Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

breakfast is ready" kallonta kawai yayi ta fice Batuul na murmurshi, suna gama shirayawa ya rik'ota hannunta suka fito, tun tana qi har ta hakura, suna sauk'a downstairs ta fakaici idonshi ta warce hannunta tayi gaba abinta, kowa na kan dinning su biyune basa nan, Ammah da Abui da Sadiq ta gaida sukayi mata ya k'arfin jiki, a kunyace ta amsa da Alhamdulillah snn ya ja mata kujera ta zauna sukayi breakfast tare





Da yamma suna zaune itada Farida a main parlour, kamar daga sama ta jiyo muryar su Ahmad, rabonta da jin muryarsu watanni kenan in ba a waya ba, da wani irin murna ta tashi t isa inda take jiyo muryar, da gudu ta isa ta rungumeshi hawaye na k'ok'arin zubowa idonta ganin duka kannenta a gabanta, d'aya bayan y'ata ta dinga rungumarsu snn ta karb'i Aabid dake hannun Sayyid tayi pecking d'inshi, sam ya manta da ita sai kallonta yake kamar yaga sabon mutum, jiki a sanyaye ta kallesu tace "Aunty fa?, batace zata zo bako?", Ahmad ya dubeta yace "ita tace muxo, zasu zo tareda Baba su dubaki wai", kai kawai ta gyad'a tana k'ok'arin maida hawayenta da bataso su gani tace "Ku shiga ku zauna, duk kunyi wani tsayi, Sayyid gashin meye haka ka tara kanka kamr wani black cotton?", dariya kawai ya mata ya sunkuyar da kanshi suka karaso ciki, Farida ta d'auki Hafiz tace "muje ka rakani sweet boy", basu jima ba ta sauk'o tareda Ammah, Ammah tace "Ashe manya bak'i ke tafe bamu sani ba, ya kuka baro gida, Ya Auntyn Ku?", Duk suka gaisheta snn suka amsa mata da tana lafiya, nan tasa aka cika musu gabansu da kayan abinci iri iri, suna nan zaune Abu da Sadiq suka shigo a tare, tausayinta yaji ganin yanda take farin ciki ganin yaran, bama yadda take yiwa Aabid wasa ba, ya k'araso wajenta batareda tasan ya shigo ba ya sunkuya daidai kunnenta yace "Hey am happy to see you happy", a d'an tsorace ta juyo ta dubeshi tayi mirmushi tace "Thank you", ya girgiza mata kai yace "You look cute holding the baby, can't wait to see you babysitting my princess", wara ido tayi tana kallon koda wanda yaji, ganin babu mai kallonsu ta sauk'e ajiyar Zuciya ta d'an bugeshi cikin wasa, dariya yayi ya mik'e ya anshi Aabid hannunta yana cakud'a mishi