Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta tace ta k'oshi, mik'ewa yayi ya yiwa Ammah sallama akan zaije ya shirya suje gidansu Ajiddeh.

Wayan hannunta ta k'urawa ido xuciyarta na bugawa da karfi ga wani mugun bacin rw da ya baibayeta, gumi yana ta tsatsafo mata, mesa takejin faďuwan gaba ne duk lokacin da taji sunan Batuul ko ta ganta, yanxu akan yarinyar nan Aliyu ya katse min waya harda yi min tsawa, danshi taji a fuskanta tana kai hannun taga hawaye a fuskanta, rai a b'ace ta mik'e ba tare da tasan mey zatayi ba, ďakin Mum ta nufa hawayen wani na bin wani, mata ne sun kai takwas a ďakin wasu kwance wasu kuma na cin abinci suna hira, ba sallama ta shiga ďakin tafaďa jikin Mum, kuka ta saka kamar wacce aka daka, a firgice Mum ta ďagota tana kallon jikinta taga ko da akwai abinda ya sameta, da taga jikinta lafiya ta tambayeta "meye ya faru haka, mey ya sameki, ko Aliyun ne wani abu ya sameshi", kasa magana tayi sai ci gaba da kukanta takeyi, Yaa zee sake gefe taja tsaki tace "waye kuwa in bashi ba, ai ďan wulakancin nan nema ko baku tambaya ba", tambayanta kowa ya shiga yi amma ta kasa basu amsa, sai da ta gaji dan kanta Mum na rik'e da ita ta ďago tace "Mum kefa kikace idan mukayi aure zai soni fiyeda koma..." bata k'arasa ba Mum ta tareta da cewa "toh meye ya faru yanxu", cikin sheshek'a tace "Mum katse min waya yayi harda min tsawa wai ya kai k'anwar shi asibiti, kuma ba k'anwarshi bace, ni bana son yarinyar nan, duk randa na ganta sai zuciyana ya rik'a faďi, har gumi nakeyi, ko a wajen dinner kuna ganin yanda ya rikice wai dan ta ji ciwo, mum na tsaneta wllh", sai da ta gama tukunna Mum ta mik'ar da ita tace mata "mey na yin kuka toh, ba wannan bak'ar yarinyar bace dai y'ar Maryam, mey zaiyi da ita yana da farar mata kamar ki, ko kuma kin tab'a ganin wanda aka yiwa kishiya duk zuri'armu, ai mun fi k'arfin kishiya, duk jarabar mutum sai dai ya rabu damu rabuwar kuma sai ya ďanďani kuďarsa amma ba dai yace zai shigo da wata matar muna ciki ba, kuma ke ďinnan da kike gani auren mutu ka raba, bare azo zancen kishiya, ki share hawayenki babu abinda zai faru dake", Yaa zee ce ta turo baki tace "Ammah nifa yaron nan bai kwanta min ba, ya rik'a wani huhhura hanci yana kallon mutane ďai ďaya, ni mugun haushinsa ma nake ji", juyowa Ajiddeh tayi cikin rashin kunya tace "ai ni dama bance mijina ya birgeki ba, kinje kin kaso aurenki kin kasa zama a ďakin miji shine zaki dameni da mijina bai birgeki ba, toh ni a haka nake sonshi kuma babu ruwanki dashi, a fusace Yaa zee ta mik'e tayo kan Ajiddeh kamar zata daketa tana faďin "da wa kike, maimaita abinda kika faďa yanxu inji in baki da hankali", Mum ce tareta da cewa "Mey kukeyi hakan wai, kuda zaku haďu ku rufawa kanku asiri kunkama kuna faďa, keh zainab babu ruwanki da mijinta, kema Ajiddeh babu ruwanki da ita" taja tsaki, Jainaba dake gefe itace ta taso ta ďago Ajiddeh tace "ke yanxu kukan na meye kikeyi haka, akan dan ya ďauki yarinyar ya kaita asibiti koko dan taji ciwo ne ya taimka mata kike kuka, share hawayenta tayi tace "Jainaba tun randa na fara ganin yarinyar kawai naji bana sonta, gashi mamarshi sai tayi ta haďashi da ita, haka ranan graduation ďinsu tace wani wai su biyu su tsaya ayi musu hoto, wlhy da na gansu tare sai da zuciyana ya kusa harbawa ga wani gumi da nakeyi kamar nayiwa sarki k'arya duk da sanyin da akeyi, ko jiya da zamuje dinner da ita yazo wai babu motoci a gidan sun k'are duk yawan motocin gidansu amma sai da ta haďoshi da ita, haka ma da aka tashi ta tafi yawonta sai da akayi ta nemanta duk sunbi sun ďagawa kansu hankali, ni wlhy bana sonta", sai da tayi shiru Janaba tace "toh meye alak'arshi da ita?", "ni ban sani ba, kullum ce min yakeyi wai cousin ďinshi ce, ban san ta ina ta zama cousin ďin tashi ba, ko a wajen wannan wushe wushen nasu kunga yadda abokanshi suka tsaya yi mata liki kamar itace amaryar, ni in bata dena shiga harkata ba Allah illatata ma zanyi", Mum ce tace "Ai ba wani alak'a na jini bane a tsakaninsu, abotace kawai a tsaksninsu na iyaye tun suna yara", kai Janaba ta girgiza tace "toh ita mamartasa mesa take son haďashi da ita kullum, ko tana son shi ne ya aureta", ďagowa tayi ta dubi Janaiba da idonta suka rine tace "babu wani, mey zaiyi da ita, kawai dai iko take nuna mishi na ita ta haifeshi dole yayi abinda takeso, kuma ni bata tab'a nuna bata sona ba", "toh ki kwantar da hankalinki, babu abinda zai sami aurenki indai muna raye, ku da zaku bar k'asar ma gaba ďaya, ki kwantar da hnklin ki kinji", kai ta gyaďa kawai ba tare da tace komai ba, haka suka ci gaba da hiran babu namijin da ya isa yi musu kishiya ko da ta wasa ce, da yadda za ayi da duk wani wanda yayi gigin cewa zai yi dashi da wacce zai auran.

