Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bata baci ba muje in keh baki iya kare kanki ni zan yi, wlhy ban san asarar haihuwa nayi ba da na zubdashi tun kamin kizo kina cusa min kuttu", ganin Ajiddeh na k'ok'arin k'wace hannunta yasa Mum cikeda fusata tace "kinsan Allah in baki kiyayeni ba sai naci mutuncinki, yarinya ana neman k'watar miki y'anci kina neman yi min tijara? Kuma wlhy kika kuskura kika tozartani saidai gidan wata uwar bani ba, tsine miki zanyi ki k'arasa lalacewa kibi duniyar gaba d'aya", ta fizgota sukayi hanyar d'akin, kan kujera Ammah ta tarar da Abu zaune ya dafe kai yana kallon marbles d'in d'akin, hannun Ammah da yaji jikinshine ya sauk'ar mishi da nutsuwa, hannayenta duka biyu tasa ta tallabo kanshi tareda shafa kanshi tace "Are you okay?", ido ya lumshe kamar maijin bacci da k'yar ya bud'esu yana kallonta ya girgiza mata kai alamun "Yeah am fine", kan nashi ta sake ta kamo duka hannayenshi tace "Badai dukan yarinyar nan kayi ba ko Aliyu, naga ta fice a guje tana kuka", ya kalli Ammah for some seconds snn ya bud'e baki da k'yar yace "I just don't want to see her anywhere around, not now not ever", Ammah da taji dad'in maganganun shi taja wata kujerar ta zauna tace "Alhamdulillah, Allah yayi mana tsari da masharranta, tayi maka admitting d'in sunada hannu ciki koh?," ido kawai ya lumshe ya bud'e dan gaba d'aya hankalinshi na wajen Batuul, ganin baison zancen tace "Ba komai ai ka kwantar da hankalinka, zamu jirayi hukuncin Abui, muji ya za ayi dasu, amma albasa batayi halin ruwa ba dan mahaifinta ba halinsa ba kenan, kuma nasan in har yaji wannan ta'asa da sukayi sai ransa ya b'aci, baiwar Allah yarinya k'arama da ita sun sata cikin azaba, mey sukeso mucewa Maryam ya sami y'arta?", ta matso kwallar dake idanunta tace " koma dai menene dukdai nina jawo shi tunda yarinya na gaban iyayenta hankali kwance nasa aka nema maka aurenta, bayin Allah ba tareda second thought ba suka bamu, Allah dai ya mata katangar k'arfe da mugaye", har Ammah ta gama magana bai bud'e bakinshi yace uffan ba, tunanin Batuul dake dad'a yi mishi yawa yasa ya zame hannayenshi cikin na Ammah ya mik'e yayi hanyar k'ofa, hannu yasa zaiyi sliding k'ofar yaji an rigashi ta d'ayan gefen, Mum ce janye da Ajiddeh ta shigo tana sababi, "Har mu za ayiwa sharri, Bilki kinyi kad'an kuma wlhy hukumace zata rabamu daku, wato tun kiyayyar da kikemin muna yarinta shine ya koma har kan y'ay'ana sai kin bisu da sharri ko, mu za ayiwa k'azafin yiwa wata figaggar yarinya can asiri, billahil azim sai kinyi Dana sani", Ajiddeh da damuwa ya cika ta rasa inda zata sa rai taji dad'i zubewa k'asa tayi tana kuka, Mum ta dubeta tace "Sun sallameki kin zama bakida amfani shine suke tunanin muma munyiwa wata can ko, kai kuma d'an mace an tura maka karuwa kanata cin amanar y'ata shine Dan Allah ya kamaku zaka lak'awa y'ata da bata san zance ba", ido Abu ya rintse yana fisting hannayenshi jin ta dangana Batuul da karuwa, kai yasa zai fice daga d'akin Ammah ta rik'oshi ta jawo shi gabanta tace "Abutturab inajin aure ne ya had'aka da y'arsu tun farko, inaso yanzun nan ba anjima ba ya rabaka dasu, mey za ayi da mugun iri irin wannan?, maza sallamar musu y'arsu, Allah ya had'a kowa da rabonshi", a firgice Ajiddeh ta tashi har wani dishi dishi take gani tazo