Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta wani lumshe ido tana d'aura duka hannayenta biyu a k'irji tace "Allah dan ita kad'ai na yadda na k'araso, kuma kasan wani abu......", bai barta ta k'arasa ba yace "Let's get going, d'an wannan surutun naki zamu kwana nan baki gama ba", suna tafiya yake tambayanta Yasu Ammah da kowa a gida, kamar jira takeyi ta dinga mishi zuba, wasu abubuwanma ba ji yakeyi ba har suka isa inda yayi parking mota, butt ya bud'e mata ta saka jakarta a ciki, sannan ta xagayo ta zauna, sai da ya tada motar suna tafiya sannan ya juyo ya dubeta yace "kina jina?", gaba d'aya hankalinta ta tattaro ta kalleshi jin yana mata magana, yaci gaba da cewa "Babu ruwanki da duk wani abu da zaki gani in mun je, Ajiddeh isn't aware Batuul is my wife", a firgice ta kalleshi tace "What?", kallonta yayi ya wani hade rai yace "Yeah you heard me right, dan haka babu ruwanki da duk abinda ke faruwa cikin gidan, am repeating it, don't try anything stupid like you did last time, babu ruwanki da Ajiddeh", tabe baki tayi ta kauda kai, yace " Baki da hankali ina maki magana kina dauke min kai" xumburo baki tayi ta gyad'a mishi kai alamar ta ji, ya hade rai sosai yace "bakida bakine?", ta dan murguda baki tace "Toh naji mana", kwafa yayi ya ci gaba da driving dinsa, ta d'auke kai ta juya tana kallon window, ranta ne taji ya baci ba k'adan ba wai Ajiddeh batasan Batuul matarsa bace, toh does that mean they weren't intimate ko me, shine har Ammah ta fara lissafin jikoki, "Chabdi" ta fad'a a ranta ba tare da tasan ya fito fili ba, juyowa yayi yana kallonta yace "kikace meye?", maza tayi ta kad'a mishi kai tace "No ni bance komai ba", ya harareta ya maida hankalinsa kan driving din da yake,farida taci gaba da sak'e sak'enta, a ranta tace masifaffe wai wani I shouldn't try anything stupid, tabdi ai kuwa wlhy sai dai in wannan matar tasa mai kama da bishiyar gwanda sai tsawo babu shape tayi hankali itama, dan indai ta tab'ani ba yadda za ayi in k'yaleta wlhy sai na rama, kuma sai nasan ynda nayi tasan wacece Batuul, "kutt, ai wlhy bama zai yiwu ba", batasan a fili tayi maganar ba saida taga yayi parking yana mata wani irin kallo yace "meye d'in ne bazai yiwu ba?", da sauri ta shiga girgiza mishi kai a rikice tace "I wasn't talking to you fa", ya jima yana kallonta fuskarsa daure kafin yayi k'wafa ya ci gaba da driving, bata kuma gigin wani tunanin ba bare har ya fito fili, kamin su isa har gari ya washe, bayan yayi parking kamin ta fito in a serious tone yace mata "hope you heard all I said clear?", kai kawai take girgiza mishi dan ita ta matsu taga Batuul, yana bud'ewa ta fita guje ta shige gidan, tun daga bakin k'ofa ta fara ihun "His beloved, His First Lady, kina ina na iso", A guje Batuul dake kitchen ta d'an samu karfi tana gyare gyaren kitchen din ta fito jin muryar Farida, Ajiddeh da Aunty dake d'aki ma fitowa sukayi lokaci d'aya ganin wake ihun, Abu kam mamakin Farida ne ya cikashi jin abinda take fad'i, ya k'asa karasawa parlorn, ita ko ta tafi da gudu suka rungume juna da Batuul cike da murnan ganin juna, farida ta tura Batuul daga jikinta tana kare mata kallo ta wara ido har da d'an tsallanta tace "Waoww waow, yayana ya iya kiwo wllh, kinga yanda kika yi wani fresh kika yi kyau kuwa love, OMG" wani tsawa da ya rikita ta daga ita har Batuul din Abuturrab ya daka mata.


