Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kai ta girgiza mishi tace "Yaaa Abu da sanyi, I don't want to remove the hijab", bai ce mata komai ba har saida ya cireshi sannan ya rungumota jikinshi ya ja musu duvet yace "I will keep you warm", murmushi kawai tayi tana tuna ranan da sukaje gidanshi a London yanda yayi keeping d'inta warm har ta gama duk abinda zatayi, a hankali ta matsa jikinshi ta gyara kwanciyarta, cikin kunnenta ya rad'a mata "are you still cold?", juyowa tayi tana fuskantarshi da kyau tace "Will you always keep me warm all the time?", ya saka hannayenshi duka biyun yana zagayeta yace "Always and forever", daidai lokacin ta tuna da Ajiddeh, tana son ta tambayeshi ina take tana tsoron kada ya sake mata fad'a kamar na ranan, a hankali taji yace "Yaushe zamu koma gida?", idonta a lumshe batareda ta bud'esu ba tace "Nanfa?", yace "This is Ammah's house", ta zumb'uro baki tace "Ni I want to stay here", yace "No gidanki kuma fa, wa zai zauna ciki?", tace "Inada gida ne ni?, d'ayan ai gidanta ne, d'ayan Kumar kace na love of your life ne", dariya yayi yace "So baki manta ba?", tureshi tayi daga jikinta tace "Ni kam ka dena min dariya, a nan zan zauna", yace "Toh bud'e idonki in fad'a miki wacece love of my life d'in?", kamar yana ganinta ta murgud'a mishi baki, juyo da ita yayi yace "Plsss mana, ki bud'e idonki in fad'a mki gidan waye?", a hankali ta bud'e idonta suna had'a ido tayi maza ta rintse su, dariya yayi ya d'agota yace "Fatima get up and listen, gidan nanfa nakine, I built it for the woman I will love, I designed everything for her, banida ra'ayin k'ara aure, I want to live with just a single wife and then Allah yayi Hauwa baza ta zauna gidan ba, then it was you, tun lokacin da akace zan aureki a raina nasa gidan zai zama naki, I then programmed everything ya koma naki, censor and all but God so kind you turned out to be the love I wanted, the love I wanted to give and take and there the house is yours, kinga sai mu koma ko tunda kinada gida, only I and you have access to wannan gidan", jin shirun yayi yawa a hankali ya k'ira sunanta bata amsa ba, da wayarshi ya haska yaga bacci take, murmushi yayi tareda pecking goshinta ya gyara mata kwanciya suka kwanta bacci





