Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zanje dubata a asibiti", d'an k'aramin tsaki yaja snn yace "in baki nutsu yanzu ba Zuwaira sai yaushe zaki nutsu, shekara kusan nawa da aure kin haifi yara har sunyi aure suma amma bakisan abinda ya kamata ba, ba dole a sako miki y'a ba tunda abinda taga kinayi shi zatayi a gidanta kuma su na tabbata da hankalinsu shiyasa suka dawo miki da y'ar, tunda abinda kike so kenan sai ki barta tayi ta shirme kina biyeta, aikinki kenan kullum bin k'awaye kamar wata yarinya k'arama? da girmanki bakisan kula da miji ba, gabaki dayanshi hakkin auren ma ba saninshi kikayi ba", had'e rai tayi tace "Nasani ai dama cin fuska zakamin, zumunci zaka hanani yinshine, menene a cikin auren da banayi maka masu aikine gasu nan kai kake biyansu, komai sunayi, so kake sai in riqa zuwa ina baka abincin a baki ina maka wanka, dududu ma sau nawa ake ganinka a wata, ni wlhy bazan
iya da zaman matsi kamar wata y'ar
k'auye ba, a matsayinka kamata yayi ina matar perm sect ace duk bayan sati biyu bana Nigeria, ka tsare ka hana kuma cikin gari ma ka hanani, wlhy bai yiwuwa, exposure ko wane irine yaci na ganshi amma duk kabi ka datse, toh ni ban iyawa", kallonta kawai yakeyi da mamaki, murmushi yayi yace "Tashi kije", dan yasan babu abinda zai fad'a taji tayi aiki dashi ta riga da tayi nisa, babu kunya ba tsoron Allah ta mik'e ta kad'a gyale ta fice daga

