Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

spaghetti lasagne tanayi sunata shan hira, saida ta gama snn tayi musu serving a bowl d'aya, tana tunkaro Batuul dashi dariyar dake fuskarta ta d'auke ta toshe bakinta, Farida tace "A'a meye hakan" da k'yar ta samu ta iya bud'e baki tace "kin saka cheese bana so", da mamaki Farida ta tsaya kallonta Dan tasanta da son cheese, sabida itama ta zuba tace "Cheese d'in ne ya saki kamar zakiyi kuka?", ta bud'e baki kenan zata yi magana taji amai na yunk'uro mata, da gudu ta sauk'o tayi sama, Faridan ma a guje ta ajiye fork d'in hannunta tabita a baya tana tambayarta ko lafiya?, saida ta gama kwarara amanta a toilet snn ta d'ago a galabaice duk batada k'arfi, Farida duk ta rud'e sai hawaye take ta rasa yanda zatayi gashi ta baro wayoyinsu wancan gidan sabida tsabar masifan shi, kamo Batuul tayi daga toilet d'in ta wanke mata fuska snn suka fito, kan gado ta kwantar da Ita sai maida numfashi take, tashi tayi ta fita ta dafo mata noodles cikin lokaci kad'an, nanma Batuul turewa tayi tace batason kamshinshi, Farida duk ta damu tace "Besty wai mey ke damunki?, dama yana miki haka kuma yaushe kika zama allergic to cheese da har zai na saki amai",Batuul dai shiru tayi mata tana maida numfashi, a hankali kamar mai rad'a tace "Orange Juice zansha da Toast", da sauri Farida ta mik'e bata dad'e ba ta dawo riqe da abinda Batuul d'in ta fad'a mata, kad'an taci ta ture tace ta k'oshi, ta kwanta bacci, Farida kam kallonta kawai takeyi jikinta duk yayi sanyi, saida ta tabbatar baccin Batuul keyi sannan ta tashi ta sauk'a k'asa dan ta fara jin yunwa, sai a snn ta tuna da girkin da tayi musu, warming tayi ta tsiyayo juice tayi sama dashi, duk bayan seconds sai ta kalli Batuul ta tabbatar tana lafiya, Batuul kam Bacci takeyi sosai, lokaci lokaci takan bud'e ido suna had'a ido da Farida zata sakar mata murmushi taci gaba da baccinta abin har tsoro ya fara bawa Faridan, Har magrib Batuul bata tashi ba sai da Farida taga gari yayi duhu snn ta tada ta suyi sllh magrib, tana farkawa tace "Yaa Abu fa?, bai dawo ba?", Farida tace mata "Ehh", take mood d'inta ya canja ta had'e rai tayi toilet abinta, koda ta fito kin yin magana tayi, Farida har saida ta gaji dan kanta tayi shiru, Kallonta Farida tayi tana murmushi dan ta kasa daurewa da sudden behavior nan nata tace "uhnnm Besty ko dai Baby za a samawa Yayana ne wannan rashin lafiya haka?", kunya duk ya rufe Batuul tayi kicin kicin da fuska tace "Baby kuma, wani irin baby, Malaria nake ya kama ni", dariya maganan ya bawa Farida tace "Ko ba Malaria ba, ai 9ja muke dole kice Malaria kikeyi", bata kulata ba dan ita rashin zuwan Abu ke damunta, itama Faridan badan ta yadda ta k'yaleta ba, haka ta zama wata shiru shiru har goman dare tana tsammanin dawowanshi amma baizo ba har sha d'aya har saida Farida ta gane, shima Abu gaba d'aya hankalinshi na kan Batuul, gashi ta zama so choosy akan abinci duk hankalinshi ya tashi






