Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

d'aya Ammah tayiwa Ajiddeh ta d'auke kanta ta d'ago Abu da ya kwantar da kanshi jikinta ta kama fuskanshi da hannayenta duka biyun tace "You have to be strong, babu abinda zai sameta da izinin Allah, just pray for her kaji?", Kai kawai ya iya d'aga mata kamar wani k'aramin yaro, gaban Batuul d'in ta dawo ta rik'e mata hannaye tace "Bitti sannu kinji, kin kusa samun sauk'i In sha Allah", Batuul kam bata iya cewa komai sai kuka da take tana k'iran sunan Aunty, Ajiddeh har lokacin tana tsaye ta rasa mey ma zatayi gashi babu wanda yabi ta kanta har Abutturab d'in, kamar dama baisan da ita wajen, wayanta ne ya fara ringing cikin jaka, gabanta ne ya shiga fad'uwa ganin mai k'iran nata, Mumm ce ke kiranta, bata d'auka ba saima sawa da tayi a silenta, tana gani haka Jainaba ma ta k'irata amma har lokacin bata d'aga ba daga k'arshe ma kashe wayan tayi gaba d'ayanshi, Addu'a Ammah ta shiga tofa mata, da kad'an kad'an kukan nata ya fara yin sauk'i sai juye juye da take, snn ta d'ago ta dubi Abu tace "kai min ita d'aki", Sadiq dake fitowa part d'insune yaga Ajiddeh tsaye har lokacin yace "Noo, badai tun d'azu kike tsaye nan gun ba, find a place and settle yourself", d'an murmushi ta k'irk'iro mishi ta nemi waje ta zauna bakin kujerun parlourn kamar wata mara gaskiya, ko kallonta Ammah batayi ba tayi side d'in Abui, Abu ta kalla tace "Babe ya jikin nata?", kai ya d'aga mata tareda cewa "she needs rest", ya haura sama da ita, a kan gadon d'akin Ammah ya kwantar da Batuul d'in, samun kanshi yayi shima da kwanciya daga gefenta, rungumeta yayi tsam jikinshi ya saka hannayenshi cikin nata, a hankali kamar wani d'an yaro ya fara mata hawaye, "Fatima I promise to give you all you ever requested for, kiyi hakuri ki tashi ki fad'amin abinda ke damunki, its gonna be hard to live with out you kinji, am used to you kinji Fatima, I will keep you and my unborn baby happy, no harm will befall you just get up and we will live happily", duk surutun nan da yakeyi ko kad'an Batuul bata san abinda yake fad'i ba don tuni baccin wahala yyi gaba da ita, haka yayi ta surutunshi, vibration d'in wayanshi ya katse shi ya kwantar da ita a hankali yayi snn yayi receiving call d'in, "Man ba yau mukayi dakai zaka dawo ba, but Ammah ta qirani wai tana nemana snn kaima ka dawo", ajiyar zuciya ya sauk'e snn yace "I had to comeback, Batuul batajin dad'i", "Subhanallah mey ke damunta, how is she feeling now?", juyawa yayi ya dubeta tana bacci snn yace "Alhamdulillah she is getting better, in kazo we talk", da haka suka gama wayan, fuskanshi ya shafa yana salati ya mik'e, kamar kar ya barta a d'akin ya fice, Ajiddeh na ganinshi yana sauk'owa kan stairs ta mik'e tsaye, saida ya ka'araso parlour ya lura da ita, jiki a sanyaye tace "Zan tafi gida", kallonta ya tsaya yi for some seconds snn yace "nanma gida ne, you can't live ke kad'ai to a new home da ba a tab'a shiganshi ba", kai ta girgiza mishi tace "gidanmu fa zan tafi", "You can stay here in zan tafi sai mu tafi tare", da haka ya k'yaleta nan tsaye yayi side d'in Abui.