parlourn







Da murnarta ta kara wayar a kunnenta tace "Hello Aunty ina wuni", sai kuma ta fashe da kuka, "Yasalam", kawai Abu ya iya furtawa snn ya rungumeta yana kad'a mata kai alamun tayi shiru ta bar kukan da takeyi, daga d'aya b'angaren Aunty tace "Kukan na meye kuma Batuul sai kace wata Yusra, ya jikinki", cikin sheshek'a tace "Aunty naji sauk'i, Aunty inaso inzo in ganki", ji tayi Abutturab ya sassauta rik'on da yayi mata ya saketa ya ja baya, kallonshi tayi idonta cikeda hawaye, maganan Aunty ya katseta daga kallon da take mishi Aunty tace "keda bakida lafiya yawon mey zakiyi, kiyi zamanki har sai kinji sauk'i sai kizo kinji", kamar Auntyn na gabanta ta kad'a kai a hankali tace "Toh", Aunty tace "yawwa maza goge hawayenki bana so a ganki kina kuka kinji, ga Yayya nan za a kai mata wayan kuyi magana da ita", muryan Yayya taji tana cewa "Kaji ja'irar yarinya kukan na meye kikeyi, yaro na zaman zamanshi kinsa ya baro aikinshi, laulayin cikin kikewa wannan rakin, maga yadda zakiyi idan lokacin haihuwar tayi", Zumb'uro baki Batuul tayi tace "keh ina ruwanki, wama ya fad'a miki hakane", Yayya tayi dariya tace "zauna can, ina uwargida har sai an fad'amin, maigidan naki da kanshi duk sati sai ya kiran a waya kuma duk ya fad'a min tab'arar da kike mishi, ai nace mishi ma had'ani dake zaiyi in wuce dake Yerwa, maga ta fad'i", Batuul tace "keh Yayyan nan ko, babu inda zan biki, wajen Aunty kawai zanje", Yayya tayi shewa tace "Aunty taki ma basai in tafi da ita Maidugurin ba, dama naji tana wani rarrashinki dan lalacewa, ita ke dad'a tunzuraki nasani", "Ni kinga tunda ba abun arziki zaki fad'amin ba sai anjima", Yayya tace "gantalallu duk halinku d'aya da y'an uwan naki, ku masu uwa ba'a fad'in lafinta koh, in Baban naku ya dawo ya kawoni gun naki dan ni na raba kaina da tuk'in gantalallun k'annenki, wataran sai nasa shi Baban naku ya tasa su su d'auki tasu uwar suyi gudun da sukeyi dani akan titi, mugaye kawai", dariya Batuul tasa tace "toh keh ki koyi tuqin mana nan gaba basai ana gudu dake ba", Yayya tace "Ina nan tafe ne badai dariya kike min ba", haka sukayita hira, saida suka gama wayan ta kalli Abu dake daddana wayarsa, saida gabanta ya fad'i ganin irin kallon da ya jefeta dashi, zatayi magana yace "tashi ki shirya in kaiki", kallonshi tayi tace in shirya? Ina zaka kaini?", mik'ewa yayi ba tareda ya kalleta ba yace "inda kika gama cewa zaki yanzu", raurau tayi da ido ganin he is so serious, hawaye ne ya cika idonta, a hankali ta tako gabanshi tace ta fad'a jikinshi ta fashe da kuka, cikin shesheka tace "Yaa Abu nifa kawai na fad'a ne, am sorry toh na fasa, kaji bazan sake cewa Zani ba dagaske", hannu yasa ya zagayeta, hakan da yayi ya sata sauk'e ajiyar zuciya, ya d'aura fuska kan gashin kanta tareda lumshe yana shaka'ar kanshinta mai dad'i yace "Its
okay, bana son kukan nan", da sauri ta d'ago tace "kayi hakuri dagaske?", kai ya gyad'a mata yana murmushi yace "I can't be angry with you Fatima, bana so kina tadawa Aunty Hankaline, in taji kina kuka she might think wani abun ke damunki", sake k'ank'ameshi tayi tana girgiza kai tace "nace bazan sake ba", ya sunkuyo yayi pecking lips d'inta yace "that's my princess, muje Malamin na jiranmu", Hijab d'in da ya gani kan gadon ya janyo yasaka mata ya riqe hannunta sukayi waje. Suna fitowa corridors ta kallesa a hankali tace " Ya Abu ina take?" Ya d'ago kanta yace "Wa?" Ta d'an yi shiru sai kuma tace "Ita" sai a sannan ya tuno da Ajiddeh ya d'an bude ido yace "Ohh Ajiddeh? She might be at the parlor" daga haka ya ja ta suka sauko parlor, janye jikinta ta shiga kokarin yi daga nasa jin muryar Ammah da Anty Amnah a parlon da alama shigowarta kenan don gaisawa suke da Ammah








Am not actually so good with words but imma thanking these lovely girls for their love
Meenarh parrot๐Ÿ’–
Rahma lurv๐Ÿ’– and every single soul that loves BATUUL๐Ÿ’–๐Ÿ’
[11/15, 11:15 AM] โ€ช+234 810 957 2036โ€ฌ: ๐Ÿ’–๐Ÿ’BATUUL๐Ÿ’–๐Ÿ’





