Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tace "of course I do know, shiyasa ma nake son nashi, ni wlhy na tsani saurayina ya fini koda five yrs bazan iya auren babba ba, ni kunyanshi ma zan rik'aji, Affan is d perfect guy for me, I soooo much love him to d extent da in akace za a rabani dashi I can jump through d window", dariya sukasa dukkansu biyun, Batuul tace "kin manta from d terrace dai", suka sake sa dariyan, Farida tace "Kinsan I had a crush on Affan tun farkon ganina dashi, I always get jealous yadda kuke, I tot ma soyayya kukeyi yadda naga you guys are so close, saida kikace min wai he wants to ask me out, wai inja mishi aji, ai ba Iya zan ba, wlhy ranan I couldn't sleep, Allah na rik'a yiwa godiya, dan dama kullum sai na rokeshi, I was just happy", dariya Batuul tasa tace "We have been best friends tun childhood d'inmu, His Mom and Aunty were cousins, kuma best friends, Aunty tana fad'a min lokacin suna Uk tareda su Ammah, she have been married for nine years amma bata samu haihuwa ba, Shekaran da akayi aurenta shekaran aka haifi Yaa Abu da Massa, kuma lokacin Ammah da Yaa Mera suna aiki, gidansu a Jere yake su ukun, dama mazajensu abokai ne sosai tun yarinta, Baba, Abui sai shehu, toh Aunty ce kad'ai bata aiki, kinsan Fulani tana gama secondary school akayi mata aure, Baba kuma yace yafi son saita haihu taci gaba da zuwa makaranta, toh a lokacin nefa sai su Ammah su rik'a kawo mata su Yaa Abu gunta in zasu aiki, ita tayi rainonsu, daga baya ma sai komai nasu ya dawo wajen Aunty, har lokacin da suka shiga school, lokacin da suka cika Nine years, lokacin
Aunty ta samu cikina, kowa yayi murna sosai, cikin Aunty nada wata shida aka yiwa Baba transfer ya koma Nigeria, lokacin yace zai tafi da Aunty, su Abui sukayita insisting ya bar Aunty dan its risky tana yawo at this stage of pregnancy, gara ya riqa zuwa yana dawowa, yace hankalinshi bazai tab'a kwanciya ba, gara ya tafi da matarshi, lokacin su Yaa Abu sun gama year 6 dinsu na makaranta shida Massa, sunsha kuka da Aunty zata tafi, especially Yaa Abu, dan komai da Uwa zatayiwa d'anta tayi musu, tacema su suka sa mata sunan Aunty har yabita muma muke k'iranta dashi,dan shi Yaa Abu cewa ma yayi zai bita, da k'yar aka samu Baba ya rarrasheshi yace anytime sukayi hutu zai turo a d'aukesu, Da haka ya tattara suka koma Nigeria, dama lokacin Maman Affan(Sakina) ta haifeshi shekaranshi biyu da wata goma, da zai cika shekara uku Aunty ta had'a mishi birthday party a gidanmu, wai zatayi compensating rashin zuwa sunanshi da batayi ba, ana cikin shagalin party Aunty ta fara labour, nan akayi rushing d'inta asibiti, bata sha wani wahala ba ta haifeni, toh kinji wannan shine yasa I became close with Affan, mun shak'u sosai, he became d elder brother I never had, He is my birthday mate, kullum tare ake mana celebrating, kuma shi gidansu Affan sai sun sauk'e Qur'an suke shiga school, su Yaa Abbass duk saida sukayi sauk'a kamin suyi joining school, Affan ne kad'ai ya shiga school lokacin yanada haddar izu sittin, kinsan yadda kan mutumin naki yake, yanaja sosai, shiyasa aka turashi makaranta akace zai iya hada duka biyun, lokacin da nake shekara biyu, lokacin Kakan Massa ya rasu aka nad'a Baban Massa sabon sarki, Amma ma tacewa Abui itama baza ta zauna ba tunda duk y'an uwan nata basa nan, shima haka suka tattaro suka dawo, su Yaa abu kuma nan aka barsu sabida school, kin dai ji how I became close with Affan", Farida tace "Wow, so you know this much shine baki tab'a fad'amin ba", dariya Batuul tayi tace "komai da lokacinshi, gashi nan yanzu da lokaci yayi kin sani", Farida tace "Tell me, how does it feel to b married, like how do you feel, ya kikeji duk lokacin da kika tuna kinyi aure?", bata amsa ba sai ma tambayar da ta jefa mata itama tace "How does it feel to b in love, ya kikeji?, wara ido Farida tayi tace "Lallai ma, keh zan tambaya wannan ma ai, ko zakice min you are not in love ne har yanzu, I just saw it da idanuwa kina nunawa Yayana soyayya", ta k'arashe maganan tareda kashe mata ido d'aya, dariya Batuul tayi ta mik'e tace "You are not serious", daidai lokacin Yaa Abu ya shigo d'akin, Farida ya kalla yace "abincin suna k'asa go and arrange them", simi simi kamar munafuka ta mik'e ta fita, Batuul ya kalla yace "nan zakici abinci ko k'asa?", cewa tayi "Ni na tab'a cin abinci a k'asa ne, a d'akina zanci, ko dan kaga Farida?", kai ya kad'a, baya ji da rigimarta yace "sai ki sauk'a ki kwashi abubuwan naki" da haka ya fita






