Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta sake tambayanta "wai meye inata magana kinyi min shiru" tsaki Farida taja tace "ai ni da dan ta nice wlhy ko kwana ďaya banyi a kasar nn, dama can ba so nake ba Ammah ta sani dole inje, wlhy saura kaďan in mutu dan baqin ciki, dama sai da kika tayi min dariyan mugunta har da wani rakani airport bakiga ko waya banyi nace miki zan dawo ba, ni nan gaba ko meye za a bani ba zanje gidan ya Abuu ba, toh meye ma yayi zafi, ni dai ban k'ara zuwa, gidan Yaa Abu bai yi ba, shi zafin kai matarsa y'ar duniya mara mutunci, gaba ďaya ta gama da Yaa Abu, Dan tausayi ma yake bani " tsaya Batuul tayi tana kallonta har sai da tayi shiru tukunna tace "tun ďazu kike surutu, tell me exactly what happened da kika dawo before time " tsaki Farida taja tace "kina son spoiling mood ďina ko, toh tunda baki ganeba, gidan ne babu daďi, tunda nayi stepping k'afa na a cikin gidan maganan arziki bai tab'a haďani da Ajiddeh ba, kai tun lokacin da na shigo gidan tana hakimce a parlour ita da wasu y'an uwanta ko k'awayenta ne oho taqi amsamin sallama ban sake bi ta kanta ba, shima Yaa Abun da ya dawo gida da yamma naje zan fara mishi complain cewa yayi wai shi fa baya son K'ananan maganganu , wai haka matar tashi take I shud let her be, ni nake dafawa kaina abinci, shima ďin sae dae Cook suyi ya ci, gara ma da naje ne take ďan sani in dafa mishi wani abun, kuma baya iya ce mata komai duk iskancin da takeyi, daga ta ganni zata fara wani shan magani tana habaice habaice, har da cewa rannan wai aikin banza, ai mun riga da mun makara daga ni har iyayena tunda har muka bari ta aureshi, toh shine shekaran jiya da naga iskancin nata kaďan ne da ta saka Ammah jiya na tashi na bita har ďaki bayan y'an iskan y'an uwan nata sun tafi nace wlhy in ta kuma faďin wani abu akan iyaye na sai na lakaďa mata dukan tsiya, kuma in daki banza babu mai ce min komai, da yake k'aramar y'ar iska ce bata ce min komai ba...." Ido Batuul ta wara ta riko hannun Farida tace "Dan Allah dagaske kike, duka fa kikace zakiyi mata har ďakinta kuma, ta girmemu fa sosai farida" hannunta ta Janye tace "Ni ina ruwana da girman ta, ai bata rike ba, y'ar rainin hankali ai da ta sake faďin wani abun wlhy da sai ta raina kanta, sai na kusa illatata, Dan ko banida karfi sai na samu wani abin na bigeta dashi, shine fa bayan Yaa Abu ya dawo, yana shigowa ta fashe da kukan munafurci wai yau wuni nayi ina zaginta har dasu dungure mata kai, dukana kadae ne bae yi ba in gaya maki, shine fa yayi maza yayi min booking flight na dawo yau, har ce min yayi fa wai hutun ya isa haka in koma dama shi bai nemeni ba bare inzo ina tayarwa matarsa hankali, Dan bakin ciki ma ko tsayawa banyi na mishi explaining komai ba na juya naje haďa kayana, a parlour ma na kwana shi kuma ya jata sukayi sama , da asuba ya sauk'o ya tulo min kuďi masu Uban yawa kamar su aka ce mishi nazo nema, ya haďani da John Driver ďinshi ya kawoni airport, da ya rakani bakin k'ofa nidai sai da na mishi magana nace mishi wlhy Hakkin su Ammah bazai barshi ba, tunda yayi aure sau ďaya ya tab'a zuwa ya dubasu waya kam ba a xancen sa don baya kira, kuma fa ba wai baya shigowa Nigeria ba, yana shigowa Dan ko randa naje a jiyan shi ya dawo, sai da naga jikinshi yayi sanyi tukunna na fita na bar mishi gidanshi, yau da asuba muka k'araso, kinji yadda akayi na dawo banyi wata ďaya ba, tagumi Batuul tayi tana kallonta cike da tausayin Ammah, shi yasa duk bata da sukuni knn ta ga ta rame, gskya ya Abuu bae kyauta ba.