Washe gari da sassafe ya fito lokacin Ajiddeh na bacci ya tafi can gidan, a d'aki ya tadda Batuul kwance, kallo takeyi amma gaba d'aya hankalinta baya wajen, da k'yar ta samu bacci ya d'auketa jiyan nan, gaba d'aya haushinshi takeji, d'auke kai tayi kamar bata ganshi ba taci gaba da abinda takeyi, hawowa yayi kan gadon ya d'agata cak yace "Wannan shariyan haka kuma fa? How is my baby?, ya fad'a yana shafa cikinta daidai nan Farida ta shigo riqe da d'an tray da glass cup a kai, had'e rai tayi ta k'araso ciki tareda gaisheshi, bai amsa mata ba saima harara da ya bita dashi, zumb'uro baki tayi tacewa Batuul "Ga lemonade d'in" ta juya zata fita, kai Batuul ta kad'a mata kawai dan kunyan yadda tazo ta samesu ta ji" Farida na fita ya juyo da Batuul yace "Hey bana son wannan silent treatment d'in mana, shout and yell yafi min da wannan shirun da kikemin", kamar ba da ita yayi maganan ba ta sake d'auke Kanta, a hankali ya fara mata magana yace "Hear me out, kinga Ajiddeh ce fa batajin dad'i shiyasa ban dawo ba jiya", kuka ta fashe mishi da ta shiga turashi daga jikinta tace "ai ni lafiyar ce dani, ka koma wajenta tunda nata lafiyan yafi damunka", dariya ne ya k'ufce mishi ganowa da yayi kishi ke damunta, nan ta k'ara k'arfin kukanta, janyota yayi jikinshi ya rungume ya shiga lallashinta, da k'yar ya samu tayi shiru, sai wajen 10 d'in safe ya fita siyo mata abubuwan da ta lissafa mishi zataci ya fita ya samo mata, lokacin da ya dawo gida a parlourn k'asa ya tadda Farida zaune tana kallon Tv yace mata "Ammah tace min Monday zakiyi resuming school dan haka nanda kwana hud'u zaki koma", tace "Ehhh", har ya fara tafiya tace "Yaa Abu wayoyinmu a gidanka, dan Allah ka kawo mana, koh jiya haka Batuul tayi ta amai kuma na rasa wanda zan fad'awa dan babu waya", har ranshi yaji aman da Batuul tayi dan yasan tana wahala sosai amma yaqi nunawa ya dake yace "anqi a kawo d'in, da uban wani ne ya saki bari can?", ya haura sama ya barta nan zaune, kullum haka yakeyi da sassafe zai zo ya dubata har sai ya sata yin bacci yake komawa wajen Ajiddeh, Ajiddeh ma bata sake mishi maganan Batuul ba, ko tambayanshi Ina take batayi ba, Dan Mummy tace mata ta kwantarda hankalinta cikin kwana biyu za ayi maganin Batuul, Farida kuma ce mata yayi ta koma Nigeria.





