Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ajiddeh tunda tana sonka you can make her all you like, zatayi duk abinda kake so, Ko Shehu bazaiyi siding damu ba saboda shima damuwanshi kenan a kanmu, sai dai ma ya ce a k'ara dani, Man kawai muyi addu'an abinda yafi alheri", cigaba sukayi da hirar neman mafita daga k'arshe kawai suka yanke shawaran ya auri Ajiddeh tunda ita kaďai ce option ďin dan basu san wacce su Abui ďin zasu zab'a mishin ba, k'arfe goman dare ya mik'e yace da Massa zai koma dan yana da flight gobe by 11:00, sun fito waje Massa na rakashi inda yayi parking mota Massa ke tambayanshi, "Man ya akayi ne baka zo ba jiya inata jiranka", tambayan ne ya sashi tunawa da duk abinda ya faru tsakaninshi da Batuul, ďan k'aramin tsaki yayi daga ciki yacewa Massa "gajiya nayi", dariya Massa yayi yana ďan tab'a kafadarshi yace "ango tun bakayi auren ba har ka fara gajiya, toh in kayi auren kuma bazamu na ganinka ba kenan", Abutturab bai ce mishi komai ba ya buďe motarshi ya shige tare da ce mishi "sai munyi waya, ni zan wuce", Allah ya tsare hanya Massa yaayiwa Abutturab sannan sukayi sallama







Bayan sallah asuba babu wanda ya koma bacci, kowa shirin tafiya ya farayi, sai hayaniya akeyi a gidan, kowa ya tashi a gidan banda k'ananan k'arshe, Janet ce tayi knocking k'ofan, bayan an mata izinin shigowa ta shigo ďakin, tarar da Aunty da Batuul a ďakin tayi,Batuul na shiryawa Aunty kayanta da zata tafi dasu a cikin jaka, Aunty ce tace mata yarannan fa har yanxu basu tashi ba Janet, maza je ki k'irawo Fa'iza kuzo kuyi musu wanka dan 8 ya wuce, da toh ta amsawa Aunty sannan ta fita k'irawo Fa'iza dan suyi aikin da aka sasu, ďaya nayin wankan ďaya kuma na shafa musu mai da sa musu kaya, Batuul na gamawa tacewa Aunty "zanje in shirya sannan ta fita daga ďakin Aunty ta isa d'akinta, wanka tayi sannan ta fito ta shirya cikin atampa exclusive green da pattern ďin yellow da bak'i, ďinkin yayi mata kyau sosai, skirt ne with peplum blouse mai three quarter hannu, ba a sa komai a jikin rigar ba sai patterns ďin atamfar aka yi mata aiki dashi, ďan kunne kawai ta saka bata sa sark'a ba, agogon gucci ta ďauka ta mak'ala a hannunta, babu wani kwalliya da tayi sai kwalli kawai da ta saka a idonta, duk da ba tsayine da ita ba, bata saka takalmi mai tudu sai slippers din versace baqi da ta saka, luggage ďin kayanta ta jawo ta ajiye bakin k'ofa sannan ta ďauko k'aramin bak'in gyale ta ajiye a kafaďarta, fitowa tayi ta sauko k'asa taga kowa ya shirya cikin kayan alfarma suna breakfast, shiyasa ma bata fara saka abaya ba dan tasan Baba sai yayi mata maganan abayar, k'arasawa tayi itama ta janyo kujera ta zauna , Aunty da Baba ta gaida a tare suka amsa mata sannan duka k'annenta suka gaisheta suma, Bismillah tayi ta fara cin abincin itama, a nutse suka gama breakfast ,tara da rabi dai dai aka fara fita da kayansu, manyan mazan kowa da hand luggage ďinshi a hannu, na Aunty, Batuul dasu Hafix kuma yana hannun su Janet, Baba ne shima ya sauk'o daga bene rik'e da nashi, Batuul na hango shi da sauri taje ta karb'a ta k'arasa dashi k'asa ta bawa driver su fita dashi, Kanta ya shafa Yace ya gode , Baba na k'arasowa duk suka tashi suka fita suka nufi inda motocin gidan ke pake, Baa Liman ne da Sunday driver zasu kaisu airport, Batuul da Ahmad, Sa'eed, Khalil, Mus'ab mota ďaya suka shiga while Baba, Aunty, Yusra, Mahir, Hafix da Aabid na mota ďaya, sai da sukayi addu'an fita daga gida da ayatul kursiyu kamin drivers ďin su fita daga gidan