πŸ’–πŸ’BATUULπŸ’–πŸ’

70

By phartiemarhk

Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*

Wani mugun kallo yake yi ma Farida yace "kin wuce kin bar nan ko sai na zo na sameki, are you stupid ku ke min ihu haka a gida", duk da tsoron da taji hakan bai hanata dakewa tayi kamar ba da ita yake kamar ba, ta d'aga kai ta kalli su Ajiddeh da ido ya k'ank'ance da masifa, harara ta galla mata daga haka ta kuma maida dubanta kan Batuul tana washe baki tace "keh kin ga gashinki kuwa yadda ya wani dad'a cika yayi tsawo, meye sirrin 'yan mata, sea foods da salads kike ci ne? Kai Amma gaskiya gidan Yayana ya......", bata k'arasa ba taga yana tunkarosu, hanjin cikinta ne suka kad'a ganin haka, Batuul kam ko a jikinta sai dariya take, yana zuwa yasa hannu ya fincikosu a tare yayi hanyan stairs yana rik'e da hannunsu, ko lura da Ajiddeh da yayarta bai yi ba a sama, Batuul ta finciketa nata hannun daga rik'on da yayi mata ta tsaya cike da masifa tace "meye haka kake wani jana kamar igiya, ni nace maka inason zuwa sama ne?", da mamaki ya tsaya kallonta da har bai san lokacin da ya sake hannun Farida ba ta sulale a guje tayi sama abinta tana 'yar dariya, abubuwane kawai ke mishi yawo a kai, badai har yarinyar nan ta raina shi ba, ita kanta Ajiddeh da yayarta sakin baki suka yi suna kallonsu, juyawa Batuul tayi zata tafi ya fizgota gabanshi yana kallon fuskanta yace "Are you stupid?, ni kike ma magana haka, are you out of ur senses?" sauk'owa Ajiddeh ta shiga k'ok'arin yi daga saman da take tsaye dan bataji zuciyarta zata iya jure wannan abinda take gani gabanta, Aunty Jainaba ce tayi saurin riketa a hankali tace mata "keh shashasha tsaya, ki bari muga iya gudun ruwansu, ai inaga ma lokacin maganinta yayi a gidan, kema dai kinyi sakaci, meye na barin budurwa haka a gidanki", da mugun kallo "Ajiddeh ta dubi Jainaba tace "dalla can toh da duk abinda nake gaya muku Kun zata wasa nakeyi, toh yau koma menene, k'arshen xamanta yazo wllh" Batuul kam turashi ta shiga yi tana murgud'a d'an k'aramin bakinta tace "Ni ka rabu dani", duk wannan abinda sukeyi baisan su Ajiddeh na sama ba, matseta yayi jikinshi ya murd'a mata hannu yace "sai kin fad'a min sudden change of behavior nan naki, wato na fara miki wasa shine zaki rainani", had'e rai tayi hawaye taf idonta ta turashi daga jikinta tace "Ni kam ka sakeni", sauk'owan da yaji ana yi daga stairs ya sa ya daga ido da sauri, Ajiddeh ya gani tana sauk'owa furiously, with full rage a fuskanta, tura Batuul d'in yayi yana mata mugun kallo yace "b'ace min daga nan", juyawa tayi a fusace ta nufi stairs, karo suka kusa yi da Ajiddeh ta koma baya da sauri ta raba ta gefenta xata wuce, a zuciye Ajiddeh ta fincikota ta hade ta da bango tana huci tace "Keh dan ubanki nayi miki kama da sa'ar uwarki da har zaki dinga min isa a gidana, to wllh xaman ki ya kare yau a gidana yanxun nan kuma ba sai anjima ba" turata Batuul tayi tace "kar ki sake ki sake gigin tab'ani wllh, zagi kuma wannan training din da aka maki kenan gidan ku, banida time d'inki", da haka ta juya ta haura sama ta bar ta nan tsaye, kwalalo ido jainaba tayi, Ajiddeh kam mutuwar tsaye tayi gun ta kasa kwakkwaran