Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gyalen dake yafe akanta ďazu sai hular kawai, idonta dake kan abinda ke hannunta ta ďago suka yi ido huďu, wani irin abu taji gaba ďayanta, shima tsayawa yayi kallonta, idonta ta ďauke daga kanshi shima yayi k'wafa ya fita daga ďakin




k'iran Massa ne ya shigo wayanshi, recieving yayi yace mishi "ka iso ne?, toh gani nan fitowa", motar da Massa ke ciki yaje ya buďe ya zauna , Massa ne ya tambayeshi "ya jikin dai Man, wannan rashin lafiyan ai sai ya bari a kwanakin nan ba, kai da kake shirin zama ango da dai ya isa wani wajen, yayi wrong timing gashi da yake ka fishi k'wari kayi fighting ďinshi", kallon Massa yayi da ďan murmushi a fuskanshi ya girgiza kai yaci gaba da danna wayarsa, "Hello", yace bayan ya an ďauki wayar da ya buga ďin, amsa akayi da "Hello baby, am missing you over here, ya gajiya dan ni gaba ďaya na gaji so nake kawai a ďaura auren nan mu tafi mu huta dan ba k'aramar gajiya nakeji ba a jikina, yanxu ma a ďaki nake ni kaďai wai za a min gyara....", yasan idan ya barta taci gaba da magana sai ya manta dalilin da yasa ya k'irata, katseta yayi yace "gajiya Alhamdulillah, ki faďawa su Mum za ayi miki kéla tul before a tafi wushe wushen a gidan Aunty ďina, kuma kayan wushe wushen ma daga can zaki sa, zan aiko mota by 5, you should be ready", ce mishi tayi "Aliyu gaskiya waďannan abubuwan naku na al'ada na gaji dasu, tunfa last week ake ta yi, kuma kayan ma mum ta riga da tasa an siyomin a turkey, ni gaskiya a bar wannan ďin kawai, ai anyi sauran, kuma ma its too late yaushe zan faďa musu su shirya", ranshi ne ya fara b'aci, cikin dakewa yace "wani shiri zakuyi, ce miki nayi zan aiko mota ki taho ke kaďai, kuma in kin faďawa mum ďin nasan ba hanaki zatayi ba", tsaki yaja dan ranshi daďa baci yayi yace "in na aiko da motar kar kizo" ya kashe wayan , Massa ne ya dubeshi yaga ranshi ya b'aci yace "lafiya naga kana tsaki", tsakin ya kuma ja yace mishi "yarinyar nan , tun last few days nayi observing that duk abinda na faďa sai ta canja, ce mata fa nayi yanxu zan turo driver a kaita gidab Yaa, take cemin ita baza taje ba", bai ci gaba ba Massa ya dafa kafadmďanshi yace mishi "Man its okay, zata dena in sha Allah", da haka suka canja hira, hotel ďin sukaje yaga abokananshi dayawa sun sake k'aruwa, sai da ya ďan huta yake tambayan Massa, "gobe what time za a tafi ďaurin auren Maiduguri", "sunce flight ďin goben k'arfe huďu ne , so muna da time da in mutane suka k'aru za a yi musu booking tunda da yamma ne", "okay" kawai yace mishi suka shiga cikin abokanan





