Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba kullum nakeyi ba sai in kaine ka.....", tsareta yayi da ido yace "ehhn, sai in nine nayi mey?", sadda kanta tayi k'asa tace "You always talk abt your wife, kullum sai kace min your wife your wife, I know she is your wife, but ai ba sai ka dinga tunamin ba", baisan lokacin da dariya ya k'wace mishi ba, dariya ya dinga har sai da abin ya bata haushi, haushin kanta ma taji da ta fad'a mishi hakan, takaicin dariyan da yake yasa taja bargo tayi kwanciyarta, sai da yayi mai isarshi sannan ya d'agota har lokacin yana murmushi, kwace jikinta ta shiga yi zata kwanta amma yaqi saketa, fuskarta ya kamo da duka hannayenshi yana kallon idonta da duk ya cicciko yace "Toh ni yau duk yaushe na ambaci my wife", baki ta zumb'uro mishi tace "ko d'azu ma ba ka....", sai kuma tayi shiru, saketa yayi sannan yace "indai wannan ke saki kuka baza ki sake ji ba, you won't hear that from me okay?, ya hade rai ya ci gaba "but promise me kema baki sake yin kukan, kinga Farida will b coming so banso tazo taga kina wannan koke koken tayi tunanin wani abun ake maki", kamar wata y'ar yarinya ta gyad'a mishi Kai, ajiyar zuciya ya sauk'e ganin yayi convincing d'inta kan kukan nata, yanzu saura Farida, itama sai yayiwa tufkar hanci tun wuri, hannunta ya kamo yace "inason shan kunu, can you make some now?", kai ta gyad'a mishi yayi d'an murmurshi yace "Thank you", tsuke baki tayi zata tashi daga kan gadon yayi saurin janyota yace "Did you just pout?", da sauri ta kad'a mishi kai tace "baka ganiba, ni ba pouting nayi ba", murmushi yayi ya janyota jikinshi sosai ya d'anyi brushing lips d'inshi kan nata yayi mata light kiss, lips d'inta na d'aya daga cikin abinda bazai Iya resisting ba akan Batuul, suke tempting d'inshi yayi abubuwan da ma bai shirya yinsu ba, mik'ewa yayi itama ya mik'ar da ita, kallonta yayi yace "muje?", a hankali tace mishi "Ehh", Hijab d'inta ta d'auka zata saka ya riqe yace "Do you really need to put on this?", kai ta gyad'a mishi kawai taci gaba da saka Hijabinta, ita tayi gaba ya biyota a baya, turus ta tsaya bakin k'ofa ganin mutanen da suka hauro wa sama, kallon mamaki suka tsaya yi mata, wani irin bugawa Ajiddeh taji k'irjinta nayi ganin ya fito daga d'akin Batuul, tun bayan dawowanta bata tab'a tunanin har lokacin yana shiga d'akin ba, baki ta bud'e zatayi magana Jainaba tayi saurin rik'o mata hannu, murmushi ta k'irk'iro tace "Aliyu ashe ana ganinku a gari", shima d'in murmushi yayi yace "ai sai in ba a nemi ganinmu ba Aunty, Ya hanya?" Ya tambaya yana k'arasa fitowa daga d'akin, murmushin nan dai taci gaba dayi tace "Alhamdulillah, hanya mun baroshi, mun sameku lafiya?", kai ya gyad'a yace "Alhamdulillah, ya jikin Mummy, kwanaki bata ji dad'i ba, I wanted going with her", ya nuna Ajiddeh da zuciyarta ke tafasa "but abubuwa held me hear", dariya tasa tace "Ai ba komai ma, ai zuwan Ajiddeh ma yayi,taji sauk'i yanzu sai dai Allah ya kiyaye gaba", "Amin" yace sannan ya juya yana kallon Batuul da ta tsaya daga bayanshi kamar wata munafika yace "baki iya gaisuwa bane kika tsaya