Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tayi wajen Aunty ta rungumeta, tana jinta jikin Aunty ta fashe kuka, murmushin k'arfin hali Aunty tayi dan itama kwana ďaya da tayi bata gidan tayi kewarta sosai, ďagota tayi tana kallon fuskanta tace "Kukan na meye kuma Batuul", sake komawa tayi ta kwanta jikin Aunty taci gaba da kukan da takeyi, da sallama ya shigo falon, ďagowa tayi daga jikin Aunty tana kallon Aunty tace "Aunty su Mahir fa", Aunty tace "Ai yau babu wanda yaje Islamiyya cikinsu, Hafiz kam kuka ya dingayi wai sai an kaishi inda kike", hawayen dake idonta ne ya k'arasa gangarowa jin abinda Aunty tace, da gudu ta k'arasa hawa sama tayi ďakinsu, buďewa tayi tagansu kamar kullum ďakin yadda yake suna kallon ball, da gudu ta shige ta rungumosu, sai da suka sake juna Yusra tace "Yaa Batuul wai inji Baba zaki tafi Uk yau zamu daďe bamu ganki ba dagaskene?", ji tayi kamar zata fasa ihu tayi murmushi tace "a ah bazan daďe ba, ai zaku rakani airport ko", da sauri suka shiga gyaďa kai, ta kalli manyan da sukayi kamar basu san tana ďakin ba tace "y'an rainin wayo dama nasan jira kuke in bar gidan shiyasa kun ganni yanxu ma baku damu ba", dariya sukayi suka juyo sukace "penalty za a buga shiyasa", duk suka taso suka dawo kan gadon da take, zama tayi suna ta hira da k'annenta har saida Aunty ta tura a k'irata, kitchen ta samu Aunty, anty ta dubeta tace "Batuul wa yace miki haka akeyi, ya zaki tafi ki barshi shi kaďai ko ruwa baki bashi ba", baki ta zumb'uro tace "Aunty toh ba su Janet zasu bashi ba", Kai Aunty ta girgiza tasan akwai aiki sosai gaban Batuul dan ba wayone ya gama isanta ba gashi lokacinsu is limited, amma ba komai ko ta wayane zatayi mata magana, kai ta girgiza ta juya ta ďauko tray ta jera abubuwa tace "ďauki ki kai mishi", baki ta zumb'uro ta kinkimi trayn tayi palo dashi dungure masa tayi a kasa ba tare da ta kallesa ba, ya bi ta da kallo har ta haura sama yyi murmushi, sai magrib lokacin suna shirin tafiya Baba ya dawo, shima ganinshi ta shiga sabon kuka, da k'yar ya samu tayi shiru, Abu kam suna haďa ido yake sakar mata harara, cewa Baba tayi sam sai k'annenta sun rakata airport, da farko da yaqi dan sai sun koma gidan Ammah zasu wuce, amma ganin yadda take kuka yasa driver ya kaisu, sai a lokacin Aunty taji baza ta iya jurewa ba itama taja Batuul sukayi ďaki, sunfi minti talatin har saida Baba ya shigo yace ya isa haka ta fito su tafi, kuka takeyi sosai har ta shiga cikin motar, bai ce mata komai ba shima ya shiga, motar su Ahmad na daga gaba nasu na baya sukayi gidan Ammah.
[8/22, 14:39] Umar Dalha: 💖💝BATUUL💖💝