motsi, bata tab'a tunanin Batuul zata iya yin abu kamar wannan ba, a zuciye ta k'araso wajen Abu har wani rawa jikinta ya shiga yi sai hargowa take tace "Aliyu wlhy wlhy, kadai ji na rantse koh, toh yarinyar nan sai ta bar gidan nan yanxun nan, in kuma bata bari ba ni zan bar maka gidanka, ai dama nasan wannan kareta da kakeyi duk sabida kana samun wani abun gunta ne, wa ya sani ma ko zagayawa kakeyi gunta da daddare zaman dadiro kakeyi da ita, in ba haka ba, yaushe har zata rainaka ta rainani, dubi yanda ka wani rungumeta yanxu, ni za a rainawa hankali a wani ce karatu tazo yi, toh koma meye ta zo yi ni bazan zauna da ita gidan nan ba , kuma in ba karuwanci takeyi ba Meye ma'anar aman da naga tana kwararawa jiya kamar mai ciki, ko daxu sai da naji kakarin amanta har sau biyu a daki, ohh wato karuwa ka kawo min gida ka.....", bata k'arashe maganan ba ya d'aga hannu ya sharara mata mari da ya gigitata, har Aunty Jainaba saida taji tsoron jin irin marin, Aunty Jainaba ce tayi saurin saukowa ta rufe mata baki tace "ke don uwar ki Meye haka kike yi, yaushe ne zakiyi hankali Ajiddeh, jibi fa irin maganganun dake fitowa bakinki, mijin naki kike yiwa magana haka?, dama bakida hankali ashe", tana yi tana k'iftawa Ajiddeh ido tayi shiru, fincike hannunta tayi daga rik'on da yayi mata, idonta har ya canza kala duk ya k'ank'ance hawaye na xuba idonta tace "ai ka mari aurenka Aliyu, akan gantalalliyar y'ar iskar nan kake mari na, ai ba sai ka mareni ba zansan mey ke tsakaninku, kuma yau zan bar maka gidanka", ta juya fuuuu tayi sama, Aunty Jainaba ce ta kwantar da murya tace "Aliyu ashe haka kake fama, ai ni ban tab'a sanin haka yarinyar nan take mara hankali ba, Dan Allah kayi hak'uri ba sai ka daka ta tata ba, kasan hankalinmu ba d'aya da naku ba, kayi hak'uri kaji?, zanje yanzu in ci uwarta, Allah ya k'ara maka hak'uri", kasa cewa komai yayi tunda yaji abinda Ajiddeh tace "wai cikine jikin Batuul, ciki kuma? toh wane irin ciki", a hankali ya maida dubanshi kan Aunty Jainaba yace "Ba komai", da haka ya barta nan tsaye ya haura sams, d'akin Batuul ya wuce kai tsaye, bud'e k'ofan d'akin yayi ya shiga rai a had'e, Farida dake zaune tana ta zuba bata san lokacin da ta fasa ihu ta mik'e tsaye daga kan gadon ba tana yarfe hannaye, sau d'aya Batuul ta kalleshi ta d'auke kanta tana kallon Farida tace "Keh wai meye haka kika hau gado kina wani tsalle, ko ce miki akayi bouncing castle ne?", kallonta Farida tayi sannan tayi mata nuni da Abu dake k'arasowa cikin d'akin da baki, kallonshi tayi ta tab'e baki tace "toh mey zai miki?", fuska a daure yana kallon Farida yace "get down", sake matsawa tayi jikin gadon tace "Dan Allah kayi hak'uri Yaa Abu, bazan sake ba", k'arasawa yayi bakin gadon ya fizgota yana mata mugun kallo, ihu ta fasa ta rintse ido tana jiran jin sauk'ar mari, "ni nayi kama da sa'an ko koh? all those warning I made clear to you basu shigeki ba?", a hankali ta bud'e idon jin bataji sauk'ar mari ba, kamar munafuka tace "Yaa Abu nifa bance komai ba, kawai cewa nayi ai ka Iya reno, Batuul tayi kyau", tsaki yayi ya hankad'ata har sai da ta fado daga kan gadon yace "Baxa ki kwana min a gida ba yau"