Hi Everyone out there reading Batuul , EID MUBARAK, Allah yasa Ibadunmu karbabbune, so sorry for the late post, alot of things came up so I couldn't write but daga yanxu har a gama Batuul In Shaa Allah baza s samu matsala ba though nasan am a lazy writer in (Sister KHALEESAT's voice 😁), but then I will try and be updating you everyday In Shaa Allah, A small Sallah gift from Phartiemarhk to you guys, Luv you [truncated by WhatsApp]
💖💝BATUUL💖💝

31

By phartiemarhk

Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*

Washe gari da asuba Batuul na xaune kan darduma ta idar da sllh Anty ta shigo dakin tace mata in gari ya gama waye ta sameta a bedroom dinta, hakan kuwa akayi wajen takwas ďin safe taje tayi knocking k'ofan Aunty, sai da taji an bata izini tukunna ta shiga, Aunty na kwance kan gado ganin Batuul ya sata mik'ewa dan dama ba bacci takeyi ba, tun daren jiya bayan sun gama magana da baba ta kasa samun nutsuwa, daga gaban dressing mirror Batuul ta tsaya ta kasa k'arasawa ganin yanayin Aunty kamar wani abun na damunta, alama tayi mata da ta zauna tukunna ta samu waje daga k'asa ta zauna tareda gaisheta, magana Aunty ta fara yi mata kamar haka "Batuul ke kika cewa Baba kina son aure" da sauri Batuul ta ďago kanta jin abunda Aunty ta faďa gabanta na faduwa, lkci daya idonta ya cicciko da hawaye ta ma rasa mey zata cewa Aunty, sai da Aunty ta sake magana tace tambayanki nake Batuul kika min shiru", hawayen dake idonta har ya fara gangarowa ta shiga girgiza kai cikin sheshek'a tace "Aunty wlhy Allah ban tab'a irin maganan da Baba ba, ni bansan wa ya faďa mishi ba, ni da nake son inyi karatu", taci gaba da goge hawayen dake kwaranya a idonta, da tausayi Aunty ta dubeta dan dama tasan babu yadda za ayi Batuul tace tana son aure, dama so take ta ga ko Batuul ďin na da ra'ayin aure sai ayi mata amma ba da mai mata ba, ae kam sam baza ta yadda da wannan batun ba, baxata yrda a cutar mata 'ya ba, Aunty ta sauke ajiyar xuciya tace "rantsuwan kuma na meye,ni bance kimin kuka ba, tambayanki kawai nayi, tashi kije kici gaba da abinda kike yi Allah shi miki albarka," kasa mik'ewa Batuul tayi daga zaunen da take sai da Aunty ta sake ce mata "Tashi kije shikenan", hak'uri ta shiga bawa Aunty tana kwalla tace "dan Allah kiyi hkuri Anty amma ni bn ce ina son aure ba" tausayinta Aunty taji tace ta tashi ba komai, in ta shirya tafiya school ta sameta tukunna, da kyar ta samu ta tashi ta fita daga ďakin dan har kanta ya fara sarawa.



