Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsukewa tace "yafi dad'i da yaji", zama yayi yana janye plate d'in gabanta yace "nidai kar a koyawa babyna cin haji", raurau tayi da ido tace "toh buh lemme have my plate back", kai ya girgiza mata yana juye yajin a d'aya plate d'in da babu komi, marairaicewa tayi tace "Da yajin fa yafi dad'i", kai ya girgiza mata yace "am not taking the risk, ga wannan na rage miki", ya mik'a mata plate d'in da d'an kad'an ciki, karb'a tayi ta zumb'uro mishi baki tana cin abinta, zama yayi yana shan kununshi bayan ya gama yace ta rakashi pool d'in dake bayan gidan, tare sukaje tana zaune ya shiga ya gama wankanshi dan ya hanata koda k'arasawa wajen bare ta shiga pool d'in, bayan sunyi sallahn magrib suka fita tare tafiya asibiti dan EDD d'inta ya kusa, snn akayi reffering d'insu asibitinsu na Nigeria dan Ammah tace Lallai Lallai su dawo tunda ta kusa haihuwa, a waje suka ci abincin dare snn ya biya dasu Trotters, waje ya samar mata ta zauna, da kanshi ya dinga zagayawa yana kwaso kayan baby da maternity clothes tunda ga kan coats, jumpers, leggings, shauls, towels, Baby bathing sets, craddles, ds duk saida ya tanada kuma duk designers, daga M&S sai Ck, duk in ya d'auko sai ya kawo mata ta gani tukunna kuma yawanci na mata yake kwasa ko kuma unisex, tun tana ganin yawansu tana cewa ya bari in ta haihu lafiya a siya sauran yana qi har tayi shiru ta zubawa sarautar Allah ido, da tayi mishi maganan yayi mata addu'a kawai, ba lallai ta haihu da rai ba, had'e rai kawai yakeyi yace mata shi tana dena fad'a, shiru kawai zatayi dan batason ranshi yana b'aci, sai wajen sha d'ayan dare ya gama siyayyan nashi yasa akayi packaging wasu aka tura Nigeria saura ya barsu a nan, kamar ba kud'i yake zubawa ba haka suka dawo gida, washegari ma da ddare suka sake fita ya sake kafa wata sabuwar siyayya, ana gobe zasu dawo Nigeria suna zaune parlour tana jikinshi yace "Glitter?", d'agowa tayi ta kalleshi yace "Kina da sunan da kike so a sawa Babyn?", kallonshi ta tsaya snn ta girgiza mishi kai a hankali tace "A ah, duk wanda ka saka ma zaimin", kitson da shi ya kama mata yake warwarewa yace "you sure?", kai ta kad'a mishi, a hankali ya sunkuya yayi pecking goshinta "I love you", murmushinta mai kyau tayi tace "I love you more", tara ya kashe musu wata ya taimaka mata suka haura sama, baccin su sukayi peacefully cikeda shak'uwa, washe gari suka shirya suka tafi Nigeria, babu yadda Abu baiyi Ammah ta barshi su sauka gidansu ba tace sam bata San zancen ba, a gidansu zata zauna, tun a waya yace "Ammah Al'ada nefa duka wannan, ya za a raba miji da matarsa bayan ba fad'in Allah bane, tun lokacin ta balbale shi da masifa, badan yaso ba suka sauk'a a gidan Ammah akan bayan kwana biyu zai kaita, ana gobe zai kaita gidan Aunty tana zaune kan gadon tana shan cream in chicken soup, shi kuma yana gaban desk top yace "Glitter yanxu kema yadda zakiyi a d'aukemin keh har tsawon wata da wani abu?, I can't even imagine a day without you, nasan in keh kika fad'awa Ammah zata yadda", murmushi tayi tace "Amore you know I will miss you more ko, with every passing second?, its a tradition, yanzu zaka ga ya wuce", pouting bakinshi yayi yace "Shikenan", ta bud'e baki kenan zatayi magana taji wani suka ta bayanta, ido ta rintse tana ambaton sunan Allah, plate d'in dake hannunta ta ajiye ta a hankali tana k'ok'arin mik'ar da k'afanta, lip d'inta na k'asa ta cije tana cewa "Yasalam", juyowa yayi ya kalleta, da hanzari ya sauk'o yana d'agata yace "Glitter mene, cikinki ne?", ido ta rintse tana riqe mishi hannu tace "Yaa Abu bayana", duk ya gama rikicewa yama rasa ya zaiyi, d'agota yayi yana yi mata sannu zai fita da ita, kamin su fita Ammah ta shigo d'akin kawowa Batuul kunu, da sauri ta ajiye abinda ke hannuta ta k'araso tana "Subhanallah, Bitti ciown ne?", Batuul da ta kasa magana Ammah ta k'araso ta riqe tace "Aliyu d'auko key, I think its delivery, duk ya gama rikicewa ya d'auko key snn ya ciccib'i Batuul dake ta cije lips sbd azabar zafi, a parking lot suka had'u da Farida ta dawo daga school tana parking mota, da gudu ta k'arasa wajensu tana tambayansu, ganin babu mai bata amsa ta koma motan ta bi bayansu, suna zuwa asibitin aka karb'e cikin gaggawa akayi Labour room da ita
[12/16, 12:15 AM] ‪+234 808 135 1434‬: 💖💝BATUUL💖💝