83













By phartiemarhk






Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*







Bayan Mum ta bar parlour rai b'ace ta fito ta dawo parking lot, da k'arfi ta shiga k'walawa driver k'ira, a guje ya taho yace "Hajiya gani", kallonshi Kawai tayi ya ciro makulli daga Aljihu ya bud'e motar ya fad'a, daga ganin yanayin yayar tata tasan ba lafiya ba, batace komai ba saida ta Shiga ta zauna tace "Yaa Zuwaira mey ya sameki naga kin canza daga shiga ki fito, wani abun ne ya faru?", Mum taja wani dogon tsaki cike da masifa tace "Dan uwarka kai jahilin ina ne iyye?, ina zaka kaini da ka karyo kwanan nan", Driver da duk ya rikice yace "Hajiya ranki shi dad'e ca nake kasuwa za....", bai gama rufe baki ba a hasale tace "bukkar uwarka zaka kaini ba kasuwa ba, shasha Kuje zamu, jahili", shidai baice komai ba dan inda sabo ya saba indai ran Mum b'ace yake a rana toh sam bai son ya zama shike duty, jiki a sanyaye yace "Ayi min afuwa Hajiya, kuskure aka samu", daga haka ya d'auki hanyar Kuje, Jainaba da ta gama tabbatarwa babban abune ya tab'a Mummy ta tab'a baki tace "Wai Daddy ne ya bata miki rai", Mum tayi k'wafa tace "Abun nayi ne Jainaba, wato ina saka ban sani ba warwara nakeyi, bamuga ta zama ba, wannan karan da zafi zamu shigi kowa, da zafi zafi akan daki k'arfe, bazanyi sanya ba wannan karon, sai naci uban kowama, baza a d'aga min hankali ina zamana ba wlh sai nayiwa abun tufkar hanci", wayarta ta d'auko daga gefenta ta shiga dialling number tasa a kunne, har ya katse ba a d'aga ba, Jainaba taja d'an siririn tsaki tace "Yaa Zuwaira nifa bakice min komai ba har yanzu, mey ya faru kuma banda matsalar Ajiddeh", Mum ta sauk'e wani nannauyan ajiyar zuciya tace "Shifa wannan baban nasu ne ya sani gaba da surutunshi na banza da wofi, akan mene zai dameni nida rayuwata, kinji wai wa'azi ya zauna zai min wai ina abubuwan da basu dace ba", Jainaba tayi dariya tace "baki mik'a mishi microphone ba dan kifi jin wa'azin da kyau", Mum tace "birki na taka mishi, inji da abinda shashashar yarinyar ta Sani ko kuma in biye mishi ya dad'a bata min rai, kuma fa duk sai nayi maganinsu, in banda taurin kanshi ma na jaraba duk abinda akayi kwana biyu yake barin jikinshi amma dai wannan karon alwashi naci sai na samu komai yadda nakeso", Jainaba tace "Yaya wai ina laifin wannan karan ayimana yadda Daddy kullum komai nashi zai koma naki, a badda hankalinshi da tunani ya zama komai a hannunki", Mum tayi k'wafa tace "Dan ubanki wace makarantar nayi da zan iya riqe wadannan abubuwan, ai sai yanxu nake takaicin kin zuwa makarantar da nayi ina Karama, da yanzu komai nashi nasan takansu", Jainaba tace "Ai ba sai Lallai ke din ba, dama su Zee ne zasuyi ai", "kinga fa dad'a tunzurani kikeyi kina b'atan rai, wadanne yaran marasa wayo ne zasuyi min abin kirki, kiga kayan takaicin da Ajiddeh ke k'unsa min, itakuma Zainab in banda yawo kamar wata hadari a cikin gari babu abinda takeyi, kedai bari duk na kusa kawo k'arshen komai", Jainaba tace "Toh Allah yasa", Mum taci gaba da k'iran wayan Zee da har lokacin taqi d'auka, Driver dake gaba yana jin komai Addu'a ya riqa Allah ya rabashi da masu irin halin Mum, kamar kullum yauma tafiya mai nisa sukayi kamin su isa gurin bokan nasu, da zuwansu Mum ta gama zayyane mishi duk abinda ke tafe dasu, k'asar dake gabanshi ya buga yace "itafa wannan yarinyar abinda muka tura Mata yana nan jikinta har yanzu kuma yana kan aiki saidai bansan mey ya hana aikin ci ta mutu ba, dan yaci ace ta mutu tun bayan kwana biyu", Mum tace "gaskiya ne yana aiki dan y'ar tawa da nayi maka bayani tanason kawo mana matsala tace min mutuwa zatayi, in da yadda za ayi ranka shi dad'e ta mutu a huta, kaga in ta mutun, ta wajen nawa zata dawo hankalinta sai musan nayi akanta itama", haka dai Mum ta dinga Zayyanowa boka abinda za ayi tun daga kan Daddy, Ammah, Abu da kuma Batuul, boka yace indai jaka a bud'e take zasuga aiki da cikawa, nan ya duk'ufa ya fara da na Batuul, Suna zaune a wajen wayar Jainaba ta shiga ringing, saida aka kira wajen sau shida snn ta d'aga, shiru tayi tana sauraren mai magana a wayan, sai da yayi shiru tace "Toh naji", ta katse wayar, boka ya gama masu tsubbe tsubbensu yace "kuje, kamin ku k'arasa gida zaku ci karo da lbrn mutuwarta" da murna fal ransu suka zube mishi kudi suka tashi akan zasu dawo in da wata matsalar, sai da suka fita zasu gun mota Mum tace "Wane d'an iskan ne yake damunki a waya, yaga baki d'au na farko ba ai sai ya rabu dake koma wani jarababben ne", Ajiyar Zuciya Jainaba ta sauk'e ta tab'e baki tace "Idrees ne", Mum taja tsaki tace "Shifa wannan k'aramin mara kunya ne, ko ba d'azun nan ya k'iraki ba", Jainaba tace "Shine ya k'irani, wai tuna min zai sakeyi indai ban dawo gobe lallai lallai ba toh inyi zamana a inda nake ba sai na dawo ba", Mum taja tsaki tace "Karamin mara kunya, sai yazo ya kinkimeki ya maidaki", da haka har suka isa mota Driver ya tada sukayi gaba suna ci gaba da hiran abinda zai faru





