Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sun bata tausayi duk da itama tana tausayin kanta na rabuwa da masoyinta amma tasan shak'uwan Affan da Batuul daban ne, ce musu tayi "you guyz there, kun tsaya kuna ta kuka and you are making me an emotional fool here, wont anyone give me a hug", hannayensu suka buďe mata taje itama ta rungumesu, Affan ne yayi k'arfin hali dan shima sun kusa sashi kukan yace musu "its okay, am always the man, just give a call and i will be there right away", murmushi sukayi a tare suka ce mishi "The man", haka sukaci gaba da hiransu sannan suka gyara fuskokinsu suka je inda sauran abokanensu suke sukayi hotuna,




K'arfe 1:30 kowa yayi shirin watsewa, Farida ce tacewa Batuul "muje gidanmu sai daga nan mu tafi prom ďin daga nan it will be easier ko", Shiru Batuul tayi sannan tace " okay muje mu faďawa su Aunty sai su turomin kayana gidanku, wajen Aunty Batuul taje ta faďa mata komai sannan tace okay kuje sai Baa Liman yazo miki da kayanki, mota su Aunty suka ahiga suka tafi , wajen dasu Ammah suke suka k'arasa taga su Ammah ma basa nan daga Abutturab sai wannan farar matar ta zauna daga gaban mota tana ta kumbure kumbure, hango su yayi yabi Farida da harara yace "ina kika tsaya inata k'iran wayanki bakya recieving", ce mishi tayi Yaa Abu a silent wayan yake, banji bane" Batuul ce a ranta addu'a take Allah yasa ba dashi zasu tafi ba, da ta sani da kawai su Aunty tabi in yaso daga baya a kawota, da taga Farida ta buďe k'ofan baya ta shiga ne yasa itama ta buďe ta shiga, tana zama ďaga kan da zatayi suka haďa ido da Abutturab, harara ya sakar mata tayi saurin ďauke kanta sannan yaja mota suka fita daga wajen
💖💝BATUUL💖💝