Hi everyone, Alhamdulillah Exams is finally over and am getting better, Thank you for d prayers, I can't really express how happy I am to know ppl out there are praying for my Health, Alhamdulillah and abt the previous page, it was from the same source you guys used to get BATUUL from, it wasn't a pirate or fake, ppl have been misunderstanding d whole thing, page 79 is genuine.Thank you allπŸ’–
[11/15, 11:15 AM] β€ͺ+234 810 957 2036‬: πŸ’–πŸ’BATUULπŸ’–πŸ’






81






By phartiemarhk






Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*






Ta kai 10mins tsaye tana jiran ganin Abu ya fito amma har lokacin shiru, jikintane ya k'ara sanyi taja k'afafuwanta ta koma kan kujeran palon, in banda masu aiki dake kaiwa da komowa bata ganin kowa, ko Farida ma bata sake ganinta ba, haka nan ta zauna jigum sai sak'e sak'e take tana warwarewa, can bayan wajen minti ashirin ta jiyo motsi, da sauri ta wartsake daga gyangyad'in dake shirin d'aukarta, k'ofan ta kafawa ido, Abui ne ya fara fitowa kamar kullum yana cikin shigarshi ta girma, murmushin nan na fuskanshi, Ammah ce daga bayanshi sai Abutturab k'arshe, kamar wata mara gaskiya tana hangosu ta mik'e tsaye, a diririce ta bud'e baki da k'yar ta iya gaishesu, Ammah kam ko kallonta batayi ba bare ta amsa mata gaisuwar, Abui ne yace "Lafiya kalau, ya gida ya kuma mai jiki, ashe y'ar uwartaki bataji dad'i ba", murmushi ta k'irk'iro tace "Alhamdulillah, tama fara jin sauk'i", Abui ya kad'a kai yace "Allah ya bata lafiya yasa kaffara Ne", daga haka yayi hanyan waje tareda Abu, itakam tsayawa kawai kallonshi tayi ganin ya fita baice mata komai akan tafiya gidansu da zatayi ba, haka ta koma ta zauna jiki a sanyaye kamar ta kurma ihu, wayarta ta ciro cikin jaka ta kunna ta, kamar jira ake ta kunna nan da nan msgs suka fara shigowa kuma duk yawancinsu daga Mum ne, ignoring d'insu tayi baki d'aya ta mik'e tayi d'akin Abu.





Ammah kam na hawa sama bayan fitansu Abui d'akinta ta wuce kai, Batuul na kwance abinta tana bacci kamar ba itace d'azu ke kukan ba, amma da gani baccin baya mata dad'i, daga gefenta ta zauna tana kallon yanda ta k'ara haske tayi kyau ta rame, hannu ta d'aura saman goshinta taji babu wani zafi, kallon Batuul d'in kawai takeyi tana jin yadda tausayinta ke ratsata, yarinya k'arama da ita amma saida aka samu wani Mara imanin yayi mata wani abin, duniya babu kyau, babu ruwanka da rayuwar mutum amma idonshi yana kan naka rayuwar, in banda rashin adalci da rashin tausayi meye ma Batuul da har za ayi mata asiri, babu komai da izinin Allah sai aikinsu ya lalace, a hankali ta furta "sannu Fatima, Allah ya baki lafiya", sannan ta mik'e ta bud'e closet d'inta ta ciro wani d'an kwalba mai d'auke da ruwan Zamzam ta dawo bakin gadon ta bud'eshi ta tsiyaya kad'an a hannunta ta shafawa Batuul d'in a fuska, wani irin numfashi taja jin ruwan a jikinta, juyawa tayi ta gyara kwanciyarta daga haka taci gaba da baccinta, intercom Ammah ta d'auka ta k'ira d'aya daga cikin masu aikinta, babu b'ata lokaci d'aya daga cikinsu tazo, "inaso ki wanko min Baby cucumber, ki tabbatar ya wanku da vinegar snn ki tafasa fresh milk sai ki jefa cinnamon da cardamom kad'an kada a saka sugar, ki Juyo min a flask, bada dad'ewa ba, snn a d'ora soup d'in offal's", yarinyar dake sanye da uniform d'in cooks tace "okay Ma, za ayi wani abin ne kuma?", Ammah tace "No for now dai babu, ba kun d'ora lunch ba?", yarinyar ta kad'a kai tace "Ehh Ma", Ammah tace "toh shikenan kije ku gama wannan, and be fast", da sauri yarinyar ta amsa ta fice abinta,