kallon mutane?", ido ta d'aga ta kalleshi sannan ta kalli Aunty Jainaba da ta bita da wani shu'umin kallo tana jira ta gaida ta, juyawa tayi ta shige d'aki ta banko musu k'ofa, gaba d'ayansu freezing sukayi ganin abinda Batuul d'in tayi, tsabar mamaki kasa magana Abu yayi, Ajiddeh ce a fusace tayi k'ofar d'akin zata bankad'a Jainaba ta rik'ota, "shegiya karamar matsiyaciya har kin isa ki wulak'anta min y'an uwa, toh koma uban wa ya d'aure miki gindi, ko kuma aka zugoki kizo ki min iskanci ko, toh dama hak'uri nakeyi nake k'yaleki, yau sai kin bar min gida y'ar abu kazan uba", Aunty Jainaba ce ta janyota da k'arfi ta d'an kanne mata ido sannan tace "Haba Ajiddeh, bakya ganin yarinya ce, kema ai kinsan hankali ba isanta yayi ba, yarinta ne ke damunta", wani irin kallo ta jefawa Aliyu da ya kasa cewa komai sai kallonsu yakeyi, a masifance tace "ai dama nasan kai ke d'aure mata tana min abinda taga dama, gashi ka janyo min raini da bai tsaya iya kaina ba, har kan y'an uwana ya koma, toh Allah zamanta ya k'are gidan nan ko kuma ni in bar muku gidan sai kuyi xaman auren da ita", Aunty Jainaba ce ta d'anyi magana a tsawace tace "keh wai wace irin yarinyace Jiddah, haka ake yiwa miji magana dama, wuce mu shige tunda bakida hankali wawiya kawae", taja ta sukayi gaba, wani irin iska mai d'umi ya furzar daga bakinshi yasa yatsunshi cikin gashin kanshi ya bajesu, juyawa yayi ya bud'e d'akin Batuul tana tsaye tana waya da alama da Farida suke wayan, a hankali ta juyo ta dubeshi, sai da y'an hanjin cikinta suka kad'a ganin irin kallon da yake tunkarota dashi, dakewa tayi da k'yar ta bud'e baki tace "Hey hold on, I will call you ltr", bata cire wayan a kunnenta ba taji ya fizge ya jefar kan gado tareda fizgota gabanshi, yana mata wani irin kallo yace "What's d meaning of what you just did, kinada hankali ma kuwa?", babu abinda k'irjinta keyi sai heaving kamar zai fito amma ta dake tace "ni kuma mey nayi?", fizgota ya sakeyi jikinshi yana mata wani irin kallo yace "you are asking, i will slap you yanzun nan in baki min magana ba, meye dalilinki na tafiya ba tareda kin gaidata ba, are you stupid?", k'wace kanta daga rik'on da yayi mata tayi zata matsa daga gabanshi ya kuma fizgota a tsawace yace "kehh! na fara wasa da ke koh, I will right away slap you, bakida hankali ne", hannunshi tacire daga rik'on da yayi mata tace "wai ni mey nayi ne na rashin hankali, dan ban gaishesu ba?, dole ne sai na gaishesu? Naga ai dama ba dole bane gaida kishiya, ita yaushe ta tab'a gaidani? Let me be plss", ta k'arashe maganan tana rolling eyes d'inta cike da masifa, kafeta da ido yayi cike da mamaki, baisan lokacin da gasp yayi escaping lips d'inshi ba jin abinda take ce masa, ci gaba tayi da cewa "kuma ni daga yau na dena gaisheta tunda itama bata gaishenin take ba", daga haka ta juya fuu zata tafi ya fizgota, kankamesa tayi jikinta na rawa tana kiran Anty, murmushi ne ya subce masa jin yadda k'irjinta ke heaving, kana ganinta kasan a tsorace take, yace "Huh kishiya?, waye kishiyar taki, ko kuma kinji nayi declaring d'inki matata ne da har kike fad'in baki