15





By phartiemarhk





Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*





Sau biyu idonsu na haďuwa ta rear mirror da Batuul tana saurin ďaukewa, daga k'arshe komawa tayi gefe owners corner yadda baza ta na kallonshi ba, ita da tasan shi zata bi ma baza ta bari y'an gidansu su tafi ba, ga wannan heart beat ďin da yaqi barinta kamar heart na shirin fitowa, gaba ďaya ma ita she is not comfortable, Ajiddeh ya duba yaga tana ta fushi, rage volume ďin music yayi sannan ya kallota a hankali yace "Babe meye ne kike ta b'ata rai", zumb'uro bakinta ta sakeyi ta juyar da kanta ga kallon window, bai sake bi ta kanta ba yaci gaba da tuk'in shi cikin kwanciyar hankali har suka isa wuse II, gaban wani tangamemen gate ya tsaya yayi horn, mai gadi ne ya buďe mishi ya sa kai ya shiga, yana shiga ya nemi waje yayi parking, Ajiddeh ce ta fito daga motan shima ya bita suka fita a tare, zagayawa yayi ta b'angarenta yayi mata magana, "wai fushin mey kike yi ne haka, tun a wajen event ďin naga kina ta b'ata rai bayan kuma lafiya muka fito", ce mishi tayi yarinyar nan wacece, meye haďinka da ita da har za a ce kuyi snapping picture daga kai har ita sannan taqi bin motar gidansu sai naku", juyawa yayi ya dubi motar ya kalli Batuul dake danna waya kanta sunkuye, side view ďinta ake gani da lashes ďinta da suka kwanta, kallon da taga yana yiwa Batuul ne ya sata cewa "Aliyu da kai fa nake magana", juyowa yayi yace mata "she is my cousin", kallon mamaki ta bishi dashi dan tasan almost duka cousin ďinshi, beside ai taga yarinyar y'ar minister ce kuma bai tab'a ce mata minister ďan uwansu bane, cikin rashin yadda tace "Aliyu baka tab'a ce min a cousins ďinka akwai yarinyar nan ba, ni gaba ďaya naji bana sonta" ce mata yayi "well there is a first time for everything, yau kin santa", shi da kanshi mamakin kanshi yayi, why did he lie, mey sa yace Batuul cousin ďinshi ce bayan ba haka abun yake ba, ce mishi ta sake "Fine naji, but duk cousins ďinka i like her least, infact i dislike her", da mamaki ya dubet yace "contro, ki tuna da wanda kike magana, i told you she is my family and you are telling it to my face that you dont like her, kar ki manta we are getting married next three weeks, you cant just disregard duk wanda kika ga dama", ranshi da ta gani ya b'aci ne sosai yasa tace "Baby am sorry, i dunno, am just pessimistic about her, i have this negative feelingl, haushi ta bashi yace mata "naji am going, we will talk later", tunda ya shiga mota take tsaye a wajen, tasan halinshi baya son wasa, bare in ranshi ya b'aci, yanxun ma haka tasan sai tayi dagaske zata shawo kanshi, yadda ya figi motan ne kamar mai shirin tashi sama ya fita daga gate ďin gidan, ya tsorata su Batuul ba kaďan ba, maza maza ta jawo seat belt zata saka kenan suka haďa ido, wani kallo ya sakar mata tayi saurin sauk'e kanta a sanyaye, a ranta faďi tayi "kai ka sani, haka kawai kayi ta b'ata rai kana b'atawa kanka rai, ai matar ma da zata aureka ina tausayamata", Farida ce ta matso kusa da Batuul tace cikin raďa "yaje ta b'ata mishi rai shine zaizo ya sauk'e a kanmu, ai kaďan ma ya gani sai ya aureta, dan da gani wannan babu abinda ta iya sai kwalliya, mu dai kar yaje ya zubar da mu", murmushi Batuul tayi tace "kai Farida ke dai , nidai babu ruwana", a wani brake sukaji yaja a gefen titi, tare suka ďago suka dubeshi dan suga abinda ya faru dan su suna ma ce hatsari akayi, ganin da sukayi lafiya yasa su ajiyar zuciya, cikin dakewar murya yace "ďaya ta dawo gaba", a tare suka ďago suka dubi junansu, Farida ce tayi saurin cewa "Batuul kije gaba", a razane Batuul ta kalli Farida, a ranta cewa tayi "Farida are you sick, ya za ayi kice inje gba", ce mata tayi " No am okay here ke kije", cewa Farida tayi kinga ni am by d road, kuma highway ne its risky in buďe k'ofa.....", bai bari ta k'atasa magana ba yayi magana cikin tsawa yace "kuna b'ata min lokaci, ďaya ta dawo gaba, ba driver ďinku bane ni", buďe k'ofan Batuul tayi ta koma front seat dan ta tsani ihu, tana shiga ya figi motar da k'arfi, sauk'e kanta tayi ta sa a tsakanin cinyoyinta dan k'amshin turarenshi ya isheta ta bugun da zuciyarta keyi, kallon ta yayi ta gefen ido yaga ko she is fine sannan ya k'arasa dasu gida