Tunda Ajiddeh ta fara Magana Kulthum ke karanto Innalillahi wa inna illaihi raji'un, sosai ta tsorata da jin lbrn snn ta tausayawa Ajiddeh, tasan duk so ne ya sata aikata abinda take nadama a yanzu, ta jima kamin ta bud'e baki da k'yar "Kuskure kikayi Babba, shirka ba k'aramin laifi bane, da lokacin kin mik'awa Allah lamuranki da ko baki had'a da kowa ba yaron nan zai zama mijinki tunda Allah ya kaddara da aure tsakaninku, amma da yake komai rubuttace ne babu yadda za ayi ki tsallake hakan, gashi nan yanxu koda ya hak'ura bazai dena kallonki da abinda kika aikata ba, kada ki gaji da bashi hak'uri koda yana korarki ne, itama yarinyar da ki nemi ta yafe miki dan ita akafi zalinta, batada haqqin kowa sai dai nata da kuka d'iba, ni bansan Mummy d'inki ya take ba da zai yiwu sai kije ki sameta kuyi magana da ita, yanda na fuskanci mijinki yana sonki har yanzu, ki sameshi ki sake bashi hak'uri", d'agowa Ajiddeh tayi da idanunta da suka rine tace "Baya sona, ya dena sona, cemin yayi in fita kada in sake nuna mishi fuskata", ta fad'a tana share hawaye, Kulthum da har ranta ta tausaya mata tace "Fushi yayi, in ya huce zai saurareki, ki bashi lokaci ya sauk'o, snn ki fad'awa Babanki cewa bazai yiwu ki koma gidanshi ba, sbd yace baya son ganinki", a tsorace Ajiddeh ke kallonta, batasan da ya Dad zai d'au zancen ba,haka tayi ta rarrashinta tareda kwantar mata da hankali, da yamma Dad da ya dawo duba ya jikin Kulthum da mamaki yake kallon Ajiddeh yace "baki tafi ba Hauwa?", hawaye ne ya fara zirya idonta, da kyar ta samu ta iya cewa "Dad ya koreni, yace I should not show my face to him ever", kallonta kawai yakeyi har ta gama magana, bayason raising family issue gaban Kulthum duk da hankali ya kwanta da ita amma baijin yin magana gabanta, Kulthum ya duba yace "ya jikin yayi sauk'i ko?", wani awkward haka take jinta, ce mishi tayi "Alhamdulillah tana jin sauk'i", yayi mata sannu da jiki snn yace in tana buk'atar abu ta fad'awa masu aikin a sama mata, ya juya kamar Ajiddeh bata d'akin ya fice, da gudu Ajiddeh tabi bayanshi, wani kallo da ya bita dashi yasa ta tsaya with pleading eyes tana so ya barta ta mishi bayani tukunna kamjn ya yanke kowane hukunci kanta, jiki a sanyaye ta durk'ushe wajen ta fasheda kuka, Daddy kam a ranshi yake tunanin irin tashi kaddarar, ko jiya da daddare saida Mum ta gama mishi tijara harda cewa mey ya tab'a mata duk zamansu, da yake ba mai son hayaniya bane bai biyeta sunyi surutu, masifa ta dinga yi akan zaman kulthum gidan, ganin yaqi kulata ta fice ta banko mishi tana cewa zai gani, duk sai tayi maganinsu, kanshi ne yaji yana sara mishi Dan abin yayi mishi yawa, Ajiddeh da yake ganin gara ita itama gashi tana fad'a mishi wani zancen daban, nan inda Ajiddeh ta durk'ushe ta jiyo k'arar wayarta, addu'a take a ranta Allah yasa Abutturab ne, da k'yar ta mik'e taje ta d'auki wayan, ganin Mum ce yasa ta maida wayar ta ajiye dan batasan mey zatayi mata ba in banda k'arin b'acin rai, har ya katse bata d'aga ba aka sake k'ira, d'auka tayi tasa a kunnen tana jiran jin mey zata fad'a mata, kamar a mafarki ta dinga jiyo abinda ake fad'a Mata, ta kasa yadda da Mum d'inta ce ake cewa tana Illorin, yaushe ta bar Abuja har ta tafi Illorin, wayar ce ta kubce mata daga hannu itama ta sulale tayi k'asa.