D'akin da ya zama nashi ya koma, a bakin gado ya tarar da Ajiddeh zaune da wata irin shiga, d'auke kanshi yayi kamar bai ganta ba ya shiga cire kayan jikinshi, tasowa tayi ta shige jikinshi, had'e rai yayi ya turata daga jikinshi, sosai ranta ya b'aci amma da yake nema take su shirya haka ta koma gun nashi, ta sake mannewa a jikinshi, hannu yasa zai janyeta tace "Haba babe meye ne haka kake min, indan abinda nayi d'azu ne am sorry, I promise you bazan sakeba, d'azun ma sharrin shaid'an ne da kuma irin son da nake maka, bana iya jure ganin wata mace kusa da Kai, amma kayi hak'uri kaji babyna", cire hannayenta yayi daga jikinshi yace "Ai this is not your first time na bani hak'uri, kinsha bani kuma kike sake aikata laifin, abinda kikaga yafi dacewa dakene kikeyi, keep on with it", marairaice mishi fuska tayi kamar dagaske tayi nadama tace "Am serious this time, bazan sakeba kaji?, in kanaso har ita zanje in bawa hak'uri", ajiyar zuciya ya sauk'e yace "Ban aike ki ba", tace "toh ka hak'uran?, tsakanin mata da mijinta sai Allah, kai kawai ya gyad'a mata ya juya yayi toilet, biyoshi tayi tana cewa "Let me help you", tare sukayi wankan, shi ya d'aukota a hannunshi suka fita, bayan sun kintsa take ce mishi "Baby jibi fa Aunty na zata koma", ya kalleta yace "Soon?, mey tazo yi dama?", shiryayyar k'aryar da zatayi mishi ta rasa, batasan lokacin da tace "kasan dama d'an mijinta anan yake karatu, toh wai zasuyi convocation d'insu shine tazo tayashi murna", kai kawai ya gyad'a yace "Okay Allah ya kaimu, gobe kamin in fita you remind me", saida suka gama shiryawa yace "Food is downstairs, sai ki d'ebi na Aunty ki kai mata", da haka ta fita shi kuma yayi shirin fita, washe gari ma haka yaje ya samo musu abinda zasuci, da yamma Batuul take ce mishi Farida zata kai wa wata k'awarta da tayi aure ziyara a Birmingham saida ya gama musu tambaye tambayenshi tukunna ya yadda sannan ya had'ata da David suka tafi.