Convoy ďin motoci sukayi shida abokanshi bayan sallar azahar har gidansu Ajiddeh, daga waje suka tsaya ya k'ira wayanta, shi yama manta da ďazu ya b'ata mata rai, a dak'ile ta amsa wayan har yanxu ranta a b'ace, ce mata yayi "ki faďawa su Mum gamu nan mun iso, zamu shigo yanxu", tsaki taja tace "meye toh sai ka k'irani ne, ko gidan bak'onka ne", cire wayar yayi daga kunnenshi ya duba ya tabbatar da wacce yake magana, mayarwa yayi ya k'ara wayar a kunnenshi yace "Ajiddeh kinsan da wanda kike waya kuwa", "na sani mana , wanda ya daka min tsawa ya katse min waya akan wata Batuul....", ji tayi an warce wayan daga bayanta anyi sallama cikin natsuwa, Janaiba ce ta anshe wayan tace mishi "Aliyu har kun iso ne", bai nuna mata kamar sunyi komai da Ajiddeh ba yace "ehh muna bakin gate", tace "toh bari a zo a shigo daku", k'wafa yayi bayan sun gama wayan a ranshi yana zanyi maganin ki, bakinki bazai sake min tsaki ba, shi ba dan Ammah ma tasa shi zuwa ba wlhy da bazai zo ba, dan ya gaji da bikinma gaba ďaya, bayan y'an mintuna aka zo aka yi musu jagora, a guest room aka sauk'esu , duk matan suna parlourn lokacin, cikin girmamawa suka gama gaishesu sannan suka sa aka shigo musu da akwatuna dozen , suka ajiye musu bandir ďin dubu d'ai d'ai sabbi guda biyar, sannan suka yi musu sallama suka tafi akan anjima zasu zo ďaukan amarya, daga nan sukayi hanyan gidansu Abutturab ďin zasu gaida su Ammah, kai tsaye side ďin Ammah yayi dasu har sama, Batuul na kwance a palon sama tana kallon e tv, bata zata ba taji sallama, gashinta a buďe, da hanzari tamik'e daga kan kujerar, kamin ta tashi ta rufe kanta har sun shigo, idonshi ne ya faďa akanta , ido huďu sukayi, lumshesu yayi kamar mai jin bacci tare da galla mats hararara, juyawa tayi zata bar falon Massa ya tareta "haba cutie, sai kiyi ta wani b'uya, inata nemanki ina kika shiga ne", a tak'aice tace mishi "ina nan mana, kaine baka ganni ba", taci gaba da tafiya Massa na biye da ita, waje Abutturab ya bawa sauran abokan nashi suka zauna shi kuma yaje ya cewa su Ammah sun iso, a bakin k'ofar ďakin ya tarar da Massa ya juya zai dawo, bai kulashi ba ya buďe ďakin ya shiga, a gaban madubi ya tarar da ita, cikin dakewa yace "ki dena zamawa mutane a gida kai a buďe kina k'ira musu aljanu, kullum za a ganki kai babu ďan kwali", idanunta ta juya dan tasan masiface kawai yakeji da ita tak'i kulashi, ai ko juya idanun da tayi yasashi fixgota har ta kusa faďawa jikinshi tukunna tayi maintaining balance ďinta ta tsaya, duk da haka tana jiyo numfashinshi a fuskanta, "did you just roll your eyes, I mean ni kika harara?", yana tambayanta fuskarsa daure, tsoro ne ya sa ta kasa ansa mishi, kiciniyar k'wace kanta ta farayi daga rik'on da yayi mata idonta taf da hawaye, janyota yayi jikinshi ta faďa k'irjinshi, shiru tayi a jikinshi tana jiyo bugun zuciyanshi, sun kai kusan minti biyu a haka babu wanda ya motsa daga k'arshe ta samu ta k'wace kanta ta gudu ta shige toilet ta rufe, binta yayi da ido ya kai minti uku tsaye daga baya ya juya yyi kwafa ya fice daga ďakin, a palo ya tarar da su Yaa Mera, Aunty, Ammah, Aunty Amna da sauran Aunties ďinsu a zaune suna gaggaisawa, bayan sun gama gaisawa sukayi musu sallama suka tafi, su Ammah sukayi musu fatan komawa gidajensu lafiya, suka haďa musu guzuri dayawa.

