Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bakida lafiya dolene sai kinzo school", had'e rai Batuul tayi tace "wa yace miki banida lafiya", dan bata jin yin magana da kowa, murmushi Aisha tayi tace "ai ba sai an fad'i ba, you look sick, red eyes, plump lips, pale face, nasan inda zan tab'a temperature d'inki nasan yayi sama", yak'e Batuul tayi tace "Am totally fine, bacci ne kawai ban samu nayi ba jiya", ta d'auke kanta tana sauraron maganan da lecturer d'insu ya fara, baki Aisha ta tab'e bawai dan ta yadda da abinda Batuul ta fad'a mata ba itama tayi concentrating da jin lecturer d'insu, Batuul dai na zaune ajin ne amma gaba d'aya mind d'inta is off, batasan ma dalilin da yake sata damuwa ba, har suka gama lecture l batayi grabbing komai ba, jiki a sanyaye ta mik'e suka fito daga lecture hall d'in, Samantha ce tace "Let's go and get some food, am hungry just as the glutton I'm, then we go home after then, no any other class, done for d day",ta fad'a tareda d'an tsalle, dariya sauran suka sa amma Batuul was absent minded bata ma san mey suke cewa ba, sai da Samantha ta sa hannu fuskanta ta fara waving sannan tace "Hello, you there", sannan ta dawo daga tunanin da take tace musu, "You carry on, I will b there right away, I need to clear somethings over here", Aisha dai batace komai ba tayi gaba abinta haka ma Samantha tare suka tafi, suna tafiya itama ta juya ba tare da tasan inda zata ba, wani guri ta hango duk bishiyoyi ne, wajen very serene, ba tareda wani tunani ba taje ta zauna abinta ta fiddo littafi kamar me shirin karatu sae dae ita kanta tasan ba karatun xata yi ba.






Abutturab da Ajiddeh kam tunda suka fita airport suke abu d'aya, da k'yar ta samu kujera shima d'in ba first class amma tace taji ta gani zatayi managing, ai Uwa tafi komi, haka dai tayi convincing d'in Abu, wayanshi da ya ciro cikin aljihu don duba karfe nawa ya tuno mishi da Batuul, ba b'ata lokaci ya shiga neman number David ganin zai kai yamma bai dawo ba kuma bai bata wayan ba, David na d'agawa Abutturab yace mishi "Where are you?", David yace Sir av dropped her at school, am at the construction site now to give out d documents", d'an iska ya furzar yace "Did she tell you when she will be done?, i mean for today?", "David yace "No Sir, she didn't", Abu ya gyad'a kai yace "okay, you should leave d site now and b there at her school, make sure you wait for her to finish and take her back home", David ya amsa da "okay Sir", daga nan ya kama hanya ya koma makarantar su Batuul, inda ya sauk'eta nan yaje ya kafa motarsa, tunda yaje yake zuba ido ko zai ganta amma shiru, tun 10:30 yake makarantar gashi har 1 tayi babu Batuul, har lecture halls d'insu sai da ya riqa bi yana yi musu describing d'inta bata nan kuma an tabbatar mishi da sun gama lecture d'insu na yau, ba tare da b'ata lokaci ya ba ya kira Abutturab yace yaje bai ganta ba, calmly yace mishi ya koma yaje ya sake dubota, sau biyu yana komawa amma bata nan har wajen 4, sai lokacin hankalin Abuturrab ya fara tashi, Ajiddeh na lura da shi sae dae bata ce komae ba, Sallama yayi mata daga karshe yace xae tafi sae sun yi waya, ta wani hade rae tace " Ban gane ba Aliyu, a kan wata can xaka tafi ka bar ni jirginmu bae tashi ba, ita din yarinya ce da baxa ta iya kula da kanta ba duk xa ka wani tada hankali haka" ya daga kafada don bai son su rabu da fada yace "Chill babe, wani takardu xae kai min office to suna gida kuma wae ta kulle gidan da makulli shi yasa kika ga na takurasa ya nemota" tsaki Ajiddeh tayi tace "Toh gidanta ne xata wani kulle da makulli kuma wa ma ya bata makullin" peck ya manna mata a lip yace "Yi hakuri mai gida" turo baki tayi, yayi dariya yace "Don't worry babe, i promise to be back soon" bin sa da kallo tayi har ya bace mata kafin ta lumshe ido ta sauke ajiyar xuciya, Allah kadae yasan irin son da take ma Aliyu, kuma In'sha Allah nata ne shi din ita kadae.
Abuturrab kam direct makarantar ya wuce daga airport din, har ya gama zagaye makarantar babu Batuul, a gajiye ya dawo gida lokacin biyar da rabi, ido ya lumshe ganin abincin da ta jera tun safe kan dinning ba a tab'a ba,sai lokacin ya tuna da zancen abinci, yasan dae baxa ta bata ba amma haka kawae ya kasa samun natsuwa.





