Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

karaso, suna Karasowa wani dake xaune gefen Shaheed yace "Hey Aysha!" Aysha ta tsaya tana murmushi tace "Hei Usman how you, how's lecture?" Usman yace "Alhmdllh, dat gal! Is she ur frnd? So haughty of her!" Sae a sannan Shaheed ya d'aga kai yana kallonsu, Batuul ya bi da kallo don ko tsayawa bata yi ba ta ci gaba da tafiyarta, ya lumshe ido ya bude ya ci gaba da karatunsa, Aysha tayi dariya tace "No, no, not at all, she's not! just dat ba ku saba bane, Well! We'll chat later Usman, bye for now" yace "Ayt! Take care of ur self bae" dariya tayi ta bi bayan Batuul da sauri. Xaune ta sameta waiter dake aiki a wajen yana tsaye kusa da ita yana tambayar me xae kawo mata, tace "Just caramel bun and frapuccino" mutumin ya juya yana kallon Aysha yace "yhu ma'am?" Tace "Same also!" Juyawa yayi ya tafi kawo masu. Aysha tace "Shine kika tafi kika bar ni koh?" Batuul ta kalleta murmushi dauke fuskarta tace "Yea naga yhu were busy ne" Aysha tace "Ayt, amma ko gaisawa ne ki dinga yi da mutane don ku saba mana" Batuul bata ce komae ba sae juya wayar Abuturrab dake hannunta take, Aysha ta ce "Kawo in sa maki digit dina, it's gud ace mun yi exchanging" mika mata wayar Batuul tayi ta karba ta kunna, "Woaww is this ur sister on the screen, kai she's so beautiful wallahi, ya aka yi ke baki yi hasken ta ba" hade rae Batuul tayi ba tare da tasan ta ma yi hakan ba, don ko lura da hoton screen din ma bata yi ba kawae ta fito da wayar daga jaka ne don ta duba agogo, Aysha bata damu da shirun da Batuul tayi mata ba tayi ta koda kyan Ajiddeh, daga karshe ta sa mata nmbrta tayi mata saving ta mika mata, Batuul na karban wayar ta maida jakarta snn ta maida hankalinta kan abincin da aka dire masu gabansu, ta riga Aysha gamawa snn ta fiddo wayar don hoton ya tsaya mata a rai haka kawae, kare ma hoton kallo kawae take, bata san lkcn da ta ja tsaki ba Aysha ta kalleta tace "Ya dae" yake tayi tace "Naga time ya wuce ne, baxa kiyi sllh ba?" Aysha tace "No bana yi" Batuul bata ce komae ba ta shiga gallery duk tayi mark din hotunan Ajiddeh dake wayar har na screen din ta watsa su a kwandon delete. Tana gama hakan ta ja tsaki ta fiddo kudi jakarta tace "Tambayar mana bill Aysha" ita ta biya kudin duk yanda Aysha ta so biya bata yrda ba, suka mike don komawa Dept.