Zaune yake a garden din gidan da yamma misalin biyar da wani abu yana kallon tsuntsayen dake ta shawagi abunsu a sama, dan yanxu bashida aiki sai na xama da tunani, wayarsa ne ya soma ringing, ya dauki wayar ganin mai k'iransa yasashi recieving da sauri cike da Mamakin kiran, daga daya bangaren Ammah tace "Ina neman ka ynxu" d'aga hka ta katse wayar, mikewa yyi da sauri ya nufi cikin gidan duk da bae san kiran da take masa ba amma ya ji ddin kiran Mahaifiyar tasa, har ya manta rabon da su yi magana ta waya da ita, bedroom dinta ya nufa da sallama ya tura kofar yaga bata ciki, dai dai nn farida ta fito daga dakinta ya juya yana kallonta yace "Ammah fa?" Tace "Tana bangaren Abui ae," a hnkli ya rufo kofar ya nufi bangaren Abui, sae dae duk jikinsa yyi sanyi ya rasa dalili, da sallama ya shiga falon kansa a k'asa ya xauna kan lallausan carpet din dake malale tsakiyar falon ya gaida iyayen nasa, Abui ne ya amsa, daga hka ya sunkuyar da kai yana jiran jin kiran da iyayen nasa suka masa, Ammah ce ta fara magana kamar hka "Aliyu kana jina koh" d'ago kai yyi yana kallonta sanin a serious issues take kiran sunansa kan tsaye, yace "Ina ji Ammah" in a serious tone tace "Aliyu a gskya mu kam bamu ga amfanin auren nn naka da kayi ba, Sam bashi da amfani, mun tilasta ka kayi aure ne don mu samu kwanciyar hankali kai ma hka, sae dae we were mistaken don tun da kayi auren nn hankalinmu ke tashe, baka yi sa'ar mata ba Abuu, da mun san abinda xae je ya dawo knn da bamu yi Na'am da yarinyar ba, kwata kwata bata san darajan iyayenka ba sae nata, don hka ni da mahaifinka mun yanke shawarar kara maka aure" d'ago kai yyi cikin rikicewa yace "Aure kuma Ammah?" Ta hade rae tace "Kwarae kuwa aure" marairaice wa yyi yace "Ammah ko shekara guda knn fa....." Tsawa ta daka masa tace "Ko ka wata guda ne, meye amfanin yarinyar da take neman rabaka da iyayenka da 'yan uwanka, kai har kana da bakin yi mana musu Aliyu, toh wllh ka guji bacin raina, 'yar mutunci da tasan darajanmu da xa kuma ta dinga nuna maka muhimmancin 'yan uwanka xa mu aura maka," ya share xufar da ke keto masa kmr xae yi kuka yace "Ammah wllh ina son Ajiddeh kuma ni bni da ra'ayin hada mata biyu, ku tausaya...." Wani tsawan da ya fi na da Ammah ta daka masa cikin fushi tace "Shknn Abuu, ni xan hakura in bar ma Ajiddeh kai sae ka maida ta uwarka, d'a na Aliyu da na sani a da baya min musu, jikinsa na rawa yake daukar duk abinda nace, ni kam wnn ba Aliyu na bne nasani...." Hawaye ne ke sakko mata sosae, jikinsa yyi sanyi ya dawo kusa da ita ya rike kafafuwanta cikin rawar murya yace "Haba Ammah, ni din bnxa xa ki xubar ma hawayenki, bani da amfani in har xa ki dinga xubar min da hawaye, kiyi hkuri ki rufa min asiri amma, hawayen ki masifa ne a gare ni, wllh na amince da kome kika ce, Aliyun ki ne ni ba a canxa maki ba wllh" duk ya rikice ba kadan ba yana rike da kafarta, kallonsu kawae Abui yake bae ce komae ba, Ammah taji ddin hkn ta shafa kansa cikin sanyin murya tace "Allah maka albarka" dagowa yyi da sauri ya daura hannunsa kan cinyarta yace "Nagode Ammah na" bata kuma cewa komae ba ya koma ya xauna ya langwabar da kai yana kallonta yace "To wace matar kika xaba min Ammah" kallonsa tayi bbu yabo bbu fallasa tace "Ba wata bace facce 'yar uwarka Bitti" xaro ido yyi ya koma baya da sauri yace "Batuul???" Ta hade rae tace "ita fa" innalillahi wa inna ilaihi raji'un, abinda ya dinga maimaitawa knn yana kallon Ammah da ke ta hararansa tana karkada kafa.