By Phartiemarhk





98









Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*





Binsu yayi a baya zuwa d'akin da aka shigar da Batuul d'in, daidai bakin k'ofa wata nurse tace "We are sorry Sir, but you can't get in", wani irin kallo ya jefeta dashi da yake mata nuni da bakida hankali ko, da sauri ta sauk'e idonta k'asa tana cewa "am sorry sir", hannu yasa ya matsar da ita gefe ya tura k'ofar shiga d'akin, kan gado ya tarar da Batuul kwance har an bata maternity wear, sun fito da duk wani abu da ake buk'ata, da sauri ya k'arasa gadon da take kwancen, ido kawai ta rintse tana ambaton sunan Allah dan yau hawayen ma nemanshi take ta rasa, dukda azabar da take sha hakan bai hanata jin d'umin hannunshi cikin nata ba, a wahalce ta bud'e idanunta ta sauk'e cikin nashi, ido ya lumshe ya bud'e, bayason ganin wannan yanayi da take ciki, a hankali tace "Yaa Abu Aunty", kamar wacce ta watsa ruwa haka sweat duk ya jik'ata, hannunta dake cikin nashi ya riqe ya kai bakinshi tareda kissing yace "You will be fine Babyna, we will make it together, am here kinji?", ido ta lumshe tana kad'a kai cikeda azaba tace "inaso inga Aunty, plss call her for me kaji Yaa Abu, inaso in ganta", ta fad'a tana sake cije leb'e, gaba d'aya ta gama rikitashi, shima so yake kawai yaga hawaye ya zubo mishi ko zaiji dad'i da wannan irin ciwon da yake jimata, daidai fuskarta ya sunkuyo yace "Glitter you will b okay, Aunty will be here anytime,Ammah zata fad'awa Aunty, am upright sure, she will b here shortly, sannu kinji?", daidai lokacin da doctor da nurses d'in suka k'araso cikin shirin aikinsu, ganin Abu zaune Doctor yasa yace "Good Afternoon Mr Kyaree, we are sorry but we need you to stay outside to carry out our work efficiently", fiyeda kallon da yayiwa Nurse d'in d'azu yayiwa Doctor dukda sabon dake tsakaninsu amma yau mantawa yayi da hakan, gaba d'aya ranshi ya gama b'aci, matarshi in such a pain maimakon yayi attending to her yake kawo masa shirmen banza wai ya fita, a fusace yace "Get yourself composed Doctor and attend to my wife, She is my wife, we are in this together, I ain't moving an inch from here", ya sake maimatawa sternly snn yace "And if anything happens to her?, am gonna shut d whole hospital down, you will all pay for it", yayi maganan idonshi na kad'awa, "Damn it, Doctorrr", ya fad'a kamar zai make doctor, ganin dagaske yake kuma zai b'ata musu lokaci yasa kawai suka fad'a aikinsu cikeda k'warewa, duk wani kuka na Batuul yau nemanshi tayi ta rasa, Addu'o'in da Abu keyi yana tofa mata duk wanda ta kama shi takeyi, da taji azaba lokacin take tuna Aunty, take zata fara Rabbir Ham huma kama rabbayani Sagira, duk wani motsi da Batuul zatayi har cikin ranshi Abu ke jinshi, sosai ya tausaya mata ganin irin wahalan da take sha, a lokacin ya sake ganin kima da daraja irin ta mata had'e da tausayinsu, in basu ba wazai iya enduring irin wannan ciwon, addu'a yayiwa duk wata mace wacce aka haifa da wacce ta haifa, a hankali ya fara tofa mata "wa tilka hujjatuna atainaha Ibraheema ata qaumihi, narfa'u darajatin man nasha, inna rabbaka hakeemun aleem", a zuci ta dunga maimaita aabinda taji yana fad'i, a hankali taji ciwon na raguwa, ba a cika one hour ba ta sumb'ulo y'ar Babynta k'arama mai kyau itama, Hamdala Abu yayi yana kai hannu zai tab'a Babyn Doctor yace Mishi "No pls, not