gaida kishiyarki?", hawaye ya cika idonta tace "Ai ko bakayi declaring d'ina ba nidai bazan sake gaishesu ba, period", jefata kan gado yayi yace "Fine, duk ranan da ta koreki daga gidanta sai kisan inda kika nufa", da haka ya fita ya barta a d'akin, mikewa tayi a fusace ta sa key a kofarta, k'ofar d'akinshi ya tura ya shiga, nan ya tarar da Ajiddeh da Aunty nata zaune tana mata magana can kasa, d'an tsaki yaja ya koma da baya dan baisan ranar hankalin Ajiddeh ba, duk d'akunan dake gidan nan ta rasa wanda zata shigo da bak'i sai nashi, key d'in mota kawai ya d'auka ya fice daga gidan, bai dawo sai bayan Sallah Isha, direct d'akinshi ya wuce amma har lokacin suna ciki, sai ma dad'a littering d'in d'akin da sukayi da kayayyakinsu, ganin shi ne yasa Aunty Jainaba jin kunya tace "Laah Aliyu ashe har ka dawo, gashi mun b'ata maka d'aki", Ajiddeh kam ko kallonshi batayi ba, Murmushi yayi wa Aunty Jainaba yace "Nah its okay, ba komai, I will use another room", da haka ya fice ya jawo musu k'ofa, d'akin Batuul ya koma ya murda kofar yaji a rufe, komawa yayi ya dauko spare key sannan ya dawo ya bude ya tura kofan a hankali, as usual yana k'anshin da ya saba, kayanta ya tarar da ita tana gyarawa, kallo d'aya ta mishi ta d'auke kanta taci gaba da abinda takeyi fuskarta daure, k'arsawa yayi ciki ya kamo hannunta ya jata, tirjewa tayi a waje d'aya tana kallonshi tace "Lafiya, ko ka mance hanyar dakin matar taka ne?", ita kanta mamakin sabon halin nan nata takeyi, shi ma haka ya tsaya kallonta cike da mamaki, ta juya ta ci gaba da abinda take yi, ganin zata b'ata mishi lokaci yasa ya d'agata cak "baki ta bud'e zata sa mishi ihu ya sa yatsa ya bige mata d'an baki yace "shout and I will drop you down d stairs, dare me ki ga", gaba d'aya kanta ne taji yana juyawa kamar d'azu ga tashin zuciya, wani k'arfi ne yazo mata ta sauk'a daga hannunshi tace "zan tafi da kaina, ba sai ka d'auke ni ba", ta fad'a tana murgud'a mishi baki, shi mamakin sabon halin nan nata kawai yakeyi har ta fito daga cikin d'akin shima ya biyota rik'eda hijab d'inta, ganin Hijab a hannunshi yasa ta ce mishi "wai ina zamu?", baice mata koma ya rik'ota ya sa mata Hijab d'in ya jata sukayi waje, mota ya bude ya saka ta ciki sannan ya xaga shi ma ya shiga ya tada motar suka bar compound din, eatry ya nufa da ita ya siyo masu abinci suka dawo gida, yana gama parking ta fice daga motar ya bi ta da kallo yana murmushi, fitowa yayi shi ma ya kwashi ledojin abincin ya rufe motar ya bi bayanta, dakinta ta shige ta fada kan gado jin yanda xuciyarta ke tashi, ya hauro sama shi ma, yayi knocking dakinsa da su Ajiddeh suke, Ajiddeh ta leko fuskarta daure ya mika mata leda daya, wani matsiyacin kallo tayi masa tace "Ae nayi xaton da yunwa xaka bar 'yar uwar tawa" daga haka ta maida kofa ta rufe ta bar sa nan tsaye, girgixa kai yayi cike da takaici ya juya ya nufi dakin Batuul, ajiye ledan hannunsa yayi ya karasa kusa da gado ganinta kwance ya xauna daga gefenta yana kallonta yace "Tashi ki ci abinci" ba tare da ta kallesa ba tace "Am OK ka kai ma matar ka" dariya ta basa ba kadan ba