Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne, haka ayanzu ma kai ɗin, you are the super hero, sannan kafi kowa sanin nakasa bata taɓa zama kasawa, sai-dai ga wanda ya bari zuciya da kuma tunaninsa suka mace, saboda haka ako yaushe kasa azuciyarka cewa, kai ɗin jarumi ne!! Sai dai kuma in salon tirjiyarka ce hakan".
Taƙare maganar tana me ɗan bubbuga kafaɗunsa tana murmshin zanca wai shi mai raunine kaji yaro da wayo wato ace bazai iya jure mu'amala da mata biyu ba.
Shiru yayi tare da lumshe idanunsa,  hakan na nufin cewa kenan bashida wani zaɓi? ko kuwa dai ƙaddaransa ne take ƙoƙarin canzawa?
Ganin yayi shiru ne yasa Adda Rahama komawa kan kujera ta zauna, nan ta shiga cin abincinta hankali kwance.

Da sallama Hayatuddeen ya shigo cikin falon Ummi, ganin su azaune ga kuma Hammansa daya haɗe fuska, yasan yashi ƙarasowa cikin falon, jakar makaranta da kuma littatafan dake hannunsa ya watsa akan kujera, zama yayi daɓas akan sofa, tare da miƙe ƙafafunsa, cikin shagwaɓa haɗi da kasala ya ɗago indo ya dubi Ummi, asangarce yace.
"Ummi am so tired, ƙafana bayana kaina idona kunennena ɗuwawuna kai ko'ina ɗina ma ciwo suke min!."
Murmushi Ummi tayi, tare da cewa.
"To sannu auta na, ae dai ku kam gaba ɗayan ku haka kuke, abu kaɗan ke gajiyar daku, sai kace ba gwaraza ba."
Sake shagwaɓe fuska yayi, cikin salon sakalci yace.
"Wallahi Ummi makaranta ba daɗi, duk acika ku da lectures, yau fa ko ɗan hutu bamu samu ba."
Ƙare maganar yayi yana me ɗago kansa, inda ya kalli Saifuddeen, wanda ya haɗe fuska, inda ya kawar da kansa gefe, da'alamu cewa ba ya cikin yanayi me daɗi, cikin kulawa haɗi da faɗuwar gaba, asanyaye Hayatuddeen ɗin yace.
"Hamma!."
Kasancewar Saifuddeen ɗin ya juyar da fuskarsa, zuwa wani ɓangare na daban hakan yasa baiji ƙiran da Hayatuddeen ɗin yayi masa ba, don dama sai yana kallon ka ne, sannan yake karantar abun da kake faɗa, ta hanyar kallon yanayin motsin bakinka shiyasa yake da yawan kallon ammanfa ga wanda yake son ya gane abinda zai faɗa.
Ganin Hamman nasa baisan da cewa yanayi ba, hakan yasa ya taso da sauri ya, ƙarasowa gaban Hamman shi hannunshi ya ɗaura a akan kafaɗan Hamman nasa, ahankali Saifuddeen ya ɗago da kansa, duban Hayatuddeen ɗin yayi, sai kuma ya kau da kansa gefe.
Hakanne yasa jikin Hayatuddeen yayi sanyi sosai.
A take kuma yaji gabansa ya faɗi, ƙirjinsa ne ya shiga duka, cikin zuciyarsa yace.
"Nashiga uku badai Hamma na yasamu labarin cewa, yau na fita amakaranta, na bi Khamis muntafi yawo ba?."
Cikin ɗari-ɗari da fargaba ya kalli Ummi, wanda ke ƙoƙarin tashi, don komawa ɗaki, da sauri ya rufa mata baya, jin mutum abayanta yasata juyowa, kafe Hayatuddeen ɗin tayi da ido, tare da cewa.
"Lafiyanka ƙalau kuwa kake biye dani, sai kace wani ƙaramin jariri, kodai ka aikata wani rashin gaskiya ne?."
Ummi tafaɗa tana me ƙare masa kallo, don tsab tasan yaranta, da zaran sunyi wani abun da ba dai-dai ba, takan saurin ganewa, ko daga halin rashin nutsuwa da zata gansu aciki, kamar dai yadda ta fara zargin yanayin canji nitsuwar Hayatuddeen.
Ƙifi-ƙifi Hayatuddeen ɗin yayi da idanunshi tare da cewa.
"A'a babu abun danayi, kawai dai naga ran Hamma Saifuddeen ne kamar aɓace yake."
Ajiyar zuciya Ummi tayi tare da cewa.
"Hmm rabu da Hammanku, gata ake son a mishi shi kuma wai baya so."
Da sauri yace.
"Ummi wanne irin gatane?."
murmushi tayi tare da cewa.
"Wai fushi yake don ance masa ya ƙara aure, shine yake ta faman haɗa rai sai kace wanda akace yayi wani abun, wanda ba dai-dai ba."