Ajiddeh na zaune d'akin Abu duk abin duniya ya taru yayi mata yawa, ta rasa mey ma zatayi taji dad'i, har ga Allah ba son Batuul takeyi ba bare ma a matsayin kishiya amma batason ta zama silar mutuwarta, ko ba kishi musulmace kuma ta san hukuncin kisa kan musulmi, ita inda yadda za ayi kawai ayi koma meye a rabata da gidan amma banda kisan kai, ko haukatata ne ayi, gabanta na fad'uwa take kallon wayan da ta saka silent na ringing, tun d'azu ake k'ira amma ta kasa d'auka, da k'yar ta sa hannu tayi sliding ta kara wayar a kunnenta, tun kamin tayi magana taji muryar Mum na cewa "Dan ubanki tunda yarinyar kanwar uwarkice dole kiqi d'aukan wayata, wlhy Ajiddeh kina jina, kada ki kuskura raina ya b'aci kanki, wani abu ya shiga kanki ne shegiyar yarinya inace akanki nayi sa'ar haihuwa ashe wahalar banza nasha, toh tun wuri kisan abunda kikeyi tun kamin inyi maganinki" Kamar wacce za a jiyo maganan da takeyi tace "Mum mey yayi zafi toh hka, naji kiyi duk yadda kike so amma fa babu ruwana inta mutu, I just want to be happy, yanzu haka mun dawo Nigeria kan ciwon nata muna gidansu Aliyu yanzu haka", kirji Mum ta dafe tace "Naga ta kaina ni Zuwaira, yanzu dan uwarki Ajiddeh kina garin nan shine baki fad'a mana ko kizo gida ba, gidansu miji yafi miki dad'i ko, ina zansa kaina yau dan takaici ni Zuwaira, anya kanki d'aya kuwa Hauwa, lokaci d'aya ki juye ki zama wata sakarya sallamamiya, Wato Bilkisun asirce min keh tayi ko, Ta Allah ba tata ba, duk sai nayi maganinsu daga ita har y'ay'an nata, kuma ki tabbata kinzo gida yau", shiru Ajiddeh tayi tama rasa mey zatace, "Toh" kawai ta iya cewa ta katse wayan, tashi tayi ta fito daga d'akin tayi hanyan d'akin Ammah, saida tayi sallama snn tajiyo muryan Ammah na cewa "Bismillah shigo", tura k'ofan d'akin tayi ta shigah Ammah na zaune kan abin Sallah ta idar da Sallah kenan, waje Ajiddeh ta samu ta zauna tana kallon Batuul dake kwance, takai 5mins kamin ta iya bud'e baki tace "Ammah ya jikin nata?", Ammah ta kalli Batuul dake kwance snn tace "Bacci takeyi tun d'azun, kuma da izinin Allah zataji sauk'i", daga haka basu sake cewa komai d'akin shiru, Farida ce tayi sallama ta shigo, da mamaki ta tsaya kallon Ajiddeh, rabonta da ganinta a d'akin tun satin bikinsu da Yaa Abu, tab'e baki tayi ta k'arasa shigowa, daga gefen Batuul d'in ta zauna tana kallonta da tausayi tace "Ammah ya jikin nata?, ta farka tun bayan fitana?", kai kawai Ammah ta gyad'a mata alamar A'a, Hannu tasa ta kamo na Batuul tace "Allasarki bestfriend , you will get well soon kinji, In sha Allah", tacewa Ammah, "Ammah mu tafi asibiti mana, turawan nan duk ba aikin kirki sukayi ba, a kaita wajen Dr Zakaa tunda gynaecologist ne zai iya duba matsalarta, tunda cikinta take cewa kullum", Har saida Farida tayi shiru kamar baza tace komai ba can tace "Ai ciwon nata bana asibiti bane, Abui sun tafi tahowa da Ashiekh Zai mata addu'a ya gane mana matsalar", k'ululu cikin Ajiddeh yayi k'ara, gani kawai takeyi Ammah tasan abinda ke faruwa, har zufa taji yana tsattsafo mata, Farida tace "Subhanallah, Ammah Jinns ne suka tab'ata?", Ammah tace "tashi kije ki kitchen ki dubamin ko sun gama aikin da na sakasu, kice su hanzarta, banaso ta farka babu komai a kusa", "Toh", Farida tace tasa kai ta fice,






