Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da makulli mak'ale a jiki, cikin tsawa yace mata "ba magana nake miki ba, ko bakiji lokacin da nace miki ki shirya zan kaiki school bane kika kwanta kina bacci", sai lokacin ta lura da kayan jikinshi taga har ya shirya zuwa farin shirt mai stripes ďin bak'i da bak'in wando, windown ďakin ta duba taga har rana na fitowa ta kalleshi taga ita yake kallo har lkcn, ta ďauke idonta tace "ai bacci ne ya ďaukeni bansan safiya tayi ba", ta faďa tana zumb'uro baki, k'wafa yayi yana kallonta yace "get ready and come down in the next 15mins", daga haka ya juya ya fita daga ďakin, tab'e bakinta tayi a ranta tace masifaffe, daga haka ta cire dogon hijabin dake jikinta da rigar baccin ta shiga wanaka, ko minti biyar batayi ba ta fito daga toilet ďin bayan tayi brush, akwatinan kayanta ta buďe ta shafa mai ta ciro wata doguwar riga blue mai dogon hannu ta saka, chappette kawai ta shafa a lips ďinta ta taje gashin kanta sannan fesa turarukanta masu dadi'n k'anshi ta shafa, a hankali take sauk'owa daga stairs ďin har ta k'araso cikin palon, yana zaune kan ďaya daga kujerun palon, Ajiddeh na jikinshi sanye da wasu shegun kayan bacci da ya bayyana duk jikinta, ita ta fara hango Batuul, wani irin harara ta sakar mata kamar idonta zai zazzago ta k'ara shigewa jikin Abu dake k'ok'arin canja channel, cikin raďa tace mishi "baby i dont want you to leave", tana yi tana kissing wuyanshi, shima janyota yayi yace mata "dont you worry, i will b back for you, kinga school zan kaita ta fara processing", ita kam Batuul ko kallon inda suke batayi ba tazo ta wuce su zata fita waje, sai a lokacin ya ganta, da ido ya bita har ta fita daga palon sannan ya mik'e yana kallon Ajiddeh yace "Baby ki kula da kanki", ya manna mata kiss a bakinta, hade rae tayi tace " Babe ko gaisheni fa bata yi ba ta wuce" yace "ni din ma ae bata gaishe ni ba, kyaleni da ita" daga hka yayi waje, a bakin k'ofan palon ya tarar da ita tana tsaye, yace "Go back nd greet my wife" daga kai tayi tana kallonsa, ya hade rae yace "Do dat fast my frnd" juyawa tayi a hnkli ta koma falon, tsakiyar falon ta tsaya ba tare da ta kalli Ajiddeh ba tace "Ina kwana" a sanyaye tayi gaisuwan, Ajiddeh ta wurga mata hararan tsana tace "Da ban kwana ba kya gan ni, munafuka 'yan maula" Juyawa Batuul tayi ta bar falon ta fita waje, har lkcn yana tsaye inda ta bar shi, ba tare da ya kalleta ba yayi wucewar shi garage ďin gidan, tana nan tsaye ya fito da wata dank'areriyar Benz, a hankali take k'arasowa inda motar take ta buďe gidan gaba ta shiga, k'anshin turarenshi ne ya cikata, juyar da kanta tayi tana kallon wajen glass, bai ce mata komai ba yaja motar ya ďau hanyar makarantan, tafiyan minti goma suka isa k'ofar makaranta sae a snn ya juya ya kalleta yace "yhu look for wat to take for breakfast a sch din," ko kallonsa bata yi ba wani irin farin ciki ya ziyarceta ganinta a k'ofar university da kullum take mafarkin zuwa tayi karatu, batasan lokacin da murmushi ya sub'uce mata ba tana kallon yadda students kowa na aikin gabanshi, jin sautin murmushinta da yasa gefen kumatunta lotsawa ya bayyana dimple ďinta ya sashi juyowa yana kallon yadda take murna, yau ne rana ta farko da ya fara kallonta tana dariya haka, driving yake amma gaba ďaya hankalinshi na wajenta har ya iso gaban wani building yayi parking motarshi, sai a lokacin ta juyo da murmushinta ta kalleshi taga shima ita yake kallo, hararanta yayi ya buďe motar ya fito, ita dai bata fito ba dan baice mata ba, har ya fara tafiya yaga bata fito ba tana cikin motar a zaune, rai b'ace zagayo ya buďe mata k'ofan yana mata mugun kallo yace "zaman mey kikeyi da baki fito ba", baki ta zumb'uro ta sa k'afanta a waje, ita batada lokacinshi dan ji tayi duk bak'in cikinta ya yaye, k'wafa yayi ya juya yaci gaba da tafiya, biyoshi tayi a baya har lokacin da murmushi fuskanta, har sukazo k'ofan shiga wani office sannan ya juyo yana kallonta