Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Yayya ta tabe baki ta mike xaune da kanuri tace "Wato har uwar taki ta xuge ki shine xaki wani shigo ma mutane ko sallama bbu, kin wani hade rae koh" Baba dae bae ce komai ba kansa na kasa, Yayya ta ci gaba da cewa "Toh auren Aliyu dae bbu fashi wllh, yaro d'an arxiki mai asali gaba da baya, waye bae san kakansa ba a Maiduguri?" Xumbur Batuul ta mike xuciyarta na wani mugun bugun da bae taba yi ba har wani rawa jikinta ya shiga yi tana kallon Kakar tata tace "Ban gane ba Yayya" da kanuri Yayya tace "Ohh ke da duk baki san abin da ake ciki ba, toh ae shirye shiryen bikin ki ake da Aliyu jikan Kyari, wato d'an wajen Ahmad" Batuul ta xaro ido cikin kidemewa tace "Ni Yayya?" Ae bata jira cewar Yayya ba ta fice da gudu daga dakin ta nufi dakin Anty, Har lkcn Anty na xaune ta xuba tagumi, ta xube jikin uwar tata cikin rawan Murya tace "Anty ban gane abinda Yayya take gaya min ba ynxu," K'asa cewa komae Anty tayi tana kallonta, hkn yasa Batuul ta fashe da wani matsanancin kuka tace "Wayyo Na shiga uku Anty, wae Ya Abuu ake cewa xan aura, ni ban gane ba" Rungume ta Anty tayi sae dae she's lost of words.

Bayan Magrib Abuturrab na xaune daki abun duniya ya ishesa duk ya rasa tunanin da xae yi farida ta shigo tace "Ya Abuu Ammah na kiranka" mikewa yyi yace "kin yi abinda nace maki farida?" Farida tace "Ya Abuu bata fa ce min komai ba har ynxu, meaning she is still unaware, ni kuma baxa ta soma jin komai a bakina ba ka bari..." ficewa yyi daga dakin ba tare da ya tsaya jin sauran xancen nata ba, dakin Ammah ya shiga ya sameta tana waya, ya xauna har ta gama snn yace "Gani Ammah" Ammah tace "Dama cewa xanyi ka shirya kaje can gidansu Batuul ka gaida Yayya, ta shigo tun da rana" rasa me xae ce da ita yyi don bae son bacin ranta, da kyar yace "Toh Ammah" daga hka ya mike ya fita hankali tashe yasan shknn wani ikon Allah kawae xae hana a manna masa Batuul, wae for God's sake me suke son yyi da 'yar yarinyar nn?? Ya ma xae fara tunkarar Ajiddeh da wnn xancen, da kyar ya iya shiryawa ya dauki makullin motarsa ya fita daga gidan.
💖💝BATUUL💖💝