Karfe hudu da wani abu suka fito daga lecture, Aysha tace "kinga tare da aunt dina xa mu wuce tana jirana, Bus xa ki hau ko taxi?" Batuul tace "No xa a xo daukana ne daga gida" Aysha tace "Ayt sae gobe, don't forget Karfe 8 muke da lecture fa" Batuul tayi murmushi tace "Insha Allah ki gaida aunt din ki" Aysha tace "Xata ji, nima ki gaidar min da pretty aunt din ki, so fyn da ita ga gashi, ina nan xuwa wataran in ganta" dauke kai Batuul tayi kmr bata ji ba har Aysha ta bar wajen, waje Batuul ta samu ta xauna, ko minti goma bata yi a gun ba wayar jakarta ya shiga vibrate ta ciro, d'agawa tayi daga daya bangaren yace "Are yhu done for today?" Mikewa tayi tace "Yea!" Ya katse wayar, ta nufi inda tasan xata gansa. Sauke glass Abuturrab yayi yana kallonta, sae kuma ya fito ya bude mata back door sanin gaba xata taho kuma Ajiddeh na ciki, Ajiddeh ta bi sa da kallon mamaki baki bude taji kamar ta rusa ihu, don da kawae so tayi Batuul ta zagayo ta bude ta ganta a xaune sae ta ga ynda xata yi, meye haka Aliyu ke yi, abinda bae taba yi mata ba wae bude mata mota ta shiga, shine yake bude ma shegiyar nan, what have come over him haka, ita kanta Batuul tayi mugun mamakin abinda Abuturrab yyi sae kallonsa take, infact shi kansa sae da ya ji wani iri a lkcn, don bae taba yi ma wata 'ya mace haka ba apart from Ammahn sa, what's he doing, A hankali Batuul ta raba ta gefensa kanta a kasa ta shiga motar, k'asa komawa seat dinsa yyi ba tare da ya kulle mata motar ba duk da hakan ya so yi don ganin irin kallon da Ajiddeh ke yi masa, samun kansa yyi da rufe motar a hankali, snn ya juya ya koma seat dinsa, banda xufa babu abinda Ajiddeh ke yi cikin motar duk da Ac'n da ke kunne, Batuul tayi mamakin ganinta cikin motar sae a sannan ta gane me yasa yayi hakan sae ta ji ddi da bae bar ta taje gaban ba, does he really care haka dama, d'an murmushi tayi tana kallon Ajiddeh tace "ina yini?" Da kyar Ajiddeh ta Hadiye wani abu da ya tsaya mata a makogwaro tace "Lfya!" Abuturrab ya d'an sata kallonta kafin ya tada motar suka bar wajen, sae da ya fara biyawa domino's, yana isa yyi parking ya fito, Ajiddeh da ke cika har lkcn tana batsewa ta bude motar ta fito ita ma, Batuul dae ta bi su da kallo, kallonta Abuturrab yyi yace "No no ba sae kin fito ba kiyi xaman ki a mota" da sauri Batuul ta dauke kai tana kallon window ta gefenta tana danne dariyar da ke shirin taho mata, bae damu da halin da Ajiddeh ta shiga a lkcn ba na kunya ya bar ta nan yyi gaba abun sa ya shiga domino's din, bayan kusan 10 mins ya fito rike da kwalayen pepperoni pizza da ledoji har biyu me dauke da cold stone ice cream, yayi mamakin ganin Ajiddeh tsaye har lkcn kmr warce ruwa ya ci, ya bude back seat ya ajiye kwalayen hannunsa da ledoji snn yana kallon Ajiddeh yace "Shiga toh mu je" Batuul dae har lkcn waje take kallo tana murmushi. Da kyar Ajiddeh ta iya bude motar kamar mara laka ta shiga, shi