Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zuciyanta keyi sae double flips lkci daya jikinta ya dau rawa, bakinshi ya kawo daidai kunnenta, a hankali kamar me rad'a yace "nan zaki bar kayan naki har sai ranan da matata ta yadda ki zama co_wife d'inta, batace mishi komai ba sai ma hawayen dake dad'a taruwa idonta, jin tayi shiru yasa ya juyo da ita, hawayen da ya gani idonta yasashi yin murmushi yace "kukan meye zakiyi kuma?", lumshe idonta tayi hawayen dake tare ciki ya shiga gangarowa, murmushi yayi yasa hannu yana goge mata hawayen da ya zubo mata, hannunshi ne ya kai kan lips d'inta masu d'umi, wani irin shock taji yabi spine d'inta kuma har lokacin bata bud'e ido ba, a hankali ya shiga zagaye lips d'in nata da hannunshi, har ya sunkuyo ya kaj bakinshi dai dai nata har tana iya jiyo sauk'ar numfashinshi kan fuskanta, kirjinta sai heaving yake, ta kuma ki bude ido, ko me ya tuna sai kuma ya mike ya kamo hannunta, sai a lokacin ta iya bud'e idanuwanta ta ganshi tsaye, mik'ar da ita yayi, ba musu tabi bayanshi har sai da suka sauk'o k'asa, sai da suka s
[8/22, 14:49] Umar Dalha: πŸ’–πŸ’BATUULπŸ’–πŸ’