Ajiyar zuciya Jainaba ta sauk'e a fili ta furta "Lallai da aiki a gabanmu", sannan ta juya ta haura saman itama, a bakin k'ofa sukaci karo da Ajiddeh janye da akwati, da mamaki take kallon Ajiddeh sannan ta riqe akwatin tace "Keh meye hakan?, ina zaki da akwati", Ajiddeh tace "kema in zaki tattaro naki ki d'auko kizo mu wuce dan ni na gama zaman gidan nan indai wannan bak'ar yarinyar tana nan, ni wlhy right from day one ba santa nakeyi ba, bare yanzu da tazo ta tare take zama min a gida, gashi har wata suka k'aro mishi dan munafurci da sa ido", kuka sosai ta fashe da, Aunty Jainaba ta ja ta suka koma dakim ta zaunar da ita, Fridge ta bud'e ta mik'o mata ruwa, ta sha sannan ta karb'a ta ajiye tace "ashe keh bakida hankali ban sani ba Ajiddeh, ashe ba da kai kike tunani ba?", kallonta Ajiddeh tayi hawaye na sakko mata tace "ban gane ba", zama itama Jainaban tayi daga gefenta tace "Gashi ko kin nunamin alamu, in banda rashin hankalinki ina kika kinkimi akwati zaki da?, wa yace miki ana yiwa namiji haka bare wannan mijin naki d'an isa da kallo ma mutane basu isheshi ba, kina gani fa ko kunyata baiji ba ya sharara miki mari, toh ina ga in kin bar gidan, ai sai abinda yaci gaba, duk danginmu kaf cikinmu babu wanda ya tab'a auren mai irin kud'in mijinki kin sani, duk da kema naki uban nada kud'i amma ko k'afar nashi uban bai kamo, gashi shima yaro dashi amma arzik'inshi yafi k'arfinshi gashi komai kikace kinaso sai ma ya miki dad'i badai ragi ba, zancen zaki bar mishi gida bai zo ba, Allah ne yayi zanzo inga rashin hankalin da kike kwab'awa, duk da nazo da shiri amma dai nasan sai mun sake akan nada, wannan duk yadda akayi ya riqe ibadarsa sosai shi yake hana aikinmu ya kamashi, kuma ina jin iyayensa ma basu bar shi haka ba, yanzu watanmu uku muna abu d'aya amma bama tab'a cin nasara, wannan karan kuwa ba da wasa zamu shigeshi ba, itama wannan yarinyar gaba d'aya b'atar da ita zamu sa ayi tunda har a dalilinta yake marinki, dan haka dole ne abi ta kanta a magance matsala, sati d'ayan da nazo yi na fasashi, jibin nan zan koma in fad'awa Yaya duk abinda ake ciki, sosai zamu tashi tsaye akanshi, sai mun sa ya gwammace kid'a da karatu", kamar wata wawiya tana nan zaune har sai da junaiba ta gama sannan tace "Toh yanxu ya zanyi, dan ni duk matar da ta rab'eshi ko tace zata shigo rayuwarshi wlhy Allah sai na hallaka koma wacece, sai dai nima a kasheni, Anty baxa ki gane irin son da nake ma Aliyu ba" cikin matsanancin kuka ta kare maganar, junaiba ta sauke ajiyar xuciya tace "Ai babu wani zancen wata matar in ba ke zakiyi sake ki bashi dama ba, yanzu ki tashi ki kintsa kije ki bashi hak'uri daga nan sai kiyi mishi zancen tafiyata dan ya bamu d'an tsoka mu samu na aikin, suma Malaman na yanzu ba abin yadda bane sai kaga da k'yar ake samun na gaske, dubi fa abinda wannan d'an isakan mutumin yayi mana", mikewa Ajiddeh tayi har lkcn xuciyarta na tafarfasa don da xa a bata wuka a lkcn babu abinda xae hanata caka ma Batuul, Allah sa ma cikin ne jikinta kamar yanda take xargi, shikenan xamanta ya xo karshe gidan cikin ruwan sanyi, kwafa tayi ta mik'e ta shiga cire kayan jikinta tana naxarin abinda Anty jainaba tace.