Cikin zaro ido Hayatuddeen yace.
"Haaah Ummi to kuce ni inyi auren mana, tunda shi baya son gatan ni kuyi mini."
Cikin mamaki da al'ajabi da zazzaro ido Ummi tayi kana tayi kasake tana kallonshi da nazartanshi.
Shi kuwa da sauri ya dawo nitsuwarsa gudun karta ramfoshi.
Ajiyar zuciya mai ƙarfi Hayatuddeen ya sauƙe, ya godewa Allah da yasa, ba asirinsa bane ya tonu, domin yasan tabbas idan Hamman nasa, ya gane irin abubuwan da yake yi, to fa kashinsa ya bushe, yasan sai anrabasa da duk wani abu nasa najin daɗi.
Gyara tsayuwarsa yayi tare da cewa.
"To Ummi me yasa zai ƙara aure, yaushe ma yayi auren?."
Harara Ummi ta watsa masa, tare da cewa.
"To kai mekasani acikin aure da kake tsoma baki cikin abun  da babu ruwanka?."
Kanshi ya jujjuya tare da cewa.
"Wallahi ba abinda na sani, kawai a auro mishi mai sonshi tunda hegiyar nan taƙi zama."
haɗe fuska Ummi tayi tare da cewa.
"Hayatu baka da kunya fa ba yayarka bace kake ce mata hegiya, to a kul wlh kada in sake jin ka zagarmin ƴata dan mu dai Zaleeha bata ƙi muba bata mana wani laifiba ita dai auren ne da bata so."
Murmushi yayi tare da ɗan shafa kansa yace.
"Afwan ya Ummi bazan sakeba, nima nasan Zaleeha na sonmu amman dai ina jin haushinta in na tuno wai bata son Hamma nane yasa ta gudu."
ya ƙarishe mgnar tare da, juyawa ya inda ya fice daga cikin ɗaki, a falo ya samu Adda Rahama, har yanzun Saifuddeen na zaune afalon,   komawa kan sofa yayi ya zauna, inda ya matso kusa da Adda Rahama wanda kecin abinci,  dubansa Adda Rahama tayi tare da cewa.
"Bafa zanci dakai ahaka ba, jeka wanko hannunka."
Ɗan shagwaɓe fuska yayi tare da cewa.
"Dan Allah Adda Rahama, muyi karɓe-karɓe, don nagaji, dama kafun na zauna ne kikace na wanko hannun nawa."
Kai Adda Rahama ta girgiza tare da cewa.
"Allah ya shiryeka, sarkin lalaci kawai, da ace kai mace ne, tabbas da anyi uwar son jiki."
Murmushi kawai yayi tare da amsan spoon ɗin dake hannunta, haka suka shigayin karɓe-karɓe, idan tayi loma guda, ta bashi spoon ɗin shima yayi, duk wai saboda tsananin ganda, ɗauko spoon kaɗai ya gagaresa.
Ummi ce tafito ɗaga cikin ɗaki, hannunta ɗauke da wayarta, duban Saifuddeen tayi tare da cewa.
"Bappa Ali ne ya ƙira."
Ɗago kai Adda Rahama tayi tare da cewa.
"Akan maganan auren ne ko?."
Kai Ummi ta jinjina tare da cewa.
"Ƙwarai kuwa, koda na faɗa masa cewa, babu wacce ayanzu Saifuddeen ɗin keso, cewa yayi wannan ba uzuri bane, za'a ne mamasa ko acikin dangi."
Idanu Saifuddeen yaɗan zaro waje, kasancewar yana kallon Ummin nasa, hakanne yasa ya fahimci me take faɗa.
Murmushi Adda Rahama tayi, ɗan satan kallon Saifuddeen ɗin tayi, cikin kulawa tace.
"Hakan ma yayi, tun da dai shi yace bashida zaɓi."
Hayatuddeen ne ya ɗago kai tare da duban Ummi, cikin nutsuwa yace.
"Acikin dangi kuma tab, nikam dai banso Hamma ya yi auren dangi, to idan ma hakane ae ga nan Amina da Asma'u, duk suna sonshi, musamman  ma Ameena, dake bala'in sonsa ae sai ya zaɓi ɗaya acikin su ko?."
Ɗan jim Ummi tayi, nan kuma tasaki murmushi, cikin gamsuwa da kalaman Hayatuddeen tace.
"Tabbas, ka ga kuwa ni na manta ma da batun Ameena, gaskiya yarinyar akwai hankali, sannan kuma tana da kirki sosai, don ko lokacin da yake jinya a Hospiatal ɗin Abuja, ta kula dashi sosai, gaskiya na yaba da hankalinta sosai tana son Babana."
Duban Ummi Adda Rahama tayi tare da cewa.
"Okay wannan nurse ɗin ba, gaskiya nima yarinyar ta kwanta min arai, sai-dai kuma wacece Asma'u, don ban shaida ta ba."