Washe garin ranan da Aunty Jainaba zata tafi, da safe Batuul ta sauk'o, wainar fulawa kawai takejin ci tunda asuba, tana kitchen tana y'an aike aikenta taji su Ajiddeh sun sauk'o, bata bi ta kansu ba ta tab'e baki taci gaba da aikinta, zama sukayi a parlour suna cin abincin da sukayi ordering, a guje sukaga Batuul ta fito toshe da bakinta, bata bar parlour ta tsuguna ta dinga kwarara amai a wajen, da ido suka kalli juna, Aunty Jainaba ta xaro ido tayi kasa da murya tace "Keh anya wannan shegiyar yarinyar ba ciki gareta ba kuwa, kullum sai tayi amai, toh na menene?", Ajiddeh dake ta kallon Batuul ita ma murya can kasa tace "Ai ni so nake ma hakan ya kasance ta tattara ta barmin gida, nasan in har ya tabbatar cikine toh ba yadda za ayi ta zauna, maidata gidansu zaiyi, ya Allah ka tabbatar da hakan", dai dai nan Abutturab ya sauk'o don shima ya ji k'ak'arin aman nata, da sauri ya k'araso ya d'agota ya rungume yana k'iran sunanta, suna ganinshi suka mik'e, gaba d'ayansu sai da zuciyarsu ta doka ganin yadda ya rungumeta, ita kam Ajiddeh ma sai gani tayi sun mata kama, Aunty Jainaba ce ta wayance da cewa "yi sauri ki mik'a mata ruwan Ajiddeh, sannu kinji", Batuul kam bata ma san mey suke cewa ba, haka shi ma don duk hankalinsa ya tashi ganin yanda take aman, k'arasawa wajensu Aunty Jainaba tayi damuwa dauke fuskarta kamar gaske tace "Aliyu bai kamata a barta haka tana ta ciwo ba a gida, akai ta asibiti dan aman nan nata yayi yawa, kar aje ba a saniba wani ciwon ne yake damunta har yayi mata illa, ku kaita asibiti yanzu gskya, dubi yanda duk ta galabaita" sai da ya tabbatar ta gama aman snn ya d'auketayayi sama da ita, Ajiddeh ta bi su da harara xuciyarta na tafarfasa, jikinta ya gyara mata ya canja mata kaya snn ya sauk'o da ita, numfashi kawai take mayarwa duk jikinta yayi laushi, David ne ya shigo daidai lokacin, Abu ya kalli Ajiddeh yace "Tunda ga david ku tafi airport kawae ni xan kai ta asibiti" caraf Jainaba ta anshe tace "Kai haba mu tafi asibitin gaba daya kawae Aliyu babu komai" yace "Xa ki iya missing flight kuma, kawae ku je bbu damuwa" bata so haka ba amma bbu yanda ta iya tace "toh shikenan, bari muje in d'auko kayana, Allah ya kara miki lafiya y'ar nan" ta ja hannun Ajiddeh sukayi sama, suna shiga d'aki tace "kina jina, kada ki sake ki wani bini airport, kije asibitin ayi komai kan idonki, sai muga ta fad'i, shegiyar yarinya mai kama da y'an Ethiopia ni na tabbata ba komai bane wannan banda ciki, ni kaina yanzu tsanarta k'aruwa yakeyi a raina wllh", Ajiddeh tace "toh", suka janyo akwatin suka sauk'o, inda tayi aman ya gama gyarawa snn ya koma ya d'auki Batuul d'in zasu fita, daidai nan suka sauk'o, har ranta takejin yadda ya rungume Batuul a jikinshi, danne zuciyarta tayi tace "Baby kaga why not mu tafi tare, kaga jikinta is very critical, you might need help, I will go with you, Anty xata tafi airport din ita kadai, she will understand", kallonta yayi yace "No ki tafi Airport din da ita its okay I will manage", Aunty Jainaba ce tace "Ah ah Aliyu ba komai ai, ba sai ta bini ba, ga mara lafiya nan, ita tafi buk'atarta ai, kuje kawai, Allah ya bata lafiya" ganin suna b'ata mishi lokaci kawai ya d'auki Batuul yacewa Jainaba, "Allah ya kiyaye hanya ya fita", Jainaba tace "maxa Bishi", da sauri Ajiddeh ta bishi ta shiga gaban mota, badan yaso ta bishi ba, a baya ya kwantar da Batuul snn ya dawo gaba ya seta rear mirror d'inshi daidai yadda zaina monitoring d'inta, motar su Jainaba ce ta fara fita sai nasu daga baya, kowa yayi nasa hanyan, suna isa asibitin ko reception bai tsaya an duba mishi file ba ya shiga office d'in doctor d'inshi kai tsaye, Ajiddeh ma jiki na rawa tazo zata kutsa kai cikin office d'in ya kalleta rai a had'e yace "stay outside, ki tsaya daga waje, bbu amfanin shigan ki", ba dan taso ba haka ta koma daga baya ta zauna kan d'aya daga cikin kujerun wajen rai b'ace, da sauri likitan ya taso ya karb'eta suka kwantar da ita kan gadon office d'in, gaba d'aya abin nan da akeyi batasani ba dan bacci takeyi abinta tun mota, hannu kawai Abu ya kalmashe sai rocking yake kan kujera yana ganin likitan na aikinshi cikeda k'warewa, saida ya ya gama gwaje gwajensa sannan ya dawo ya zauna kan kujera, Hannu ya mik'a mishi da murmushi a fuskanshi yace "congratulations, you are going to be a Father, your wife is one month and few days pregnant", gaba d'aya jin maganar yayi wani iri, ya kasa daina kallon likitan, he wasn't expecting it, Batuul is pregnant?, bai janye hannunshi ba har saida likitan ya janye nashi snn yayi maza ya janye hannunshi, ganin irin kallon da likitan ke mishi yyi saurin k'irk'iro murmurshi, take ya nunawa likitan yaji dad'i