Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuma nace musu bama gida", d'ago kanta tayi tana kallonshi tanaso ya fad'a mata wacece Rahama dan batasanta ba, yayi murmushi ya sak'e damtse hannunta yace "Mustapha's fiance", batace komai ba ido ta lumshe kawai hawayen da ta kasa riqewa na dad'a taruwa,  shima bai sake cewa komai ba amma yana riqe da hannunta d'aya yaci gaba da driving d'inshi, bakin wani baqin gate taga sun tsaya, horn yayi aka wangale musu gate d'in suka shiga  tunda suka shiga gidan take k'arewa gidan kallo , ba wani babba bane sosai, duplex ne amma yayi kyau sosai, fitowa yayi daga mota, Lukman dake tsaye jingine jikin tashi motar ya k'araso wajenshi, saida ya gaisheshi snn ya mik'a mishi key d'in, Batuul ya hango zaune cikin mota yace bari su gaisa da Madam, Abu ya girgiza kai yace "No Lukman not now okay, next time", Lukman da murmushi fuskar shi yace "Hokay Sir, Hi will leave now", daga haka ya koma motarshi ya shiga ya tafi, Abu ya zagaya ta wajenta ya kamo hannunta sukayi gidan, parlour ne mai girma sosai, sosai tsarin gidan yayi mata kyau, bai sake mata hannu ba har saida ya zauna bakin gadon bedroom d'in gidan dake sama, Wani fridge ya bud'e ya fiddo ruwa roba d'aya kamin ya dawo ya zauna daga gefenta snn yasa hannu ya juyo da ita tana fuskantarshi ya bud'e ruwan ya mik'a mata, a hankali tasa hannu ta karb'i ruwan tasha kad'an, sai kallonta yakeyi yana lumshe ido ya bud'e, Miko mishi tayi yace "Ya isheki?, ta d'aga mishi kai alamar ehhh, shima shan ruwan yayi ya ajiye gefe snn ya rik'o hannayenta duka biyun, wani irin bugawa kawai zuciyarta keyi, a hankali ta lumshe ido, kamar daga sama taji muryanshi yace "Do you need to see a therapist?", bata san lokacin da ta bud'e ido ta kalleshi ba jin abinda yace", wara ido tayi a sanyaye ta fara k'ok'arin janye hannunta ya riqe da k'arfi, rungumeta yyi yana d'an rocking d'insu yace "sorry its okay baza ki ga wani therapist in baki so,", a hankali ta d'ago kanta da wani irin smile fuskarta tace "I look mental huh?, ta goge d'an hawayen dake fuskarta, kai ya girgiza mata ya sake rungumeta yace "ko kad'an Fatima,  I just want you to be happy, banason ganinki kina wannan kukan, you barely spend 5hrs batareda kin zubda Hawaye ba, and  yana damuna, gani nakeyi kamar ban kyauta miki ba, its hurting me nima", kallonshi takeyi har yayi shiru batace komai ba, yace "Say something, bana son kallon nan, I just want you to be happy, I love you sosai Fatima", kamar yanzu ta fara jin kalmar I love you d'in bakinshi, abin nan da takeji kullum shi taji yauma, a hankali tace "Then why where you ignoring me if so d'azun?", wara mata manyan idonshi yayi yace "Dagaske?, I did that?", kau da questions d'in tayi ta sake cewa "those ladies da suka zauna suna maka magana suna dariya fa?, who were they?", sai yanzu ya lura da kishi ya sata kukan nan, shi sam ya ma manta da dasu wlhy, dariya ya fasheda da ya sake kufular da ita, rai b'ace ta tashi daga kan gadon zata bar wajen yayi sauri ya fixgota ta fad'a kanshi, idonshi yasa cikin nata da yasa tayi saurin rintse su zata mik'e, hannu yasa ya zagayeta ya matseta jikinshi har yana jiyo heartbeat d'inta,  cikin wata iriyar murya tace "Nikam let go of me, ba dariya kayi min ba", dariyan ya sakeyi yace "ashe kina kishina tinda har kikayi kuka dan kin ganni da wasu", tsuke baki tayi tana son barin jikinshi yaqi saketa, ya tsagaita dariyan