Bayan kwana uku ana gobe Farida zata koma da yamma Batuul na baccinta a d'aki ita kuma Farida na gefenta tana chatting da Affan d'inta sai murmushi takeyi abinta, a firgice Batuul ta farka tareda sakin k'ara, Farida dake gefenta ta mik'e a rude ta rik'ota tana tambayarta ko lafiya, kasa yi mata magana tayi sai riqe cikinta da tayi ta sulale k'asa tana yarfe hannu, hankali tashe Farida ta shiga neman layin Abutturab dan ko 2hrs baiyi da barin gidan ba, baccin ma da takeyi ajikinshi tayi snn ya kwantar da ita ya fita, kullum a rana yakan shigo sau biyar kuma da sassafe yake shigowa, watarana sai dai ta farka ta ganta a jikinshi, kwana ne kawai bayayi, kuka Farida ta fashe da ganin har ya katse bai d'auka ba, a karo na biyu ne da ta k'ira yana fara ringing ya d'aga, cikin kuka ta fad'a mishi abinda ke damun Batuul, bata gama ba ya katse wayan cikin tashin hankali, in few minutes ya iso kamar dama can yana area, a guje a ya hawo sama, ganin Batuul riqe da cikinta tanata murk'usu ya sake tada mishi hankali, nan ya rungumota ya shiga tambayarta mey ke damunta taqi cewa komai sai kukan da takeyi tana riqe da cikinta duk yanda yaso tyi magana batayi ba sai juye juye da takeyi, Shida Faridan duk hankalinsu tashe yake sosai, ganin sae gaba abun yakeyi duk ya rud'e, Farida daketa hawaye tayi k'arfin halin cewa Yaa Abu mu kaita asibiti Dan Allah kar wani abin ya sameta, sai lokacin tunanin Hospital ya fad'o mishi, ko second d'aya bai k'ara ba ya d'auke ta cak yayi waje da ita, mota ya sata shima ya shiga yaja motar duk hankalinsa tashe, a gurguje doctors suka karb'eta suka shiga dubata, duk iya kwarewarsu sun nuna amma basuga komai ba, haka suka hak'ura suka yi mata allurar pain reliever suka k'ara mata ruwa Dan ganin yanda taji jiki ta jigata, har ta fad'a daga d'an lokacin nan, likitocin na fita ya taso ya rungumeta yana sake tambayanta ta fad'a mishi inda ke mata ciwo, duk yanda yayi da ita k'in cewa komai tayi sai kukan da take tana juye juye, iyakar rudewa ya rude, Farida har fuskarta ya kumbura tsabar kukan da tasha, shikam ji yakeyi kamar ya cire mata ciwon ya dawo dashi jikinsa, Farida ce ta matso gaban gadon ta riqe hannunta d'aya ta shiga tofa mata addu'a a hankali, ta kusa minti sha biyar tana mata addu'a, ko Abutturab baisan abinda takeyi ba, a hankali ta fara tsaida kukan da takeyi jin ta fara samun relieve har dai tayi shiru tayi lamo jikinsa tana sauk'e numfashi, a hankali ya d'ago kanta yana kallon idonta da ya kumbura tsabar kukan da tasha, cikin sanyin Murya yace "Fatima don Allah tell me mey ke damunki, ina ke maki ciwo?", kyar ta iya bud'e baki tana nuna masa cikinta tace "cikina kemin wani iri", rungumeta yayi tsam jikinshi kamar wacce za a k'wace ya dinga rad'a mata sannu a hankali.
πŸ’–πŸ’BATUULπŸ’–πŸ’