now", yatsina fuska yayi ya janye hannunshi, tareda shi suka taimaka aka gyara aka kimtsa Batuul da Baby, bayan an fito da Babyn yana zaune bakin gadon da Batuul ke kwance yana mata sannu suka mik'o musu Babyn, da Bismillah yasa hannu ya karb'eta daga wajen nurse, gaba d'aya komai na jikinta farine, babu komai nata a waje sai d'an k'aramin face d'inta, wani irin k'auna da nutsuwa da baisan daga inda yake sauk'o mishi ba yakeji jin d'umin Babyn jikinshi, murmushi ne ya kufce Mishi ganin komai na fuskan Babyn irin nashi, lips d'inta ne Kad'ai irin na Batuul hatta heart shape d'in bottom lip d'in nata irin na Batuul ne, a hankali ya matso da Babyn kusa da Fuskan Batuul yace "Fatima our child, our Baby, kyautar da Allah yayi mana Fatima, look at her please, she is too cute for me", murmushi kawai Batuul tayi dan bata jin k'arfin jikin nata sosai, daidai kunnen Babyn ya sunkuya tareda k'ira mata Sallah, ya karanto "inni sammaituha (A'eesha) wa inni u'ixuha bika wa xurriyatiha minash shaaid'anir rajim" yayi mata addu'o'i sosai tareda yi mata Hud'uba da Suna A'eesha, Dabinon Ajwan da dama yana cikin kayansu yasa aka mik'o mishi da ruwan Zamzam ya tauna ya d'iga mata tareda ruwan Zamzam d'in, kamar wacce tasan abinda akeyi ta yatsina fuskarta tana lashe baki, dariya yayi ya sunkuya yayi kissing goshinta snn ya matsa jikin Batuul d'in yace "Glitter?", a hankali ta d'ago lumsassun idanunta ta dubeshi, yace "kin bani kyautar da duk duniya babu mai bani irinta, you have given me the best gift I would ever ask off, I will forever be grateful, Allah ya barmin keh Glitter kici gaba da bani wasu Babies d'in, just tell me anything you want, ko meye shi indai akwai shi a nan duniyan, I promise to get it for you, you have given me the best gift of life, I promise you, just ask me duk abinda kikeso zanyi miki shi, just tell me jinni", a hankali ta bud'e idanunta da suke a lumshe, kallonshi takeyi da murmudhi d'auke kan fuskarta tana tunanin abinda takeson cewan, tasan duk murna ne ya cikashi amma da wuya ta samu abinda takeson, a hankali ta bud'e baki tace "You Promise?", kallonta yayi for seconds kamin ya kad'a mata kai, zai yi magana doctors da nurses d'in suka zo za a canja mata d'aki, tana kwanace suka turata zuwa wani d'akin, badan ta saba da ireirensu ba da zatace d'aki ne kawai ba na asibiti sbd girma da kuma kyansu, saida Nurses d'in suka gama duk wani necessary abu da ya kamata suyi mata itada Babyn snn suka kwantar da Babyn gaban Batuul suka fita suna mata sannu, kallonsu yayi with so much adoration yana yiwa Allah godiya da kyautan nan da Allah yayi mishi, Batuul is one part of him da baya tunanin zai iya rayuwa babu ita, hannunshi yasa ya kamo na Batuul d'in yana d'an murzawa a hankali yace "Fatima you are the best thing that ever happened to me kinsan da haka ko?", a hankali ta kad'a mishi kai yaci "I know I love, ban san amfanin kud'ina ba if I can't give you abinda kike nema, komeye shi kike so indai bai sab'awa addini back just mention the anything, zanyi miki shi Glitter", ya fad'a yana sassauta muryarshi tareda sak'ale yatsunsu waje d'aya, a hankali ta bud'e baki tace "Yaa Abu ka dawo Ajiddeh gidanka, zamanta haka ya isa batareda sanin makomarta ba, banasone ka shiga hakkinta, na fad'a maka nikam na yafe mata wlhy, nobody is above mistake, kuma everything