Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ajiddeh kamar na kirki ta dinga kwantar masa da hankali wai she will be fine. Likitocin na fita ya shiga Ajiddeh na biye da shi a baya, rungumeta yayi ta kankamesa tana kiran sunansa cikin kuka, a rikice yace "Don't worry Fatima xa a cire babyn ki huta kin ji" girgixa masa kai kawai take tana kuka sosai, Ajiddeh ta xauna gefenta tana '' tana kallonta lokaci daya jikinta yayi sanyi jin ta ambaci mutuwa.
[11/15, 11:14 AM] ‪+234 810 957 2036‬: 💖💝BATUUL💖💝







78




By phartiemarhk





Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*




A hankali Ajiddeh ta shiga girgixa kai da kyar tace "No! Baxa ki mutu ba, Allah xai baki lafiya kin ji" Abuturrab da ya gama rudewa jin abinda tace ya rike hannayenta yace "Noo no baxa ki mutu ba Fatima, don't worry xa a cire babyn ki huta, bana so kuma, xa a cire soon kin ji, kar ki kuma cewa xa ki mutu plss" ko kadan Batuul bata san abinda suke cewa ba don ita kadai tasan abinda take ji a lokacin, tayi wani kara da ya kuma rudar da Abuturrab da Ajiddeh tace "Don Allah Anty ki ce ya kai ni gun Antyna nasan mutuwa xan yi, wayyo cikina" Abuturrab ya rungumeta a rikice yace "Stop this Fatima, ki daina kiran mutuwa plss" hawaye ne ya ciko idonsa yace "No! Baxa ki mutu ba wife, baxa ki mutu" Ajiddeh da duk jikinta yayi sanyi ita ma ta shiga hawayen a hankali tace "Baxa ki mutu ba, Allah xai baki lafiya" mikewa tayi da kyar ta fice daga dakin, ta tafi nesa da ward din, layin Mum dinta ta shiga kira, bugu uku aka daga, bangaren Mum tace "yauwa 'yar gari dama yanxu nake kokarin kiran ki, ya ake ciki kin ga alamar...." A sanyaye Ajiddeh ta katse ta tace "Mum kinsan me? don Allah kice a dakatar da aikin nan tukun....." Cike da mamaki Mum tace "A dakatar da aiki? Saboda me?" Da kyar Ajiddeh muryarta na rawa tace "Mum kinga fa kila mutuwa xata yi, kuma..." Sai ta fashe da kuka tace "Mum ni dai a dakata tukunna....." Wani uban ashar mum ta kunduma mata a fusace tace "Shegiya sallamammiya, kin san nawa na kashe 'yar abu kaza kaza, a dakatar da aiki??? Wani irin zagi Mum ta kuma k'undumo mata da har saida ya tsorata ta, a fusace ta diro daga kan gadon da take cikeda masifa tace "Keh kinsan mey kike cewa? to kinyi kadan Ajiddeh, a xuri'armu bbu warce ta taba zama da kishiya, baxa kuma a fara a kan 'yar cikina ba, Aliyu naki ne ke daya don ubanki, Ajiddeh cikin kuka tace "Mum nifa bance zan zauna da ita ba, kawai dai bana son ta mutune", Fusata Mummy ta sakeyi har wani gumin masifa ke tsattsafo mata a goshi, rai a b'ace tace "keh don ubanki ki fita idona kinaji, shegiyar yarinya da bata san abinda takeyi ba, zur'armu kaf babu wacce ta zauna da kishiya, mey ma za ayi da zama da kishiya, Allah bai d'aura mana ba kema kuma baki zama da ita, ita da