Lokacin dasu Abutturab suka fita kai tsaye airport sukaje d'auko Asheikh, shike tuk'a motar Abui da malamin a baya amma gaba d'aya hankalinshi na
Kan Batuul, wayan Batuul dake wajenshi ya katse mishi tunani jin yana ringing, dubawa yayi yaga ansa Anty with all sort of hrt Emojies, baiyi picking call d'in ba har ya katse, haka a karo na biyu ma bai d'auki wayan ba, uku da rabi suka iso gida, a guest side aka sauk'eshi, saida Abu ya tabbatar komai daidai snn yayi d'akin Ammah, so kawai yake yaga lafiya, a hankali ya tura k'ofan d'akin ya shiga, babu kowa cikin d'akin sai sanyi da k'anshi mai dad'i, har lokacin Batuul na kwance tana bacci, ajiyar zuciya ya sauk'e snn ya k'arsasa shiga, bargon ya janye bayan ya zauna daga gefenta,murmushinshi mai kyau yayi ganin cute face d'inta da ya k'ara haske, a hankali ya d'aga y'ar rigar dake jikinta ya tsurawa flat tummy d'inta ido, hannunshi yakai kai yana shafawa, bakinshi ya kai ya d'ora mata kiss kai a hankali ya furta "Your Mommah will get better soon kinji Lil princess", jin hannu jikinta yasa ta bud'e lumsassun idanunta tana scanning d'akin, murmushi ya sakar mata da yasa itama ta mayar mishi, da sauri yaga ta tashi ta zauna idonta tab da hawaye, tace mishi "Aunty", hannu yasa ya rungumota ya zaunar da ita kan cinyarshi yace "No Fatima kar ki fara, kiyi hak'uri kinji, kinga bakida lafiya, Aunty da kanta zatazo wajenki kinji, keda zaki koma gidanta ma gaba d'aya ko kin mantaa ne", k'ara widening smile d'inta tayi ta d'ago tana dubanshi tace "Bazan koma UK ba?", yana kallon idonta yace "a ba haka kikeso ba, kince in kin bani Babyna zan maidaki wajen Aunty", zumb'uro mishi baki tayi tace "Toh ai nafison gidan Aunty ne kuma kaine kace in na baka Baby zaka kaini", kallon d'an k'aramin lips d'inta da yafiso kawai yakeyi, yadda ta zumb'uroshi tana pouting, a hankali ya d'aura d'an yatsanshi kai yana zagayesu ya kafeta da ido yace "Will you miss me in kin koma gidan Aunty?", kai ta shiga gyad'a mishi da sauri kamar wata yarinya tace "Ehhen, sosai ma, you are kind ai, you have stopped being bad to me", dariya ta bashi yayi murmushi yace "Was I?", tace "Of course , but that was then ai, da fa ko bansan kana waje ba if nayi approaching wajen heart beat d'ina increasing yakeyi, it runs at a faster pace, I thought ma mayune suka kamani, Aunty kuma sai tayi ta cewa banida gaskiya, but daga baya sai ya dena, I don't know mesa?", matseta yayi jikinshi a kunne ya rad'a mata "Its same with me, duk Inda kike indai naje wajen toh I feel that restlessness, shiyasa I don't want you kusa dani but nima nawa ya daina, kinsan mey ya janyo duka haka?", jiki a sanyaye tace "A ah ni ban sani ba", yayi murmushi ya kamo d'an k'aramin hancinta yace "Its gonna be an assignment, shima sai kin nemo reason d'in before in kaiki gidan Aunty", ta kalli idonshi da ya fara canja kala tayi murmushi tace "Toh ai zan tambayi Aunty ta