58






By phartiemarhk




Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*





Murmushi yayi ya d'auke idonshi daga kanta, abincin dake gabanshi yaci gaba da ci, sae kuma ya ajiye fork d'in hannunshi ya juyo da wani irin smirk a fuskanshi ya sake matso da ita jikinshi yace "you didn't tell me, are you still on your period", tsoron tambayar ne ya kamata amma ta dake ta tsuke d'an k'aramin bakinta tace "nima ban sani ba", yanda tayi maganan ne ya bashi dariya, hannunshi ya d'aura kan mararta yace "Lemme check to see if you are still on it tunda kince keh baki sani ba", a razane ta yar da fork d'in dake hannunta ta zaro ido ta d'aura k'aramin hannunta kan nashi ta rik'e tace "Yaa Abu am still on it, kayi hak'uri, bai bi takanta ba yaci gaba da abinda yakeyi, kallon kyakyawan fuskanta da ya jik'e da hawaye yayi, yayi murmushi yace "Toh ai kema ba sani kikayi ba, kinga I should check for us both", babu abinda jikinta keyi in ba rawa ba, rintse ido tayi tana hawaye jikinta ya dau rawa jin yadda hannunshi ke yawo kan mararta, gaba d'aya jikinta ya saki, a hankali ya shiga daddana mata mara, hannu tasa ta sake rik'e mishi hannu, ido a rintse tace "Yaa Abu dan girman Allah ka bari, nace maka am still on it, yana min ciwo", murmushi yayi yace "dama doctor yace ayi massaging lower abdomen if it hurts, shi nake miki to reduce d pain", a hankali hawayen suka ci gaba da kwararowa, ji tayi kawai ya d'auketa cak, wara ido tayi ta shiga wutsil wutsil, wani irin kallo ya sakar mata yace "I will slap yhu in baki tsaya ba, da kinsan you are on it kika ce min baki sani ba, yanzun nan zan sake ki ki fad'i k'asa", shiru tayi jin yace zai saketa, bata bud'e ido ba saida taji ya direta kan lallausan gado, a hankali ta bude idonta tana kallon fuskanshi, tashi tayi da sauri ta zauna tana goge hawayen dake fuskanta da bayan hannu, muryarta na rawa tace "Yaa Abu nace kayi hak'uri fa, ", ta fad'a tana marairaice fuska, dariya ta bashi yanda tayi maganan ya zauna daga gefenta ya hade rai yana kallon fuskanta yace "kukan meye kike min", kin cewa komae tayi ya fixgota ta fad'a jikinshi, wani sabon kukan ta fashe da tace "ni wllh zan fad'awa Ammah", dariya sosai yayi yace "da kika nace aka aura min keh, sai kicewa Ammah meye"?, sadda kanta tayi k'asa ta mayar kan cinyarta, dabara ne ya fad'o mata ta d'ago kai ta kalleshi, suna had'a ido ta d'auke nata tareda juya kanta ta hade rai tace "toh zan fad'awa Ajiddeh ni dae", baisan lokacin da ya tuntsire da dariya ba ya juyo da kanta tana kallonshi, yana rik'e da hab'arta da ta kasa yadda su had'a ido, har lokacin murmushin nan na fuskanshi yace "da kinbar gidanta a yau ba sae gobe ba kuwa", bata kulashi ba yace "ko don kinga har ta fara kulaki", jin yayi shiru ta d'ago ta kalleshi taga ita yake kallo, ya daga kafada yaci gaba "in kin shirya barin gidanta sai ki fad'a mata in kin k'oma" mik'ewa yayi ya isa wani k'ofa, a jikin bangon ya danna abu k'ofan ya bud'e, shigewa yayi ciki, sai lokacin Batuul ta d'ago rinannun idanuwanta, d'akin ta shiga k'arewa kallo, Babba ne sosai da makeken walk-in closet d'in