Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sake tambayanta "For God's sake tell me where your house is" cikin kakkausar murya yayi mata maganan, take jikin ya fara b'ari hawayen dake mak'ale ya k'arasa gangarowa, shiru tayi ta kasa ce mishi komai, magana ya sake yi " Are you this dumb naji Sadiq na cewa kina da ilimi", tsaki ya sake ja yace mata "okay tell me right now cuz you have wasted my time alot", ce mishi tayi "Nifa ban gane hanyan nan da ka bi ba, ba ta hanyan nan muke bi ba mu in zamu....., bai bari ta karasa magana da ta keyi ba yace mata "GET OUT" da k'arfi, kai ta d'ago ta kalleshi dan ta k'ara tabbatarwa da gaske yake, ce mata ya sake yi "I SAID GET OUT", kasa yin komai tayi a lokacin saida ya mik'a hannunshi ya bud'e mata k'ofan sannan ya k'ara ce mata "OUT" ko ledan da Ammah ta bata bata tsaya dauka ba ta bud'e motan ta fita, tana fita ya fizgi motan kaman wanda zai tashi sama




A wajen Batuul ta tsaya ba tare da tasan abun yi ba, ga tsoro da ya cika ta, tsoro ma takeji tayi motsi dan gani take wani abun zai kama ta, kuka ta saka a hankali tana k'iran Baba, wayanta ta ciro ko xata ga mis cal din Ahmad amma taga bbu, takaici yasa ta ki kiransa kuma mayar da wayar cikin jaka, tsugunawa tayi a wajen ta kifa kanta a cinya ta ci gaba da kuka dan ita bata ma san inane nan ya kawota ba, gashi anguwan babu commercial vehicles bare tace zata hau d'aya ya kaita gida, shirun da anguwan yayi ne yasa ta d'ago kanta ta sake dubawa ko zata samu mafita, da taga babu yadda zatayi ne ta yanke shawaran kawai ta tashi tayi ta tafiya ko zata samu yadda zatayi,




Tunda ya bar wajen hankalinshi yake kanta, tuk'i yake cike da damuwa, "yama za ayi mutum yace baisan hanyan gidansu ba idan ba rainin wayo ba"? Tambayar da ya yiwa kanshi kenan tare da jan tsaki, Tunawa da yayi da fuskanta da yadda hawayen ke gangarowa daga idonta ne yasashi saurin taka brake da k'arfi, mutane ne ke ta yi mishi horn amma bai kulasu ba, parkin gefen titi yyi, lkci daya yace "ta ci sa'ar nasan darajar human" wayanshi ya d'auko ya lalubo number Farida ya k'ira, tana d'auka yace "ke inane anguwansu k'awarki", ce mishi tayi "lah Yaa Abu har yanxu baku k'arasaba" a tsawace yace "Tell me what i asked you and dont question me" ce mishi tayi "Lagos street ne behind Leventis, Yaa Abu wani abune ya faru" bai jira ta k'ara magana ba ya katse wayan, yana ajiye wayan ya juya motan hanyan da ya bar Batuul a wajen, yana isa inda ya bar ta ya duba yaga bata nan sai d'an kwalinta da bata san ya fad'i ba a kasa gun, fitowa yyi ya dauka ya jefa bayan motanshi, a hankali ya dinga bin hanyan, daga can ya hango ta tana tafiya tana share hawayen dake zubowa a idonta, karasawa yayi inda take yayi mata horn, bata juyo ba sai ci gaba da tayi da tafiya da sauri, wani horn din ya sake mata amma bata juyo ba sai ma sauri da ta k'ara sabida tsoro, gabanta yaje ya tsaya da motan, bude mata k'ofa yayi yace mata "GET IN," ko kallonshi bata yi ba taci gaba da tafiya, fitowa shima yayi daga motan yabi bayanta dan ranshi ya soma b'aci, yana isa wajenta ya kama hannunta ya jawota har wajen da yake, fixge hannunta tayi da karfi tace "dole ne sae na shiga motar ka malam" bata ankara ba sae ji tayi sa ka ta cikin motar, yyi banging kofar snn ya zaga ya shiga ya tada motan ya bar wajen, kuka ta dinga yi a motar uwa wata karamar yarinya, kara gudunsa yyi had'e da dukan steering wheel din motan yace "Damn it" sae kace warce ya sato, a ranshi fadi yake "Duk su Ammah ne suka jawo masa yana xaman xaman sa" gnin har lkcn bata fasa kukan da take ba yasa ya bude pidgin din motar ya dauko handkerchief ya miko mata, kin karb'a tayi, wani haushi ya kuma kama sa ya mayar da handki din, wani gida suka kusa wucewa tayi sauri tace mishi ga gidanmu nan, brake ya taka yayi horn a gate din yana jira a bud'e, bata jira an bud'e ba ta fita da sauri ta shige gidansu, bin ta da kallo yyi cike da bacin rae, yafi minti goma a k'ofar gidan ba tare da ya tafi ba, idonshi ya fad'a kan ledan dake ajiye, d'auka yayi ya fito yayi sallama da mai gadin ya mik'a mishi yace mishi na Batuul ne, k'iran sunanta da yayi ne ya sashi jin wani iri ya juya ya koma mota ya tada ya tafi.
💖💝BATUUL💖💝