Hanyan Maiduguri international airport suka bi, goma da rabi suka isa, ana shiga cikin airport ďin heartbeat ďin Batuul ya k'aru idonta ya fara tara hawaye, addu'a ta soma har taji ya ďan ragu, bayan sun shiga har ciki sun sauk'a ta isa wajen Aunty ta ce mata, "Aunty tunda muka zo Maiduguri heartbeat ďina baya running at a normal pace, yanxu ma muna shigowa airport naji ya k'aru sosai", Aunty ce ta dube ta tuna da ranan da ta dawo idanunta sunyi ja, ce mata tayi "baki da gaskiya shi yasa yak'e karuwa, dariya sosai Batuul tayi sannan tace "kai Aunty, wane rashin gaskiya zanyi har heartbeat ďina ya rik'a karuwa, ni dai babu abinda nayi", ta juya ta tafi, binta Aunty tayi da ido dan itama ta tab'a shiga yanayi irin na Batuul na k'aruwan bugun zuciya, murmushi tayi ta girgiza kai sannan ta tattara kan yaran sukayi departures waiting room suna jira a k'ira su in jirgi ya shirya
💖💝BATUUL💖💝






11





By phartiemarhk





Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*





Suna zaune suna jiran jin announcement ďin departure su, Mahir yacewa Aunty zai sha smoothie, sauran yaran naji yace zai sha suma duka sukace zasu sha, Aunty ganin dukkansu na son sha kuma ba wai suna son bane dagaske kawai dan sunji ďaya daga cikinsu yace zai sha ne dan kawai suje yawo yasa faďin cewa za su sha Aunty cewa Batuul, "Batuul jeki da Fa'iza ku kawo musu , bazan iya da yawon yaran nan a cikin airport ďinnan ba , yanxu sai in nemi wani in rasa, Murmushi Batuul tayi sannan ta mik'e ita da Fa'iza suka karb'i kuďin a hannun Aunty suka tafi, suna tafiya yaran na ihun faďan shi ice cream yake so wani kuma yace milk shake yakeso, bata kula kowanne daga cikinsu ba tayi tafiyar ta, mutanen dake zazzaune sai kallonsu sukeyi ,suna tafiya suna ďan hira da Fa'iza har suk'a k'arasa eatery ďin dake airport ďin, order ďin smoothie ta bayar ta zauna jiran a gama packaging su tafi, ana gamawa aka mik'o musu Fa'iza ta karb'a, suna juyowa zasu tafi taji bugun zuciyanta ya sake k'aruwa, saurin tafiyanta ta rage tana Hasbunallahu wa ni'imal Wakeel, juyowa Fa'iza tayi ta dubi Batuul tace "Yaa Batuul lafiya ,naga kina tafiya a hankali, Ce mata tayi "Lafiya Fa'iza, muyi sauri mu k'arasa" Suna cikin tafiya daga gefe ta hango Abui da wani mutum a tsaye, bata ga fuskanshi ba dan ya juya bayanshi, Abui ke facing ďinsu sai bayan mutumin kawai take gani, Hasbunallahu wa ni'imal wakeel ta sake sabida yadda bugun zuciyanta ya k'aru, da sauri ta k'arasa inda ake zaman jiran , a ranta tana cewa in sun koma gida zata faďawa Aunty dagaske bugun zuciyan nata ya k'aru, suna zuwa suk'a mimmik'awa kowa abinda yace yana so suka koma wajensu suka zauna, basu fi minti biyar da zama ba akayi announcing passengers ďin Maiduguri to Abuja su fara boarding yanxu jirgi zai tashi, mik'ewa sukayi suka isa inda jirgin Med View ke tsaye suka hau matakalar suka shiga ciki, a first class suka sami waje suka zazzauna, Batuul ce k'arshen shigowa, duk seats ďin sun cika sai last two seats ďin k'arshe ne da daga shi sai economy class babu kowa a wajen ta k'arasa ta zauna, tana zama ta cire wayarta daga cikin jaka da ear piece sannan ta saka jakar daga sama inda ake ajiye luggages, wayarta tasa a flight mode ta jona ear piece ďin da wayan ta mak'ala a kunnenta, a hankali ta jinginar da kanta a kujerar tare da lumshe idanuwanta, heart beat ďinta ne ya k'ara k'aruwa kamar zai fito daga ciki, seat belt din jikinta tayi unfasten snn ta shiga karanto addu'a a hnkli a xuciyarta tana dan jujjuya kanta, ji tayi kmr mutum na tsaye kanta don wani dad'da'dan kamshi ne ya bugi hancinta, duk da hka ba ta buďe idonta ba sai da ta gama addu'ar da take snn ta bude idonta a hnkli, wani mugun faduwa gabanta yyi ganin Wanda ke tsaye kanta