fad'amin", ya d'age girarshi yace "okay..., yanzu malami yazo yayi miki addu'a, kinga hospital duk ba asan mey ke damunki ba, kuma kinga in ya fara kina shan wahala, so we will try na Asheikh, he is a great scholar", tayi murmushi tace "But ai na warke, kaga I can even jump, dama d'azun kawai shine ya fara", ta shiga k'ok'arin mik'ewa zatayi tsalle, da sauri ya jawota jikinshi ya had'e rai yace "Baby mana, you will get hurt, da Babyn dake jikinki", ganin ranshi b'ace itama taji ba dad'i tace "Na dena toh, but ni ai ba baby bace, your other wife is baby, haka kake ce mata itama haka take qiranka", yayi murmushi ya lakuce mata hanci yace "Okay then you are?.....", ya tsaya kamar mai tunani, caraf tayi tace "Am Batuul", kai ya girgiza mata yace "Yeah nasan wannan, I want a name da ni kad'ai zan na k'iranki dashi", tace "Ni bana so just call me Batuul d'ina, nafisonshi", tayi maganan tana barin jikinshi, kamata yayi yace "Wait, ina zaki", tsuke baki tayi tace "Na gaji da magana ka tafi", ido ya wara yace "Yaushe kikayi magana, I was d one talking fa, do you know how much I missed you?", kamin tace wani abu ya had'e bakinsu, tun tana tureshi bataso har ta hak'ura ta biyeshi, jin an tab'a k'ofa yasata saurin turashi amma har lokacin tana jikinshi, Ammah ce ta shigo d'akin, da mamaki ta tsaya kallon Abu da batasan lokacin da ya shigo d'akin ba, raurau Batuul tayi zata sauk'a daga jikinshi amma yaqi sakinta, Ammah ce tace "Kai yaushe ka shigo, yarinyar ba lafiya tana bacci shine saida ka tadata dan neman magana?", murmushin jin kunya yayi ya shiga sosa kai yace "Ammah ki tambayeta bani na tasheta ba, zaune nazo na sameta tana game", Batuul kam nok'ewa ta dingayi wai ita kunyan Ammah, ido ta wara jin abinda ya fad'a, da sauri ta sauk'a daga jikinshi, Ammah tace "Bitti ya jikin, yayi sauk'i kenan", da k'yar Batuul ta iya gyad'a Kai, Ammah ta k'araso gaban gadon tace "Tashi kici wannan zaisa kiji dad'in jikinki, tun d'azu nake jira ki tashi", Ammah ta mik'o mata plate d'in baby cucumber da akayi slicing akayi cling filming, sannan ta tsiyaya mata fresh milk d'in dake ta k'anshin Cinnamon da cardamom, kasa karb'a tayi sai Abune ya karb'a yace "Ammah ai baza taci ba, sai na bata", Ammah ta hararesa tace "Make sure taci, Asheikh ne yace a fara bata, tasha madaran sosai", yace "In sha Allah" daga haka Ammah ta juya ta fita daga dakin, mikewa yayi ya kuma jawota jikinsa ta fashe da kukan karya tana cewa "Ya Abu ni bana son haka gashi kasa Ammah ta gan ni naji kunya" ya wara idonsa yace "So? Ae bari ma ta dawo ta hada mana ruwan wanka in maki" cusa kanta tayi kirjinsa ta rufe ido tana kai masa duka tana kukan karya, ya kai bakinsa a hankali kan wuyarta ya lumshe ido murya can kasa yace "I... I like you..." Da sauri ta bude ido tana kallonsa, ya wara ido ya shafa cikinta yace "Yes I like my baby"
[11/15, 11:15 AM] β€ͺ+234 810 957 2036‬: πŸ’–πŸ’BATUULπŸ’–πŸ’