Batuul kam Na zaune wannan gurin har 4:15, sosai wajen ya mata dad'i har yasa ta manta damuwar dake ranta, sai kallon tsuntsaye takeyi suna shawaginsu kan bishiyoyi da water fountain d'in dake tsakiyar wajen, agogon dake hannunta ta duba taga 4:15, a razane ta miqe ta tattare kayanta ta fito daga gun, tasan dan bata sallah ne shiyasa time ya qure har haka bata sani ba, rana har ya kusa fad'i lokacin, tafiya kawai ta shiga yi har ta iso dpt dinsu ta tsaya tana kalle kalle, bataga kowa da ta sani ba, haka kawae taji hawaye sun cicciko mata ta nufi hanyan gate a sanyaye zataje ta tari cab ya kaita gida, tafiya takeyi tana ta share hawaye, har wani blur take gani, dab bakin gate taji mota na mata horn, matsawa tayi ta bashi hanya ta koma gefe taci gaba da tafiya, ji tayi horn d'in na dad'a k'aruwa, "Fatima", a tsorace ta juyo tana kallon mai k'iranta, parking yayi ya fito yazo ya sameta inda take tsaye, fuskanta ya gama examining sannan yace mata "do you always cry?", d'ago idonta tayi ta kalle shi tace "Are you stalking me?", dariya tambayarshi ya bata yace , "Mey ya faru baki tafi gida ba tun d'azu and you finished your lecture for d day tun 10", shiru tayi bata ce mishi komai ba, tambayanta ya sakeyi jin tayi shiru yace "ina zaki yanzu?", a hankali tace mishi "gida" ido ya wara yace "by yourself, do you normally go by yourself, mey kika zauna yi a school d'in har kika kai this time?", kai kawae ta girgiza mishi, ya juya zai koma mota yace "let's go, I will drop", ba musu ta shiga gaba yana biye da ita a baya, shi da kanshi ya zaga ya bud'e mata k'ofa, wani kanshi ne mai dad'i yayi mata sallama, ido ta lumshe ta jinginar da kanta jikin kujera, Hamdala ta dinga yi a ranta dan dama tsoron shiga cab d'in takeyi, sai da ya fita gate d'in ya juyo ya dubeta yace "yace where are we heading to?", sai a lokacin ta bud'e idonta tace mishi ST.Georges No 15, daga nan bai sake cewa komai ba ya d'au hanya.





Waya Abuturrab ya bugawa Mr Steven akan ayi enquiring abt Batuul dan har yanzu bata dawo gida ba kuma school d'inma bata can, daga nan ya shiga yayi wanka ya canja kayan dake jikinshi, ko mai bai shafa ba ya sake d'aukan key yayi waje, yana zuwa bakin k'ofa yaga wata bak'ar Rolls Royce ta shigo compound d'in, sai da motan yayi wajen two minutes da parkin tukunna maishi ya bud'e ya fito, ajiyar zuciya ya sauk'e ganin Batuul ta fito cikin motar yayi tucking hannuwanshi cikin aljihu yana kallonta, "Thank you" tace da Shaheed tana kallonsa, Sam bata lura da mutum na tsaye ba sai da ta juyo zata shiga gida, gabanta ne ya bada sautin dam ganin Abu tsaye bakin k'ofa ya zuba mata lumsassun idanunshi ko kifta wa bae yi gashi ya wani hade rai, dakewa tayi ita a dole tana fushi taci gaba da k'arasowa, Sai da tazo dab dashi ta kasa d'aga k'afa ganin yadda idonshi ya canja kala yana kallonta dasu, shi kam Shaheed tuni ya bar compound din ba tare da ya lura da Abuturrab ba ma, a hankali Batuul tace "Ina yini" bae amsa ta ba ya kama hannunta suka nufi cikin gida fuskarsa a daure, gabanta ya dinga faduwa har suka shiga Palo, kulle kofar yayi ya juya yana facing dinta yace "Daga ina kike?" Sunkuyar da kai tayi ganin he's serious, murya can kasa tace "School" wani tsawa ya daka mata yace "I will slap you idan kika ce min school, I repeat my self where are yhu coming from, kuma waye yayi dropping din ki yanxu" hawaye ne ya xubo idonta har lkcn bata d'ago kanta ba.
πŸ’–πŸ’BATUULπŸ’–πŸ’