Aunty Amna dake tsaye tana magana ta hango Abu rik'e da Batuul suna sauk'owa downstairs, juyawa tayi ta dubi Ammah snn ta juya tayi stairs d'in, tana zuwa ta rungumo Batuul jikinta tace "Ayyyyy Batuul Habibty, bakiji dad'i ba ashe, Allahumma yashfiki, Allah yasa Kaffara ne Allah ya k'ara miki lafiya, baiwar Allah kina zamanki mutane na binki da sharri, kiyita Addu'a kinji, In sha Allahu duk wani mugun nufinsu akanki bazai tabbata ba da izini Allah", murmushi Batuul tayi tana tunanin maganganun da Aunty Amna ta gama fad'a mata yanzu, ita bata gane ma zancen mey takeyi ba", lumshe ido tayi ta bud'e snn tace "Namafa ji sauki Alhamdulillah Anty", Aunty Amna tace "Zaki warke kinji, Allah ya rabaki da sharrin masharranta", daidai nan Ajiddeh ta fito d'akin Abu zata sauk'o down stairs itama, jin maganan da Aunty Amna keyi yasa ta kasa d'aga k'afarta kuma, ta tsaya tana kallonsu, Aunty Amna ta dubi Abutturab da ya had'e rai tace "kai kuma yarinya batada lafiya kaje ka ajiyeta baka fadawa mutane ba", hannun Batuul ya janye ya dawo da ita gabanshi yace "Bata fa jin dad'i, she is weak", wara ido Aunty Amna tayi tace "Iyye, kaji mara kunya, da kasan she is weak ka barta tana shan wuya a can, kai a dole mai mata ko, ai sai ka kinkimeta tunda she is weak" sunkuyar da kai Batuul tayi dan kunya, kamar jira yakeyi ko sai gani sukayi yasa hannayenshi duka biyu zai d'auketa, wara ido Batuul tayi tareda matsawa baya tana girgiza mishi kai alamun kar ya mata haka, kamar bai gane mey take nufi ba ya sa hannu ya kamota zai d'agata taji kamar ana kulle mata ciki ta fasa wani razanannen k'ara da yafi na ko yaushe had'e ta rike cikin tana kiran Anty da kyar, lkci daya ta sulale yayi maza ya bita ya kamata a rikice yace "Ya salam, Not again baby, you will get well soon", Aunty Amna da ta tsaya kallon tsiyar Abutturab a tsorace da jin karan ta tsuguna itama ta kamo Batuul duk ta rud'e tace "Abu ciwon nata ne", kasa bata amsa yayi sai d'aukarta da yayi cak yayi k'asa da ita yana k'iran sunan Ammah, Ajiddeh da ke tsaye har lokacin tana kallonsu idonta ciccike da hawaye ta kasa d'aga k'afarta, ta rasa me ke mata dadi a duniylar, ganin yayi k'asa da Batuul ta fashe da kuka ta koma d'akin da take da sauri, a rikice Ammah ta fito tana tambayan mey ya faru, Farida da Sadiq dake side d'in Abui tare suka fito suna tambayan mey ya faru, Aunty Amna ma na tambayarshi ko ciwon nata amma ya kasa ce mata komai sai sunan Ammah da yake k'ira yana girgiza Batuul d'in ta tashi, Gaba daya duk sun rud'e kowa ya rasa abinda zaiyi ganin jikin Batuul