34

By phartiemarhk

Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*

Kuka sosai Batuul ke yi kanta kife jikin Anty dake hawayen ita ma, ďagowa tayi daga karshe jin Anty ta ki cewa komae cikin rawan murya tace "Aunty mesa za a min aure nida ke karatu, mesa Yayya ta matsu inyi aure har tasa Baba ya yadda zaimin ynxu, Aunty dan Allah ki tashi muje ki faďa musu banason yin aure, idan basu yrda ba to su canxa min wani mijin ba ya Abuu ba, don Allah Aunty ki tashi mu tafi nasan in kika faďawa Baba zai yadda", ganin Aunty ta ki tashi yasa Batuul mik'ewa har lkcn tana kuka tana faďin "Nasan in na faďawa Baba zai yadda, kullum duk abinda nace mishi yana min, wannan ma zanje in bashi hak'urin ince mishi karatu xanyi...." cikin hanzari Aunty ta mik'e ta tareta ganin tayo baya zata faďi, ta fada kanta, sabon kuka Aunty ta fashe da ta shiga girgiza ta ganin jikinta duk ya saki idonta lumshe, sunanta ta shiga k'ira tana cewa "Batuul, Batuul ki tashi kinji, babu wanda zai miki auren nan, wasa sukeyi miki dama, ki tashi yanxu zanje in samu Baba da Yayya ince suyi hak'uri, kiyi hak'uri ki tashi kinji Batuul, babu mai sake saki kuka, ki tashi muje tare Batuul", Batuul kam ko motsi batayi sai dai har lkcn hawaye na tsiyaya daga idanunta, wani ihun Aunty ta sake sawa tana jijjiga ta, buďe k'ofan ďakin akayi su Ahmad suka shigo jin ihun Anty, cirko cirko suka tsaya ganin kan Aunty kife jikin Batuul tana ta Kuka, da k'yar ya iya yin k'arfin hali ya ja k'afanshi ya k'arasa inda su Aunty suke, tsugunawa yayi dab da Batuul ya rik'o hannunta, ďayan hannun kuma ya ďaga Aunty, cikin sanyi yace "Aunty ciwon kan nata ne har yanxu", kasa bashi amsa tayi sai hawayen dake ta zuba daga idonta, juyawa yayi ya dubi sauran k'annen nashi da har lkcn sun kasa motsi suna nan inda suke sai hawayen da suma suka fara har y'an k'ananan yace "kuje ku k'ira Baba, yana ďakin Yayya", ya juya yaci gaba da murza hannun Batuul yana ďan jijjigata, ba a fi minti biyu ba da fitansu Baba ya shigo ďakin yana tambayan tana ina, ganinta kwance jikin Aunty ya kasa magana, sosai jikinshi yayi sanyi, yasan duk yadda akayi kan maganan auren nan da taji ne ya dameta, Bai sake cewa komai ba sai da ya sunkuya ya ďauketa cak sannan yacewa Ahmad, "ďauko key mu tafi asibiti", a bakin k'ofar ďakin suka ci karo da Yayya tana tambayar "meye ya faru wai, inata magana ja'iran yara kun qi kulani kun zuba min idanuwanku kamar na mujiya", ido ta wara ganin Batuul hannun Baba tasa ihu tana cewa na shiga uku ni Zara'u, mey zan gani haka, meye hakan wai kunyi min shiru, mey ya sameta, baza kuyi min magana ku faďamin mey ya samu Batuul ďin ba", babu wanda ya kulata a dakin, gaban Aunty ta k'araso tace "Maryam bafa nason wulak'anci, mey kuka yiwa Batuul ďin ina tambayanku kika min shiru, mayafi Aunty ta ďauka ta yafa tabi bayan su Baba ko kallon inda Yayya take batayi ba, tasan indai ta buďi baki toh kowa bazai ji da daďi ba dan ranta yayi k'ololuwar b'aci, hanyan Nizamiye hospital Ahmad yabi dan nan ne family hospital ďinsu, har lokacin bata farfaďo ba, suna zuwa cikin gaggawa aka karb'eta akayi emergency da ita, har lokacin babu abinda Aunty take sai kuka da addu'a Allah ya bawa y'arta lafiya, Abuturrab kam xaga gari yyi ya koma gida Karfe tara saura ya shige daki yyi kwanciyarsa.