take gantalalliyar kishiya ma har aka munafurce ki akayi komai shine kike tausayinta, indai ni haifeki kika kuma tausayin yarinyar nan sai. na tsine dan haka in zaki dawo hankalinki tun wuri ki dawo kisan inda dare yayi miki, wawiyar yarinya kawai, kina abu sai kace bani na haifeki ba, K'anwar uwarki ce yarinyar da zakice mituwa zatayi ko kuma in ta mutun asara ne dake, mutuwa kuma kamar tayi shi daga ita har shegen dake cikinta, kaji min wahalalliya mara wayo, to kin yi k'adan yanxu ma shiri nake xan koma kauyen don ba a gama aikin ba" Ajiddeh ta fashe da kuka sosai tace "Allah mum ni dai ba ruwana, kar ta je ta mutu...." Wani raxanannen tsawa Mum ta daka mata ta dinga kunduma mata zagi tace ", Ajiddeh ta katse wayar ta jingina da bango hawaye na sakko mata, da kyar ta ja kafa ta koma ward din, hankalin ta ya kuma tashi ganin halin da Batuul ke ciki, likitoci biyu a kanta, karasawa tayi da sauri ta xauna kusa da ita jin abinda take ta cewa, ta rike hannunta hawaye na sakko mata tace "Baxa ki mutu ba, sai lokacin ki yayi" Abuturrab dake xaune ya rike kai ya d'ago da kyar yana kallonsu da idanuwansa da suka kada, ya karbi wayar Ajiddeh don bai ma san inda nasa yake ba, ya fita don kira Ammah shi da likitocin xa su ji ta nasa da an cire cikin a nn take kawai amma sun ki wai sai bayan awanni idan suka gama binciken da suke, rungume Batuul Ajiddeh tayi, sai ce mata take cikinta, dubara ne ya fado ma Ajiddeh ta shiga tofa mata addu'a a hankali, Abuturrab na fita ya kira Ammah, tana d'agawa ya kasa ce mata komai, tayi sallama yayi uku kafin da kyar yace "Ammah, Batuul...." Jin muryarsa Ammah tace "Abuturrab, lafiya me ya faru" da kyar ya kuma cewa "Batuul..." Nan hankalin Ammah ya tashi ba kadan ba tace "Kayi min magana mana Aliyu, me ya samu Batuul din" k'asa bata amsa yayi hawaye na sakko masa, nan hankalin Ammah ya kuma tashi barin da taji yayi shiru kuma tasan hawaye yake shirun nan, don ita ta haifi abunta, tsawa tayi masa tace "Kana da hankali kuwa Aliyu, baxa ka fadi abinda ya samu Batuul din ba" da kyar ya bude baki yace "Bata da lafiya ne" tayi kokarin boye tashin hankalinta tace "Subhanallah! Tun yaushe?" Yace "jiya" sosai hankalinta ya tashi don tasan ba abu kadan bane Abuturrab xai ma hawaye, tace "Me ya sameta?" Ya girgixa kai bai ce komai ba, Ammah tace "ka bude baki ka min magana Aliyu, farida fa?" Da kyar ya iya cewa 'Daxu na Kai ta airport " Ammah tace "Dawo min da ita immediately" "toh" kawai ya iya ce mata ta katse wayar hankali tashe tayi part din Abui. Juyawa yayi ya koma ward din, har lokacin Batuul na jikin Ajiddeh idonta lumshe, sai dai a hankali take kukan yanxu sai ajiyar xuciya da take saukewa jin kamar an xare mata ciwon, ita ko Ajiddeh bata fasa to fa mata addu'a ba, don bata ma san Abuturrab ya shigo