d'in duk ya saki, Farida na kuka tace "Ammah ni kam nace ku kaita wajen Dr Zakaa zai dubata ya fad'a mana abinda ke damunta," hawayen dake idonta ta goge tace "Sadiq Abui na Guest room tareda bak'onshi, kace ciwon nata ya dawo", a rud'e Sadiq d'in ya amsa ya fita amsa aiken da Ammah ta mishi, da k'yar Ammah tayi k'arfin hali ta kamo Abun dake riqe da Batuul ya kasa cewa komai tace "Babana kawota ka kwantar da ita, zataji sauk'i In sha Allah, yanzu za ayi mata magani", ta fad'a tana k'ok'arin karb'an Batuul daga hannunshi, girgiza kanshi yakeyi hawaye na gangarowa idonshi, zama yayi kan kujerar Batuul na rungume jikinshi, gefenshi Ammah ta dawo ta zauna zatayi magana kenan Abui yayi sallama shida Ashiekh da Sadiq, Abui yace "Subhanallahi, jikin nata ne kenan", Abu bai iya cewa komai va don shi kadai yasan mey yakeji cikin ranshi, bayason kowa ya tab'ata sbd fargaban abinda za a ce mishi ya biyo baya, bayajin ko d'aya daga cikin nerves da pulses d'in jikinta na aiki, Ammah ce ta kawo hannunta ta rik'o na Batuul d'in, gabanta ne ya rik'a fad'i ganin hannun Batuul d'in ya saki, d'agowa tayi tana kallom Abu da idanunshi suka kad'a, lumshe ido yayi snn ya bud'e yace "Ammah babu abinda ya sameta ko?, I know she will be alright, nasani Fatima zakiji sauk'i i know you won't leave me just like that isn't it Batuul, you have to get up", Aunty Amna Abui ya kalla yayi mata alamun taja Farida da Ammah da ta matsa baya tana girgiza Kai, hakan ko tayi ta kama hannun Ammah tace "Ammah zataji sauk'i fa, ba dama haka yakeyi mata ba, yanzun nan zata farfad'o, muje muyi mata addu'an samun sauk'i", Itama Aunty Amna k'arfin hali kawai takeyi gaba d'aya jikinta yayi sanyi sai hawaye da takeyi, Farida ce ta karb'e hannunta daga rik'on da Aunty Amna tayi mata ta dawo gaban Abu ta tsuguna dab fuskar Batuul d'in tana kallonsa hawaye na sakko mata tace "Yaaa Abu saida nace maka a kaita asibiti fa, don Allah mu tafi", ta kalli Abui dake tsaye ta mike ta isa kusa da shi cikin kuka tace "Abui don Allah nace mu kaita asibiti da yanzu ta warke, ka ganta yanxu kwance ko motsi batayi, Dan Allah muje a kaita", Hannu Abui ya d'aura kanta ya shafa snn yace "Babu abinda ya sameta kinji, zataji sauki" yacewa Sadiq " *Sadiq tai sha samiro Leno*, Sadiq kamata ka kaita sama", tana girgiza kai tana kuka haka Sadiq ya jata yayi sama da ita ya rage daga Abui sai Abu dake riqe da Batuul snn Asheikh, Asheik ya dubi Abui yace "Alanguro akwai Zamzam a kusa?" Abui yace "Ehh bari a d'auko",
[11/15, 11:15 AM] โ€ช+234 810 957 2036โ€ฌ: ๐Ÿ’–๐Ÿ’BATUUL๐Ÿ’–๐Ÿ’