ma ya shiga ya tada motar suka bar wajen, tafiyar minti goma yayi suka iso gida, yana gama parkin Ajiddeh ta fice tayi cikin gida kmr xata tashi sama, Batuul ta fito ta kwashi kwalayen, fitowa yyi shima ya fito da ledan ice cream din snn ya rufe motar ya fara tafiya, bin bayansa tayi har suka shiga falon, Ajiddeh na tsaye tsakar falon, Batuul ta ajiye kwalayen pizzan hannunta shi ma ya ajiye ice cream din hannunsa, kwashe kwalin da ice cream din gaba daya Ajiddeh tayi ta nufi sama don dama shi take jira a falon, Abuturrab ya bi ta da kallo yace "Hey! Guda daya fa kadae ne naki a wajen nan babe" ko kallonsa bata yi ba ta haura sama fuu, Batuul ta kauda kai tana murmushi, Abuturrab ya juya yana kallonta yace "Ohh dariya ma kike koh, ae ko xa ki tsaya da yunwa ko kuma ki shiga kitchen kiyi girki" yana kai wa nan ya haura sama, Batuul ta tabe baki ita ma ta haura sama, dakinta ta shiga ta cire kayan jikinta ta shiga bayi ta sakar ma kanta warm shower, ta jima a bayin kafin ta fito daure da towel tana goge dogon gashinta da karamin towel, bude kofar aka yi ta kwalalo ido ta tsaya cak gabanta na faduwa, Abuturrab ya shigo dakin, kauda kai yyi da sauri suna hada ido yace "Erm my.. my phone, ina wayata?" kmr munafuka ta nuna masa jakarta, ba tare da ya kalleta ba ya nufi jakar ya bude ya fiddo wayar, kunna wa yyi yaga blank screen sae wall paper bbu photon dake gaban screen din, kallonta yayi kafin ya shiga gallery, mamaki ya cika sa ganin wayam sae few photos dinsa da ya rage bbu na Ajiddeh ko daya, hade rae Batuul tayi sanin abinda yasa yayi still a wajen, ta ci gaba da goge gashinta ta nufi gaban mirror, bin ta yyi da kallon mamaki, ta ja kujera ta xauna tana ci gaba da goge gashinta, karasawa gun mirrorn yyi ya fixgota ya juyo da ita yana mata wani irin kallo yace "Yhu deleted my wife's pics from my phone" ta wani hade rae tace "Toh na sani ne, ko ba mistake bane" bude baki yyi yana kallonta, ta turo baki ta kauda kai, bae san lkcn da murmushi ya subce masa ba, yana kallonta a hankali yace "Me ya shigar dake gallery nah?" Ta bude ido tace "Mistake I said!" Kallonta ya shiga yi daga kasa xuwa sama, ta dauke kai fuskarta daure, bata ankara ba sae ji tayi ya fixge towel din jikinta, ta rike gam ta xaro ido a tsorace Tace "meye haka ya Abu" yana mata wani irin kallo yace "Mistake" ta bude baki xata yi magana sae gani tayi ya kuma fixge towel din, a rikice tayi kasa tace "Nashiga uku don Allah stop this" bin ta yyi kasan yace "Sae kin gaya min me hoton matata ya tsare maki a waya da kika goge" a rude tace "No plss, Don Allah kayi hakuri ban san...." Janye towel din yyi gaba daya ta kwala ihu yyi saurin jawota jikinsa ya hade bakinsu, daukewa ne kawae numfashinta bae yi ba lkcn, shi kansa sae da yaji wani shock a lkcn, ya lumshe ido a hankali ya shiga kissing dinta kamar xae hadiyeta.
[8/22, 14:49] Umar Dalha: πŸ’–πŸ’BATUULπŸ’–πŸ’