82






By phartiemarhk






Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*






Duk da batayi tsammanin fiyeda haka daga maganganunshi ba amma jikinta saida yayi sanyi, janye jikinta tayi daga nashi ta sauk'a ta zauna kan gadon, wani iri ta dinga ji ranta batasan lokacin da hawaye ya shiga zubo mata ba, a d'an tsorace ya kalleta ganin ta fara hawaye da sauri ya kamo hannunta yace "Not again, tashi muje malamin na k'asa.....", bata bari ya k'arasa ba ta warce hannunta daga nashi had'e da murgud'a d'an k'aramin bakinta, da serious expression shimfid'e kan fuskarshi yace "Hey watch out", yayi sauri ya sake rik'ota ganin yanda ta mike kamar zata tashi sama, hawaye ne ya cicciko idonta cikin b'acin rai ta tureshi tace "Let me be, I don't wanna talk to you", ta fizge jikinta hawayen dake fuskanta na k'arasa gangarowa, cikin zafin nama ya dad'a fizgota yana mata wani irin kallo yace "Fatima are you okay?, kinada hankali kuwa, na fad'a miki you should stop being rough okay?, you are carrying my baby, i cant risk anything happening to my baby, beside kema bakida lafiya, are you trying to hurt yourself?, mesa bakijin magana ne", ido ta lumshe snn ta bud'esu a hankali hawayen na ci gaba da zubowa, wani matsanancin kuka ta fashe dashi, baisan lokacin da ya furta "Yasalam", ba ya rungumota sosai jikinshi, zama yayi bakin gadon yana patting bayanta tareda d'an rocking d'inta, yanzu ne yake tabbatar da zancen da yayi da Ammah d'azu da ta ce ciwon Batuul ba normal ciwo bane da sa hannu, in ba haka ba she was jovial yanzun nan lokaci d'aya ta fara acting strangely, ajiyar zuciya ya sauke a hankali ya sunkuyo daidai kunnenta yace "Kinaso nima inyi kukan ko Fatima, I don't like you crying yana d'agamin hankali fiyeda komai, I can feel it a duka pulses d'ina in kina kukan nan, Dan Allah ki dena kinji?", bata d'ago ba
sai ma ci gaba da kukanta da takeyi, ido ya lumshe tareda sake matseta jikinshi yayi pecking goshinta snn yace "Tell me mey ya saki kukan", a hankali ta iya bud'e baki tace "zanje wajen Aunty?", kallonta ya tsaya yi for seconds snn yace "I thought we were done with that Fatima, haka kikeso Aunty ta ganki ba lafiya?, ko kinfiso hankalin Aunty ya tashi in taga yadda kika koma, kinga fa duk kin rame", ya fad'a yana d'aura hannunshi saman wuyanta, "I want you to get better kamin Aunty ta ganki kinji, she will b happy okay?", d'agota yayi yana share mata hawayen dake fuskarta, idanunshi gaba daya na exploring fuskarta kamar maison gano wani abun, Four months back da za a ce mishi akwai ran da zai zauna rarrashin mace kallon you are sick upstairs zai yiwa maishi, amma yau shi da kanshi ya zauna rarrashin yarinya k'arama har yakejin shima kamar zai biye mata suyi kukan tare, murmushi yayi ya jawo plate d'in Baby cucumbeya d'auki slice d'aya ya kai mata shi baki, batayi musu ba ta bud'e mishi baki ya saka mata, haka ya dinga bata har ta cinye slices uku tace mishi ya isheta snn ya d'auki cup d'in madaran nan ya fara bata, shima saida ta kusa shanyewa snn ta kauda kanta, zaiyi magana wayarta dake aljihunshi ta fara ringing, hannu yasa ya ciro wayar, ganin mai k'iran yasa ya mik'a mata