gashi yace "Hey Champ", dariya Aabid yayi mishi cute dimples d'inshi na appearing, da maamki ta bishi da kallo, gaba d'aya ba shine Abutturab d'in da ta sani ba months back, murmushi kawai tayi tana jin wani farin ciki a ranta da takeson ya d'ore a haka,d'aya bayan yaran suka gaisheshi yana amsawa, ya kalllesu yace "Maybe we should go out for ice cream ko, Movie or anything? am offering the treat, who wants to join?", Yusra da kamar jira take tace "Ni zanje, muje Blue cabana, they got the best ice cream and Chapman, yafi na ko ina and their Kebab, omg its so yummy, kasan ko Aunty sai ince mata akaini weekends wai saitace saidai a siyomin, am happy you are taking me.....", bata k'arsa ba Khalil ya sakar mata da wani harara, shiru tayi zata koma ta zauna ganin an harareta Abutturab da tunda ta fara magana yake murmushi ya kamo hannunta yace "Then you will get us all in munje ko" kai ta kad'a mishi, Batuul da mamaki take kallonta ganin yanda yarinyar ta k'ara tsayi, Abu yayi dariya yace ku fad'awa Ammah we are going tunda yamma tayi, Farida ta mik'e tareda Batuul zasuje su shirya, Abu yace "Farida ki sauk'o mata da Hijab in kinje sama", kallonshi tayi idonta yayi rau rau har hawaye ya ciko jin yace a kawo mata Hijab ta dawo kusa dashi a hankali tace "Hijab kuma?, dashi zanje?", ya kad'a kai yana wasa da Aabid ba tareda ya kalleta ba yace "Yeah, anything?", matsawa tayi daga kusa dashi ta zumb'uro baki ta zauna kan sofa, Farida ta sauk'o tareda Amamh riqeda Hijab d'in Batuul ita kuma ta d'aura veil kan cape top da skirt d'in dake jikinta, ta mik'awa Batuul hijab din, duk suka mik'e Ammah tayi musu Allah ya kiyaye sai sun dawo, Batuul ce kad'ai bata tashi ba tana fushin da babu wanda ya lura da ita, Ammah ce tace "Bitti tashi ki bisu kema ki warware jikinki kinji, zaman gidan ai babu dad'i, tashi kije", batason yiwa Ammah musu, mike we a tayi ta zura Hijab d'inta ta fita, koda taje k'in shiga motar Abu tayi dukda taga ya bud'e mata front seat, zagayawa tayi ta shiga ta Sadiq tayi zamanta batareda ta kalleshi ba, baima lura da Fishin da takeyi ba, bayan kowa ya shiga yaja mota suka fita tasu Sadiq ta biyosu a baya.
[11/22, 11:21 PM] ‪+234 803 698 6494‬: 💖💝BATUUL💖💝