idonsa a kanta ko kiftawa baya yi, dauke kai yyi da sauri fuskar nn tasa a daure yace "Excuse me" sae a snn ta lura da handbag dinta da ke ajiye kan seat din dake gefenta, daukewa tayi ta mayar cinyarta snn ya xauna, mamaki ne ya cika ta ba kadan ba, mikewa tayi ta ajiye handbag dinta xata fita duk da bbu takamaiman abinda xata je yi amma ya ki bata hanya, ita kuma taki cewa ya matsa mata, komawa tayi ta xauna ranta yyi mugun baci, to wae shi wnn guy din me yake daukan kansa, me ma yasa zai zo kusa dani ya zauna at d first place, ko ina ne sae mun hadu, su Farida ma basu dawo ba shine shi zai tafi ya barsu, ko mey zaije yi shi kaďai oho" ďan k'aramin tsaki taja ta kawar da kanta tana kallon waje ta window, tsakin da taja ne ya sashi kallonta, lokaci ďaya yyi kwafa ya dauke kansa da yaga hankalinta baya wajen, announcement aka shiga yi nacewa " passengers on board should pls fasten their seat belts, Med view flight is about to take off" fasten din seat belt dinsa yyi ganin bata da niyar yin hkn ita yasa ya juya yana kallonta, a lumshe ya ga idonta snn ga earpiece a kunnenta, da farko dan tsaki ya ja ya kawar da kansa, amma ganin few minute ya rage flight yyi take off yasa ya dan buga hannun seat dinta, ko kadan batuul bata ma san yana yi ba don kure Karatun da take saurara tayi, ya kuma buga handle din seat dinta da karfi nn ma bae ga alamar tasan yana yi ba, jin announcement din da ake yasa yyi saurin jawo seat belt din ya shiga kkrin fasten din mata, Batuul kam kawae jin hannun mutum tayi jikinta, ta bude ido da sauri tare da cire earpiece din kunnenta tace "What...." Shiru tayi ganin har ya gama sa mata ya dauke kai, lkci daya ya lumshe ido kamar mai bacci, takaici ne ya isheta bata san lkcn da ta furta "Hw dare yhu!" Bude ido yyi da sauri ya xuba mata manyan idonsa yana kallonta, murya can kasa yace "fuck does words of urs!" hawaye ne ya cika idonta, lkci daya ta rufe fuskarta da mayafin jikinta, dauke kai yyi ba tare da ko dar ba, bayan yan mintuna Batuul ta bude fuskarta suka hada ido, hawaye ya gani fuskarta, lkci daya jikinsa ya dan yi sanyi don ya tsani kukan mace, a hnkli ya furta "Damn her, ita kenan kullum hawaye, ko meh nayi mata oho," kusan a zuciyanshi ya faďi haka, handkerchief ďinshi dake aljihun jeans ďinshi ya ďauko ya mik'a mata ba tare da ya kalleta ba fuska daure, k'in karb'a tayi, haushi ne ya kamashi ya maida handkerchief ďinshi ya ruk'o kafaďanta da k'arfi, "clean that face, bana son sake ganin hawayen nan, don bbu abinda nayi maki I only helped yhu, ko kuma you leave this seat immediately" saketa yayi dan k'aruwa hawayen sukayi, ya ja dogon tsaki ya ďauke idonshi daga wajenta, sake juyowa yayi bayan y'an mintuna yaga har lkcn hawayen take, da kanshi ya ďauki handkerchief ďin ya fixgota ya shiga goge mata hawayen , ture hannunshi tayi daga fuskanta tace mishi "malam ka rabu dani da hawaye na, ai fuskana ne kuma hawayena ne, let me be plss" ta juyar da kanta tana kallon gajimare da sauri , magana zaiyi mata kenan hostess ďin jirgin ta tsaya a daidai kujeran da suke, plate holder ďin seats ďin nasu ta jawo ta ďora musu ruwa akai a ďan k'aramin disposable cup, hak'oranta ta washe ta gyara murya tana yiwa Abutturab magana, "Sir what would you like to have", bai ďago kanshi ba yace mata "Get me coffee", okay tace sannan ta dubi Batuul tace mata "Ma'am what would you like to have", k'in juyowa Batuul tayi, sake tambayanta matar tayi sannan ta juyo tace mata, "am okay, i need nothing" murmushi matar tayi sannan ta wuce" wayanta ta ďauko dake mak'ale a pocket ďin seat ďin gabansu ta sake mak'ala ear piece ďin a kunnenta taci gaba da jin karatun qur'anin da takeji ďazu, hostess ďince ta dawo da coffee ta ajiye mishi ta juya.