Da daddare akaje ďauko amarya, kuka sosai tayi kamin su fito kamar ba ita ke ďaukin ayi auren ba, sosai babanta ya zaunar da ita yayi mata faďa, wa'azi da Nasiha sannan suka tafi, a side ďin Ammah aka sauk'eta ita da y'an uwanta bayan su Ammah sun gama masu fatan alheri sukace akaita side ďin Abutturab, can dare wajen k'arfe goma ya raka abokanshi ya shigo ya tarar da Batuul da Affan zaune sun rakoshi yazo yi musu sallama dan yaje gida wajen Aunty tace mishi ai tana gidansu Farida, shima faďa Aunty tayi mishi kan in yaje school yayi abinda ya kaishi ya maida hankali ya kula da ibadunshi don gobe zai wuce, sunsha kuka sosai, bear hug tayi mishi tace zata koma ciki dan baza ta iya ganin tafiyanshi ba, Farida taje ďauko mishi wani abu, Abutturab ne ya shigo ganin su tare ya bisu da harara, komawa tayi daga ciki zata wuce ta corridor taji an fixgota, baki ta buďe zata saka ihu ya toshe mata baki da ďayan hannunshi, jikinta a sake yake dan bata da k'arfin yin kokawa dashi, dab da ita yake numfashinshi na bugun fuskarta, idonta da ya cika da hawaye yayi ja yake gani, lumshe idon tayi ba tare da ta buďe ba hawayen dake tare suka zubo, jikinshine yaji yayi sanyi , baya son ganin hawayen mace, sassauta rik'on da yayi mata yayi yace "wane moron ďinne ya biyoki har cikin gida kike hugging ďinshi, kasa yi mishi magana tayi dan tasan in ta buďe bakinta to kukane, janyota ya sakeyi yace "ba tambayanki nake ba, waye shi nace",a hankali ta buďe baki zata yi mishi magana ta kasa, sulalewa tayi a k'asa ta shiga rusa kuka, binta yayi ya kamota jikinshi, "mey aka miki kike kuka kuma yanxu, salon ki kuma hada ni da Ammah koh", ya faďa tareda ďagota yana hararanta, cikin sark'ewar murya tace "Affan , he is going", kallonta yayi sannan yace "who is he nace?", a hankali tace "my bestfriend, cousin, everything", dubanta ya sakeyi sannan ya saketa daga rik'on, jin ya sake ta ta ruga ciki a guje tana share hawaye, kusan kwana sukayi itada Farida suna jin tafiyar Affan, kamar ance musu bazai dawo ba.