gaban Ammah ta had'a hannayenta duka biyu tana kuka tace "Ammah Dan Allah kimin rai, nasan ban tab'a zame miki sirikar kirki ba, babu abin arziqi da na tab'a yi miki amma Dan Darajar Annabin tsira da aminci kar kisa ya sakeni, nasan ko bai sakeni ba tunda yace bai kuma son ganina nasan mutuwa zanyi, ki yafemin, ki roka min yafiyar Batuul ki rok'a min yafiyarshi in mutu da aurensa akaina, badan halina ba sai dan nasan ke uwace ta gari mai halin dattako, inayiwa d'anki son da bansan adadinshi ba a rayuwata", sanyi jikin Ammah yayi amma ko kallonta batayi ba tace "Babana ina jiranka, ka sallamesu su bar min gida", Jiki a sanyaye itama Ajiddeh ta kalleshi amma ko kallon inda take baiyi ba ya karb'e hannunshi daga rik'on Ammah ya fice daga d'akin, Duka Mum ta d'aka mata tace "Dan uwarki sai ki tashi tunda ke asararriyace, ban taba sanin ke mara hankali bace sai yau, har uwarsa ta bud'i baki tace ya sakeki uwar mey zaki zauna yi gidanta, kike wani cewa keh kinsan uwace ta gari ita, da y'arta ce baza ta tsaya....", ko kallonsu Ammah batayi ba ta fice daga d'akin itama, a guje Ajiddeh ta biyo Ammah tana ci gaba da magiya, Sau d'aya Ammah ta dubeta tace "Ba yafiyata zaki nema ba, wacce kika cutar zaki tambaya ta yafe miki", har ta sauk'o k'asa bata dena binta abaya ba, Abui da Farida tare suka fito jin hayaniyar Ajiddeh da Mum, kallon Mum yayi yace "Bilkisu lafiya?, mey ya sameta?", jin muryar Mum sukayi tana cewa "Ki fita harkar k'ananan mutane kizo mu wuce, kema uban ki nada gidan", Abui ya kalleta jin mey take fad'i snn ya kwalawa Abutturab k'ira, ba b'ata lokaci ya fito d'akin da Batuul ke kwance, yana ganin Ajiddeh ya had'e rai, Abui ya dubi Ammah yace "Mey yayi mata kina wajen baki hanashi ba", Ammah ta had'e rai ta tab'e baki tace "cewa nayi ya saketa", Abui ya dubeta da kyau jin abunda ta fad'i yace "Kan wane dalilli zakisa ya saki matarsa?, kaji shirme, kai Aliyu da hankalinka zaka saki matarka, kuskurene tayi kuma yarinya Allah ya tashi kafad'unta sai dai fatan Allah ya tsare gaba", Ammah ta fashe da kuka tace "Abui ya saketa kawai, dubi fa yadda suka cutar da Fatima amma uwarta ke musun sharri mukayi musu har da cewa k'ara zata kai mu munyi musu sharri", Sai lokacin Farida ta fuskanci kan zancen, Ajiddeh ta duba da wani mugun kallo ta tab'e baki ta matso wajen Ammah, Mum cikeda masifa tace "Yo ba Sharrin kukayi mana ba, wacece Maryam ma bare Fatimar har a wani yi mata asiri, kai kaga", ta nunawa Abu yatsa taci gaba "In ka fasa sakin nata baka cika haifaffen d'an bilki ba", Abui da mamaki yake kallon Mum, Abutturab da tunda yazo ya kasa d'ago kai a hankali cikeda nutsuwa batareda ya kalleta ba yace "I don't need a second thought, get out of my sight before I loose my cool, before you regret ever knowing me", yana fad'in haka ya juya batareda yabi ta kan kowa ba", Ajiddeh na jin haka ya fito daga bakinshi kuma a gaban Abui tasan zamanta gidanshi ya k'are, har wani dishi dishi take gani ta miqe tayi waje cikin hanzari batareda ta kula kowa ba ta fita a guje, Mum ce ta bita a baya tana kwala mata k'ira, girgiza kai Abui yayi yace Allah ya kyauta yayi sama , bayan kamar minti biyu Mum ta sake shigowa ta nuna Ammah da d'an yatsa tace "duk mey zai Samar min 'ya wlhy ki kuka da kanki", ta juya ta fice fuuu kamar wata iska