💖💝BATUUL💖💝





93




By phartiemarhk




Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*



Gabanta ne ke fad'wa, batason son tabbatar da abinda kunnuwanta ke jiyo mata, yaushe Mum ta bar gida har ta tafi Illorin, so take ta k'aryata zancen amma tunanin da wayar Mum aka k'irata ya sata saurin mik'ewa, a guje kamar wata mara lafiya tabi bayan Daddy, ba tareda tasan ta inda zata fara ba ta isa gabanshi tace "Daddy Mummy", Kallonta yayi yanason jin mey ya samu Mummy, a ranshi yace mey ma zai sameta, a daburce cikin kuka tace "Daddy wai Mummy ce wai sunyi accident", duk da maganar tazo mishi a ba zata bai nuna ba, dakewa yayi yace "Hauwa mey kuma kikeson sake aikatawa bayan wanda kikayi, burinku ne a kullum ku kunyata ku tozartani ku sani magana, dake da y'ar uwar taki duk kunyi nasarar cikar burinku, kun biyewa son zuciya, ki koma kiyi zamanki tunda shi d'in ya fiye miki shi kika zab'a", wani sabon kukan ta fasheda hawaye d'aya na bin wani tace "Dan girma Allah Dad kayi hak'uri ka saurareni, wlhy ba k'arya nake ba, yanzun  nan aka min waya da wayar Mum akace tayi accident hanyar Illorin, Dad dagaske ne dan ko da naje side d'inta bata nan, kayi hak'uri kasa a bincika muji ko itance dagaske", kallon Ajiddeh kawai yake a ranshi yana tunanin abinda zai kai Zuwairah Illorin, wa ta ajiye wa take dashi can garin da har zata tafi bada sanin shi bs", juyawa yayi ya tafi Side d'inshi a Ajiddeh na biye dashi a baya tana hawaye, yana k'arasawa d'aki ya d'auki waya yasa a bincika mishi ko dagaske ne abinda Ajiddeh ta fad'a mishi, ba a jima ba aka k'irashi aka tabbatar mishi da "Ehhh gaskiyane, matane uku da Driver d'insu sukayi accident d'in", ajiyar zuciya ya sauk'e dan ya rasa tak'amaimai abin fad'a, tashi yayi zai fita Ajiddeh dake zaune tana hawaye gefenshi ta taso tace "Kaji ko Daddy, an tabbatar maka da Mummy ce ko?, Na shiga uku Dan Allah Dad muje mu dubata, wayyo Mummy na",wani irin kallo da ya watsa mata ne ya sata saurin had'iye maganar dake bakinta, tun da take harara Dad bai tab'a yi mata shi ba sai yau, jiki a sanyaye ta koma ta zauna, fita yayi shida driver yana neman yanda za ayi a dawo dasu gida dan sai an had'a da police, baisha wahala sosai ba kasancewarshi d'an siyasa ko ina sunada mutane,