Ana gobe Abutturab da matarshi zasu tafi Batuul ta koma gida dan Ammah tace sai ta warke zata tafi, ko sau ďaya basu tab'a magana da Batuul ba, in ta shigo wajen Ammah iyakanta tabi Batuul da harara, itakam Batuul ďauke idonta takeyi tace kya ji dashi, ranan da ta koma gida Aunty take faďa mata Baba ya samo mata admission a Nile, tayi hak'uri da London university of economics ďin, bata faďa mata dalili ba, ranta baiso ba amma tayi addu'an Allah yasa hakan ne yafi alkhairi, a ranan da daddare yazo yiwa su Aunty sallama shida matarshi, sai da suka fara zuwa gidansu Ajiddeh tukunna sukayi gidan su Massa, haka sukayi ta yawo, wajen sha ďaya sukaje gidansu Batuul, tana kwance a parlour ita kaďai tana kallo taji bell na ringing, da mamakin waye mai buga k'ofa war haka ta tashi taje ta buďe, manyan idanunshi na masu kama da mai bacci ya watso mata, da sauri ta ďauke nata idon dan wani iri takeji ganin idonshi, matsawa tayi ta basu hanya suka shiga ciki, Ajiddeh bata sanma nan bane gidansu Batuul sai da taga Abutturab ďin ya matsa ta hango Batuul, tsaki taja itama ta shigo, hanyan sama tayi zata hau taji ya biyota a baya, sai da ta hau sama yana biye da ita tukunna ta tsaya, a dake ya ce mata "Aunty fa, i want to meet her", bata ce komai ba tayi hanyan ďakin Aunty, tafiyan a hankali yake kallo daga baya har ta shige ďakin, ya sauk'o k'asa, ďakinta ta wuce bayan Aunty ta sauk'a, samun kanta tayi da tsayuwa a bakin window tana jiran taga tafiyansu, ta daďe sosai tukunna taga sun fito, sai da taga tafiyan nasu tukunna ta faďa kan gadonta, bata murna kuma bata farin ciki, ta rasa gane meke damunta, washegari karfe tara jirginsu ya ďaga suka tafi UK.

Alhamdulillah, a nn xan dakatar da rubuta littafin *Batuul* har xuwa bayan Ramadan idan Allah ya Kai mu da rae da lfya. Duk Wanda na bata ma knowingly nd otherwise, ya yafe min ni ma na yafe masa from the bottom of my heart, Allah Ubangiji ya karbi ibadunmu a wnn wata mai girma, ya sa mu cikin 'yantattun bayinsa don son ma'aiki S.A.W.

