Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta juyo bayan ta ajiye wayar da take dannawa tace Tabawa fa ko har yanxu aiki take ba à samu tayi wanka ba, Janet tace à ah Aunty taje dakine zatayi wanka, tace okay






Tafiya sukeyi suna ta gaisawa da dimbin jama'ar da suka halarci sallah Massa ya dubi Abutturab ''Man yaushe zaku koma Abuja ne ?
Abutturab ya furzar da iska daga bakinshi sannan yace " Yeah i want to leave in the next four days dan inada appointment da Minister amma nasan su Abui sai next week cuz su sai Sun gama sallah anan. I cant wait that long"
"Massa yace okay nima sai next week din zan shigo ", suna tafiya har suka iso inda su Abui suke, Abui ne ya Juyo ya dubesu tare da cewa mutumin da suke tsaye tare, "ai gasu nan ma", mutumin ne ya fadada murmushinshi tare da fadin "Masha Allah" ya miqa musu hannu suka gaisa, yacewa Abui "Its been long i met them , almost 19 yrs nasan bazasu tunani bama, anyway ya kuke ? Ana karatu ko kuma an gama ? Ko kuma aure za Ayine ya fadi maganar tare da dariya ? " , take fuskan Abuturrab ya canza dan baya so ana mishi maganan aure in Abui na kusa , yanxun nan zai tada maganar har sai ya dinga magiya taré da bashi hakuri





Abui ne ya bawa mutumin ansa tare da fadin "ai aure kam sunqi shi, Shi Aliyu(Abutturab) architect ne dan yanxu ma yana da contact da minister Abuja, Mustapha(Massa) kuma Doctor ne tunda yayi karatu à Germany sukayi retaining dinshi, but munaso ya dawo dan baza mu barshi cikin turawa ba", mutumin yace "gaskiya kam, Allah ya taimaka. " *Alai*(Alhaji) Ahmad Kyaree zan wuce yanxu dan nasan su Madam suna jira, tare mukazo dasu kuma ga ruwan da akeyi, zan kawosu before ku koma in sha Allah " , Abui yace okay à gaidamin su, ace musu muma muna nan zuwa.





Tunda mutumin ya fara magana Abutturab bai dago kanshi ba har sai da mutumin ya fara maganan aure, a snn ne ya dago kanshi ya k'arewa mutumin kallo har yaso gano inda ya sanshi amma ya kasa, sai cewa Abui yayi bayan mutumin ya karasa barin wajen, " Abui is he an old friend"?

"Yeah à good one too inji Abui ", tare da basu labarin tare da ce musu su tafi kamin ruwan ya kara yawa "






Ta miqe kenan tana cewa Aunty zata haura dakinta tayi wanka ta canxa kaya dan Sun jike ta hango Babanta na saukowa daga bene, da gudu taje ta rungumeshi, "tace Baa yanxu nakeso inje wajenka, ya d'an janyeta daga jikinshi yana tambayarta




"Batuul ya kayanki à jike" ? "Tace Baa ai anyi ruwa à waje ku tun dazu kuka dawo ko ? Ya sake ce mata "Batuul yanxu sallahn Allah shine kika saka baqin kayan nan kikaje har masallaci dashi ? Batuul ta danyi kasa da ido ta zumburo karamin bakinta kamin tace "Baa sabone fa kuma designer ne na Hauté Èlan kai ka siyomin mafa " , yace mata "toh naji maza Je ki cire su kar kiyi mura, tayi murmushi tace yanxu zan dawo ai, ta haura sama shi kuma ya karasa saukowa kasa .