distressed raw wood da ya cinye side d'aya, daga gefe shelf d'in takaddu ne, sae wani sculptural rope lamp da ya sauk'o daga gefen shelf d'in, sai lokacin ta juya ta kalli gadon da take, traditional bed ne, makekene sosai da wasu brass lamps da suka bada wani irin unified look, da extra reading light, sai wasu faux leather headboard kujeru biyu daga gefe suna facing juna, hankali idonta ya fad'a kan crispy curtains, da glass d'in dake bayan curtains d'in, tab'e baki tayi snn a hankali ta mik'e ta isa wajen tare da yaye curtains d'in, numfashinta ne ya kusa d'auke ganin yadda wajen yake, sai a lokacin tasan sama ya hawo da ita, gaba d'aya filin grass ne shimfid'e da ya sha gyara, sai pond d'an madaidaici da swan farare a ciki suna ta shawagi, sai k'ananun kifi duk cikin pond d'in, daga can d'aya side d'in Lazy S-shaped pool ne, da toskana brown lounge kujeru biyu daga gefensu, bataji fitowanshi ba sai jin k'anshin shower gels da sabulun da yayi amfani dasu taji, juyowa tayi suka hada ido, da sauri ta d'auke kanta ganinshi daga shi sai d'an towel, kamin ta matsa daga wajen ya k'araso yasa hannayenshi ya zagayo waist d'inta, a hankali ya sauk'e fuskanshi kan wuyanta, sanyin ruwan dake jikinshi da sauk'ar numfashin shi wuyanta yasata shivering, a hankali yace mata "kina son gidan?" da k'yar ta iya gyad'a mishi jikinta na rawa, kafad'unta ya kama ya juyo da ita tana fuskantarshi, kasa d'ago ido tayi ta kalleshi, hannu yasa ya d'ago hab'arta yace "hmmmm well I built it for my love, my wife, kin santa?" ya tambayeta yana kallon cute face d'inta, batasan lokacin da ta murgud'a d'an k'aramin bakinta ba ta tsuke fuska ta dauke kai, murmushi yayi ya kuma juyo da fuskarta, d'aura d'an yatsanshi kan lips d'inta yayi yace "I like it when you twist your lips", a hankali ya sunkuyo ya lumshe ido yayi wa lips d'inta light kiss, lumshe ido tayi ita ma jin lips d'inshi kan nata, sai da ya d'ago yana kallonta yace "zaki sani sabon wanka ko", a hankali ta d'ago idanuwanta jin abinda yace eyes d'insu yayi locking, da sauri tayi k'asa da Kai, saketa yayi ya juya ya isa inda closet d'in yake, bayanshi tabi da kallo a xuciyarta tace is this the Abuturrab she knw, lallai namiji bashi da kunya, tab'e baki tayi tana kallon broad figure d'inshi, jiki a sanyaye ta sake curtains d'in ta dawo kan gadon ta zauna, kanta a k'asa har ya gama sa kayanshi ya tada sallah, tana nan zaune har ya idar, sai da ya mik'e daga kan abin sallah yace mata "Let's get going, nasan matata na nan tana jirana", tsuke fuska tayi ta mike ta nufi kofa, bin bayanta yayi yana murmushi, da mamaki ta dubeshi ganin kwanukan da suka bari gun basa nan, tab'e baki tayi taci gaba da tafiya abunta jin baice mata komai ba, Hijab d'inta dake kan sofa ta d'auka ta zira tabi bayanshi har suka fito inda yayi parking, da kanta ta bud'e gidan gaba ta shiga, takurewa tayi jin sanyin ACn dake kunne, observing d'inta da yayi yasa shi controlling temperature, hannunta na hagu ya kamo a hankali ya shiga murzawa, ta fixge hannunta don ta gama gano sa yanxu, jikinta kawae yake so kuma baxata bashi ba.