      Wanka tayi ta zauna bakin gadon daga ita sai d'an towel, shima lokacin ya fito daga toilet d'in yace "Bata kawo kayan ba har yanzu?", kallonshi tayi ta zumb'uro mishi d'an k'aramin bakinta tace "Nace fa zanje In d'auko ka hana, nasan bacci takeyi ka tada ta", bai kulata ba ya d'auko wayarshi ya k'ira Farida a waya, yana bugawa ta d'aga yace "Har kin kawo kayan kenan ko?", kamar tana gabanshi ta girgiza kai tace "Yanzu nakeson in k'irata ta fad'amin wanda zata saka fa",  yace "Get the whole box here", ido ta wara kaman yana gabanta tace "Kai Yaaa Abu, da nauyi fa", bai jira mey zatace ba ya katse wayan", kayanshi dake ajiye kan gadon ya d'auka ya sanya, kinkiman akwatin ta shiga yi a ranta tana mitar tada da yayi daga bacci, gefen Batuul ya zauna ya shafi gefen fuskarta tareda juyota ta fuskanceshi yace "Fushin meye ne wai har yanzu haka?", ya fad'a yana shagwab'e mata fuska, d'auke kai tayi tace "Ni fa sanyi nakeji ka hana kuma inje in d'auko kayana", kallonta yayi cikin ido da ya sata tayi saurin sadda kai k'asa yace "bana son kina stressing kanki, am there all the time", ya kamo hannunta ya damtse cikin nashi, daidai lokacin Farida tayi knocking tareda turo k'ofan ta shigo da akwatin tana haki,Batuul na jin k'arar tab'a k'ofa dama ta janyo hijab d'inta ta saka, jan akwatin tayi har cikin d'akin ta snn ta dubi Abu tace "Ina kwana", daga gani daga bacci ta tashi yace "Baki iya jiran izini ba kawai you barged into d'akin mutane ko?", zumb'uro mishi baki tayi a ranta tace "Hmmmm ai saidai idan ba Yaa Abu ba", a fili kuwa cewa tayi "yayi nauyi ne shinefa na shigo kuma saida nayi knocking", idonta ne ya fad'a kan Batuul dake zaune daga ita sai d'an towel da hijab, duk ta shagwab'e fuska kamar zatayi kuka, batasan lokacin da dariya ta kubce mata ba, dariya takeyi harda hawaye snn ta tsagaita dariyar tayi pointing Batuul tace "Ya Allah, you have started gaining weight, Affan have to hear of this, kin ganki kuwa?" Abu da ya tsaya kallonta da mamaki ya daka mata tsawa yace "kina da hankali kuwa?, c'mon get out kamin in tashi in sameki", kallon Batuul da tayi raurau da ido yayi, yasan kuka take shirin mishi, Farida da ke tsaye wayarta ta ciro cikin aljihun rigan baccinta zata k'ira Affan, tsawa ya sake daka mata yace "Na fara wasa dake ko Farida?", kamin tace wani Abu ya tashi ya fizgota ya karb'e wayan ya turata waje, dawowa yayi bakin gadon yana kallon Batuul dake jiran k'iris ta fashe da kuka baki a tab'e, a hankali tace "Dagaskene av gained weight?", in banda iskanci irin na Farida babu ta inda yaga Batuul ta k'ara jiki, dalilin da yasa ma kenan bayason kaita gida sbd yadda duk ta rame, ya d'aura hannu kan wuyanta yana tab'a collar bone d'inta yace "I want you to, kin rame dayawa kuma banaso ni", tasan bazai fad'a mata ba, cire hannushi tayi ta mik'e ta isa gaban human size mirror dake d'akin tana kallon kanta, itama d'in babu ta inda taga ta k'ara k'iba, tasowa yayi ya biyota gaban mirror ya rungumota ta baya tareda tareda sauk'e ajiyar zuciya yana shak'an k'anshinta masu dad'i, ido ya lumshe ya bud'e dai dai nan hawayen da take ta rik'ewa suka gangaro, da sauri ya juyo da ita yana girgiza kai yace "Glitter noo, kar kiyi kuka plss", muje kisa kaya yau sai Farida ta fad'amin yadda akayi kikayi gaining weight" ya  fad'a tareda kamo mata hannu, d'ayan hannunta ta saka kan nashi, juyowa yayi ya dubi fuskanta yaga duk sai glittering d'in hawaye suke, rungumota yayi, bai tab'a ganin mutumin da hawaye bai mishi wuyar zuba kamar Batuul ba, jawota yayi suka koma bakin gadon, a hankali tace "Nasan ban k'ara jiki ba but nan gaba in nayi fa?, you will stop loving me ko?", yanzu ya sake tabbatar da harda yarinta cikin lamarin Batuul, dan kawai tayi jiki sai ya dena sonta?, he love her for whatever she is and whatever she will become of, wani light peck yayi mata a goshi ya rik'o hannuta cikin nashi yace "Hey look at me", kasa d'agowa tayi ta kalleshi saida taji yace "Glitter look at me", d'azu ma taji word d'innan daga bakinshi sai yanzu ta san da ita yake, sunaye biyu kenan ya saka mata yanzu, Haya da Glitter, har cikin ranta takejin sunan, a hankali ta d'ago ta dubeshi, Hannu yasa ya share hawayen dake shirin zubo mata yace "what will make you change the way you feel about me?", shiru tayi ta kasa cewa komai saida yace "Uhmm ina jinki", jiki a sanyaye ta girgixa mishi kai, yace "Ki bud'e baki kiyi min magana a hankali tace "Babu", yace "mesa kike tunanin gaining weight zaisa in dena sonki, wa yace miki jikinki nakeso Haya, wa yace miki structure d'inki nakeso?, Ina sonki for who you are da kuma what you are yet to be, banason sake jin kin sake fad'an haka, zamuyi fad'a kinji ko?", kai ta gyada mishi yace "Good" yana sa hannu cikin gashinta da bai bushe ba yace "zakiyi mura fa kina barin gashinki da ruwa", tace "yanzu fa zansa kaya inyi drying d'inshi", ta fad'a tana k'ok'arin tashi ya rik'ota yace "No ki bari in mun sake jik'ashi sai kiji dad'in drying da kyau", sarai tasan abinda yake nufi da hanzari ta mik'e tana dariya tace "A ah nikam, I can dry it haka nanma", dariyan yayi shima ya kamata ya zaunar kan stool ya shiga drying mata dogon gashin kanta mai santsi da shek'i, sai da ya gama snn ya taimaka mata ta shirya cikin navy blue lace mara nauyi mai k'ananan jan patterns yace su sauk'a ya fara jin yunwa, ya rik'o hannunta suka sauk'o dinning area, suna k'arasowa tayi maza ta janye hannunta cikin nashi, kallonta kawai yayi baice komai ba har ta zauna