Har ta wuce wani daki à sama sai kuma ta dawo daga baya, cikin sand'a ta bude kofar dakin, a hankali take turawa, sai da ya fara karane ta bude shi gaba daya tana fadin Taraan, yara ne maza a dakin su biyar, kowa da game controller a hannunshi suna ta ihu,typical dakine na maza da akayi littering gwangwanaye drinks, kayansu da suka cire daga k'asa, gadajen à hargitse sai plates din abinci da spoons.Yan manyan guda biyu da baza su wuce 13-15 yrs ba sanye suke da wandunan shadda sai fararen vest à jikinsu hannunsu kuma maqale da agogo, sai mai bi musu shi kuma sanye yake da complète kaftan dinshi brown harda hula akanshi ya tsaya akan sofa yana ihun ni zanyi winning, dayan kuma sanye yake da three quarter da T-shirt shima yana riqe da game controller, karamin cikinsu ne snn duk yafisu haske yana daga gefe riqe da Ipad à hannunshi yana ta aikin dannawa, Suna ganinta suka yadda abubuwan dake hannunsu, Manya ukun na ihun Aunty ta dawo kanana biyun kuma suna cewa Mama ta dawo, a guje suka fito kowa na rige rigen ya riga dan uwanshi fita daga dakin, Da sauri Baatul ta matsa daga bakin kofa dan kar su bigeta tana ta dariya ta juya ta bar kofar dakin ta karasa nata dakin ta murda kofan ta shiga.
💖💝BATUUL💖💝






5






By phartiemarhk






Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*






Tana shiga daki ta nufi inda towels dinta ke rataye, ta janyo daya sannan ta cire kayan jikinta da suka jiqe, ta daura towel din a kirjinta, ta nufi toilet din dake dakin nata, bayan minti goma ta fito tana kanshin shower gel da sabulun Makari,da towel a jikinta daya kuma a daure a kanta kamar turban, gashin goshinta ya kwanta lub lub, fuskanta ya kara haske da kyau, ta karaso gaban mirror dake cike da turararruka da yan kayan kwalliya da na shafa , ta jawo stool din mirror ta zauna sannan ta dauko man Makari, a hankali ta riqa shafa man kamar baza ta gama ba, bayan ta gama ne ta karasa gaban closet din kayanta, ta bude ta dauko peplum blouse da skirt din atamfa baqi mai pattern din purple ta saka à jikinta, kayan ba karamin kyau yayiwa jikinta ba, komawa gaban madubin tayi ta shafa powder a fuskarta sannan ta saka kwalli a idonta, ta shafa nude lipstick a bakinta , ta bude costume box dinta dake kan madubin daga gefe ta dauko dankunne da sarka silver masu duwatsu a jiki, sai abun hannu da zobe shima silver, sannan ta fesa turare, ta kalli kanta a madubin tare da murmushi sannan ta koma ta zauna a kan gadonta tare da d'aukan wayanta,





bayan ta d'an daddana wayan ne ta kara à kunne tare da fadin "Hello Riri, shine kikace min a Ramat Square zakuyi sallah, kuma bakije ba,
Daga daya bangare aka amsa ana dariya tare da fadin


"Yo babe nan naje mana, i wanted calling you inji inda kike sai sai da na duba wayana naga ban fito dashi ba, You know anytime Yaa Abu na gida toh komai nawa doesnt seems to be ryt"



"Batuul tace babu wani Yaa Abu, anytime kika samu matsala sai kice shine, toh duk ranar da zan ganshi sai na fada mishi



"Riri tayi dariya,tace mata dan baki sanshi bane ai, koh face dinshi idan kika gani zakiga ko smiling bayayi, brows dinshi kullum a hade, bayayiwa mutane ma magana wai surutu na saka mishi ciwon kai, kuma ko bashi zaiyi ba wai baza ayi a kusa dashi ba,




"Batuul tace all these apart, ni zanzo yau dan Baa yace nan da kwana hudu zamu koma dan yana da aiki sosai kuma gobe da jibi zamuje wajen su Yayya da sauran Family




"Riri tace yawwa bae of earth,daman ina ta tunanin yadda zan ganki, I missed you soo much wlhy, kizo yanxu i have have So many things for you alone, Batuul tayi dariya tace
"You are not serious, ai sai na fadawa Baba tukunna, sai yayi approving zuwana




"Riri ce ta marairaice murya hade da cewa nasan Baba zai barki sai dai in kece bakison zuwa, pls kizo, am bored over here, kuma kinsan Yaa Abun in yana nan ba a yawo "




"Batuul ce ta cemata ni ba ruwana and i told you zan fada mishi whenever i meet him"



"Ai bazaki iya ba nasanki, I wish zaki zo yana nan shima yaga wanda ya fishi rashin magana,ai mantawa ma nayi halinku daya nake fada miki