Yana komawa d'aki ya d'auki Batuul cak a hannunshi ya rungume ya fito da ita, ganinshi riqe da Batuul Ammah ta tambayeshi "lafiya ka d'aukota, ko ta tashi ne?", kai ya kad'a mata yace "Inaso ne ta huta a saman" snn ya k'ira Farida ta biyoshi, yana shiga d'akinshi ya kwantar da ita kan gado, dai dai nan Farida ma ta shigo, yace "Je ki samo mata kaya mara nauyi, I want her to change", kai ta kad'a mishi tace "okay", ta fice, ya kurawa fuskan Batuul ido y'ana kallonta a hankali ya kamo siraran yatsunta ya kai bakinshi ya manna mata kiss yace "I love you Batuul", kamar taji abinda ya fad'a a hankali ta bud'e ido ta kalleshi, ido ya lumshe ya bud'e yana so ya tabbatar dagaske ta farka, da sauri ya matso yana riqeta yace "Alhamdulillah, am glad kin farka", murmushi tayi mishi ta shiga k'okarin tashi ta zauna, shima d'in murmushin yayi mata ya rungumeta jikinshi yana lumshe ido yana shak'ar k'anshinta da yakeso a koda yaushe, jin yaqi saketa yasa ta d'an turashi, ya d'agata daga jikinshi yana kallon fuskanta, hawaye ya gani cike da idonta kuma har lokacin da murmushinta a fuska ta k'arewa d'akin kallo tace "Yaa Abu inane nan?", ya dad'a matso da ita kan cinyarshi yace "Cry no more kinji, baza ki sake kuka ba sai na farin ciki In sha Allah, We are home, and you will be safe here in sha Allah", Farida ce ta shigo riqe da kaya a hannunta, watsar da kayan tayi ta fasa ihu ta hawo kan gadon ta k'ank'ame Batuul tace "Alhamdulillah, omg Batuul am happy kin warke, don't fall sick Dan Allah kinji?", sai kuma ta fashe da kuka, Abu ya kalleta yace "Keh mey haka, kin shigo kina ihu, ina aiken da nayi miki?", Farida ta cunno baki tace "Yaa Abu am just happy my friend is well again", Batuul tayi murmushi ta kamo hannunta tace "Yeah Alhamdulillah, am feeling much better now, Ammah fa", zata bata amsa yace mata "Leave", ta zumb'uro baki ta sauk'o daga kan gadon, Batuul ta kalleshi da idanunta da sukayi raurau tace "Yaa Abu mana, let her stay", bai kulata ba ya sake kallon Faridan data fita kamar mai shirin karya k'ofan, ya kalleta yace "Baby you hungry ko?", kai ta girgiza mishi, hancinta ya d'an ja yace "Nasan kina jin yunwa, and my lil champ too", ya kai hannu kan mararta, sam ta manta da wani ciki a jikinta sai yanzu, murmushi kawai tayi mishi, yace "Let's freshen you up, sai kici abinci", tace "Ni bacci zanyi, am not hungry", tashi yayi ya tattare kayan da Farida ta watsar snn ya dawo kan gadon ya shiga k'ok'arin cire mata kaya, hannunshi ta riqe tace "Zan cirefa", kamar baiji mai take cewa ba yaci gaba da abinda yakeyi, cak ya d'agata yayi toilet da ita, wanka yayi mata tayi brush snn tayi alwala ya d'aukota suka fito, shi ya shiryata ya canja mata kaya, a lokacin Ammah da masu aikinta suka shigo da abinci, ba abin mamaki bane dan tasan irin son da Ammah ke yi mata tun kamin ta auri d'anta, ranan ko Sallah Abu bai fita ba a d'aki yake yinshi ya jasu jam'i, lokaci lokaci Ammah ke shigowa dubata, da daddare ma shi yayi mata wanka ya shiryata cikin kayan bacci snn ya tofa mata addu'a tareda ja mata bargo,wutan d'akin ya kashe ya jawota jikinshi yayi pecking lips d'inta yace "Have a sound sleep Haya", sake shigewa jikinshi tayi, a hankali kamar mai rad'a tace "Ban ganta ba duka yau?, ina ta tafi?, kamar baiji abinda tace ba ya dad'a gyara mata kwanciya yace "You need rest, kiyi bacci", sake maimaita mishi tambayar tayi tace "Yaa Abu mana, she needs to know na warke, ina Ajiddeh?", jin ambaton sunan Ajiddeh yasa yaji abubuwa da dama na taso mishi, hannunta ya kamo cikin nashi yace "Fatima Kiyi bacci Dan Allah", k'ok'arin tashi ta shigayi tace "Toh ina taje mana, I just need to know", a fusace ya janyota yace "I will slap you right away in baki kwanta ba, bakisan you are still weak bane? komawa tayi ta kwanta, ajiyar zuciya yaji ta sauk'e, yaja d'an tsaki, bada son ranshi yayi mata fad'an nan ba, so yake ya dena tunawa da Ajiddeh, gabanshi har fad'uwa yakeyi in ya tuna abinda tayi, he have to caution Batuul d'in da kanta ta dena tuna mishi da ita, atleats for the mean time, ajiyar zuciya ya sauk'e ya rungumota jikinshi yace "Am sorry Fatima", bata ce mishi komai ba, hakan yasa ya mirginota tana fuskantarshi yace "You should rest Fatima Dan Allah, I love you"