Ganin ya katse wayan ne ta tsaya ta k'urawa wayan ido kamar wanda sukayi wayan dashi ďin zai fito, Mesa Aliyu yake min hakane take tambayar kanta, jibi nefa ďaurin aurensu amma kawai dan ta faďi magana ya katse mata waya harda cewa in ya turo motar kar tazo, ai gaskiya ta faďa tun kwananki suke ta yi musu abubuwa wai al'ada, shi kuma kawai sai ya ďau fushi, a ranta take cewa "dan yaga inasonshi ne yake wasu abubuwan", k'wafa tayi ta cewa mai yi mata gyaran jikin zata je ta dawo, matar tace mata babu komai sai kin dawo, fita tayi daga ďakin, tun daga bakin k'ofa gidan cike yake da y'an uwa d abokan arziki, matane kyawawa, farare da gashi kowa taci kwalliya an zuba gwalagwalai, ďaďďaya zaka bak'i a gidan nan, tana tafiya mutane na ta gaisheta wasu ta gaishesu cikin yarensu shuwa, wani ďaki ta buďe ta shiga, ďakin babba ne mai kyan gaske, babu mutane a ciki sosai, daga Mum , sai wata mata da zatayi sa'ar Mum sai Yaa zee, k'arasawa tayi ta zauana daga gefen mom, matar kawai tace wa "Jainaba inta afe", matar ce tace mata "afe selai Ajiddeh, ya shirye shirye, da gajiya", tace gashinan fa na gaji sosai, ina su Attutu, Abba Mahammad da Adum", ce mata tayi "suna gida bamuzo tare ba anjima za a kawosu", juyawa tayi ta dubi mum da ke jiranta ta gama ta faďa mata dalilinta na fitiwa ana mata gyaran jiki, ce mata tayi "Mum yanxu Aliyu ya k'irani wai zai turo a ďaukeni k'arfe biyar a kaini gidan k'anwar mamanshi, wai akwai wani abu da zasu yi min daga can zamu wuce wajen wushe wushen, kuma ma wai kayan da zan saka ma su zasu bani", cikin ďaga murya Mum ta fara magana "nifa Abun nan nasu Hajiya Bilqees ya isheni, wace al'adarsu ce bamu gani ba fara bikin nan, ni sanin da nayiwa Hajiya Bilqees ma ba kanuriya bace amma gaba ďaya dan tana auren kanuri ta canja gaba ďaya, a ina ake wani kéla tul a Ndjamena, kuma da suke cewa su zasu baki kayan kisa ai ganin kasawarsu ne yasa muka ce zamuyi miki , ko ďari mukace muna so ai yaci a kawo miki, kinfi k'arfin akwatuna arba'in, ba dan Babanku yace a bari ba kuma zai sab'awa duk wanda ya tada maganan wlhy da sai an maida musu tunda dama cewa tayi a dawo dashi in muka k'i karb'a", Yaa zee ce tace "Mum ai ita tabi ta liqewa yaron kamar babu wani namiji a duniya sai shi, ni gaba ďayanshi bai min, sai girman kai da uake dashi kamar mutumin da", matar da aka k'ira da Jainaba ce tace "toh ku yanxu menene na tada jijiyoyin wuya, ai damu suke zancen , ku bari kawai a gama bikin zasu shigo hannu, tayi yadda yace ďin, anjima in ya turo driver kije, tashi kije a gama miki gyaran kamin lokacin yayi", da haka ta mik'e ta koma ďakin, tana zama ta k'irashi, ansawa yayi shiru yana jiran yaji mai zata ce mai zata ce mishi, cewa tayi "Hello baby, toh mey na kashe wayan, in ka shirya ka turo motan na faďwa su Mum sunce inje", ce mata yayi "okay yayi kyau, by five zaizo", ya katse wayan





