Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tace "Kai ka tabbata, Hajiyar gidannan fa nake nufi", ta nuna mishi gidansu Ajiddeh, juyawa yayi ya dubi gidan sannan ya juyo yana kallonta yace "Ye shine gidanmu din ai, gida na Alhaji namu, sunanshi ya fada a TV munji ma lokacin Abba Ahmad Jidda", kallon juna Aunty Amna da Ammah sukayi jin bayanin mai gadin, Ammah ce tayi magana wannan karon tace "Hajiyar gidan ba rashin lafiya tayi aka kaita asibiti ba?", kai ya shiga girgizawa kamar zai yadda k'asa . "Hajiya baije asibiti ba, yapot ne Abor ya kaishi ya tafi gari nasu can", da mamaki Ammah take dubanshi tace "Toh Hauwa kuma fa, ta dawo itama ko tare sukayi tafiyan", kai ya d'aga alamar yana tunani sannan ya kallesu yace "Hauwa din ni ban sanshi ba, ba a gidan nan yake ba", dariya Aunty Amnah tayi tace "Toh mangal ai Hauwan macece ba namiji ba, Ajiddeh fa muke nufi, wacce tayi aure", yace "Owo, ai baka fadamin Aunty ne kana nema ba, ai shi din yayi auren tun ya dade, so daya ne naga ya dawo gida tun lokacin da yayi aurenshi ya tafi da miji mai kyau wannan, yana bamu kudi in yazo kullum, Kai wannan mutum da Aljanna ne nace", Kai Aunty Amna ta gyad'a tace mishi "Toh Mangal mun gode, in sun dawo zamu dawo muma", ta ciro kud'i daga jakarta ta mik'a mishi, godiya ya dingayi musu yana washe baki, suna barin k'ofar gidan Aunty Amnah ta dubi Ammah dake tunani tace "Ammah kinji wai basa nan, kuma Ajiddeh ma batazo ba, can kuma su Abu sunce miki ta dawowa mamarta ba lafiya, anya wannan abin da akwai kanshin gaskiya kuwa?", Ajiyar Zuciya Ammah ta sauk'e tace "Amina koni abinda na kasa fahimta kenan, kuma kinji fa wai ita Ajiddeh ma bata nan, toh Allah dai ya tsare", baki Aunty Amna ta tab'e tace "dama can ni Ammah hankalina bai kwanta ba, Allah dai ya rufa asiri", "Amin",basu sake yin maganan ba har suka isa gida, sai da ta sauk'e Ammah sannan tayi mata sallama ta wuce nata gidan, Ammah na isa gida ta buga waya Maiduguri, nan take ta bada order akan ayi addu'a da sauk'an Qur'ani ta tura musu kud'in sadaka, don ga dukkan alama ba abun kirki ya dawo da Ajiddeh gida ba.

Batuul ta kusa minti sha biyar xaune kan gadon bayan fitarsa ga yunwa da taji ta fara ji, mikewa tayi daga karshe tana share hawayen fuskarta ta nufi closet dinta, shiryawa tayi cikin y'ar gown mara hannu purple mai kyau, tana kkrin fiddo hijab da xata daura kan kayan ya shigo dakin, still tayi gabanta na faduwa, dad'da'dan kamshin turarensa ya cika dakin, a hankali ta juya tana kallonsa ta ga tsayawa yayi bakin kofar dakin yayi folding din hannunsa yana kallonta, maxa tayi ta dauke kai ta ciro hijab dinta xata sa yace " Drop that!" zumb'uro baki tayi tace "Ni sanyi nake ji" murmushi yayi yace "Did you just pout?", maza tayi ta maida bakin da ta zumb'uro ta girgiza Kai, karasawa yayi ya fizgo hannunta ta kusa fad'awa kanshi, bata ankara ba sae ji tayi ya hade bakinsu, sai da yayi kissing d'inta son ranshi sannan ya saketa, yana kallon idonta dake xub da hawaye yace "if you pout again, I will do more than this", hannunta ya kama tana hawaye suka fita daga dakin suka sauka downstairs, makullin motarsa ya dauka a palon sannan suka fita, shi ya bud'e mata motar ta shiga sannan ya zaga nashi side d'in, sai da ya tada sannan ya rik'o hannunta ya fara driving, a hankali yace "kin ma ci abinci yau kuwa?" Kin cewa komae tayi, yayi murmushi yana driving dinsa, har suka isa babu wanda yace komai sai murza hannayenta da yake cikin nashi, ganin gaban gidan da yayi parking yasata yin murmushi don haka kawae take son gidan ita dae, juyowa yayi ya dubeta ganin yadda fuskanta yayi lighting da murmurshi, hannu yasa ya juyo fuskanta tana kallonshi, a hankali ta sauk'e idonta kasa, giranshi ya d'aga yace "My wife's house, don't be over joyed being here uhh?", baki ta tab'e ta had'a rai ta janye fuskanta tareda bud'e motan ta fita, shima d'in murmushi yayi ya bud'e ya fita.