56











By phartiemarhk








Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*







Ba karamin rudewa Batuul tayi ba a lkcn, duk jikinta ya dau rawa sae tutturasa take tana neman kwace kanta amma ta kasa, gajiya tayi ta tsaya ganin ba saketa xae yi ba, banda hawaye babu abinda take, duk jikinta yayi sanyi, ko lura da halin da ta shiga bae yi ba don idonsa a lumshe suke, yakai minti biyar yana abu d'aya kmr wanda ya tuna abu ya xame bakinsa daga nata a hankali, sae dae ya kasa kallonta, kuka ta fashe da ta xame jikinta daga nasa tayi saurin janyo towel dinta ta rufe jikinta, bae bari sun hada ido ba ya mik'e ya fice daga d'akin da sauri, kuka sosai ta shiga yi bayan ya fita, takai minti goma tanayi daga baya ta mik'e da kyar ta koma toilet ta wanke fuskanta, vanity stool d'in ta jawo ta zauna jiki a sanyaye, kallon lips d'inta da ya koma ja ta tsaya yi jikin mirror, a hankali ta d'aura babban yatsan ta kai tare da lumshe ido hawayen dake makale idonta ya gangaro, bud'e ido tayi ta janyo man shafanta, jiki a sanyaye ta gama shafa man taje ta sako kaya, har ta gama ta kwanta jin lips d'inta take ba daidai ba, gashi bata daina jin taste din bakinsa a nata ba, lumshe ido kawai tayi ta kwanta.