sosai, a kanshi kuwa Ajiddeh yake hangowa idan taji wannan lbrin da yake ji, likitan ne ya katse mishi tunani tareda prescribing mata magunguna da advises kan abinda zata riqaci, da kuma wad'anda are not good to her health, ita dai har lokacin baccinta takeyi, mik'ewa likitan yayi zai bar office d'in yace "Mr Kyaree, I will be right back" a hankali ya mik'e ya isa bakin gadon yana kallonta ko kiftawa bai yi, likitan na fita a bakin k'ofa ya kusa cin karo da Ajiddeh, da sauri ta koma baya tana yak'e, murmushi yayi mata yayi gaba abinshi, a guje ta biyo bayanshi da damuwa kamar gaske fuskarta tace "Excuse me doctor" juyowa yayi yana kallonta, tace "Hope she will be okay, I don't want anything to happen to her, she is my only Sister, tell me what is wrong with her Doc", murmushi yayi yana girgiza mata kai yace "Yeah she is okay, she will b fine surely, congratulation your sister is pregnant", kwalalo ido tayi waje da dafe k'irji tace "What?", ganin irin kallon da yake mata yasa tayi maza ta kirkiro murmushi tace "Omg, Am happy, Thank you sooo much Doctor", ya mayar mata da murmushin yace "you are welcome" ya juya ya tafi, wani irin farin ciki da ta dad'e bataji irinshi bane taji yana ratsa ta, tana zama ta k'ira Aunty Jainaba dake airport ta sanar da ita komai, Anty junaiba tace "Wayyo ni da ban tafi yau ba" nan dai sukayi ta murnan k'arshen zaman Batuul gidan yazo karshe cikin ruwan sanyi tunda cikin shege ke jikinta, Abutturab kam jikinshi duk yayi sanyi, daidai kanta ya tsaya yana kare mata kallo, yasan yana da son yara, yanada burin ganin yayanshi amma bai taba sa damuwa ranshi ba na Ajiddeh bata haihu ba, tunda yasan Allah ke badawa a lokacin da ya dace but with Batuul, its totally out of it, yana d'aura ido kan cute face d'inta yaji wani courage yazo mishi na son ganin babyn da Batuul zata haifa mishi, wani abu da bai tab'a ji bane yau ke mishi yawo gaba d'aya jikinshi, d'an murmushi ya saki ya d'an sunkuya yayi kissing y'an cute lips d'inta da bai iya resisting, cak ya d'auketa ya rungemata tsam jikinshi yana jin abin nan na mishi yawo a jiki, barin office din yayi yana rike da ita ya fito, a zaune ya tadda Ajiddeh tana waya da sauri ta katse ganinsu, kamar ta samu wuk'a ta cakawa Batuul takeji amma ai k'arshen zamanta ma yazo, fuskarta d'auke da murmurshi ko tambayarshi abinda ke damun Batuul batayi ba sai murmushinta takeyi, shima d'in baice mata komai ba, kallonta yayi yace "muje", tasa kai gaba suka tafi, ganin gaba d'aya mood d'insa ya canja a ranta sai cewa takeyi, "wato so yake ya rufa mata asiri ko, toh ai ta Allah ba taku ba, Allah ya toni asirinta yau", mota ya bud'e ya kwantar da Batuul ya gyara mata kwanciyar kallonsa take tana lullumshe ido sbda irin baccin da take ji, ya zaga ya shiga ya tada suka fita, suna isa gida Ajiddeh ce ta fara fita daga motan ta shige cikin gida ya bi ta da kallo, da sauri ta haura sama ta shige d'akin Batuul ta shiga fiffido mata akwatinanta, kafin su Abu su shigo har ta sauk'o downstairs dasu, yana rike da hannun Batuul suka shigo parlon, da mamaki duk suka tsaya kallon ikon Allah, shewa ta saki tana tafa hannaye tace "In kana tunanin ni xa ayi ma wasa da hankali kayi karya Aliyu, don zaman karuwan nan ya k'are gidan nan," ta juya tana kallon Batuul tace "Munafuka algunguma, ashe karuwanci kike yi dama, toh yau Allah ya toni asirinki, iskanci ba a gidana za ayishi ba dan ban gada ba, a tafi can inda aka saba aci gaba dayi, Dan ni dai kam ban zama da mai cikin shege a gidana", kallonta kawai Abu yake da mugun mamaki don baisan ya akayi ta sani ba, Batuul kam d'aurewa kanta yayi ga jirin da ke d'ibarta, Jiki na rawa Ajiddeh tayo kanta ta fizgota da kargi tayi k'ofa da ita ta hankad'ata waje tana hakki tace "k'arshen karuwanci dai yau ya k'are gidana, aje gaba aci gaba daga inda aka tsaya," da sauri Abu ya k'araso ya d'ago Batuul duk ya gama rud'ewa ya shiga dubata ko taji ciwo, ita ko banda kuka babu abinda take, ganin komai normal babu abinda ya sameta ya mik'e, cikin zafin rai ya fixgo Ajiddeh ya wanka mata lafiyayyun mari har biyu ta both sides, ya shaketa cikin tsawa yace "kika kuskura ki sake tab'ata ko kika yi gigin k'iranta da karuwa sai na hallaka ki wllh, don matsayinta d'aya yake da naki a gidan nan" ranshine ya dad'a baci cikin kaushin murya yana mata wani irin kallo yace "Let me tell you what you don't know jiddah, kamar yadda kike matata a gidan nan, toh haka Batuul ma take matata ta sunna, snn cikin dake jikinta ba na kowa bane, nawane", yana kai wa nan ya Kama Batuul da komai ya tsaya mata yayi sama da ita, nan yabar Aunty Ajiddeh da numfashinta ke neman barin jikinta, idanunta sun firfito.