πŸ’–πŸ’BATUULπŸ’–πŸ’

63

By phartiemarhk

Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*

Had'e rai tayi tareda zumb'uro d'an bakinta ta tsuke shi tayi gaba ta bar sa nan tsaye, sai da taje bakin k'ofa ganin k'ofar glass d'in rufe yasa ta tsayawa, rau rau tayi da ido ta juyo xata kallesa suka kusa cin karo, sadda kanta tayi k'asa zata juya ya saka hannunshi waist d'inta ya juyo da ita, fuskanshi dab da nata har tana jin numfashin sa na brushing jikinta da kamshin turarenshi mai dad'i, ya dan wara mata ido yace mata, "mey ya hanaki shiga, ai na fad'a miki its my wife's house, ni kad'ai keda access to it, da kinace zaki iya bud'eshi ne", bakinta ta zumb'uro mishi ta d'auke kai zata juya, hannu yasa ya juyo da kanta yana kallon fuskanta yace "Did you just pout again", kai ta shiga girgizawa da sauri dan ita bata ma san tana yi ba cikin murya kamar zatayi kuka tace "Yaa Abu banyi ba, kayi hakuri", murmushi yayi ya d'auke idonshi daga kanta sannan ya jawo hannunta sukayi k'ofar gidan, hannunta ya d'aura kan security lock d'in dake mannne jikin bangon, k'ofan ne ya bud'e da kanshi, da mamaki ta kalleshi, smirking yayi tareda d'age mata girarshi d'aya, kauda kanta tayi kamar bataga abinda yayi d"in ba, hannunta ya kamo cikin nashi su shiga, tur jewa tayi nan gun taqi motsi, da mamaki ya juyo don ganin mey ke damunta, dawowa yayi gabanta yana kallon fuskanta yace "Are you okay", tsuke bakinta tayi ta juyar da kanta, hannunshi yasa ya juyo da fuskan nata tana fuskantar shi yace "Hey!, talk to me, what's wrong with you", raurau tayi da idonta taqi ce mishi komai, sassauta muryanshi yayi yace "mey ke damunki wai", baki ta sunkuyar da kanta cikin sanyi tace "you just said I shouldn't be overjoyed being here, its your wife's house, so why asking me wats wrong?", abinda ta fad'a da yadda tayi maganan ne ya bashi dariya amma ya dake, had'e rai yayi yace "and what does that have to do with entering in, in zaki shigo ki shiga, you are wasting my time", hawaye ne ya shiga taruwa idonta, juyawa tayi zata bar wajen, yasa hannu ya fixgota, cak ya d'agata ya rungumota, ko'k'arin sauk'a ta shiga yi daga jikinshi tana wuntsila k'afafu, matsetata yayi k'irjinshi sannan ya sunkuyo daidai kunnenta yace "if I should slap you right away, ina miki wasa ne", lamo tayi jikinshi ta rintse ido tana shak'ar k'anshin turarenshi mai dad'i, bata bud'e ido ba sai da taji ya direta kan lallausan gado, a hankali ta bud'e lumsassun idanuwanta ta sauk'e kansa, ya kwanta gefenta ya lumshe ido, kyakkyawan fuskanshi ta tsurawa ido, lumsassun hazel like idanunshi da lashes yabi ya kwanta, sai chiseled nose d'inshi, da d'an k'aramin plumpy pinks lips d'inshi, tab'e baki tayi ta d'auke Kai a ranta kuwa haushin kanta taji na kallonshi da ta tsaya yi bayan bama wani kyau bane dashi, a hankali ta sake juyowa bayan kamar 3mins, har lokacin yana kwance kuma bai bud'e ido ba, Idonta ne ya fad'a kan broad k'irjinshi da buttons d'inshi na sama guda biyu da suka bud'e, gabanta ya fadi ba kadan ba, a hankali ta dinga jin abu na yawo spines d'inta, rintse ido tayi dan batason cigaba da jin abinda take jin, samun kanta tayi da son jinta kwance jikinshi, ita kanta ta rasa gane dalilin hakan, ta kuma runtse ido xuciyarta na double flipping, dai dai lkcn da ya bude nasa ya juya yana kallonta, a hankali ya mirgina kusa da ita ya dagota ya mai da ita kan faffad'an k'irjinshi, kamar wacce akayi electrocuting a firgice ta bude ido ta yunk'ura xata sauka daga jikinsa, kamin ta sauka taji ya sako hannayenshi a waist d'inta ya dad'a rungumota jikinshi, ajiyar zuciya ta sauk'e tareda yin lamo tana jin yadda heartbeat d'insu ke gudu lokaci guda, hannu yasa
kan gashinta ya warware k'ullin da ta yiwa gashin, ya d'aura fuskanshi kan lallausan gashin nata yana shak'ar k'anshin da sukeyi mai dad'i.


