Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

komai.

Tuk'i sukeyi hanyar Jere, Driver sai dariya lbr raha yake yi yana kyakyatawa, yana son fita irin wannan da Dad keyi ba tareda entourage d'inshi ba, kamar daga sama sai ganin mata sukayi sanye da Hijab d'inta ta shigo titin a guje, ji kake k'iiii ammma ina saida suka buge ta, daga nan sukayi losing control d'in tasu motar, Babu abinda Daddy yake fad'i sai "Innalillahi wa inna illaihi rajiun", abinda ya dinga nanatawa kenan har motar taje ta bugi wata bishiya snn motar ta tsaya, kan kace meye mutane har sun cika wajen wasu suna wajen matar da aka buge wasu kuma sunyi wajen motar, jin surutun mutane yasa Dad sanin lallai da sauran ransu, a hankali ya d'aga hannunshi da yakeji kamar ba nashi ba ya tura k'ofar motar, Driver dake gaba sai faman kokuwa yakeyi da airbag da ya rufe mishi fuska, mutanen dake wajen ne suka taimaka musu suka fito daga cikin motar, daga can Side d'in sukaji ana ihun "ta mutu", wasu suna "ba mutuwa tayi ba ayi saurin kaita asibiti", da sauri Daddy ya karasa gurinsu, ganin matar taji ciwo sosai yasa cikin hanzari yace "Dan Allah bayin Allah akwai wani wanda ya santa cikinku sai muje dashi asibiti dake cikin gari", duk mutanen dake gurin kowa yace su gaskiya basu tab'a ganinta ba, haka duk suka riqa zuwa suna kallonta suna basu santa ba, ganin ana b'ata lokaci yasa Dad yace musu "Toh koh zaku had'a mu da wani da kuka yarda dashi mu tafi asibitin dashi, sai yaje ya gano inda muke ko daga bayane in Allah yasa an samu y'an uwanta sai mu dawo da ita", duk yawan mutanen dake gurin nan kowa mak'e kafad'a yayi yace shi baxa shi ba, Mutumin birni ba abun yadda bane", d'an k'aramin tsaki Dad yaja yace "Ado zo mu taimaka mu sata mota, mutanen nan ba lafiya ne dasu ba", Ba b'ata lokaci Ado yazo suka kamata suka sata mota, mutanen ganin dagaske suke tafiya zasuyi da ita yasa suka kama surutu, kota Kansu Daddy baibi ba yacewa Ado yaja motar su tafi, Abuja suka karaso direct suka wuce asibiti lokacin ana kiraye kirayen Sallar Magrib, suna zuwa aka karb'eta aka fara bata taimakon gaggawa

Bayan Asheikh ya koma guest side ne Abu ya d'auki Batuul yayi d'akin Ammah da ita ya kwantar da ita kan gado, ya jima yana yi mata addu'a da fatan samun lafiya kamin Ammah tace yaje ya watsa ruwa yayi Sallah dan ko azahar da la'asar d'inma duk a gida yayisu, sam yaqi barin wajenta, abinci kam har lokacin ba a samu ya shiga cikinshi ba, tunda ya dawo sai yanzu ya shiga d'akinshi, gaba d'aya ya manta da zancen wata Ajiddeh a gidan, ajiyar zuciya ya sauke ganinta zaune bakin gadon kamar mai jiran ace cas ta sa gudu, K'araswa yayi cikin d'akin ya zauna kan gadon tareda riqe kan da duka hannayenshi, a hankali ta dawo gefenshi ta zauna ta d'an dafashi tace "Sannu, how is she feeling now?", bai bata amsa ba sai rungumeta da yayi tsam a jikinshi, har saida ta tsorata jin irin force d'in da yasa a hug d'in, kok'arin kwace kanta takeyi amma sam bai saketa ba, maganganun Asheikh kawai yake tunawa da yace da abinda akayiwa Batuul ta fara wannan ciwon, a hankali ya d'aura fuskarshi kan wuyanta ya fara magana a hankali "I can't risk losing her for anyone, they were trying to hurt her, so suke su rabata da rayuwarta, Mey tayi musu zasu maka haka?", kyarma jikin Ajiddeh ya fara bugun zuciyarta ya tsananta har wani danshi takeji yana bin jikinta, saketa yayi ya rik'o kafad'unta yace "Hauwa do you know they wanted killing her?, an encounter with them will have to b their worst nightmare, I will make them pay for each pain they caused her", da sauri Ajiddeh ta d'ago itama idonta duk ya cicciko da kyar tace "Its okay babe, they will surely pay for it, amma kasan su waye?", kai ya girgiza mata alamun No, ta saka hannayenta cikin gashinshi tace "Everything will b fine kaji, kaje kayi wanka, you need rest", mikewa yayi ya shirya ya shige toilet, baki Ajiddeh ta toshe ta saki wani irin kuka, tausayin rayuwarta ta fara, in dai Abu ya gano she is behind komai tasan zamansu ya xo karshe, har ya fito daga wanka tana nan inda ya bar ta, cikin few minutes ya shirya cikin kananun kaya ya dawo kusa da ita ya xauna yace " You also need some rest, ki tafi kiyi wanka, farida will get you something to eat sai ki kwanta" mikewa yayi ya fiddo mata da towel ya mika mata ta karba a sanyaye ta mike ta shiga bathroom din, kwanciya yayi ya lumshe ido ya dafe kansa da yayi masa nauyi, ji yake kamar ciwon Batuul ya dawo jikinsa kawai, da yake a gajiye yake gashi tun jiya rabonsa da bacci, lokaci daya baccin ya daukesa.