Ficewa Farida tayi daga dakin tana xumbura baki a xuciyarta tace "Ae ko da na kira maka Ammah yanxun nan, kuma in fita in fasa gaskiyan komai" bin ta yayi da harara sannan ya dawo daga gefen Batuul fuskarsa daure, kamar bata ganshi ba ta mik'e k'afafuwa zata kwanta ya rik'ota cikin kaushin murya yace "I will slap you idan baki tsaya kin saurareni ba", kuka ta fashe masa da, nan da nan ya rude ya dago kanta yace "me ya faru kuma, me nayi maki" kin cewa komai tayi sai kukan da take, nan ya shiga rarrashinta kamar wata jaririya, da kyar ya samu tayi shiru, ya rungumota jikinsa ya lumshe ido yayi shiru, mamakin kansa kawai yake, ya rasa gane dalilin da yasa yake behaving haka, maganar Ajiddeh ne ya fado masa, ya bude idonsa a hankali yace "Are you noticing some changes a jikinki?, I mean do you feel anything unusual?", had'e rai tayi ta dago kai tana kallonshi tace "Meye toh kake tambayata", yanda ta had'e ran ne ya kusa bashi dariya amma ya dake yace "wai yaushe kika koyi rashin kunya ne, ina miki magana kina had'e min rai, ehhn tell me", ya k'arashe maganan tareda zame mata hular dake kanta, tsuke mishi baki tayi tace "Ina ruwanka da hulata da zaka ciremin, ni ka maida min abuna", yace "bazan mayar ba har sai kin fad'a min mey ya canja ki lokaci d'aya", sake had'e fuska tayi tace "wai wani canjawa, ni dama can haka nake kaine baka sani ba", dariya yayi yace "d'azu fa naga har my wi.....", sai ya tuna alk'awarin da yayi mata na cewa bai sake k'iran Ajiddeh da my wife gabanta, kwana biyu bata yi kuka ba har wani dad'i yakeji, kallonta yayi yaga ta tsareshi da ido yace " I meant Ajiddeh, d'azu har gani nayi kin kare kanki gunta, hmmm I lyk that courage, d new you, but banda wannan sabon attitude d'in towards me, kuma idan xaki mata fitsaran ki tabbatar ina gida", kallonshi tayi ta d'an tabe baki tace "ni ka tafi bacci zanyi", yace "bacci? mey ke damunki ne, we have to see a doctor, dan baccin nan naki ba na lafiya bane", zumb'uro mishi baki tayi tace "inji waye banida lafiya, am fit and fine", yace "ina wani fit and fine, bakida aiki sai amai da bacci, ko breakfast ma bakiyi ba yanzu, ko jiya ma bakici dinner ba", kamar jira takeyi ya gama magana tace "Yawwa kaga ma ko, ice cream nakeso in sha yau ma, amma ba na Gelatorino ba yau, na Cold stone nakeso, sai ka siyo ma farida breakfast", kallonta kawai ya tsaya yi yadda cute lips d'inta ke moving, ganin baice komai ba ta tsuke baki tace "I knew it dama baza kayi min ba, toh kaje zanyi da kaina", lumshe ido yayi ya janyota ya had'ata da jikinshi ya shiga kissing d'inta passionately, ita kam sai tutturashi takeyi amma yaqi saketa, Farida ce ta tura k'ofan d'akin ta shigo riqe da waya, turasa Batuul tayi da sauri ta koma baya, ganin condition d'in da suke ciki yasa tayi maza ta juya ta riqe bakinta tace "Oooops, am sorry, Ammah ke son yin magana da Batuul", Batuul dai kasa d'agowa tayi ta kalleta sai shine da ya bita da harara yace "out", da sauri taja musu k'ofar ta fita tana kyalkyala dariya.