Ajiddeh kam tun a airport tayi magana da Mummy tace mata suna Ndjamena, tana sauk'a airport a Nigeria ta sake booking wani ticket d'in da zai kaita har can d'in, awanta shida tana zaune kamin jirgi yazo suka tafi ko cikin gari bata shiga ba, taxi ta tara ya kaita har hotel d'in da su Mummy sukace mata sunyi lodging, kai tsaye ta wuce d'akin da suke bayan ta sallami d'an taxi, knocking k'ofar d'akin tayi ta tsaya tana jiran a bud'e mata k'ofa, Yaa Zee ce ta bud'e mata k'ofan, babu yabo babu fallasa suka gaisa tun daga bakin k'ofa, Mummy da Aunty Jainaba ne zaune d'akin hotel d'in, k'arasawa tayi itama ta zube kan makeken gadon tana maida numfashi, takai minti biyu a haka sannan ta mik'e daga kwancen da take tana kallon Mummy tace "Mum sannunku", sannan ta juya ta dubi Aunty Jainaba dake kallonta itama, murmushi tayi mata tareda mik'ewa tana k'ok'arin rage kayan jikinta tace "Mummy duk abinda zamuyi cikin kwana biyu zamu gama dan cewa zaiyi zai biyoni, dan da k'yar na samu ya hak'ura bai biyonin ba, jarababbe, dan haka yau da gobe ayi komai mu koma da wuri", baki Aunty Jainaba ta tab'e tace "Dan shi sarkin k'wak'war mata ai sai ya biyo kin, kwana biyun da zakiyi shine harda wani kuzo tare, ai ko da yaxon ma kuma babu abinda zai hanamu tahowa", Yaa zee ce ta taho riqe da can drink da ta d'auko fridge ta bayan ta rufe k'ofan, zama tayi tana kallon Mum tace "mummy kinsan mutumin nan appointment yake badawa, in bakazo ba time ya wuce sai dai a sake booking, Ku shirya mu wuce tun wuri kamin time d'inmu ya k'ure muyi asara, ba musu su Mum aka hau shirin tafiya, lokacin Ajiddeh ta fito cikin toilet d'aure da towel har ta watsa ruwa, itama shirin ta hau yi, suna gamawa suka fito waje, taxi suka tare sukayi mishi kwatancen inda suke son zuwa, babu b'ata lokaci ya fad'a musu amount d'in da zasu bashi sannan suka d'au hanya, tafiyar awa uku suka isa, driver ya tsaya dab inda suka mishi kwatance, gidane d'an madaidaici mai kyau, gabanshi da bayanshi kuma duk jeji ne, da mamaki Ajiddeh ta juyo tana kallonsu tace "nan ne gun?", kai suka kad'a mata a tare, cewa tayi "ca nake wajen wannan mutumin zamu koma na kwanaki", Aunty Jainabace tace "wa?, wa zai koma wajen