happens for a reason, maybe for us to realise each others worth, how much we mean to each other, Yaa Abu plssssss", ta k'arasa maganan tana lumshe ido , shi kad'ai yasan irin impact d'in da Batuul ta yiwa rayuwanshi, mesa baza ta fad'i wani abin ba sai wannan, har ga Allah ko jiya da Abui ya sake mishi zancen Ajiddeh  ce mishi yayi zai rabu da ita, zai sallameta, duk da ya yafe mata shima amma ya kasa samun wajen da zai ajiye abinda ta aikata ya manta dashi, baya tunanin zai iya d'aukan wani abin da zai sami family d'inshi ya qyale maishi nan gaba, amma its about Batuul yanzu, she is worth more than that, He can sacrifice that atom of happiness da ya rage mishi for her to be happy, tana son ya maida Ajiddeh d'akinta, kuma alk'awari yayi mata akan ta fad'i abinda takeso, how can he just deny her , a hankali ya sauk'ar da idonshi kan fuskan Batuul ya shafi gefen fuskarta da d'aya hannun nashi yace "will that make you happy?", kai ta kad'a mishi, murmushi yayi mata yace "Anything for you Fatima, just know I will always love you", murmushin ta mishi amma jin yanayin da yake  sab'ule hannunshi cikin nata yasa murmushin dake fuskarta bajewa, duk da rashin k'arfin da takeji hakan bai hanata damqe hannunshi ba, kallonta yayi, ganin hawaye idonta yasashi zama da wuri yana girgiza mata kai, cikin siririyar muryarta tace "Are you sad, angry about what I requested for?, ka bari na fasa if you are not okay with .....", bai bari ta k'arasa ba ya d'aura dogayen yatsunshi kan lips d'inta yace "Shhhh, am happy with whatever that makes you happy, okay?", kai ta kad'a mishi yayi murmushi yace "Good girl, get some rest", ya fad'a yana d'aga mata girarshi d'aya, murmushin tayi mishi itama tareda lumshe ido, ido ya tsura musu itada y'ar Babyn dake gabanshi yana kallonsu yana dad'a yiwa Allah godiya da ya bashi wad'annan precious kyautan a rayuwanshi, yana nan zaune yana kallonsu aka turo k'ofar d'akin, Abui ne sai Ammah, Farida sai Sadiq, lokacin doctors suka sanar dasu da Batuul ta sauk'a lafiya zasu iya shiga su kanta, tsabar murna Farida har rawa jikinta keyi sbd d'okin zuwa taga niece d'inta, y'ar yayanta y'ar Bestyn ta that turn out to be a sister, Abui ne ya fara d'aukan Babyn da murmushi a fuskanshi yana tuna lokacin da ya fara riqe Abu for the first, yace "This is how I held Aliyu , kamar jiya fa gashi yanzu Allah ya bani tsawon rai nayi witnessing haihuwar y'arshi, Allah yayi muku albarka baki d'ayanku", ya fad'a tareda kissing goshin yarinyar, duk suka amsa da "Amin", Ammah ce ta karb'eta daga hannun hannun Abui murmushi d'auke fuskanta snn ta kalli Batuul dake kwance tana bacci tace "Allasarki Bitti, yadda kukaga wannan jaririyar haka Fatima take lokacin da aka haifota, tun ranan Allah ya dasa min sonta a raina kamar ni na haifeta, ashe itace zata fara samar min jika, Allah ya k'ara miki lafiya ya d'ayyiba miki zuri'a", duk suka amsa da Amin, Abu ya dubi Ammah yace "Ammah an fad'awa su Aunty? Tun d'azu take nemanta", ya fad'a yana kallon Batuul, Ammah tayi murmushi jin Batuul nata Neman Aunty tasan zafin haihuwar yasa ta neman Aunty, tace "Dama ana shiga da ita na fad'a musu toh bayan doctor ya fad'a mana sauk'arta lafiya nayi maza na sanar dasu, da yake ma can d'in za a kaita basai sunzo nan d'in ba ai", ya d'an tsuke baki yace "Ammah har yanzu wai zancen kaitan na nan?, wlhy