yana k'arewa fuskanta kallo yace "You have changed me Fatima, you have changed me a lot cikin k'ank'anin lokaci, ban tab'a kawo zama ina rarrashin mace ba sai gashi kin sani na fara, I get emotional anytime nayi tunanki", "your eyes", ya d'an hura mata iska a fuska, "your lips", ya fad'a yana zagaye lips d'inta da k'aramin yatsanshi, "your cute chiseled nose", ya fad'i tareda  had'e hancinsu, "I like everything about you, duk wani uneasiness da nakeji a da yanzu nasan mesa nake jinshi, inasonki but I couldn't realize", hawaye yaga ya ziraro mata a ido, d'an murmushi yayi yace "Bana son zama sanadin zubar precious hawayen nan pls kinji, anytime nayi miki abu just yell, shout, tell me na b'ata miki rai amma banda kuka kinji?, kuka sosai tasa tana son ta tashi daga jikinshi ya sake matseta yace "fad'amin kukan mey kikeyi?", kasa motsi tayi zuciyanta na tsananta bugu, tsorata yayi jin yadda zuciyanta ke bugu ya mik'e tareda zama yana kallonta yace "Fatima are you okay wai, meke damunki ya Allah?", a hankali kamar mai koyon tace "I... love.... you", kamar wani shigewar iska haka yaji maganan ta daki dodon kunnenshi, kallonta yakeyi yanason tabbatar da abinda yaji ya fito daga bakinta, idonta yake nema ya gani dan ko zai tabbatar mishi da abinda ta fad'an, hab'arta ya d'ago yana kallon fuskarta, sauk'e ido tayi tanajin nauyin abinda ya fito daga bakinta, ta d'auka iya zuciya kad'ai ta fad'eshi saida ta gama furtwa tasan a fili ta fad'eshi, yace "Look at me Fatima, pls", da k'yar a hankali ta iya d'ago kai ta kalleshi, suna had'a ido tayi maza ta kauda nata, wani irin runguma taji yayi mata, tare suka sauk'e ajiyar zuciya, a kunnenta yace "son nawa ne ya saki kukan da kikeyi?", a hankali ta girgiza mishi kai, ya d'agota kamar da damuwa a ranshi yace "Toh mey ke saki kuka?" Cikin sanyin magana tace "The very first day i met you, i know something in me has changed da har uanzu bai koma daidai ba, You came into my life lokacin da banyi zato ba, na d'auka you are just here to snatch my happiness, na d'auka duk wani farin ciki da zanyi ragagge ne tunda ka shigo rayuwata, I never thought I could fall for anyone so easily but then I realised kullum anytime nayi tunaninka, I get emotional, anytime I see you, I feel happy, anytime you come in contact I feel shivers down my spine, that feeling that I can't express, tsoro nakeji Yaa Abu, am scared", ta rik'o hannayenshi duka biyu ta rik'esu da k'arfi, kallonta kawai yakeyi, Batuul ce zaune gabanshi tana expressing mishi son da take Mishi, jiya ya gama expressing mata but bai tab'a kawowa kanshi anytime soon Batuul will fall for him, ta fad'a mishi itama heartbeat d'inta is  never stable when ever they are close amma ya d'auka tsoronshi ne duka ya janyo hakan, ya sake damtse hannunta ya sunkuyo yana kallon fuskarta yace "Kalleni, mey ke tsorataki, tsoron mey kikeyi when you have me?", ido ta lumshe ta bud'e tayi d'an murmushin jin dad'in abinda yace, mey zai bata tsoro bayan tana dashi, ajiyar zuciya ta sauk'e da tayi tunanin ba nata bane ita kad'ai, she have to share him da wata, "Fad'a min mana, tsoron mey kikeji?", a sanyaye tace "Of losing you", wani irin farin ciki yaji har ranshi, ya sake tabbatarwa dagaske take tana sonshi, wani lallausan murmushi ya saki ya d'ago hab'arta da tak'i yadda su had'a ido yace "And you think this will happen?, kin rigada kin sameni Fatima sai yanda kikayi dani, I