Washegari Aunty Jainaba bata koma gida ba sai da ta k'ara kwana har biyu snn ta shirya Mum ta had'ata da kulle kullensu da suka koma gun boka suka amso bayan sun gama planning irin wulakancin da za ayiwa Idrees, shi da kanshi yaje ya d'aukota a airport, tun daga airport d'in taga yadda yanayin shi suka canza, ganin yana wani shan kanshi itama ta watsar da kashinshi a ranta tana ayyana yadda zataci ubanshi har suka isa gida, Babu kowa a gidan tasan duk yaran na makaranta masu aiki na b'angarensu, d'akin ta bud'e ta shiga, turus tayi ta tsaya ganin komai na d'akin an canja shi snn ga jerin sabbin akwatuna an a d'akin har set uku, juyowa tayi zata mishi magana cikeda bala'i, dama kan wannan surprise d'in nashi ne ya sata baro aikin da takeyi can Abuja ta taho amma ganin ba fuska ta kasa bud'e baki
[11/15, 11:15 AM] β€ͺ+234 810 957 2036‬: πŸ’–πŸ’BATUULπŸ’–πŸ’






85






By phartiemarhk






Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*





Cikeda masifarta take kallonshi, shiko karasowa yayi hannunshi cikin aljihun wandonshi yace "Sit!, magana zamuyi", kallonshi ta tsaya yi a tsagere kamin ta zauna ganin duk ya canja mata kamar ba Idrees d'in dake shakkarta da gudun b'acin ranta ba, wanda in ta fad'i abu jiki na rawa zai d'auki maganan, had'e rai tayi ta dake tace "Wai kai yanzu sabida tsabar wulakanci kan wadannan tsinannun kayan naka kasa na taso na baro muhimman abubuwan da nakeyi a Abuja na taho Lagos?, toh wlhy yanzu maza maza ka kwashe tsiyarka kuma gyaran ma ni ba irin wannan nace maka inaso ba ai", ba yabo ba fallasa ya fara magan yace "Tun baki san kayan mene ba kike wannan b'ab'atun, toh kaya dai nakine in baki sonsu ki zubar dan haka al'ada yace min kuma itama d'in haka nayi mata", katseshi tayi da hannu tace "Kayi wa uwar wa irin wadannan kayan, dan cin mutunci irin naka ma ba ni kadai kayiwa wadannan kayan ba harda had'ani da banzaye, nasan bazai wuce wad'annan masu kafar sauron bane da ke yawo a cikin gari kayi mana tare dasu, nasha fada maka ka dena had'ani da wadannan matsiyatan kana mana kaya tare......", bata rufe baki ba sai ji tayi yace "Aure zanyi next week, Kayan fad'ar kishiya ne gashinan snn wannan yawon naki daka yau kin barshi kenan, in har badaa izinina kika fita ba toh koma inane kikajeshi karki dawo min gida, kiyi zamanki a can", brain d'inta ne ya dena functioning for a minute, kamar a planet Neptune take jinta sbd yadda taji tana yawo saman iska, komai na juya mata, ido kawai ta zuba tana kallonshi har saida hankalinta ya dawo snn ta miqe tana cire duk wani abu dake kanta dan ji takeyi sun mata nauyi, takowa tayi tazo gabanshi tana mishi wani mugun kallo tace "Kace meye?, Aure?, Idrees ashe ko lallai zaka tafka babban kuskure na rayuwanka da baka taba yi ba wlhy, tun wuri ka gyara maganarka, kai d'in banza har ka isa tozartani kayi min kishiya?, wlhy Allah baka isa ba, bamu gaji ayi mana kishiya ba, You had better take back your words tun muna mu biyu da kai kamin duniya ta jimu, kai ka ma isa kayi aure, toh duk munafikan da suka saka yi dan ganin bayana sunyi kad'an, Ka koma kace musu ta Allah ba tasu ba ni nafi karfinsu, ai babu mai yimin wannan tijarar ni nasani inba wannan tsohuwar da ka ajiye can gida ba", Tasss ya d'auketa da mari da yasa hawayen dake idonta ya shiga zubowa, mik'ewaKame tayi cikin zafin rai ta cakumo rigarshi tana "Wlhy sai kasan ka mareni, munafiki kawai maci amana, azzalumi, wlhy ba ni ka wulakanta ba sai tsohuwar banzar