hankalina zaifi kwanciya in ina kusa dasu, zan kula dasu Sosai In sha Allah, Plssss Ammah", ya k'arashe maganan kamar mai shirin yin kuka, dariya ma yaso ya bawa Ammah amma ta dake tace "Kai nifa ban cike da shirme kana jina, ba al'ada bace da zaka wani ce kafison a bar maka su?, toh ba kanka za a dena ba, gidansu ne sai ta tafi yin wanka", badan yaso ba ya hak'ura ya miqe tareda yin sallama dasu, Farida da batasan me ke faruwa ba duk hankalinta na kan jaririyar kamar zata maidata ciki ya duba yace "Farida let her be plssss, bacci takeyi", kallonshi tayi da murmushi a fuskanta tace "nifa nasan da ni take Kama, bari ta tashi zaku gane abinda nake fad'a muku", kai kawai ya kad'a yace "Naji ai ke zakiyi rainaonta but for now barta ta huta, bata ma saba da iskan duniyar ba bare wahalar cikinta", cikeda murna Farida jin yace ita zata yi raino ta matsa da baya da sauri tace "Ai na ma matsan, Allah ya raya mana Babyn mu, Sunan waye za a saka mata?", har ya fara tafiya kamar ya fad'a mata ko sunan wa yarinyar zataci ya fasa, Abui ne kad'ai yasan meye sunan jaririyar, yayi murna sosai ya sa musu albarka su dukkansu, tareda fatan Allah ya k'ara had'a Kansu, Sallama yayi da Ammah da Farida ya fice daga d'akin, Kai tsaye gidan Aunty ya, yasa akayi mata magana dan bata parlour ko kince, kamar kullum cikin shigarta ta alfarma da gayu ta sauk'o, ganin Abu ne yasa ta d'an fad'ad'a murmushin dake fuskarta, yana hangota ya sauk'o daga kan kujeran tareda d'an duk'awa ya gaidata, wani kunyan Aunty yakeji yau na daban, ta amsa mishi snn ta mishi barkan k'aruwan da ya samu tareda addu'o'i, murmushi kawai yakeyi yanajin dad'in addu'ar da take musu, tasa aka kawo mishi refreshments, ruwan kawai ya bud'e bai kai ga sha ba ya fad'a mata abinda ke tafe dashi, might murmishi Aunty tayi, ita da kanta taji tausayin Batuul, tasan wahalan haihuwan da ta sha ya sa take son ganinta, da murmushinta tace "Kaima Aliyu sai ka biyewa shirmenta Batuul kaima, me zuwan nawa ma zai mata in banda shirme irin na Batuul, addu'a kawai zamuyi mata da fatan sauk'a lafiya kuma Alhamdulillah Allah ya amsa mana addu'a, sai kuma yanzu muce Allah ya k'ara musu lafiya ita da abinda ta haifa", kanshi a k'asa yace "Aunty ayi hak'urin dai muje in ta farkan ta ganki dan tun d'azu take ambatonki, she will be to wake up to you by her side", Murmushi kawai Aunty tayi tace "Tohh shikenan bara insa a shirya mata abubuwan da na sa akayi mata sai insa Baa Liman ya kaini in tq gannin hankalinta ya kwanta na dawo", Sam Abu yaqi yadda saidai Aunty ta bishi, badan taso ba ta haqura suka tafi, a asibiti da kanshi ya bud'e mata k'ofa tareda samo ma'aikata su shiga da kayayyakin dake baya, har lokacin Batuul bacci takeyi, har mamakin yawan mutanen dake d'akin yayi, sai barka suke mishi da Allah ya raya, gaisawa yayi dasu snn yayi musu sallama ya fita, yana fita ya qira Massa akan zaizo ya sameshi zai rakashi, kai tsaye gidan ya wuce, Abu ke tuk'a motar Massa na daga gefe yana taya Abun murnar k'aruwa, sai shak'iyanci yake mishi, ganin yaqi kulashi yace "Wai kai inama zamune haka?", Abu ya shafe fuska yace "Gidansu Hauwa zani, I promised Batuul to take her back", Massa ya wara ido yace "Amma kai duniyanci duk ka iyashi, are you telling me all these while tana gidansu da aurenka kuma kanta?", Tsaki yaja yace "Kaga ni karka