Ramadan Kareem fanz.
Urz *Phartiemarhk*
💖💝BATUUL💖💝

24

By Phartiemarhk

Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*


"Wai ba magana nake maka bane Abu, mey ya sami Batuul ďin", Ammah ta fada tare da k'arasawa gadon da ya shimfiďar da Batuul ďin, jikinta ta tab'a taji yayi zafi rau, ďankwalin dake kanta ta cire mata shima taji shi a jik'e, a fusace ta juyo ta dubeshi tace "tun kamin raina ya gama b'aci ka faďa min abinda ya sami Batuul Aliyu", da damuwa a fuskanshi ya ďan dubi Batuul ďin da Ammah ke k'ok'arin cire mata jik'ak'k'en kayan dake jikinta tana kuma sauraran amsarsa, da kmr baxae ce komae ba don yasan ko ya buda baki gskya xae gaya ma Ammah don shi baya karya, gnin kallon da take jifansa da shi yasa yace "Ammah nifa banyi mata komai ba, muna tafiyane a mota ta rik'a min kuka ba gaira ba dalili, ni kuma i couldn't endure it nace mata ta fita min a mota, taki fita kawae na kamata na fitar da ita, nayi tafiyata, gnin ruwa yasa na koma na ďaukota muka dawo", baki sake Ammah ta tsaya tana kallonshi da mmki, rae a 6ace tace "hankalinka ďaya kuwa Abuturrab?, ka ma san mey kake faďa min? tsakiyar dare ka cewa y'ar mutane ta fita maka a mota, don rashin kunya kuma ka bude baki kke min tsari? mesa baka dawomin da ita kace baza ka ďauketa ba Aliyu, yanxu da wani abun ya sameta mey kakeso in cewa Maryam?, wato baza ka dena wannan bakin halin naka bako Abu, a haka mukayi maka auren aka baka amanar y'ar mutane da wnn halin xaka rike masu 'ya, maimakon da kaga tana kukan ka tambayeta kaji mey key damunta shine zaka koreta tsakar daren nn don rashin imani, Allah ya rufa maka asiri da wannan mugun hali naka, ni y'ar mutane da aka aura maka ma nake tausayawa", jikinsa yyi sanyi ssae don ko kadan bae son 6acin ran Ammartasa, har kasa ya durkusa kansa a kasa cikin sanyin murya yace "kiyi hkuri don Allah Ammah, ba mugun hali bane, kullum haka naga take kuka babu dalili kmr wata yarinya karama, plss ki yafe", katseshi Ammah tayi a fusace "rufe min baki, waye baisan Batuul yarinyar arziki bace, magana ma bata isheta ba kukan mey zatayi maka, ko a ina kke ganinta, in ma tayi kukan ina ruwanka da ita, nace ina ruwanka? Toh wlhy ka fita idona in rufe, wannan halin naka tun wuri kayi watsi dashi dan ba na arziki bane", ganin ran Ammah ba karamin bacewa yyi ba yasa ya marairaice mata kmr wani karamin yaro yace "Ammah nace fa kiyi hak'uri, don Allah kar kiyi fushi da ji, wllh hkn bazai sake faruwa ba in sha Allah, plss Ammah na" bnxa tayi masa na wajen minti biyu, shi dae har lkcn yana durkushe inda yake, juyowa tayi tace "nidai na faďa maka kuma ka tabbata gobe da sassafe ka shigo kunje asibiti , bazanyi taking risk ďinnan ba , zakaje ka halaka y'ar mutane sbda wani banxan hujja taka, in kai baka da hankali ni ina dashi", atishawan da Batuul tayi ne ya maida hankalinsu kanta, Da sauri Ammah ta zauna ta dagota ta zaunar da ita tare da ce mata "sannu bitti, ina ke maki ciwo", a hankali ta buďe idanuwanta tayi scanning ďakin, akan Abutturab ta sauk'e idonta, shima ita ya zubawa manyan idanuwanshi kamar mai shirin bacci har lkcn bae mike daga durkushen da yyi ba, baka tantance fushi yake ko akasin sa, maza tayi ta kawar da idonta daga kanshi ta cewa Ammah "sanyi nakeji", cikin hanzari Ammah ta mik'e tare da cemata "tashi bitti ki cire kayan nan jik'ak'k'u, ki canjasu kinji", k'ok'arin cire mata rigan jikinta ta fara, cikin jin kunya ta rike rigan tace "Ammah tulukin"(Ammah zan cire da kaina), sake mata tayi tana jiran ta cire taga kuma