snn ya zauna, daga kitchen Ammah da Sadiq suka fito, da alama daga exercise yake saboda kayan jikinshi, yana riqe da apple yana taunawa biye da Ammah yana mata magiya, juyawa tayi ta dubi Sadiq tace "Kana jina fa Sadiq nace bansan zancen ba, ka samu Abui kuyi maganan dashi", ta k'arasa dinning d'in, Da sauri Batuul ta tashi ta karb'i pan d'in dake hannun Ammah tace " *Ammah Nda wattu* Ina kwana Ammah", "Ammah da murmushi fuskanta tana goge hannunta tace " *Bitti k3lewa selai, k3lewan fanema? Lafiya Kalau Bitti, kin tashi Lafiya?", ta tambaya tana gyara tray d'in fruits, a kunyace Batuul ta ajiye pan d'in dake hannunta tace "Alhamdulillah", ta dubi Abu tace "Ya jikin nata?", Saida ya gaisheta snn ya amsa da Alhamdulillah, ya dubi Sadiq da duk ya shagwab'e fuska yana tauna Apple d'inshi yace "Shi kuma wannan mey ke damunshi?", ya fad'a yana tambayan Ammah, Ammah ta zauna ba tareda ta dubi Sadiq ba tace "Ka tambayeshi gaka gashi, kunfi kusa inajin", kallon Sadiq yayi yace "Whats wrong?", a hankali Sadiq yayi wata magana da babu wanda yaji, Abu da ya had'e fuska yace "In ka shirya fad'an matsalarka ka biyoni ka fad'amin", Ammah tace "Shima da kanshi yasan hauka yake shirin yi shiyasa bazai iya fad'a makan ba, ni bara in fad'a mishi yaji yasan rashin hankalin da yake min", Ammah taci gaba tace "Wai aure yakeson a mishi", daidai lokacin Abui ya k'araso dinning d'in yana cewa "wakeson ayi mishi auren?", Sadiq da sam baiso Abui ya Karaso at this time ba yayi maza ya sadda kai k'asa, Abutturab tsabar mamaki kasa cewa komai yayi sai baki da ya bud'e yana kallon Sadiq d'in, Ammah tace "Wai Sadiq keson a mishi aure", murmushi Abui yayi yace "Har ka shirya kenan, ka shirya kula da y'ar mutane", d'agowa yayi suka had'a ido da Abutturab, Abutturab yayi mishi kallon you are not okay yace "wace yarinyar ce zata aureka bakada aikin yi?, Serving d'inma ba gamashi kayi ba bare ka fara maganan settling ", D'an kafad'a ya d'aga alamun am due fa snn yace "But ai inada gida, what else?" Sosai Sadiq ya bawa Abui dariya, Ammah da Abutturab kam ko kad'an abun wasn't funny to them, Farida ce ta sauk'o sanye da kayan bacci da hula kanta tana danna waya, jin maganan da akeyi ya sata k'arasowa da sauri tana maida wayar cikin aljihu tace "Laaah Ammah ku baku San ma yarinyar bafa, wai fa Layla k'anwar Uncle d'in Aunty Amna yakeso, ina jinshi yana waya da ita kullum, ko wallpaper d'inshi picture d'inta ne, bara ma ku gani" taja kujerar gefen Abui ta zauna tana mik'a hannu zata d'auki wayarsa dake ajiye gefe, Hannu Sadiq yasa y make nata hannun, b'ata rai tayi ta zumb'uro baki ta kalli Abui tace "Abui kana ganinshi ko", tunda Abu ya harareta tayi shiru ta d'auki plate ta d'ebi pomegranate tana sha, Sadiq ma harara ya sakar mata, Abui yace "Sadiq ba gida bane aure, it takes a lot fiyeda wannan, you are just 22, kana buk'atar time da kuma nutsuwa kamin kace zakayi settling, ka bari in ka gama Service ka samu aiki then you talk of settling amma banda yanzu, parents d'in yarinyar da kanta ma ba yadda zasuyi da zancen ba in ba aiki ka fara ba", Ammah da tayi serving Abui soup tana mik'o mishi tace "Sadiq in baka rabani da shirman nan ba ranka zai b'aci, itama Laylan da ta biye maka", Wani kallo ya jefi Farida dashi da ta tona mishi asiri, d'auke kanta tayi tana jin haushin make mata hannu da yayi, Sai da kowa ya nutsu yana cikin cin abinci Abu ya kamo hannun Batuul ta k'asa yana kashe mata ido, kallonshi tayi na ya sakar mata hannu, bai sake ba saima sunan Abui da Ammah da ya k'ira, a tare kowa ya kalleshi suna jiran suji mey zaice musu, Batuul dai gabanta sai fad'uwa yakeyi tana tunanin abinda zaice musu tana k'ok'arin kwace hannunta amma ya dad'a k'arfin rik'on, jin yayi shiru Abui ya maida hankalinshi kan abincin da yakeci, Ammah ce tace "Muna jinka", a nutse yace "Ammah inaso mu koma ne, inada aikin dayawa that are pending", tace "Dama can kai ne kayi zamanka, tunda taji sauk'i ka tafi abinka ka rik'a dawowa kana dubata, ido ya lumshe ya bud'e jin abinda Ammah tace snn yace "Ammah tare fa nakeson tafiya da ita, ba nan zan barta ba", Wani kallo Ammah tayi mishi a taqaice tace "baza ta koma gidan nan ba, ka barta nan in ya so ka riqa dawowa kana dubata", marairaice fuska yayi ya kalli Abui da puppy eyes d'inshi, yace "Ammah ba gidan nan zata zauna ba, tun kamin ta fara ciwo take d'aya gidana, Plss Ammah", Abui yace "Anytime you are ready ka d'auki matarka ku tafi", Kallonshi Ammah tayi zatayi magana yace "Meye amfanin barin nata da zaiyi a nan, ko ya tafi hankalinshi ba kwanciya zaiyi ba, su koma kawai zai ci gaba da kula da ita In sha Allah babu abinda zai sameta", Badan ta yadda ba ta hak'ura, Abu kam dariya yayi yace "Nagode Abui, Allah ya k'ara girma da d'auka, Allah ya k'ara Nisan kwana, Allah ya gafartawa magabata yasa a gama da duniya lafiya", "Amin" dukkansu suka amsa, dariya ma ya bawa Abui Dan kawai yace zai iya tafiya da matarsa shine duka wannan addu'a haka, yace "Kaje ka dubo Hauwa?", gaban Batuul sai da ya fad'i jin sunan Ajiddeh, take expression d'in fuskan Abu ya canja jin sunan Ajiddeh, har idonshi ya fara canja launi yace "Abui am not ready, bana so inyi taking decision out of anger, kar inyi abinda we  all will regret", kai kawai Abui ya gyad'a mishi alamar he understands him, Batuul dai gaba d'aya kanta ya gama d'aurewa, mey zaiyiwa Ajiddeh da har zaisa suyi regretting, kuma meye sa tunda ta farka bata gidan, tana sak'e sak'enta har suka gama cin abincinsu,