rai a haďe, haďe dariyanta tayi ganin yadda yayi kicin kicin da fuska sannan ya tura k'ofan ya shige, a sanyaye itama ta shiga a ranta tace masifaffe kawai, nidai yau is my happy day banida time ďin kowa ta shige cikin office ďin itama, Office ďin ta k'arewa kallo, an manna hotunansu su Adam smith, Alfred Marshal, David Ricardo, J.S mills da sauran manyan economists ďin duniya, wani bature ne zaune kan kujera a office ďin, da gani shekarunshi zasu kai 60, dogo sannan yana da jiki, hannu ya mik'awa Abu yace "Mr Kyaree you are welcome", baki ta kyab'e jin har sunanshi ya sani, juyowa yayi yana kallon Batuul yace "You can sit down madam", yayi mata nuni da kujeran gefen Abu, kallon Abu tayi taga shima kallonta yake da lumsassun idanuwanshi, kujeran ta jawo ta zauna, tana zaune suka gama maganganun da zasuyi, mutumin ya ďago yana kallonta yace "Mrs Fatima are you single?", question ďinne ya zo mata bazata, ta ďago tana kallon Abu dake danna wayarsa, a hankali ta ďauke kanta ta kalli mutumin da taga sunanshi Stephen xata yi magana ta ji Abuturrab yace "No! She's nt, she's married" kallonsa tayi sae kuma ta sunkuyar da kai, mutumin yyi murmushi yace "Dat's Gud, yhu are welcome to London University of Economics Mrs Fatima kashim Goni" murmushi Batuul tayi jin ynda yyi pronouncing sunan nata, nan Mr Stephen ya shiga yi mata bayanin abubuwan da ya kamata, shi dae Abuturrab danna wayarsa kawae yake, sun kusa minti ashirin office din bayan ta cike wasu forms din da ya bata ta kuma yi signing kafin ya dauko ID dinta na makarantar ya bata, ya kuma yi mata maraba snn ya mika mata timetable da wasu textbuks har uku yyi directing dinta zuwa dept dinta, godiya tayi masa tana murmushi, Abuturrab ya mike ya kuma yi masa godiya mutumin ya basa hannu snn suka fita office din, bin bayansa kawae take farin ciki shimfide fuskarta, da alama ya san kan makarantar sosae ganin ynda yake tafiya with courage abunsa kuma short cut yake bi, xaro ido tayi da ta tuna ae shi ma makarantar yyi if she remembered rightly, ko kadan bata damu da ynda ya hade rae ba farin cikin da take ji a lkcn baxae ma bari ta damu da hkn ba, jefi jefi tana ganin bakaken fata kmr su suna wucewa, har gaban dept din ya kai ta, wata baturiya ce ke tafiya rungume da litattafenta, ya karasa inda take yace "Excuse me Ma'am!" D'an kallonsa tayi tace "Pardon?" Yace "Just a minute or two" Tambayarta ya shiga yi da harshen turanci ko a Dept din nn take, ta masa nodding tace "Yea!" Murmushi yyi yace "Dat's gud Ma'am, am handing my sister over to yhu, assist her for today, yhu know! she's new in here" Baturiyar da baxata wuce shekaru 18 ba tayi murmushi tana kallon Batuul tace "She's welcome, she will really like it in here, from Africa I guess!" Yace "Yea! Exactly Africa! Africa Nigeria." Karasawa gun Batuul dake kallonsu tayi ta kamo hannunta tare da shaking dinta tace "Welcm frnd, yhu will really enjoy it in here, I am Samantha Brown, yhu" Batuul tayi murmushi tace "Am Fateema kashim" k'asa pronouncing din sunan yarinyar tayi Batuul tayi dariya, yarinyar ta bude deep green eyez dinta tace "your looks are more like dat of Britney Smears a pop artiste, just dat yhu are a dark, I will cal yhu Britney! Nyc meeting yhu Britney" kallon Batuul dake dariya bakin rai Abuturrab yyi, sae ta basa dariya don bae taba ganinta cikin farin ciki haka ba, murmushi yyi yana kallon Samantha yace "Dat's a gud start! I will take my leave now Miss Samantha, it's nyc meeting yhu for the first time" hannu tayi masa stretching ya karba tace "Nyc meeting yhu too Mr..." Yana murmushi yace "Aliyu Ahmad" murmushin ita ma tayi tana nodding ta sake hannunsa, karban timetable din hannun Batuul yyi yana dubawa, snn ya mika mata, ya ciro 20 pound sterling hade da wayarsa d'aya ya mika mata yace "Driver xae kira ki anjima" risinawa tayi ta karba kanta a kasa tace "Nagode" bae tanka ta ba, ya ma Samantha waving ya juya ya bar su wajen.