k'arfe 12:10 daidai jirginsu yayi landing a filin jirgin Nnamdi azikiwe international airport dake Abuja, jirgi na tsayawa Batuul ta tashi zata fita daga seat ďin da sauri fuskar nn tata a daure, k'in matsawa yayi ta fita har saida mutanen dake can economy class suka gama fita na first class ďin ma sun k'are, ita dae bata ce mishi komai ba har ya gama zaman mulkinshi ya mik'e cikin isa, ko gama barin wajen be yi ba ta bangajesa ta fice ta ďauko jakanta, sae da ya gama bari ta dauki jakarta snn ya fixgo ta yace "Are yhu blind" buge hannunsa tayi ta fita da gudu, tana fita taga y'an gidansu a waje ďaya, Aunty ce tace mata "mey kika tsaya yi ke baki fito ba sai yanxu", cewa Aunty tayi "bana so inzo fita ina jiran mutane shiyasa na jira kowa ya gama fita", Abutturab ne ya k'araso inda yake fuskarshi a sake kamar ba shi ke ďaure fuska ba ďaxu a cikin jirgi, Hannu ya mik'awa Baba tare da ce mishi "Baba ya gajiyan jirgi", murmushi Baba yayi yace mishi "Alhamdulillah Aliyu, mun godewa Allah mun iso lafiya" juyawa yayi ya dubi Aunty ya ďan sunkuyar da kanshi tare da gaisheta, itama amsa mishi tayi cikin sakin fuska, hannu ya mik'awa duka k'annen Batuul suka gaggaisa, Aabid ne kawai bai gaisa dashi ba sai kanshi da ya shafa tare da murmushin da ya bayyana dimple ďinshi yace mishi da "Hello champ" dariya sosai Aabid ya saka kamar yasan abinda aka faďa mishi, tsayawa Batuul tayi tana kallonshi da mmki a ranta take cewa "Yaushe yasan su Baba kuma" shi kam ko kallon inda take bae yi ba, tab'e baki tayi ta juyar da kanta, suna tsaye motoci suka k'araso inda suke, Baba ne yacewa Abutturab "toh Aliyu sai kaje ka huta ko gobe za a fara aiki" da murmushi ya amsawa Baba da "In sha Allah", sai da ya jira sun shiga motocinsu sannan ya shiga nashi shima da aka zo ďaukanshi dashi, hanyan Gwarimpa su Batuul sukayi, motar su Abutturab kuma tabi hanyar Asokoro.
💖💝BATUUL💖💝