8





By phartiemarhk





Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*





Tana shiga gida hanyan garden tayi ta wanke fuskanta da kyau dan kar a ce tayi kuka, da sallama ta shigo palon, ba kowa sai Aunty da Aabid a hannunta tana bashi madara, karasawa tayi cikin palon zata hau bene bayan ta cewa Aunty ta dawo taji Aunty tace "Batuul zo nan, mey ya sami idonki ya canja kala, kuka kikayi" da sauri ta ce " a ah Aunty kaina ne yake ciwo tun da naje, nace zan dawo ma Ammah tace in bari sai da yamma a dawo dani, tana gama maganan ta hau stairs da gudu, da ido Aunty ta bita ba wai dan ta yadda da abunda ta fada din ba, tana kaiwa last stair case din taji sallaman mai gadinsu ya shigo da leda wai a bawa Batuul inji mutumin da ya kawota, Aunty ce tace ya ajiye, yana ajiyewa ya tafi abunshi, Batuul kam tsayawa tayi tana kallonshi har saida ya ajiye ya fita tukunna ta tab'e bakinta ta tafi , dan ita ta ma manta gaba daya da batun abunda Ammah ta bata, dakin k'annenta ta bud'e ta lek'a dan a cike take da Ahmad da yaqi picking call dinta kuma bai k'irata ba bare yazo d'aukanta , tana budewa taga dak'in ba kowa, an tattarashi tsaf sai k'anshi da sanyi yake yi kamar ba shine a hargitse ba d'azu, rufewa tayi ranta a b'ace dan taso ta sameshi ya fad'a mata dalilinshi na qin d'aukan wayan, ďakinta ta k'arasa ta bude, tana shiga ta tarar dashi kamar yadda ta fita ta bari sai d'an gyara da aka sakeyi, kayan jikinta ta cire ta shiga toilet, bath tub ta shiga ta cika shi da ruwan dumi, tana shiga ta dinga kukan da bata san dalilin yinshi ba, sai da tayi mai isanta sannan ta fito daga daga cikin bath tub din ta nufi sink tayi alwala,fitowa tayi daga toilet din, gaban mirror taje ta shafa mai, ta fesa turare masu sanyin k'anshi, da ta gama ta k'arasa gaban closet dinta ta bud'e ta dauko kayan bacci, gown ne na sponge bob iya gwiwa ta saka, ta saka hula blue sannan ta shimfid'a sallaya ta hau ta tada Sallah Isha, tana idarwa ta hau makeken gadonta ta kwanta, remote din AC ta d'auka ta k'ure to the highest volume, duvet dinta ta janyo ta rufe duka jikinta dashi, wayanta taji yana ringing, kamar baza ta d'auka ba ta janyo shi da k'afa ta k'ara a kunnenta , a hankali ta amsa da "Hello" daga d'aya bangaren aka amsa da "sweetheart i was worried about you, inata trying number ki it wasnt going,kun isa gida lafiya", a hankali Batuul tace Farida ina gida, jin muryan Batuul yayi k'asa ya sata tambayanta "Batuul are you okay", a hankali Batuul ta ce " yeah am okay" Ya Ammah, kice mata na gode....", katseta Farida tayi ta ce mata "Yaa Abu ya k'irani wai in fada mishi inda gidanku yake , Baatul tace mata " eh ina ta yi mishi describing ne bai gane ba shine nace ya k'iraki ya tambayeki amma ai tun dazu mukaxo, har ma na kwanta, ce mata ta sakeyi "bari in barki sai da safe tunda har kin kwanta" jikin ta sanyaye ta ajiye wayan dan tasan ba lafiya bestyn ta take ba saboda ko zatayiwa ko shiru bata yiwa Farida, tasan mayb wani abun ya haďa ta da Yaa Abu