77






By phartiemarhk






Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*






Tana nan rungume jikinshi har tayi bacci, a hankali yaji numfashinta na sauk'a kad'an kad'an alamun baccin nata ya fara nauyi, ajiyar zuciya ya sauk'e amma har lokacin tana nan kwance jikinshi bai kwantar da ita ba, sai bayan 15mins snn a hankali ya d'an d'agota daga jikinshi ya kwantar da ita kan gadon, kallon k'aramin cute face d'inta ya tsaya yi yana lumshe ido, ciwon rana d'aya amma duk ta fad'a ta rame, dama can ba wani jikin bane da ita, sai haske da ta k'ara, yafi five minutes idonshi na kanta daga baya ya d'auke idanunshi ya sauk'esu kan Farida dake tsaye gefe duk tayi sanyi yace "Taci wani abune bayan na fita?", kai ta girgiza mishi a hankali tace "Babu abinda taci, ko baccin daka sa tayi ma fa bata tashi ba, kawai ina kwance naga ta mik'e ta riqe cikinta, shine tace yana mata ciwo ne", kallon Farida kawai yakeyi har tayi shiru snn yasa hannu cikin gashin kanshi masu santsi ya bajesu yace "take care I will b right back", daga haka yayi exiting d'akin, har ya dawo bacci Batuul keyi, Farida na zaune kan kujera ta jingina kai ta baya ta tsura ma Batuul idanu, tausayinta kawai take cikin ranta, ji takeyi kamar ta fasa komawan gobe ko kuma su tafi tare, motsin k'ofan da taji ne yasata duban wajen, Abuturrab ne ya shigo riqe da paper bags a hannyenshi har ya k'araso cikin d'akin snn Farida ta miqe tana mishi sannu da zuwa ta anshi kayan dake hannun nashi, zama yayi daga kan kujeran idonshi nan kan Batuul d'in, sai da Farida tace mishi sannu da zuwa yaya snn ya dubeta ba tareda ya amsa ba ya jeho mata tambayar "Ta tashi bayan na fita?", kai ta kad'a mishi tace "No! Bata tashi ba, baccinta takeyi tun d'azu" bai ce komai ba ya juya ga kallon Batuul d'in da yakeji kamar ya cire mata ciwon gaba d'ayanshi ta huta, hannunta da babu drip ya kamo cikin nashi ya rik'e gam yana jin wani feeling na circulating dukkanin nerves d'inshi, a hankali ya juyo ya dubi Faridan yace "Kinci abinci ne?", ta kad'a mishi kai alamar a'a, yace "gashi nan ki duba packs d'innan", yayi mata nuni da bags d'in da ya shigo dasu, bags d'in ta janyo ta shiga bubbud'esu, tab'e baki tayi ganin irin abincin da ya siyo musu, ita bata cika son jagwalgwalon turawa ba, daga k'arshe dai pasta with Lamb ragu da cauli flower crisp ta ciro ta ajiye gefe, kallon Abu tayi tace "Yaa Abu in ciro maka?", kamar me nazari yake kallonta snn ya girgiza mata yace "No am okay", batayi mishi musu ba ta koma kan kujera ta shiga cin abincinta, sai da ta gama tayi disposing packs d'in yace mata ta mik'o mishi ruwa, Fridge d'in d'akin ta bud'e ta mik'o mishi bottle d'aya bayan ta bud'e, har lokacin hannunshi na cikin na Batuul, yana jin yadda pulses d'inta ke kaiwa da komowa, basu fi thirty minutes ba bayan nan ta bud'e lumsassun idanunta a hankali, kanshi tafara sauk'esu, ido ya wara shima ya matso kan gadon ya d'agota sai ji tayi ya rungumeta jikinshi, ya kai minti biyu rungume da ita bata yi k'ok'arin k'wace kanta ba har saida ya saketa ya d'ago hab'arta yace "Ina ke miki ciwo yanxu Fatima?", murmushi tayi mishi kawai ta shiga k'ok'arin tashi ta zauna, da kanshi ya d'agata ta zauna yana making sure bata takura ba, ganin yanda Farida ta tsaya tsuru tana kallonta ya bawa Batuul dariya, tace "Hey what's up duk kin zama wata iri, am okay fa", murna ne ya cika Faridan tayi maza ta dawo kan gadon ta zauna, tace "Don't get sick pls, you scared d hell out ta me pls kinji?" murmushi tayi kamar ba ita ke ciwo ba d'azu snn ta kalli Abu da yake lumshe ido yana bud'esu yana kallonta ta d'an shagwab'e fuska tace "Mu tafi gida Yaa Abu, ni bana son asibitin nan", kai ya girgiza mata yace "No sai kin fad'amin mey ke damunki, baza mu tafi ba bamusan mey ke damunki ba", had'e rai tayi tace "Yaa Abu nifa na warke, mu tafi gida", ta fad'a tana k'ok'arin sauk'owa kan gadon, hannunta ya rik'o ya k'ura mata hazel brown idanunshi, cikin wani irin murya yace "Fatima mana, I want you to fully get better, bana son kina shan wahala kamar na yau, nafiso ki zama under medication, under proper care kinji?", zumb'uro mishi baki tayi tace "Toh