Washegari kamar yadda Ammah tayi alk'awari, k'arfe biyu ta shirya tayi gidan Yaa Mera, da driver ta tafi dan so take ya jirata su koma, a falo ta tarar da ita zaune ta mik'e k'afa dogaranta mata biyu na mata tausa, sallama tayi ta sa kai cikin ďakin, da fara'a ya Mera ta tashi ta yiwa y'an matan alaman su wuce, kansu a k'asa suka gaida Ammah sukayi waje, waje ta samu daga palon ta zauna tace "Maryam wannan gidan naki da tafiya yake, dubi duk na gaji", murmushi tayi tace "kai Yaya, ai babu wani tafiya kawai dai kin daďe ne baki zo ba", biyu ďaga cikin y'an matan da suka fitane suka shigo ďauke da manya tray ďauke da fruits, abinci, sai nama iri iri, direwa sukayi suka koma daga waje, Yaa Merace ta fara magana "jiya kawai sai ga Babana, nayi mamakin ganinshi, shine yake cemin wai yayi sati ma", ruwan dake kan tray ta ďauko ta ajiye gefenta sannan tace "ai yanxu ma zuwan nan dan shi nayi, auren Mustapha nan da sati biyu kenan ko, toh inaso a haďa ayi da na Abutturab, dan matar nan tasa bazan zauna in zuba mata ido su cutar min da ďa ya zama mara amfani ba", ido Yaa Mera ta wara tace "Yaya aure Babana zai k'arayi, yaushe? kuma wa zai aura?", kai ta girgiza tace "Maryam auren ne kawai zai min maganin halin nan da yake ciki, yaro gaba ďaya ya zama bashiba, shine nayi magana da Babanshi ya nema mishi auren Batuul, so nake ma a haďa da na Massa tunda saura sati biyu, in yaso sai ya koma bakin aikinshi da ita, dan yarinyar na da nutsuwa, kamar jinina nake jinta", kallonta Yaa Mera ta tsaya yi tace "Yaya badai Batuul ďin Maryam ba?", kai ta kaďa tace "k'warai kuwa ita", tace "toh Yaya ai na Massan ma jiya Babanshi ke cemin wai sun ďan ďaga, sun k'ara wata ďaya dan Mamar yarinyar bata jin daďi, yanxu haka an fita da ita waje, Amma Yaya baku tunanin ko Batuul nada wanda takeso, ko kunyi magana da iyayenta sunce bata da kowa, dan kar azo a shiga hakkin yarinya", Ammah zatayi magana kenan wayanta ya shiga ringing, ďauka tayi taga Farida ke k'iranta, recieving tayi tasa a kunnenta tace "Farida ya akayi", cikin shesheka tace "Ammah Batuul", cikeda da damuwa jin ta ambaci Batuul kuma tana kuka tace " Batuul kuma, mey ya sameta", cewa tayi "Ammah tana kwance a asibiti bata da lafiya, tun jiya she is still unconscious tun.....", Ammah bata bari ta k'arasa ba tace "Farida, kina jina, kije ki samu Abu kice mishi maza ya tashi ku tafi asibitin tare, nima yanxu zan wuce daga nan", maida kukan nata tayi tace "toh Ammah", suna gama waya ta mik'e tace "Maryam kinji, Batuul din ma ba lafiya tana kwance asibiti, yanxu gunta zani in duba ta", bakin k'ofa Yaa Mera ta rakota tayi mata sallama tace Allah ya bawa Batuul ďin lafiya ta gaisar mata da Anty, itama zasu zo dubata idan mijinta ya dawo, da haka sukayi sallama akan zasuyi waya.