bata da alamun cirewa, ďagowa tayi ta dubeta tace "bitti cire mana, sanyin kar yayi miki yawa", ďago kai Batuul tayi ta dubi inda Abuturrab yake, idonshi kyam a kanta, sunkuyar da kai tayi, Ammah ce ta dubi inda Batuul ďin tabi da ido ta ganshi a durkushe ta hade rae tace "Mey kuma ka tsaya ka sata a gaba kana kallo, kaje kuma da sassafe kazo kai kaita asibiti", murmushin da bae shirya ba yyi a sanyaye ya mike yace "Sai da safe Ammah" snn ya juya , da yaje bakin k'ofa sai da ya kuma juyowa sukayi ido huďu da Batuul ta ďauke idonta da sauri ya juya ya fice, yana fita Ammah ta dubeta tace "Bitti, tashi muje kiyi wanka ki canja kaya, ni bansanma ina yarinyar nan ta karkaďa ba, ita taimaka mata ta cire kayan jikinta da sarkan da komai ta kaita toilet, ta haďa mata ruwan wanka mai zafi tukunna ta fito, Ammah na fita ta tub'e kayan dake jikinta ta shiga bathtub ta zauna a ciki, ta kai minti ashirin a ciki sai da taji ruwan ya fara hucewa tukunna ta fitodaga ciki, da bathrobe ďin da yayi mata yawa ajikinta ta fito, Ammah ta tarar ita da Farida har ta canza zuwa kayan baccinta zaune suna hira, Farida na ganinta ta mik'e cikin sauri ta isa wajen Batuul, rik'eta tayi tareda da zaunar da ita akan gadon a hankali tana kallonta kamar wacce aka ce mata Batuul zata karye in tayi k'wak'waran motsi, sai da ta tabbatar Batuul ta zauna tukunna tace "yanxu Ammah ke faďa min abinda ya faru, ni bansan baki tafi ba ai, na nemi ki a hall ďin ban ganki ba, daga baya Yaa Massa yazo yana tambayana ina kike, wai tare zaku tafi shi zai maidaki, toh i thought ma har ya dawo dake gida sai daga baya Ammah ke tambayana wai muna tare, sorry Sweetheart, bs nasha faďa miki Yaa Abun nan mugu bane kina k'in yadda gashi nan ai yana so ya illata mana keh, yanxu ai kya yarda, ni matarshi ma nafi tausayawa, ko da shike ma bana tausayinta tunda ita ta gani zata ita, tayi ta yiwa mutane kallon....", Ammah ce ta tareta da cewa "toh meye na maganan y'ar mutane zaki sa gabanta yayi ta faďuwa babu gaira babu dalili, bana son hiran mutane, ki dai yi na yayan naki tunda shi ya jawowa kansa da bak'in halin nan nashi", a marairaice Farida ta juyo ta dubi Ammah tace "Ammah dagaske nefa, sai waďanda taga dama take kulawa, a gidan nan daga Yaa Abu sai Sadiq take kulawa kamar su kaďai ne mutane", "toh keh meye naki a ciki, dama Abun ne dolenta a gidan ai, tunda shi tana kulashi ai an wuce komai, ke dai ina faďa miki babu ruwanki da ita", baki Farida ta zumb'uro tare da cewa "toh Ammah in sha Allah", Batuul dai bata ce musu komai ba, tana nan zaune tana ta tunanin abinda ya sameta yau, tunani tayi da yanxu wani abun ya sameta mey zai dawo yace ya sameta, wata zuciyar tace mayb yayi k'aryan shi bai ganki ba mana, ai gaskiyan Farida ne da take ce mishi mugu, Ammah ce ta katse mata tunaninta da cewa "Bitti shafa mai ki saka kaya ki kwanta kinji", ta mik'a mata mai da wasu rigunan bacci masu kyau riga da wando milk da brown masu kauri, sai da ta shafa man ta saka kaya tukunna tasa aka kawo mata abinci da magani tasha bayan taci abincin, Ammah ce tace su tafi wajen Abui su kwana dan nan ďin zaiyi musu hayaniya, hakan kuwa akayi, Farida ce ta taimakawa Batuul suka isa har side ďinshi, ko ina duhu an kashe wuta sai ďan hasken tv dake haskawa da alama Abui na ciki bai yi bacci ba, wani ďaki Farida ta shigar da Batuul tace mata ta kwanta zataje dubo Abui taga ko bai yi bacci ba, in yayi bacci zata kaso mishi tv ta dawo, tana fita Batuul ta jawo bargo ta rufe jikkinta dashi tayi kwanciyarta,