Karfe biyar saura suna xaune ita da Samantha da wata Linda sae 'yar uwarta yar Nigeria Aisha, ba karamin farin cikin haduwa da Aisha tayi ba ko ba komae ta samu 'Yar uwa a makarantar, sae dae ita a hostel take, fitowarsu lecture knn suna ta hiransu ita kuma tana duba textbuk din hannunta, wani guy ne ya karaso inda suke yana kallonsu yace "Hi" duk suka amsa bnda Batuul da bata dago ba, xauna wa yyi daga gefenta yana kallonta yace "Assalamu alaikum!" D'agowa tayi da sauri tana kallonsa, sae a snn ta ga bahaushe ne me kyau, sunkuyar da kai tayi ta amsa masa sallamarsa, da harshen hausa yace "Ya lecture 'yar uwa" tace "Alhmdllh tnxx" ya d'an yi murmushi jin ynda ta amsa masa yace "Am Shaheed Mukhtar by name, yhu?" Wayarta ne ya shiga ring ta mike tana kallon screen din tace "Srry Shaheed, I will be on my way ynxu" kallon Aisha dake ta kallonsu tayi tace "Plss ki d'an rakani outside gate, driver ya xo dauka na" bata jira cewar Aisha ba ta shiga yi ma su Samantha sallama, daga nn tayi gaba da sauri Aisha ta bi bayanta, binta da kallo Shaheed yyi yana murmushi, sae da suka yi nisa Aisha tace "me yasa xa ki yi masa hka Fatima, kinsan waye Shaheed kuwa, a vry popular guy a makarantar nn, he's so intelligent, course din mu daya, nd he is in his final year, ni na yi mamakin ganinsa wllh, don bin sa 'yan mata ke yi ba shi ke bin su ba" Batuul tayi murmushi tace "Gskya ne" tana ganin motar Abuturrab ta gane ta juya tana kallon Aisha tace "Toh sae gobe idan Allah ya kai mu, thnk for ur company frnd" murmushi Aisha ta mata ta gyada mata kai, Batuul ta juya ta nufi motar, duk a xaton ta driver ne, har xata bude baya sae kuma ta fasa ta bude gaba, ido hudu suka yi da shi, ta sunkuyar da kanta, yace "Baki ga daman d'aga call din ba knn" shiga motar tayi ta rufe ya tada motar suka bar wajen, a hnkli tace "Ina yini?" Ba tare da ya kalleta ba yace "Lfya lau" sae da suka kusa gida yace "Ya lecture" kmr an tilasta sa tambayar don can ciki yyi ta, ta kallesa tace "Alhmdllh" yana gama parking ta bude motar ta fita, sae dae bata yi gigin tafiya ba ta jira har ya fito, sae da ya shiga gaba ta bi bayansa, Ajiddeh na kwance falo ta kure Ac tana kallo sanye da kananun kaya as usual, a hnkli Batuul tace "Ina yini" Ajiddeh ta d'an saci kallon Abuturrab, ganin kallonta yake yasa tace "Lfya lau" sama Batuul ta nufa, ajiye wayarsa dake hannunta da long notes din da ta siya a makaranta tayi ta kwanta tare da lumshe ido, ta kusa minti goma kwance snn ta mike ta cire watch din hannunta da jewelry ta cire doguwar rigar jikinta xata shiga bayi tayi wanka, bude kofar dakin taji anyi ta juya a rikice suka yi ido huda da shi, xaro ido tayi ta durkushe wajen, ya dauke kai ya juya da sauri ya fice daga dakin.
[8/22, 14:47] Umar Dalha: 💖💝BATUUL💖💝