[11/22, 11:21 PM] ‪+234 803 698 6494‬: 💖💝BATUUL💖💝






89






By phartiemarhk






Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*




      Ba Zuciyarta kad'ai ba , har jikinta rawa yakeyi jin kalaman da suka fito bakin Abu, tasha jin ana fad'in wadannan words d'in a films da kuma novels amma bata tab'a tunanin  haka mutum keji ba in aka furta mishi su, bata tab'a jin irin wannan abinda take experiencing ba yanzu, wani irin fad'uwa gabanta ya shiga yi lokaci d'aya zuciyarta na mata nauyi, hawaye ne taji yana gangarowa kan  fuskarta, ta d'auka baza ta tab'a jin wad'annan kalaman daga wajen wani ba bayan y'an uwanta, shak'ik'anta, tasha jin Farida na ce mata "I love you" duk randa wani abin farin ciki ya giftasu a lokacin, batasan mesa wannan ya fita daban ba, wannan har cikin ranta take jinshi gabanta na tsananta faduwa, she wasnt expecting it, not from him, tunani takeyi itama kamar yadda taji ana fad'a a movies "I love you too zatace?, ta dad'e da sama ranta salama akan jin wadannan kalmomi sabida tasan har sai in ana sonka za a nuna maka, batasan ko tana son nashi ba but tasan yayi casting effect ba kad'an ba cikin rayuwarta, jin tayi shiru snn jikinta na kyarma yasa Abuuturab dafata, kamar jira take taji hannunshi jikinta ta fashe da wani irin kuka, da hanzari ya miqe ya zauna tareda kunna bedside lamp d'in snn ya d'agota, ganin hawaye shimfid'e fuskarta yasashi furta "Subhanallah, Batuul kuka kuma, kinsan I hate jin kukanki, Dan Allah kiyi shiru, am sorry kinji, you don't have to love me back, its okay, ni d'in I will love you with all my myth kinji, just keep yourself safe for me, Be happy", kamar wacce aka daka sai ci gaba da kukan nata takeyi, hannayenta duka biyu ya kamo cikin nashi ya d'an murzasu a hankali yace "Its okay I won't say it to you again tunda bakiso, I promise, kwanta ki huta kinji, its getting late", har lokacin batace komai ba sai jinta take kamar akan iska take zaune, rungumeta yayi ganin kukan nata yaqi tsayawa, jin ya rungumeta yasa feeling d'in da take experiencing yafi Nada,bakin shi ya d'aura daidai kunnenta ya d'an hura mata iska yana patting bayanta snn cikin rad'a yace "Shhhhh, I won't say it again kinji, its a prom....", kasa k'arasa maganar yayi jin fragile tiny hannayenta da tasa ta zagayeshi ta baya dukda ba k'arasawa sukayi ba, nutsuwa da baisan yana da ita ba a yau yaji na ratsa shi jin hannayenta zagaye jikinshi, wani irin ajiyan zuciya ya sauk'e tareda sake k'ank'ameta a jikinshi ya lumshe ido yana shak'ar k'anshinta, dukda yadda yakejin heartbeat d'inta is at a faster pace amma bayason wannan yanayin ya wuce shi ko kad'an, sunfi minti biyar a haka snn ya d'an sassauta rik'on ya d'ago hab'arta, har lokacin idonta lumshe suke, kallon kyakkyawan cute face d'inta yayi da yadda lips d'inta suka koma pink sbd kuka tana d'an twitching d'insu,murmushi ya saki yanajin wani kasala na sauk'o mishi tareda sunkuyowa ya had'e goshinsu waje d'aya sunajin sauk'ar numfashi su na fanning juna, a hankali ta bud'e