Tuki yake yana tsaki kwata kwata fitar da yayi niyyan ma fasa ta yayi, wayanshi ne yayi ringing, duba mai kiran yayi sannan ya jona wayan da speaker motan kamin ya d'auka, yana ďauka yace " said yanxu kika ga daman k'irana kenan" , daga daya bangaren cewa akayi cikin siririyar murya da kanaji kasan an lank'washeta " Bae kaima kasan ba da gangan naqi kiranka ba, kasan muna ta ibada ne kuma muna tare da family so...." bai bari ta k'arashe maganan ba ya katseta da cewa " Yasu Mummy, yaushe ne dawowanku" , "su Mum na lafiya, next week zamudawo ai zakazo d'aukanmu ko, i even have something for you, ďazu mun fita dasu Mum munje bin Dawood naga wani turare ance shi ne latest of d month,na siyamaka dan har su prince Hamdan ma shi ne nasu for this month, bai bari ta karasa maganan ba ya ce mata " okay yanxu ina driving ne , i will get back to you when i reach home", a sanyaye tace "Aii bae take care" ta katse wayan, kullum sukayi waya sai yayi mata hali, amma babu komai ai Mum dinta tace mata indai ta aureshi komai zaiyi normal, said yadda tayi dashi, shima har yazo ya fita sonshi,ayyanawa tayi a ranta ai tunda tana da kyauzatayi anything possible ya sota fiye da komai, tunanin hakan ne ya sata wani daria mai sauti , y'an dakin hotel din ne suka juyo suna tambayanta mey take yiwa wannan dariyan, murmushi ta sakeyi ta ce musu "Tunanin yadda zanyi da Abutturab nakeyi da yadda zai so ni in munyi aure" ta tab'a matar dake gefenta tace "Yaa zee wlhy ina sonshi, baza ki gane bane, wacce aka k'ira da Yaa zee dince ta ture mata hannu daga jikinta tace "rabu dani dallah, anyi anyi ki rabu da yaron nan kink'i, ni banga ma wani abu da yake dashi ba in banda tsawo da ya ďebo kamar isha da girman kai kaman wani basarake, ga manyan mutane nan na sonki amma kin nacewa k'aramin yaro da ya baki y'an shekaru, in banda wulak'antaki babu abinda yakeyi, dubi fa ko yanxu da kika k'irashi ce miki yayi sai yanxu kika ga daman k'iranshi, shi mesa bazai kirakin ba ďan rainin wayo kawai" taja tsaki ta ci gaba da danna wayarta, yarinyar ta sake cewa "Yaa Zee baza ki gane bane, da kinsan wahalan da nasha kamin ya fara kulani ,ke da kanki zakice inci gaba da hak'uri saboda in inyi fulfilling dream dina in aureshi , kuma ai ina sonshi, tun first day dina a school nake bin shi yana shuning dina har na samu yana kulani yanxu ai bazanyi missing wannan opportunity ba, yanxu kawai jira nake muyi aure komai zaiyi daidai yadda muke so , Yaa Zee tace mata" ke kika sani, Ni ki rabani da labarin wannan sarkin tsawon naki," taci gaba da abinda take, tashi yarinyar tayi ta fita daga ďakin tana dariya





Aunty ce ta tura Fa'iza ta duba mata ko Batuul idonta biyu, da taje sai da ta lek'a ,hasken da ta ganine ya sata shiga , a hankali tace mata, "Yaa Batuul Aunty tana qiranki, bata tashi ba tacewa Fa'iza "gani nan zuwa" Fa'iza na fita ta tashi tabi bayanta after ta duba fuskanta a mirror taga ya ďan zama normal , tana sauk'a k'asa taga duka yan gidan a palo kowa ya baje ledoji a gabanshi sai hira sukeyi suna dariya, Baba ne ya fara hangota yayi mata alama da tazo wajenshi, kusa dashi taje ta zauna , Ahmad ne ya kalleta ta doka mata harara, dariya yayi ya ďauke kanshi yaci gaba da abinda yakeyi, Baba ne yace mata "Da zamuje mu ďaukeki da muka fita dan Ahmad ya ce min ya bar wayanshi a gida, sai da mukayi waya da Aunty ta ce mana kun dawo , a hankali tace mishi "Ehh Baa, inata kiran shi baya picking shine kawai Ammah tace a dawo dani, tun dazu ma na dawo", tashi tayi ta koma wajen Aunty tace mata "Aunty gani", "kinci abinci ne da kika shiga kika kwanta, kuma da kikace kanki na ciwo wane maganin kikasha", kamar zatayi kuka tacewa Aunty "Naci abinci har na sha panadol, bacci nakeson yi yanxu", da ta tashi tafiya ne Aunty ta nuna mata ledan da mai gadi ya shigo dashi yace nata ne, Faiza tacewa ta hawo mata dashi ta k'arasa sama ta
kwanta, binta kawai Aunty tayi da kallo dan ta san duk bacin ranta baya nunawa amma yau wani abun ya sameta,