Take a minute of silence and pray πŸ™‡ for Burma, (our Muslim brother and Sisters) Ya Allah, Dan sunayenka kyawawa, Dan tsarkin mulkinka ya Zul jalali wal Ikram, Ya Allah ka kawowa bayinka sassauci cikin al'amarinsu, ka gafartawa wadanda magabatanmu, wad'anda suke raye Ya Allah ka kubutar dasu daga sharrin masharranta, Allah ka kawo musu Agaji Ya Rabbal Alamin.Amin






Hey to everyone reading Batuul, zaku jini shiru kwana biyu, abubuwane suka min yawa snn ga Exams da zan fara next week (Allah ya bamu sa'a), am not promising you guys update all the time, but In sha Allah I will try my best inga nayi muku update whenever I get d chance, and I thank you all for your prayers, naji dadi sosai gaskiya, Allah yasa mudace

πŸ’–πŸ’BATUULπŸ’–πŸ’






73






By phartiemarhk






Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*






Sulalewa kasa tayi wasu hawaye masu d'umi na bin kuncinta bayan tayi recover daga shock din da ta tafi na kusan minti goma, ta kai minti ashirin xaune nan gun ta kasa motsi, so take kawai taji wani yace mata a mafarki take jin duk abin nan da ya faru a while a ago, kuka ta fashe da da karfi, wanda hakan ya tabbatar mata ba mafarki takeyi ba, komai a zahiri yake faruwa, ba gizo kunnenta ke mata, sai a lokacin taji zuciyanta na bugawa kamar mai shirin fitowa, a hankali ta shiga girgiza kai tana tariyo duk abinda ya faru kanta, yanzu duk wannan abinda Abu ya fad'a mata duk gaske ne, Batuul matar Abu ce, ji tayi zuciyarta na shirin fitowa don wani irin bugu yakeyi da ya tsorata ta, a hankali ta kai hannu kan fuskarta ta shafo hawayen dake ta kwaranya ba tareda ta shirya fitowansu ba, maganganun Abuturrab ne ya rik'a dawowa a hankali yana mata yawo kwakwalwarta "kika kuskura ki sake tab'ata ko kika yi gigin k'iranta da karuwa sai na hallaka ki wllh, don matsayinta d'aya yake da naki a gidan nan, "Let me tell you what you don't know jiddah, kamar yadda kike matata a gidan nan, toh haka Batuul ma take matata ta sunna, snn cikin dake jikinta ba na kowa bane, nawane" wani irin ihu ta saki tana toshe kunnuwanta ta fad'a k'asa tana rik'e da kanta tana birgima kamar wata yarinya, gaba d'aya ta fita hayyacinta sai ihu takeyi, abunka da farar fata har ta canja kamanni tayi jajir, tun ranar da ta fara ganin Batuul a gun graduation d'insu har aka sashi yin pictures da ita kawae ke tariyo mata, ranan dinner d'insu da ya d'aukota a motarshi, ranan da ya dawo mata da Batuul gida wai karatu tazoyi har yau da ya bud'i baki yake ce mata Batuul matarsace kuma shi keda cikin jikinta, wani abune taji ya tokare mata mak'oshi ta rintse ido ta bud'e jikinta ya dau rawa, wani kara ta kuma saki tace "Inaaaa, Bazai yiwu ba wlhy, zakuyi dana sanin rainamin hankali da kukayi daga ku har iyayenku, bakusan wacece Ajiddeh ba, Aliyu sai na sa kayi dana sanin cin amanata da kayi wlhy, ita kuma tsinanniyar nan wlhy na rantse sai ta d'and'ani azaba da zata gwammace gara ta mutu da ita snn in aikata Lahira da ita da shegen dake cikinta, wlhy sai nasa na Lahira ya fiki jin dad'i, da haka ta mik'e ta haura sama da k'yar dan ji take zuciyarta kamar zata fito ga wani mugun jiri da take gani, tunda take bata taba shiga tashin hankali da rudani irin na lokacin ba.






