Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ke kikkifta ido, ganin irin dariyar da suke ya fusatar da Ajiddeh tayi bayansa da gudu xata fixgo Batuul, tura Batuul yyi bedroom dinsa da sauri shi ma ya shiga ya rufe, ae tsit kke jin Batuul don ta tsorata ssae, shi kam bae fasa dariyar da yake ba, Ajiddeh kam dakinta tayi hawayen takaici na bin kuncinta tana da ta sanin kallon potatoe'n, kallon Batuul Abuturrab yyi bayan ya gama dariyarsa ya hade rae yace "Xaki yi spelling Doom yau, ba dae dariya kike mata ba" kmr xata yi kuka tace "Wllh ni ban sani ba... Sharrin shaidan ne" sae ga hawaye na bin kuncinta, wani sabon dariyar Abuturrab ya shiga yi, Batuul ta durkushe wajen a sanyaye tana kallonsa don ita har ga Allah tsoron Ajiddeh take, ya shafa kansa yace "Ki tashi mu je ki bata hkuri idan ba hka ba ta kora ki daga gidanta yau" mikewa tayi tace "Toh" ya mike shi ma ya nufi kofa tana biye da shi a baya, yana bude kofan ya juya da sauri yace "Gata nan" a guje Batuul ta juya xata bar wajen cikin rashin sani ta take dogon gown din jikinta, ji kake tim a k'asa ta fadi, wani kara ta saki ta fashe da kuka tana kiran Anty, ya durkusa da sauri ya d'ago ta yana kallon kafarta yace "Ohh sorry!" Kuka take tana yarfe hannu don ji tayi duk jikinta na mata ciwo, ae fa nn ya rikice yana dube duben ko ta ji ciwo, gefen gado ya xaunar da ita yace "Yhu c, me ya kai ki sa kayan da ya fi ki tsayi" kukan ta kawae take bata ce komae ba idonta a runtse, ya galla mata harara yace "Ina ke maki ciwo?" Kneel dinta ta nuna masa, ya daga gown din jikinta idonsa ya sauka kan smooth fresh long leg dinta, k'asa dauke idonsa daga cinyarta yyi don har cinya ya kai rigan, ita kam jin ya daga mata riga kuma bae ce komae ba yasa ta bude ido, da sauri ta janye kafarta daga gabansa ta sauke riganta, ji yyi kmr ya nutse don kunya amma da yake gogagge ne, wayancewa yyi ya mata mugun kallo yace "Don kin samu ina tofa maki addu'a" sae kuma ya mike yace "Idan kin ga dama ki tashi mu je ki bata hkuri" a hnkli ta mike ganin ya fara tafiya ta bi bayansa, suna isa kofa ya juya yaga dingishi take, yace "Meye hka?" Kmr xata yi kuka tace "Ciwo yake min" fixgo hannunta yyi suka koma dakin ya xaunar da ita gefen gado snn ya nufi gaban mirror ya dauko man xafi ya dawo, ya wani hade rae shi a dole Lol, nan dae ya daga mata rigar kuma ya bude man ya diba, ya fara shafa mata a gwiwan, runtse ido tayi jin xafi ta dafa kafadarsa tana kiransa, kallonta kawae yake har ya gama snn ya mike ta bude idonta, ganin ya nufi kofa ta mike ita ma ta bi bayansa da sauri, a hnkli ya murda kofar Ajiddeh Batuul na boye bayansa, xaune ya sameta ta cika tayi fam tana girgixa kafa, yace "Babe!" Wani wawan kallo ta jefa masa, ya gintse dariyarsa ya juya yana kallon Batuul don yasan bata san tare suke ba, a hnkli yace "Baxa ki bata hakurin ba" Batuul kmr xata yi kuka tace "Don Allah Anty kiyi hkuri ni ba da ke nake dariya ba fa" mikewa Ajiddeh tayi da sauri tace "Ohh biyo ni daki kika yi don kin isa?" Batuul tace "A'a kiyi hkuri ni ban san xa ki ji haushin dariyar ba" Ajiddeh tace "Ae sae kin gaya min me kike ma dariya xa ki kwana gidan nn yau" shiru Batuul tayi, hkn yasa Abuturrab ya fara dariyar da yake gintsewa yace "Ta fa baki hakuri Anty" Ajiddeh ta fashe da kuka tace "Aliyu ni na gaji da wnn walakancin naka, na gaji" dariya kawae yake yace "Babe ita fa ba potatoe'n da kika ci ya bata dariya ba, aman da kika tafi kitchen kike yi shi ya sa ta dariya, ko ba hka ba Batuul" a hnkli Batuul tace "Ehh!" Ajiddeh ta kuma rushewa da kuka kmr an aiko mata da sakon mutuwa, me Abuturrab zae yi bn da dariya, dariyar da bae taba yi ba a rayuwarsa, ita kanta Batuul hadiye dariyan take tana lekan Ajiddeh.
[8/22, 14:47] Umar Dalha: πŸ’–πŸ’BATUULπŸ’–πŸ’