42






By phartiemarhk






Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*





Kanta ta kifa tsakanin cinyoyinta ta dinga rusa kuka, shi dai bai ce mata komai ba sai kallonta da yake ta gefen ido yaga if she's fine, sai da suka shiga cikin gida bayan yayi parking ya juyo ya dubeta ganin batada niyyan tashi ya sa ya bude motar ya fito ya wuce gun motar k'annenta, sai da k'annenta suka fito suka nufi motar Abuturrab tukunna ta shiga goge hawayen dake fuskanta, dan murmushi tayi masu ta sauk'o daga cikin motar tana kallonsu tace "mu shiga mana", ba musu sukayi gaba, yana daga gefe yana kallonsu, yaran masu kyau duk sun fita haske, juyawa tayi ta dubi inda yake tsaye yasa hannu ďaya cikin aljihu, wani kallo ya shiga yi mata, ďauke kanta tayi daga dubanshi tabi bayansu, ita ta buďe musu k'ofa sai da suka gama shiga itama ta shiga da sallama, da murna Farida dake zaune tare da Ammah ta mik'e tana k'ok'arin ďaukan Hafiz, waje suka samu suka zazzauna daga k'asan rug ďin palon, da fara'a Ammah ta shiga ce musu "Ahmad ku tashi ku zauna kan kujera mana", babu abinda sukeyi sai murmushi, ta dubi Batuul tace "Bitti ce musu su hau kujera mana su tashi daga k'asan nan", kallonsu kawai Batuul tayi ta kasa musu magana, ganin sunqi tashi Ammah ta mik'awa Yusra, Mahir da Hafiz hannu alamun suzo wajenta, Yusrace kaďai taje dan ita tana da saurin sabo, Janet Farida tashiga k'walawa k'ira, babu b'ata lokaci ta fito tace "Aunty gani nazo", ta dubeta tace "kawo musu ruwa", ba b'ata lokaci ta juya ta tafi kawo musu ruwa, Ammah zatayi magana kenan ya turo k'ofa ya shigo yana tafiyarshi ta k'asaita, palon ya k'araso ya zauna, Ammah ta dubeshi tace " tare da su xa ku airport knn", Batuul da kanta ke k'asa taqi ďagowa yake kallo kamin ya kalli Ammah yace "Ehhh kuka tayi ta musu kamar yarinya wai tanaso su rakata", Ammah tayi dariya tace "Babu wani yarinta, ai gaskiyanta da tace su rakota su yi bankwana", baice komai ba sae tab'e baki da yyi ya mik'e yana kallon Ammah yace "Ammah Sadiq ďin ya fito ne, saura thirty minutes tafiyan namu", Ammah tace "Ai yanxun nan ya shiga wanka", daga jin haka ya wuce, Ammah ma tashi tayi tace "Bitti muje ki shirya kar lokaci ya k'ure kinji", ba musu ta mik'e amma har lokacin ta kasa yadda wai itace za a rakata airport zata bar garinsu dan tayi aure zataje zama da wani, take idonta ya fara kawo ruwa, jiki a sanyaye ta bi bayan Ammah, tana shiga bath tub ta dinga kuka dan kanta ta mik'e ta fito bayan ta kusa minti goma a ciki, wasu kaya ta gani Ammah ta ajiye mata kan gado, Lace maroon ne mai green designs da jewellery ďinsu na gwal, ba b'ata lokaci ta ďauka ta sakasu cikin rashin kuxari, riga da skirt ne, kayan sun mata kyau sosai, a bakin gado ta zauna bayan ta gama y'an shafe shafenta ta shiga tunanin irin rayuwar da xata yi ynxu.