Carab Hayatuddeen yayi inda yace.
"Wata jarumar film ne, kinma santa ae, wannan Asma'u Ahmad Matawalle wanda take rawa da waƙa, tauraronta yana haskawa sosai."
Idanu Adda Rahama ta ɗan zaro tare da cewa.
"Mai rawa da waƙa kuma? chab awani gidan? gaskiya a'a, Ameenan dai tayi, don ƴar gidan mutumci ce da dukkan alama, kuma Saifuddeen da yawan kishi ai bazai iya aurenta ba."
Cikin gamsuwa Ummi tace.
"Tabbas nima Ameenan tafi kwanciya min arai, don dai ita Asma'un kam sam batayi ba, don idan ma muka zaɓeta bamusan da wanne ita kuma zata zo ba, duba da irin lalurar da yake fama da ita ma, sam baidace ya auri wata ƴar nanaye ba, wanda suka saba cuɗanya da maza, ko yaushe suna cakuɗe da maza awaje guda ga Saifudden da ɗan karen kishi, balallai ma yasamu ingantacciyar kulawa daga gareta ba, Ameena ɗin dai ita muka zaɓa."
Nan Adda Rahama ta jinjina kai cikin gamsuwa.
Shikuwa Saifuddeen daya duƙar da kanshi kasa, sai alokacin ya ɗago, kasancewar bai kallesu ba, hakan yasa baiji mai suka tattauna ba.
Madanannin wheellchair ɗinsa ya danna, kai tsaye yanufi hanyar barin falon, don yagaji so yake yaɗan je ya kwanta ya huta.

Yana fita Ummi ta dubi Hayatuddeen wanda keta aikin zubawa cikinsa abinci, cikin kulawa Ummi tace.
"Hayatuddeen bani wayarka."
Adaburce ya ɗago kansa, kasancewar yakai loman abinci bakinsa, hakanne ya sakashi ƙwarewa, take tari ya sarƙesa, da mamaki Ummi ke kallonsa, yayinda Adda Rahama kuma keyi masa sannu, botle water ta miƙo masa, nan ya amsa haɗe da kafa bakin goran abakinsa, saida yasha sosai kafun yaji ya samu relief,   cikin kulawa Ummi tace.
"Sannu, haba kaima sai cikawa cikin ka abinci kake babu ko tsayawa, tayaya bazaka ƙware ba, bacin abincin ba guduwa zaiyi ba, kana abu kamar mara gsky."
Shiru yayi tare da ƙoƙarin neman hanyar barin falon.
Dubansa Ummi tayi tare da cewa.
"Ina kuma zakaje? bacewa nayi kabani wayarka na ɗau number'n Ameena ba."
Jin haka yasashi sauƙe gagarumar ajiyar zuciya,  zaro wayar daga cikin al'jihun wandonsa yayi, nan yashiga contact ɗinsa, inda ya laluɓo number'n Ameena'n, nan ya miƙawa Ummin nasa.
Tsab Ummi ta kwafe number'n Ameena'n, inda ta sanya awayanta, kana ta miƙa masa wayarsa, haka ya wuce sama sumu-sumu, daganinsa kasan bashida wadataccen gaskiya.