fa na warke ni, bazan sake yin rashin lafiyan ba", Ido kawai ya zuba mata yanason ta gano abinda yake hange amma baya son stressing d'inta tunda ba isasshen lafiya bane da ita, a sanyaye yace mata "ina zaki yanzun?", ta zumb'uro mishi baki tace "toilet", da sauri Farida ta mik'e ta riqota tace muje in rakaki, kai ta kad'a tace "zanfa Iya da kaina na warke", kamar jira yake ta rufe baki ya sunkuceta yayi toilet da ita itako sai wuntsila k'afa takeyi ya sauk'eta, bai bi ta kanta ba har saida ya Isa toilet snn ya ajiyeta a hankali, d'an murgud'a mishi bakin tayi snn ta kalleshi tace "Toh ka tafi", wani irin kallon da yayi mata yasata yin shiru ta kasa motsi, ganin ta nemi waje ta tsaya yasashi k'arasawa gabanta ya shiga k'ok'arin d'age mata skirt d'inta, ihu ta fasa ta riqe skirt d'in da k'arfi tace "Bafa komai zanyi ba, alwala nakeson yi", kallonta kawai yakeyi snn ya kamata suka koma gaban hand wash basin d'in, kamar wata yarinya shi yayi mata alwalan, bags d'in da ya shigo dasu ya janyo bayan ya sata ta zauna kan gadon, pack d'aya ya Ciro mai d'auke da malted custard roast da Lamb Kebab salad, da kanshi ya bata abinci har saida tace ta k'oshi snn yace tayi sllhn shi kuma ya fita wajen doctor yayi maganan discharging d'inta, bai jima ya shigo lokacin har ta idar da sllh suna hiransu da Farida, ce musu yayi zasu tafi, murna Batuul ta shiga yi dan ta tsani asibiti ita kam, da murnarta ta shige gaba kamar ba ita aka kawo a galabaice ba, driving yakeyi amma duk bayan seconds biyar sai ya juyo ya dubeta, cikin lokaci kad'an suka isa gida lokacin ana k'iran Magrib,saida sukayi sllh snn suka kafa hira ita da Farida, ganin ya shigo d'akin yasa Farida fita, daidai tazo wuceshi yace " You should Get ready gobe flight d'in by 8 ne", sai a lokacin Batuul ta tuna da tafiyan Farida, jiki a sanyaye ta amsa da "toh", sam hankalinta bai kwanta da barin Batuul ba gashi shi bama zama yakeyi ba, cikin d'akin ya k'araso ya zauna bakin gadon yana kallon Batuul da har idonta ya cicciko yace "How you feeling now?", baki ta bud'e zatayi magana hawayen dake tare idonta ya shiga gangarowa, har ranshi ya ji zubowansu da hanzari ya gyara zamanshi kan gadon ya rungumota tareda cewa "Yasalam, Fatima what is it again?, I told you mu zauna asibitin amma kikayi insisting mu dawo gashi nan yana damunki kuma koh", ji yayi ta sake lafewa jikinshi a hankali tace "Does she have to leave tomorrow?", sai da ya tsaya for some seconds snn ya gano abinda take nufi, ajiyar zuciya ya sauk'e jin ba ciwon cikin nata bane ta d'ago kanta yace "School zata koma, dama mid semester break ta zo", a hankali ta d'ago ta dubeshi tace "toh ni yaushe zaka kaini gidan, I want to go home" muryarta na rawa ta kare maganar, rungumota ya sakeyi jikinshi yana shafa kanta yace "very soon, ko har kin manta deal d'inmune?, ba nace zan kaiki gida da kaina ba in kika haifa min baby na", d'an zumb'uro baki tayi jin ya ambaci Babyn shi ta kauda kanta, murmushi yayi tareda juyo da kan nata, idonshi kan lips d'inta yace "I like them when you pout, I miss them so much", kamin ta ankara har kai nashi lips d'in kan nata, passionately yake kissing d'inta kamar yau ya fara kissing d'in nata idonsa lumshe, haka yayita tarairayarta har wajen sha d'aya bayan yayi mata wanka ya jasu Sllh Isha ya kwantar da ita ya shiga sata bacci, a jikinshi tayi baccin wajen 11:30, saida ya tabbatar tayi nisa a baccin tukunna ya saka mata temperature d'in d'akin ya koma moderate, ya tabbatar she is fine snn ya fita, a parlourn k'asa ya tadda Farida ta kashe wutan ko ina tana kallon CBS, Ce mata yayi ta koma d'aki gun Batuul snn yayi mata sai da safe ya fita akan gobe da safe zaizo kaita airport ta zama cikin shiri, sai da ya shiga mota tukunna ya tuna da wayoyinsa, missed calls ya gani babu adadi daga mutane daban daban amma duk na Ajiddeh yafi yawa, d'an murza goshinshi yayi snn yayi igniting motar ya d'au hanyan gida, lokacin da ya isa Ajiddeh na kwance parlour tayi bacci da alama tasha kuka ba kad'an, tausayinta yaji Sosai har cikin ranshi yasan bai kyauta mata ba, kashe appliances d'in yayi snn ya dawo ya d'auketa yayi sama da ita