D'akin Abuu Ammah ta shiga bayan Batuul ta shige toilet, har ya canja kaya lokacin yana zipping wani akwati, ganin Ammah da yayi ďakinshi ne ya sashi barin abinda yake cikin hanzari ya k'araso inda take, bata ce mishi komai ba har ta k'arasa shigowa tukunna ta zauna daga bakin gadon, rabon da Ammah ta shiga ďakinshi har ya manta, jiki a sanyaye ya bita ya zauna daga k'asa, ce mata yayi "Ammah ai da kin k'irani nazo ba sai kinzo da kanki ba" har ta buďe baki zata fara mishi magana ta fasa tace "in ka gama ka sameni a ďaki toh", daga haka ta mik'e tayi waje, ajiyar zuciya ya sauk'e dan yasan da magana bakin Ammah, koh minti biyu batayi ba da fita shima ya fita yabi bayanta, zaune ta tadda Batuul bakin gado har lkcn, ganin Ammah ta shigo yasa ta sauk'e kanta k'asa zata sauk'a k'an rug ďin Ammah tace mata tayi zamanta, kin zama tayi kan gadon ta sauk'o k'asa, da sallama ya shigo ďakin shima ya zauna kan stool ďin mirror, Ammah na kallonshi ta fara magana "Abuu ga amanan Batuul nan na baka da hannuna", da sauri Batuul ta ďago jin abunda Ammah tace, jiki a sanyaye ta sauk'e kanta dan har idonta ya fara tara ruwa, Ammah taci gaba tana kallon yadda ya sauk'e idonshi k'asa tace "tunda kayi aure kasa k'afa ka fita daga garin nan hankalina bai kwanta ba, ni bansan tsakaninka da matarka ba amma mu dai kam babu abin alheri da tayi mana, ni da kaina na sa aka nemo maka auren Batuul dan tun kamin aurenka da Ajiddeh Batuul naso ka aura amma Allah bai yi ba sai yanxu, ko sau ďaya ban yadda kasa hawaye zuba daga idon Batuul ba, ban yadda ko da wasa matarka ta wulak'anta min ita ba, yadda take zab'inka haka nima Batuul take zab'ina sannan amana na baka ita kamar yadda iyayenta suka aminta dakai suka baka y'arsu, ka kula da ita fiyeda yadda xa ka kula da kanka, sannan makarantarta ba denawa zatayi ba, an sama mata admission a can, ka taimaka mata da dukkan k'arfinka har sai ta kamalla dan tana karatunta muka nema maka aurenta, Allah ya tayaka rik'o ya baka ikon yin adalci tsakaninsu", ta juya tana kallon da Batuul da ta jik'a gyalenta da hawaye a lokacin tace "Bitti ga yayanki nan xa ku tafi, na faďa miki duk abinda zaiyi miki mara daďi, don't hesitate in zama ta farko da zaki faďawa, ki zama mai respecting ďinshi kinji, he will be your guide In sha Allah, tsakanin ki da matarsa girmamawa, ki goge hawayenki kinji, kuma duk lokacin da kike son dawowa ki faďa mishi zai dawo dake kina yin kwana biyu kinji", Sadiq ne ya turo k'ofan tareda sallama, da murmushi a fuskanshi ya dubi Abu yace "ba dai kun fasa tafiya ba yau", Abuu ya dubeshi fuskanshi babu walwala yace "We are coming", Ammah ta dubi Batuul ta ďagota tace "Bitti share hawayenki ki tashi kuje, Allah yayi muku albarka, ya baku xuri'a dayyaba", da k'yar Batuul ta iya mik'ewa tana gyara gyalen dake kanta har wani shidewa take don kuka, Sadiq sai tsokananta yake sae dae shi ma xuciyarsa fal yake da tausayinta, suna sauk'a k'asa suka tarar da Massa shima yazo, gaba ďayansu suna zaune palon sun gama shanye drinks ďin da aka kawo musu, Ammah tace "jeka Abui ya shigo yanxu kuje kuyi sallama dashi, tare sukaje sukayiwa Abui sallama yana gaba tana biye da shi a baya, Abui ya sake musu Nasiha tareda yi musu Allah ya kiyaye hanya, mota uku suka yi suka nufi airport.