50

By phartiemarhk

Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*

Had'iye dariyarshi yayi ganin kukan da Ajiddeh keyi kamar wacce aka daka ya juyo yana kallon Batuul da tayi saurin gintse dariyarta ta sunkuyar da kai, hannunta ya kamo ya dawo da ita gaban gadon Ajiddeh ya hade rai yace "sake bata hakurin", a hankali Batuul tace "kiyi hak'uri" jajayen Idonta da suka rine ta dago tana mata wani mugun kallo, kallon Batuul yayi yace mata "Get out", kamar munafika ta fice daga d'akin, tana fita ya dawo bakin gadon ya zauna tareda janyo Ajiddeh jikinshi, kukan ta sake fashewa da, bayanta ya shiga bubbugawa yace "Hey babe, tace fa ba dake take ba, beside meye Na zuwa da yin amai bayan har ta ganki kinci, ai cemata zakiyi ta zubo miki ma tunda gidanki ne" ya k'arashe maganan yana murmushi, d'ago kanta tayi tana hararansa da rinannun idanuwanta a fusace tace "toh kai dariyar da kake yi ta me? Memakon kayi mata fad'an abinda tayi shine ka biye mata kuna min dariya don walakanci koh", har lokacin yana murmushi yace "its okay yanxu ai na sata baki hakuri, i will deal with her next time she tries anything stupid thing" d'ago kanta tayi ta sake kallonshi , kai ya kad'a mata yace "i mean it wife, kin ma yi sllhn kuwa" shirun da yaji tayi yasashi gane batayi ba, yace Mata "tashi kije kiyi sllh, I will b back right away" daga haka ya mik'e ya fita