Yana xuwa gida, ta back door ya shiga dan baya son had'uwa da kowa saboda ranshi ya gama b'aci, ďakinshi ya nufa ya buďe ya shige, toilet ya shiga ya watsa ruwa yayi alwala ya fito, pjs dinsa ya saka sannan ya shimfiďa abun sallah ya hau ,dan yaso yayi a shehuri idan yaje amma saboda yarinyar nan bai samu yayi ba sai yanxu wajen after 9, tada sallahn yayi , bayan ya idar ya gama azkar ďinshi ya hau gadonshi tare da janyo Mac book dinshi yana duba aikin da zaiyi nan da kwana huďu, yana gamawa ya kashe wutan ďakin ya kwanta
💖💝BATUUL💖💝






9





By phartiemarhk





Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*





K'arfe biyar 5:00 daidai adhan din sallah Asuba ya fara dai dai lokacin Abutturab ya farka daga bacci, addu'ar tashi daga bacci yayi, k'afafuwanshi ya sauk'ar daga kan gadon a hankali, tashi yayi ya isa inda comfy fararen towels dinsa ke rataye yayi, guda ďaya ya janyo, kayan baccin dake jikinshi ya cire sannan ya ďaura towel din ya shiga toilet, brush yayi ya watsa ruwa sannnan ya haďa da alwala ya fito, closet ďinshi ya buďe ya ciro farar jallabiya ya saka bayan ya goge ruwan jikinshi da towel, gaban mirror ya koma ya fesa turaren jéan pául Gaultiér ya k'ara da Hugo sai Arabian oud ya shafa, abin sallah ya shimfiďa yayi nafilfili, bayan ya idar ya karanta suratul Mu'minun cikin murya mai daďi, tashi yayi ya fita masallacin dake manne a jikin gidan daga waje, yana k'arasa yayi raka'atul fajr sannan ya zauna jiran Ladan ya tada sallah su fara, k'arfe 5:40 ladan ya tayar suka fara sallah, suna idar da sallah bayan y'an azkar suka fito daga masallacin, Abui da Sadiq ya hango ya k'arasa inda suke, "Nda wattu" yacewa Abui tare da mik'a mishi hannu, Abui ne ya amsa mishi da kélewa sélai, Sadiq ne shima ya mik'o wa Abutturab hannu suka gaisa, suna tafiya Abui ya k'ira sunan Abutturab, "yaushe ne tafiyanka" Abutturab ya amsa da "Na so in tafi on monday but naga i have things to cover before meeting dina da minister on tuesday, so i have decided to leave tomorrow monday", Abui yace "okay sai kayi rescheduling flight dinka to gobe, kuma ka fad'awa Ammah dan bata sani ba, mu sai next week dawwanmu inaga" yace "okay Abui" sannan suka k'arasa cikin gida kowa yayi ďakinshi