90



By phartiemarhk



Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*



      Har suka Isa Blue Cabana duk surutun da akeyi a motar batace komai ba, Sadiq ma duk tsokanarshi haka ya gaji ya kyaleta, bayan anyi parking da kamar bazata fito ba ganin kowa ya fito itama ta fito sai b'ata fuska takeyi, Abu na gama parking shima bayan yaran sun sauk'a ya rufe motar yacewa Farida ta karb'i Aabid hannun yaran nan ta rik'eshi snn ya zagaya ta wajen Side d'in da Batuul take, cikin wasa ya harareta ya kamo hannunta yace "Keh wa yace miki ana shiga motar Sadiq, he drives roughly, bare keda kike carrying baby na", ya d'aura hannunshi kan cikinta, da sauri ta wara ido ta kalleshi jin hannunshi a jikinta tayi maza ta ture hannun tana kalle kallen ko wani ya gansu, ko a jikinshi saima tsareta da yayi da ido, kauda kanta tayi ta matsa baya, yaci gaba "Kina ganin irin gudun da ya riqa shararawa kamar mai shirin barin garin, plss kar ki sake shiga driving d'inshi, I will be there for you always, In sha Allah kinji, Let's get going", d'an k'aramin bakinta ta tsuke tareda murgud'ashi tana janye hannunta, daidai kan idonshi, ido ya lumshe ya bud'e su kanta a ranshi yace "Damn, komai tayi kyau yake mata koda kukane, shi bai tab'a ganin wanda kuka keyiwa kyau ba kamar ita, badan bayason ganin kukanta ba yana damunshi yana sashi jin wani iri da kullum sai tayi mishi ya gani sbd in tanayi face d'inta na zama cute, ainihinta yake gani batareda k'arin komai ba sai lips d'inta da suke sake komawa pink, matsowa ya dad'a yi gabanta yace "Hey mey ke damunki", yasan wani abin ne ya sameta wannan attitude d'in da ta fara displaying, kamar jira takeyi ya tambayeta hawaye ya fara bin kuncinta, wani abin yaji har cikin ranshi, wlhy ko kad'an baya son ganin hawayenta, "Ya salam" ya furta snn da sauri ya jawota ya rungumeta sosai a jikinshi, duk da hijabin dake jikinta hakan bai hanashi jiyo d'uminta dake soothing d'inshi ba, Su Sadiq suka k'araso ganin basu taho ba, "Bro, for real?, a nan d'inma?", ya fad'a muryarshi cikeda tsokana, wani kallo Abu ya jefa mishi da yasashi fashewa da dariya, sai a lokacin ya lura da Batuul dake hawaye yace "Subhanallah, mey ya sameta haka?", ya juya yana tambayan su Farida da su Ahmad da suka tsaya cirko cirko suna kallonsu, kafad'a Farida ta d'aga mishi alamun she has no idea, muryan Abu yaji yace "You guys should get going, make sure kowa ya sami abinda yakeso, anything okay?", ya mik'o mishi ATM card d'inshi da ya ciro cikin aljihu yace "We will join you shortly", Sadiq da damuwa duk ya cikashi yace "Yeah okay....but then is she fine?, like babu matsala", Kai Abu ya kad'a mishi yace "Bakomai, Farida ki kula da yaran nan, let them have all they want", Farida ta kad'a kai ta kama hannunsu suka fara tafiya, suna tafiya ya jasu suka jingina jikin mota a hankali yake patting bayanta yace "Hayat meye kuma?, what is it now, kukanki yafi komai tada min hankali, you should please stop it and tell me mey ya sameki, mey kikeso?", ajiyar zuciya takeyi har lokacin, sassauta rik'on yayi snn ya d'ago kanta yana kallon fuskarta da ta b'aci duk da hawaye, sauk'e idonta tayi k'asa bata bari sun had'a ido ba, yasa hannu ya share mata hawayen yayi cupping fuskarta da duka hannayenshi yace "Okay now tell me, mey kikeso", kamar baza tayi magana ba a hankali tace "Ko ba kaine ba", jin tace shine ya wara ido ya kalli fuskanta da kyau yace "Huh?, Really?, Ni na saki kukan?, Me nayi toh, tell me please , I will rectify it right away kinji", ya k'arashe maganan kamar zaiyi kukan shima jin shi ya sata kuka, cikeda shagwab'a kamar zata sa wani sabon kukan tace "Ko ba kai bane ba kace sai in saka hijab bayan zafi akeyi kuma fa its an evening outing sai kowa ya rik'a