Ajiddeh kam na xaune dakinta bayan ta watsar da kwalaye da ledan da ta shigo da, duk abun duniya ya taru yayi mata yawa, banda huci babu abinda take yi ita kadae, wannan wace irin jarabace aka turo mata gidan ta, anya ma kuwa zata iya ci gaba da yin wannan abinda Mummy ta fad'a mata, wai dan wulak'anci Aliyu har shi zai wani tashi ya zaga ya bud'ewa y'ar iskar nan k'ofa bayan ita ba yi mata yake ba, to me hakan ke nufi, fad'awa tayi kan gado tana maida numfarfashi, da tun farko tasan zuwansu Nigeria da Abutturab zai zama haka da bata barshi ya tafi ba, ko ita da taje ta dawo, wani hawayen bak'in ciki ne ya shiga zubowa daga idonta, ta mike xaune ta fashe da kukan takaici, ita kam ya xata yi da Batuul? wayanta ne ya shiga ringing, jawowa tayi da sauri ta kara a kunnenta, jin mai k'iran ya sata share hawayenta da sauri, daga d'aya b'angaren Mummy tace "Ajiddeh Jiddeh, jiddum fi khair ana, useki y'ar albarka, naga abin kirkin da kika turo, ba b'ata lokaci yanxu zan turawa su Zainab, daga can za a turo miki ba sai sun dawo gida ba, zamuyi maganan duka details d'in in suka iso", toh kawai ta iya cewa dan wani irin tuquqi da zuciyarta keyi mata, Mummy ce taci gaba da ce mata "kuma kici gaba da yi kamar kina son nata, dan komai yazo mana da sauk'i, ko meye ya sameta kinga baza ayi zarginki ba dan babu wanda yasan kina k'inta, shi kuma sai sun dawo d'in sai muji yadda nashi abun yake", tace "toh Mummy duk zanyi", da haka suka katse k'iran dan maganar ma wahala take bata, turo k'ofar d'akin yayi ya shigo, da ido yabi kwalayen da ice cream packs d'in dake zube a k'asa har wasu sun fara malalewa, tattarewa yayi yazo bakin gadon ya zauna, hannu yasa ya d'agota kanta yana kallon yadda idonta ya canja, "kina da lafiya kuwa, zaki d'ebo abincin kixo ki watsar dasu anan kamar a bola na tsinto kudin, kina ma da hankali kuwa?", zuciyarta ta shiga dannewa tasa hannu tana d'an murza kanta tace "Baby kaina ke min ciwo, har jiri jiri nake gani shiyasa ma kaga komai a k'asa, ba zubarwa nayi ba", kallonta yayi yana examining d'inta gabaki d'aya sannan yace "kin fad'amin? ko kuma kinada maganin sha ne", kai ta girgiza ta shige jikinshi tace "c'mon babe, kasan banso kana damuwa shiyasa ban fad'i maka ba, I will b fine, you don't worry", ta k'ara shige mishi jiki, hannu yasa kanta yana shafa gashinta mai d'an karan laushi ya lumshe ido sae dae ji yake kmr har lkcn bakinsa na cikin na Batuul, a hankali yace "tashi kici abinci sai ki kwanta", ba musu ta tashi ta janyo kwalin pizza, har ta bud'e ta d'au d'aya zata kai baki, ta kalleshi da wani irin murmushi fuskanta ta wara ido tace "babe", d'ago kai yayi ya kalleta tareda d'aga mata giranshi d'aya yana jiran jin mey zata ce mishi, "our Sister, bari inje in kai mata share d'inta, nasan she is famished, daga school ma take kaga dole taji yunwa", k'ok'arin mik'ewa tayi yasa hannu ya dawo da ita ta zauna tana kallonshi, murmushi yayi yace "rabu da ita, in tana jin yunwa zata sauk'o ta samarwa kanta abinci", kai ta shiga girgiza mishi zatayi magana ya sa hannu kan lips d'insa yace "shhhh, eat and get some rest, bakya jin dad'i you shouldn't bother, she will b okay", wani irin murmushi tayi murna fal ranta kamar tayi yaya, bata damu da ko yanaci ba, haka ta dinga tunkud'a abincinta, tunanin abinda ya faru tsakanin shi da Batuul kawai yakeyi yana kallonta don tun da yake kissing dinta bae taba samun natsuwa irin wanda ya samu gun Batuul yanxu ba, it was just amazing, lumshe ido yayi ya kwanta kan gadon Ajiddeh, gaba d'aya komai dawo mishi ya shiga yi a hankali, hotunan Ajiddeh dake kan wayar da ta goge ya tuna, baisan lokacin da wani slight murmushi yayi escaping lips d'inshi ba, then why did she delete the pictures ita da ba ma son shi take ba what made her jealous, wayanshi dake gefen Ajiddeh ne ya shiga ringing, zuciyanta ya bada sautin dam, ganin mey k'iran, jiki a sanyaye ta d'au wayan, wani zuciyan ke ce mata ta katse wayar dan ita tsoro takeji, kamin tayi abinda zuciyarta ke kissa mata ya bud'e lumsassun idonunshi, a