Hijabi kawai Farida ta ďaura kan top da wandon dake jikinta tayi ďakin Abutturab, knocking tayi taji bai amsa mata ba, buďewa kawai tayi ta sa kai, wani sanyi ne ya kaďa har cikin jikinta duk da hijabin dake jikinta, kai ta ďaga ta dubi Acn ďakin nashi taga yana lowest temperature, k'arasawa tayi daga ciki ta ďau remote ďin ta kashe Acn gabaki ďayanshi, yana kwance kan gadonshi rigingine ya ďaura hannunshi kan goshinshi idanunshi lumshe kamar mai bacci, a hankali ta k'araso cikin ďakin ta zauna daga bakin gadon, sunanshi ta shiga k'ira taji bai amsa mata ba, sarae tasan kuma idonsa biyu, ce mishi tayi "Yaa Abu Ammah cefa tace inzo in faďa maka ka shirya mu tafi asibiti", jin ta ambaci asibiti ya sashi buďe idonshi dake lumshe ya zuba mata su, bai tashi ba yace "waye ba lfya?", a hankali tace "Batuul ce bata ji daďi tun jiya, shine.....", wani tsawa ya daka mata, "tashi ki fita", a gigice ta mik'e sai da taje bakin k'ofa ta juyo tace mishi "Yaa Abu Ammah cefa ta aikoni", wani harara yabita dashi, ba shiri ta saki k'ofan tayi waje, tana fita ta k'ira Ammah ta faďa mata yadda sukayi da Abutturab, ran Ammah ba k'aramin b'aci yayi ba ta katse wayan ta shiga neman numbershi, jin wayanshi na k'ara ya janyo wayan, ganin mai k'iran yasashi saurin tashi zaune yayi recieving, yana ďagawa Ammah ta fara magana "Abu kana jina, bana son shashanci, in aiko yarinyar ta faďa maka sak'ona shine zaka korata, toh yayi maka kyau, ina kan hanyan zuwa asibitin, ka tabbata kamin in isa kana can", tana kaiwa nan ta katse wayan, ji yayi gaba ďaya kanshi na sara mishi, mesa Ammah baza tayi understanding ďina bane, mik'ewa yayi ya ďauki key ďin mota ya sauk'o k'asa rae ba ddi, a palo ya tarar da Farida zaune tana ta jimamin rashin lafiyar k'awarta, tana ganinshi ta mik'e, harara yabita dashi ya fita waje a fusacd, yana tafiya tabi bayanshi a ranta tana tausayin halin da k'awarta zata shiga in ta auri masifaffen nan, sai da ya shiga motar tukunna itama ta shige, bayan ya fita daga gidan ne ya tambayeta asibitin ba tareda ya ďago ya kalleta ba, faďa mishi sunan asibitin tayi daga nan ya ďau hanya.