Shi kam yana haurawa sama, kan gadon d'akin da yake kwana ciki yanzu ya kwantar da Batuul da kanta yake a d'aure, gaba d'aya jiri ke damunta, idonta taf da hawaye, k'ok'arin rage mata kayan jikinta ya shiga yi, dukda bata jin k'arfin jikinta hakan bai hanata rik'e rigan ba, lumsassun idanunshi ya sauk'e kan fuskarta yace "stay still or I slap you", ture hannunshi tayi daga jikinta tace "Ni ka bari sanyi nakeji", mik'ewa yayi yaje ya kaso ACn d'akin ya dawo ya zauna kan gadon, kallonshi kawai Batuul keyi har saida yayi noticing d'in kallon ya d'age girarshi d'aya yace "Anything", d'auke kanta tayi daga kallonshi ta rintse ido, gaba d'aya maganganun da Ajiddeh ta fad'a mata ke dawo mata yanzu, "In kana tunanin ni xa ayi ma wasa da hankali kayi karya Aliyu, don zaman karuwan nan ya k'are gidan nan, Munafuka algunguma, ashe karuwanci kike yi dama, toh yau Allah ya toni asirinki, iskanci ba a gidana za ayishi ba dan ban gada ba, a tafi can inda aka saba aci gaba dayi, Dan ni dai kam ban zama da mai cikin shege a gidana, k'arshen karuwanci dai yau ya k'are gidana, aje gaba aci gaba daga inda aka tsaya", idonta taf da hawaye take kallonshi, a hankali ta bud'e baki tace "I don't get abinda matar ka ke cewa, waye mai ciki a gidan?" jin tambayar da ta mishi yasashi juyowa yana kallonta, had'e rai yayi yace "wane cikin? were you eavesdropping?", had'e rai tayi itama ta harareshi tace "Ba ina wajen ba naji ta fad'a", had'e rai ya sakeyi yace "look! Lie down and sleep, bana son shirme", daga haka ya Shiga k'ok'arin kwantar da ita, ture hannayenshi ta shiga yi tana kokarin saukowa kan gadon tace "I have classes today, ni zan shirya in tafi" ta fad'a tana k'ok'arin sauk'a daga kan gadon, jiri ne ya d'ebeta tayi baya zata koma yayi sauri ya jawota jikinshi yana mata wani irin kallo yace "ina miki wasa ko, I will slap you if you dare move an inche daga nan", da k'arfi ta shiga janye jikinta daga nashi tace "Nikam ka kyaleni, I told you school zanje, av missed a lot", har lokacin yana rik'e da ita yace "You are going no where," kuka ta fashe mishi da tace "nikam sai naje, kuma zan fad'awa Ammah baka barin ina xuwa makaranta", kallon fuskarta yakeyi yanda hawaye ke kwaranya daya na bin d'aya har cikin ranshi yakejin kukan da takeyi, ji yakeyi kamar zaiyi affecting abinda ke cikinta, yace "not just today, daga yau baki sake fita ko ina, and dare going anywhere kiga abinda zan miki", birkice mishi tayi tana kuka ta shiga dukan k'irjinshi tana turashi ya saketa tace "I knew it dama you are always against my happiness and you will surely stop it someday, gashi yanzu ka fara da hanani zuwa school, why? What have I done to you to deserve all this, why why why me?", rintse

1 Comments On BATUUL
avatar
hafsat-9-3

12 months ago

Reply

Nice book

Please Login or Register in order to submit comment