ganina kamar matar aure fa", sosai magananta ya bashi dariya da mamaki, bai san shirmen nata har ya kai haka ba, d'ago kanta yayi yana kallonta tareda sa hannu yana zagaye shape d'in da Hijabin yace "Fatima Hijab din ne baki so?", bata d'ago ta kalleshi ba tace "Ni ai bance banaso ba, kawai fa Kaine, kowa sai yace ni matar aure ce", ta sake fashewa da wani kukan, rungumeta ya sakeyi yanzu kam dariya yayi da kyau yace "And that's exactly dalilin da yasa nace ki saka Hijab, banason ana kallemin keh, bazan saurarawa duk wanda yayi miki wani irin kallo ba, you are married Fatima, married to me, you are just mine", ajiyar Zuciya ta sauk'e jin maganunshi tace "Ba toh zan iya saka Abaya ba or any gown", yayi murmushi yace "Yeah hakane but then, hijab zaifi rufemin keh all, nafison ganin ki so modest da kowa na ganinki yasan yes you are married, don't you know immodest dressing shike attracting filth, shike janyo duk wata musiba ta yanzu da ake facing tsakanin opposite gender", dogon numfashi taja jin abinda yace kuma tasan gaskiya ya fad'i, a hankali ta janye daga jikinshi tace "toh shikenan, am sorry", kamota yayi yayi pecking goshinta yace "I love you", wani irin rumbles taji a cikinta kamar jiya jin ya sake maimaita mata I love you, yace "Let's help you ki cire Hijabinki sai muyi zamanmu cikin mota tunda kinga zafi kikeji, I will order duk abinda kike so here", ya fad'a yana ciro wayarsa daga aljihu, da sauri ta riqe mishi hannu ta girgiza kai tace "No am fine, ai na dena jin zafin", murmushi yayi yace "Sure?", ta kad'a mishi kai tace "Yeah", da haka ya riqe hannunta suka isa wajen dasu Sadiq suke, lokacin har kowa yayi ordering abinda yakeso,  ido suka zuba musu su dukan suna jira suji mey ya sameta , kujera Abu Abu ya ja mata ta zauna snn shima ya zauna, raurau tayi da ido ganin duk ita suke kallo ta kalli Abu, murmushi yayi ya kallesu ya d'aga musu gira yace "She is fine, babu abinda ke damunta, y'all should relax", explanation d'in abinda ya sata kuka suke jira yayi musu amma ganin kamar bazai yi ba sukayi shiru kowa yaci gaba da abinda yakeyi, waiter ya k'ira ya bashi order abinda za a kawo mishi snn ya ce Batuul ta fad'i abinda take so, tace "Chicken wings in marinated sauce with plenty garlic, Large Lasagne, cream in chicken soup with emm french bread... ", tsayawa kowa yayi ya zuba mata ido jin taqi dena ordering, a hankali Farida tasa hannu ta d'an tab'a ta tace "kee ina zaki zuba duka wannan abinda kike ordering, mey zakiyi dasu?, k'asa k'asa tayi maganar, murgud'a mata baki tayi tace "Keh kam ina ruwanki, inma zubdawa zanyi", ta juya taci gaba da bashi order "With spicy lamb kebab, sour cream sauce, butter scotch ice cream with some toppings, just any and strawberry shake", Abu kam danna wayarsa yakeyi har saida ta gama ya kalleta yace shikenan?, kai ta kad'a mishi yace "Okay you can go",  ganin Expressions dake shimfid'e fuskarsu ta d'aga musu kafad'a tace "Wai meye nayine, nifa zanci kayana",  Sadiq ya saka wani irin dariya da  yasa Abu ya d'ago yana neman mey yakewa dariya, cikin dariyar yace "Do you eat this much ko kuma dai da wani abun, am not getting this seriously", ya sake saka dariya, Farida ma tasa dariya, wara ido tayi snn tayi raurau dashi ta kalli Abu kamar  zatayi kuka, kujerarshi ya ya matsar kusa da nata with stern voice yace "Saaadiqq", snn ya watsawa Farida dake k'ok'arin had'iye dariyarta harara, "don't mind them, shiyasa kikaga basuda lafiya, Eat as much as you want, babu ruwanki dasu", ta tsuke baki tace "Bafa dayawa ma nayi ordering ba, kad'an ne fa dan inajin kwad'ayinsu ne duka", ya jawota jikinshi yace "Shhh don't worry, ya kwantar da kanta kan kafad'arshi, suna zaune har aka kawo mata duk abinda tayi ordering