don't need to remind you how much you have changed me, but zan fad'a miki cewa you have gotten Aliyu sai yadda kikayi dashi, Aliyu nakine ke kad'ai, baza kiyi sharing d'insa da wani ba", batason yana mata irin wannan alk'awrin, tun kamin ta sameshi tasan wata ta sameshi kuma babu yadda za ayi ya zama nata ita kad'ai, tasan ba mantawa yayi ba, badai yasone yayi ruining moment d'innan shiyasa yaketa wannan zubar haka", hannu tasa tayi cupping faces d'inshi tace "Ka dena fad'an haka, before me there was someone a rayuwarka, she got you before me", tayi wani irin murmushi tace "am okay with it, just love me, kar ka dena sona that's I want", sai lokacin ya lura da maganan da takeyi, sai lokacin hankalinshi ya nuna mishi cewa da Ajiddeh take, wani irin b'acin raine yaji ya ziyarce shi lokaci d'aya, ya kai hannu kan hannyenta dake fuskarshi ya riqe yace "ki riqe a ranki ke kad'ai keda ni and no one else", kallonshi take tana dad'a tabbatar da what he is saying, from his eyes tana ganin he meant what he is saying, kai ta girgiza mishi zatayi magana yace "I promise, ke kad'ai kike dani nima ke kad'ai gareni", ajiyar zuciya ta sauk'e ta lumshe ido zuciyarta na bugawa tana kokonton abinda zuciyarta ke shirin sata tayi, a hankali tayi leaning ta cikata gap d'in dake tsakaninsu ta had'e bakinsu waje d'aya, wani irin dogon numfashi yaja kamin ya amshi bak'uncin abinda yakeji yanzu, a hankali yayi parting lips d'inshi suka  shiga kissing junansu with so much affection, kamar wacce ta tuna abu tayi maza ta janye bakinta daga nashi, a raunane ya d'ago ya kalleta da puppy eyes yace "Plssss", had'e rai tayi tace "Su waye y'an matan d'azu da suka zauna suna maka magana harda dariya?", ajiyar zuciya ya sauk'e tareda lumshe ido ya sake kamota ya had'a bakinshi da nata, saida ya gaji don kanshi ya k'yaleta ya cire mata hijab tareda da kwantar da ita jikinshi ya na yamutsa mata gashinta da yake a tsefe, ya bud'e baki zaiyi magana  daidai lokacin wayarsa tayi ringing, dubawa yayi yaga Ammah ke k'ira, jiki ba k'wari ya d'aga, muryar Aunty Amnah yaji tana cewa "Sannunka Abu, ina ka kai y'ar mutane ana zuwa dubata bata nan?, Massa da Rahama tun d'azu suke zaune baiwar Allah kasa ta zaman jira, ka dawo da ita", murmmushi yayi yace "She is my wife, nafi kowa buk'atarta, suyi hak'uri su barni da ita, I need my wife", baki Aunty Amnah ta bud'e tace "Lallai Abu, yanzu ko kunyata baka ji kake cewa a bar maka matarka you need her ko?, toh ga Ammah nan kayi mata bayani", muryar Ammah yaji tana cewa "Abu bana son wasa, ina ka kai yarinyar mutane?", a hankali yace "Ammah she is my wife kuke magana kamar wata nayi kidnapping", Ammah tace  "Kana jina ko, Batuul d'in da bata da lafiya ko k'warin jiki bata gama samu ba shine zaka d'auketa ka tafi da ita gantali?", kallon Batuul dake kwance jikinshi yayi suna had'a ido ya sakar mata murmushi har lokacin hannunshi d'aya na cikin gashinta, itama ta maida mishi murmushin a ranta tana tunanin yadda zatayi facing Ammah,  yace "Ammah relax, dagaske babu inda na kaita, muna gida fa, she will be safe, I promise" tace "Ban gane gida ba, yanzu haka k'annen nata zasu tafi basuyi sallama da ita ba?", yaja numfashi yace "Ammmaaahhh, we will be back soon, ayi mana hak'uri, kuma ma zan kai ta ta gaishesu ai some other time", Ammah taja tsaki  tace "inace jikinta lafiya babu matsala?", yace "She is fine, yanzu zamu dawo", da haka ta katse