84

By phartiemarhk

Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*



Wani nannauyan ajiyan Zuciya Aunty ta sauke lokacin da Yusra ta mik'o mata wayanta tace "Mama ga wayan inji Yayya wai ta gama", karb'an wayan Aunty tayi tace "Kuje ku shirya, its getting late, kice wa Fa'eezah a gama sa muku kaya ku tafi", kai Yusra ta kad'a tace "Toh Mama", daga haka ta fice tana tsalle, wayar ta sake janyowa ta dialling number Baba, ringing biyu ya d'aga, jin muryan Aunty a sanyaye ya sashi saurin cewa "mey ya samu muryanki haka, its so weakening", kamar jira takeyi taji muryan Baba hawayen dake cike idonta ya gangaro, ido ta bud'e ta lumshe snn tace "Uncle ashe Batuul ce bataji dadi ba saida aka dawo da ita d'azu Ammah tamin waya tana fad'amin wai sun dawo da ita tana can gidansu, shine nakeso in ganta koma mu taho gidan tare, we should treat her here a gida hankalina sam yaqi kwanciya, inason ganinta Uncle", "Maryam", Baba ya kirata daga d'aya b'angaren, kasa amsawa tayi har saida ya sake cewa "Maryam", kuka ta fasheda ta kasa amsa kiran da yakeyi mata, Baba dake zaune office yace "Subhanallahi Maryam kuka kuma, mey kikeso?", cikin sheshekar kuka tace "Uncle gida nakeso ta dawo, hankalina zaifi kwanciya in ina ganinta, kaga fa cewa Ammah tayi batasan mey ke damun Batuul d'in ba, toh haka zatayi ta zama da ciwo ba'a nema mata magani ba Uncle", D'an Murmusawa Baba yayi yace "Haba Maryam, kada son y'arki ya rufe miki ido ki manta da cewa tanada aure, kinfi kowa sanin yanzu duk wani nauyi da responsiblity d'inta na kan mijinta, in kikace zaki dawo da ita gabanki bakya tunanin kin musu shishigi har ma suyi tunanin gazawar su muka gani, am very sure kin san su masu kula da Batuul ne dama duk sauran yaran nan ko bama nan", tana share hawayen dake zubo mata tace "Uncle nifa bawai gani nayi sun kasa ba, rashin sanin takamaimai abinda ke damunta da ba ayi bane yafi d'aga min hankali", Abui yace "Duk naji wannan, ki kwantar da hankalinki da izinin Allah zata samu sauk'i, tunda shi Aliyun ya sanar dani rashin lafiyarta, yanzu haka sun d'auko masu magani ana dubata, kiyi mata add'ua sosai kinji, sai kiga ta samu lafiya kamar da, amma in taga kina tada hankalinki itama nata hankalin kinsa tashi zaiyi", kamar Baban na gabanta ta shiga gyad'a kai tana share hawayen fuskarta, da haka ya samu ya rarrasheta ya kwantar mata da hankali