idonta jin yayi shiru ko motsi bayayi, suna had'a ido tayi maza ta mayar ta rufesu, hannunshi ya d'aura bayan kanta d'ayan kuma kan waist d'inta ya matso da kan nata ya cikata gap d'in dake tsakaninsu, lips d'inshi yayi crashing kan nata har wani sauk'e ajiyar zuciya yayi ya shiga kissing d'inta with passion, batasan sanda ta fara maida masa martanin kiss d'in da yakeyi mata ba a hanKali, saida ya gaji dan kanshi ya k'yaleta yana maida numfashi, jawota yayi ta fad'a kanshi shima ya fad'a ya kwanta, hannu yasa kan lips d'inta yana making circles,yana shaping lip d'in nata a hankali, yana sata jin kamar ana royal rumble a cikinta, rintse ido tayi da k'arfi dan baza ta iya d'aukan feeling d'in da takeji ba yanzu, cikin maganarshi da ke dad'a sata jin wani iri yace "I missed you, your kiss though.....", sake shigewa jikinshi tayi batace komi ba ta k'ank'ameshi dan tasan mey yake shirin cewa, dukda bata ma ganin fuskanshi tasan murmushi yayi jin chuckles d'inshi datayi, turo baki tayi ta kai mishi dukan wasa tace "But I did well today ai", caraf ya rik'e hannun ya d'an matse, d'an k'ara ta saki tace "oucchh, it hurts mana Yaaa Abu, let me be I want to sleep", "That's exactly what I want you to feel, its okay you not loving me, but then missing me, shima bakiyi?", shiru tayi kamar bazata yi magana ba, batasan much about love ba ita, batasan ya yakeba, dukda taji wani al'amari na daban d'azu da ya furta mata yana sonta amma har yanzu ta kasa gane yaya wanan feeling d'in yake, she doesn't know if she loves him but missing d'inshi, ko bata fad'a mishi yasan she did, yasan tayi kewarsa, she is used to him now, kamar zatayi kuka a shagwab'e tace "Toh do I have say it, ai kasan nayi, much more than you do, I missed you more", ko da wannan ta barshi zaiyi baccin farin ciki ba sai ta furta son da take masa ba, yasan with time kamar yadda ya samu kanshi da sonta, yadda ya shigeshi farat d'aya ba tareda ya tab'a kawo hakan a ranshi ba, itama zata soshi da yardar Allah, murmushin dake fuskarshi ya fad'ad'a ya gyara mata kwanciya, bayanta na a jikinshi yayi cuddling tiny figure d'inta da duka hannayenshi biyu, Addu'a ya kuma yi, saida ya gama ya tofa ya shafeta dashi , ya sauk'o da hannunshi saman cikinta cikin rad'a yace and "Lil princess too, sleep safe Daddy loves you" snn ya shafawa kanshi ya dad'a matso da ita jikinshi yaja duvet ya  kashe musu bedside lamp d'in, Batuul duk rufe ido da zatayi kalmar "I love you" d'innan ke ringing cikin kanta, ta kasa dena jiyoshi, batasan lokacin da bacci ya d'auketa ba a haka, saida ya tabbata tayi bacci snn ya fara tunanin abinda ya faru yau, mesa Ajiddeh zata mishi haka, does he really deserve this?, laifin nashi ne, meyasa suka zab'i Batuul ba shi ba, how could she be so heartless and cruel, duk irin wannan azaba da Batuul tasha was because of her, wani d'aci yakeji daga mak'oshinshi, ya tabbata da wani ne ba Ajiddeh ba to da saidai yayi kwanan prison, ido ya rintse yana son kawar da tunanin, daga haka bacci ya d'aukeshi