Hasken ranar da ya hudo window ďakinta ne ya sata buďe idonta a hankali, ranan da ta gani ne ya sa ta wara y'an madaidaitan idonta ta dubi agogon dake kan bed side drawer taga 6:30, da tsalle ta tashi daga kan gadon, gashinta mai tsayi da shek'i da ya baje tana bacci ta kama ta haďe su in a messy bun, toilet ta shiga ta kuskure bakinta da Listerine mouth wash tayi maza tayi alwala ta fito, sallah ta tada , bayan ta idar tayi azkar ta fito daga d'akinta ta bud'e ďakinsu Ahmad, fridge din ďakinsu ta buďe ta ďauko ruwan sanyi ta shiga kwara musu, a firgice kowannensu ya tashi suna mitsitsika ido, Sa'eed ne yace mata "haba Yaa Batuul yanxu kuma mey mukayi kika tashemu da ruwan sanyi", dukkansu ransu a b'ace suna kallonta suna jiran suji mey sukayi da ta katse musu bacci, "Y'an rainin wayo kunga ban fito sallah ba shine babu wanda yayi knocking min k'ofa, ai tunda baku ganni nazo gaida Baa ba sai kuzo ku dubani, amma kowanne da yaje masallaci dawowa yayi yaci gaba da baccinshi, sai yanxu nayi sallah asuba, yan rainin wayo kawai, Khalil ne yace " toh mu mun san baki tashi bane, kuma ai Aunty ma munsan zata tasheki" Harara ta watsa mishi, Ahmad kam ko uffan baice ba dan ya san harda haushin jiya yasa ta zuwa da watsa musu ruwan sanyi suna bacci, Mus'ab ma baice komai ba, tana faďan dalilinta na watsa musu ruwa yaja bargonshi ya kwanta dan inda sabo sun saba da masifanta, saida ta gama faďanta sannan ta juya tare da banko musu k'ofa ta fita, k'asa ta sauko taga babu kowa ta koma d'akinta





11:00 ta sauko cikin abayar Al layl tayi kyau sosai, fuskanta ba komai sai kwalli da ta saka, duk y'an gidan na parlour, Su Ahmad ne suka bita da kallo ransu a b'acen abinda tayi musu ďazu,itama palon taje bayan ta gaida Baba da Aunty ta sami waje ta zauna, Baba ne yace mata "Batuul tafiyanmu gobe ne dan haka yau zakuje ku gaida su Yayya da kowa da kowa, meeting dina tuesday so dole mu tafi gobe, kuma kinga graduation ďinki saura two weeks, sai ki fara shirye shirye ko" tace "yo Baa", Aunty ce tace mata "kan naki ya dena ciwon", ita ta manta ma gaba ďaya da tayi ciwon kan k'arya, tunowa tayi da abinda ya sata yin k'arya, ďan k'aramin tsaki tayi daga ciki, a ranta tace wannan mugu ne dagaske shiyasa Farida bata sonshi tafi son Sadiq, da sauri tacewa Aunty, " eh da nayi bacci na tashi ya dena", "sai kije kici abinci ki fito mu tafi dan muna da wajen zuwa dayawa a yau" toh tace sannan ta nufi dinning ta bubbuďe food flaskses da kwanunkan dake kan dinning ďin, plate ta ďauka ta saka pancake guda da ďaya da strawberry syrup sannan ta ďauki Fanta ta zauna ta ci a hankali har ta gama ta dawo palon tace ta gama, Aunty ce tacewa yaran toh ku tashi mu tafi Baa Liman na jiranmu shi zai kaimu, dukkansu sukayiwa Baba sallama suka fita, wata range rover 2011 suka dosa dukkansu, Baa Liman ne ya buďe kofan driver ya shiga, motan duk ya hargitse da surutu kowa yana faďin ga wak'an da yakeso a sa, daga k'arshe ne Batuul tace a saka musu wak'okin Wael Jassar, ana sawa duk suka fara bin wak'okin shi na farko a album din 7aareg damohom, motar cike da hayaniya ba a jin abinda wani ke faďi har suka isa gaban wani gate sukayi horn, mai gadi ne ya buďe musu su ka shiga, basu bari an gama parking ba suka buďe k'ofofin motar suka fito, da gudu suka shiga gidan suna faďin *yayya ishena*, *yayya ishena* Yayya munzo, Yayya munzo)da kanuri, wani ďaki suka buďe suka shiga, ďan madaidacin parlour ne mai kyau sai k'anshi turaren wuta yake da sanyi, suna shiga suka nufi wajen wata tsohuwa fara sol, dukda ta tsufa amma kyanta na nan, anyi mata kitson gaba da ya zubo daga gefe, na bayan kuma ta tufke shi, murmushi tsohuwar tayi ta rungeme yaran, Batuul na shigowa taje wajenta ta ture yaran daga jikin tsohuwar tare da cewa "Ku ďaga min takwara kar ku ballamin ita, tunda kuma bana yiwa takwarorinku haka, rungume tsohuwar tayi sannan tace mata Yayya *tussuna nya rukéi*, (na daďe ban ganki ba, nayi missing ďinki), Yayya tace mata " *nda rui sha, jirem géi*(dubeta kamar dagaske ban yadda ba), Aunty ce ta k'araso ďakin ta zauna sannan suka gaisa da Yayya, cikin girmamawa suka gaisa sannan yayya ta k'ira daya daga cikin masu aikinta, "ki kawo musu abinci da kayan sha ki jera a kan dinning,cikin kanuri ta faďi maganan don bata jin Hausa, sunajin abinda yayya ta faďa kowa ya fara faďan choice dinshi na abinda zaici, duk saida aka kawo musu abinda sukace sunaso aka jera musu, a gidan suka wuni har dare