K'arfe shida na yamma Aunty ta dawo gida lokacin har Batuul sundawo, a palo ta zauna ta k'irawo wayan Batuul tace mata ta dawo, sauk'owa tayi mata sannu da zuwa, zama tayi daga gefenta tace "Aunty ya gidan bikin", ce mata tayi "lafiya Batuul, masha Allah , gobe zasuje Maiduguri ďaurin aure, har Baba ma zaije, amma shi sai ranan ďaurin auren, jibi kenan", baki Batuul ta tab'e tace Allah ya basu zaman lafiya", "Amin" tace sannan tace mata tace "yaushe kuka dawo ne", "tun three thirty suka sauk'eni a gida ita kuma Farida ta wuce gida", ta sake cewa "Aunty maganan admission ďin nawa kunyi da Baban, time yana wucewa", Aunty ce tace "ni na manta ma Batuul amma yau zamuyi maganan in sha Allah , Allah dai yasa kar in manta, "Amin ta amsa da sannan suka mik'e a tare sukaje yin sallah dan an fara k'ira, Batuul na ďaki bayan ta idar da sallah ta zauna tana game a Macbook ďinta, Yusra ce ta shigo tace mata "Yaa Batuul, Mama tana k'iranki tana ďakinta", cemata tayi "kice ina zuwa", ta juya ta fita, tana fita ta ďauke Macbook ďin akan cinyarta ta mayar gefe, mik'ewa tayi tabi bayan Yusra, da sallama ta shiga ta tarar Aunty tana duba abu a closet ďin kayanta, k'arasawa tayi cikin ďakin tare da sallama ta zauna aka makeken gadon ďakin, cewa tayi "Aunty gani", sai da gama dubo kayan da take nema sannan tace wa Batuul "kije ki shirya zamu tafi wushe wushen Aliyu, k'arfe 8 zamu fita, kije maza ki shirya", da sauri Batuul ta ďago kanta tana kallon Aunty, ganin Aunty ko noticing kallon da take mata ma batayi ba yasa ta cewa "Aunty wushe wushe kuma, nifa bazan je ba , tun ďazu ma na faďawa Farida, kuma ma ban shirya bafa", ba tare da Aunty ta kalleta ba tace "ki tashi kije shirya, jama'a sai tambayana ina kike akeyi, wasu ma cewa suke ni ke hanaki fitowa bayan halinki ne na k'in jama'a yake hanaki shiga taro, ki tashi kije ki shirya" tana faďa mata tana warware laffayan da ta ďauko, baki Batuul ta zumb'uro ranta a b'ace ta mik'e ta fita, ďakinta ta isa ta zauna akan gado gaba ďaya ranta a dagule, toh ita wane kaya ma zata sa , bayan angon ma ba son mutane yake ba shine za ace wani sai anje bikinshi, mik'ewa tayi ta shiga toilet ta watsa ruwa ta fito, zama tayi shafe jikinta da mai sannan ta isa closet ďin kayanta ta ciro abaya ďaya a hanga na Al layl mai kyau da purple crystals a jiki ta sa, gashinta ta taje ta k'ara parking ďinshi sannan ta shafa powder ta saka kwalli a idonta da chappete a bakinta, turarenta masu k'anshi ta fesa ta sauk'o k'asa tana jiran Aunty, Aunty na sauk'o zata cewa ďaya daga cikin masu aikin ya k'ira mata Batuul ta ganta zaune a palo, ce mata tayi "Batuul bana son iskanci, kina jina, ince kije ki shirya shine zakije ki wani sako min doguwar bak'ar riga, dama naga ranki bai so ba shiyasa dole ki b'ata min rai ko?, toh ki wuce kije ki canza su kuma karki b'ata min lokaci, mik'ewa Batuul tayi tace "Aunty bansan kayan da zan saka bane", "duk kayanki kice min kin rasa na sawa, ba wushe wushe bane, ai kina da dongashua da zaki saka, ki wuce kije ki canja ki dena b'ata min lokaci", rafiya tayi ta haura sama ,kaya ta canja ta saka shadda duck mai blue da bak'i, ďinkin riga robe da straight skirt, ta ďauko k'aramin jan gyale ta yafa, ta saka sark'a da ďan kunne suma ja da abun hannunsu, shoe Rack ďinta ta nufa ta ďauki slippers ďinta louis vuitton mai ja da bak'i ta saka, tayi kyau sosai har ta fi da, sauk'owa tayi, Aunty batace mata komai ba tayi hanyan waje, Batuul ma ta bita a baya, mota Aunty ta buďe ta shiga, Batuul ma ta shiga gidan gaba, Fa'iza da ke rike da Aabid suka zauna a baya itada Yusra, Aunty ke tuk'a motan suka ďau hanyan inda za ayi event ďin, parking sukayi a wajen parking ďin motoci , suna fitowa daga mota, sautin kiďa ke tashi a wajen, tana fitowa daga mota wata rolls royce ta danno kanta wajen, daidai fuskan Batuul motan ya haska, tsayawa tayi mai motan ya gama iskancinshi na haske mata ido sai ta tafi dan bata gani, su Aunty har sunyi gaba sun barta, k'ofan motan aka buďe, iska ne ya buso mata k'anshi turaren, kanta ta ďago dan tasan mai turaren, kashen wutan motar akayi tana ďaga ido, fuskan Abutturab idonta ya sauk'a akai, ba kaďan ba yayi kyau, kaftan sky blue ya saka, yayi kyau sosai, shades ďin ray ban ne mak'ale a idonshi, gani tayi yana tahowa hanyanta, tsayawa tayi ta kasa motsi sai bugun da zuciya ya fara