Batuul na fita ta wuce d'akinta, kan gado ta fad'a taci gaba da dariya, sai da tayi mai isarta tukunna ta gyara kwanciyarta kan gadon, nan bacci ya d'auketa, bata dad'e da kwanciya ba taji k'iran sllhn wayarta Na bugawa, a kasalance ta tashi dan ba isanta baccin yayi ba sannan baccin bayan la'asar ne, da k'yar ta mik'e ta kashe, ta Shiga toilet tayi alwala, abun sllh ta shimfida ta hau kai, bayan minti biyar ta tashi tayi sllh magrib, nan ta zauna har akayi Isha tayi, daga nan ta mik'e tayi shirin Kwanciya, wanka tayi ta fito ta saka kayan baccinta riga da dogon wando, snn ta koma kan gadon ta kwanta bayan ta rufe k'ofar d'akin, tafi awa d'aya kwance baccin yaqi xuwa mata, babu abinda takeyi sai tsaki, tashi tayi ta janyo system d'inta, in to the bad lands ta kunna zataci gaba da kallo, tura k'ofan d'akin akayi, a tsorace ta d'ago kanta ganin waye , mamaki ne ya kamata dan tasan ta rufe k'ofarta, toh mesa zai wani ce ta dinga rufe k'ofarta bayan yasan he have access to it, d'an murgud'a baki tayi ta sunkuyar da kanta taci gaba da kallo, shigowa yayi ba tareda yyi bother ya kunna wutan d'akin ba, a bakin gadon ya tsaya, yace "Abinci kike jira a siyo maki da baki sakko neman dinner ba, or are yhu afraid of my wife" zumb'uro baki tayi cikin duhun ganin baya ganinta, a ranta tace shi wannan mutumin ina ruwanshi ne da cin abinci na, jin tayi shiru yasa ranshi ya b'aci, a tsawace yace "ba magana nake maki ba", tsorata tayi ba tare da ta shirya ba ta rufe system din ta mike ta yi kneel kan gadon bata ce komae ba, fixgota yyi tayi 'yar kara ya dago ta da sauri tun kan ta kai kasa, tsayar da ita yy gabansa ya ciro wayanshi a aljihu ya haska fuskanta, a hankali tace "bana jin yunwa" d'an k'aramin bakinta dake motsawa yabi da ido, hka kawae gabansa ya shiga faduwa yana kallonta, ita kanta faduwa gabanta ke yi a lkcn, duk kamshin turarensa ya cika ta, kashe wutan wayar yyi ta juya a hnkli xata bar wajen ya fixgota ta fado kansa, runtse ido tayi a tsorace tace "Ya Abuu ni bna jin yunwaa" D'ago kanta yyi amma taki bude idonta, kallon lips dinta kawae yake cikin duhun ko kiftawa bae yi, murda kofar dakin aka yi, ya tura ta da sauri ya koma baya, ita kam rawa jikinta ya dau yi, da sauri ta haye kan gado, ya kunna fitilar wayarsa, Ajiddeh ce ta shigo ta tsaya tana kallonsa tace "Wae me kke a nn Babe?" Tana masa tambayar tana kallon Batuul da tayi kmr me bacci, Abuturrab ya juya yana kallon Ajiddeh yace "Erm dama amma ce ta kira wae a bata shine na shigo naga tana bacci" hade rai tayi tace "Toh ita bata da waya ne da sae kai xa ace ka bata" ficewa yyi daga dakin ba tare da ya tanka ta ba, sae dae tunawa da yyi ba mutunci gare ta ba yasa ya tsaya daga bakin kofa yace "Mu je" tsaki tayi ta fito daga dakin. Batuul ta sauke ajiyar xuciya ta mike ta rufe kofarta da key ta dawo ta kwanta.
Washegari Batuul na gaban mirror xaune tana shafa lotion don fitowarta daga wanka knn, taji ana bude kofar dakin, turo baki tayi ta jawo hijab da sauri ta sa, yana shigowa yyi mata kallo daya yace "Daga yau, duk safiya kika tashi kafin kiyi shirin sch ki sakko ki tsaftace gidan gaba daya, snn breakfast da dinner ke za ki dinga yi ba kuma wa cikin ki kadae ba, is dat clear?" Shiru tayi tana kallonsa a hnkli tace "Idan ina da lecture da sassafe fa?" Ya galla mata harara yace "Sae ki tashi da asuba!" Juyawa yyi ya fice, ji tayi kmr ta fara kuka, yaushe ne xata tsaya hada breakfast a gidansu tana da lecture da safe, a sanyaye ta mike ta ciro doguwar riga na kanti pink da adon blue ta sa ta fito, bbu kowa falon ta nufi kitchen, breakfast ta hada cikin kankanin lkci na fried Irish da soyayyan kwae sae ruwan Lipton, ta jerasu kan dinning, ta koma kitchen din ta wanke utensils din da ta bata ta gyara kitchen din ta fito, falo