61






By phartiemarhk




Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*





Hade rai Abuturrab yayi yana mata wani mugun kallo yace "if I shud slap yhu! Na maki wani abun ne kike min kuka, waye ya sauke ki a mota nace" share fuskar ta tayi ba tare da ta d'ago ba tace "A frnd!" Yana mata wani irin kallo yace "A frnd? Male or female" a takaice tace "Male" wani xaro ido yayi cikin tsawa yace "What, Male? Da aure nawa kanki kika hau motar wani kato, are yhu insane?" Wani takaici ne ya rufe ta wasu hawayen suka dinga xubo mata, bata san lkcn da ta mayar masa da amsa ba tace "Ohh ashe kasan da auren ka kaina, toh ai ni ban san da haka ba, nayi xaton wanda ka raka airport kadae auren ka ke kanta" tana kai wa nan ta nufi stairs ta bar sa wajen tsaye, bin ta yayi da kallo baki bude, har ta haura sama, sae kuma ya shafa kai yana murmushi ya koma cikin Palo ya xauna, ba dai kishin sa Batuul take ba, No! Ya ma san it's impossible tunda ba son shi take ba. Batuul kam tana shiga daki ta jefar da jakar hannunta tayi xamanta gefen gado, sae dae banda tukuki babu abinda xuciyarta yake, ta fi minti goma xaune kafin ta mike ta rage kayan jikinta ta shiga toilet, warm shower ta sakar ma kanta, ta kusa minti sha biyar a bayin sannan ta fito daure da towel, gaban mirror ta nufa tayi shafe shafenta, xata dauki kaya a closet dinta ta ji wayarta na ring, juyawa tayi ta koma gaban mirrorn ta dauki wayar, ganin me kiran yasa tayi murmushi ta daga tare da sallama "Tace Ammah ina yini?" Maimakon ta ji muryar Ammah sae taji kmr muryar Anty Amnah, daga daya bangaren Anty Amnah tace "Kina ji na Batuul?" A d'an kunyace Batuul tace "Ina ji Anty ina yini" don kunyar matar ita dai take, Anty Amnah tace "Lfya lau Batuul, ya ku ke gaba daya" Batuul tace "Lfya muke Anty" Anty Amnah tace "Toh madalla, cikin kayan da aka kawo maki kinga wani parcel da aka yi wrap kuwa" Batuul ta d'an yi shiru tana tunani, Anty Amnah tace "shi kadae ne karami cikin kayan" Batuul tace "Eh na gan shi Anty" Anty Amnah tace "Yauwa! Kin bude kuwa" girgixa kai Batuul tayi kamar tana ganinta tace "A'a Anty, ina ce turare ne ae" Anty Amnah tace "A'a ba turare bane, maxa dauko yanxu ki bude in maki bayani" xaro ido Batuul tayi tunawa da tayi ae duk kayan na can gidan, tace "Toh Anty bari in dauko" ajiye wayar tayi ta fita da sauri ta sauka Palo, Abuturrab na xaune har lkcn ya jinginar da kai jikin kujera idonsa lumshe, ta wani hade rae ta tsaya gabansa tace "Ya Abu, Anty Amnah ta kira wae xata min bayanin wasu daga kayan da aka kawo kuma basa nan ai" a hankali ya bude ido yana kallonta, gyara xama yayi da sauri yana ci gaba da kallonta, jin yaki cewa komae tace "Kaji, she's still on the line fa, ni ban san me xan ce mata ba" ko kadan bae san ma abinda take cewa ba, ganin haka yasa tayi saurin kallon kanta ta ga me yake kallo, wani kara ta saki ganin ashe towel ne jikinta har lkcn, ta juya da sauri xata bar wajen yayi saurin fixgota ta fado kansa, tsorata tayi ta shiga turasa xata mike yaki sakinta, tace "plss ya Abu, she's still on the line...." Bata rufe baki ba taji bakinsa cikin nata, still tayi na wasu yan dakiku kafin ta fara kokuwa da shi, duk ta rude, shi kam bae ma san tana yi ba, kan kace me sae ga su a kasa, nan jikinta ya dau rawa tana hawaye, danna bell da aka yi yasa ya saketa da sauri, ita ma ta mike a gigice ta koma baya don Ajiddeh ce kawae ta fado mata, a tare suka mike ita ta nufi sama da sauri shi koma yayi gun kofa, murda kofar yayi ya ga drivernsa ne David, ya sauke ajiyar xuciya yace "It's ok david, she's back minutes ago" Batuul kam daki ta shige ta fashe da kukan da bata san dalilinsa ba, wayarta ta dauka ta ga Anty Amnah ta kira ya fi a kirga, wani kiran nata ne ya kuma shigowa ta dauka da sauri, ta fara kame kame "Anty kiyi hakuri, dama naje ina dubawa ne, ga gashi na gani" Anty Amnah tace "Yauwa toh kin bude" xaro ido tayi sae kuma