Sadiq ne ya d'auko Zamzam d'in da ake buk'ata a side d'in Abui, a cup Asheikh ya d'an tsiyaya snn ya samu waje ya zauna ya fara tofi cikin ruwa, Abu dai har lokacin ya kasa cewa komai sai ido da ya zuba mata idonshi duk ya kad'a, motsin kirki ya kasa yi, he is so freaked, gani yakeyi duk wanda ya tab'ata ce mishi za ai ta bar rayuwa, Asheikh da ya gama tofin shi ya miqe ya dawo gaban kujerar da Abu ke riqe da ita, Abui yace "Aliyu ko zaka samu a gyarata tasha maganin", kamar badashi akayi maganan ba, saida Asheikh ya sake maimatawa snn ya d'ago rinannun idanunshi dake cike taf da hawaye kamar wani yaro, kai Abui ya kad'a mishi alamun he should be strong tare da zuwa kusa dashi ya zauna ya dafa mishi kafad'a yace "Abutturab you have to be strong okay?, zata samu lafiya In sha Allah kaci gaba da yi mata addu'a, ido ya lumshe snn yace "Abui bata mutu bako, baza ta mutu ba In San Allah", sosai Abui ya tausaya mishi yace "ciwo ai ba mutuwa bane Aliyu, zataji sauki da yardar Allah, kayi yadda yace d'in ka kwantar da ita a nema mata lafiya", gani yakeyi kamar in ya sauketa daga jikinshi wani abun zai sameta, kallonta yayi for some seconds snn jiki a sanyaye ya shimfid'eta kan doguwar kujerar amma har lokacin hannunta na cikin nashi, Asheikh ya karaso gaban kujeran ya tsuguna daidai kan Batuul snn ya mik'awa Abu ruwan yace "amshi ka shafa mata a fuskarta", hannu Abu ya mik'o ya tsiyaya mishi ruwan snn ya shafa mata shi a fuska, bayan ya gama ya sa a mik'o k'aramin spoon yace Abu yana sa mata droplet a baki, jiki a sanyaye ya anshi cup d'in ya d'ebi kad'an ya d'iga mata shi a baki, wani irin dogon numfashi taja da ya sa Abu saurin kamota yace "Batuul am glad you are alive, don't leave me again kinji, don't plsss", sai ga hawaye nan idonshi, bata bud'e ido ba haka nan batasan abinda akeyi ba, kamar ba ita tayi wannan numfashin ba ta koma yadda take d'azu, Asheikh yayi gyaran muryan yace "Alhamdulillah, wannan ruwa da ta sha ya dad'a tabbatar mana da lallai asiri akayi mata kuma yana nan cikin jikinta, yawo yakeyi gaba d'aya jikin nata dan a ruwa aka jefa sihirin da akayi mata, yadda yake yawo cikin ruwa haka itama yake yawo cikin jikin nata snn gaba d'aya rayuwar aka so ta bari da ita da abinda ke cikinta amma da yake Allah yayi tana da saurin numfashi bata mutu ba sai dai za a ci gaba da magunguna snn anayi mata sauk'ar Qur'ani da kuma tofi kullum, In sha Allah da yardar Allah zata samu sauk'i", Abui yace "Subhanallahi, La hawla wala quwata illa billahil aliyyil Azim", Sadiq dake tsaye shi ma tun d'azu ya rasa ma abin fad'a, yanzu har Batuul abar ayi ma asirice, duniyan nan is so cruel, Allah ya bata lafiya su kuma Allah ya toni asirinsu koma su waye sukayi mata", kamar wanda aka tsikara haka Abu ya mik'e ya isa gaban Asheikh yace "Asheikh inaso in san su waye sukeson cutar da ita da dalilinsu na cutarta, yanzun nan bama sai anjima ba, Ko su waye su sai nasa sun gane kuaransu na cutar min mata da sukayi", Asheikh yayi murmushi yace "Toh mu dai baza muce ga wadanda sukayi mata ba har sai ta samu sauk'i, in akwai likita sai a samoshi ya riqa dubata da abinda ke jikinta, snn tunda ba abinci zata ci ba, su sai su duba suga yadda za ayi tana samu, mu kuma a namu b'angaren zamuyi kok'arin ganin mun taimaka da addu'a", Jinshi kawai Abu yayi amma ba wai ya aminta da zancen ba, Abui yace "Toh Asheikh mun gode sosai", yace a k'ira mishi Aunty Amna ko Ammah yayi musu bayanin sauran magungunan nata da yadda za ayi amfani dasu, Aunty Amna ce tazo amma Abu sam ya kasa ya tsare sai shi aka bawa magungunan yace "Zaitun d'in za a riqa shafa mata shi a dukkan jikinta, Ma'ul ward d'in kuma ana d'iga mata shi a baki, kad'an kuma a saka a wool a kai mata hanci ta shak'a, Habbatus saudanma jikinta za a riqa shafewa dashi kamin ta kwanta, Abu ne ya anshi

1 Comments On BATUUL
avatar
hafsat-9-3

12 months ago

Reply

Nice book

Please Login or Register in order to submit comment