tsorace ta mik'o mishi wayan ganin ya bud'e ido, tashi yayi daga kwance ya risina ganin mai k'iran ya karba wayar, a kunnenshi ya kara a nutse ya amsa da sallama yace "salamu alaikum, nda dubdo Ammah", amsa mishi sallamar tayi tace "Ya kuke Abu, yasu Hauwa'u", kallon Ajiddeh yayi sannan yace "suna lafiya Ammah, ya gida ya k'arfin jiki?", tace "Alhamdulillah, kana jina, kayan Batuul da aka turo yau zasu iso, dan haka in suka iso kaje ka karb'o su sannan sai inyi magana da ita, inaso in mata explaining abubuwan dake ciki da yadda amfaninsu yake, mik'amin Hauwa'u inyi magana da ita in tana kusa", Ajiddeh ya mik'awa wayan sai muzurai takeyi da ido don gaba daya hankalinsa ya tashi don bae san me Ammah xata ce mata ba, jiki a sanyaye ta karb'i wayan tasa a kunne, xuciyanta sai double flip yakeyi, sai da Ammah ta k'ira sunanta sannan ta amsa, a daburce kamar mara gaskiya tace "Na'am Ammah ina wuni", sau d'aya Ammah taji muryarta tun bayan aurensu da Abu, ba yabo babu fallasa Ammah ta amsa mata da "kuna lafiya Hauwa, ya y'ar uwarki", har cikin ranta take jin yadda Ammah ta k'ira Batuul y'ar uwarta, kamar munafika tace "muna lafiya", Ammah tace "yayi kyau, ki kula da ita kamar yadda zaki kula da taki k'anwar kin ji, nasan Batuul batada Matsala, nasan abin yazo miki bazata, ki d'auka kaddara ce, tun can da rubutacce ne, ki barwa Allah komai sai kiga yazo miki da sauk'i, Allah yayi muku albarka, ya kad'e duk wata fitina cikin zamanku, kuyi zaman lafiya keda Y'ar uwarki, Allah ya baku zuri'a d'ayyiba ya baku zaman lafiya, Allah yayi muku albarka", har Ammah ta gama maganan da zatayi k'wak'walwarta ta kasa processing maganganun da takeji, gaba d'aya kanta ya gama d'aurewa, suyi zaman lafiya ita da y'ar uwarta, wannan magana ai kishiyoyi ake fad'awa, maza tayi ta cire tunanin daga ranta tace "Toh Ammah mungode", daga haka ta mik'awa Abu wayan tana kallonsa, bayan sun gama maganan da zasuyi da Ammah sukayi sallama, kallon Ajiddeh yayi, she wasn't looking herself anymore dan abincin ma ta denaci, yana bud'e baki zaiyi mata magana wayarshi ta sake ringing, bai d'auka ba har ya katse dan lamba ce bak'uwa, sai da aka sake k'ira a karo na biyu ya dauka, muryan namiji yaji yace "This is Daniel speaking from Birmingham port authority, we call to notify you d arrival of your cointainer, we would like you to come and claim your property", ajiyar zuciya yayi, kayan da Ammah ta fad'i kenan, cewa yayi "Aiit, I will be there surely soon", "Thank you", mutumin yace mishi sannan suka katse wayan, Ajiddeh dae ta kafa mishi k'ananan idanuwanta ko kifta wa bata yi, iska ya hura mata yace "what are you thinking about wife, obviously me", a hankali ta kalleshi har lokacin hankalinta tashe tayi murmushi tace "Ba komai", ta juya taci gaba da cin pizza ta, ba wai dan ya yadda ba ya k'yaleta, mik'ewa yayi yana kallonta yace "I will b back soon, take care", da haka ya fita daga d'akin da ido kawai ta bishi dan ba daidai take jinta ba, sai da ya kalli kofar d'akin Batuul kamin ya sauk'a k'asa, d'akinshi yaje ya d'auko key ya fita, tafiyar minti 25 ya isa gun port authority, container number ya fad'a musu bayan ya k'ira Ammah ta sanar dashi number, da mamaki yake kallon kayan, bai tab'a tunanin haka kayan keda yawa ba, ta ina ma zai kai kayan nan gidanshi, kana gani kasan lefe ne na aure, idea ne ya fad'o mishi kawai yasa akayi loading kayan a babban mota, yana gaba babban mota na biye a baya, gaban wani gida da rabinshi duk glass ne suka tsaya, nan aka sauk'e kayayyakin, mutanen ne suka shigar da komai ciki, sai da suka gama ya sallamesu suka tafi, shiga yayi ciki ya kwanta kan sofar parlour, wayanshi ne ya shiga ringing, Ammah ce take k'ira , yana recieving tace "Ka amso kayan?", hannu yasa cikin gashin shi a hankali yace "Ehhh Ammah, but ban k'arasa gida ba", yasan tunda Ammah tace zatayiwa Batuul magana yau d'innan sai tayi, ya lumshe ido yace "In sha Allah Ammah, ina komawa zan bata wayan ", bata tsaya jin komai ba ta katse wayan, bai bar gidan ba sai bayan 30mins,