da ko tafiya batayi daka ajiye a gida, kwace rigarsa da ta cukwuikuye yayi daga hannunta snn ya kara mata wasu lafiyayyun marin, cikeda fushi ya shiga bugunta ko ta ina, duka yakeyi tana ihu tana zage_zage, duka yayi mata sosai har saida yaga ta jikata snn ya jefar da ita yayi yace "Keh kinyi kad'an, nan gaba koda wasa kika kuma zagar min Family sai nasa kinyi regretting, keh d'in har wata matar kirki ce da baza ayiwa kishiya ba?, mey kika iya a auren da har zai hanani yi miki kishiya kullum in kika fice kika bar gari sai lokacin da kika ga dama kike dawowa, wane mijin ne zai yadda matarsa take irin wannan shashancin, Y'ay'an da kika haifa da kansu basu san dad'in uwarsu ba, basu taba samun time d'inki, I have finally made my decision, aure ne nan da sati biyu zanyi shi" ya tsallaketa yayi ficewarsa daga d'akin amma har lokacin bakinta bai mutu ba sai zazzaga rashin mutunci takeyi, da k'yar ta iya samu ta mik'e ta janyo jakarta ta ciro wayarta daga ciki, tana kuka ta shiga neman layin wayar Mummy, bugu d'aya ta d'aga daga d'aya b'angaren tace "Wai uwar mey ya miki da ya uzzura miki da dawowa, jarababbe", Jainaba ta fashe da wani matsanancin kuka tace "Nikam na shiga uku, Yaya kasheni yakeson yi", Mummy tace "Kasheki? Dan uwarsa shi ya haifake da zai kasheki, shege matsiyaci", Jainaba na sheshek'a tace "Yaya wai aure zaiyi shine ya kirani harda kayan fad'ar kishiya", Mummy ta buga k'irji ta miqe tsaye tace "Ni Zuwaira, Jainab Bakal Abuki, da hankalinki kike kiramin mijinki aure zaiyi?", Jainaba na kuka ta gama fayyacewa Mummy gaskiya da karyar abinda ya faru, Mum tasa salati, nan ta rarrashi Jainaba akan zasu nemo maganin matsalar snn suyi maganinshi, daga nn sukaci gaba da zaginshi da yadda za aci uban nashi daga nan sukayi sallama






Tun da suka karb'eta sukayi emergency suka fara aiki akanta basu fito ba saida suka tabbatar she is fine, sai bayan awa uku suka fito suka barta ta huta bayan sun mata allura, Office d'inshi doctor ya dawo bayan ya sa an maidata Amenity, nan ya tarar da Dad zaune anyi mishi treating hannunshi da yaji ciwo, bayan ya zauna ne ya fara yiwa Dad bayanin abinda ya sameta "Sir she is fine, Yeah she had a minor cut on her at her back, some wounds on her head which made her lose a lot of blood, that's what cause the fainting and a broken arm, but she will be awake in some hours time and then she can be taken home", wani irin ajiyar zuciya Dad ya sauk'e jin tana raye snn zata samu sauk'i In sha Allah yace "Can we see her now?", Doctor ya kada kai yace "Yeah sure Sir, lemme calk the Nurse to lead you there", haka akayi yana danna bell Nurse ta shigo ya fada mata inda zata kai Dad da haka yayi mishi sallama tareda godiya yabi Nurse har d'akin da aka kwantar da matar, a hankali suka tura kofar d'akin suka shiga, kwance take abinta tana bacci amma da gani ba mai dad'i bane, sun canja mata kaya zuwa wani blue yard, tausayinta yaji a ranshi ganin duk an d'aura mata bandage, daga bakin gadon yace "Sannu Baiwar Allah, tsautsayi ya ritsa dake, Allah ya baki lafiya",,, sosai yake jin tausayin nata har ya fara tunanin ko ina y'an uwanta suke, yanzu hankalinsu gaba d'aya ya gama tashi duk Inda suke, Allah ya basu hakuri, da ta warke zai maidata gida yayi musu bayanin komai snn ta basu hak'uri game da tsautsayin da ya samesu, daga haka yacewa Nurse d'in zai turo masu zama da ita, da haka ya fita lokacin Ado ma an gama duba shi lafiyarsa kalau, sukayi waje suka nufi gida