Aunty(Mama) haka k'annen Batuul ke k'iranta
💖💝BATUUL💖💝

19

By phartiemarhk

Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*

Ganin yana nufota ne tayi maza ra rik'e rigan cikinta, ray ban glass ďin dake fuskanshi ya cire , ido huďu sukayi da Batuul, kasa ďauke idonta tayi daga kallonshi shima hakan bai ďauke nashi ba, sai da ya iso har inda take sannan ya tsaya, idonta ta ďauke daga kallonshi shi kuma yaci gaba da kallon nata, a hankali ta sake rik'on da tayiwa riganta, ya buďe baki kenan zaiyi mata magana ta juya a guje ta bar wajen, ranshi ne yayi bala'in b'aci ya daka mata tsawa, " *Batuul*", ko juyowa batayi ba taci gaba da gudunta, sosai ranshi ya b'aci, ba sau ďaya ba yanxu tana mishi irin haka sai yana mata magana ta gudu, tunawa yayi da ranan da ya fara ganinta ranan idi, haka ya buďe baki kenan zai ce mata ta gyara gyalen kanta, gashinta na a waje tak'i ko da tsayawa jin mey zai ce mata ta gudu, ko ďazu ma haka tayi mishi ta gudu daga ďakin yana k'wala mata k'ira, inda tabi ya kafawa ido yana daga tsaye, ji yayi an dafashi ta baya, Massa ne ya zagayo gabanshi yace mishi "Yanxu amarya ta k'irani wai suna ciki tun ďazu, sun jiramu bamu zo shine suka shiga", juyowa yayi ya dubi Massan sannan yace "toh mu shiga", shi da tawagar sauran abokanshi da kana ganinsu kasan dagaske suke suja k'arasa ciki, fili ne babba zagaye da canopies sai kujeru daga ciki biyu aka kasa wajen, side ďin amarya da gefensu, k'awayenta da dangi, sun sha ankon atamfa maroon, sunyi kyau sosai kasancewarsu farare, ďayan side ďin dangin ango ne suma da ankonsu na irin kayan da Batuul ta saka, daga gefe side ďin amarya ne da ango anyi musu rumfan fulawa da kujeru biyu, mutanene cike a wajen wasu na zaune wasu na kai kawo, Kamal da Mansur ne daga tsakiya rik'e da mic suna ta rero wak'a, ganin ango da abokansa sun shigo ya sa mawak'an k'ara kaimin wak'arsu, k'anshin turaren wuta ke tashi ta ko wane angle,tuni wajen ya kaure da hayaniya, k'awayen amarya aka fara k'ira suyi rawa da danginta, sun shiga sun tattaka rawa sosai sannan aka k'ira Family ďin ango, Batuul na zaune ita da Farida duk ranta a b'ace, gaba ďaya bata so Aunty ta sata zuwa wajen nan ba, ta k'agara ayi abinda za ayi ita ta koma gida, k'iran y'an uwan angi ne ya sa Farida mik'ewa zata shiga wajen rawa tare da janyo hannun Batuul, warce hannunta tayi daga rik'on da Farida tayi mata tace "mey haka kike jana, mey zan tashi inyi miki", "rawa mana baki ji an k'iramu bane, ai ni komin rashin shirinmu da Yaa Abu sai nayi rawa, ba namu bama munyi bare na gida", ta faďa tana dariya, "A dawo lafiya", inji Batuul ta sunkuyar da kanta taci gaba da dannan wayanta, Farida ganin dagaske Batuul take ya sata juyawa ta shiga filin rawa, rawa