       Tunda Ajiddeh ta shiga d'aki bata fito ba sai washegari da safe, tasha kuka har ta godewa Allah, da yamman ranan ta fito daga d'akin da ta kwanta ta taga masu aiki sai kai kawo suke wani d'aki, k'arasawa tayi taga waye cikin d'akin, ta manta da sam Mummy tace mata akwai matar da Daddy ya kawo gidan, wata mata ta gani da bandage d'aure jikinta, sai kuma a kanta, sosai ta tsaya tana kallon matar snn ta tab'e baki ta juya ta koma d'akin da ta kwana ciki ta ci gaba da zamanta, ko sau d'aya Mum bata lek'o ta ganta ba sai masu aiki da take tura mata, wayarta da Mum ta bada a kawo mata ta d'auk'a ajiye nan kan gadon, samun kanta tayi da logging wajen calls da neman sunanshi, a hankali ta shafa sunan hawaye na zubowa idonta, tana son Aliyu amma abinda tayi mishi bata tunanin zai yafe mata shi, dialling number tayi, tun kamin yayi ringing tayi maza ta katse k'irar, gallery ta shiga tana kallon hotunansu da sukayi a tare, tana jin inama ya saurareta ko sau d'aya ya bata chance d'in nuna mishi she has changed for good, koda bazai sota ba ita zata soshi, tana cikin tunanin nan ta jiyo tafiyar Dad, sai a lokacin gabanta ya shiga fad'uwa, batasan mey zata ce mishi ya dawo da ita, tashi tai zata shige toilet ta b'oye daidai nan ya hangota, da mamaki k'arara a fuskarshi yake kallonta da ta k'ame waje d'aya hannunta rik'e da knob d'in k'ofar, da mamaki a muryarshi yace "Hauwa, yaushe kika dawo gida?", a hankali ta shiga takowa gabanshi hawayen da take k'ok'arin maidawa na zubowa, a hankali ta k'araso tace "Daddy ina wuni", kallonta kawai yakeyi da ganin yanayinta snn mey take nema side d'in nan, "lafiya", abinda yace kenan snn yace "Tun yaushe kike gida haka, tareda Aliyun kuka dawo?", kai ta shiga girgizawa ta fashe da kuka mai tsanani da k'yar ya lallasheta tayi shiru snn ta da kyar tace, "jiya muka zo shine banajin dad'i nazo gida", kallonta kawai Dad keyi yasan there is more to wannan maganan ba abinda ya faru kenan ba, yace "Shine da shirme da bakida lafiya zaki taho gida, mu lafiyan zamu baki anan gidan d'in kome?", jiki a sanyaye ta rik'o hannun Dad tace "Dad kuma ina missing d'inku shiyasa fa nazo, kayi hak'uri zan koma gobe", tanayi hawaye na ci gaba da zubowa, yace "Its okay, bar kukan, but next time kar ki sake wannan wautar, bakida inda yafi gidan mijinki daraja, yaron kirki mai mutunci ma da yasan darajar mutane, he calls me every two weeks and kowane Sallah da previous azumi in zai bada Sadaka, sai ya k'aramin da wanda zan bawa mutane, he is a good son really, ki kula dashi sosai Hauwa kinji, I don't want you to be like your Sister da ta zama kamar itace k'anwarki, kiyi hak'uri kiyi zamanki gidanki, Allah ya miki albarka", wani kuka taji yaxo mata da batasan yana shirin zuwa ba ta rungume Dad, murmushi yayi ya d'agota yace "Karki damu, my prayers are always with you", ya kamo hannunta yace "I got a patient a wannan d'akin, muje ki gaisheta", suna tafiya yana bata labarin yanda accident d'in nasu ya faru, har suka k'arasa d'akin, ko da sukaje zaune suka tarar da matar da Qur'an gefenta alamar karatu ta gama yanzu, bayan sun gaisa yayi mata ya jiki yace "Ajiddeh wannan itace Kulthum, Kulthum ga d'ayar y'ar tawa sunan ta Hauwa", da murmushi matar tace "Masha Allah, Allah ya rayata, d'azu naga ta lek'o banma san itace ba", Dad yace "Toh ni zan koma inda matsala sai a nemini, Ajiddeh stay here with her for today, keep her company", kai ta kad'a ya fita daga d'akin, kallon Kulthum Ajiddeh ta tsayi, mata mai kyau da ita ko ina y'an uwanta suke, baki ta tab'e ta nemi guri ta zauna dan tunanin nata matsalar