Tashi yayi ya zauna yana salati tareda fad'in "Innalillahi wa inna illaihi raji'un", juyawa yayi gefenshi yaga Ajiddeh kwance daga d'aya side d'in tana baccinta hankali kwance, mafarkin da yayi keh mishi yawo akai, cikin hanzari ya sauka daga kan gadon ya fita daga d'akin, d'akin Ammah ya nufa kai tsaye ya bud'e k'ofan ya shiga, ko ina babu haske, karasa shiga yayi snn ya kunna wutan bedside lamp, Batuul ya gani kwance sai juyi takeyi a hankali kamar wani abin ke damunta, goshinta duk yayi zufa, Tashi yayi maza yayi switching Ac d'akin, a nan yaga Farida dake kwance kan Sofa, stool ya jawo ya zauna gaban gadon yana kallon Batuul dake kad'a kai, siririn hawaye na bin kuncinta, hannu ya d'aura kan goshin nata tareda k'iran Sunanta shima yana jin kamar yayi hawayen "Fatima", a hankali, kamar taji kiran sunan ta bar yatsina fuskarta da takeyi, gumin ya soma share mata snn ya cire hular dake kanta ya fara tofa mata addu'a, tun tana motsi a hankali har ta dena alamun tayi bacci, nan ya zauna yana tofa mata addu'a har bacci ya d'auke sa zaune kan stool d'in, Ammah da ta shigo da asuba ta ganshi yana bacci zaune kan stool hannunshi cikin na Batuul sosai ta tausaya mishi, a hankali ta matso gabanshi ta d'an tab'ashi, a d'an firgice ya mik'e yana kallon Ammah, tausayin na fuskarta tace "Abu lokacin Sallah yayi kaji", kallon Ammah yayi snn yace "Ammah Batuul ta tab'a zuwa Ndjamena ne?", kallonshi tayi tana son gano wani abu snn tace "Menene?", Kai ya kad'a snn yace "No its okay, am just asking", bata matsa ba ta kyaleshi tace "Jeka masallaci kaji, lokacin zai wuce", mikewa yayi yana
Kallon Batuul haka ya fita yayi nashi d'akin, Ajiddeh na nan kwance kamar kullum, wanka ya shiga yayi a toilet snn ya fito ya tadata yace tayi Sallah, har ya fita bata tashi ba, haka nan akaci gaba da yiwa Batuul magani, kullum doctor sai yazo ya dubata kuma, Ajiddeh sau d'aya in ta shigo ta dubata take komawa d'akin Abu, sai in an gama abinci ta sauk'o in taga dama, in kuma batayi niyya ba haka zata zauna, amma ko da wane lokaci gabanta fad"uwa yakeyi, ta rasa yadda zatayi da Mum har ta kashe wayarta gaba d'ayanshi, fargabanta d'aya kada Batuul ta farka asirinsu ya tonu, wata zuciyar nace mata ta fad'i gaskiya ko don son da take yiwa Abu amma sam d'ayar zuciyar ta haneta, bayan sati ranan da za a gama yiwa Batuul sauk'ar Al Qur'an ranan ta yanke shawaran fad'iwa Abu gaskiya koda zaiyi sanadiyyan rabuwarta dashi, daren ranan kasa bacci tayi sai juyi takeyi, har Abu ya fita ya barta idonta biyu, lokacin da ya dawo tashinta sallah ma zaune ya ganta tayi tagumi, kallonta yayi yace "Babe what's wrong with you?", ajiyar zuciya ta sauk'e tace "Ba komai", bai sake ce mata komai ba yace "tashi kiyi Sallah, its time", daga haka yayi hanyan waje "Har yaje bakin k'ofa yaji tace "Aliyu", juyowa yayi yana kallonta , kasa fad'a mishi abinda tayi niyya tayi jiki a sanyaye tace "Naga ka rame ne, you should rest, ka rage stress d'in", murmushi yayi mata kawai yace "I will babe, je kiyi Sallah" daga haka ya fita, fad'awa tayi kan gadon ta saki kuka mai cin rai, tasan ko Abu ya hakura ya barta iyayenshi baza su hakura ba, har ya dawo daga masallaci tana nan batayi Sallah ba, ganin ta kwance inda ya fita ya barta yasa ya shigo ya zauna bakin gadon tareda d'agota, jikinshi ne yayi sanyi ya rungumeta a jikinshi yana patting bayanta, kamar wacce aka dad'a tunzurawa ta fashe da wani sabon kukan, cikin rad'a a kunne yace "Shhhh baby, its alright, she will b fine okay?, pray for her", hawaye na zuba idonta ta shiga girgiza kai ta d'ago tana kallonshi, cikin kuka tace "Aliyu pls forgive me, kaji Dan Allah ka yafemin, wlhh ban San mey ya kaini........", kallonta ya tsaya yi da kyau snn ya sake jawota jikinshi ya matse yace "She will be fine kinji, babu abinda kika mata, it wasn't your fault, azzaluman da suka sata in this condition will pay for each pain they caused her, its okay ki dena kuka kinji, she needs your prayers more than your tears, your sister is gonna be alright kinji", kuka sosai ta shigayi har saida ya tausaya mata, ya d'agota ya kama mata gashinta da suke a baje yayi making mata messy bun snn yace "kinyi Sallah ne?", kasa bashi amsa tayi hakan ya tabbatar mishi da cewa batayin ba, kamo hannunta yayi ya kaita toilet ya jirata har tayi brush tayi alwalan snn suka fito ya shimfid'a mata abin sallah ta hau tayi, yana nan zaune har ta idar kuma har lokacin hawaye takeyi, gado ya maidata ya kwantar ya lulluba mata duvet yayi mata peck snn yace "Get some rest and pray for her, she is gonna be alright and back to us okay?", kai ta kad'a mishi, murmushi yayi mata da ta kasa maida mishi snn ya juya ya fita tareda rage mata wutan d'aki
[11/15, 11:15 AM] β€ͺ+234 810 957 2036‬: πŸ’–πŸ’BATUULπŸ’–πŸ’