K'arfe uku saura suka isa gida , Suna shiga gida bayan yayi parking suka buďe k'ofofin suka fita, har sunje bakin corridor taji yana cewa "keh", tsayawa tayi taqi juyowa dan tasan sunanta ba keh ba kuma tasan yassn sunanta, saida taji yace waye zai rufe miki k'ofa sannan ta tuna ashe bata rufe mishi k'ofa ba, komawa tayi taje ta tura k'ofan sannan ta dawo ta shiga, A falo ta tarar da Ammah da Sadiq, Ammah ce tace "Batuul kuda zakuyi shirin fita mey kuka tsaya yi, ai da kunyi sauri kun dawo yunda kuna da abun yi", Farida ce tayi maza tace "Ai Yaa Abu ne ya tsayar damu sai da muka kai Ajiddeh gidansu ya tsaya suna ta hir.....", bata k'arasa ba ya shigo da sallama, Ammah akwai yacewa sannu da hutawa yabi Farida da harara ya wuce ďakinshi, basu zauna a falo ba suka haura sama dan basuyi azahar ba, Farida ce ta fara shiga toilet bayan ta cire kayan jikinta tayi wanka tayi alwala ta fito, tunani Batuul ta zauna yi na mesa ma ta yadda da idea Farida na zuwa gidansu bayan akwai wannan masifaffen, bata san lokacin da Farida ta fito ba sai ji tayi ta tab'ata, a ďan tsorace ta juyk tace "hell you scared me", dariya Farida tayi tace "sarkin tsoro, tunanin mey kikeyi", mik'ewa tayi daga kan gado ta fara cire kayanta itama zata shiga toilet da murmushinta na tsokana tacewa Farida "My charming prince", da gudu Farida ta janyota suka zauna a kan gadon a tare tace "Omg, i have been waiting for this moment, bari in k'ira Affan in faďa mishi, tell me about him dan Allah, dogone, fari ne, is he handsome, shekarunshi nawa, ďan inane", dariya Batuul tasa bata barta ta k'atasa tambayoyinta ba tace "I live for you Riri", mik'ewa tayi zata tafi , tayi sauri ta sake janyota tace "Batuul dagaske nake ki faďamin waye shi, finally mun same shi", ce mata Batuul tayi "wasa fa nake miki Farida, ai in zai zo you will b first to know tun ban zauna tunaninshi ba", tsaki Farida taja ta saketa tace "ke dai positive vibe killer ce Allah, ni ban sani ba ko 18 birthday ďinki kike jira kiyi legalizing boyfriend ba", "You still love me", sannan ta shige toilet da murmushi a fuskanta, tana fitowa ta tarar da Farida tana Sallah, itama doguwar riga mara nauyi tasa ta saka hijab ta tada sallah, basu fito ba sai da suka jira aka k'ira la'asar sukayi suka fito, ďan kwali kawai ta ďaura, shima bai rufe duka gashinta ba, irin square scarf ďinnan tayi triangle dashi , dinning suka nufa zasu ci abinci dan rabonsu da abinci tun breakfast, tafiya kawai Batuul takeyi amma ta gaji da bugun zuciyan nan nata dake k'aruwa all the time, addu'a kawai tayi ta ci gaba da tafiya, suna isa dinning suka ga Yaa Abu a kan kujera yana cin abinci hankalinshi kwance, wani irin kallo ya bita dashi ganin gashinta da ya kwanta a kafaďunta har sai da taji wani iri ,kujera Farida ta ja ta zauna, Batuul juyawa tayi zata koma sama dan baza ta iya zama inda yake taci abinci ba ga gashinta da yake a buďe, Ammah ce ta fito daga kitchen ta ganta a tsaye, ce mata tayi "Zauna mana bitti kici abinci, kujeran dake facing Abutturab ta nuna mata, jiki a sanyaye taja kujeran ta zauna, kasa tab'a komai tayi sai da Ammah ta sake mata magana, plate ďaya ta ďauka ta jawo food flask ďaya taga pasta ne a ciki, mayarwa tayi ta ďauko wani, duk abin nan da takeyi in ta ďaga idonta sai sunyi ido huďu dashi, ďayan ne da ta ďauka taga shinkafa a ciki, kaďanta ďiba ta zuba a plate ta janyo bowl ďin salad shima ta ďan saka kaďan, a hankali take ci dan a takure take, hannunta na hagu ta ďago zata mayar da gashinta dake buďe, tana ďaga ido idanunsu suka sake locking, bugun zuciyantane ya k'aru da k'arfi har saida hawaye ya taru a idonta, hawayen da ya gani yana shirin zubowa ya sashi yin tsaki ya mik'e, ido Farida ta bishi dashi tana tab'e baki a ranta tace "masifaffe ko mey aka mishi kuma yanxu yana cin abinci ma sai yayi faďa", Batuul ta duba taga kanta a sunkuye, bata yi tunanin komai ba dan tasan haka cin abinci Batuul yake a hankali, k'ok'artawa Batuul tayi ta mayar da hawayen sannan tayi ajiyan zuciya ta fara cin abincinta