ta shiga nan ma duk ta share tayi mopping ko ina, falon ya dawo yana kyalli, dakinta ta koma, ta kuma shiryawa tayi rolling kanta da plain mayafin kayan jikinta blue, ta shafa chappette a lips dinta ta feshe jikinta da turare, ta fiddo flat shoe dinta ta sa, sannan ta dauki jakarta bayan ta sa wayarta a ciki ta fito falo, har lkcn bbu kowa falon, kallon agogo tayi taga har tara ya kusa, duk taji kmr ta rusa kuka to ta ina xata fara ce masa xata tafi suna dakinsu, ta kusa minti goma tsaye falon wata xuciyar tace kawae tayi wucewarta da kafa tunda bbu nisa sosai, amma ta kasa aikata hakan sbda tsoronsa, hawaye na ya cika idonta sanin da wuya ta samu 1st lecture, tara dai dai ta koma sama ta shige dakinta ta fada kan gado ta dinga rusa kuka kmr yarinyar, tara da minti sha biyar Abuturrab ya fito har xae sauka downstairs sae kuma ya nufi dakinta, har lkcn tana kwance tana kuka, ya karasa cikin dakin ya tsaya daga bakin gadon yana kallonta da mamaki yace "Me ya faru" kauda kanta tayi taki basa amsa, yace "Ke kina da hnkli kuwa ina maki magana kina kauda kai" wani sabon kukan ta fara, ba tare da yyi wani tunani ba ya xauna gefen gadon ya d'agota yana kallonta da mamaki yace "What's that, what happen?" Still taki cewa komai bata kuma fasa kukan ba, ya dafa kafadunta yace "Talk to me mana, an maki wani abu ne wae?" Ganin ynda ya tsare ta da ido yasa ta shiga girgixa masa kai sae dae bata ce komae ba, jawota jikinsa yyi ya dago kanta ya hade rai yace "Idan baki bude baki kin min magana ba I will slap yhu" ta sauke idonta kasa wani sabon hawayen ya xubo idonta a hnkli tace "Am late, nayi missing 1st lecture" kallonta ya tsaya yi ko kifta wa bae yi, ya dake yace "What made yhu late?" Shiru tayi bata ce komae ba, yace "Yhu are not deaf fa, ansa me now" a hnkli tace "ko ba kai bne!" Bude idonsa yyi yace "Ni?" Kauda kanta tayi ya juyo da ita da sauri ya hade rae yace "daki daya muka kwana da xan sa ki latti? Ohh har kin kirkiro wani karyar da xa ki ma Ammah ki hada ni da ita koh, wae yhu are late! Did yhu sleep in my room ne xaki ce yhu are late or tunda kika tashi yau kin tsinana mu da wani abu ne a gidan nn, No of course u are just busy sleeping" sake kauda kanta tayi ita ma ta hade rae, ya juyo da kanta yace "Kika sake dauke min kai I will slap yhu wllh" rufe ido tayi da sauri, yyi shiru yana kallonta, sauke idonsa yyi kan lips dinta, hka kawae gabansa ya shiga faduwa, ita kanta Batuul faduwa gabanta ya shiga yi idonta rufe, without thinking twice kawae ya samu kansa da kai lips dinsa nata, a tsorace ta bude ido jin soft lips dinsa a nata, dai dai lkcn da suka ji an bude kofa, mikewa yyi da sauri ya k'asa kallonta, ya nufi kofa, suka kusan cin karo da Ajiddeh bakin kofar xata shigo, ae da sauri ya tsotse tsarabar chappette din da ya yo a lips dinsa, ta wani hade rai tace "Wae me kke dakin nn tun daxu Aliyu?" Daburcewa yyi da farko sae kuma ya wayance daga baya yace "Erm naga lkci ya wuce bata fito ba shi yasa na shiga in ga abinda take, nd nd.. I found her crying" Ajiddeh tace "Gskya idan kana son xaman lfya Aliyu ka daina shigowa dakin nn, bana so, idan tana bukatan abu ne ta jira idan muna falo ta sauko ta same mu" barin ta yyi a nn yyi ficewarsa, ta juya tana kallon Batuul ta galla mata hararan tsana tace "Munafuka kawae, 'yan maula" daga hka tayi ficewarta, ko kadan Batuul bata san me Ajiddeh ta gama cewa ba don har lkcn gabanta bae bar faduwa ba ji take kmr lips dinsa na nata har lkcn. Ta kusa minti sha biyar xaune sae gashi ya dawo, daga bakin kofa ya tsaya ba tare da ya kalleta ba yace "Idan kin ga dama ki fito driver ya kai ki sch" daga hka ya fice, mikewa tayi a sanyaye ta dauki jakarta ta d'an gyara fuskarta kuma snn ta fito.
[8/22, 14:47] Umar Dalha: πŸ’–πŸ’BATUULπŸ’–πŸ’