πŸ’–πŸ’BATUULπŸ’–πŸ’





71___72






By phartiemarhk




Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*






D'ago kai tayi ta kalleshi bayan Farida ta fita, suna had'a ido tayi maza ta dauke nata tace " kagani ko, ni dai ka tafi daga d'akina", hannu yasa ya d'ago hab'arta yace "ita tace gidanta (Ajiddeh) keh kice d'akinki, kamar kun ma san sanda aka yishi", yana murmushi ya kare maganar, janye hannunshi tayi tace "toh ba d'akina ba, d'akinka, ka tashi ka tafi ni dai" ta k'arashe maganan tana zumb'uro mishi baki, ya buda ido yace "You are totally changing from what you were, kin koyi fad'a da rashin kunya, korata fa kikeyi, I can decide to stay with you for a whole year if you didn't change, beside I lyk being with you all d time, I can't get enough of you, your warmth, body texture, scent everything, next time bakin ki ya sake ce min in tafi sai na dawo d'akinki gaba d'aya da xama, ko kuma keh in maidaki nawa d'akin da zama", zumb'uro mishi k'aramin bakinta tayi tace "toh ba turarenka bane kullum sai ya rik'a min yawo akai, ni bana sonsu yanxu", ta fadi tana kauda kanta, kalllonta yakeyi har ta gama maganan snn yace "baki sonsu?", kai ta gyad'a mishi da sauri, yace "toh wanne kikeso in na amfani da? nuni tayi mishi da kan vanity table d'inta tace "ba ga nawa ba, kaita using ni bazan hana ka ba ai", dariya ta bashi yace "yanzu keh sai ki yadda in shafa turarenki, toh su meye ma naki turaren in banda humra, ni kuma mey ya had'ani da shafa humra", had'e rai tayi tace "ai akwai wasu ba Humra bane kawai", yace "naji toh, yanzu zaki rakani in sai wasu sabbin turaren wanda basa damunki", da sauri ta kad'a mishi kai tace "Ni babu inda zani", girarshi ya d'age mata yace "woooh , fine I will go by myself, but in na kawo wani karki ce min shima na
damunki tunda kece kika qi zuwa kiyi selecting", murgud'a Mishi bakinta tayi tace "Na yadda", mamakin kanshi yake gaba d'aya, shi kanshi baisan mey ke damunshi ba, wai shine yayi stooping to Batuul's level har yake biyewa shirmenta, har wani murgud'a mishi baki takeyi amma he couldn't do a thing sai ma burgeshi da take, kallonta yayi yace "Okay, now tell me mey zakici, I will get it right away", ya had'e rai yace "don't tell me bakijin yunwa ko kuma ice cream zakisha, solid abinci nakeson kici", kallonshi tayi tace "Toh sai ka had'o min ice cream d'in da Burger na burger kings, kada a samin cheese, sai pizza shima na pizza hut amma fa beef, da chips d'in KFC sai kace su baka spice d'in da yawa, sai daga gefen school d'inmu akwai wani road side food vendor, shi kuma sai ka siyamin Tacos da chicken rolls a wajenshi, shima ya samin spice da cream dayawa", shikam kallonta ya tsaya yi tana magana tana lumshe ido, har wani tsayawa tunanin abinda zatacin takeyi , tace "Yawwa sai kuma Raffaello, a pack of twix and what keeps me moving Nutella", ta k'arashe maganan da dariya abinta tana wara ido, shi kam kasa cewa komai yayi sai kallonta yake ko kiftawa bai yi, ganin irin kallon ta had'e rai tace "Kaji?", d'an tab'e baki yayi ya kalleta yace "Naji, amma wai ke zakici duka wannan abinda kika lissafo?", kai ta gyad'a mishi tareda d'age girarta tace "toh zance ka siyo ne in baxan ci ba?, duka nikeson ci", yace "Fine", tareda da d'age mata hannayenshi, yace "wannan lissafin naki its better we order it, kowanne fa venue d'inshi daban", da sauri tace "Ah ah, nikam its better you go by yourself, kar suje sumin mistake", mik'ewa kawai yayi dan yasan rigima take jin yi, ta kalleshi tace "sai ka tambayi Farida ma abinda zataci", har ya kai bakin k'ofa tace mishi "kaga ko, baka maidamin hulata ba", sai ta fashe mishi da kuka, da har bazai juyo ba jin ta fashe da kuka yasashi dawowa da sauri ya wara ido ya sa mata hularta ya gyara mata kwanciya murmushi dauke fuskarsa yace "I've done that" mikewa yayi yana kallonta yace "I will send in Farida", da haka ya juya ya fita, a corridor ya tadda Farida na waya, harara ya bita dashi ya sauk'a batareda ce mata komai ba, dariya tayi ta juya ta shige d'akin, da sauri Batuul dake kwance ta juya mata baya, zuwa tayi ta fad'a kan gadon ta yaye bargon da Batuul d'in ke rufa da tace "Hey c'mon get up, ya tafi shine zaki wani kwanta, toh ga Affan nan, he is on the line", d'an tsaki taja tace "Riri you will never change wlhy", lumshe Ido tayi ta fad'a da baya snn ta d'ago tace "Ohhh how I missed this name, babe I missed you sooo much baza ki ganeba", dariya ta bawa Batuul, jin muryar Affan cikin wayan tayi maza ta mik'a mata tace "he is on the line", ture wayan tayi tace "ba ruwana dashi ai ni, ba ya manta dani ba, I don't want to talk to him nima, he promised to call me back rannan but he never did", ta k'arashe maganan tareda lank'washe hannayenta a k'irjinta, Farida ce ta maida wayan kunnenta tace "Mine", da sauri Batuul ta d'ago ta kalleta jin sunan da ta k'ira Affan dashi, a ranta tace "Sabon salo", "Mine kaji ko, kayi mata lefi, ita fushi take dakai", tace "Baby mine ina jinta, samin wayar speaker muyi maganan da ita", speaker ta danna snn ta ajiye wayan, yace "Hey sweetheart best friend, am so sorry for not calling back, these days kullum busy nake sabida shirin exams dake gabanmu, nayi miki alk'awari I will come immediately after my exams, not even before going home", da sauri ta d'auki wayan jin yace zaizo tace "Yaay that's my best friend", haka dai sukaci gaba da hirarrakinsu har ta gama ta mik'awa Farida wayar sukaci gaba da hirarsu ta soyayya, saida suka gama sannan Batuul tace "wai ke yanzu Farida dagaske kike son Affan dinnan?, he just 3yrs older than us fa", Farida

1 Comments On BATUUL
avatar
hafsat-9-3

12 months ago

Reply

Nice book

Please Login or Register in order to submit comment