tace "Eh na bude" da sauri ta juya jin an murda kofar dakin, Abuturrab ya shigo, sunkuyar da kai tayi ta ci gaba da sauraran Anty Amnah, ganin ya nufota ta bar wajen da sauri ta koma can karshen dakin, bin ta yayi, ta kuma barin wajen da sauri ta ga ya kuma biyo ta, kamar xata yi kuka take kallonsa gashi ko kadan bata ma gane bayanin Anty Amnah, shi kam murmushi kawae yake yana kallonta, ta haye kan gado shi ma ya bi ta, rudewa tayi jin Anty Amnah na cewa "Hello Batuul are yhu there" kai ta shiga gyadawa tana koma wa baya tace "Eh eh Anty!" fixgota yayi ta fado kansa, bata san lkcn da tace "Wayyo ya Abu kayi hakuri pls" Anty Amnah da ta saki baki tace "Meye haka?" Kamar xata yi kuka tace "Anty ya Abu ne ya ki ya bar ni in ji me kike cewa" Anty Amnah tace "Ji min fitsararre da'alla ka fita ka ba mu waje" Abuturrab ya danne dariyarsa don ya ji ta sarai ya rungumo Batuul jikinsa yace "Toh Anty sorry na tafi" lamo Batuul tayi gabanta na faduwa, Anty Amnah tace "Ya tafi?" A hankali ta dago kai tana kallonsa ya mayar da kanta kirjinsa, tace "Uhm Anty" kunnensa ya kai dai dai nata don jin me Anty Amnah ke ce mata, Anty Amnah tace "Yauwa, wannan garin da kika gani me yawa da milk xaki kada ki dinga sha, shi kuma dayan da honey, you make sure you do that frequently," Batuul tace "Anty na Meye?" Anty Amnah tayi dariya tace "It will make yhu fresh kiyi kyau abun ki, sannan akwae tiger nut da date da aka hado maki cikin kayan sae ki sa ya siyo maki coconut kin dae san yanda xa ki sarrafa ba sae na gaya maki ba ki maida shi drink din ki, sannan ki xama me yawaita shan kayan itatuwa kin ji" daga nan Batuul ta fara gane inda xancen Anty Amnah ya nufa ta ji wani mugun kunya ya rufe ta ga Abuturrab na sauraren Anty Amnah shi ma, a hankali ta dago kai tana kallonsa ta ga kallonta yake yana murmushi turasa tayi ta mayar da wayar daya kunnenta, ya kuma kankameta yana dariya ciki ciki ya kai kunnensa inda ta maida wayar, bbu yanda ta iya haka ta tsaya tana sauraren Anty Amnah, kunya duk ya isheta, ita kanta Anty Amnah tana yi ne tana jin nauyin wasu abubuwan, can dae tace "Bari dae xan maki text kin ji" da sauri Batuul tace "Toh!" Anty Amnah tace "bari in kai ma Ammah wayar ku gaisa koh" Batuul bata iya cewa komae ba har bayan wasu 'yan mintuna ta ji muryar Ammah, suka gaisa Ammah na tambayarta gida tace "Lfya Ammah ina farida" Ammah tace "Tana lfya bitti, ina yayar ta ki" Shiru Batuul tayi sae kuma tace "Ae ta taho Nigeria daxu" saketa Abuturrab yayi da sauri yana kallonta, irin kallon me yasa xata fadi din nan, Ammah tace "Haba lfya dae koh?" Batuul bata damu da kallon da Abuturrab ke mata ba tace "Wae mumynta bata da lfya" Ammah tace "Ayya, ae ko ba mu sani ba nan ma, gobe xan je idan Allah ya yarda in dubo ta, Allah ya sauwake" Batuul tace "Ameen" Ammah tace "Ina Abun fa?" Batuul ta dan kallesa sannan tace "Yana Palo" Ammah tace "Toh ki dae maida hankali a karatu kin ji Bitti, ki kula da tsaftar jikin ki da na dakin ki, Allah maku Albarka" Batuul tace "Ameen Ammah na gode" nan suka yi sallama Batuul ta ajiye wayar, yana mata wani irin kallo yace "na aike ki kiyi announcing matata ta taho Nigeria" kokarin sauka Batuul ta shiga yi daga kan gadon ya fixgota, ta fashe da kuka tace "Don Allah ya Abu ka bari in sa kaya plss" d'an murmushi yayi yana kallon cute lips dinta yace "Wae me Anty Amnah take maki bayani a kai?" Da sauri ta dauke kai ta fara kokarin kwace kanta tace "Oho!" Ya bude ido yace "Oho ma xaki ce? Meye amfanin fruits din da tigernut drink da ta ce ki dinga sha?" Kamar xata yi kuka tace "Wayyo ni ma ban sani ba fa" a hankali ya daura bakinsa kan wuyarta wanda hakan sae da yasa jikinta ya dau rawa, murya can kasa yace "Toh in fada maki na menene ni?" Rikicewa tayi tace "Noo" yace "Okk then, which means kin sani, oya fada min kar in nuna maki abinda take nufi" ta fashe da kuka tace "Allah ban sani ba ya Abu"