A bangaren Ajiddeh kuwa tun ranan da sukayi waya bata sake k'iranshi ba saima ďagawa su Mummy hankali da tayi akan abinda ke shirin faruwa tsakaninta da Abutturab, su Mummy ganin abin na nema zama matsala ne dan ta dena kula kowa ita fa sai ansan yadda za ayi mijinta ya zama kamar yadda yake a da, Jainaba ce ta kawo shawaran su ziyarci sabon bokan da taji ance yana aiki kamar da bakin wuk'a amma fa ba a k'asar nan yake ba, yana can Tchad, a ranan sukayi shiri akan gobe zasu tafi, da daddare Mummy da kanta take sanarwa Daddy akan zasuyi tafiya gobe, da ya tambayeta inda zasu tace mishi ai kakar su Ajiddeh zasuje gaidawa sabida tun kamin aure rabonta da ita kuma ba lafiya bane da ita, da mamaki yake tambayan Mum akan dama Ajiddeh bata koma ba tun bayan bikin dan shi sam baisan ma tana gida ba, Mummy ce tace mishi "ehhh wai mijinta take jira akwai abinda yakeyi a nan ďin", cewa yayi "kuna dawowa ta koma wajenshi, in ta zauna a nan ďin amfanin mey take mana, taje can gidan nashi su zauna idan kun dawo", toh kawai Mummy tace ,cheque yayi musu signing yace su rubuta amount ďin da zasu buk'ata tunda ziyara zasu, basu sanar dashi ma cewa da mota za a yi tafiyar ba, washegari k'arfe shida suka ďau hanyan Maiduguri daga nan zasu shiga Tchad ta can, tafiya sosai sukayi bayan sun isa Tchad kamin su isa k'auyen da bokan yake, da k'yar suka samu sukaje inda yake, wata bukka ce da gani ta daďe ko ina duhu sai wani đan haske dake fitowa daga windon bukkar, da zuwansu yace musu yasan abinda ke tafe dasu duk ya sai dai akwai abinda har yanxu ya kasa ganowa, shima baisan meye bane amma abin babba ne, kuma nan gaba yake shirin faruwa, har saida yace musu duk laifinsu ne da tun farko kamin bikin sun nemeshi da duk matsalan babu, hankalinsu ne ya k'ara tashi gaba ďayansu babu ma irin Ajiddeh suka shiga bashi hak'uri kamar sun mishi laifi, zata iya yin komai in dai akan Abutturab ne, gaban bokan ta sake matsawa tace "naji ranka shi daďe, amma tunda al'amarin bai faruba yanxu, ni ayi min abinda zai manta da kowa kuma bazai sake waiwayen gida ba, sannan daga baya sai mu san yadda zamu b'ullowa abun dake shirin faruwan", kai ya kaďa bayan ya gama jin batunta yace " hakan ma yayi", tashi yayi ya shiga wani ďaki daga cikin bukkar ya fito rik'e da wani k'warya, sai da ya zauna ya zauna ya mik'o mata wani kuttu yace "ga wannan nan zaki samu tsohuwar bak'ar tsamiya, da hannunki zaki jik'ata, sai ki ajiyeshi a waje mai danshi da sanyi, kada ki bari rana ya tab'ashi, shi kuma wannan", ya mik'o mata wata bushashiyar fata yace "garin maganine a ciki, tunda dama yace kiyi tafiyarki toh aikin zai zo ma da sauk'i, wannan garin a k'ofar gidanki zaki barbaďa, sai kuma wajen kwanciyanshi nanma zaki barbaďa, Kinga yadda wannan tsamiyar keda tsami da duhu, haka zai rik'a ji duk lokacin da ya tuna gida, sanyin nan kuma da kika ajiye a wajan, duk lokacin da ya ganki ko ya tuna dake haka zai rik'a ji, g'arin nan kuma da zaki barbaďa, yadda iska zai kwasa ya tafi dashi wajen ya shafu haka zai shafe babin gidansu a k'wak'walwarshi", duk maganan har suka gama da yarensu sukeyi, wani irin murna Ajiddeh takeji har cikin ranta shikenan zata samu yadda takeso, kuďi masu yawa suka zube mishi tareda mishi alk'awarin dawowa bayan kwana biyu, suna fita Ajiddeh ta dubi su Mummy ta ce "Mum, gobe zan koma, inada Visa ticket kawai zan siya shima online zanyi dan bansan lokacin da zai koma ďin ba, gara inje tun wuri in gama abunda zanyi", Mummy ce tace "toh shikenan, duk yadda akayi sai ki faďa mana a waya, Allah dai ya taimakemu ya bamu sa'a, a daren suka ďau hanyan birnin Tchad, murna fal cikin Ajiddeh.

Batuul na gama shirin makaranta tazo yiwa Aunty sallama zata wuce, bayan ta gaidata ne tace "Aunty yau in na tashi daga school zanje gidansu Farida", dagowa Anty ta da sauri tana kallonta tace, "mey zakije yi a gidan?", da mamaki Batuul ta dubi Aunty dan bata tab'a hanata zuwa ba, asalima ita ke sata zuwa ko bata son zuwa, cewa tayi "wajen Farida zanje, nace mata zanzo jiya banje ba shine zani yau" a takaice Anty tace "No ki bar zuwan , some other time kya je, ki dawo gida in kin gama lectures kawae", jiki a sanyaye Batuul tace "toh Aunty na tafi", "Allah ya dawo dake lafiya", a hka ta fita dakin, tana fita k'iran Abdallah ya shigo wayanta, sai da ya kusa katsewa tukunna ta ďauka, a hankali tace "Hello", wani k'ayataccen murmushi ya saki yace "Habibty hope ba tada ki nayi ba, naji voice ďinki so low", ce mishi tayi "No am okay, yanxu ma school zanshiga, tun ďazu na tashi", yace "okay okay durlyn, i will meet you there cux nayi missing cute face ďinki", ce mishi tayi "toh, sai kazo", ta shige mota ta wuce school.
💖💝BATUUL💖💝