dakin ba, tsaye yayi jikin bango yana kallonsu hankalinsa ya d'an kwanta ganin Batuul ta nutsu, karasawa yayi gun gadon ya xauna gefensu ya kamo hannun Batuul yana kallonta, a hankali ta bude rinannun idonta tana kallonsa, Ajiddeh ma ta juya tana kallonsa, kauda kai Batuul tayi, murya can kasa tace ma Ajiddeh xata je bayi, Ajiddeh ta mike ta d'agata ya bi su da kallo har suka isa bayin, a nan bakin kofa Ajiddeh ta jira ta tafito ta kuma kama hannunta suka koma kan gadon, A hankali Abuturrab na kallon Batuul yace "Ya daina cikin?" Kai kawai ta gyada masa, ya kalli Ajiddeh yace "We are leaving for Nigeria gobe" ita ma ta gyada masa kai kawai. Wayarta ne ya shiga ring a hannunsa ya mika mata ta karba ta ga Jainaba ce, gabanta ya fadi ba kadan ba taki d'agawa ta ajiye, ta juya tana kallon Batuul da ta rufe ido har bacci ya fara daukanta ta ci gaba da mata addu'a a xuciyarta, Abuturrab ya mike ya fita, ba a dau lokaci ba ya dawo, yana kallon Ajiddeh yace "Xa a cire cikin yanxu, it's time" Ajiddeh tayi shiru tana kallonsa sai kuma tace "saboda me?" A hankali yace "She's suffering babe" girgixa masa kai tayi duk da wani abu da taji ya tokare xuciyarta tace "No! Allah xai bata lafiya a bar mata" a sanyaye yace "A'a gwara a cire mu samu rest of mind" da kyar Ajiddeh tana kokarin maida hawayenta tace "if dat's ur only child or hers a duniya fa," d'an murmushin karfin hali yayi yace "baxan iya jure ganin tana wahala haka ba, ke kya haifa min masu yawa idan Allah ya yrda" duk yanda Ajiddeh ta so convincing dinsa a bar cikin kin yarda yayi, mikewa tayi daga karshe ganin da gaske cire cikin xa ayi, ta dau wayarta ta fita, Ammah ta kira yana fara ringing ta d'aga, sama sama Ammah ta amsa gaisuwarta don tun kiran Abuturrab bata da nutsuwa barin da ta kira can Maiduguri taji ciwon Batuul har da sa hannu, Ajiddeh da ta ma rasa abinda xata ce a hankali daga karshe tace "Ammah dama wai Batuul ce ba lafiya kuma laulayi take, shine Aliyu wai a cire cikin nayi masa magana ya ki saurarata" tana maganan ne da kyar don wani tukuki take ji a xuciyarta ta rasa dalili, a dakile Ammah tace "Toh don uwarsa tunda bashi da hankali ba sai yasa a cire ba muga, wawa da shi ba xai rike addu'a ba an tasa shi da iyalinsa a gaba sai haukan banxa shi d'an boko, ni ban taba gani soko mara wayau kamar Aliyu ba, kuma yana tare da wahala in har baxai rike addu'a ba, Batuul kuma ta Allah ba ta mutane ba, bbu abinda xai sameta sai Wanda Allah ya rubuto mata, babu abinda aka isa ayi mata, ciki kuma sai ta haifesa lafiya idan Allah ya yrda, ki bani gantalallen" jikin Ajiddeh yayi sanyi ba kadan ba lokaci daya hawaye ya cika idonta ta ja kafa da kyar ta koma ward din ta mika ma Abuturrab wayar, hannu yasa ya karb'a batareda yasan ko waye ba ya kara wayan a kunnenshi