dameni, she caused everything, and I can do it bitter and better than what I did, am talking about Fatima, she is my reality, I can't risk anything da zai cutar da ita, and taking back Ajiddeh is a compromise, she told me she dd be happy, so please spare all these naggings", Kafad'arshi Massa ya dafa yace "You are a man, you can take whatever, kawai Addu'a zakayi Allah ya shige maka gaba", a sanyaye ya amsa da "Amin", shi gaba d'ayanshi baisan ta ina zai fara ba, seven months amma bai tab'a waiwayarta ba sai Yanzu, har yazo k'ofar gidansu Ajiddeh yana sak'e sak'e a ranshi, masi gadi da sauran ma'aikatan dake bakinta da murna suka dinga gaidashi dan sun sashi da kyauata da yi musu alheri, saida yayi parking yasa a duba mishi ko Dad na gidan, in yana nan ayi masa iso dashi, hakan kuwa akayi akace musu yana daga garden, can wani yayi musu jagora suka isa, yana zaune kan d'aya daga cikin kujeraun dake k'ark'ashin hut d'in wajen da ruwa gabanshi, da mamaki Dad ke kallon su har suka k'araso wajenshi, a ladabce suka gaida Dad, da fara'a ya amsa musu kamar wani abu bai shiga tsakaninshi da y'arshi ba, har saida Abu yaji kunya ganin yanda Dad ke janshi a jiki, shiru ne ya biyo baya kqmin Abu yayi k'arfin hali a sanyaye yace "Dad munzo mu bada hak'uri kan abinda ya faru, kuskurene da muka aikata bisa son zuciya, nazo in koma da Hauwa d'akinta, Allah ya have mana baki d'ayanmu" Dad da ya k'ura mishi ido ya cire glass d'in dake idonshi yana kad'a kai yace "Aliyu tun lokacin da Hauwa tazo min da zancen kai zata aura nasan tayi sa'an miji, nayi murna sosai dan nasan zaka kula da ita iya gwargwado, tun kana k'arami lokacin Ina aiki k'ark'ashin mahaifinka nasan kai yaro ne mai dattako, Aliyu ta fad'amin duk abinda ya faru tsakaninku da ita saidai kunyar mahaifinka da nakeji bazai barni inje baku hak'uri, nasan sunyi muku kuskuren da bai canci wannan yafiya ba, saidai duba da irin gidan da ka fito yasa bazanyi mamaki ba, ina mai sake baka hak'uri kan abinda suka aikata muku,, maganar kkmawar Hauwa kuma Aliyu tunda ka tako da k'afarka bazan iya hanaka ba, amma tunda hakane inason duk wani kuskure da zata sake maka ka hukuntata fiyeda yanda zanyi dan in har ta yadda ta sake takowa gidan nan da sunan tayi maka laifi toh saidai ta nemi wani uban ba ni ba kuma", daidai Abu zai amsa wata mata ta k'araso da babbar rigan a hannunta, bata lura da mutannen dake wajen ba ta k'arso tana cewa "Daddy nikam baka gama karanta Jaridan ba, you are getting late fa", sai lokacin ta lura da su Abu, dukda face d'in Abu looks familiar but ta kasa tuna inda ta sanshi, Dad yayi musu introducing juna kan itace sabuwar matar da ya aura 4months back sunanta Kulthum, su kuma ya nuna Abu yace "wannan shine mijin Hauwa Aliyu, wannan kuma d'an uwanshi ne Mustapha", sai lokacin ta tuna inda ta sanshi, duk d'akin Ajiddeh hotunan shine hatta gaban wayarta hotunanshine, da murmushi suka gaisa, Dad ya karb'i riganshi yace "Sai su shiga daga ciki, ni inada meeting, yanda kukayi duk ka sanar dani Aliyu", ya Amsa mishi da Insha Allah da yi mishi fatan a dawo lafiya, a d'akinta Aunty Kulthum ta tarar da ita kwance duk ta rame tayi duhu, kamar ba ita bace ba wannan Ajiddeh sarkin gayu da d'osana lipstick ba, gashin nan ma da yake shan gyara duk ya kad'e, wutan d'akin Aunty Kulthum ta kunna tana mai k'iran sunan Ajiddeh