32






By phartiemarhk






Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*





Gaba ďaya ji yayi kanshi yayi mishi nauyi, idonshi ya canja kala ya zama ja har wani gumi ne ya tsatsafo mishi a goshinshi, ya girgiza kai yana ci shiga gaba da ambaton innalillahi wa inna illaihir raji'un, sai da yaji bugun zuciyanshi ya ďan daidaita tukunna ka kalli Ammah dake hararansa har lkcn ya marairaice murya yace "Ammah ki min rai ki aura min wata daban amma ba Batuul ba, yarinya ce fa karama, kuma kila ma baxa ta rasa saurayin da take so.....," wani irin kallo Ammah ke mishi, hkn yasa ya sunkuyar da kai ya kasa k'arasa maganar, Ammah tace "ko ma dae jaririya ce, ita din muka yi niyyan hada ka da, don nasan xata fi mana babban macen da ka aura, in kuma nuna mana xaka yi ba mu isa ba bismillah, ae dama ka saba daga sanda kayi aure" Runtse ido yyi a hnkli yace "Wane ni Ammah, in'sha Allah yanda ku ka ce hkn xa ayi." jin ya faďi haka yasa Ammah sakin fuska ta juya ta kalli Abui tace "dama nasan ďana zaimin biyayya, tashi kaje, Allah shi maka albarka, bbu 6ata lkci xa ayi komae don ka koma bakin aikin ka", shafa kanshi tayi tace " Allah maka albarka" da k'yar ya samu ya mik'e daga tsugunen da yake, yayi musu sallama ya fita daga falon, abubuwa ne suka mishi yawa a kanshi, shi ta ina zai fara sanarda Ajiddeh ma aure iyayensa xa su masa, kuma ma matar ba wata bace illa Batuul, yarinyar da bata wuce sha takwas ba tsabar a ja masa raini, me zaiyi da Batuul yarinyar cikinsa? shi if he can clearly remember ma ai Massa ke sonta tun kamin ya bar gari, tunawa da yayi da Massa ne ya sashi saurin ciro wayarshi daga cikin aljihu ya lalubo number shi Massan, dialing biyu ya ďaga, "dama ana jinka a gari", abunda Massa ya fara faďa kenan, share tambayar da Massa ke mishi yayi yace "Kana inane?, inaso mu haďu", ya tsaya jin mey Massan zaice mishi, cewa yayi na fita yanxu bana gida but i will b back in an hour", yace "Aii then, zanje gida yanxu before ka dawo zan shiga in gaida Yaa Mera, sai ka dawo ďin, i need to discuss some issue with you", da haka suka katse wayan, suna gamawa ya murďa k'ofan ďakinshi ya shiga ya ďauko key ďin mota ya fito waje, direct hanyan gidansu Massa ya ďauka, cikin y'an minutes ya isa gidan yayi parking bayan an buďe mishi gate ya shiga, Side ďin Yaa Mera yayi, tayi mamakin ganinshi, dan rabonshi da gidan tun aurenshi da Ajiddeh da yazo yi mata sallama, mamaki shimfiďe fuskanta tace "Wata sabon gani Babana kaine a gidan nan yau, ashe ka shigo gari", k'arasowa yayi gabanta ya zauna yace " *Yaa Nda dubdo, aaah u' bèlan amma tusen gèi*, "ina wuni Yaa, ehhh na shigo amma banma daďe ba", ya k'arashe maganan da murmushi a fuskanshi, hira sukayi sosai da Yaa har tana ce mishi matarshi dai ba 'a ganinta, har sun manta kamanninta,suna nan zaune Massa ya shigo da sallama, tun daga can ya tsaya k'are ma Abutturab dake gaban Yaa Mera kallo, ba makawa Abu ne sai dai ya ďan rame, ko meye dalili oho yaci gaba da shigowa abunshi cikin ďakin, hannu ya mik'awa Abutturab tareda cewa "Man an dena ganinka, rabona dakai fa tunda naje wajenka kamin kazo gida, that is two months after your wedding, i tot baza ka shigo bama sai aure na ai", Yaa Mera ce tace "Abunda na gama faďa mishi kenan, nace gashi matar bata haihu ba bare mu muje can suna tunda su sunqi su zo gunmu", sauk'ar da kanshi yayi k'asa dan shima abin nan da yayi na damunshi, gashi nan har yana