Tagumi tayi ta zubawa wayar dake hannunta idanu, yaushe ma ya zama mutum da har zai wani nemi ta dawo, Mummy ce ta fito daga bedroom dinta sai k'anshi take zubawa ta tsaya kallon Jainaba da tayi tagumi tana kallon wayar hannunta tana mata magana bata amsawa, a d'an tsawace Mum tace "Keee kinada hankali kuwa, tunanin uban wa kike tun d'azu na fito ina miki magana baki sani ba kuma koh shiryawar bakiyi ba bayan tun d'azu nace miki zamu fita", a firgice Jainaba ta juyo snn ta sauk'e Ajiyar zuciya tace "kinga ni banma jiki ba, wai wannan shasha shan ne yake son d'aga min hakali wai lallai lallai gobe in dawo", Mum tana kallonta tace "Waye kuma, shi Idrees d'inne yake ce miki sai kin dawo a goben?, sai yayi himma yazo ya kinkime ki ai, in kinje can dinma uwar mey zai miki in banda jaraba, y'ay'ansa ai kin samo masu kula dasu toh meye zai wani ce ki koma", tab'e baki Jainaba tayi tace "jarababbe d'aya ko biyu, ni da kaina bansan mey zan mishi ba, ni Lagos dinnan ba sonshi nakeba, zama cikin k'abilu ba iyawa zanyi ba", "Mum tace rabu dashi tashi muje inda zamu, zamuyi maganinshi ne ai, so nake inyi maganin wannan sallamammiyar yarinyar nan da batasan mey takeyi ba, wai har ni take cewa babu ruwanta in wannan tsinanniyar ta mutu, kai nasan ba banxa ba har da sa hannu Ajiddeh da hankalinta baxa tayi haka ba", Jainaba tace "Nima haka nake gani wllh in banda haka yaushe ne Ajiddeh zataji tausayin wanna
yarinyar, tsanar da tayi mata koda wuk'a aka bata tsaf zata kasheta amma lokaci d'aya ta wanice ita ba haka ba, gaskiya da ayar tambaya", Mum tayi k'wafa tace "ni tashi muje inma yi mata akayi inma yin kanta ne duk zasuci uwar ubansu, badai ni Bilkisu tayi shirin tozartawa ba, ta Allah ba tata ba, ki taso muje kada raina ya kuma b'aci", Mik'ewa Jainaba tayi tace "muje", a parking lot suka had'u da Daddy zai fita, tsuru tsuru suka tsaya suna muzurai kamar wasu munafukai, har zai shiga motar ya fasa ya kallosu, a d'arare Mum ta k'arasa gurinshi tace "yanxu nakeson shiga wajenka, ashe har zaka fita", kallon shigar dake jikjnta yayi alamar fita zatayi yace mata "ki sameni a part d'ina", ya kalli driver da guard d'inshi yace musu "zaku iya tafiya", da haka ya juya ya koma ciki, gaban Mum na fad'uwa tabi bayan Dad, tasan shi ba mai magana bane kan abu koda yana damunshi amma inhar yayi magana toh lallai abin ya girmama, babban parlour shi ya koma ya shiga tana biye dashi a baya, waje ta samu ta zauna bayan ya zauna cikin nutsuwa yace "Ina Zainab ta tafi sati d'aya kenan rabona da ita", murmushi ta k'irk'iro tace "Laah ai tana gidansu Salma, ai inace ta fad'a maka kafin ta tafi tunda Salman tayi kwana biyu da zata koma shine suka tafi tare", kai ya kad'a yace "Zuwaira keh yanzu zaman yarinyar nan gabanki bai isheki ba har sai ta had'a da yawo", ido ta wara tace "Bafa yawo ta tafi ba, gidansu Salma taje ko nan dinma yawo ne", kallonta kawai ya tsayayi yama rasa mey zaice mata can yace "shirin ina kuma kikayi keh yanzun", tsuke fuska tayi ta had'e rai tace "Y'ar Sa'adatu da akayiwa aure kwanaki toh ta haihu kuma aiki aka mata shine

1 Comments On BATUUL
avatar
hafsat-9-3

12 months ago

Reply

Nice book

Please Login or Register in order to submit comment