Suna isa asibitin da gudu Farida ta buďe ta fice, bata damu da hararan da yake binta dashi ba tayi wucewar ta ciki, k'in fitowa yayi daga motan har sai da Farida ta dawo tace mishi Ammah tace ya shigo, tana gaba yana biye da ita suka isa har ďakin da aka kwantar da Batuul, a VIP ward aka kwantar da ita, Su Aunty da Ammah na daga palon yayi sallama ya shigo kanshi a k'asa, durk'usawa yayi ya gaida Aunty, fuskanta babu yabo ba fallasa ta amsa mishi sannan yayi mata ya mai jiki tace mishi "Alhamdulillahi taji sauk'i", daga nan bai sake cewa komai ba sai hararar da Ammah ke jifanshi dashi da sun haďa ido, juyawa yayi zai fita Ammah tace "ka shiga ka gantan ne da ka juya zaka fita", juyowa yayi yana kallon Aunty yace "i tot ba a shigane dan naganku zaune a nan", murmushin karfin hali tayi tace zaka iya shiga , bacci take", ta nuna mishi k'ofan ďakin, a hankali yake ďaga k'afanshi har ya isa bakin k'ofar ďakin, hannu yasa zai murďa kenan wata nurse ta buďe k'ofan zata fita, hanya ya bata ta wuce tukunna yasa kai cikin ďakin, xaune ya ganta tana hawaye cotton wool a hannunta alamar allura nurse din ta mata, Yayya na xaune d'aga gefenta tana mata sannu, suna hada ido da shi gabanta yyi mugun faduwa ta gyara zip din skirt dinta da sauri, sunkuyar da kai yyi ya karaso ciki kmr bae son taka kasa, Yayya ta washe baki ganinsa tace "A'ah sannu da xuwa mai gida," gaisheta yyi murmushi dauke fuskarsa don ba laifi sun d'an saba, ta amsa da fara'a tace "Ehh ynxu da taku ce ta kawo ka ae na ganka, tun jiya na iso ban ga keyar ka ba sae ynxu da kishiyata ba lfya koh" murmushi kawae yake yace "Jiya ae na xo aka ce min kina bacci" ta yo waje da ido tace "Kai Haba, halan wnn yar bakin cikin ce tace maka hka" ta fadi ta na nuna Batuul da kanta ke kasa har lkcn gabanta na faduwa don ko kallonsa bata son yi, Abuturrab yace "Ae kam ita tace min kina bacci" Yayya tace " kaji bakin ciki kiri kiri, toh ko taki ko taso dae ni ce ta farko ita ta uku, bbu ynda xata yi" daga hka ta mike tace "bari dae in baku waje kadda inyi rashin hnkli" duk da Mood din Abuu sae da ta basa dariya, ya bi ta da kallo har ta fita, snn ya hade rae ya juyo yana kallon Batuul, hawaye ne ke sakko mata, ya kusa second talatin yana kallonta, kafin ya karasa gadon ya ja kujera ya xauna bbu yabo bbu fallasa yace "I knw by now kina da masaniyan abinda ke shirin faruwa koh?" K'in cewa komae tayi sae hawayen da take ssae, cikin rashin damuwa da shirun da tayi yace "Wato ke kika ce masu ni kike so knn koh?" Da sauri ta d'ago kai tace "Allah ya kyauta! ko kuma kai kace kana sona ba!" Ido ya kafa mata cike da mamakinta, ita kanta tayi Mamakin furucin nata don unexpectedly taji ya fito bakinta, ya mike tsaye yana mata wani irin kallo yace "Kinsan Allah kika kuskura kika yrda suka makala min ke, kin dauko hanyar tarwatsa farin cikin ki ne, ni ina da mata kuma ina sonta, infact ko bani da mata ma ni me xanyi da ke? Kawae daukan magana ne wnn, wllh tun wuri kice masu ke kina da wanda kike so, kar ki yrda a soma kai xancen nn da nisa idan ba hka ba...." Kuka ssae take har da shessheka tana kallonsa, hkn yasa ya kasa karasawa ya koma ya xauna xuciyarsa na masa xafi, can ya kalleta yace "Dama ki daina wnn silly tears din mu sama ma kanmu mafita ynxu, kina da saurayi ko baki da?" Wani kallo tayi masa ta dauke kai ya mike a fusace xae yi magana Ammah da farida suka shigo dakin. Sunkuyar da kai Batuul tayi, Ammah ta Karaso tana kallon Abuu da ya shiga shafa kai daga tsayen da yake, Ammah tace "Kukan me kike bitti?" Da sauri yace "shine nima nake tambayarta taki bani amsa tun daxu" Farida ta kallesa ta gefen ido ta tabe baki sanin karya yake ta xauna gefen kawartata da damuwa tace "Sannu Dear, I was so worried da Ahmad yace baki da lfya" Ammah ta xauna kujerar da Abuu ya tashi tana kallon Batuul tace "Sannu Bitti, ya jikin?" A hnkli tace "Da sauki ynxu" Ammah ta galla ma Abuu harara tace "A garin ku hka ake xuwa duba mara lfya empty handed?" Shiru yyi bae ce komae ba, ya rasa me yasa Ammah ke yi masa hka shi kam, gefen Farida ya karasa yana kallon Batuul yace "Me kike son in siyo maki?" Farida ta amshe tace "Fruits, Shawarma, Chill yoghurt da gasasshen kaza will do" harara ya maka mata rae a bace ya juya ya fice daga ward din, ko da ya dawo Ammah sun tafi da farida dake son xuwa yi ma Bestien nata girki ta dawo asibitin, Yayya ma Ahmad ya maida ta gida, Anty kadae ce ward din sa Batuul gaba tana cin abinci, don tun jiya rabonta da abinci, kansa a kasa ya karaso ward din, ledan hannunsa ya ajiye kan table din dake gefen gadon bayan ya kuma gaida Anty, Anty tayi masa gdya ta dauke abincin gaban Batuul sanin ba ci xata yi ba ta rufe, ta tattara komae a basket tace "Bari in je gida ynxu in dawo Abuturrab" yace "Toh sae kin dawo Anty"
💖💝BATUUL💖💝