"Ni dai yanxu a bar maganan, yanxu zanje in fadawa su Aunty zanzo wajenki ,


"Aii sai kinxo"



sannan suka katse wayan, tashi tayi ta jona wayan a caji ta juya ta fito daga dakin, har ta karaso kasa, ta sauka daga benen ta jiyo muryoyin yan gidan a dinning suna cin abinci, karasowa tayi wajensu, Mahir na ganinta yace Yaa Batuul kinyi kyau, Hafix ma yabishi yace kinyi kyau, tayi murmushi tace musu nagode, kuyi shiru ku gama cin abinci,



kujera itama taja ta zauna a gefen Baba daga hagu, Baba ne ya ce mata


"kinga kayan nan yayi miki kyau amma ba kiyi ta saka baqin kaya ba a kowane occasion",




Aunty ce tace ai Y'ar kauye ce,"



ta juyo ta dubi Baba tai raurau da ido, yana ganin haka ya yace



"À ah Mamana ba y'ar kauye bace, ai kayan nayi mata kyau" ko ? ya tambayeta ,murmushi tayi sannan ta dauki plate, ta janyo wani babban tray da aka rufe da foil paper ta bude,Danderu ne na kaza yana ta tiriri da kanshin kayan yaji, kadan ta saka à plate din sannan ta sake janyo wani food flask din ta dauki masa daya a ciki tare da miyar masa, a hankali ta riqa ci ba tare da cewa komai ba har suka gama




Sun gama cin abincin ne suka tashi suka koma palo, Fa'iza da Janet ne suka zo suka gyara dinning din tare da kara turaren wuta à duka electric burners din gidan



Sai da kowa ya zauna ya nutsu sannan ta dubi Baba tace



"Baa inason inje wajen Farida tunda gobe da jibi we Will ne busy,


"Okay what time zakije ?



Cewa tayi "ko yanxu tunda naga its already after 12"




" Tunda su Baa Liman(Driver)suna hutu sai Ahmad ya kaiki dan ya fiki iya driving kuma bana Son kina driving ke kadai especially a Maiduguri da ba a bin régulations din driving "



"Okay Baa nagode, " Aunty dai bata ce komai tunda Baba ya yadda shikenan. Tashi tayi ta k'ara haurawa sama ta dauko jakarta ta channel purple shima irin kayan da karamin gyale shima purple amma light, ta kara duba fuskanta a mirror sannan ta sauko



Tana saukowa taga Ahmad riqe da key din mota a hannunshi yana jiranta, karasowa tayi ta ce wa su Baba zasu tafi, "



yayi musu sai sun dawo sannan yace mata idan ta gama sai ta kira a zo a dauketa, tace toh",




Tacewa Aunty sai Sun dawo, Aunty tace mata ki gaishe da Ammah kice mata nima zanzo ko bayan mun koma Abuja ne, Toh tace sannan suka fita suka nufi inda akayi parking motocin gidan suka shiga wata Audi fara sol, Ahmad ne ya tambayeta anguwan da zasu bayan yayiwa mai gadi horn kamin yazo ya bude mishi kofan, ce mishi tayi Old GRA ne in munje zan nuna maka hanya, Ya juyo yace mata




"Yaa Batuul Allah kwatancanki akwai wahala yanxu sai mu kai two hours muna neman wajen da baifi muje a 20 mins ba "



"Tace toh ka bani inyi driving"



baice mata komai ba yaja motan suka bar gidan bayan mai gadin yayi musu a dawo lafiya









Tafiyan minti goma sha biyar suka isa gidansu Farida a old GRA ,Horn yayi aka bude musu gate suka shiga, suna shiga gidan bugun zuciyanta ya karu, ambaton Allah ta riqa yi har sai da taji ya dan ragu sannan ta bude motan ta fito daga ciki tare da yiwa Ahmad sai anjima akan in ta gama zata kirashi




Farida na Jin tsayuwar mota ta fito daga cikin gida a guje tazo ta rungume Batuul ta na ihun i missed you so much babe,




"Batuul ce tace mata sakeni kar ki ballani Baba ya hanani zuwa nan gaba"



Dariya tayi sannan tace nasan Baba bazai hanaki zuwa sai dai in ke zaki min halin naki ki qi zuwa, Batuul batace komai ba har suka karasa ciki ,tacewa Farida Ammah da Abui da Sadiq fa ?