12





By phartiemarhk





Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR* , Thank you sister, you are one in earth, you are truly an inspiration, Thank you soo much for being there for me, we love you❤





A hanya Baba ke tambayan Batuul abubuwan da take buk'ata na graduation ďinta, ce mishi tayi "Baa dama kayan graduation ne ,prom da zamuyi a ranan da yamma sai walima shi kuma inada kayanshi", kallonta Baba yakeyi har ta gama sannan yace mata "Sai kuje ko Dubai ne ku duba tunda babu time kuma shi kaďai kuke da visanshi, sai ki siyosu a can", murmushi tayi tace "Baa ai nayi magana ma da designer ďita har na gama faďa mata yadda nakeson kayana, next wek ma tace zata gama", tambayanta Baba ya sakeyi "are you sure babu matsala Mamana zaki samu yadda kikeso", kai ta gyaďa tace ehh Baa In sha Allah", murmushi yayi ya shafa kanta yace, "Allah ya miki albarka" daďin addu'an ne ya sata saurin jnfrr da "Amin", hira suketayi suna tafia, k'arfe biyu daidai suka isa gaban wani gate saboda nisan tafiyar dake tsakanin airport ďin da cikin gari ga hold ups hornsukayi, gidan exactly irin gidan da suka baro ne a Maiduguri, sai dai wannan cream paint ne da brown gate wancan kuma farin paint ne da black gate, masu gadi ne guda biyo suka taso suka buďe musu, a lokaci ďaya suka ce musu sannu da zuwa tare da yi musu ya hanya, cikin sakin fuska suka amsa musu da Alhamdulillah Friday da Jonathan driver ya k'arasa ciki dasu wajen parking, firfitowa sukayi daga motocin suka nufi cikin gida, shima cikin iri ďaya ne da wancan abinda kawai ya banbantashi da wancan shi cream and brown live wallpapers ne manne a bangon, sai wani large human size family picture daga gefe manne da bango, k'arasawa kowa yayi cikin gidan ya samu waje ya zauna a falon, Baba ne kaďai ya haura sama,khalil ne yace "Home sweet Home" Ahmad ne yace mishi "ai nan ba home bane, dole zamu koma maiduguri saboda Abuja ba garinmu bane", "but still this is where we live" inji kalil, tsakaninsu suke ta hiransu abunsu, Mus'ab ne ya tashi zaije ya kunna Tv, Aunty tayi maza tace mishi "koma ka kashe TVn nan ku wuce kuje kuyi alwala kuzo muyi salla" komawa yayi ya kashe TVn duk suka tashi suka tafi sama yin alwala, basu fi minti biyar ba suka sake sauk'owa bayan sunyi alwalan, Baba ne yajasu Sallah dukkansu kasancewar an idar a masallacin gidan, suna idarwa sukayi y'an addu'oinsu suka shafa, hannu suka mimmik'awa junansu har Baba da Aunty suna cewa *Baa nda dubdo, Auntu nda dubdo*, (Baba ina wuni Aunty ina wuni), "Wassalatu wassalamu ala Rasulillah" Al'adan gidan kenan indai sukayi sallah sai sun gaida junansu , suna gamawa wata mata siririya da baza ta wuce 25 