35






By phartiemarhk






Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*





Aunty na fita ya jawo kujera ya zauna kusa da gadon yana kallonta, ita kam kanta a k'asa yake, dan ji tayi kamar ta bita su tafi, har ji take ďakin na suffocating ďinta, tabe baki yyi ya mik'e ya isa wajen da ya ajiye ledan da ya shigo da ya ďau wani bowl da Batuul ta wanke a hannu ciki da zata ci abinci ya zuba apple, grapes sai pomegranate a ciki ya bude table water dake wajen ya juye ciki ya nufi toilet, tana zaune ya fito ya zuba fruits din kan plate ya dawo ya zauna kan kujerar da ya tashi ya fara b'are pomegranate yana shan abin shi, Batuul kam kin ďagowa tayi ta kalleshi bare tasan abinda yake, cikin nutsuwa ya shiga maimaita mata maganan ďazu ya kara da cewa "yhu beta pretend yhu are nt recovering, ki kuma gaya ma likita auren dole xa a maki, I bet he will find a solution" ko kadan Batuul bata san mey yake cewa ba dan ji tayi abincin da taci yana son dawo mata tsabar tashin xuciya, ranshi ne yayi mugun b'aci ganin ynda tayi banxa da shi tak'i cewa komai, a fusace ya tashi ranshi a haďe, cikin tsawa yace mata "keh kurma ce ina miki magana kin wani min shiru kina jina, are yhu stupid", ko ďagowa batayi ba bare ta nuna mishi tasan abinda yake faďi, ranshi ne ya daďa b'aci yace "Kehh!" k'ala bata ce mishi ba, jin amae na shirin taho mata yasa ta tuge drip ďin hannun ta ta yunk'ura xata sauka daga gadon yyi saurin rik'eta yana mata mugun kallo yace "ina zaki?", hawaye ne ya shiga zuba daga idonta tana girgiza mishi kai alaman ya saketa amma yaqi, sai ma daďa rik'eta da yayi da k'arfi don mamaki reaction din nata ya bashi to ko dae ba ita kadae take ba, bai ankara ba kawai yaji ta kwararo mishi amai a jiki.