"Ammah da Sadiq basu dawo ba inaga Sun tsaya wajen Ayyi, Abui yana Shehuri, Nida Yaa Abu ne a gida kawai shima yana sama,



Batuul tace "okay",



sama suka haura suka isa dakin Faridan, suna shiga ta cire gyalenta ta ajiye a akan gadon ta juya inda fridge din dakin yake zata dauki Fanta, tana budewa taga babu Fanta à fridge din, "kinsan zanzo shine baki saka Fanta a Fridge dinki bako, sai tarin bakaken drinks da kika ajiyewa mutane(coke),ni na sauka fridge din kasa in dauko, batajira jin abinda Farida zata ce mata ba ta sauka ta isa dinning area ta bude standing fridge din zata dauki Fanta taji wata Murya cikin sanyi an Ce "Farida kawomin bottle water daya", bugun zuciyantane ya k'ara tsananta, Bata juyo ba kuma batayi magana ba har sai da ya k'ara maimaita maganar amma yaji shiru, ransa ne ya b'aci ya taso yaga abinda takeyi da har ya hanata amsa mishi, yana zuwa ya fizgota da k'arfi da har saida ta fada kirjinshi kamin yayi sauri ya janyeta
💖💝BATUUL💖💝






6





By phartiemarhk





Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*





tsayawa yayi ya na kallonta ita kuma kanta à kasa, ba a Jin komai sai bugun zuciyanta da ya kara tsananta, riqon da yayi mata ne da kuma bugun zuciyanta yasa hawaye taruwa à idonta, kiciniyar kwace kanta ta fara yi daga wajenshi amma yaki saketa, Dumi yaji a hannunshi ya juya yabi hannun nashi da kallo, hawayen da ya gani ne yasa shi sakinta a hankali ya juya mata baya, juyowa ya sakeyi zai yi mata magana yaga bata wajen,



Parlour ya koma zauna yabi stairs din da ta hau da kallo, lokaci daya ya shiga kwada ma Farida qira, A bakin kofa ta kusa cin karo da Farida, Farida tace "kinga abinda nake gaya maki, I Wonder why he is calling me yanxu" bata karashe maganan ba ta ta riqe Baatul tana tambayarta "Why are you sore ? Mey ya sameki kuma idonki ya canja , kamin ta bata answer ta sukaji ya sake kwada ma Farida kira, bata jira cewan Batuul ba ta sauka kasa tace "Gani Yaa Abu" a nutse yace "Who is she ? I mean that lady, doesnt she talk ko kuma gaisuwa ne bata iya ba ? A zuciyanta cewa tayi "Innalillahi wa inna illaihi rajiun, Yaa Abun nan komai ba a yi mishi daidai, in nayi magana yace na cika surutu, yanxu kuma Batuul bata yi magana ba zaiyi fada" Tana cikin tunanin taji yace "am i not asking you ?"
"No Yaa Abu bata jin dadi ne shiyasa bata gaisheka ba, Ce mata ya sakeyi "daga ina take"? "Batuul cefa kawata tun muna Centagon wacce ka kaini gidansu a Maitama last year da ka dawo har kace bazan kwana ba",



Hannu ya daga mata alaman ya isa,


"ki miqomin ruwa a fridge", a kan center Table din gabanshi ta ajiye ta juya ta bar falon





D'aki ta nufa, tana shiga ta tarar da Batuul à tsaye tana riqe da jaka da gyalenta a hannu, "Zan tafi gida"




"Ban gane zaki tafi ba saboda mey" Farida ta tambaya , Yaa Abu yayi miki fada ne dan nasanshi da yiwa mutane fada, "Ni baiyi min komai ba kawai zan tafi ne"

"In kinje toh mey zaki cewa Aunty ya dawo dake bayan kince har dare zaki kai " kuma in Ammah ta dawo mey zan fada mata ? That kinzo har kin koma ? If Yaa Abune baza mu sake bin hanyan da yake ba nima haka yake min



"Toh naji bazan tafi ba amma baza muje inda yake ba " Farida ta kyalkyale da dariya tace,




"Keh da kika ce zaki fada mishi ina gulman shi yanxu kuma ke da kanki zaki qi bin hanyan da yake "




"Ni ki rabu dani, kuma ai ni babu abinda yayi min kuma zan fada mishi din ai", haka suka ci gaba da hira har Batuul ta manta da Abutturab na gidan