Sai da suka shigo gida hankalinta ya fara tashi, Abu kam ko a jikinshi kai tsaye ya shiga cikin gidan ta bi bayansa kamar munafuka, Ajiyar zuciya ta sauk'e ganin Ajiddeh bata palon ta nufi sama da gudu, murmushi yayi dan yasan gudun mey takeyi shima ya haura sama, dakinsa ya shiga ya fada kan gado ya lumshe ido, murmushi kawae yake ba tare da yasan dalili ba.





(Sorry πŸ™‡ for d short chappy sisters, I got test to write tomorrow, wish me luck πŸ€, I promise to update you guys tomorrow In sha Allah)
[8/22, 14:50] Umar Dalha: πŸ’–πŸ’BATUULπŸ’–πŸ’

59

By phartiemarhk

Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*

Da mamaki Ajiddeh ke dubanshi daga bakin k'ofa ganin ya dawo da wani kayan ba da wanda ya fita ba, kuma tun biyar ya fita yace mata yanzun nan zaije ya dawo amma sai Yanzu yake shigowa, ga shegiyar nan ma tun d'azu take mata knocking taqi bud'e mata k'ofa, tsaki tayi ta k'arasa shigowa d'akin, kai tsaye gadon da yake kai ta nufa ta zauna daidai kanshi ta shiga tashin shi, a hankali ya bud'e lumsassun idanuwanshi ya d'aura kanta, had'e rai tayi a dole ya b'ata mata rai tace "Aliyu tun yaushe ka fita ka barni gidan nan, daga cewa yanzu zakaje ka dawo shine ka shanya ni nan", murmushin shi mai narkar mata da zuciya yayi ya riqo hannunta ya janyota jikinshi, a hankali ya d'aura bakinshi daidai kunnenta cikin rad'a yace mata "keh wai baki iya kula da miji ba?, ba girki, ba gyaran gida, babu tsaftace ko ina sai kanki kawae, amma kinfi kowa iya mita, a haka ake nuna son?", jikin tane yayi sanyi jin abinda ya fad'a mata, toh me kuma ya kawo wannan maganan, d'ago kanta tayi ta kalli fuskanshi taga idonshi na lumshe ne har lkcn, rolling idanunta tayi a ranta tace kai ka sani, har lokacin idonshi lumshe ya sake jawota ta fad'o jikinshi yaci gaba da cewa "ko kinaso in samo wacce zata na yi min dukka wannan abun kinga kema sai ki koya gunta?", a firgice ta d'ago tana kallonshi tace "mey kake nufi Aliyu", sai a lokacin ya bud'e lumsassun idanunshi ya zuba mata su, murmushi yayi ganin expression d'in dake fuskanta ba tare da ya damu ba yace "sai in qara aure mana, kinga kin samu mai koya miki nima na samu mai bani abinci ba sai ina zuwa restaurants ba", gaba d'aya ji tayi iskan d'akin yayi mata kad'an, hannu tasa ta warware dogon gashinta mai tsayi da laushi tana mishi wani matsiyacin kallo cike da masifa tace "A ina d'in wai zakayi aure, ba dai ina gidan nan ba, wlhy Allah indai da raina baka k'ara aure, sai ina maka girki sannan zaka san ina sonka?, tun farko daga gidanmu ni ban saba da wahala ba shiyasa aka nema min masu aiki kace baka sonsu ka koresu to ya kake son inyi da kai? sai yanxu kuma kace min wani ban Iya komai ba, dama can meye auren, abun da yake ciki ai ina yi maka, shine yanzu zaka tsiro da zancen aure, duk shegiyar ma da tayi gigin aurenka sai na lahanta ta ta rasa mai aurenta wllh", tana huci ta kare maganar, da mamaki yake kallonta, dariya maganarta ya bashi sosae, wai in tans raye bai k'ara aure", kanshi ya kad'a yace "calm down, wannan hargowa tun banyi auren ba, ki bari in nayi sai kiyi using energy d'inki sai kiyi fad'an dagaske", idonta ne ya cicciko da hawaye jin abinda Aliyu ke fad'a mata, a fusace ta mik'e zata bar d'akin yasa hannu ya fizgota ta fad'o kanshi, kokawa ta shigayi dashi a kan ya k'yaleta amma yaqi, ta fashe da wani matsanancin kuka, a hankali ya d'aura bakinshi kan wuyanta ya fara kissing har ya gangaro kan lips d'inta, kasa resisting d'inshi tayi da kokawar da takeyi dashi, lkci daya ta hadiye kukan ta bada Kai.