     Koda aka kawo musu abincin, babu wanda tayiwa ci biyu, shake d'in nema tasha da d'an yawa, sudai da mamaki kawai suke kallonta, Su Yusra ne sukace sunason a kaisu XD cinema, Farida da Sadiq sukace su tashi su kaisu, Batuul dake shan shake d'inta Farida ta duba tace "You going?", d'auke kanta tayi tace "Kuje, kaina zaimin ciwo in na shiga wajen nan, harara Farida ta sakar mata tace "Kedai kyaji dashi, you and your unending problems", had'e rai tayi ta  kalli Abu snn ta kalli Farida zatayi magana Abu yace "Farida!!!, ta zumb'uro baki ta kama hannun yaran tace "Kunga kuzo mu tafi, mulki take ji dashi yau d'innan", daga haka suka k'ara gaba abunsu, Abu ya kalleta yayi murmushi yaci gaba da danna wayarsa, sau biyu tana kallonshi taga danna waya kawai yakeyi yana murmushi, yana zaune bai lura da  lokacin da ta tashi daga kujerar ta bar wajen ba, wasu mata ne suka zo suka zauna kan kujerun, da mamaki ya d'ago yana kallonsu jin wasu muryoyi daban, kallonsu ya tsaya yi yana so ya tuno inda ya sansu, they look familiar, d'ayar ce yaji tace "AAK, ashe ana ganinku a gari, tun daga makaranta shikenan kun b'uya ba a jinku, though kwanaki naje ance ka auri wannan yarinyar Ajiddeh, ya kk ya kwana biyu", sai a lokacin yayi recalling faces d'insu amma bazai ce ga sunayensu ba, kallonsu yake d'aya bayan d'aya snn yace "Excuse me Dan Allah, baku had'u da wata zaune nan kujerar ba?", tab'e baki sukayi sukace, "No we didn't meet anybody gaskiya, ya kk toh ya matar taka?", gaba d'aya hankalinshi baya kansu yace "Yeah she is fine, sorry excuse me, I need to go now", daga haka ya mik'e ya barsu nan zaune, ransu duk ya b'aci amma inda sabo sun san halinshi ne hakan, wayar Batuul ya shiga k'ira amma bata d'auka daga baya ma kasheta akayi, hankakinshi gaba d'aya ya gama tashi, su Sadiq ya k'ira yaji ko tana tare dasu sukace mishi bata zo ba, ya ma rasa ina zai fara nemanta, itakam bakin wani pond taje ta zauna tana kallon swans d'in dake cikin ruwan, sosai suke birgeta, tana daga zaune lokaci lokaci take kallon shi taga yana zaune abunshi, ita da kanta bata san haushin mey take ji ba, wani irin fad'uwa gabanta yayi lokacin da ta hango matanan nan zaune wajenshi, da sauri ta d'auke idonta daga kansu amma curiosity ya sata juyawa ta sake kallonsu, dariya taga sunayi, da sauri ta sake juyawa sbd yadda taji zuciyanta na bugawa, hawaye ne taji ya tarar mata a ido, tana ganin kiranshi tasa wayar a silent, daga baya ta kasheshi gaba d'aya, duk inda yasan zai ganta sai da ya zaga, duk abin nan da yakeyi idonta na kanshi, yana d'aga ido ya fad'a kanta, tana zaune tana kallonshi, da wani irin hazari ya k'araso wajenta tareda fizgota yana k'are mata kallo ya tabbatar if she is fine, wani irin kallo ya bita dashi yace "kinada hankali kuwa?, mey ya tadaki daga wajen da kike, are you even okay wai?, mey ke damunki, tell me now", d'auke kai tayi ta ki yadda ta had'a ido dashi sai da ya sake dad'a k'arfin rik'on yace "I will slap you right away, ina miki magana kina d'aukemin kai, what's wrong with you?", wani irin kuka tasa da yasa jikinshi yayi sanyi, d'an tsaki yaja yasa hannayenshi duka cikin gashinshi ya bajesu, d'aukarta yayi cak ya nufi hanyar mota da ita, lamo tayi jikinshi gabanta na fad'uwa, sai da ya bud'e mota ya sakata ciki snn ya kira Sadiq a waya yace "Sadiq you can take the kids home when they are done, daga nan sai a kaisu gida", bai jira mey Sadiq zaice ba ya kashe wayan
[11/22, 11:21 PM] ‪+234 803 698 6494‬: 💝BATUUL💖💝