Tunda suka ďau hanyan airport take kuka ba k'akk'autawa dan tasan farin cikinta ragagge ne tunda har ta yadda tabi Abu wani garin da babu kowa nata, tausayin kanta take sosai tana kuka, sai da tabi y'an uwanta ďaya bayan ďaya tayi hugging ďinsu tana kuka su din ma kukan suke, har ta iso kan Farida dake kukan itama ta rungumeta, da k'yar suka sake juna don itama kukan da take ya hanata yin magana, ta kasa yin komai sai gyaďa kanta da takeyi, cikin hanzari ta sake Farida xata bi Sadiq da ya kasa ci gaba da kallon emotional scene din ya juya xae bar wajen, Abuturrab ya fixgota jikinshi, sosai ta shiga yin kukan kmr ana tunxura ta, dai dai saitin kunnenta ya sunkuyo a hnkli yace "control, its a public place baza mu tafi kina kuka kamar wacce na sato ba", kwanciya tayi jikinshi tayi lamo tana ajiyar xuciya, yana jin yadda heartbeat ďinta ke up and down, hannunshi ďaya ya ďaura bayanta, ďayan kuma yayiwa su Sadiq alamun suja su Ahmad su tafi, hakan kuwa akayi, takai minti biyar kwance jikinshi, can da ta tsagaita kukan ta fara dawowa normal ta ďago kanta, jinta jikinshi yasa ta kallon fuskanshi taga shima ita yake kallo, da sauri ta matsa baya ta juya bayanta ganin ko su Farida na nan, taga wayam babu kowa wajen, kallonshi tayi da idonta da yacicciko tace "Yaa Abu dan Allah mu koma kar mu tafi plss", wani irin kallo ya bita dashi yaja akwatin dake gabanshi yace "When you are done ina ciki", babu yadda ta iya haka tabi bayanshi a sanyaye tana share hawayen dake sakko mata, a departures waiting room ya xauna yana jiran jin announcement din departure'n su sanin few minutes ya rage, ya juya yana kallonta ganin a tsaye take, a hnkli ta xauna nesa da shi kanta a kasa, tabe baki yyi ya kauda kai, bayan kusan minti takwas akayi announcing cewar passengers din Abuja to UK su fara boarding ynxu jirgi xae tashi, mikewa yyi yana kallonta, wasu sabbin hawayen ne ke sauko mata duk jikinta yyi sanyi ta kasa tashi, har ya fara tafiya yana jan trolley dinsa ya tsaya, juyawa yyi yana kallonta ganinta xaune yasa ya dawo yana kallonta bbu yabo bbu fallasa yace " Ko in daga ki ne" a hnkli ta mike tana rufe bakinta da mayafi kar ta saki ihun da taji na shirin fitowa, sauke idonsa yyi daga kallonta ta kama hannunta ya shiga tafiya tana binsa har suka isa inda jirgin British Airline (B.A) yake tsaye, yana rike da hannunta suka shiga jirgin, a first class ya samar masu empty seats, a hnkli ta xauna ta jinginar da kanta jikin kujerar tare da lumshe ido, ya saka trolleyn hannunsa daga sama inda ake ajiye luggages, snn shi ma ya xauna, announcement aka shiga yi na cewa "Passengers on board shud pls fasten their seat belts, British Airline flight is about taking off" Abuturrab yyi fasten din seat belt dinsa yana kallonta, gani yyi ko motsi bata yi ba, ranan da suka yi boarding same plane daga Maiduguri xuwa Abuja ya tuna, yyi shiru yana kallonta, a hnkli ya kai hannunsa ya mata fasten din belt din da kansa, ta bude rinannun idonta tana