Washegari kamar kullum da ya tashi sllh saida ya tashi Ajiddeh amma bata tashi ba, shi kam daga masallaci d'ayan gidan ya wuce, a kitchen ya taddasu su biyun duka Farida har ta shirya, k'arasowa yayi cikin kitchen d'in yana amsa gaisuwan Farida ya isa inda Batuul ke jingine jinkin Fridge, yana zuwa ya jawota jikinshi ya d'aura hannunshi kan mararta a hankali, da sauri ta d'aga ido taga ko Farida na kallonsu, ai kuwa ido hud'u sukayi da Faridan, maza tayi ta d'auke idonta cike da kunya snn ta riqe mishi hannu, rankwafowa yayi daidai wuyanta da muryan shagwab'a da ya sauqe mata kasala gaba d'aya yace "Ina duba Baby na", cike da jin kunya a hankali tace "Yaa Abu Farida fa na nan" kallon Faridan yayi, suna had'a ido ya sakar mata wani irin kallo, babu shiri ta bar abinda takeyi ta rage wutan stove d'in tayi waje da sauri, tana fita ya juyo da Batuul d'in, y'ar rigar dake jikinta ya d'age ya shiga making circles a flat tummy d'inta da yasata jin wani sabon feeling na daban na ratsata, a hankali yace mata "Meh zaki bawa Farida?", sai lokacin abin ya fad'o mata d'ago kai tace "Nima ban sani bafa, kawai zan bata kosu bracelets d'ina ko?", ta tambayeshi, murmushi yayi ya janye hannunshi cikin rigan nata ya kamota yace "muje ki gani sai ki duba ki ga In yayi a bata", babu musu ta bishi a baya suka fita waje, Farida na ganin fitansu ta koma kitchen taci gaba da abinda takeyi tana murmushi cike da jin dadin irin xaman Bestyn nata da yayanta, suna shigowa daidai nan Faridan ma ta fito riqe da bowl d'in oat a hannuta tana jujjuyashi, a nan ya bar Batuul ya haura sama, ba a jima ba ya sauko yace su wuce, cikin y'an minutes suka isa airport, sai lokacin Batuul ta dad'a tabbatar da tafiyan Farida, kamar kar su rabu harda k'wallanta, k'ok'arin fitowa ta shigayi daga motan zata raka Farida yayi maza ya rik'ota yana kallonta yace "Ina zakije haka?" , zumb'uro mishi baki tayi cike da shagwab'a tace "zan rakata mana", kai ya girgiza yace "kinada hankali zaki fita a haka ko mayafi babu?, dubi kayan dake jikinki?", kallon kanta tayi taga koh kayanta are, wandone jikinta sai jacket iya gwiwa da hood amma yake fad'a mata wai kada ta fita a haka, rai b'ace ta koma ta kwanta sai Faridan ce ta zagayo tayi hugging d'inta, dan takaici kasa magana tayi sai hawaye da ta dinga yi, shi ya d'auki jakan tsaraban ya rakata dashi yace mata inji Batuul, ya k'ara mata da kud'i masu yawa, har saida yaga ta shiga jirgi sannan ya juyo, a mota ya tadda Batuul har tayi kukanta ta gode Allah, ko sau d'aya bata kalleshi ba bayan ya dawo, haka ya k'arashi surutunshi suka isa gida, yana parking ta bud'e mota ta fita a guje, a gujen shima ya bita dan har ranshi yakejin gudun nata