munafikin nan, ai kud'inmu kawai yacinye babu wani aiki da ya iya, macuci ne, bok'an k'arya", (Lol boka ma harda na k'arya da gaskiya, Allah ya tabbatar damu kan shiriya), Ajiddeh ce ta ciro kud'in ta baiwa mai taxi kud'inshi, yana tafiya suka shiga knocking, mai gadine ya bud'e musu gate d'in gidan bayan ya gama yi musu tambayoyi sannan yayi musu jagora har palon gidan, palone babba, babu komai ciki sai carpet da aka shimfid'a su wasu throw pillows, wani farin dattijo ne zaune yana sanye da farin kaya da dogon farin gemunshi, gefenshi kuma littafai ne tuli guda, a tare sukayi sallama, saida ya amsa musu sannan suka shigo daga ciki suka samu waje suka zazzauna, shi ya fara yi musu magana kamar haka, "nasan abinda ke tafe daku baki d'ayanku, Keh!", ya nuna Yaa Zee yace "senator Gamji ke son aurenki amma yana da mata ku kuma baku son mai mata, ita kuma wannan", ya nuna Ajiddeh yace "tabbas akwai wani al'amari tattare da ita mai rikitarwa da ni kaina na kasa fahimta, abune babba da ya shige min duhu na kasa gano komai game dashi duk iyawata, kuma shi wannan abun na tare da ita dan har ya faru ya k'are sannan ba alheri bane gareta", a tsorace suke jin bayanin malamin da abinda yake fad'a musun, a d'arere mummy ta kalli malamin tace "Allah gafarta malan, wane abune haka har zaifi k'arfinka, mu nan munyi maka alk'awari daga miliyan goma har zuwa hamsin zamu iya badawa in dai aikinmu zai yi yadda mukeso, Allah gafarta malan, a taimaka a dubo mana wannan abun dake shirin jawo mana matsala", wani shu'umin murmushi yayi yace "ai ni d'in nan duk abinda kikaga banyi shi ba a fad'in garin nan toh tabbass babu mai iya yi dan ni keda iko ga kowanne aljani da muke amfani dasu, dan haka ku kwantar da hankulanku, anjima da yamma za a fara aiki, yanzu haka masauki za a kaiku kamin yamma tayi, su wad'anda za ayiwa aikin kowacce d'akinta daban, ku kuma za a had'eku d'aki d'aya ku da babu aikin da zaku buk'ata, Dan aikin nada son sirri", hakan kuwa akayi, wani d'an saurayi ne ya kaisu d'akunan da aka umurceshi da ya kaisu, y'an madaidaitan d'akuna ne masu kyau ba laifi, Zainab da Ajiddeh aka basu d'ad'd'aya kowannesu sai mummy da Aunty Jainaba aka had'esu a guda d'aya.