48






By phartiemarhk






Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*






Yana fita ta mike da sauri ta rufe k'ofar ďakin, har lokacin jikinta b'ari yake, she wasnt expecting anyone, komawa tayi ta zauna daga bakin gadon hannunta zagaye a k'irjinta duk kunya ya isheta, tafi minti biyu a haka daga baya ta mik'e ta faďa toilet, ta daďe cikin bath tub ďin kamin ta fito, a hankali ta lek'o kanta dan tsoro takeji kamar zataga wani a ďakin, ganin babu kowa yasa ta k'arasowa cikin ďakin, akwatinta na kayan shafa dake gefe ta cicciro waďanda take buk'ata ta shafa ta maidasu cikin akwatin, gown ďin atamfa holland bak'a mai manyan patterns ďin ja da purple ta saka, bata ďaura ďankwalin ba , comb ta ciro daga cikin kayanta ta dawo gaban mirror ta shiga taje gashinta, sai da ta gama ta haďeshi in a bun, tunanin shirya kayanta dake cikin akwati a closet ďin ďakin tayi, bbu b'ata lokaci ta tashi ta buďe closet ďin, tana buďewa taga electric burner a ciki, sai da ta karkaďe k'uran wajen tukunna ta shiga jera kayayyakinta a ciki, sosai ta shiga gyaran ďakin, har bedsheet ta canja wanda ta gani a cikin closet ďin ďakin, cikin lokaci kaďan ta gama gyaran ďakin ta kunna burner ta saka sandal woods, babu abinda ďakin keyi sai k'anshi, sai da taga ďakin ya koma yadda takeso sannan tayi ajiyar zuciya , faďawa tayi kan gadon tana maida numfashi, idonta ne ya faďa kan wayarshi da ya bata dake ajiye kan bed side drawer, hannu tasa ta dauko wayar, ta d'an tabe baki ta shiga gallery duk hotunan Ajiddeh ne wayar wasu da shigar mutunci wasu kuma bbu kyan gani, k'an wani hotonsa da yyi shi kadae yana xaune office ta tsaya tana kare ma kallo, yyi mugun kyau sanye da suit blue da fadin shirt daga ciki, murmushin sa me rikita Ajiddeh yyi a hoton Lol, Batuul tayi tsaki hade da tabe baki ta wuce hoton, wani hoton ta kuma gani yana sanye da farin 3qtr da farar polo, ainahin kyansa ne ya fito a hoton, ita kanta ta san yyi kyau amma hkn bae hanata kyabe baki ba, ajiye wayar tayi ta juya abun ta ta rufe ido kmr me shirin bacci.






Abuturrab na fita daga ďakin dama dakinsa ya wuce, direct toilet ya shiga yayi wanka, tsakin da baisan dalili ba ya riqayi har ya fito daga toilet ďin, sweatpant grey da farar shirt ya saka, zama yayi gaban system ďinshi yana dudduba abubuwan da zaiyi, bayan wajen thirty minutes ya mik'e tare da jan ďan siririn tsaki ya fita daga ďakin dan ya fara jin yunwa, ko coffee ne zuwa zaiyi ya haďa kamin ya samarwa kanshi abinda zaici, tunda ya fito daga ďakinshi yakejin wani k'anshi mai daďi, lumshe ido yayi yana shak'ar k'anshin, sauk'a yayi k'asa yayi hanyan kitchen, Ajiddeh na kwance nan inda ya barta ta tasa bowl ďin Tacos a gaba tanaci, ďauke kanshi yayi cike da haushinta ya wuce cikin kitchen, coffee maker ya nufa ya haďa sannan ya fito, sama ya koma yayi hanyan ďakin Batuul don ce mata ta fito ta samawa kanta abinda zataci, tun kamin ya kai ga shiga ďakin yakejin k'anshin nan na daďa k'aruwa, a aljihunshi ya fiddo makulli ya buďe ďakin ya shiga, a figice ta mike daga kwancen da take dan tasan saida ta rufe k'ofarta kamin ta kwanta, lumshe ido yayi ya bude ya shiga bin ďakin da kallo ganin yadda ta gyara shi yayi kyau, abinda dakinsa bae samu daga Ajiddeh ba, tashi tayi daga kwancen da take ta zauna tana kallonshi, kyab'e baki yayi ya k'arasa shigowa cikin ďakin, gashin kanta da yasha gyara yabi da kallo, ita kam wasa ta shigayi da zoben hannunta zuciyanta na bugawa taqi ďagowa ta kalleshi, kyab'e bakinshi ya kuma yi ya ďauke idonshi daga kallonta yana daďa bin ďakin da kallo yace "abincin da zakici sai ance ki fito ki nemawa kanki?, ko dan ki samu na fađa wa Ammah cewa bana baki abinci", bata ce mishi komai ba kuma bata ďago ta kalleshi ba, sipping coffee ďin dake hannunshi yayi yace mata "in kin gama zaman sai ki sauk'o ki nemawa kanki abinci don baki taho da Cook daga Nigeria ba", daga nan ya juya har xae fita ya dawo ganin wayarsa gefensa ya dauka, gabanta ne ya fadi tunawa da tayi a gallery take, kunna wayar yyi ya ga hotonsa, kallonta yyi yace "Ohh hotona ma kike kallo knn," dariya yyi yace "Lallai kina da wahala yarinya, xa ki iya kishi da matata?" Ji tayi kmr ta rusa ihu don takaici sae dae bata iya ta ce masa komae ba, yyi murmushi yace "Ae kam da kin gamu da aiki" daga hka ya fita daga ďakin, bayanshi ta bi da kallo tareda da fadawa kan gado tana kukan takaici.