Batuul na shiga d'aki ta fad'a gado, lumshe ido tayi tana tunanin abinda ya faru yau gaba d'aya, tunda ya sauk'e ta makaranta ya bata kud'i, bud'e mata k'ofa da kuma tafiyansu gidanshi mai kyau da abunda ya dinga yi mata yau, lumshe ido tayi tana tariyo duk event d'in da ya faru yau, wani iri ta dinga jin kanta, gaba daya ta k'asa daina tunawa, jiki a sanyaye ta mik'e ta cire Hijabin jikinta da kayan dake jikinta, jin k'anshin turarenshi jikin kayan yasa ta d'aura rigan kan fuskanta, wani irin weakness taji k'afanta ya fara, a hankali ta koma kan gadon ta zauna har lokacin rigan na fuskanta, a hankali ta cire ta ajiyeshi gefe, da kyar ta mik'e ta janyo towel ta d'aura ta fad'a toilet, nanma tafi 15mins cikin bathtub d'in da ta cika da ruwan zafi, sai da ta gaji da zama dan kanta ta mik'e ta fito daga ciki, alwala tayi ta canja pad d'inta sannan ta fito, gaban vanity table d'inta ta zauna ta shafa mai ta fesa turarukanta masu sanyin kanshi sannan taje closet d'inta ta ciro kayan bacci, short sleeping gown fari da fuskan Panda daga gabanshi ta saka, sai da ta karanta Qur'an a wayarta sannan ta kwanta bacci, ta dde kwance sae juye juye ta ke, da ta bude ido Abuturrab take tunawa, ta rasa dalili, sae kusan midnyt bacci ya d'auketa, washegari kamar yadda ta tashi jiya haka yau ma tayi, da kayan baccin nata ta sauk'o kitchen ta shiga had'a musu breakfast dan 8 take da lecture, pancake paste ta kwab'a sannan tayi strawberry syrup ta tafasa musu fresh milk ta juye a flask, a jikinta taji kamar ana kallonta daga bakin k'ofa, a d'arare ta juyo ta kalli k'ofan, wani irin k'ara ta saki zata bi k'ofan baya ta fita ganinshi tsaye bakin kofar yayi folding arms d'inshi yana kallonta, cikin hanzari ya k'araso cikin kitchen d'in yayi maza ya kamota, babu abinda jikinta yakeyi sai rawa gashi ta kasa barin su hada ido, a hankali ya jawota jikinshi ya rungumeta tsam ganin ta tsorata, patting bayanta ya shiga yi yana rad'a mata subhanallah kunnenta, har sai da yaga b'arin da jikinta keyi ya ragu sannan ya sassauta rik'on da yayi mata yana kallon kyakkyawan fuskarta da hawaye ya ziraro yace "sarkin tsoro, ni d'in kike tsoro, ina zakije da kika sa gudu, ko kamanni na ne ya canja maki?", ya sa yatsanshi yana share mata hawayen, d'an k'aramin bakinta ta turo snn ta d'ago kanta ta kalleshi tace "ni ba tsoro ka bani ba, meye xa ka tsaya a bakin k'ofa kana kallona", dariya maganarta ta bashi amma ya dake ya d'ago fuskarta da ta sauk'ar yace "jiya ma by this time kika tashi?", kanta kawai ta gyad'a mishi, saketa yayi ya koma inda burners d'in suke, pancakes d'in da ta fara soyawa ya tsaya yana kallo, "did you make all this?", ya fad'a tareda juyowa yana kallon fuskanta, a hankali ta gyad'a mishi Kai, d'ayan tukunyar dake kan wutan ya bud'e, aroma d'in ne ya sashi yaja d'an baya yana kallonta yace "wannan ya sunanshi?", wara ido tayi a hankali tace "cream in chicken soup", kai ya gyad'a yana murmushi don ji yayi ta burgesa ba kadan ba, dawowa yayi gabanta yana kallon fuskanta yace "who taught you all this", a tak'aice tace "Aunty", ya daga kafada don yasan amsan kenan, "What time do you have lecture today?", ya tambayeta yana kallonta, tace "8:00", waje ya samu ya zauna kan kujeran island din yana duba kitchen timer yace "and its 6:30 now" "kin iya kunu", mamaki tambayan ya bata a hankali tace mishi " Yeah na iya,wane iri?", murmushi yayi yace "any type", kai ta gyad'a mishi tace "Na iya kunun gyad'a, Mard'om, tsamiya, kanwa, alkama sai Kunun Accha", kai ya gyada alamun he is impressed yace mata "Na gyad'a nake son sha yanxu, zaki iya yi", d'an karyar da kai tayi tace "toh ai babu gyad'an yin kunun", bai ce mata komai ba ya tashi ya isa cabinet d'in ya bud'eshi sannan ya Ciro bucket d'in nik'akk'en gyad'a, da mamaki ta tsaya kallonshi, smiling yayi ganin irin kallon da take mishi yace "Ammah packed everything for me, I love traditional food yhu knw", tab'e baki tayi ta isa Inda bucket d'in yake ta bud'e tare da d'an duk'awa tana duba gyad'an, a hankali bayan ta d'ago ba tare da ta bari sun had'a ido ba tace mishi "zanyi", yana zaune yana kallonta cikin 25mins ta had'a kunun gyad'a mai scrippers, sai da yaga ta gama ta fara kaiwa dinning shima ya fito daga kitchen d'in ya koma Palo, shi yace basai ta share gidan ba yau tunda time ya k'ure, bata ce komae ba ta koma kitchen din don tsaftace ko ina.
Ajiddeh kam K'aran wayanta ne ya tasheta daga bacci, tsaki tayi ta jawo wayar, time ta fara gani taga k'arfe shida da rabi na safe, juyawa tayi taga Abutturab baya d'akin sannan ta d'aga wayan a tsorace ganin mai k'iranta at wannan lokacin, a d'arare tace "Hello Mummy" tana jin tsoron kar ace wani abun ne ya faru a gida, daga d'aya b'angaren Mum tace "kina jina, Malamin nan yace aiki fa bazai yiwu ba sai kina nan kuma yace Cikin kwanaki uku in baki zo ba komai zai iya faruwa da shi kansa bae gano ba, dan haka duk yadda za ayi kisan yadda zaki yi ki iso yau d'innan ba sai gobe ba", a tsorace da jin abinda Mum ta fad'a mata tace "Mum ban san ko zai bari inzo ba", inji Ajiddeh, "kina ma da hankali kuwa, nace miki komai zai Iya faruwa shine kike cemin bazai barki ba, toh koh bai bari ba bazaki taho ba inyaso a San abin yi daga baya", maganganun Abuturrab na jiya ta tuna, hankalinta a tashe tace "toh toh naji Mummy, yanzu zanje in sameshi ince mishi an min waya ance bakida lafiya kuma kinason ganina, nasan in yaji haka zai bari, sai kiyi all things possible yadda bazai gane ba", da haka sukayi sallama akan zata k'irata duk yadda akayi, tashi tayi tana matsar k'walla yadda zatayi pretending wa Abu.