πŸ’–πŸ’BATUULπŸ’–πŸ’

62

By phartiemarhk

Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*

Jawota yayi ya d'aura ta kan cinyarsa yasa hannayenshi cikin towel d'in dake jikinta, numfashinta ne taji yana neman d'aukewa jin hannayenshi a k'ugunta, kuka ta saka sosai tace "Yaaa Abuuu dagaske ban sani ba, kayi hak'uri
ka barni", dariya ta bashi ya sake janyota jikinshi ya d'aura bakinshi kunnenta, cikin rad'a yace mata "then, shine zan nuna miki abinda take nufi", girgiza kai ta shiga yi tana hawaye, bata ankara ba sai ji tayi ya juyo da ita tana fuskantarsa, rintse ido tayi dan bata iya kallon idonshi, jikinta sae rawa yake, cikin wani irin murya da taji har cikin ranta yace "open your eyes", sake rintse su tayi kamar abinda yace tayi kenan, a hankali ya sunkuyo yayi kissing idon nata d'aya, wani irin shock taji yabi jikinta, sake rintsewa tayi hawayen na dad'a silalowa, d'agowa yayi yana kallon yadda jikinta ke shivering, kirjinta sai heaving yake, murmushi yayi ya sunkuya ya sake kissing d'ayan, nan ma shivering jikinta ya dinga yi, d'agowa yayi ya sake kallon k'aramin pink lips d'inta da hawaye ya jik'a, har lokacin hannunshi bai bar cikin towel dinta ba, sunkuyawa ya kuma yi yayi brushing lips d'inshi kan nata, a tsorace ta bud'e ido tayi 'yar kara dan ita yanzu Yaa Abu ya fara bata tsoro, murmushi yayi ganin ta bud'e ido don dama haka yake so, lips d'inshi ya maida kan nata ya shiga yi mata wani deep kiss, wani irin ajiyar zuciya ta sauk'e jin yadda yake kissing d'inta, a hankali ya kwantar da ita kan gadon har lkcn bakinsa na nata, ta rike towel dinta gam jin yana kkrin cire mata, kuka sosae take tana kokuwa da shi, da kyar ta kwace bakinta ta turasa da duk karfinta ta mike xaune tana kuka sosai ta shiga komawa baya tace "Am on my period ya Abuu" kallonta ya tsaya yi da idanuwansa da suka sauya kala ko kifta wa bae yi yana sauke numfashi a hankali, ta tsorata ba kadan ba, xata sauka daga gadon ya fixgota yana kallonta cikin husky voice dinsa yace "Na fiki sanin u are not clean, Laifi ne don nayi kiss din ki, ke baki ji dadi ba ma na hada baki na da naki?" Sunkuyar da kai tayi jikinta na rawa bata ce komae ba, murmushi yayi yana kallonta cikin sanyayyan muryarsa yace "xaki gaya min ma'anar tsoron nan nawa da kike, soon" mikewa yayi ya nufi kofa ya fice daga dakin, ta bisa da kallo xuciyarta na bugawa.