k'arfe goman dare Baba ya iso gidan yayya shima, bayan sun gaisa da yayya sun ďan tab'a hira yace su tashi su tafi dan gobe flight dinsu eleven ne,tsaraba dayawa yayya ta haďa musu ta saka masu aikinta su kai musu mota, bayan kowa ya gama shirinshi zasu fita daga ďakin yayya ta k'ira Baba ckin ďakinta, zama tayi a kan gado shi kuma ya zauna a k'asa kanshi a duke, magana ta fara kamar haka "Batuul tace min ta gama sashen karatun nan nata amma zataci gaba, kuma har waje naji tana cewa zata, toh ni bance kar taci gaba ba amma ban yadda har waje ba, in kuma har wajen zaka fita da ita toh lallai saida mijinta , haba wane karatu ne haka da tunda aka haifi mutum yakeyinshi bai k'are ba, yarinya shekara sha shida zata shiga na bakwai amma babu abinda takeyi sai boko, toh inma uwarta ke zugaku da kai da Batuul ďin ni bazan ďauka ba, bazan yadda yarinya tayi ta girma babu aure ba, ai uwartata ma abinda ya sa na k'i ta kenan lokacin aurenku wai tana boko, toh mutane da dama ma ai sunyi bokon a gidan mazajensu, dan haka Batuul baza ta ci gaba ba sai tayi aure", duk maganan nan da tayi cikin kanuri tayishi, tunda ta fara magana Baba bai ďago ba sai da ta gama, a sanyaye ya ďago kanshi yace mata "In sha Allah yadda kikeso za ayi Yayya, nima ďin bana son fitanta waje karatu babu muharrami, dan haka zan duba yadda za ayi", Yayya tace "yawwa gara a duba , Allah yayi muku albarka, toh yaushe ne tafiyan naku gobe" yace "11" tace Allah ya kaimu ya kiyaye hanya sannan ta fito yana biye da ita a baya har suka k'araso parking lot, yaran nata tsokananta har Babansu ya tayar da motan tana ďaga musu hannu har suka fita daga gate ďin
💖💝BATUUL💖💝






10





By phartiemarhk





Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*





Sweat pant blue ke Jikinshi da riga bak'a yana dadanna Macbook dinshi, tea ne a flask daga gefenshi idan yayi aikin sai ya ďan sha kaďan, wayanshi ne yayi k'ara ya ďauka yaga Amma keh k'iranshi, rusuna yayi yace "Hello Ammah", daga ďaya bangaren Ammah ce ta amsa da " ina falon sama, kazo maza ina jiranka", tunani ya fara yi akan dalilin wannan k'ira da take mishi dan tun daga muryanta ya san ba lafiya ba, maganan Ammah ya sakeji tana cewa "banji ka amsa ba", da sauri yace "Ammah ina zuwa" ya katse wayar, matsar da Macbook ďin yayi gefe ya tashi ya fita daga ďakin, hanyar falon sama yabi har ya isa, yana zuwa yaga Abui da Ammah a zaune tare a kujera ďaya, k'arasawa yayi ya nemi waje ya zauna akan tattausan rug ďin dake shimfiďe , a kusa da Abui dab ya zauna daga k'asa, kanshi dake duk'e ya ďago ya gaida su a tare, Abui ne ya fara amsa mishi sannan Ammah, bayan y'an seconds Abui yayi gyaran murya tare da k'iran sunan shi, "Abutturab magana zamuyi dakai kamar kullum akan dai maganan kayi aure ne, mun gaji da zaman ka haka", Ammah ce tayi sauri ta karashe maganan da cewa "bazan yadda da tafiyanka waje babu mata ba, wane aiki ne zakaje ka k'ara banda wanda kayi musu ba, yanxu Abui

1 Comments On BATUUL
avatar
hafsat-9-3

12 months ago

Reply

Nice book

Please Login or Register in order to submit comment