K'arfe 6:30 mai shiryasu for prom tazo, sama suka hau da ita ďakin Farida, tunawa sukayi da ba a kawo kayan Batuul ba, ďakin Ammah taje ta faďa mata ta sameta tana waya, sai da ta jira ta gama waya sannan tace mata "Ammah har yanxu fa ba a kawo kayan Batuul ba kuma tana ta k'iran wayan Aunty not reachable", da damuwa a fuskanta ta tashi tace "toh muje in duba in Sadiq na nan ya kaita ta ďauko ke kuma sai ayi miki kamin su dawo ko" wayan Sadiq ta k'ira yace mata baya gida, driver kuma sun fita da Abui, k'asa suka sauk'o , Abutturab ta gani a palo da remote a hannunshi yana kallon Fast8 a MNET, wajenshi ta k'araso tace "Abu, zaka kai Batuul gida ta ďauko abu, tayi mantuwa ne", tsayawa processing wacece Batuul yayi dan yasan babu Batuul a gidan, sai da tace mishi "kana jina", ce mata Yayi "k'awar Farida ko, Ammah babu wanda zai kaita ne, ina drivers ďin gidannan, ni yanxu ma nake shirin fita", ce mishi tayi "ai sai ka kaita ka dawo sai ka wuce inda zaka ďin", ba dan ranshi yaso ba yace a ce mata ta fito, Farida ce ta koma sama a guje tace mata ta fito za a kaita su ďauko, cikin hanzari ta tashi ta ďauki hijab ta saka suka sauk'o k'asa a tare, Ammah ce tace mata "Bitti maza kije ku dawo da sauri", da toh ta amsa mata ba tare da tasan waye mai kaitan ba, parking space taje taga babu alamun motan da akwai mutum, horn taji daga gefe, anyi wining glass ďin ďayan side ďin k'asa, wajen wannan motan ta k'arasa , tana ganin Abutturab ne a ciki tace "innalillahi wa inna illaihi rajiun" a fili, "Yaa Abu da kai zamu tafi", mamakin salatin da tayi ya tsaya yi kamar na taga wani mugun abu, bai ce mata komai ba ya sa hannu ya buďe mata k'ofa , jiki a sanyaye ta shiga ta zauna, tun kamin ya tada motan yace mata "inane gidan", ce mishi tayi Gwarinpa, Tai Solarin crescent", bai ce komai ba ya tada suka fita daga gidan suka ďau hanyan Gwarinpa
💖💝BATUUL💖💝






16





By phartiemarhk





Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*





Suna shiga Tai solarin crescent gidansu ne na uku by the right, maza tayi ta nuna mishi dan sun kusa wucewa, dan tsaki ya ja ya danna horn aka buďe musu suka shiga lokacin 6:50, fitowa tayi daga motan ba tare da tace mishi komai ba, shima fitowa ya bi ta da kallo yace "Dake ni drivern ki ne shi sa c'mon sense din ki bae nuna maki ki bude baki kiyi godiya ba koh" bae jira cewarta ba ya nufi masallacin dake jikin gidan don yin sallahn magriba, tsaki batuul ta ja ta kama hanyar shiga gida a xuciyarta tana cewa ae ba ni nace ka maido ni ba dae, shi kam yana zuwa bakin gate ya haďu da k'annen Batuul sun idar da sallah xa su shigo gida, gaisheshi sukayi ya amsa musu da smile a fuskarsa ya k'arasa masallaci, Batuul na shiga ta wuce ďakin Aunty, a kan sallaya ta tarar da ita tana sallah, jiranta tayi sai da ta idar tayi azkars ďinta sannan ta juya ta dubi Batuul, ce mata tayi " tun ďazu fa Batuul na aiki Baa Liman ya kai miki kayan shine ya fita ya dawo nace yaje yace shi ya manta ma sam da aiken, kuma Baba na nemanshi a office, yanxu nake jiran Ahmad ya shigo ya kai miki wllh, cewa Aunty tayi "Ammah ce tace a kawoni dan har mai make up tazo" mik'ewa tayi tace bari inje in ďauki kayan, Aunty ce tace mata mu sauk'a k'asa ai kayan ma suna can ba a hawo dasu sama ba , k'asa suka sauk'a suka k'arasa parlour, akwati ne mai kyau purple da bak'i na victoria's secret ajiye daga gefe, akwatin ta k'arasa ta ďauka sannan suka fito waje tare da Aunty, "Batuul banda rawan kai a wajen don Allah ki kama kanki, event ďin dare in banda ma na gama makarantane da bazan bari kije ba, kuma duk inda 10:30 tayi ku dawo gida keda Faridan, ku kula da kanku", "In sha Allah Aunty zamu kiyaye" a tare suka fito compound ďin gidan da Anty, daga gefen gidan k'ark'ashin wani rumfa na bunu mai kyau da hasken wuta ya haska da farin florescent suka hango su Ahmad suna tennis, tsayawa Batuul tayi taga mutumin dake tare da k'annen nata ya rungume hannayensa yana kallon ynda suke buga tennis din with interest murmushi dauke fuskarsa, bata tab'a ganinshi yana murmushi ba sai yau, mamaki ne ya sata tsayawa dan tana ce ma ya tafi, Aunty ce tace "ba Abutturab bane wannan ko shi ya kawoki dama", juyawa tayi ta dubi Aunty tace "Eh shi ya kawoni" Anty tace "Batuul shine kika barshi a waje ko ruwa ba a kawo mishi ba, ke kam wace irin yarinya ce", cewa tayi "Aunty ban san zai tsaya ya mai dani ba", ganin Aunty da yayi ne yasa shi k'arasowa wajensu, a nutse yace "Aunty ina wuni", da murmushi ta amsa da "lafiya Abutturab, ya gida, mun saka aiki ko, ai bansan kana waje ba da an kawo maka ruwa", murmushi yayi yace "a ah Aunty ba komai, ai ba aiki bane, kuma inaga bata san bn tafi ba," ya k'arashe maganan yana kallon Batuul, k'in ďago kanta tayi sai da ya dena kallonta ta ďago, Aunty ce tace "toh maza kuje Batuul karki b'ata mishi lokaci, Allah ya kiyaye", tafiya sukayi suka isa inda motar ke pake bayan yyi ma Anty sallama, buďewa tayi ta saka akwatin nata daga baya bayan ya buďe da controller hannunshi sannan ta koma gidan gaba ta shiga shima ya shiga ya tada suka tafi, dan tsaki ya ja can kasa a xuciyarta yace " Was i even suppose to wait for her" haushin kansa ya ji ssae, ko da yake wasan da kanninta ke yi ya tsaya kallo, yyi assuring kansa, babu wanda ya cewa kowa komai sai wak'an dake playing.