k'iran, yaja numfashi ya sauk'e ajiyar zuciya, da sauri ta mik'e ta zauna tace "Kaga mu tafi, su Ammah na nemanmu", ya maidata position d'inta na da yace "We are staying here for the night", ta wara ido tace "No Yaa Abu, inajin kunyan Ammah fa", ya d'aura hannu kan flat tummy d'inta yana shafawa yace "Kin manta ma da tambayar da kika min, well those ladies da kika gani, all I can remember is we had classes together when I was in college", tace "toh shine suka zauna har kuka dad'e kuna magana dasu", yayi pouting lips d'inshi yace "Bake kika tafi kika barni ba, you unveiled me kika barni ni kad'ai, they thought banida mata shiyasa suka zo wajena", D'auke ido tayi da sauri, a ranta tace "Subhanallah", wani irin kyau yayi mata da yayi pouting, he will be the dead of her in har taci gaba da kallon face d'inshi da yayi pouting da girarsa da suka had'e waje d'aya, tace "su basusan mey mata bane Kai, I cried because of that, my heart was aching da na ganku a tare", ya sake tab'are fuska yace "Noooo, karki damu baki sake ganinsu anywhere close to me, kema promise not to leave me", pouting d'in tayi itama tace "I can't even do that, I love you", wani farin ciki na daban ke ziyartarsa, ya sunkuya yayi pecking d'inta "You know I do more", lumshe ido tayi tana jin wannan sabon yanayi da ta samu kanta ciki, a hankali tace "kaga fa kukana shi da kanshi yake zuwa, bani keyi ba", ya d'agota yace "And you know it hurts me ba?, I hate to see you cry", a hankali kamar zatayi kukan tace "I promise not to again", yace "Thank you, tashi muje kiyi alwala muyi sallah, its Magrib, ita ta fara yi snn ta jirashi ya fito shima yayi  suka dawo ya jasu sukayi sllh, zama yayi bayan sun idar yace zai musu ordering abinci su dan nan zasu kwana, da k'yar ta samu ya yadda suka koma gida, gabanta har fad'uwa yakeyi tana tunanin Ammah zata gane komai ga kunyarta da takeji yau, da Aunty Amnah suka fara had'uwa da ta bishi da harara tayi hugging Batuul tace "kika yadda kika bishi yawo?, gantalinshi fa ba mai k'arewa bane da kike ganinshi", murmurshi kawai tayi ta sunkuyar da kai, ya kalli Aunty Amnah yace "Nima haka zanje in samu uncle ince mishi ya dena zuwa ko ina dake, dama gashi kin fara tsufa, sai a d'auka yayarsa ce",  Aunty Amnah ta wara ido tasa salati tana tafi tace "Abu ka gama rainani, zamu had'une da kai har gida zakazo ka sameni", dariya kawai yayi dai dai lokacin Ammah ta k'araso ta harareshi tace "ai ka kyauta", murmushi yayi yana sosa kai yayi mata k'asa da puppy eyes d'in da yayi alamar tayi hak'uri, Ammah ta kama Batuul tace "muje kisha magani, ga soup d'in  kifin tun d'azu Amnah taxo dashi", ta manta sam da tacewa Aunty Amnah ma tana son soup d'in kifi, a kunyace tabi Ammah a baya, k'arfe tara Uncle yazo suka tafi da Aunty Amnah bayan ya yiwa Batuul ya jiki tareda yi mata alk'awrin kawo su Nawal kamin su koma Paris, wanka Batuul tayi ta shirya ta sulale d'akin Farida, hiransu sukeyi abinsu sukaji an bud'e k'ofa, duk suka dubi k'ofan a tare suka ga Abu ne, bai cewa kowannensu komai ba ya shigo yad'auki Batuul cak, tace "Yaaa Abu kayi hak'uri ka sauk'eni, kaga fa akwai su Ammah a gida", yace ba guduwa kikayi kika barni ba?", tace "naga fa kana wanka ne shine na tafi kamin ka fito", bakinshi ya d'aura wuyan da yasata kasa yin wata maganr, ranan kwanan farin ciki sukayi , sosai Abu ya gwadawa Batuul irin son da yake mata da missing d'inta da yayi a daren.