yace "Uhnn! Ae sai da na fara kai mata kafin in kawo maki" tace "Nawan ma ka hada mata ta cinye" dariya yayi ya dago ta yace "Ashe kema haka kika iya masifa, wannan ba halin Anty bane" kwace kanta tayi tace "Ni ka kyaleni" yace "Sakko ki ci abinci toh" tace "Ban ci" sakko da ita yayi kasa ya jawo ledan yace "Look am not joking fah" bude kofa aka yi daga waje, yyi saurin mikewa yana kallonta yace "Kafin in dawo ki tabbata kin cinye" daga haka ya juya ya nufi kofa ya fita, mikewa tayi da kyar ta koma ta kwanta don duk ta rasa me ke mata dadi ga tashin xuciyar da yasa ta gaba, tana kwanciya bacci ya dauketa. Shi kam Abuturrab duk ya kagu Ajiddeh ta koma gun 'yar uwarta ya je yaga ko Batuul ta ci abincin don xuwa tayi ta sa shi gaba a palo, har sha biyu bai ga alaman xata tafi ba yace "Kin bar Anty ita kadae" tace "Ehh ita tace in tafi gun mijina bacci xata yi" bai kuma ce mata komai ba, har dai ya mike daga karshe yace "Am going to bed yanxu" ta mike tana mitsika ido, ya kashe kayan kallon parlour'n da wuta ya nufi sama ya bar ta, ta bi bayansa, kwanciyarsa yayi a bedroom ya juya mata baya ta shige jikinsa, ko ta kanta bae bi ba ya lumshe ido kamar me bacci, yana jin alaman tayi bacci ya xame jikinsa daga nata ya mike daga gadon ya fita daga dakin, dakin Batuul ya shiga, ya karasa yana kallonta, kwata kwata bai ji dadin rashin cin abincin da bata yi ba, ya xauna gefenta ya cire duvet din da ta lulluba da a hankali, ya ji jikinta da d'an xafi, ya jima yana kallonta sannan ya lumshe ido yayi pecking lips dinta ya mayar mata duvet din jikinta ya mike ya dauke ledan abinci yasa a fridge ya fita daga dakin ya koma nasa.
πŸ’–πŸ’BATUULπŸ’–πŸ’

69

By phartiemarhk

Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*

Washe gari da safe kamar yadda ta saba tashi haka ta tashi, sai da tayi Sallah tukunna tayi wanka ta gyara d'aki, ta koma toilet ta wanke sannan ta fito tayi kwanciyarta kan gado saboda jirin da take ji, jin jikinta ya d'anyi dama dama yasa ta mike ta fita daga dakin ta sauk'o k'asa yin breakfast kamar yadda ta saba, a gurguje ta shiga gyaran parlour dan bata son yin latti, lecture 11 ne da ita, gashi jiya ma bata samu taje ba, kitchen ta shiga ta harhad'a kayan abincin da zata dafa grilled fish da salad ta shiga had'awa, tana jin saukowan sa parlor da Ajiddeh ta tabe baki ta ci gaba da aikinta, kunun gyad'a ta dama sannan ta shiga baking musu chicken pie, Oven d'in da kifin ke ciki ta bud'e zata duba ko yayi, tiririn dake fitowa ciki yasa taji kanta ya fara juyawa ga tashin da zuciyarta ya fara, ba shiri ta yadda hand napkin dake hannunta jin amai na yunk'urin zuwa mata ta fito daga kitchen din da sauri, yana kwance a parlour ya lumshe ido, Ajiddeh na kwance jikinshi duk ta wani kanainayeshi, abubuwane kawai suke mishi yawo akai, duk he was just confuse, Ajiddeh kuma ba hankali ta cika ba da komai zaizo mishi da sauk'i, dan ko jiya shirmen da ta dinga mishi darajar Auntyn ta dake gidan taci da yayi maganinta, gaba d'aya bayajin zai iya yin nesa da Batuul, she has become part of him, duk da shi dai yasan ba wai sonta