son zame mishi matsala, Massa ne yasa dariya yace "Kaji ko, ashe su Yaa zaman jiran jikansu suke, sai kayi k'ok'ari ku samo musu kai da Ajiddeh, kaga sai suji daďin bin naku can garinku mai daďi da baku son bari", wani kallo ya sakarwa Massa da ya sashi k'ara yin dariya yace "toh ba gaskiya bane", mik'ewa Yaa Mera tayi ta shige daga ciki su kuma suka wuce chamber ďin Massa, suna shiga ďakin ya zauna a ďaya daga cikin kujerun ďakin tareda mik'e k'afafuwanshi, Massa ya dubeshi yana buďe fridge zai ďauko ruwa yace "wai gajiya kayi ne haka na ganka so slow, ko kuma duk cikin canjawan da kayi ne", wani irin glare ya wurgawa Massa ya tashi daga kwancen da yake ya zauna, k'arasowa Kujeran Massan yayi shima ya zauna tareda mik'awa Abutturab ruwa, karb'a yayi bayan yasha ya rufe ya ajiye bottle ďin daga gefenshi ya fara msgana kamar haka "Musty, kwanankin baya lokacin biki na kamar naga you showed interest akan yarinyar nan, har yanxu kuna tare ne?", yayi tambayar yana kallonshi, gaba ďaya kan Massa ya ďaure dan shi baisan ma wace yarinyar yake tambaya ba, cewa yayi "wacce yarinyar wai, dan ni ban gane wacce kake nufi ba", ce mishi yayi yarinyar nan k'arama mana, yarinyar Aunty", tsaki Massa yaja yace "kaji ka da wani zance, Aunty ďaya muke da mai k'aramar yarinya, specify inji", shiru yayi ya kasa furta sunan nata, da k'yar ya iya buďe bakinshi yace "Batuul", "ohhh dama wai Batuul kake nufi kake ta wannan abin, wait!, dont tell me bakasan zancen aurena ba", da mamaki Abutturab ya dubeshi yace "kayi aurene?", kai ya girgiza yace "No banyi ba but nan da two weeks za ayi", kan Abutturab ne ya ďaure, yaushe Massa zaiyi aure har bai sani ba, kuma wa zai aura inba Batuul ba, yes ba Batuul bace tunda har su Ammah sukace ya aureta, da sauri ya juya ya dubi Massan da ya zuba mishi ido ganin yadda yake abu kamar ba shi ba yace "Tell me wacece zaka aura inba Batuul ba, kuma ya akayi haka bayan at that time kace min sonta kakeyi", murmushi Massa yayi yace "Toh kai duk mey ya kawo zancen nan, kai da kace mey zanyi da yarinyar tayi k'arama shiyasa na rabu da ita", kai Abutturab ya girgiza yace "c'mon jokes apart, ba wasa nake ba, mesa ka rabu da ita kuma wa zaka aura?", Massa ne yace "Rahama mana zan aura, y'ar Sultan, Batuul tun lokacin ta nuna bata sona shiyasa ma ban kai abun wajensu Ammah ba, but naso in aureta, she will make a good wi.....", wani tsaki Abutturab yaja yace "hold it, okay?", gaba ďaya ranshi ya b'ace, sai da ya ďan nutsu tukunna yace "Mustapha am in a problem, kuma babu mai iya fiddani sai kai, kasan auren nan da nayi shekara kenan, kuma su Ammah suna ganin shine ya hanani zuwa inda suke, and ni inason Ajiddeh, like banima da ra'ayin mata biyu, i cant cope, toh ďazu su Ammah suka tareni da zancen sai na k'ara aure, da nace suyi hak'uri, amma ganin ransu ya b'aci yasa nace na yadda, toh shine da na tambayesu wa suke so in aura, dan ni i have no one in mind shine sukace min wai Batuul", yadda ya k'ira sunan nata kamar ba daga bakinshi sunan ya fito ba yayi maza ya ďauke idonshi daga kan Massa , dariya Massa yasa harda kyakyatawa ya kwanta akan kujeran, sai da ya gaji dan kanshi ya gama dariyan tukunna ya mik'e ya zauna, Abutturab ko kallonshi baiyi ba har ya gama dariyanshi, sai da yayi shiru tukunna yace mishi "ka maidani

1 Comments On BATUUL
avatar
hafsat-9-3

12 months ago

Reply

Nice book

Please Login or Register in order to submit comment