Kai tsaye d'akin Batuul yaje da ya koma gida, kwance ya tadda ta tana bacci abinta hankali kwance, daga ita sai d'an bum short da crop top ta takure waje daya ga xanin ta a gefenta, yafi minti biyu tsaye yana kallonta daga baya ya janye idonshi ya bud'e closet d'inta ya Ciro mata dogon hijab, hannu yasa cak ya d'auketa, baki ta bud'e zata sa ihu ya matseta jikinshi, ajiyar zuciya ta sauk'e jin k'anshin turarenshi tayi lamo jikinshi sae dae gabanta faduwa yake, har sai da ya kaita mota sannan ya bud'e ya direta ya jefa mata hijab d'in da ya d'auko mata shima ya zaga ya shiga daga gefen driver ya tada ya bar compound d'in, kallonsa take a tsorace sae dae ta kasa cewa komae, a hankali ta saka Hijab dinta da ya jefa mata.
[8/22, 14:49] Umar Dalha: πŸ’–πŸ’BATUULπŸ’–πŸ’

57

By phartiemarhk

Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*

Driving yake ba tare da yace mata komai ba, duk ta takure cikin motar a tsorace, ga sanyi da takeji dan gaba d'aya wajen sai traces d'in snow ake, a hankali ta juyo kanta daga kallon waje ta kalleshi, wani irin kallo da ya sakar mata yasa tayi saurin d'auke kanta, idonta har ya cicciko, kanta ta kifa kan k'afarta ta sake k'ank'ame jikinta sabida sanyi, bata d'ago ba har sai da taji yayi parking tukunna ta d'ago kanta a hankali, inda ya kawo su tabi da ido tana kallo, xaro ido tayi ganin irin gidan dake gabansu, bud'e k'ofar motan yayi ya fita ya fara tafiya, bata yi yunk'urin fita daga motan ba har saida ya juyo yaganta zaune har lkcn, wani irin kallo ya watsa mata, sannan ya dawo ya bud'e motan, bata jira yace komae ba ta fito, ya kama hannunta, yana tafe tana binshi a baya, kalle kalle Batuul ta shiga yi ganin irin gidan da ya kawo su, don rabin gidan duk glass ne, sosai gidan ya mata kyau, duk wanda yayi designing gidan yayi k'ok'ari, baki ta tab'e da ta tuna shima d'in architect ne fa, amma gaba d'ayanta a tsorace take, stairs yabi da ita ya nufi d'akin da aka zuba kayanta, da mamaki tabi kayan da ido, ta d'ago kai tana kallonsa, kallonta yayi shima snn ya d'auke ido ya xauna ya fixgota ita ma ta xauna daga gefensa, wayarsa dake hannunsa ya kunna yayi danne danne snn ya mika mata, sai da ta kalli fuskanshi taga shima ita yake kallo sannan ta karb'i wayan a sanyaye ta kara a kunnenta, muryan Ammah taji tana cewa "Bitti ya gida?", a kunyace tace "Alhamdulillah Ammah, ina yini?", Ammah tace "Alhamdulillah Bitti, kinga kayanki sun iso ko?", sai da ta kalli Abu, taga kallonta yake sannan ta gyad'a kai kamar Ammah na gabanta tace "Ehhh Ammah, gasu nan na gani", Ammah tace "Yawwa akwai wani kwali a ciki anyi packaging, ki bud'e yanzu in miki bayanin abubuwan ciki da yadda zakiyi amfani dasu", "toh tace" sannan ta mik"e ta isa wajen da kayan ke ajiye, a hankali tace "Ammah kwalin ba d'aya bane, suna da yawa", Ammah tace "Ehhh k'aramin ciki zaki bud'e, manyan duk turarrarukanki ne ciki", tace "toh Ammah", karasawa tayi inda k'aramin kwalin yake ta shiga k'ok'arin bud'e kwalin, kasa bud'ewa tayi harda sauk'e numfashi, a hankali ta juyo ta dubi Abu dake zaune, kallonta shima yayi yaga tayi rau rau da ido, ganin yaqi cewa komai ta juya taci gaba da kiciniyar bud'e kwalin, d'an murmushi yayi ya mik'e ya isa inda take, k'anshin turarenshi da taji yasa tayi Saurin juyowa, kamin ta tashi yazo ta bayanta ya mik'o hannayenshi daga gaba kan kwalin, sama sama ta rik'a jin numfashinta jin sauk'ar numfashinshi kan wuyanta, still tayi har ya gama bud'e kwalin, bai bar bayan nata ba sai ma sake kwantowa da yayi, jiki a sanyaye ta d'auki wayan ta maida wayan kunnenta, sai da Ammah ta gama mata bayanin komai sannan sukayi sallama, wasu ma duk ba fahimta tayi ba jin numfashinshi na sauk'a jikinta yana sending shivers to her spine, a hankali ta shiga k'ok'arin tashi daga wajen, hannayenshi yasa ya zagaye waist d'inta ya sake matseta jikinshi, babu abinda

1 Comments On BATUUL
avatar
hafsat-9-3

12 months ago

Reply

Nice book

Please Login or Register in order to submit comment