Batuul ta d'auko flask d'in fresh milk d'in kenan zata fito daga kitchen taga Ajiddeh na sauk'owa hankali tashe, duk gashin nan an baje shi, ae fa nan gabanta ya shiga faduwa ta k'asa karasawa dinning,
a tsorace take kallonta ganin yanayin da take, wani irin mugun kallo tabi Batuul dashi ganin irin kayan dake jikinta, har sai da tazo zata wuce ta dinning d'in a hankali Batuul tace "INA kwana", wani kallo ta watso mata tareda hararanta, tab'e baki Batuul tayi ta d'auke kanta, dama ita kirkin da Ajiddeh ke mata ba yadda tayi dashi ba, gara tana masifan da ta Saba kawae, tana dire flask d'in hannunta ta haura sama abinta da sauri.

Da wani irin kuka ta fad'a jikin Abutturab dake kwance kan sofa da remote hannunshi yana kallon TV, don yi yayi kamar bae san ta sakko falon ba da farko, a rikice ya d'agota ya shiga tambayanta lafiya, tana kuka kamar zata had'iyi rai tace "Mummy", tashi yayi yana kallonta yace "What happened to her", cikin sheshek'a kamar dagaske ta kasa ce mishi komai, a d'an tsawace ya d'ago fuskarta yace "talk to me Ajiddeh, what happened to Mum", a sanyaye tace mishi "Yanzu Yaa Zee ta k'irani, wai Mummy ba lafiya kuma tana son ganina", ajiyar zuciya ya sauk'e ya jawota jikinshi ya rungume yace "shhhhh, its okay , she will be alright, okay?, gobe zamuje gida", da hanzari ta d'ago tana kallonshi tace "baby bazan iya ba, inason inje inganta yau, bazan Iya ba", ta k'arashe maganar da kuka sosai, tashi yayi ya kamata suka haura sama, sai da ya shiga d'akin ya zaunar da ita kan gado yace mata tashi ki shirya kayan da zakiyi amfani dashi, yanzu zamuje muyi booking flight ko na evening ne sai mu bi", rinannun idanuwanta ta d'ago tana tana kallonshi tace "Baby ai kana da aiki, ba komai ba sai kaje ba, you should stay back ka kula da abubuwan da kakeyi, In sha Allah she will b fine", haka tayi ta insisting har sai da ta samu tayi convincing d'inshi ya fasa bin ta, bakwai da arba'in da biyar daidai suka sauk'o shida Ajiddeh tana riqe da trolley d'inta a hannu, Batuul na palo suka sauk'o tare, mik'ewa tayi tsaye har suka k'araso inda take, Ajiddeh sai hararta takeyi ta gefen ido, sai lokacin ma ya tuna da ita, kud'i ya ciro daga aljihunshi ya mik'a mata sannan yace "David ya kaiki school", da haka suka fita suka barta nan tsaye ko wayanma bai samu ya bata ba yau. Haka kawae taji ranta ya baci ta bi bayan Ajiddeh da harara, suna fita ta ja tsaki ta haura sama don xuwa dauko jakarta ta bar gidan ita ma.
[8/22, 14:50] Umar Dalha: πŸ’–πŸ’BATUULπŸ’–πŸ’