86






By phartiemarhk






Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*





D'akin Ammah ya koma bayan ya fito d'akinshi, bai tadda kowa ba sai Batuul dake Lullub'e cikin comfy bargo tana bacci, d'akin ya shigo ya tura k'ofar ya karasa ya hau gadon ya zauna, bargon nata ya janye yaga gashinta da ya bud'e tun jiya na nan a bud'e, kallonta yakeyi with so much affection da tausayinta a idonshi, hannu yakai ya gyara mata gashinta ya maida shi baya, kallon face d'inta da ya kara haske ya tsaya yi kamar ba ciwo takeyi ba, dukda ta rame amma kyanta na nan, satinta d'aya kenan kwance anan batareda tasan ina kanta yake ba, d'an murmushi yayi tunawa da yayi yau za a gama yi mata magani in Allah ya yadda ta samu sauk'i ya kai hannu ya shafi gefen fuskarta tareda lumshe ido yace "Haya", hannunta ya kamo cikin nashi cikin sanyin murya yace "Fatima you are more than life itself, nasan kina jina ko Fatima, you are worth everything good life can offer, GWS kinji, I need to tell you how much you mean to me, you've become part of me, you know I never thought I could love anyone, I never tot someone could mean this much to me until I met you, The first moment I saw you, I knew there was something great about you, some vibes I can't explain, Mesa tun a da ban dawo gareki ba, I wish I had known you long ago, You have become a part of me, my Haya, I never knew I had life until I met you, in such a small period you have made me understood what love means, I never knew how it felt to b loved, at the beginning inace k'in ki nakeyi sabida effect da kike casting a kaina, but I was wrong, I was growing fond of you, you became an acquaintance, a friend and the very best person I could ever ask for", d'agota yayi ya d'aura kanta kan cinyarshi ya kama fuskanta da duka hannayenshi, idonshi ya rine har ya fara hawaye yaci gaba "Fatima pls get up, get up and don't leave me, I need to tell you how much you mean to me, I promise to keep you Happy all the time, Plssss Fatima, I really need you, just give me a second Chance to show you how much I love you, I really do", bai damu da drip d'in dake hannunta ba, rungumeta yayi Idonshi duk ya kad'a, a haka Ammah ta shigo ta sameshi, tun daga bakin k'ofa take jiyo maganganun da yakeyi, sosai take tausaya mishi itama har idonta ya cicciko, jiki a sanyaye tazo ta zauna daga gefenshi ta dafa kafad'unshi tace "Babana I've told you times without number addu'a zakayi mata, zataji sauki yau d'innan In sha Allah", kallon Ammah yayi da rinannun idanunshi ya kad'a kai yace "Ammah cewa fa yayi in har aka cikata na kwana bakwai ba a samu nasara saidai wadanda sukayi abin nan sun karya da kansu, su waye haka zasuyi mata irin haka, mey tayi musu Ammah?", Ammah ta girgiza kai hawaye taf idonta tace "Abu be optimistic, Da izinin Allah ya fisu, kuma zata samu sauk'i, mu jira har anjiman a gama mata magani sai muga abinda zai faru, kaci gaba da yi mata addu'a", shiru kawai yayi ya kasa cewa komai, tashi Ammah tayi tace "bari inje in sa a shirya shigowan Asheikh d'in sai inzo in shiryata", da haka ta fita daga d'akin zuciyanta duk ba dad'i ga fargaban dake tattare da ita, bayan ta fitane ya gyarawa Batuul d'in gashinta snn ya saka mata hularta