A hankali Abu ya d'aura plumpy lips d'inshi kan goshin Batuul yayi pecking, haka ya dinga yi har saida ya sauk'o wuyanta, babu abinda jikinta keyi in banda rawa, k'ok'arin barin jikinshi ta shiga yi amma bai saketa ba, a nutse ya kwantar da ita kan gadon ya d'an sunkuyo kanta, sai lokacin tayi regretting dadewan da tayi kwance kan gadon, hawaye ne ya shiga silalowa daga idonta, baki ta bud'e zatayi magana Abu ya had'e bakinshi da nata, sosai ya shiga kissing d'inta, numfashinta ne ya kusa d'aukewa jin irin abubuwan da yake mata, kuka ta fasheda tace "Yaa Abu dan Allah kayi hak'uri plss bana son irin haka", baima san tana yi ba yaci gaba da abinda yakeyi, Batuul kam kuka takeyi sosai, saida taji ya fara wuce limit kuma duk magiyarta bai sarara mata ba tace "Yaa Abu am not pure wllh, kayi hak'uri ka barni bazan sake ba dagaske", sai da ya jagwalgwalata son ranshi kamin ya saketa ya fad'a gefenta yana maida numfashi, hannu yasa ya jawota jikinshi ya rungumeta tsam jikinshi ta gefe tareda kwantar da ita kan faffad'an k'irjinshi, kuka kawae take idonta a rufe, a hankali yayi brushing lips d'inshi kan nata tareda mata light kiss, har lokacin idonshi lumshe suke shi ma, sunfi awa d'aya a haka sai ajiyar zuciya Batuul ke sauk'ewa da haka har bacci ya d'auketa, a hankali ya kwantar da ita daga jikinshi ya mik'e ya shige toilet, wanka yayi ya fito ya canja kaya, murmushi yayi yasa hannu cikin gashin kanshi ya bajesu ganin tiny figure d'inta na bacci peacefully, karasawa yayi gadon yayi pecking d'inta, motsi tayi tare da gyara kwanciyarta, wani nutsuwan da bae taba sanin da shi ba yake samu gun Batuul, gown d'inta ya d'age har zuwa cinyoyinta, ya janyo duvet d'in gadon ya ninka biyu ya rufa mata, kanta kawai ya bari a bud'e, key d'in motanshi ya d'auka kan side drawer ya fita, if he can clearly remember yau babu abinda taci, driving yakeyi amma gaba d'aya hankalinshi na kan Batuul, murmushi kawai yakeyi ba tareda yasan dalili ba, but shi dai yasan being with Batuul na sashi jin exceptional feeling d'in da bai tab'a experiencing ba, a wani restaurant d'in kusa dasu ya shiga ya siyo musu abinci, baifi thirty minutes ba da fita ya dawo, har lokacin tana bacci, kan gadon ya hau ya d'agota jikinshi, daidai kunnenta ya rad'a mata "Wake up, sleepy head", a hankali ta bud'e lumsassun idanunta ta sauk'e kanshi, komawa tayi zata kwanta ya d'agata cak ya zaunar da ita, a tsorace ta wara ido, abubuwan da suka farune ya dinga tariyo mata, rintse ido tayi bata son ganinshi ga wani kunyansa da take, a ranta ta godewa Allah da yasa tace mishi she is not pure, iska ya hura mata fuska yace "Hey tashi kici abinci", sai lokacin ta bud'e ido ta kalli inda ya zuba ledojin, ce mata yayi "Brush first", a hankali ta yaye bargon da ya rufa mata, ganin cinyoyinta waje yasa tayi maza ta rufesu, a hankali ta kalleshi