yrs ba ta shigo falon ta k'ofan kicin , sanye take da kayan kuku tana rik'e da wani food flask mai kyau zatayi hanyan dinning su Yusra ne suka hangota suka ruga wajenta da gudu suna faďin "Aunty Esther mun dawo, ashe kina nan shine baki fito ba, mey kike dafawa, jawosu tayi jikinta tace muje kuga abinda na dafa in baiyi muku ba sai ku faďa min wanda kukeso, murna suka sa suna jin daďi, sai da tazo ta gaida Baba da Aunty sannan taja yaran suka tafi, Baba ma mik'ewa yayi yace yana da aiki gobe sosai yanxu zai fita, tare suka ce mishi "Baa adawo lafiya, Allah ya bada sa'a" , Amin ya amsa musu da sannan ya fita, Mik'ewa Batuul tayi ta k'ira janet tace ta hawo mata da jakanta, ana kawo jakan ta ciro Macbook ďinta ta kunna, skype ta shiga ta duba ko Farida na online, da taga bata nan ne ta ďau waya ta k'irata, tana amsa tace kixo skype sannan ta katse wayan dan tasan in Farida ta fara magana ba yanxu zata gama ba, connecting tayi da Farida, tana ganin Batuul ta mik'e cikin sauri ta zauna, cewa tayi "babe i missed you soo much, ji nakeyi kamar Nigeria gaba ďaya kuka bari ba Maiduguri, i just cant wait to be back, katseta Batuul tayi tana dariya tace "Riri you can talk for Africa, tun ďazu fa kike magana , har na tausayawa Affan", dariya Farida ma tayi tace " He loves me, babu yadda zaiyi, infact he enjoys surutuna and not only Africa, the whole planet", dariya suka sa dukkansu biyun a tare sannan Farida tace "Ya hanya, what time kuka isa", "Hanya Alhamdulillah , tun 12 but sai 2:00 muka isa gida" sunanta ta k'ira tace "Farida Yaa Abun ku yau ya dawoDawo Abuja ko" dan ita gani take ba shi bane, da sauri Farida ta amsa da "Ehh, kinji yadda gidan yayi daďi, dama so nake ya tafi, naji ance ma country ďin gaba ďaya zai bari, ni daďi nakeji, kinga ko yau da ya tafi har na samu na fita" Batuul ce tace nifa babu ruwana kullum kiyi ta gulmanshi, nidai babu ruwa", tsaki Farida taja tace "ai idan ka nuna kana tsoronshi ya fi baka wahala, ni yazo yayi aure ma ya tafi" dariya Batuul tayi tace "zaki sani, nifa about grads na k'iraki, gown zan saka , kefa" ta tambayi Farida , "Ni wando zan saka" inji Farida, "wane wando kuma sai kace su Hamra, its either gown or skirt, am not wearing any trouser" dariya maganan ya bawa Farida tace "woh calm down lady , am just kidding, yadda kikace haka zamuyi, but a ina zamuyi ordering", "dont worry about that, just send me irin wanda kikeso zan bayar ayi mana" inji Batuul, "aii zan tura miki details ďin duka " da haka sukayi sallama, suna gama wayan Batuul ta cire kayanta ta shige toilet ta watsa ruwa ta fito, wani doguwan riga ta saka mra nayi bayan ta shafa mai, ta ďan fesa turare