yake ba amma har cikin ransa yake jin ta, dole ne ma yasan yadda zai sanar da Ajiddeh dan bazai iya cigaba da b'oyewa ba, inma ya b'oyen to dole attitude da movements d'inshi su nuna, lumsassun idanunshi ya bud'e jin motsi kamar an fito a guje, inda yaji motsin nan yabi da ido, Batuul ya gani bakin staircase ta durkushe wajen tana kwarara amai, baisan lokacin da ya ture Ajiddeh dake jikinshi ba ya mik'e a rud'e ya iso inda take, rik'ota yayi ya jawota jikinshi yana rik'e da ita har saida yaga ta gama aman, Ajiddeh ce ta k'araso wajen ta rik'e k'ugu sai karkad'a jiki take taja wani dogon tsaki tace "iskancin banza, ke iskancin naki har ya kai da yi min k'azanta a parlour, jibi yadda kika b'ata min gida da amai, toh wlhy sai kin gyarashi tsaf, nan yayi maki kama da toilet", ko ta kanta Abu baibi ba ya d'aga Batuul da ta gama galabaita cak yayi sama da ita, bai ajiyeta ba sai da ya shiga toilet d'in d'akinta sannan ya taimaka mata ta wanke bakinta, tana rik'e jikinshi har lokacin, suna fitowa ya kalleta with care yace "mey ki kaci ya saki amai?", ko kulashi batayi ba saima k'ok'arin k'wace jikinta da ta shiga yi daga hannunshi, suna zuwa bakin gado ya saketa, kamar jira takeyi yana saketa ta sulale tayi kwanciyarta kan gadon ta lumshe ido tana maida numfashi, ganin ta lumshe ido yasa kawai ya k'yaleta ya gyara mata kwanciyarta yayi waje, k'asa ya sauk'o ya tarar Ajiddeh bata nan, kitchen ya shiga ganin stoves a kunne duk ya kashesu sannan ya d'auko Vacuum cleaner ya shiga gyara gun da tayi aman, d'akin ya koma yaga alamun tayi bacci, ya sauke ajiyar xuciya yaja k'ofan ya rufe, toilet d'in d'akin da ya kwana ya shiga yayi wanka ya canja wasu kayan, key d'in motarshi ya d'auka ya fita daga gidan yaje eatery siyo musu breakfast, har lokacin baiga Ajiddeh ba, d'akinshi da yasan zai samesu yayi knocking, ita ta taso ta bud'e mishi k'ofa, tana ganin shine cike da masifa tace "inji dai ta fito ta gyara min parlourn dan ni I can't withstand wannan K'azantar," wani mugun kallo ya sakar mata sannan ya dungure mata ledan ya juya ya barta nan tsaye baki a sake, kwafa tayi ta d'auki ledan ta juya ciki, d'akin Batuul ya koma da sauran ledojin dake hannunshi yaga tana bacci har lkcn, bakin gadon ya zauna ya zuba mata lumsassun idanunshi, tausayinta ne gaba d'aya yaji yana ratsashi, har ta d'an fad'a, to wai ma me ke damunta haka, deciding yayi idan ta tashi still not ok su tafi hospital kawai, hannu yasa ya gyara mata gashin da ya zubo mata fuska sannan ya d'an shafi fuskan nata ya miqe ya fita waje, yunwa yakeji amma baijin cin abincin waje at all, kitchen ya shiga yaga kunun data fara, k'arasawa yayi ya ciro kifi da meat pie d'in da tayi baking, ya nufi dining ya zauna yaci, sai lumshe ido yakeyi yana cin abincin, a ranshi kuwa cewa yakeyi "She is angel, always different", addu'a samun sauk'i ya dinga yi mata har ya gama cin abincin shi, parlour ya koma ya kwanta dan bai tunanin yau zai iya fita ya bar Batuul, duk bayan 30mins sai ya shiga ya dubata, Sallah azahar ma yau a gida yayi baije masallaci ba, baiso ta tashi baya nan, mamaki ne