Yana zaune a palo bayan ya kurbi ruwan da Farida ta miqo mishi, tunani yayi na lokacin da Baatul ta bigeshi a masallaci da yadda tace mishi sorry har yanxu da ta zo gidansu yaga hawaye a idonta, hawayen da ya tuna ne ya sashi ajiye ruwan yana fadin "Damn it" à hankali, "does shi always cry"? Yana cikin tunanin yaji an bude kofan palon , Ammah ce tare da Sadiq a bayanta suka shigo suna hira, ciki suka karaso suka zauna a palon, Abu ne yayi musu sannu da zuwa, Ammah ce tace "baku tsaya anyi hawa bane da ku "? "Ehh naso mu zauna sai kuma na fasa amma Abui yana can" , "Muma munje mun duba Ayyi ne, sannan ta kwalawa Fanne kira,cikin hanzari Fanne ta karaso tacewa Ammah "sannu da zuwa,Gani"
"kije ki duba min Farida kice mata mun dawo, sama Fanne ta haura ta fadawa Farida sakon da aka bata sannan ta fita, Farida tacewa Batuul "muje ki gaida Ammah nasan baza ta hawo palon sama ba shiyasa ta sa a fadamin"



"Ni sai kinje kin duba in Yaa Abu baya palo tukunna zanzo"
"Farida tace you are kidding me,taso mu tafi ai in Ammah tana nan bazai yi komai ba" Hannun ta Farida ta jawo suka sauko k'asa, lokaci daya ta d'ago kanta suka hada ido hudu dashi, ta dauke nata da sauri ta karaso cikin falon ba tare da ta kallesa ba suka iso gun Ammah, Farida da gudu ta karasa gun Ammah tana fadin "shine Ammah kuka qi dawowa da wuri inata jiran ku, Ammah bata yi mata magana sai Batuul da ta cewa " A ah Batuul yaushe kikazo, su Aunty na lafiya ? Ashe kunxo, Aunty da mukayi waya tace mayb baza ku zo ba dan Baba na aiki, anyi sallah lafiya ? Batuul da murmushi a fuskanta ta k'arasa wajen Ammah ta zauna daga k'asa sannan tace Alhamdulillah, ta tambayeta ta karfin jiki, "Alhamdulillah Batuul, kun gama karatu lafiya ? Next two weeks zakuyi graduation dinku ko ? Da "Eh" ta amsawa Ammah, Ammah tace "Allah yasa kuyi a sa'a, suka amsa da Amin dukkansu, Sadiq ne ya cewa Batuul "Wane school kikayi applying admission ne , ko har yanxu oxford din zakije ya k'arasa maganan yana dariya, Batuul tace " ban sani ba ko Baba nan yake nema min but if ban samu ba may Baze ko Nile zai kaini dan bayason inyi nisa, Sadiq yace "ai dama oxford makaranta masu ilimine ko da yake ai kema kina da ilimi you can do it", tayi murmushi tace kai Yaa sadiq"


Abutturab na zaune yana kallon TV amma duk hankalinshi yana kansu, tunani yake yaushe ma suka santa and everything about her,wai har Sadiq ma yasan makarantar da take son zuwa, tab'e baki yayi ya ci gaba da kallonshi, Ammah ce ta tashi ta hau sama, yan matan ma suka bita, da ido ya bi bayanta har saidai suka shige ciki






7:20 na dare duka y'an gidan na kan dinning suna dinner,Abutturab ne kadai baya nan Ammah ce ta tacewa Batuul "kwana zakiyi amma ko" Batuul tace "a ah Amma zan tafi yau, yanxu ma Ahmad nake kira baya picking, shi zaizo daukana Ammah tace , "No ai ba sai kin kirashi ba , gasu Sadiq sai su mayar dake bari a gama dinner, Toh kawai tace dan batason yiwa Ammah musu





Abui ne yace "su tafi da Abutturab dan yanxu zamu fita da Sadiq", mik'ewa yayi yacewa Batuul in taje gida ta gaida Baba, tace mishi yayi ta trying number dinshi its not going" Ta amsawa Abui da "Toh" sannan ya ciro rafar kud'i daga aljihunshi yace ga Barka da sallahn ta nan,tayi godiya.