sosai su Farida sukayi da sauran family, sai da suka gama lokacin aka k'ira ango da amarya su fito suyi rawa, mik'ewa sukayi a tare shi da Ajiddeh, sosai tayi kyau, bak'in lace ta saka da blue laffaya, anyi mata kéla yaskè(kitson gaba) da aka bi akayi mishi ado da gold sai ya k'ara mata kyau, ko ina a jikinta gold ne , har anklet sai da ta saka na gold da nose ring, hannayensu mak'ale cikin na juna suka tasi suka isa filin rawar, mutane ne suka shigo ana ta yi musu lik'i, abokan ango dollars, Euros suke zubawa amarya, sau ďaya Batuul ta ďago kanta ta kallesu ta mayar, wayanta ne taga yana ringing, Aunty ke k'iranta, jutawa tayi ta dubi inda Aunty ke zaune taga tana mata alama da tazo da hannu, tashi tayi ta isa inda Aunty ke zaune, sai da ta zauna a empty kujeran dake gefen Aunty sannan tace "Aunty gani", jakanta ta ďauko sannan ta ciro bandir ďin 1000 sabbi dal ta mik'awa Batuul, da ido Batuul tabi kuďin tana jira taji na meye na "Kije kiyiwa ango da amarya lik'i, ni bana son tashi saboda da Aabidĺ, Batuul gaba ďaya bata yi zaton abinda Aunty zata sata yi ba kenan, ranta ya b'aci amma ba tayi musu ba dan bata son b'atawa Aunty rai kamar ďazu, kuďin ta ansa sannan ta mik'e Kamar mai shirin yin kuka rai b'ace ta isa inda suke, y'an dubu dubun nan ta rik'a cirowa tana yiwa amarya lik'i dashi, wani mugun harara Ajiddeh tabi Batuul da, daga k'arshe ma barin wajen tayi ta koma daga gefe wajen danginta, Batuul bata sanma tana yi ba, kuďin da yake hannunta tabi da ido, ko rabi bata lik'a ba, juyawa tayi ta dubi Abutturab taga idonshi na kanta, sauri tayi ta ďauke nata idon, Aunty ta sake waigawa ta duba a inda take zaune taga tana kallon wajensu, babu daman ta bar wajen, kawai kuďin ta fara zara tana yiwa Abutturab lik'i da, ido ya kafa mata yana kallon yadda tayi kicin kicin da fuska tana b'ata rai, Massa ne ya hango Batuul tana yiwa Abutturab lik'i, zuwa yayi inda take ya fara mata ruwan dollars a kanta, gaba ďaya sauran abokan ango ma hankalinsu kan Batuul, lik'i suka dinga yi mata kamar itace amaryar, ba k'aramin haushi Ajiddeh taji ba, ji take kamar ta shak'e yarinyar nan ta huta, gaba ďaya bata sonta , hankalinta sam bai ďauki Batuul ba, wani irin b'ata fuska Abutturab ya rik'a yi ganin yadda abokansa ke yiwa Batuul lik'i bayan ga amaryar basu yi mata ba, niyya yayi yaje yace su dena wannan shirmen, A guje Batuul ta sake kuďin hannunta a jikin Abutturab ta fice daga filin dan ta tsorata sosai da yadda dukkansu ke mata lik'i ita da bama rawa tayi ba, wajen zamanta ta k'arasa ta zauna, tana zama Massa ya bita shima ya zauna a kujerar Farida dake gefen nata, wani irin murmushi yayi mata yace "Fatima ko", kai ta gyaďa mishi ba tare da ta ďago ta dubeshi ba, k'anshin turarenshi