Thank you to these amazing beautiful Sisters, I feel motivated to type whenever i see your messages, thank you for your prayers and all, Allah ya karamin lafiya to keep on with you girls

~MRS ❣❣SPLENDID❣❣
JAMMY JAMMY
SUGRAH❤
MEELA ADEEL
MOM SADIQ
RUQAYYA (ZUMA)
NAJA'ATUU
UMMIEE
MISS😍 SOFTIE
JUWAIRIYYA
[11/15, 11:14 AM] ‪+234 810 957 2036‬: 💖💝 *BATUUL*💖💝



79




*By Phatiemarkh*




Jin muryar Ammah ya d'aga kai yana kallon Ajiddeh, a fusace Ammah tace "Kana ji na ka min shiru Aliyu" yyi kasa da kai yace "A'a Ammah ina yini?" cike da fada tace "Rike gaisuwar ka, maxa tun muna mu biyu gobe ka taho min da Batuul gida, ai tun ba yau ba nasan kai shashasha ne, uwar ka cikin ya tsare maka kake son a cire" kasa cewa komai yayi, Ammah tayi ta bambami ya bari tayi mai isarta sannan a hankali yace "Ammah tana wahala ne, ki tambayi farida in ta iso gobe" Ammah tace "Ya baxa tayi wahala ba kana xaune da makira a gida a matsayin mata sun sa min ita a gaba, ina me tabbatar maka xaka ga the other side of me idan abu ya samu Bitti, maxa ku bar asibitin nan gobe ku biyo 1st flight ka dawo min da ita Nigeria" Ammah na kai wa nan ta katse wayar, ya daga kai yana kallon Ajiddeh dake jingine jikin bango duk jikinta a sanyaye, ajiye wayar yayi yace "Why did you call her?" Bata ce komai ba ta juya ta fice daga ward din, juyawa yayi a hankali yana kallon Batuul dake bacci, dawowa yayi kusa da ita ya daura hannunsa a hankali kan fuskarta, sosai ta rame daga jiyan xuwa yau, lumshe ido yayi cikin sanyin murya yace "Get well soon wife" mikewa yayi jiki ba kwari ya koma gun likitocin don dakatar da su, A asibiti suka kwana ranan don gani yake suna komawa gida ciwon xai tashi, sai dai throughout daren ko farkawa Batuul bata yi ba, a spare bed din dake dakin Ajiddeh ta kwanta, sai dai kwata kwata ta kasa bacci ta rasa me ke damunta, Abuturrab dake xaune kan darduma a dakin yana kula da yanda take ta juye juye sai dai bai ce mata komai ba, da asuba suka bar asibitin don bai son suyi missing 1st flight kamar yanda Ammah ta bukata duk da he is not sure xa su samu, a mota yana driving ya d'an kalli Ajiddeh yace "We will be leaving for Nigeria, xan maida Batuul gida, you take care...." Bai karasa ba ta katse shi tace "Nima xan je" kallon ta ya kuma yi sai dai bai ce komai ba ya ci gaba da driving dinsa yana yi yana kallon Batuul da har ta koma bacci a bayan motar. Ba tare da bata lokaci ba duk suka shirya, Batuul dama shi ya taimaka mata tayi wanka ta shirya don yaga alamar in suka biye ta nata bacci kawai xata yi tayi, Biyar saura suka isa airport yayi masu booking, biyar da rabi suka yi set off for Nigeria, duk motsin da Batuul dake rungume jikinsa xata yi idonsa na kai don waje daya suka xauna har lokacin kuma bacci take, lkci lkci kuma ya kan juya ya kalli Ajiddeh dake gaba ta saka earpiece, sai a sannan ya fara tunanin sudden change dinta is it for real, maganganun da Ammah ta fadi masa jiya suka fado masa, wai sun sa Batuul a gaba, ya sauke ajiyar xuciya don shi bai yrda da wannan belief din ba, a hankali Batuul ta bude ido tana kallonsa, ganin yanda ta bata fuska gabansa ya fadi a hankali yace "What?" Ta rike hannunsa tace "Ya Abu cikin xai fara" hankalinsa ne ya tashi ya daura hannunsa a cikin yace "No, no baxai fara ba idan Allah ya yarda" runtse ido tayi jin kamar ana murda mata cikin ta sakar masa kuka tace "Wllh ya Abu ya fara" ya rungume ta sosai yace "Noo wife baxai fara ba in'sha Allah, ko yunwa dai kike ji..." Ta fashe da wani kukan tace "Wayyo ya Abu cikin ya fara min" Kallon su kawae Ajiddeh ke yi, can kuma ta maida kanta kan wayarta, ganin kuka sosai Batuul ke yi jikinsa tana rike da cikinta ya kalli Ajiddeh suka hada ido, dauke kai tayi, ya sake Batuul ya mike ya tafi gunta cike da damuwa yace "Babe kin ji wai cikin ya