Yana isa ďakinshi ya zauna a coffee chair ďin ďakin, kanshi ya dafa ya kai wajen minti 5 a haka tukunna ya mik'e daga k'arshe tare da jan tsaki ya cire jik'ak'k'en kayan jikinshi ya ďaura towel ya shige toilet, sai da yayi wanka tukunna ya ďaura da alwala yazo ya sa kaya tukunna yayi sallah, bayan ya gama addu'o'inshi ya hau ya kwanta, kasa baccin yayi, tunanin yakeyi daga gobe fah Shida Ajiddeh har sai mutuwa ce zata rabasu coz shi saki baya daga tsarinsa, ya rasa gane farin ciki yake ko bakin ciki, toh ya ma akayi na aureta ko tun can dama ina sontane, mik'ewa yayi cak daga kan gadon kamar wanda aka tsikara, kasa bawa kanshi ansa yayi kuma yasan babu mai bashi wannan ansa, yanxu komai nashi sai da Ajiddeh hatta gadon da zai kwana, shine komai nata yanxu a rayuwa, responsibility ďinta gaba ďaya ya dawo kanshi, he has to protect her with all his life kamar yadda zai yi protecting nashi, zuwa ya farayi yana kaiwa da komowa a tsakar ďakin, idonshi ne ya sauk'a akan hannunshi, glitters ďin jikin kayan Batuul ya gani da suka mak'ale mishi a jiki, duk da yayi wanka amma baisa sun bar jikinshi ba, zama yayi daga bakin gado yana bin duk inda glitters ďin yabi, tunowa yayi da ranar da ya fara ganinta har ixuwa yau ďinnan da yazo ya kwantar da ita kan gado, ranshi ne yaji yana mishi duk babu daďi, duk sanda ya ganta sai yaji zuciyarshi na yi mishi double flip, gashi Ammah kullum sai ta haďashi da ita har ya kai ga yau Ammah tayi fushi dashi duk a kanta, iska ya furzar daga bakinshi tare da cea damn it ya daki gadon da yake zaune a kai da k'arfi, yanxu gobe ma tace sai na kaita asibiti, da damu wa fuskarshi yace Allah ya kaimu.

Abui da kanshi ya shigo ya tada su Batuul suyi sallah asuba tukunna ya wuce masallaci, a can ya haďu da Abutturab suka gaisa bayan an idar da sallah, ce mishi yayi ya sameshi idan gari ya waye ya amsa da toh kowa yayi side ďinshi, Su Batuul kuwa na yin sallah suka koma bacci, k'arfe 8 yayi side ďin Ammah dan ta shaida mishi yazo da safe ya kai Batuul asibiti a duba ta, yana shiga ya

1 Comments On BATUUL
avatar
hafsat-9-3

12 months ago

Reply

Nice book

Please Login or Register in order to submit comment