duk ya cikata har yana neman sa mata murya, juyawa tayi ta dubi inda Aunty take taga hankalinta baya ma wajensu, ita masu rawa take kallo, "masha Allah", yace sannan yace "ranan grads ďinku i wanted talking to you sai kuma ban samu chance ba, you know kin burgeni, ni ban tab'a sanin Su Baba nada yarinya babba haka ba sai ranan graduation ďin da naji sunanki, kin tab'a sanin Aunty ce ta yayemu ni da Aliyu, ina zaki sani ai ba a haifeki bama lokacin", ďagowa tayi ta dubeshi , toh ita mey ruwanta da Aunty ta yayesu, ina ruwanta ma in a gidansu aka haifeshi shi da Aliyun, juyar da kanta zatayi taga idon Abutturab a kansu rai a b'ace, ďauke idonta tayi taci gaba da wasa da awarwaron hannunta, "Cutie, it seems your mind is totally not here, mayb you should share your contact with me, sai muyi magana anjima, nima ďin yanxu am busy", dariya ne ya kusan kufce mata na sunan da ya k'irata dashi wai cutie, da har zata bashi number ta na da sai kuma ta tuna ai zai iya tambayan Farida ma ta bashi, deciding tayi da ta bashi natan , ai ba lallai ne in ya k'ira ta ďauka ba, karanto mishi tayi numbers ďin ya rubuta a wayanshi, mik'ewa yayi tareda kai hannun zai shafi fuskanta rayi maza ta matsa da baya, idon Abutturab akansu duk abunda sukeyi yana kallonsu sai ma harara da yake binsu da, tashi yayi zai fita daga filin ranshi b'ace, Massa ne ya hango shi zai fita yayi maza ya cewa Batuul "Aii cutie we will talk later", yayi maza yabi bayan Abutturab yaji lafiya zai fita ana cikin event, daga waje ya tarar da shi wajen da sukayi parking motoci, zuwa yayi yacewa Abutturab"Ya ka fito ka bar amaryarka a ciki, ana ta event, wato halinka ko a ina sai ka nun.....", bai k'arasa ba ya katse shi da "Mustapha what is wrong with you, for Gods kaga abinda kuka dinga yi a wajen nan, duk kun wani juya kuna yiwa yarinya lik'i bayan amaryar ma baku yi mata wanda kukayiwa yarinyan nan ba, kuma da ta bar wajen ka wani bita a baya , wannan ai neman raini ne a wajen yara, mey zaka nema a wajen Batuul yarinya k'arama, k'annenmu nefa, y'ar Aunty ce inma baka sani ba toh ka sani, k'anwar kace", kasake Massa yayi yana kallonshi, wannan faďa da yake yi kuma na meye haka, ce mishi yayi "toh menene in k'anwata ce ko kuma y'ar Aunty ce, ai nan nema zanyi yadda nakeso ko akwai inda aka hanani nemanta, kuma right from day one na faďa muku ni k'aramar yarinya zan aura, manyan mata wannan sai ku, kuma Batuul is d right choice for me saboda abinda ya fara min tarbiya shi yayi mata tarbiya dan haka ana gama bikinka zan kai nawa maganan gaba sai dai in itace tace bata sona" ya faďa yana maida numfashi, wani irin kallo Abutturab ya bishi dashi ya rasa mey zai ce mishi, tsaki yaja ya koma cikin wajen Massa ya bishi a baya