      
         Tana fita Allah yasa taci karo da cab, lokacin da Mum ta fito bata ganta ba drivern ta dake zaune yana jiran ta tambaya ko yaga Ajiddeh yace yaga fitanta a guje, komawa tayi ciki tayiwa Ammah gargad'in wani abin in ya samu Ajiddeh she wont take it lightly, snn ta fito suka tafi da driver, sai kalle kalle takeyi ko zataga Ajiddeh, saida sukaje gida taga cab d'in parke k'ofar gida, ta tambayeshi ko shi ya kawo Ajiddeh by description yace ehhh amma bata bashi kud'i ba kuma ta fita ba tareda bayani ba, Mum ta ciro kud'i cikin jakarta ta mik'a mishi ta koma mota driver ya k'arasa da ita cikin gida, sak'e sak'e kawai takeyi a ranta, abubuwan sun mata yawa as of this time, batasan da wanne zata fara bama, komai ya dagule mata lokaci d'aya, masu aikinta ta kwalawa kira sukazo su biyu a tare, ta tambayesu ko sunga shigowar Ajiddeh, "Ehhh ta shigo amma tayi side d'in can na gefen na Sir", Mum ta wara ido duk da tasan nan ne wajen zuwan Ajiddeh duk lokacin da ranta ya b'aci tace "Ba nan aka ajiye matar nan ba da Daddy ya mask?", sukace "Nan ne Hajiya", tace "Kuje, Keh Sadiya ki tabbata kin kai mata abinci da duk abinda zata buk'ata snn ku zauna kuna lura da ita da duk motsinta", suka amsa kai da baki suka fita, suna fita ta janyo waya ta shiga neman layin mutum d'aya da tasan lallai zai samar mata mafita