Ji tayi wayanta na ringing, ta duba taga Aunty ke k'iranta, da sauri ta goge hawayenta cike da murna ta ďaga ta gaida Aunty tace "Aunty har na fara zuwa school yau, Aunty sai kinga makaranta, i couldnt believe it sai da na ganni a lecture hall, da i thought i will never get d chance to study there, but God has other plans, am just happy tun ďazu", Aunty tayi murmushi daga ďaya b'angaren tace "Ai dama every disappointment is a blessing in disguise, kinga you were sad abt getting married, but God knows best, sai kinyi aure zaki samu kiyi fulfilling dream ďinki", ajiyar zuciya Batuul ta sauk'e tunawa da tayi auren da tayi ne yayi silar zuwanta makaranta, jiki a sanyaye tace "Aunty its so nice, Nagode", Aunty tayi dariya tace "godiya kuma, Allah zaki godewa ai", tace "Ai nagode mishi sosai shima, saura Baba shima zance mishi nagode", Aunty tayi dariya tace "toh shikenan, kayanki sun iso?", da mamaki tace "Aunty wane kaya?", Aunty tace "kayayyakinki mana da kuma su turaren wuta", tace "A'ah Aunty, ni kawai wanda nazo dashine, sai turaren wutanma ďan kaďan ne", Aunty tace mata "toh shikenan, in sun iso Abu zai kawo miki, sai ki gayamin", tace "toh", hira sukayi da Aunty daga nan sukayi sallama, tana ajiye wayar aka bude kofa, mikewa tayi da sauri sanin shi ne ya dawo, wani mugun kallo yake mata daga bakin kofar ta sunkuyar da kai a hankali tace "Anty ce ta kira ni" juyawa yyi ya bar kofar ta bi bayansa da sauri, downstairs ya sakko tana biye da shi a baya, xama yyi gefen Ajiddeh yana kallonta yace "Kin yi sllh babe?" Xata basa amsa idonta ya kai kan Batuul dan zaro ido tayi kafin ta mike cikin fada ta fara magana "Aliyu meye hka xata wani sakko mani falo da kwalliya hka kmr gidan mijinta? Ohh dama ita ce ta cika min gida da turare hka?" Kallon Batuul da ta k'asa ci gaba da tafiya Abuturrab yyi don shi bae ga wani kwalliya da tayi ba banda kaya da ta sa, xae yi magana Ajiddeh ta ci gaba da masifarta "Toh gskya baxan yi tolerating haka ba, cin arxiki ta xo yi gida na don hka ta bi ni a hankali, daga yau ni kar ta sake sa min turare a gida kuma kar ta kuma sakko min falon miji bbu hijab, idan ba hka ba gskya xa a ga bala'i" murmushi Abuturrab yyi ya ajiye cup din coffesn hannunsa ya kalli Batuul dake tsaye har lkcn a tsawace yace "Baxa ki bar wajen nn ba" juyawa tayi a d'an tsorace xata koma sama, yace "C'mon kin wuce kin yi abinda xa ki yi ko sae na xo kan ki" kitchen din ta nufa hawaye cike idonta, rasa abinda xata girka tayi gashi tana tsoron kar ya shigo ya ganta tsaye, bude deep freezer tayi ta ga kayan miya kala kala da nama, deciding kawae tayi ta soya Irish, tayi sauce kadan, cikin mintunan da basu wuce ashirin ba ta hada abincin ta kashe gas, kan kace me tuni kamshin d'an sauce din da tayi da hanta ya bade gidan, Ajiddeh sae wani yatsine fuska take tana kyabe baki, Abuturrab ya juya ya kalleta yace "What's that?" Tsaki tayi bata ce komae ba, ya mike ya nufi kitchen din, goge goge ya sameta tana yi ga abincin ta ajiye gefe, juyawa tayi tana kallonsa, kmr baxae ce komae ba sae kuma yace "Iyakar girkin knn?" A hnkli tace "Um!" Tabe baki yyi har xae fita sae kuma ya karaso cikin kitchen din, plate ya dauka ba tare da ya kalleta ba ya nufi inda ta ajiye abincin ta bi sa da kallo, kadan ya dibi Irish din da sauce a gefe, ya daga kai suka hada ido, sauke idonta kasa tayi tace "ya ishe ka hka?" Juyawa yyi yace "Yea!" Snn ya fice, hade rae Ajiddeh tayi tana kallonsa har ya xauna gefenta tace "Haba babe, wnn ae xub da girma ne, maimakon ka fita ka siya ko ka aiki driver" yace "koh? In xa ki ci ki sa hannu mu ci" tsaki tayi ta dauki remote, fork ya dauka ya fara cin abincin, he was so surprise at the taste of the food, bae taba tunanin Batuul ta iya girki hka ba, lumshe ido yyi yana cin abincin, amma sbda bae son ta rainasa bae cinye potatoe din ba duk da bae ishe shi ba ya ajiye, dai dai nn Batuul ta fito bayan ta gama tsaftace kitchen din rike da plate din abincin ta, bata yi gigin kallon inda suke ba ta haura sama. Abuturrab na gama kallon program din da yake kallo ya mike ya haura sama ya bar Ajiddeh nn falon, har xae shiga dakinsa sae kuma ya nufi na Batuul, ya kusa minti biyar tsaye don bae ma san me xae kai sa dakin ba, bude kofar dakin aka yi ya koma baya da sauri duk ya daburce, kallonsa take da mamaki, ba tare da yyi wani tunani ba ya samu kansa da cewa "Tnx!" Sae kuma ya juya da sauri ya nufi dakinsa, bin sa da kallo tayi sae kuma ta kyabe baki ta sauka downstairs, dai dai lkcn da Ajiddeh ta duka ta dauki plate din potatoe'n da Abuturrab ya rage xata d'an d'ana taji taste din girkin da ya cika ma mutane gida, sae a idon Batuul, sake plate din tayi duk da har ta kai daya baki, duk ta daburce.
[8/22, 14:47] Umar Dalha: 💖💝BATUUL💖💝