     
[11/22, 11:22 PM] ‪+234 803 698 6494‬: 💖💝BATUUL💖💝






92






By phartiemarhk






Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*




  Tunda Dad ya fita ya barta d'akin Kulthum Ajiddeh  bata sake cewa  komai ba, angle ta samu daga gefe ta zauna a takure, duk bayan minti d'aya sai ta duba wayarta tana jiran tsammanin k'iran, a hankali siraran hawayen ke bin fuskarta, rayuwarta a baya take tunawa, tun ranan da ta fara ganin Abutturab a school Allah ya d'aura mata sonshi, babu irin wahalar da batasha ba dan kawai ya fara koda kallonta ne amma yaqi, babu irin nacin da batayi akanshi ya nuna duk baisan abinda takeyi ba, gashi ko aboki d'aya bata tab'a ganishi tareda ba, shekarar da zai gama ita tana third year, sosai hankalinta ya tashi ganin har zai gama ya tafi, shawara ta yanke kawai na ta sanar da Mum, at first mum bata biye mata ba saida taji ko d'an waye shi d'in, lokacin ne Mum tace mata ko sau d'aya ta samu ya bud'e bakinshi yayi mata magana daga nan zasusan abin yi, baza ta manta ranar da suka shirya itada friends d'inta akan in taga ya shigo makaranta ran sunday ta shige gaban motarsa ba ya bigeta ko dan yayi mata magana ne, tunda duk Sunday a school yake yinta kuma babu mutane da yawa, hakan kuwa sukayi ranan Sunday babu mutane da yawa school, daidai ta hango motarsa ta tashi ta shiga drive way shikam da ya taho sam bai lura da ita ba, kiiiii ya taka brake, da hanzari ya fito, ranshi b'ace zai fara yiwa maishi fad'an rashin kula, sai a lokacin ya gane mace ya kad'e, duk nacin da take mishi baisa ya gane wacece ita ba, baki ya bud'e zaiyi magana ta fashe da wani irin kuka, babu sautin da yafi tsanar jin irin kuka bare na mace, duk masifar da ya kwaso kasa k'arasa yin ta yayi, kuka take sosai tana yarfe hannuwa dukda ba wani ciwo taji ba, d'aukarta yayi ya sata mota, friends d'inta na daga gefe sukayi mata signalling zata wuce, ido d'aya ta kashe musu alamun taji dad'in accomplishing mission d'inta, murna fal cike ranta tana jin ta jikinshi kamar lokaci yayi ta zama a haka, a mota ya sakata yace mata sannu daga haka ya fara driving, asibitin da yake zuwa can ya kaita aka dubata sukace bata wani ji ciwo ba amma sam taqi yadda ta taka k'afar, ya tausaya mata ganin yadda take kuka, Wheel chair yayi requesting da a bata, badan taso ba ta zauna Kai, sai da suka fito yake tambayarta makaranta zai kaita?, tace mishi kada ya damu ya kaita gidanta, yana tsaye bai shiga gidan ba yasa tayi waya aka zo aka shigar da ita, yana barin wajen da mortarsa