Abutturab na isa gida ya shige ciki yasa key ya buďe dan babu kowa, ďakinshi ya nufa yana shiga ya zauna akan gado, tunanin aikin dake gabanshi yayi, mik'ewa yayi ya shiga toilet ya watsa ruwa yayi alwala ya fito, kaya ya canja amma basu kai waďanda ya cire nauyi ba, sallah ya tada, uana idarwa bayan addu'oin da yayi ya mik'e ya sauk'a k'asa, kitchen ya nufa ya fara neman abinda zaici dan ko breakfast baiyi ba, coffeee ya haďa ya zauna a kujerun island ďin kitchen ďin ya fara sha, sai da ya gama juye saurin a wani ďan madaidaicin flask ya koma sama dashi, wani ďaki daban ya nufa na glass, komai na ďakin farine da glass, sanyi ke fitowa daga ciki, yana shiga ya isa wajen wani drawing board ya zauna a kan kujeran dake gaban board ďin, kayan aikin architects ne a ďakin irinsu irregular curves, french curves, desktop ďin apple, daga gefa akwai wani table akai an ďaura su set squares, CAD,pencils da sauransu, wayanshi ya ciro ya k'ira layin Amma, tana ďauka yace mata "Ammah ina wuni" da lafiya ta amsa sannan ta tambayeshi ya hanya, "Alhamdulillah ya amsa mata da sannan yace sun isa lafiya" tambaya yayi ko Abui na gida tace ehh, mik'awa Abui wayan tayi sannan shima suka gaisa, addu'a yayi mishi akan aikin da zai fara sannan Ammah ta karb'i cewa Ammah yayi "Ammah ki faďawa masu aikin dake BQ na dawo suzo su dafa min wani abu am hungry", cike da damuwa tace "Abu saida nace kayi breakfast kace ba yanxu ba gashi 2:30 yanxu, kuma kasan condition ďinka,zance suyi maza su shigo suyi maka " sannan ya katse wayan bayan yayi godiya, gaban desktop ďin ya koma ya fara danne danne, wayanshi ne yayi k'ara, ganin mai k'iran ya ďan saki tsaki sannan yayi recieving tare da sawa a kunnenshi, daga ďaya bangaren aka fara magana "Hello baby, ranan i called you kace min in ka koma gida you will call me amma baka k'ira ba", shiru yayi baice komai ba har saida ta gamana sannan yace mata "ya kk", cikin yanga da karairaya murya tace mishi "lafiya inata missing ďinka amma kai babu ruwanka dani, ko da kace zaka k'irani inata jira naji shiru", ce mata yayi "yeah i was busy shiyasa, Yasu Mum" bata ji daďin amsan da ya bata ba amma ya ta iya tunda tana aonshi haka zata hak'ura , ce mishi tayi "su mum lafiyansu rannan ma tace in garish ska", "ina amsawa, in kun dawo zamuyi discussing wani issue, i dont want to take long, so in kun dawo sai muyi magana", tunanin maganan da zasuyi ďin ta tsaya yi a ranta, tana ta addu'an Allah yasa maganan aurensu ne dan ta daďe ta nuna mishi ya fito ya ncewa ba yanxu ba, shirun da yaji yayi yawa ne ya sashi tambayanta "kina jina" da sauri ta katse tunanin tace mishi "Eh ina ji, amma baby wane magana ne baza muyi ba sai na dawo, ai waya ma ya isa" katseta yayi da cewa "nace sai kin dawo ba awaya zanyi maganar ba" jiki a sanyaye tace "okay sai mun dawo" ta katse wayan, sai da ya gama wayan ya koma wajen CAD ďin yana daddanawa







Batuul na saukowa ta nufi palo inda Aunty ke zaune, kusa da Aunty taje ta zauna sannan tace mata "Aunty sannu da hutawa", "yawwa sannu Batuul", magana ta gani a bakin Batuul dan taga yadda take ta fidgeting da zoben dake hannun ta, tace mata "Menene Kinxo kin sani gaba kin kasa mgana", a hankali Batuul ta buďe bakinta zatayi magana sai kuma ta fasa, da Aunty taga Batuul

1 Comments On BATUUL
avatar
hafsat-9-3

12 months ago

Reply

Nice book

Please Login or Register in order to submit comment