49

By phartiemarhk

Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*

Sunkuyar da kai Batuul tayi ta karasa sakkowa, Ajiddeh ta ji kmr ta nutse wajen don kunya, mikewa tayi tana yatsine yatsinen borin kunya ta nufi kitchen da sauri, hannu ta wanke da bakinta a sink ta shiga kakarin amai, Batuul bata san lkcn da dariya ya subuce mata ba, ta juya da sauri ta koma sama ta dinga tuntsirar dariya a corridor, bude kofa Abuturrab yyi yana kallonta da mamaki, xae yi magana sae ga Ajiddeh kmr xata tashi sama, ganin dariya Batuul take ya sa ta tsaya daga stairs tana huci, Abuturrab ya kalleta ya kalli Batuul da ta k'asa daina dariya ganin ynda Ajiddeh ke huci, a fusace Ajiddeh tayi kanta ae bata san lkcn da dariyar ta koma ciki ba tayi bayan Abuturrab a tsorace tana kiran Anty, ya hade rae yace "meye hka wae?" Lamo Batuul tayi bayansa, a fusace Ajiddeh tace "Honey ni fa take ma dariya hka kmr sa'arta fa?" Juyawa yyi yana kallon Batuul yace "kina da hankali kuwa? Dariyar me kike mata?" Batuul ta turo baki tace "Ni ba da ita nake ba fa" wani kallo ya shiga mata ya fixgo ta daga bayansa yace "ki fadi Dariyar me kike idan ba hka ba I wil slap yhu" sunkuyar da kai tayi don wani dariyar taji na taho mata, ya daka mata tsawa yace "Baxa ki yi magana ba" a hnkli tace "Kaga abincin da ka rage fa naga tana ci a falo kuma tana gani na sae ta shige kitchen ta fara amae...." Bata karasa ba ta shige bayansa ta dinga dariya har da kyakyatawa, dariyar shi ma ya fara yi yana kallon Ajiddeh da

1 Comments On BATUUL
avatar
hafsat-9-3

12 months ago

Reply

Nice book

Please Login or Register in order to submit comment