ta daka wani uban tsalle, tayi hugging kawayenta, take ta bugawa Mum ta fad'a mata duk yadda abin ya faru, tun daga lokacin suke asiransu kanshi, wasu suyi tasiri wasu baza suyi ba, lokacin da yazo mata da zancen aurensu suma ne kawai batayi ba sbd dad'i, kamar a mafarki takejin lbrn, tasan Aliyu baya mata son da har zaice zai aureta, son da yake mata baifi 2% ba cikin 100% d'in da take mishi, tsoron kada wani abu ya sa ta rasashi ta shiga neman maganin mallaka, duk inda tasan za a bata abinda zaisa Aliyu ya sota ita kad'ai har abada saida suka zagaya itada su Mum da Aunty Jainaba, wani hawaye mai d'umi ta share daga fuskarta tana ci gaba da tunani, tunda ta zauna Kulthum ke kallonta, a hankali taji muryarta tace "Komai yayi zafi maganinshi Allah, ki fawwalawa Allah dukkan lamuranki shi zai miki jagora", wani iri taji maganar kamar ma ba da ita akayi maganan ba amma sanin su biyu  ne kad'ai d'akin yasa ta gane da ita take, bata kulata ba har lokacin, da dare ma haka Ajiddeh bacci kad'an tayi, washe gari ne ganin yanayin Ajiddeh duk ya canja tace "Hauwa tunane tunanen nan da kuka duk da kikeyi matsala zasu k'ara miki, ki samu ki sassautawa kanki, bance ni ba ko inason sanin matsalarki ba, a ah, ki samu wani amintacce da kika yarda dashi kika san zai baki shawara mai kyau ki fad'a mishi matsalarki zaki samu sauk'i a ranki, ko da mahaifiyarki ce ko mahaifinki, zasu fahimceki ko da wacce iriyar matsala kikazo musu, kallonta kawai Ajiddeh keyi ta kasa ce mata komai, batasan komai game da matar ba amma daga yanayinta tasan bazata cutar da ita ba, tashi tayi ta fice daga d'akin tayi side d'in Mummy, masu aiki ne sukace mata Mummy tun da asussuba ta fita amma tace kada a bari ki fita ko inane, wani kallo ta jefeshi dasu kamar in tayi niyyan fitan zasu iya hanata, juyawa tayi ta koma side d'in can, a hankali ta fara magana ta shiga zayyanowa matar abinda ke damunta, matsalarta da kuskuren da duk ta aikata, batace dai asirin kisa sukayiwa Batuul ba, tace kawai na zubda ciki ne da kuma barin gidan sukayi mata


        Da asuba shi ya fara tashi, bai tada Batuul ba dan yasan bacci bai wani isheta ba, kwanciyarta ya gyara mata snn yayi wanka ya zira jallabiya ya fesa turarukanshi masu sanyin k'anshi ya fita zuwa masallaci, a masallaci ya had'u da Abui da Sadiq, Bayan an idar da Sallah snn suka gaisa, Abui yana tambayanshi ya jikin Batuul ya amsa mishi da "Alhamdulillah taji sauk'i", Sadiq ma ya gaisheshi yayi mata ya jiki daga haka suka shigo gida kowa yayi side d'inshi, a hankali ya turo k'ofar d'akin,  da mamaki ya kalleta ta kunna bedside lamp tana zaune kan abin Sallah riqe da Qur'an tana karanta Suratul Qasas cikin muryarta mai dad'i, Ido ya lumshe ya bud'e snn ya shigo d'akin tareda mai da k'ofar ya rufe, tunda yake da Ajiddeh bai tab'a ganin ta tashi Sallah batareda ya fad'a mata ba, ko ya fad'a sai lokacin da ta ga dama take tashi tayi, da sauri ya kawar da tunanin Ajiddeh yayi da sauri, daga gefenta yazo ya zauna, godiya ya dinga yiwa Allah cikin ranshi da ya bashi Batuul, a zuci yana bin duk ayoyin da take karantawa, kamar yau ya fara jin Qissoshin Annabawa