51






By phartiemarhk






Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*





A dinning d'in ta ganshi zaune yayi serving kanshi breakfast din da ta yi yana ci, Ajiddeh na daga gefenshi tana ta kumbure kumbure, tana ganin Batuul ta watso mata wani mugun harara, ko kallonta Batuul batayi ba ta karaso cikin falon ba tare da tace musu komai ba ta wuce, har ta kai bakin kofa idon shi na akanta, sai da yaga fitanta snn ya maido da hankalinshi kan Ajiddeh da ta zuba mishi ido rai a b'ace tana kallon yadda yake kallon Batuul, yasan driver bazai tafi ba sai ya jirashi ya fito dan yana son bata wayanshi in ta tashi a k'ira a d'auketa kuma ya bata kud'i, yi yayi kamar bai San kallon da take mishi ba yace "so you ain't eating har yanzu, kilan zaki dafa ne ko kuma sai na tafi zaki faraci ta shigo ta ganki kinaci kije kina amai koh", ya karashe maganan yana murmushi, sake hade rai tayi tace "kaga nifa wulakancinka ne banaso Aliyu, koh jiya a gabanta ka dinga min dariya, ko ta rainani ai kai ka jamin, bare ma bata isa tayi hkn a gidana ba", bai ce mata komai ba yaci gaba da cin abincinsa yana murmushi, sai had'iyar miyau take tana kallon yadda yake cin abincin, duk yadda akayi abincin nada dadi ganin yadda yake ci sannan ga k'anshi duk ya gama bad'e ta a gun, kallonshi tayi rai a b'ace tace "magana fa nayi maka amma kaqi kulani sai tunkud'a abinci kakeyi kamar wanda bai tab'a ci ba", kallonta yayi da idanunwanshi dake piercing zuciyarta yace "ko kin taba dafa irin wannan ne a gidannan da kike cewa inaci kamar ban tab'a ba", baki ta turo tace "nifa duk ba wannan ba, ai abinci ga ka gashi, baby ni abinda na tambaya tun jiya, I urgently need it, gashi har ka shirya bakace komai ba fa", cike da shagwaba ta kare maganar, shi kam har ta gama maganan bai ce mata komai ba, da alama santin chips d'in Batuul yasashi kasa magana, ran Ajiddeh ne ya fara b'aci, tashi tayi a fusace zata tafi ya riko hannunta da sauri, ya dawo da ita ya zaunar kan dinning chair din, kallonta yayi da murmushi a fuskanshi yace "keh bakisan in mutum na cin abinci bai son damuwa ba, da kinci abincin kema nasan all your worries will b cleared away" wani irin kallo ta mishi yace mata "tunda bakici je d'auko min cheque d'ina a sama", da murna ta mike ta haura sama, bata jima ba ta sauko rike da cheque book dinshi a hannunta, har saida ya gama cin abincin tukunna ya janyo ya rubuta mata amount din da take bukata, murna ta dinga yi kamar mey, har bakin kofa ta rakoshi tareda yi mishi peck a kumatu sannan yayi mata sallama ya tafi.