Bayan Ammah ta gama waya dasu Batuul, Ammah ta juyo ta dube ta tace "Amnah ashe mahaifiyar Hauwa bataji dad'i ba wae", da mamaki Anty Amnah ta dubi Ammah tace "wacce Hauwa?", Ammah tace "Ajiddeh ko, matar Abu", baki Aunty Amna ta tab'e tace "Au! Allah ya bata lafiya", taci gaba da abinda takeyi, Ammah tace "kaji min yarinya, toh fa har Hauwan ta taho wae yau, kin ga kenan jikin yayi tsanani, ai baza a daka ta halinta ba, auren d'an uwanku ne kanta, dan shi zakuyi ba dan ita ko halinta ba", Aunty Amna tace "Ammah bance komai bafa, addu'a nayi mata", Ammah tace "kin dai ji, tun wuri ku gyara halin nan naku", da murmushi Aunty Amnah ta dubi Ammah tace "Allah ya k'ara nisan kwana Hajiya Ammah, yadda kikace haka za ayi", hararanta Ammah tayi tace "tashi ki koma gidanki, nasan su Nawal da Babansu na can suna jiranki", girgiza kai tayi tace "Ammah kullum sai kin korani in nazo gidan nan, can ma in Babansu na nan babu ruwansu dani shima haka, tare sukeyin komai nasu basa sani, in kuma a can ne baya nan har rasa yadda zanyi dasu nakeyi, shiyasa nake zuwa gidan nan, amma kullum sai an korani", Ammah tace "da bakya barinsu ai da zasu na sakoki a abubuwan nasu, ni yanxu tashi ki tafi, nima yanzu zan shirya a kaini gidansu Hauwan inji ya jikin mahaifiyar tata" mik'ewa Aunty Amna tayi tareda ziran gyalenta tace "Ammah kinga sai muje a tare mu dubata, ko na koma babu abinda zanyi musu in banda wahala da zasu taramin", Ammah tace "A ah ban yadda ba, kama hanya ki koma gidanki sun fi buk'atarki fiyeda zuwa gaisuwan da zakije yi, nima da driver zanje yanzu in dubota, daga baya sai mu koma da Abui", kamin Ammah ta gama magana Aunty Amnah ta shiga dialing number a wayarta, ana d'auka tace "Hello honey, zamuje mu duba Maman matar Abutturab tareda Ammah bataji dad'i ba wllj, you guys should not miss me nasan zakuyi, I will b back shortly", murmushi yayi yace "as though bamu saba ba, you know we are not going to do that, ki gaida Ammah, Allah ya bata lafiya ita kuma, ki gaishesu", tafiyanta Ammah tayi dan tasan halin Amnah, sama ta haura daga nan, Aunty Amnah ma dariya tayi tabita a baya, basu jima da hawa ba suka sauk'o, Aunty Amnah na riqe da keyn mota, tare sukaje har gidansu Ajiddeh a WUSE II, a bakin gate suka tarar da masu gadin su Ajiddeh, da sauri d'aya daga cikinsu ya taso ya fara musu magana cikin Hausarshi da ba dai dai ba yace "Sannunka da zuwa Hajiya, kazo wajen dayan Hajiya na ciki ne", kai Aunty Amnah ta gyad'a mishi tareda cewa "Ehhh", Allahumma salli Ala, kamar jira yake ta gyad'a Kai ya fara zuba "Hajiya, ai Hajiyan ciki dinma baya nan, kwananshi biyu Kenan, dayan Aunty dinne ya fara tafiya tun ya dade sai kwana guda biyu sun wuce sai babban Hajiya din shima ya tafi, toh tun rana din har yanzu basu dawo ba, Alhaji ne kawai yana nan sai masu yin aiki din na gidan suma y'an iska tun Hajiya Babba da ya tafi basa bamu abinci mai dadi yirin na da, toh munason Hajiya ya dawo, Dan Allah kayi mishi waya sai kace mangal ne yace ya dawo Dan ........", hannu Aunty Amna ta d'aga mishi

1 Comments On BATUUL
avatar
hafsat-9-3

12 months ago

Reply

Nice book

Please Login or Register in order to submit comment