dake cikin surar jin yadda take karanto shi, har saida tayi kusan rabi snn ta rufe ta shafa addu'o'inta ta maida Qur'anin kan bedside drawer, a hankali ta juyo ta kalleshi tace "Ina kwana", wani farin ciki yakeji a ranshi da ganinta, ji yakeyi kamar ya d'auketa ya kaita wajen da babu kowa, inda babu abinda zai sameta sai farin ciki, ido ta d'an wara ganin yana kallonta bai amsa mata gaisuwarta ba tace "Yaa Abu ina kwana", sai lokacin ya lumshe ido ya bud'e yace "Waye malamin da ya koya miki Qur'an?", cike da farincikin tuna mata malamin da baza ta tab'a mantawa dashi ba tace "Malan Ahmad shine malami na, mey yayi?", ta fad'a tana d'an yatsina fuska yace "Har Tajweed duk shi ya koya miki?", ta kad'a kai tace "Har komai ma shi ya koya mana dukkanmu dasu Ahmad da Sa'eed", yace "Ya complete sunanshi yake and yana ina yanzu?", tunanin mesa yake son sani a hankali tace "Sunanshi Ahmad Abu Hamira Daiba, su Ahmad sun san  inda yake, nasan har yanzu yana koyar dasu", a hankali ya janyota jikinshi yayi wrapping duka hannayenshi jikinta yace "In na bashi kujerar Hajj da Umara this year yayi?", da sauri ta shiga k'ok'arin juyowa taga dagaske yake nufin abinda yake fad'i amma bai saketa ba saima k'ara gyara mata zama da yayi ya d'aura fuskanshi kan wuyanta, duk da hijab a jikinta bai hanata jin d'umin numfashinshi dake sata jin wani a iri a jikinta ba, da k'yar ta iya bud'e baki tace "Dagaske?", yace "Kuma a bud'e mishi Tahfeez, inaso in princess ta girma ya koya mata", ya fad'a tareda sauk'e  hannunshi kan cikinta, "Inaso in ta girma itama tana min irin k'ira'arki", wani irin juyawa tayi ta rungumeshi sosai, yana jin yanayin bugun zuciyarta, shima d'in sake rik'ota yayi, kamar mai jin tsoron abinda zata fad'a tace "I love you", ido ya lumshe ya bud'e yana jin kamar kullum ta zama magana da zata fito daga bakinshi, ta d'ago da sauri tana kallon fuskarshi tace "Yaaa Abu tun yanzu ka fara sani farinciki, am scared yayi min yawa and mayb you might change nan gaba", kallonta kawai yakeyi for seconds ya kasa ce mata komai, da k'yar ya iya samu yace "Baki yadda da son da nake miki ba ko?, baki yadda I can forsake duk wani farin ciki nawa for you to be happy ba ko?", kunya ce taji ta kamata, lafewa tayi jikinshi hannunta kan k'irjinshi tana jin yadda yake heaving a hankali tace "Na yadda, bana so ne yayi min yawa", bakinshi ya d'aura kan nata ya rufe mata baki, saida ya d'ago yace "You deserve all happiness, ki kwantar da hankalinki kinji, you have got me for yourself", shiru tayi lafe a jikinshi, d'agata yai cak ya kwantar kan gado yace "You need sleep, kwanta kiyi bacci", ya shiga k'ok'arin cire mata Hijab d'in dake jikinta zai gyara mata kwanciya,

1 Comments On BATUUL
avatar
hafsat-9-3

12 months ago

Reply

Nice book

Please Login or Register in order to submit comment