ya kamshi ganin har la'asar tayi amma bata farka ba, kuma baccin nata normal, yasan bata irin wannan baccin haka, ita kuwa da ta tashi wani baccin ke dauketa, bayan yayi sallahn magrib a gurguje ya fita ya siyo musu abinci, sai da ya fara kaiwa Ajiddeh nata sannan ya shiga d'akin Batuul har lokacin tana bacci, deciding kawai yayi ya tasheta sabida baccin yayi yawa, a hankali ya shiga tashinta bayan ya hau kan gadon, da k'yar take iya bud'e ido tana maidasu ta lumshe, d'agota yayi ya jinginar da ita jikinshi yace "Hey wake up, wannan wani irin bacci ne, tashi kici abinci, its already late, bacci tun safe", a hankali ta bud'e lumsassun idanunta ta k'arewa d'akin kallo, a kanshi ta tsaida kallonta tace "Farida bata iso ba?", tana sake lafewa a jikinshi, d'agota yayi yace "tashi kici abinci", had'e rai tayi ta zumb'uro mishi baki tace "Ina Farida nace?", tana magana tana dad'a sulalewa jikinshi, ganin baza ta tashi ba yace "Farida anyi delaying flight d'insu sabida bad weather baza su iso yau ba sai gobe da safe", daga haka ya d'agata ta zauna, hannu yasa ya janyo pack d'in abincin yace "C'mon zo kici abinci", ya bud'e pack d'in, da sauri ta matsa baya tace "mey wannan d'in?, ni banaso", da mamaki yake kallonta yace "ba kya so kuma, duk yau baki ci komae ba fa, c'mon have it, ya d'ebo daga cikin spoon d'in ya kawo mata baki, da sauri ta toshe bakinta da d'ayan hannunta d'ayan kuma ta ture hannunshi da ya mik'o mata gabanta tace "Nace banaso, banason k'anshin abinci bazan ci ba, ka fita dashi", kallon mamaki kawai yake mata, rai b'ace cike da masifa tace "ka matsar mana, nace fa bazanci ba", abincin ya matsar gefe kamar yanda tace ya rik'ota da damuwa yace "toh mey zakici", kamar jira takeyi da sauri tace "Ni ice cream zansha", baki ya bude yace "kina ma da hankali kuwa, ina tambayanki mey zakici kina ce min ice cream, I will slap you right away in baki bar wannan shirmen naki kin fad'amin abinda zakici ba, duk yau mey kikaci da zakice min wani ice cream zakisha, you were sleeping all day kamar wata jaririya", tutturashi ta shiga yi daga jikinta tana murgud'a baki tace "Ni dama bance dole sai ka samomin ba ai, kuma ma ni da kaina zan iya zuwa inyi, bana ma so na fasa, ko ka kawoma bazan sha ba, ka tafi min daga d'akina ni", ta d'an ja tsaki tayi kwanciyarta ta juya masa baya, ya kai minti biyu zaune yana kallonta da mamaki, can dai ya mik'e daga karshe ya nufi kofar d'akin, jin motsin kofa ta juyo da sauri tace "ice cream d'in zakaje kawo min?", wani irin kallo ya watsa mata, bata damu da kallon da yakeyi mata ba tace "Ni kar kaje Cold stone fa, ko na lick ko scoop, ba na can nakeso ba, na gelatorino nakeso, sai flavour Kuma pistachio, strawberry, Madagascan vanilla, kuma banason na corn, su min scooping a cup, yawwa with a couple of some more exotic options kamar su coconut lemon grass, pepper mi.....", bai jira ta gama surutun nata ba ya kad'a kai ya fice ya rufo k'ofan, baya ya jefa key d'in aljihunsa, gaba d'aya ya kasa gane what came over this girl, mota ya shiga sannan ya kunna map navigator yayi searching wajen da ta