snn gashi ba lafiyane da ita isasshe ba, daidai takai k'afanta kan 5th stair case ya cimmata, wani razanannen k'ara ta saki da yasata durk'ushewa k'asa, binta yayi ya kamota jikinshi yana mata wani irin kallo yace "Fatima ban hanaki tsalle ba?, bakida hankali koh?, next time you try this shit I will slap you", gaba d'aya bata sanma mey yake fad'i ba sai yarfe hannu da takeyi, kuka sosai ta shiga yi tana k'iran sunan Auny tana riqe da cikinta, rud'ewa yayi ganin da gaske take ya d'agota yace "Batuul talk to me, cikin ne?", a hankali ta shiga gyad'a mishi kai a wahalce, duk ya rasa mey ma zaiyi dan duk ya rud'e, cak ya d'auketa sukayi asibiti, ikon Allah ne kawai ya kaisu lafiya dan baisan irin driving d'in da yayi ba, likitocin this time ma cikin gaggawa suka amsheta, sai kukan wahala take tana k'iran sunan Aunty, har dare likitocin na kan Batuul sun kasa gano Ina matsalar take gashi duk wani taimako da zasuyi sun mata shi amma babu wani ci gaba, Abu kam tsayawa kawai yayi yana kallonsu ya kasa cewa komai, kamar shi ke ciwon har fad'awa yayi daga yini d'aya. Sai karfe takwas da wani abu na daren bacci ya dauketa shi ma sai juye juye take, Abuturrab dake xaune gefenta ya tsura mata ido cike da tausayinta ganin yanda ta wani rame daga safen xuwa dare, mikewa yayi da kyar ya nufi office din likita, nan ya shaida ma likitan in dai cikin xai bada matsala kawai a cire sa, ficewa yayi daga office din ya nufi gida kafin ta tashi don dauko wayarsa, Ajiddeh na xaune parlor kamar ko da yaushe, yau dai sai ya gaya mata ma'anar fitar da yake da asuba ko sallama babu baxa kuma ta kara ganinsa ba sai dare, bin sa da kallo tayi ganin ko kallonta bai yi ba ya haura sama, mikewa tayi ta bi bayansa, xaune ta samesa gefen gado, da ganinsa kasan akwai matsala, ta karaso da sauri ta xauna gefensa tace "Me ya faru babe? What's wrong?" Rike kansa yayi bai ce komai ba, ta dago kansa tace "Talk to me mana, me ya faru" Da kyar ya iya bude baki yace "Batuul!" Ji tayi kamar ya soka mata mashi, lokaci daya xuciyarta ya shiga tafarfasa, ta dake tace "What about her?" Cike da confusion yace "I just don't know, tana asibiti" wani farin ciki ya lullube Ajiddeh, sai dai cike da damuwa kamar gaske tace "Ayya, Allah ya bata lafiya" mikewa yayi da kyar ya dau wayarsa xai fita, tace "plss xan bi ka muje in dubata babe" bai tanka ta ba ya fita, ta mike cike da murna ta dau hijab ta sa ta bi bayansa da sauri, har ta shiga motar bai ce mata komai ba ya tada suka kama hanyar asibitin, ba karamin tashi hankalinsa ya kuma yi ba ganin likitoci a kanta, su

1 Comments On BATUUL
avatar
hafsat-9-3

12 months ago

Reply

Nice book

Please Login or Register in order to submit comment