Saukowa yayi daga stairs sanye da grey sweats da farin shirt hannunshi rik'e da key din mota, Ammah ce ta tareshi tana tambayanshi inda zashi,yace mata shehuri zashi, Ammah tace mishi "zakayi droping Batuul a gida , shi ya manta da yarinyar ma saida Ammah ta ambaci sunanta , cewa Ammah yayi "Sadiq fa baya nan ne, "tace sun fita da Abui, iska ya fitar daga bakin shu snn yacewa Ammah " a kirata mu tafi, am in a hurry, Fanne Ammah ta kwadawa kira tace taje ta kira mata Batuul ace ta fito su tafi, fitowa tayi bayan Fanne ta fada musu sakon Ammah, wannan karon babu gwagwaro a kanta sai gyalen kawai ta yafa,tana saukowa Ammah ta tambayeta ta shirya ? Tace "ehh" Toh ga Abu nan zai kaiki gida" Ido ta wara ta dubi inda Abun ke zaune yana jiranta
💖💝BATUUL💖💝






7





By phartiemarhk





Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*





A hankali take tafiya sabida yadda bugun zuciyanta ke k'aruwa, tana zuwa bakin k'ofa ta juyo ta kalli Farida da pleading eyes ko zata rakata amma sai taga tana d'aga mata hannu da wide smile a fuskanta, Ammah ta sake juyawa ta duba taga ko tana wajen, itama hannu ta d'aga mata tare da mata murmushi, horn dinshi ta sake ji da k'arfi , murda kofan tayi ta fita daga palon har ta k'arasa wajen da motocin gidan ke pake, rasa wanne motan yake ciki tayi sai da taga ya dallo hasken motan daidai inda take tsaye tukunna ta k'arasa amma bata bud'e ba, tsayawa ta sakeyi tana contemplating gaba zata shiga ko baya ? Ranshi ne yayi mugun b'aci ya sake danno mata horn din da k'arfi, kofan dake gaba na gefen driver ta bud'e ta zauna ba tare da tace mishi uffan ba, tada motar yayi sai da sukaje gaban gate kamin mai gadi ya bud'e mishi gate bayan yayi mishi horn ne ya jeho mata tambaya ba tare da ya dubi inda take ba yace "wane anguwane", a hankali cikin sanyin magana tace mishi "Lagos street", tambayanta ya sakeyi " Which side of Lagos street? , "In munje area din zan nuna maka" Baisan Lokacin da ya juyo ya watso mata wani irin kallo ba, a ranshi fadi yake "Is she kidding me, muje zata nunamin, bata san ma hanyan gidansu ba kenan" bai ce mata komai ba ya fita daga gate din gidan ya d'au hanyan anguwan da ta fada mishi, tafiya sukeyi babu wanda ke cewa kowa komai sai k'ira'ar Juhanny dake karanta suratul Qasas da k'arar air conditioner, gaba daya hankalinshi na kan tukin da yake , Batuul kam skirt din jikinta ta riqe da k'arfi har hannunta na yin gumi saboda kwata kwata she is not comfortable, Allah Allah take su k'arasa gida, wani hanyan Lagos street din yabi wanda bata tab'a bi ba har suka isa, suna zuwa ya sake tambayanta " Ta ina gidan yake" juyawa tayi tabi window motar da kallo taga bata san wajen ba, a hankali tace mishi " ba nan bane fa" , wani kallon ya sake watso mata wanda yayi saurin sata sadda kai k'asa , tare da gangarawa gefen titi ya tsaida motan, dago kanta tayi taga ita yake kallo yana jira ta k'ara yi mishi bayanin ina ne idan ba nan ba, ce mishi tayi "Ni ban taba ganin nan ba a anguwanmu, mu koma gidanku sai in nuna maka daga farko inda hanyan gidanmu yake ko kuma in qira Ahmad sai ya d'aukeni a can" sai da ya bari ta gama magana bai ce mata komai ba sannan ya tada motan yaci gaba da tafiya, tsaki yayi tare da duba agogo yaga k'arfe takwas 8 daidai, Sun kusa minti talatin suna yawon neman hanyan gidan basu samu ba, ita dai babu abinda takeyi sai addu'a gashi tana ta k'iran number Ahmda baya d'auka, sai da ya gaji da yawon neman tukunna ya

1 Comments On BATUUL
avatar
hafsat-9-3

12 months ago

Reply

Nice book

Please Login or Register in order to submit comment