💖💝BATUUL💖💝

By Phartiemarhk

99

Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR* lolllx

Binsu yayi a baya zuwa d'akin da aka shigar da Batuul d'in, daidai bakin k'ofa wata nurse tace "We are sorry Sir, but you can't get in", wani irin kallo ya jefeta dashi da yake mata nuni da bakida hankali ko, da sauri ta sauk'e idonta k'asa tana cewa "am sorry sir", hannu yasa ya matsar da ita gefe ya tura k'ofar shiga d'akin, kan gado ya tarar da Batuul kwance har an bata maternity wear, sun fito da duk wani abu da ake buk'ata, da sauri ya k'arasa gadon da take kwancen, ido kawai ta rintse tana ambaton sunan Allah dan yau hawayen ma nemanshi take ta rasa, dukda azabar da take sha hakan bai hanata jin d'umin hannunshi cikin nata ba, a wahalce ta bud'e idanunta ta sauk'e cikin nashi, ido ya lumshe ya bud'e, bayason ganin wannan yanayi da take ciki, a hankali tace "Yaa Abu Aunty", kamar wacce ta watsa ruwa haka sweat duk ya jik'ata, hannunta dake cikin nashi ya riqe ya kai bakinshi tareda kissing yace "You will be fine Babyna, we will make it together, am here kinji?", ido ta lumshe tana kad'a kai cikeda azaba tace "inaso inga

1 Comments On BATUUL
avatar
hafsat-9-3

12 months ago

Reply

Nice book

Please Login or Register in order to submit comment