Inda Batuul taga driver na tsaye nan ta nufa, da kanshi yazo ya bud'e mata k'ofa tareda ce mata "Morning Ma'am" kai ta gyad'a mishi ta shiga ta zauna ba tareda ta iya ce mishi komai ba, ganin bai tada motar ba yasa tace mishi "am getting late, let's get going" babu musu ya tada ya d'au hanya, har suka isa school ranta b'ace yake, tasan ta riga da tayi missing first lecture, har gaban department dinsu ya kaita, kamin ya fito ya bude mata kofa ta bude ta fito, wucewa tayi lecture hall ta tadda ana lecture , shiga tayi ta zauna ba tareda ta cewa Kowa komai ba, Aisha dake gaba sai kallonta takeyi haka ma Samantha, sai da ta zauna tukunna suka juyo suka ci gaba da sauraren lecturer, batafi 45mins da shiga ba lecturer ya gama ya fita, a tare Samantha da Aisha suka yo wajenta, Aisha ce ta fara ce mata "don't tell me har kin fara latti daga farawa", kamin tayi magana Samantha ta karb'e da cewa "Hey love you were late today, and you missed almost two lectures today, you okay?" , hawayen da take ta kokarin maidawa ne ya shiga zubomata, a tsorace su Samantha ke kallonta ganin yadda take hawaye, janyota Aisha tayi ta rungume, Samantha ce tayi mata alama da ta jata suyi waje, sai da sukaje inda babu mutane tukunna suka zaunar da ita, kuka sosai ta shiga, babu abunda sukeyi sai rarrashinta, har suka gaji suka rabu da ita, sai da tayi mai isarta tukunna tayi shiru dan kanta, hawayenta tashiga gogewa da hannu sannan ta dubesu tace "what were we thought, I mean d topic", Aisha dan haushi ko kallonta batayi ba, Samantha ce tana kallonta tace "It seems you are hungry, let's go and get something to eat, am also famished" kallon Aisha tayi taga ta had'e rai, jiki a sanyaye tace "Aisha cikina ke ciwo", cikin sanyi Aisha tace "toh Fatima koh baki d'aukemu komai ba ai kinsan bazamu cutar dake ba, ciwon ciki dai ko clinic ai sai muje a baki magani, amma kinzo late we were worried sannan kuma kiyita kuka kiki bamu ansa", Samantha dai baki ta bud'e tana kallonsu, sai da taji sunyi shiru sannan ta dubi Aisha tace "She said what, what's d problem?", a takaice Aisha tace "stomach ache", ido Samantha ta xaro tace "then?, we should be in the clinic, let's rush her", kai Batuul dake zaune ta girgiza tana kallon yadda Samantha ta rud'e tace "I will b fine dear, you shouldn't worry, it usually does, I will take my medication when am back home", da rashin gamsuwan abinda ta fad'a musu Aisha ta girgiza kai tace "Fatima bafa cutar dake zamuyi ba, nanfa kika zauna kina kuka amma kice wani wai you are okay, how does that even makes sense", ta k'arashe maganan ranta b'ace, a hankali Batuul ta kamo hannunta ta zaunar gefenta tace "dagaske nake ya daina, kinga Kuma inada magani na a gida, ba lallai school clinic suyi min prescribing irinshi ba" sai yanxu Aisha ta yadda ta fad'awa Samantha yadda sukayi, littafin dake hannun Samantha Batuul ta ansa tana Kallo tace "Did I miss so much", Kai Samantha ta girgiza tace "you got no worry, I will explain everything", giranta d'aya Batuul ta d'aga, Samantha na kallonta ta fashe da dariya tace "yeah you gat my back" tanayi tana kad'a kai, dariya su dukan suka sa, Samantha tace " SHIT!,But girl you scared me, you shouldn't cry again when am there, I have this terrible phobia of tear, it doesn't even have a name", dariya ta basu, Batuul tace, "not in my weirdest dream, its not happening again I promise" ta k'arashe maganan tareda mik'ewa dan taga duk jikinsu yayi sanyi, sai da ta mik'e ta fara tafiya tukunna ta juyo ta dubesu tace "who is joining me for a cup of frapuccino", a tare suka mik'e suka biyota, suna isa wajen taji cikinta ya k'ulle, a hankali ta fara d'aga k'afarta ba tare da ta bari sun gane, har suka samu waje suka zauna cikin bai barta ba, k'aryan da tayiwa su Aisha ne ya dawo mata, dama ance babu kyau k'aryan ciwo, d'an k'aramin tsaki taja dan tasan period d'inta can come anytime tunda har cikinta ya fara ciwo, waiter dake aiki a wajen ne ya iso wajensu, ya tambayasu abunda xa a kawo musu, Samantha tace "Serve me caramel", juyawa yayi ya kalli Aisha yace "Ma'am what would you like to have?" , kallonshi tayi tace "Hazel nut sugar free and and chicken lasagne", daga haka ya juya yana kallon Batuul da taketa tunani hankalinta ma baya wajen, sai da Aisha ta d'an tab'ota tukunna ta d'ago tana kallonsu, tambayanta yayi itama me take so, tunda har cikinta ya fara ciwo in tasha abu mai zak'i wahala ne zai k'aru mata gashi batada magani, ita pad d'inma bata dashi, tunanin hakan yasa ta hawaye da tayi k'ok'arin maidawa, jiki a sanyaye tace mishi "peppermint sugar free", da haka ya tafi yaje kawo musu, baifi minti biyar da tafia ba ya dawo riqe da tray, ajiyewa kowa abinda yayi ordering yayi sannan ya bar wajen, sai da suka kusa gamawa kanta a k'asa taji anyi musu sallama, bata d'ago ta Kali mai sallaman ba amma tasan namiji from his voice, kujeran dake gefenta taga yaja ya zauna, ji tayi yana cewa "This isn't fair, you girls enjoying without an invitation?", Samantha ce tace "Hey lemme order one for you, ta juya zata k'ira waiter, hannu ya d'aga mata alamar surrender yace "Hey No Thank you, am okay", kallonshi Aisha tayi da mamaki ganin baya tab'a kula matan dake binshi ma amma yanzu shi da kanshi yake zuwa inda suke, a hankali Aisha tace "You sure?", kai ya gyad'a mata tareda da yi mata murmushin shi mai kyau, kallon Batuul yayi yace "Sai dai in wannan da bata magana xata bani nata, I will gladly take it", Batuul batasan ma sunayi ba dan hankalinta ma baya kansu, kud'in frapuccino da zata biya ma bata dashi a yanzu haka da take zaune, tunaninta sam bai kawo bata da kud'i ba har sai da ta tuna ba da jakan jiya ta fito ba kuma yau

1 Comments On BATUUL
avatar
hafsat-9-3

12 months ago

Reply

Nice book

Please Login or Register in order to submit comment