Da yamma aka dawo dasu Mum asibiti aka wuce dasu kai tsaye, ita Jainaba, sai wata mata da Dad d'in bai Santa ba, babu wanda baiji mugun ciwo ba cikinsu, Da ya dawo gida suka taho tareda Ajiddeh, in banda kuka babu abinda Ajiddeh keyi, ta rasa bakin cewa komai, Zainab ma sai da Daddy ya qirata snn ta taho, itama kukan ta saka ganin yanayinsu, Dad baice musu komi ba ya tafi wajen Doctor, Doctor yayiwa Dad bayanin cewa Mum ta sami raunika hannu da k'afa da kuma spine d'inta, babu ita babu tafiya a yanzu, d'ayar matar kuma Brain d'inta ya tab'u amma suna fata in ta farfad'o a samu a sake dubawa, sai Jainba ita kuma hannayenta ne kawai suka ji raunin sai kuma kafar ta da sai an yanke sbd ya lalace, tunda doctor ya fara magana Dad ke danne zuciyarshi yana addu'a sbd wani irin abu da yakeji yana taso mishi, saida likita ya gama bayani yayi mishi godiya ya fita, gida ya wuce kai tsaye dan bayajin zai iya komawa cikin d'akin, har ya isa gida yana tunanin abinda ya kai Zuwaira Illorin.