91






By phartiemarhk






Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*




"Lukman get the key to my house, right away", daga d'aya b'angaren Lukman ya amsa da "Hokay Sir but which of the Ouses?", "Mississippi Street, you should get there right now, I will soon be there", yace "Hokay Sir Hi will do that", ya katse wayar ya ajiye, kallonta yyi har lokacin hawaye ne idonta ya bud'e baki zaiyi magana kenan suka iso bakin gate,  ya mik'owa masu gadin card d'insu ya fita daga harabar Blue cabana, kallo d'aya yayi mata ya maida hankalinshi kan tuk'in da yakeyi, hijabin jikinta taja taci gaba da goge hawayen dake zubo mata, ita da kanta ta rasa hawayen mey takeyi, attention d'in da bai bata bane ya zauna yana danna waya  ko kuma matan da ta gani suna magana dashi harda dariya ya sata b'acin rai, wani iri taji da ta tuna da matan har saida gabanta ya fad'i, batayi yunk'urin goge hawayen ba dan ba daina zubowa zasuyi ba, hannunshi taji a fuskarta yasa ya shafo hawayen yana murzasu yana kallonta, a hankali ta sauk'e idonta k'asa, zaiyi magana wayarsa ta fara ringing ya duba ganin mai k'iran yasa ya d'aga tareda cewa "Sorry badai har kun fito ba", daga d'aya b'angaren Massa ya amsa da "Yanzu haka ita na d'auko, baku dawo bane?", d'an siririn tsaki yaja yace "God man am sorry wlhy ba yanzu zamu dawo ba, I had to but am sorry", Massa dake d'aya b'angaren yace "For real?, I told you gobe zata koma Sokoto kuma dan Batuul zata, ita ta tsaya dubawa", Abu yace "I know, I understand, am having issues over here so nake inyi clarifying before getting back home, bawa Rahamar waya muyi magana da ita", Tsaki Massa yaja yace "You are a jerk kaima ka sani ko", dariya Abu yayi yace "Not better than you, d'an bata wayar nikam, da ita zanyi magana ba kai ba", cikin siririyar muryarta tace "Hello", Abu yace "Hey, am so sorry, wlhy abune ya tsaida mu nan kiyi hak'uri, next time har gida zan kawo miki ita ku gaisa kinji", ya juya ya kalli Batuul yaga har lokacin kanta a k'asa yake, a hankali Rahama tace "No fa, ba komai, there will surely be next time, Allah ya bata lafiya ya k'ara mata lafiya", wani irin sanyi yaji har cikin ranshi jin addu'ar da Rahaman tayiwa Batuul da murmushi a fuskarshi yace "Amin ya Allah, sorry once again and Thank you", murmushin tayi itama tace "Ba komai fa", yace "Yawwwa mun gode Allah ya kiyaye hanya", ta amsa da Amin snn ta mik'awa Massa wayan, Abu yace "Ita mai zuwa dubiyan da kanta ta hak'ura, ka dawo goben ka dubata", Tsaki Massa yaja yace "Kaga ni kai ta sani, zan kaita ta gaida Ammah in kuma ka dawo daga gantalin naka ka samemu, fine", Abu yayi dariya yace "kaima zaka fito  gantalin ne anytime soon, just get married", Massa yace "My regards to her, kayi mata ya jiki pls", Abu yace "Sure zataji", ajiye wayan yayi ya d'ago kanshi suka had'a ido, da sauri ta d'auke nata idon tana twitching d'an k'aramin bakinta, murmushi yayi ya kamo hannunta yana murzawa a ranshi yace "She will b the death of me", bata yi yunk'urin k'wace hannunta ba kuma batace mishi komai ba, yace "Rahama tace inyi miki ya jiki?, they wanted coming now

1 Comments On BATUUL
avatar
hafsat-9-3

12 months ago

Reply

Nice book

Please Login or Register in order to submit comment