fara, how are we going to do it, gashi ba muyi rabin journey ba har yanxu fa" ba tare da ta kallesa ba tace "Ba sai kayi ta tofa mata addu'a ba" yace "Yea haka ne kuma" juyawa yayi da sauri ya koma gun Batuul da ta hade kanta da gwiwa har ta hada xufa don axaba ita kanta baxa ta ce ga yanda cikin yake mata ba, ya xauna ya dagota ya kwantar da ita jikinsa yace "Sorry wife xai daina in'sha Allah" a hankali ya dinga tofa mata addu'a tana jikinsa, sun kusa awa biyu a haka har dai yaji ta daina kukan da take a hankali, ya leka fuskarta ya ga bacci tayi, ya sauke ajiyar xuciya ya lumshe ido ya manna mata kiss a forehead dinta, yana bude ido suka yi ido hudu da Ajiddeh dake kallon su, dauke kai tayi da sauri, ya ji wani iri shima ya dauke nasa kan. Shidda na yamma jirginsu yayi land a Nnamdi Azikwe Airport, ya kunna wayarsa ya shiga kiran layin Sadeeq, yana d'agawa yace "Hello Bro, ka taho kayi picking dinmu muna airport" daga haka ya katse wayar, ya kalli Batuul dake kwance jikinsa idonta lumshe duk da ba bacci take ba and he can see how happy she is to be home, ko bata fadi ba, Ajiddeh kam nesa da su ta xauna, bude ido Batuul tayi da sauri, yace "What?" Kallon matar dake xaune daga gefensu tana cin popcorn tayi ta bata fuska tace "Bana son kamshin xai sa ni amai" mikewa yyi da sauri ya d'agata suka bar wajen, Ajiddeh ta bi su da kallo, wani gun ya koma suka xauna, boye fuskarta tayi da sauri a kirjinsa yace "What again?" Kamar xata yi kuka tace "Bana son kamshin turaren mutumin nan" juyawa yayi ya kalli Mutumin dake xaune gefensu, ya mike ya dagota suka kuma barin wajen suka koma wani gun suka xauna, plantain chips taga wani yaro na ci ta kallesa da sauri tace "Ya Abu xan ci" yace "Me za ki ci?" Ta turo baki ta nuna masa chips din, kallon ta yayi, sai kuma ya mike ya nufi inda yaron da Mamarsa ke xaune yayi masu sallama yace "Don Allah a ina ku ka siya chips din nan Anty" matar tace "Ai kam ba nan muka siya ba" yace "Toh nagode" juyawa yayi ya koma gun Batuul ya xauna yace "Ki bari idan xa mu gida in siya maki a hanya suma ba nan suka siya ba" kamar xata yi kuka tace "Noo Ya Abu yanxu nake so wllh, kila anjima baxan iya ci ba xai fita raina" murmushi yayi ya jawota jikinsa yana shafa cikinta a hankali yace "Shi babyna yake son ci yanxu koh?" Bata fuska tayi, yayi dariya ya manna mata kiss ya cheeks dinta yace "Don't worry, it's nothing don babynmu yasa mu roko a airport" mikewa yyi ya koma gun masu chips, yana d'an Shafa kai yace "Anty ko xaku d'an san mana chips din k'adan, matata ce wai shi ke ranta taki bari mu fita mu siya" dariya matar tayi tace "Allah sarki duk mun cinye a jirgi amma bari in dibar mata na Kamal" yayi murmushi yace "Toh mun gode" ta karbi na hannun yaronta tace "Kamal idan mun fita xan siya maka wani ka ji" ya gyada mata kai, ta d'an dibar masa k'adan ta mika ma Abuturrab sauran na ledan ya karba yana murmushi ya shafa kan yaron yace "Toh mun gode kwarai Anty da kamal" tayi dariya tace "Babu komai, Allah dai ya raba lafiya" murmushi yayi ya juya yace "Toh Ameen" duk wannan abinda suke Ajiddeh na kallon su kuma tana ji, ya koma gun Batuul ya d'ago kanta yace "Oya ga chips Maman twins" hararansa tayi ta fada kansa ta shagwabe murya tace "Ni Allah bana so" dariya yayi ya dauki chip daya yace "toh na daina, bude bakin" ba musu ta bude ya d'an gutsura k'adan ya saka mata sauran a baki. Mikewa Ajiddeh tayi ta fice daga waiting room din ba tare da ya lura da hakan ba, haka yayi ta ba Batuul chips din har tace ya isheta, wayarsa ya shiga ring ya fiddo ya ga sadiq ne, mikewa yayi ya dagota yace "Sadeeq na jiranmu" sai a sannan ya kalli inda Ajiddeh take ya ga ba ta, waige waigen inda xai ganta ya fara yi amma bai ganta ba, yana rike da Batuul suka fita.
[11/15, 11:14 AM] ‪+234 810 957 2036‬: 💖💝BATUUL💖💝