Yana barin wajenta ta sauk'e ajiyar zuciya, ďazu a wajen lik'in nan taji an k'irashi da Massa, da ma shine, tab'e baki tayi a ranta tace toh wannan ne prince , ai surutunshi yayi yawa, dama Abutturab ďin ne prince zai fi dan shi yafi ji da kai, ku kuka sani dai, dama sune take ganin pictures ďinsu a album ďin gidansu suna yara , baki ta tab'e tace ku kuka sani dai,

Mik'ewa tayi daga indactake zaune ta isa wajen Aunty, marairaicewa tayi kamar zatayi kuka tace "Aunty, ciwon kan ďazun fa ya dawo, insaso in je gida", dubanta Aunty tayi sannan tace "baki sha magani bane ďazu", da sauri ta kaďa kai, "nasha, mayb effect ďinshi ne ya sakeni, inaso in sake shan wani", Aunty bata sake cewa komai ba ta ďaga waya ta k'ira Ahmad, yana amsawa tace "ga Batuul nan zaka kaita gida, kanta na ciwo", bayan ta katse wayan ta cewa Batuul "ki tashi ku tafi, Allah ya sauwak'a, in kuma zaki iya ku bi ta asibiti Dr zaka ya dubaki", cewa tayi "toh Aunty bari muga idan na sha na yau ďin bai yi ba sai mu tafi gobe ya dubani", da haka ta mik'e tayi hanyan waje, a bakin k'ofa tazo zata fita shi kuma zai shigo suka kusa bugewa, matsawa tayi da sauri kar ya bugeta dan taga ranshi duk a b'ace, tsayawa yayi kallonta har sai da ta wuce, Massa ne da ya ganta ya fara smiling, "Cutie ia zuwa", sunan da yaji ya k'irata dashine yasa shi saurin juyowa, tsayawa yayi yaji mey zatace, a hankali kamar mai raďa ta ce mishi "kaina ne yake ciwo za a mayar dani gida", baiji mai tace ba, haushi ya sake turnuk'e shi yaja tsaki ya shiga ciki, tsakinshine ya jawo hankalinsu suka dubeshi, su sunace ma ya tafi, da damuwa Massa ya dubeta "let me drop you mana", "No brother na yana jirana shi zai kaini, nagode" tace ta juya ta bar wajen bata sake ce mishi komai ba, a mota ta tarar da Ahmad yana jiranta, buďewa tayi ta shiga ta zauna, with concern yace mata "sannu Yaa Batuul", ta amsa da "yawwa muje", dan so take ta bar area nan gaba ďaya, rage Ac motar yayi sanan ya tada suka tafi

A kujera ya tarar da Ajiddeh ta cika tayi fam, yana zama ta dubeshi tace "Aliyu dama wushe wushen naku kenan, muzo a wulak'anta mu", tunda ta fara magana bai ce mata komai ba sai da yaji ta ambaci wulak'anci, katseta yayi tareda da tambayanta "wulak'anci mey aka yi muku", "ehh mana wulak'anci mana , dubi fa yadda abokanka da yan uwanka suka dinga yiwa bak'ar yarinyar nan lik'i kamar itace amaryar, da kunsan ita kuke son yiwa lik'in kaje ka aureni, ai da an aura maka ita sai kuji daďin yi mata lik'in da kyau, wani kallo ya bita dashi da ya sata haďiye magananta da sauri, "mey ke damun kankine wai, wa yace miki ana faďa min ko wane irin magana, ba ni ba ko mutum dake kusa dani bana yadda a faďa mishi magana anyhow bare ni da kaina, da kike cewa a aura min ita ai da naso tare za a haďa min dake akai min ku ko kuma in fasa nakin in aureta, sai ki rik'a yin magana kamar yarinya, jibi ne ďaurin aurenmu inma zaki gyara tun wuri ki gyara dan bazan yi tolerating shit ďinnan a gidana ba, you have change", ya faďa yana mai kallon agogon hannunshi, duk maganan da sukeyi a hankali suke

1 Comments On BATUUL
avatar
hafsat-9-3

12 months ago

Reply

Nice book

Please Login or Register in order to submit comment