         K'arfe hud'u Abu ya farka, har lokacin yana jin Zuciyarshi bata mishi dad'i, idonshine ya fad'a kan Batuul da yasashi jin wani sanyi cikin ranshi, ya lumshe ido ya bud'e snn ya gyara mata kwanciyarta kamin ya sauk'o da k'afafunshi a hankali dan bayason yayi motsin da zata farka ya mik'e ya shiga toilet, wanka yayi tareda yin alwala ya fito ya zira farar rigarsa ya shimfid'e abin Sallah ya hau, raka'a biyu yayi snn ya d'auko Qur'an kan shelf ya fara karantawa a nutse yadda bazai tasheta ba, saida ya karanta Rabin Suratul Tauba cikin kira'arsa mai dad'i snn ya dakata yayi addu'o'insa, jin ana k'iran Sallah ya tashi ya gabatar da raka'atanil fajr kamin ya koma kan gadon, bayason fita ya barta ita kad'ai a d'akin, shi zai jasu suyi Sallah tare , hannu yasa ya shafi gefen fuskarta a hankali ya shiga k'iran sunanta, "Fatima wake up, lokacin Sallah yayi", a hankali ta bud'e idon da ya cika da bacci snn ta mayar ta lumshesu, murmushi yayi yace "You sleep too much, Sleepy head", tashi kiyi Sallah, its time", sai a lokacin taji mey yake fad'i, zuciyantane ya fara pounding tunawa da jiya da tayi, words d'innan na ringing cikin kanta, sake rintse ido tayi ta kasa bud'ewa, tsoron bud'e ido takeyi kar daren jiya ya zame mata mafarki, She have longed to hear someone say he love her, duk da ba sani tayi tana son nashi ba bataso wannan karon da ta samu taji ya zama mafarki, "Fatima", sulalewa tayi daga jikinshi tace "Toh kayi nima zanyi nawa anjima", mamakinta ne ya cikashi ganin taqi bud'e ido amma tana magana yace " Fatima Open your eyes", kamar baza ta bud'e ba a hankali ta bud'esu ta sauk'esu kanshi, cak ya d'auketa yayi toilet da ita, ya zaunar bakin bathtub d'in, brush d'inshi ya samata toothpaste ya mik'o mata, turo baki tayi ta ansa ta shiga wanke bakinta, tana gamawa ya jawo kan shower ya shiga tsiyaya mata ruwan, saida ta gama alwalan snn ya sake d'aukarta cak ya fito da ita ya saka mata dogon Hijab d'inta dake ninke gefe, saida suka idar yace "Tashi kiyi rak'atainil fajr", mik'ewa rayi ta jero raka'a biyu snn ta bishi suka ci gaba da addu'a, Hannu yasa jikinta yaji temperature d'inta yace "Good morning", kallonshi tayi taga murmushi shimfid'e fuskarshi, bata tab'a ji ya gaidata ba sai yau, kuma from his look its sincere, a hankali cikin jin kunya tace "ina kwana", ya rik'o hannunta yace "Baki amsa min ba", sunkuyar da kai tayi batace komai ba, "How you feeling right now?, kinajin wani ciwo?", kai ta girgiza mishi tace "Am fine", ya sauk'e ajiyar zuciya yace "Mai idon bacci, go back and sleep", mik'ewa tayi ta cire Hijabin ta ninke zata koma gadon taji ya rik'o mata hannu, yace "Hey, My princess, I couldn't say Hi to her", juyar da kai tayi tayi murmushi snn ta dake ta kalleshi tace "Its not like I care" ta k'wace hannunta ta koma kan gado, yayi dariya yace "Really?, well her Papa cares, Say Hi to her for me pls and tell her that Papa Loves her so much ", murmushi tayi ta shige cikin bargo tanajin kamar moment d'innan yayi ta zama haka, kada komai ya canja mata, cikin baccinta taji an rungumeta ta baya, gyara kwanciyarta tayi suka koma bacci, k'arfe goma ya farka itama ya tasheta, wanka ta farayi snn ya k'ira Farida a waya ta kawo mata kaya ta saka, bacci ma takeyi kasancewar yau weekend, idonta cikeda bacci ta taso ta kawo mata kayan, sai wani irin kallo take bin Batuul dashi tana dariya k'asa k'asa, Hararta Batuul tayi ta anshi kayanta tace "Kyaji dashi dai", bakin gadon ta zauna tace "Keh ni mey nace miki toh, kawai dan nayi dariya", Abu ya fito daga toilet, ya kalleta yace "kayan fa?", nuni tayi mishi dasu tace "gasu nan", yace "zaman na meye toh?", ta zumb'uro baki ta mik'e zata fita tace "Ammah tace ince muku

1 Comments On BATUUL
avatar
hafsat-9-3

12 months ago

Reply

Nice book

Please Login or Register in order to submit comment