Aunty na komawa gida tasa aka kawo mata Aabid dake wajen Fa'izah ta bashi abinci, dan rabonta dashi tun jiya da Batuul ta zama unconscious, tana gama bashi ta mik'ashi ta shiga yin wanka, fitowanta kenan daga toilet taga Baba zaune akan gado, har ta ďan tsorata, ganin shine ta k'arasa fitowa daga toilet ďin, dubanshi tayi taga ita yake bi da ido, ce mishi kawai tayi "Uncle sannu da zuwa", snn tayi gaban mirror, kwaso mayukan da zata shafa tayi ta dawo bakin gadon itama ta zauna, Kallonta yayi yadda takeyin abu kamar bata san yana ďakin ba, hannunta ya rik'o tare da cewa "Maryam", bata ďago ta kalleshi ba tace "Na'am", yace "ya jikin Batuul ďin, waye a wajenta", k'ok'arin maida hawayen dake shirin zubo mata tayi a hankali tace "Abu na wajenta, wanka nazo inyi in kai mata kayan da zata canja itama", matsowa yayi kusa da Aunty ya jawota jikinshi, hawayen da take ta k'ok'arin maidawa ne ya shiga zubowa, kuka sosai ta shiga yi mishi, patting bayanta ya shiga yi , bai hanata ba har sai da ta ďan tsagaita dan kanta tukunna ya ďago tareda da k'iran sunanta, ajiyar zuciya tayi tace "ina jinka", yace "Maryam yanxu akan nace zanyi wa Batuul aure shine kika bi kika ďagawa kanki hankali?" yayi tambayar yana kallonta, ganin tak'i magana sai hawayen dake zuba daga idanunta yasa yace "auren nan da zatayi kamata yayi kifi kowa murna, wannan yaron ďanki ne, kinfi kowa sanin waye shi, ke da kanki kinsan babu wanda Batuul zata aura hankalinmu ya kwanta da yafi Aliyu, da bakin ki kin yabi nutsuwarshi, toh sai yanxu dan zai auri y'arki shine kike qi, wani hali garesa da har baki son ba shi 'yar ki? Naga dae auren nan ko ba yanxu ba dole ta yishi, toh meye amfanin a barshi nan gaban bayan yin hakan shine gatan da zamu iya yi mata, kuma shine rufin asirinta da namu baki ďaya, inma karatunta kikeji, da kaina zan sa a nemo mata admission a can inda zatayi auren, babu abinda zai tauye mata karatun ta, kiyi hak'uri kiyi mata addu'a Allah ya bata zaman lafiya da kwanciyar hankali a duk inda zata tsinci kanta", jikinta ne yayi sanyi har yanxu hawayen na ci gaba da zubowa ta shiga gogewa cikin sheshek'a tace "Uncle Batuul k'arama ce fa, batasan meye aure ba bare abinda ke cikinshi, kuma fa mai mata zaku aura mata, abin ai zai yi mata yawa, kai da kanka kasan yadda Batuul ke da rauni, haka zataje a cutar da ita tunda ita ba wani wayo gareta ba", murmushi yayi tareda ďagota yace "yanxu naji dalilinki na k'in auren, bakiso y'arki ta auri mai mata saboda kema ke kaďaice gidanki ko, nima ďin ai zan k'ara", da sauri ta ďago tana kallonshi ya sake jawota jikinshi yana murmushi yace " Be optimistic Maryam, in kika nuna tsoron kishiya y'ar taki kuma tayi yaya, addu'a zakiyi musu Allah ya haďa kansu ya basu zaman lafiya, shi kuma Allah ya bashi ikon rik'esu da amana, sannan Batuul fa University take, tana second year ďinta, kinga ba yarinya bace, she is matured enough, she can decide what is wrong and right, tasan abinda zai cutar da ita da wanda zai amfaneta, mubita da Addu'a Allah yasa hakan ne mafi alkhairi", ya faďa yana goge mata hawayenta, da haka Baba ya rarrashi Aunty har ta hak'ura da zancen auren, tace Allah sa hkn shine mafi alkhairi.






Su Ammah na isa gida tayi summoning chefs guda biyu, mace ďaya dattijuwa sai ďayar budurwa, order ta shiga basu na abinda takeso a dafawa Batuul kuma kar su ďau lokaci, waya ta ďauka ta k'ira Farida data haura sama, ba jimawa ta sauk'o, Ammah tace mata "je ki ďauko min computer yanxu kizo kimin ordering wasu abubuwa, babu b'ata lokaci Farida ta haura sama bata jima ta sauk'o rik'e da Macbook ďinta ta ďaurashi kan table ďin dake gaban Ammah sannan ta samu waje daga k'asa wajen k'afan Ammah ta zauna ta buďe system ďin tana k'ok'arin jonawa da internet, sai da ta gama taga yayi connecting to internet ta ďago tace "Ammah mey zakiyi ordering, Jumia za a shiga ko konga ko kuma universal shopping zakiyi? ta dubi Ammah tana dariya, zama Ammah ta gyara tace mata kayan lefen Abu nakeson haďawa, lokaci ya k'ure bazan samu aje a haďo kayan ba, shiyasa zanyi ordering komai", da sauri farida ta kalleta tace "Ammah wai auren nan dagaske kukeyi sai anyi, rashin lafiyan nan mafa da take nasan lbrn da taji ne ya sata" harara Ammah ta maka mata tace "sannun gyatuma,

1 Comments On BATUUL
avatar
hafsat-9-3

12 months ago

Reply

Nice book

Please Login or Register in order to submit comment