ta gefen ido taga ita yake kallo yana murmushi, zumb'uro baki tayi ta sauk'o daga kan gadon ta nufi toilet da sauri, ya bi ta da kallo, brush d'aya kawai ta gani, fitowa tayi ta tsaya bakin k'ofan baki a tsuke, ya tsaya yana kallon yadda ta tsuke bakin, a ranshi yace "she is cute, Not beautiful", ce mata yayi "fito mana, ko tsayuwan bakin toilet d'in ke miki dad'i?", raurau tayi da ido tace "Ai ba brush ciki, guda d'aya na gani", ba tareda ya kalleta ba yace "then you use that one, it's mine", wara ido tayi jin abinda yace, ta had'e rai tace "I can't use it, its yours", murmushi yayi ya tashi ya isa inda take ya fixgota ta fasa ihu, ya had'a bakinshi da nata, ya kai two minutes yana kissing d'inta sannan yace "you can now go and brush", hawayen da ya zubo mata ta goge da bayan hannu ta koma cikin toilet d'in jiki a sanyaye, ruwan d'umi ta kunna zata wanke brush d'in sai kuma tayi tsaki ta shafa toothpaste d'in ta wanke bakinta a haka, a d'akin ya baje abincin da ya siyo musu, a hankali ta k'araso ta zauna bakin gadon, kallonta yayi yace get down and eat", ba musu ta sauk'o dan yunwan da takeji, a hankali ta dinga cin abincin har saida taji ta k'oshi, shi kam babu abinda yakeyi banda kallonta, birgeshi tayi yadda takecin abincin, ganin ta dena ci ya harareta yace "me?", a hankali tace mishi "am full", had'e rai yayi yace c'mon finish dat before I meet you there", baki ta zumb'uro ta matso taci gaba da ci a haka har suka gama, ita ta tattare packs d'in duka waje d'aya, hannunta ya kamo yana kallon fuskanta yace "kin manta ma mey ya kawoki ko, you were busy engrossed in being hugged by me and feeling the warmth of my body huhh?", had'e rai tayi ta d'auke kai kamar bata ji shi ba, murmushin shi mai kyau yayi ya jata suka tafi d'akin da ya zuba kayanta, ce mata yayi "Get what you are here for" sannan ya sake mata hannu, k'arasawa tayi ta d'auko d'an kwalin da kayan ke ciki, hannu yasa ya amshesu daga gunta, kallon mamaki ta bishi dashi, wai wannan Yaa Abun da ta sani ne kuwa, har wani trying yake ya zama gentle, Lol, kallonta shima yayi tareda smirking yace " Hey kina kallewa Ajiddeh miji ko, zata dawo ne, before then let's get going", ya kamo hannunta, kin tafiya tayi har saida ya juyo yana kallonta "What's up", ya fad'i tareda d'age mata girarshi d'aya, raurau tayi da ido kamar mai shirin kuka a shagwab'e tace "Yaa Abu I don't want to leave, ni nafi son xaman nan kai ka tafi", sai da ya tsaya for some seconds yana kallonta bayan ta gama maganan sannan yayi murmushi yace "har kin manta, d house is my wife's, my love, we have to leave", had'e rai tayi ta tsuke baki jin abinda yace mata, warce hannunta tayi daga nashi tayi gaba abinta, dariya ta bashi shima ya biyota a baya, yana danna lock d'in motar ta bud'e ta fad'a ciki, shima baice mata komai ba ya bud'e ya shiga yana murmushi.