K'arfe bakwai Ajiddeh taji wayarta na ringing, kin dagawa tayi ganin Mum keh kira, duk fargaba ya cikata har wani sanyi sanyi takeji, zata kashe wayar kenan taga text ya shigo, budewa tayi ganin daga Mum ne, ce mata tayi "In baki d'auki wayan nan ba toh wlhy yanzu zaki ganni gidan da kika maida yafi iyayenki", jiki a Sanyaye ta gama karantawa kamin tayi wani abu aka sake Kira, saida ya kusa katsewa ta d'aga da k'yar tasa a kunneta, muryar Mum taji da daki dodon kunnenta tace "Don uwarki har kinyi girman da zan rika kiranki kina kashemin waya ko Ajiddeh, toh gani nan tafe gidan naku sai kin fad'amin dalilin da ya sa duk kika canja, kamin tayi magana taji kiit an kashe wayar, b'ari jikinta ya hau yi jin abinda Mum tace mata, hawayen ma kasa yinshi tayi tsabar tashin hankali, a ina zata samu mafita ita yanzu, tana yiwa Aliyu son da har in ya rabu da ita toh lallai itama zata rabu da tata rayuwar, d'aukar wayar tayi zata kira Mum tace mata zatazo ita gidan basai Mum d'in tazo ba amma har k'iran ya katse Mum bata d'auka ba, sau uku tana k'ira amma har lokacin bata d'aga ba, hannu tasa a ka ta saki wani razananna ihu ta tsuguna a wajen ta saki matsanancin kuka, shawara kawai ta yanke ta fadawa Abu ganin batada wata mafita, wayar ta jawo ta kirashi taji wayar na ringing a cikin d'akin, takaici duk ya isheta, mikewa tayi taje ta sameshi ta fad'a mishi komai, a ganinta hukunci da zai yanke mata ba zai zama mai tsauri ba snn yana sonta zata bashi hakuri tace duk sharrin shaidan ne, hakanan ta fito ko d'ankwali babu daga ita sai y'ar rigar baccinta, gashin da Abu ya tufke duk ta baje shi, Tana fitowa ta kusa cin karo da Ammah, kallonta Ammah tayi ganin duk ta rikice, da k'yar Ajiddeh ta iya had'a kalmomin daga bakinta tace "Ina kwana", Ammah da ta tsaya kallon yanayinta tace "Kin tashi lafiya?", kai kawai ta iya gyad'awa, Ammah ta tab'e baki tayi tafiyarta tana mamakin Abunda ya sami Ajiddeh yasa duk ta rikice da idonta ya kumbura ya rine kamar wacce tasha kuka, ganin Ammah da Ajiddeh tayi ya sake tsoratata, ji tayi jikinta duk

1 Comments On BATUUL
avatar
hafsat-9-3

12 months ago

Reply

Nice book

Please Login or Register in order to submit comment