "yace ba magana nake miki ba kinyi shiru kina kallo na, sai da ta tuna da sunan wacce ta aikotan sannan jiki a sanyaye tace mishi "Yaa mera ce tace in zo nan chamber in k'ira mata Massa, i didnt know inace kaine Massa, kuma ďakin ne da duhu shine nace bari in tashe shi, kayi hak'uri", gaba ďaya ta gama tsorata da ganinshi, juyawa tayi zata tafi yayi maza ypa fixgota, ce mata yayi "tab'a min fuskan kuma na meye", "innalillahi wa inna illaihi rajiun ta ambata a zuciyanta, ba ta faďa mishi tashin Massan zatayi bane kuma da duhu ita bata san ma fuska bane, cikin dakewa tace "ďakin ne da duhu, ban san fuskan ka bane" ta warce hannunta daga ruk'on da yayi mata tayi ta fita daga ďakin a guje, sunanta ya k'ira amma ko sauraronshi bata yi ba tayi tafiyarta, ranshi ne yayi mugun b'acin k'in amsawa da tayi, tashi yayi ya shiga toilet dake bedroom zaiyi wanka





Sai da ta iso k'ofar ďakin sannan ta tsaya ta daidaita numfashinta, ganin ta samu nutsuwa ya sata tura k'ofan ďakin a hankali, da sallama ta shiga ta zauna sannan tace "Yaa Mera , Massan baya nan" kamar kar ta faďa mata taga Abu sai kuma tace "amma naga Yaa Abu a ďakin yana bacci", jin ance Abutturab na ďakin yasa ta cewa "ohh shi yana gida, toh dama ai dan shi nake neman Massan, yau zasuyi wushe wushen ko?", ta tambayi Batuul, ďago kai Batuul tayi tana dubawa ko wani ake tambaya, da ta ga babu kowa a ďakin sai ita ya tabbatar mata da ita Yaa Mera ke magana, " No, ni ban sani ba fa Yaa, bansan mey zasuyi yau ba, sai dai in Farida ta shigo mu tambayeta" inji Batuul, Yaa Mera ce ta sake cewa "ai tunda ma yana gidan bari in k'irashi yazo in ganshi muyi magana dashi", mamakin matar takeyi kamar ba sarauniya ba, babu ruwanta, ita ko bayi ma bata ajiyewa kusa da ita gata da fara'a, ga kyau, kammansu ďaya da Ammah, Abutturab ďinma dasu yayi kama, hasken sune kawai bai ďauko ba sai yayi duhun Abui, su Farida da Sadiq ne sukayi kama da Abui amma suka ďauko hasken Ammah, tana zaune tana ta zancen zuci Farida ta shigo da plate ďin kisre da miyar kuka da yaji kaji, gefen Batuul taje ta zauna ta cewa Yaa Mera "Yaa sun iya kisren sosai, kamar fa da engine sukeyi , ya burgeni yadda sukeyi shiyasa ma na ďebo kaďan, Batuul ci kiji", Yaa Mera ce tace "shiyasa mamanku tace sai anan za ayi, yanxu ma daga nan za a kwasa akai gidansu matar Abun", ido Farida ta wara tace "Yaa drums dayawa fa akayi, kuma duka za a kai musu, wannan matar ta Yaa Abu suna yi bada wasa ba", dariya ta bawa Yaa Mera tace mata "al'adanmu kenan Farida, haka mukeyi in zamu aurar da yara", cewa Farida tayi "lallai, su suka sani", taci gaba da cin abincinta, lura tayi da Batuul bata ci tace "meye kika sani gaba, kici mana", harara Batuul tabita dashi tayi magana a hankali yadda Yaa Mera baza taji ba "ce miki nayi inajin yunwa, ki gama mu tafi ni", Yaa Mera ce ta ďagi taga Batuul ďin bata cin kisren, ce mata tayi "Batuul bitti, beri bei" (Batuul y'ata, kici abinci), a hankali ta amsa da "toh", sannan ma matso tasa hannu a cikin plate ďin





Yana fitowa daga toilet ďin bayan yayi wanka da alwalar la'asar, wayanshi ya ďaga ya k'ira Massa, yana ďagawa yace mishi " Kana inane", Massa ne ya amsa da "muna tare dasu Imran a Protea, ya kan naka, yayi sauk'i", ce mishi yayi "Yeah sosai, ina jiranka kazo ka ďaukeni", sannan ya katse k'iran, kaya ya saka cikin sabbin kayanshi da suke gidan da ya ďinka na biki, bayan ya gama ne yayi sallah la'asar, yana idarwa wayarshi tayi k'ara, ďauka yayi yasa a kunne, "salamu alaikum, Yaa Mera nda dubdo", ehh ina gida, toh bari in sauk'o sannan ya katse wayan", sosai yayi kyau da kaftan ďin da ya saka, ya ďaura hula akanshi sannan ya fita, side ďin Yaa Mera yayi, da shiga ya samu waje ya zauna ya sake gaisheta, Farida ma gaisheshi tayi , bayan ya amsa ne Yaa Mera ta dubeshi tace "yau ne wushe wushen naku ko", kai ya gyaďa tare da amsa mata da "ehh", ce mishi tayi "wane time za ayi?", "k'arfe bakwai ne zuwa sha ďaya", "toh yanxu kace musu su shiryata k'arfe biyar, anan za ayi mata kéla tul kamin ku wuce wajen wushe wushen, zamu tura musu mota, daga nan zamu kaita wajen, har kaya zamu bata ta saka, mun gama magana da mamanka", cewa yayi "okay Yaa, In sha Allah zan faďa mata, sai ta faďa a gidan nasu" , sallama yayi da ita ya mik'e kenan zai yi hanyan waje yaga an buďe wani k'ofa, k'ofan yabi da kallo, Batuul ce ta fito daga ciki hannunta rik'e da hand napkin tana gogewa, ta cire

1 Comments On BATUUL
avatar
hafsat-9-3

12 months ago

Reply

Nice book

Please Login or Register in order to submit comment