80






By phartiemarhk






Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*






Suna cikin tafiya ta tsaya, ya juya yana kallonta yace "What?" Murmushi ta k'irk'iro ganin irin kallon da yakeyi mata tace "Am fine", kallonta yakeyi har lokacin yace "are you sure? Ko dai ya fara?", da sauri ta shiga girgiza kai tana sake wani murmushin da kana gani kasan ba na gaske bane, kyaleta yayi badan ya yadda ba ya tallafota jikinshi tareda kwantar da kanta kan kafad'unshi yace "okay let's get going Sadiq is waiting", suna d'ago kai suka hango Sadiq na waving musu da wide smile shimfid'e a fuskanshi, ya tara gashi a kanshi sai ya k'ara mishi kyau, ido ya wara ganin Batuul yace "Batuulan Aunty is that you?", baki ta zumb'uro mishi tayi raurau da ido tace "Its Batuul ba Batuula ba", dariya ta bawa Sadiq yace "kin ganki kuwa?, Yaa Abu mey kake bata haka, you can see her glow from a far, she has changed tayi kyau sosai", harara Abu ya sakar mishi tareda turo mishi trolley d'in yace "Let's get going, you are tiring her da unending surutunka", tafiya Sadiq d'in ya fara yana dariya yace "Its okay ba sai kin fad'amin yanzu ba, we will meet ltr ko Batuulan Aunty, rabu da Yaa Abu, he doesn't know", ya fad'a mata yana kashe mata ido d'aya, tsaki Abu yaja yace "hand me the key, in ka gama surutun ka samemu a gida", dariya kawai Sadiq yayi bai sake cewa komai ba, a mota suka tarar da Ajiddeh, sai lokacin ya tuna fa suna a tare tun lokacin da ta bar wajen, da unreadable expression d'in dake fuskanta ta kalleshi ganin yanda yake riqe da Batuul tace "bari in dawo baya in zauna da ita, you can sit here ta fad'a tana k'ok'arin barin gaban motan, kai ya kad'a mata yace "No you can stay back babu komai, she will be fine", shiru Ajiddeh tayi tana kallon yadda yake handling Batuul d'in har ya zauna ya gyara mata zamanta, a hankali ta janye idonta a kansu tana jin wani abu har cikin ranta ta maida kallonta gaba jin mey Sadiq ke fad'i, da k'yar ta bud'e baki tace "Handsome you said?", hannu Sadiq yasa a cikin gashinshi jin dad'in sunan da Ajiddeh ta k'irashi da yana murmushi yace "Naga ne kun canja Batuul totally, tayi wani irin fresh da zuwanta for months, ko nima in zo ne a rik'a bamu abinda ake batan tare" kallon Batuul dake d'an mutsu mutsu Abutturab na mata magana k'asa k'asa tayi ta mirror sannan tayi maza ta d'auke kallonta daga kansu tayi murmushi tana kallon Sadiq, ya kad'a kai yace "gaskiya UK ya karb'eta, haka sukayi ta hira yana tuk'in, suna cikin hiransu sukaji kukan Batuul d'in, a hanzarce suka juyo ganin mey ke faruwa, rungume suka ga Batuul jikin Abutturab