kallonsa, lkci daya ya hade rai, da sauri ta sunkuyar da kanta, wayarsa ya fiddo ya maida shi flight mode ya jona earpiece ya sa a kunne ya lumshe ido, jirginsu na tashi ta fashe da wani kukan tausayin rayuwarta, bude ido yyi yana kallonta sae dae bae ce komae ba, tayi mai isarta bayan wani lkci tayi shiru ta kwantar da kai jikin kujeranta lkci daya bacci ya dauketa, sae a snn ya cire earpiece din kunnensa ya rike kansa dake sara masa xuciyarsa a dagule, from Where is he going to start this long explanation to his Ajiddeh, just ta ina xae fara ce mata iyayensa ne suka makala masa Batuul, ya xata dauki xancen, will shi even believe him, tunanin hkn ya sa ciwon kansa ya tsananta, jinginar da Batuul tayi jikinsa tana bacci ya dawo da shi duniyar tunanin da ya tafi, juyawa yyi yana kallonta ya ga bacci ssae take, ya fuzar da iska tare da lumshe ido ya jawota jikinsa don gyara mata kwanciya, muryar wata hostess din jirgin ya sa shi bude idonsa, tana tsaye dai dai kujeran da suke plate holder din seats dinsu ta jawo ta dora ruwa a kai a karamin disposable cup, murmushi dauke fuskarta tace "Sir what would yhu like to have?" Yace "Just coffee" kallon Batuul tayi xata yi magana yace "She's OK" juyawa tayi ba a dau lkci ba ta dawo da cup din coffee ya karba yace "Thank you" d'an bow din masa tayi tana murmushi tace "Yhu are welcome Sir" daga hka ta juya ta bar wajen. Karfe sha biyu saura na dare Batuul ta bude idonta ganinta jikinsa yasa ta kallesa, idonsa lumshe yake alamar ya fara bacci, a hnkli ta xame jikinta ta xauna da kyau, ta shiga rera kuka tunawa da tayi shknn fa ta rabu da Anty, bude ido yyi yana kallonta, ya gyara xamansa a fusace yace "God! What again? Ke wae baki gajiya da kuka ne, am tired of this pls, aiki kawae su Ammah suka hada ni da I knw" jin ta kara sautin kukan yasa ba tare da yyi wani tunani ba ya jawo ta jikinsa murya can kasa yace "are yhu hungry" kin cewa komae tayi, ya watsa mata wani kallo yace "Kina jina dae koh?" Girgixa masa kai tayi, ya hade rai yace "Gud! Go back to sleep ynxun nn" rufe idonta tayi, tayi lamo jikinsa sae dae yana jin ynda xuciyarta ke bugawa. Har asuba daga ita har shi basu rintsa ba, da ta bude ido xae tambayeta ko tana jin yunwa ta girgixa kai ta kuma rufe idon, Karfe bakwae na safiyar washegari jirgin British Airline ya sauka airport a UK, nn fa Abuturrab ya ji duniyar gaba daya tayi masa xafi, da ya tuna Ajiddeh sae gabansa ya fadi ba kadan ba, da kyar ya mike yana kallon Batuul da idanuwanta suka rine ssae, hade rae yyi lkci daya ta mike kanta a kasa, ya fiddo trolley dinsa ya shiga tafiya, bin bayansa tayi hawaye cike idonta har suka sauko daga jirgin, duk da ta sha xuwa kasashen turawa da Baba har ma da Anty Hafsat yau komawa tayi kmr bakauyiya a haraban airport din, don sae shishshige masa take, ba komae kuma ya janyo hkn ba sae don duk a tsorace take, ba kuma wae turawan suka bata tsoro ba sae don tunawa da tayi da Ajiddeh
[8/22, 14:41] Umar Dalha: 💖💝BATUUL💖💝