fad'a mishin, dan shi baisan ma inda gun yake ba, tafiyan 15mins ya isa wajen, duk abubuwan da ta lissafo mishi sai da ya siya harda k'ari, da snacks, bai jima ya dawo gidan, har lokacin bai ga Ajiddeh ba, d'akin Batuul ya wuce kai tsaye da ledojin hannunshi, tana jin motsinshi ta mik'e da sauri, daga bakin gado ya zauna ya mik'o mata ledan hannunshi, da sauri ta anshe, na snacks d'in ta fara ansa, rai b'ace ganin abinda ke ciki tace "nifa ba abinda nace inaso ba kenan", ta tura mishi gabanshi, jin d'ayan ledan da sanyi yasa tayi hanzarin jawoshi ta shiga bubbud'ewa, ba tareda b'ata lokaci ba ta shiga shan ice cream d'in, kallonta kawai yakeyi ganin yanda takesha d'agowa tayi suka had'a ido, murmushi ta mishi tace "Thank you, you can have some", tayi mishi nuni da ledan dake ajiye, kai kawai ya iya girgiza mata, tab'e baki tayi taci gaba da shan abinta, ko rabin na cup d'in batasha ba ta ajiye tace "Alhamdulillah, am full", ta ajiye zata juya ta kwanta yayi maza ya rik'ota yace "meye hakan?, wai kina nufin har kin gama sha? kai ta gyad'a mishi tareda d'age mishi girarta d'aya tace "Ehh", yace "abincin kuma fa?", d'an had'e rai tayi jin ya ambaci abinci tace "Nifa bana jin yunwa, am okay", ya d'an yu shiru sannan yace "toh brush d'in kuma fa da kike k'ok'arin kwanciya, and baki yi sallah ba, tace "nifa bacci nakeji, xan yi anjima wllh", "Bacci?", ya tambayeta dan yau wuni yaga tayi tana bacci kuma its just 8:08 yanxu, bata bashi amsa ba ta kwanta abinta, tana kwanciya kuwa bacci ya d'auketa, ya dad'e zaune yana kallonta daga baya ya tashi ya ciro mata kayan baccinta cikin closet ya cire mata na jikinta ya saka mata wanda ya ciro?, mamakin irin baccin nata kawai ya dinga yi dan har ya canja mata kayan bata tashi ba ita da bata da nauyin bacci, addu'ar bacci ya tofa daga baya ya kashe mata wutan ya tafi d'akin da ya kwana jiya, wanka yayi sannan ya d'auro alwala yayi sllhn Isha ya koma gado, kamar jiya yau ma a waya ya dudduba ayyukan office da baiyi ba snn ya kwanta, sai wajen sha biyu snn Ajiddeh ta shigo d'akin, yana jinta sai wani shige mishi jiki takeyi, ganin yayi bacci ta k'yaleshi itama ta kwanta.

Washe gari da asuba bayan yayi Sallah direct airport ya wuce d'aukan Farida, arrivals ya wuce kai tsaye bayan ya gama parking, dai dai lokacin da Farida ta fito daga terminal janye da akwatinta, ita ta fara hangoshi, da gudu ta k'araso ta rungumeshi, shima d'in rungumeta yayi, cike da farin cikin ganinsa tace "Yaa Abu ina kwana, thought tare xa ku xo da Anty Batuul" da xolaya ta kare maganan da wide smile d'inta mai kyau shimfid'e fuskarta, murmushin shima yayi yace "Lafiya Alhamdulillah, Ya hanya?", zumb'uro mishi baki tayi jin yace ya hanya tace "hmmmm ai ni shiyasa bana son bin wani flight inba B.A ba ko Emirates, kasan transit kawai muka tsaya amma suka fake da wani wai bad weather, baza mu taso ba sai bayan nan da 14hrs , ni ai da so nayi in koma Nigeria, amma sabida ina son ganin my other half",

1 Comments On BATUUL
avatar
hafsat-9-3

12 months ago

Reply

Nice book

Please Login or Register in order to submit comment