K'arfe 7:20 suka isa gidansu Farida, sauk'a tayi bayan yayi pakin ta zagaya ta ďauko akwatin ta, tunawa da abinda yace mata daxu yasa ta hade rae tace "Na gode" ko kallonta bae yi ba ta ja akwatin ta ta yi gaba, yadda take jan akwatin ya gani kamar ta ďauki wani abun mai girma, ďauke kanshi yayi tare da jan tsaki har yazo ya wuceta ya shiga cikin gida, bayan shiganshi da minti biyu ta shigo janye da akwatin, mai aikinsu Farida, Fanne ce ta k'araso inda take ta karb'i akwatin tace mata "sannu", da mrmushi ďauke a fuskanta tace "yawwa Fanne na gode", sannan suka hau sama, ďakin Farida suka shiga suka sami Farida an mata kwalliya tayi kyau sosai, blue English gown ta saka da black accessories, tayi kyau ba kaďan ba kasancewarta fara, "Masha Allah kinyi kyau Riri" inji Batuul, murmushi tayi haďe da batting lashes ďinta tace "yeah i know", bata bi ta kanta ba ta wuce toilet tana dariyan ansa da Faridan ta bata, ruwa ta watsa sharp sharp, ta fito tana tsane ruwan jikinta da towel, mai ta shafa da sauri tazo ta zauna a gaban mai makeup ďin, kayanta ta fara taimaka mata ta saka, red fench floral gown, sannan ta fara mata make up, red matte lipstick ta shafa mata, sosai Batuul tayi kyau, sai da ta gama da fuska sannan ta saka mata accessories ďinta silver sai red agogo, gashinta ta gyara mata ya kwanto daga gefe, k'asan yayi curls, ba kaďan ba Batuul tayi kyau, k'arfe takwas da sha huďu suka fito daga ďakin sukayi ďakin Ammah, tana ganinsu tace "Masha Allah kunyi kyau", a kunyace Batuul ta amsa tace "mun gode", k'asa suka sauk'o suna jiran mai kaisu yazo, Abutturab ne ya sauk'o daga stairs har ya canja kayan dake jikinsa ya saka ralph lauren shirt da blue sweats, k'afanshi sanye da slippers ďin Fenty, hanyan waje yabi zai fita ba tare da ya kalli palon ba rike da makullin motarsa, mabuďi k'ofan ya buďe zai fita yaji Amma na cewa "Abuu, don Allah ga su Farida nan zaka ajiyesu a Tulip bistro, tunda kai ma fita xaka yi, 8 ma ya kamata su tafi amma yanxu har 8:30, kuma bana so suyi driving da kansu, dare yayi", bai juyo ba saida yaji ta gama, shi bai ma san mey zai cewa Ammah ba, amma ransa yyi mugun baci, wato dae ysu shi ya xama drivern wa ennan yaran, cewa kawai yayi "toh" snn ya sa kai ya fita kmr xae tashi sama, tashi sukayi suka bi bayanshi, har bakin k'ofa Ammah ta rakasu tace musu kar suyi dare kamar yadda Aunty ta faďawa Batuul, hasken dake filin gidan ne ya haska Batuul, sai ya k'arawa accessories ďin jikinta glitters, ďago kanshi yayi zai duba ko sun fito idanunshi suka sauk'a kan Batuul, tsayawa yayi yana kallonta da gashinta da yasha gyara sosai iska na swaying ďinshi, yadda take tafiya yake kallo a hankali kamar baza ta k'araso inda motar take ba, wani takaici ya turnuke shi ya danna horn da karfi, Farida ce ta fara zuwa, shiga motan tayi ta zauna a gidan baya, ganin babu yadda Batuul ta iyane yasa ta shiga gaba dan ďazu ma ce musu yayi shi ba driver ďinsu bane, k'anshin turaren Batuul ya nuna mishi cewa ta iso, ya dubesu su biyun ya daka masu tsawa yace "ina kuke tunanin zan kaiku haka da gashi a buďe kmr wasu mahaukata, ku fice min a mota kuje ku rufe kanku kuma kar wacce ta b'ata min lokaci, it seems kuna wasa da ni ne yau, duk gidan nn a rasa Wanda xae dinga yawo da ku a mota sae ni", Farida ce ta b'ata rai tace Yaa Abu toh Ammah ma bata ce komai bafa, kuma ma ai baza mu daďe ba", harara ya jefa mata ta mirror ba shiri ta bude mota ta fita da sauri, Batuul dai batace komai ba dan ranta ya gama b'aci saura kaďan tayi kuka , ta buďe k'ofa zata fita ita ma Farida tace "bari in dauko mana" hkn yasa ta koma ta xauna, kafin farida ta dawo Abuturrab ya ja tsaki fiye da sau goma, ita dae Batuul kanta na kasa sae wasa take da xoben hannunta, Farida na dawowa ta mi'kawa Batuul k'aramin jan gyale ita kuma bak'i, suna yafawa yaja motar suka tafi, hanyan Tulip suka bi, sai da ya tsayar da motan ya ce musu "duk iskancin da xa kuyi ku tabbatar by ten kun gama" Farida ta dan turo baki ta amsa mishi da "okay" suka fita daga motan suka shiga Cikin hall ďin event ďin, wajen ya haďu sosai kowane table kujerun mutum biyu ne da sunayensu a jikin kujerun, Runtown ne akan stage yake wak'anshi na Mad over you, anata ihu, Affan da Farida kujeransu ďaya , kujeran Batuul ne kawai ita kaďai, sai kuma na waďanda suka je wajen rawa, suna zaune ana ta yin abubuwa har aka iso lokacin bada award, Batuul ce ta cinye cutest da most classy, Farida most beautiful, Affan kuma Ladies Man, bayan an gama raba sauran awards ďin ne mutane suka hau wajen rawa.