43






By phartiemarhk






Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*





Amma na ganin tafiyarsu ta koma cikin gida itama tana jimamin rashin Batuul da zatayi, ďakin Abui ta wuce ta sameshi zaune yana kallo da glass idonshi, daga gefenshi ta zauna tace "Barka da zama Abui", yace "Yawwa Ammah, naga har kin fara missing yaran naki", murmushi tayi mishi tace "Ai ni tausayin yarinyar nan ke cikani, sosai nake tausayinta danma dai tana da nutsuwa", juyawa tayi ta kalli Abui with full attention tace "Abui amma hankalina gaba ďaya yaqi kwanciya, matar Abu nake jiyewa Batuul dashi kanshi Abun, ko wancan karan ni nasan Abu ba yin kanshi bane zaman da yayi ba tareda dawowa gida ba har na shekara ďaya", with full concentration Abui yake kallonta har saida tayi shiru yace "Ehhh shiyasa this time da mukaje Maiduguri kamin a ďaura aurenshi sosai nasa aka mishi addu'a, sauk'an Alqur'ani kuma kullum sai anyi har yau ďinnan Allah ya rabasu da sharrin masharranta", wani ajiyar zuciya Ammah ta sauk'e tace "Alhamdulillah", ta gyara zamanta tana fuskanta Abui tace "Nima tun lokacin da Ashiekh yace a dage da addu'a ban daina ba, yanxu naga komai ya fara daidaita, dan banga alamun abinda akayi mishin har yanxu yana jikinshi ba, sai dai mu sake dagewa Allah ya sake rufa asiri, wannan karan har Batuul ďin sai da na sa ana yiwa sauk'an Qur'ani da addu'a, daga baya ma zan sake tura mata maganin kariya dan yanxu lokaci ya k'ure shiyasa ban basu ba" Abui yace "Allah ya sake karewa, tare suka amsa da "Amin", mik'ewa tayi tana kallon Abui tace "Abui abincin fa baka ci ba gashi har takwas ya wuce", murmushi ďauke fuskanshi yayi mata alama da tazo ta zauna gefenshi, ba musu ta dawo ta zauna gefenshi tana kallonshi yace "naga kina ta hidiman yaranki bakizo bani abinci ba shiyasa nima banci ba", murmushi tayi dan tasan tsokanarta yake ta ďan kalleshi tace "Toh su ba yara bane, kai ai kullum inayi maka kuma daga yau su tafiya zasuyi", k'ok'arin tashi take daga wajen tana cewa "Abui bari in kawo maka tea toh tunda baza kaci abincin ba", jawota yayi jikinshi yace "No am okay, kiyi zamanki nima bana jin yunwa, i ate late in d evening shiyasa banci abincin ba, kuma tea ďinma i dont feel like taking it", batace komai ba ta sake shigewa jikinshi daga nan sukaci gaba da hiransu,