💖💝BATUUL💖💝


Da 94






By Phartiemarhk




Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*



Da yamma suna zaune garden itada da Farida da take ta mata iya shege kan ta k'ara k'iba, bata kulata ba dan Yaa Abu ya fad'a mata babu wani k'iba da ta k'ara, gaba d'aya hankalinta yana kan fruit Bump game d'in da take bugawa, Juyo mata da Macbook d'in dake kan cinyarta Farida tayi tace "Kinga nacewa Affan in zaizo ya taho min da wannan cradle d'in, its cute ai ko?", sai a sannan ta d'ago ta kalli cradle mai kyau dashi snn ta kalli Farida with confusion fuskarta tace "Huh?, cradle nefa, kwana zaki koma yi kai?", Farida ta d'ago ta dubeta tayi mata kallon you ain't okay ta girgiza kai snn tace "Babynmu na siyawa, the newest niece/ Nephew, kinga fa unisex nace ma tunda bansan mey zaki haifa ba, Dan Allah kicewa Yaa Abu kuje a duba cuz in san irin kayan da zan riqa keeping", ta fad'a with soo much excitement a muryarta, Sai lokacin Batuul ta fahimci ina ta dosa ta tsuke fuska tace "Ni nace miki zan haihu toh?", Farida ta kyalkyale da wani irin dariya da ya bawa Batuul haushi tace "Wake jiran sai kin fad'a mishi, tun da naje wajenki UK na gano, shiru kawai nayi maki ina kallonki kawai", Jin ambaton sunan UK ta tuna da Ajiddeh, jiki a sanyaye tace "tun yaushe ne bata nan, ni tunda naji sauk'i ban ganta ba", ba tareda ta dubeta ba Farida tace "Wa kenan?", a hankali Batuul ta furta Ajiddeh, kafad'a Farida ta d'aga tace "Oho, da yake she is not my cup of slush", Batuul ta dawo kusa da Farida tana k'ok'arin rufe System d'in tace "Riri mana, dagaske fa nake, she was nice to me da banida lafiya, har Addu'a fa tayimin", wani irin kallo Farida tayi mata, kallon lallai you are not okay, har ta bud'e baki zatayi magana ta fasa, ta sake janyo System d'in zata bud'e, Batuul tayi maza ta riqe tace "dagaske nake I could remember everything har da kukanta, she insisted mu dawo fa ayi min magani a nan, amma tunda na warke ban ganta ba, kuma d'azu naji Abu na cewa bayason ganinta cuz bayason taking decision out of anger, mey ya sameta Dan Allah?", Sai yanzu Farida ta tabbatar da Lallai Batuul batasan mey ke faruwa, kuma baza taji

1 Comments On BATUUL
avatar
hafsat-9-3

12 months ago

Reply

Nice book

Please Login or Register in order to submit comment