60






By phartiemarhk




Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*






A bakin mota ta tarar da David tsaye yana jiranta, hannu tasa ta bud'e motan ta fad'a sannan shima ya shiga, sau biyu David na maimaita gaisuwarshi, sai a na ukun ta amsa mishi, zuciyanta ne taji yana mata xafi ta rasa dalili, ta ja tsaki yafi sau biyar zamanta cikin motan, hawaye ne mai d'umi ya shiga sirarowa daga idonta, hannu tasa ta shafo hawayen ta tsaya tana kallo da mamaki, kifa kanta tayi tsakanin cinyoyinta ta fara kukan da batasan dalilinshi ba, daga sama taji David na fad'in "We ve arrived", a hankali ta d'ago kanta ta k'arewa wajen kallo, batace mishi komai ba ta d'auki jakanta ta fita daga motan, department d'insu ta nufa taga Su Samantha da Aisha da wasu students d'in na tsaye hall way d'in, agogonta ta duba taga saura 15mins su fara lecture, tana juyawa zata bar wajen suka had'a ido da Aisha, d'auke kai Batuul tayi kamar bata ganta ba, can bayan faculty d'insu ta nufa ta zauna taci gaba da kukanta, k'anshin turare mai dad'i ne ya bugi hancinta amma bata d'ago taga daga ina k'anshin yake ba, cikin wani irin masculine voice mai dad'i da nutsuwa taji ance "Here, take this", ta d'ago rinannun idanuwanta ta sauk'e kanshi, da sauri ta d'auke idonta ta juyar da kai gefe ta hade rae, har lokacin bai bar wajen da yake tsayen ba, juyowa ta kuma yi ta ga har lokacin hannunshi na mik'a mata farin handkerchief d'inshi, a sanyaye tasa hannu ta karb'a, wani k'anshi mai dad'i ne ya bugi hancinta da takai fuskanta, ido ta lumshe ta shiga goge hawayen dake fuskanta, daga d'an nesa da ita ya zauna, bai ce mata komai ba har sai da ta juyo ta dubeshi sannan yayi mata murmushin shi mai kyau, kau da kai tayi ta fara wasa da biron da ta ciro cikin Jakarta, a hankali ya fara magana "if you don't mind, may I know d reason behind those tears, I might help", sai lokacin ta sake tunowa da yadda taga Abu ya riqe Ajiddeh, wani siririn tsaki ne yayi escaping lips d'inta ta fara k'ok'arin maida hawayen dake shirin dawowa, jin tayi shiru batace komai ba yasa ya sake kallonta, suna had'a ido ya d'aga mata girarshi d'aya yana jiran jin mey zatace, agogon hannunta ta duba taga lokacin lecture yayi, da hanzari ta mik'e ba tareda ta bari sun had'a ido ba ta miqa mishi handki d'inshi, ganin bai amsa ba ta ajiye mishi tace "Thank you, I need to go right away", bata jira jin cewarshi ba ta tafi cikin sauri ta bar wajen", murmushi yayi yabi bayanta da kallo tare da lumshe ido, tana isa taga har an fara shiga class itama taje ta zauna, waje d'aya suka zauna itada Aisha, bayan sun zauna ne Aisha tace "Fatima wai meye problem d'inki, ko yau you look pale, in

1 Comments On BATUUL
avatar
hafsat-9-3

12 months ago

Reply

Nice book

Please Login or Register in order to submit comment