Gidansu Massa Abutturab yaje, sai da ya fara shiga cikin gida , Maman Massa ya tarar zagaye da mutane a falonta da ma'aikatan gidan, gaishe shi suka farayi tun daga bakin k'ofa, k'arasa yayi ya tsuguna dab da k'afanta yace mata "Yaa Mera nda dubdo"(ina wuni Yaa Mera), kanshi ta shafa tace "Baanyi wushe" (lafiya Babana), ya shirye shiye", shi ya manta ma gaba ďaya da aurenshi nan da sati uku, sai da ya tuno shirye shiryen mey take nufi sannan yace "Alhamdulillah Yaa", "Masha Allah" tace sannan ya mik'e yace "bari in duba Massa Yaa", tace "toh Babana, sai ka fito", mik'ewa yayi ya tafi chamber Massa, tura k'ofar ďakin yayi ya shiga tare da sallama, su biyu ya gani a zaune suna playing game a tv, tsakin sallamar shi da basu amsa ba yayi, inda socket ďin ďakin yake ya wuce directly ya kashe, tsayawa sukayi suna kallonshi da mamakin yaushe ya shigo, Massa ne yace mishi "Man final tournament fa muke bugawa ka kashe", bai ce mishi komai ba sai da ya samu waje a kan gado ya zauna sannan yace "sai kace yara kun rik'e controller kuna ta game, nayi sallama babu wanda yayi responding a cikinku" ya sake jan k'aramin tsaki, a tare mazan Massa da ďayan suka dubi juna suka sa dariya, dubansu yayi yaga dariyan mey sukeyi sannan yace musu "abin yi ne baku da" ya ciro wayanshi daga

1 Comments On BATUUL
avatar
hafsat-9-3

12 months ago

Reply

Nice book

Please Login or Register in order to submit comment