Har suka fito daga terminal ďin bata dena kuka ba, shidai bai ce mata komai ba dan kukanta ya ishesa, tafiya yake tana biye dashi sai shishige mishi take har lkcn abun har yaso bashi dariya, Taxi ya tarar bayan sun fito yace mishi "GEORGE'S street", driver da kanshi ya fito zai buďe musu k'ofa yace "No its okay you can sit back", gidan baya ya buďe mata ta shiga sannan ya zagaya ya buďe ya shiga shima, babu abinda zuciyan Batuul yake sai faďuwa, hawayen da take ta k'ok'arin mayarwa yaqi tsayawa sai ma daďa zubowa yake, sau ďaya ya kalleta ya ďauke kanshi, har sukayi nisa bata dena kukan ba, ranshi ya gama b'aci sosai, juyowa yayi yana kallon yadda take ta sheshek'a kuka, hannu yasa ya kama kafaďunta yace "Behave! Kinaji na ko, tun farko i gave you option, da kin buďi baki kince bakyaso am sure babu mai miki dole, but kikayi kunnen k'ashi shine yanxu zaki dameni da kuka", jajayen idanunta da suka rine ta ďago ta kalleshi taga shima idonshi akanta yake, hannunshi dake kafaďunta ta ture taja da baya tana goge hawayen fuskarta, kallonta ya tsaya yi da mamaki daga baya yayi k'wafa ya juya jin wayarshi na k'ara, iska ya ďan furzar daga bakinshi ganin mai k'iranshi, recieving yayi tare da sawa a kunnenshi a hnkli yace "Babe am back", wani irin k'ara tasa da har ya sashi cirewa daga kunnenshi tukunna ya mayar yace "Hae chill ba sai kinzo ba ina hanyan dawowa ko David ban faďawa muna hanya ba", da mamaki a ranta tace suna hanya kuma, shi da waye? oho ko ma dai waye shi ya sani, abunda ta shirya mishin in yaso duk munafikin da ya biyoshi shi ya sani ya faďa musu, da sauri ta kawar da tunanin tace "Baby ai da ka faďamin da ko breakfast nayi maka, but ban tashi ba ina bacci har yanxu, babe kazo min da Domino's pepperoni Pizza da Cold stone Ice cream tunda akwai a hanya dashi nakeson yin breakfast", kai ya girgiza yana mamakin halin Ajiddeh, ko yaushe ma ta iya girkin da har zata ce wai da ya faďa mata tayi mishi breakfast, ya sauke ajiyar xuciya yace "Fine naji, mun kusa isowa gida you should get up from your slumber and get ready", yana iya jiyo murnar da takeyi tace "Right away baby", da haka ya katse k'iran, suna gama wayan ta dirk'o daga kan gadon, straight away garden ta wuce da ďan bingel ďin rigar bacci dake jikinta taje duba kuttun data ajiye, ganin yana nan very safe ta dawo bakin palo dan tun ranan da ta dawo zuba abin ba ayi shara a gidan ba sai bayan ta aiwatar da abinda tayi niyya, sai da tabbata komai daidai ta koma cikin gida tayi wanka ta sako wata y'ar crop top da bum short, sosai ta gyara dogon gashinta ta baďe jikinta da turare ta koma ta kwanta, Batuul kam banda bugu babu abinda zuciyarta keyi, haďuwarta da Ajiddeh ba wani mai yawa bane tasan babu abin arzikin da ya taba haďata da ita in banda hararta da takeyi kullum in sun hadu, maganganun da Ammah tayi mata ne suka dinga dawo mata kai, Ammah tace mata kar ta yadda su rainata, yes hakane baza ta yadda su rainata ba, toh ita inama ruwanta da ita ne, ba sai ta kulata bane bama zata rainata, ďan tsaki taja ba tare da ta san tayi hkn ba, juyowa yayi yana kallonta jin tsakin da tayi, ganin za a wuce Domino's yasa shi cewa driver ya tsaya, parking driver yayi ya fita ya shiga Domino's bayan 10 mins ya fito rik'e da kwalaye a hannunshi na pizza da ledan Ice cream, kanta na daga jikin window tana ta kalle kallenta ta ďago tana kallonshi, wani irin relief yaji ganin idonta ba hawaye, shiga yayi ya zauna driver ya tada motar suka tafi, tafiyar 8mins suka isa anguwansu, gini ne uniformly masu kyau duk iri ďaya da red bricks, bambancin wani da wani kawai motocin dake pake ko kuma yadda flowers ďin ke jere, bin ko ina da kallo ta rik'ayi zuciyanta na ci gaba da bugawa, har compound ďin driver yayi parking, tsayawa yayi yana kallonta bayan ya fito daga motan ganin taqi fitowa yace "you can come out, ba motata bace", ďauke kanta tayi a sanyaye ta fito, ta bi bayan shi, murďa k'ofan palon yayi ya shiga da sallama yana kalle kalle, kan vanity table ďin palon ya ajiye boxes ďin hannunshi, Batuul ta kasa Karasowa cikin falon, Ajiddeh ce ta sauk'o a guje daga kan bene tazo rungume shi da murna tare da lumshe ido, shima ya rungume ta ssae, sam bata lura da Batuul dake bakin kofa ba, cikin muryar shagwaba tace "Babe shine ka daďe a Nigeria ina ta jiranka, ka kawomin pizzan?", idonta ne ya faďa kan vanity table ďin ta juya zata ďauko kwalin cike da murna, cak ta tsaya ganin Batuul a bakin kofa, lkci daya komai ya tsaya mata, zuciyanta ne ya shiga bugawa da sauri da sauri tana kallon Batuul da itama ke kallonta duk

1 Comments On BATUUL
avatar
hafsat-9-3

12 months ago

Reply

Nice book

Please Login or Register in order to submit comment