sai kuka take tana riqe da cikinta, da sauri Sadiq ya ja brake gefen titi yace "What's wrong with her Yaa Abu ko mu k'arasa asibiti ne if she isn't feeling well?", kasa magana yayi sai alama da yayi mishi da yaci gaba da driving, Ajiddeh ce tayi k'arfin hali tace "Sadiq let's get going, she needs rest", hakan akayi Sadiq ya tada motan sukaci gaba da tafiya, Batuul kam sai kuka takeyi tana riqe da cikinta duk ya rikice ya rasa ya zaiyi, tunda Ajiddeh taga an d'auki hanyan gidansu Abu jikinta yayi sanyi gabanta ya rik'a fad'uwa, taso a kaita gidansu ko kuma gidanta da bata tab'a sanin ya yake ba dan ba tab'a zuwa tayi ba amma tasan yanzu its already late, horn Sadiq yayi bakin k'ofa yana jira a bud'e gate daidai nan Ajiddeh ta d'ago kanta jiki a sanyaye tana kallon cikin gidan, tun Sadiq bai gama parking ba Abu ya bud'e k'ofa ya fita, duk tsayawa sukayi suka bishi da ido ganin yanda ya rikice gaba d'aya, jiki a sanyaye ta sauk'e idonta, Sadiq ne da yayi noticing uneasiness da restlessness d'in dake tattare da ita yayi maza ya bud'e ya zagayo ta gefenta ya bud'e mata k'ofa da murmushinshi mai kyau yace "Muje ko Anty?", haka ta janyo handbag d'inta ta fito daga motar, Sadiq yace "Let me help with d bag Ma'am", wai ko ta d'an saki jiki, batace komai ta mik'a mishi jakar ya shiga gaba ta biyoshi a baya, da sallama ya Abu ya shigo parlour dake d'auke da wani ni'imtaccen k'anshi da sanyi kamar kullum, Ammah dake zaune cikin hanzari ta mik'e tana kallon yanda Batuul d'in ke jin jiki tace "Subhanallah, Abu yanzu haka yarinyar nan ke wahala amma kaje ka zauna kaqi dawo min da ita, wane irin hali ke gareka wai?", kasa cewa komai yayi sai kwantar da ita da yayi kan doguwar kujera, ya zauna daga gefenta ya dafa kanshi da duka hannayenshi biyu, Farida ce ta sauk'o a guje tana fad'in "Ammah na fad'amiki haka yakeyi mata kullum, koh ranan fa tana bacci kawai cikinta ya fara ciwo, Ammah mu kaita asibiti Dan Allah kar wani abin ya sameta, am with a key", ta fad'a tana k'ok'arin jin d'umin jikin Batuul, Ammah ce ta dubi Abu tace "Abu ba magana nakeyi maka ba, tun yaushe ta fara ciwon?", jajayen idanunshi da suka rine ya d'ago saura kad'an hawayen dake cikinsu ya zubo, ji kawai Ammah tayi ya rungumeta, cikin sanyi yake cemata "Ammah plss help her, bazan iya jure rashinta ba I need her to get well Ammah, kuyi wani abu nima bansan mey ke damunta ba, I don't want to lose her, Plsss Ammah", daidai nan Ajiddeh da Sadiq suka shigo parlour, kallo

1 Comments On BATUUL
avatar
hafsat-9-3

12 months ago

Reply

Nice book

Please Login or Register in order to submit comment