πŸ’–πŸ’BATUULπŸ’–πŸ’





64






By phartiemarhk




Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*





Bai ce mata komai ba ya tada motar sukayi gaba, lokaci lokaci yake juyowa yana kallon yadda ta tsuke fuska, murmushi kawai yake yi yana tuk'in, Batuul kam ko sau d'aya bata juyo ta kalleshi ba sai ma window da ta juya tana kallon waje, hannunshi ya mik'o ya kamo nata cikin nashi har lokacin bata juyo ta kalleshi ba wai a dole fushi takeyi anqi barin ta a gidan glass, gaban wani fruit stall yayi parking, sai snn ya sake mata hannuwa ya fita, ba a jima ba ya dawo riqe da paper bags da fruits a ciki, daga bayan mota ya zuba su ya zagayo ya shiga ya tada suka tafi, har lokacin su Batuul rai a had'e, a hankali ta juyo da kanta suka had'a ido, tsuke baki tayi ta d'auke kanta da sauri, ganin expression d'in fuskanta bai san lokacin da dariya ya k'wace mishi ba, dariya sosai ya shiga yi harda dukan steering wheel, juyowa tayi tana kallonshi da idanunta da suka cicciko, ganin yana kallonta baice komai ba ta kifa kanta a cinya ta fashe da kuka, kuka sosai takeyi kamar wacce aka Zane, dariya hakan ya dad'a bashi, dakewa yayi yace "Wai What's wrong kike cikamin kunne da kuka, mey akayi miki?", bata d'ago ba, saima k'arawa da tayi, daidai nan yayi parking, k'ofa ta bud'e zata fita ya fixgota, d'ago kanta yayi yana kallon yadda cute lips d'inta suka koma ja, kallon idonta yayi in a serious tone yace "mey ya sameki"?, fashewa tayi da wani sabon kukan, janyota yayi ya rungumeta jikinshi tsam, babu abinda take sai sauk'e ajiyar zuciya jinta kwance kan faffad'an k'irjinshi da k'anshinshi mai dad'i, har saida yaji tayi shiru sannan ya d'agota yana kallon fuskanta yace "tell me mey ke damunki kike kuka", zumb'uro baki tayi ba tareda ta bari sun had'a ido ba tace "ba kai ne ke min dariya ba, kuma kace baxan tsaya wancan gidan ba", baisan lokacin da dariyan ya sake kubce mishi, rai b'ace ta tsaya tana kallon yadda ya dage yana mata dariya, a fusace ta bud'e k'ofar motan ta fice, bata tsaya ko ina ba saida ta shige d'akinta, kan gado ta fad'a taci gaba da kukanta, sai da ya gama dariyarshi ya fito cikin motar, abubuwan da ya siyo da kuma wad'anda suka d'ebo can gidan ya kwaso sannan ya rufe motar shima ya shigo gida, a kan kitchen island ya xuba kayan da suke hannunshi ya haura sama, direct d'akin Batuul ya wuce, kwance ya tarar da ita a kife har lokacin kukan takeyi, hannu yasa ya d'agota yana kallonta yace "I told yhu d house is my wife's, dariya kuma ai ke kika sani yin dariyan", d'an murgud'a bakinta tayi ta janye jikinta ta juya mishi baya, murmushi yayi ya matsa inda take ya rungumota ta baya, ajiyar zuciya ya sauk'e jin k'anshin jikinta mai dad'i, cikin sanyin murya yace "okay sorry, I will ask my wife, if she permits then you stay there", wani bak'in ciki ne ya sake turnik'e ta jin sai ambatar wife d'inshi yakeyi, d'an k'aramin tsaki tayi daga ciki ta shiga k'ok'arin kwace kanta daga rik'on da yayi mata ta miqe ta shige toilet ta rufo k'ofar da k'arfi, dariya yarinyar ke bashi in tayi wani abun, waje ya samu kan gadon yayi kwanciyarshi abinsa, tafi minti talatin cikin toilet tana zaune cikin bath tub, sai da tayi wankan tsarki sannan tayi normal wankan ta ta fito, ganin dad'ewan da tayi tasan ya bar d'akin, tana d'aure da towel jikinta d'aya kuma tana goge gashin kanta dashi ta fito, gaban mirror taje ta jawo stool ta zauna tana goge gashin, sunkuyawa tayi ta d'auko hand dryer, d'agowan da xata yi ta hango mutum jikin mirror, wani irin k'ara ta fasa zata koma cikin toilet don bata yi tunanin yana nan har lkcn ba, da hanzari ya mik'e ya fixgota kan ta shiga bayin, kuka ta fashe da zata sulale k'asa dan ta tsorata sosai, k'afafuwanta duk suka yi weak, tsam ya rik'ota ya rungumeta, har lokacin kuka takeyi, hannu ya d'aura bayanta ya shiga patting, a kunne ya dinga rad'a mata addu'a har ta samu nutsuwa, "sorry i didnt mean to startle you", kan gado ya maidasu suka zauna, kallonta kawai yakeyi, gashinta dake d'igar da ruwa ya kalla sannan ya kalleta yace

1 Comments On BATUUL
avatar
hafsat-9-3

12 months ago

Reply

Nice book

Please Login or Register in order to submit comment