Nan Adda Rahama da Ummi suka ci gaba da tattaunawa akan sabon auren da za'a ƙarawa Saifuddeen ɗin, sai ayanzu ne suma suke ganin cancantar yin hakan, saboda Zaleeha ta gujesa, tana ganin cewar shi nakasashshe ne, yayinda su gani sukeyi dan shi nakasasshene yasa ta gujeshi sannan babu wata mace wanda zata iya zama dashi, hakan yasa dole ne ma su Aura masa Ameena, tun da dai ita tana son shi, sun tabbatar da cewa kuma zata kula dashi. Sun ɗan taɓa hira kafun Adda Rahama ta tafi, Ummi kuma ta nufi ɗaki ta kwanta, bayan taƙira Bappa Ali ta sanar masa zaɓin da tayiwa Saifuddeen ɗin, sosai shima Baffa Ali'n yayi na'am da batun, nan take yaƙirayi Baba Malam ya sanar masa, da batun,  sosai Baba Malam yaji daɗi, don kuwa ko ba komai hakan da sukayi sun karramasa.

Saifuddeen kuwa yana shiga ɗakinsa, ya soma rage kayan jikinsa,  ƙarasawa gaban tankamemen bed ɗinsa yayi, nan ya sauƙa akan wheellchair ɗinsa, inda ya hau gadon.
Lumshe idanunsa yayi tare da jawo blanket ya rufe jikinsa,   maganar ƙarin auren nasa daya dawo cikin kunnensa ne, ya sashi jin wani ɗaci a maƙoshinsa, sam shi baima ɗauki abun agaske ba, yasan suna faɗa ne kawai, amma shi ina yaga ta wani ƙara aure, shiru zaiyi ya ƙyalesu, yasan nan da kwana biyu suma zasu daina batun.

Yana nan kwance, yaji vibration na wayarsa, don dama akusa dashi take.
Kasancewarsa wanda bayajin magana, ko kuma wani sauti, hakan yasa koda yaushe wayarsa a vibrate take,  domin ta hakanne kaɗai zai gane cewar an turo masa saƙo, domin idan kunnensa baya ji, to ai jikinsa naji, don aduk sanda wayan ke kusa dashi, ko kuma take jikinsa, to zai jita tana rawa, hakan kuwa alamane na cewar an turo masa saƙo, ɗaukan wayar yayi tare da dubawa, ganin  saƙon na Ummin sane ya sashi buɗewa.
Number'n wayane arubuce da kuma rubutu aƙasan sa kamar haka.
"Wannan number'n itace number'n matar da na zaɓa maka amatsayin wacce zaka aura, saboda haka kayi saving ɗinta."
Yana gama karanta saƙon ya tashi zaune cikin hanzari, jiyayi gabansa ya faɗi, cikin sauri ya jawo rigarsa wanda ya cire, nan ya sanya tare da hawa kan wheellchair ɗinsa, ahanzarce ya nufi part ɗin Ummi'n dan yafa lura su da gask suke nufin ƙara mishi auren.

Koda yaƙarasa falon ta bai ganta ba, kai tsaye yanufi bedroom ɗinta.
Tsayawa ajikin ƙofar yayi, tare dayi mata knocking,  Ummi dake kwance jin ana knocking yasa ta tashi ta zauna, murmushi tayi don tasan cikin biyu za'ai ɗaya, ko Saifuddeen ko kuwa Raleeya.
"Shigo." Ta faɗa ataƙaice.
Da sauri ya tura ƙofar ya shiga, Ummi na ganinsa taɗan tsume, tare da dubansa.
Ƙarasowa yayi har gabanta, inda ya kamo duka hannayenta, kansa ya shiga girgiza mata, alaman "a'a."
murmushi tayi tare da cewa.
"A 'a me? bazakayi auren ba ko kuwa me? ko bakason zaɓin danayi maka, ba kuma zaka iya karɓanta matsayin zaɓina ba?."
Shiru yayi tare da ɗan lumshe idanunsa, kansa ne ke sarawa, cikin body language ɗinsa, yace.
"Bawai zaɓinki bane banaso Ummi, ni auren ne banaso, ki dubeni ki gani fa, tayaya zan iya rayuwa da mata biyu, ko kun manta abun da Dr. ya faɗa ne, ina ɗauke da nakasa banjin cewa, zan iya bawa mata biyu kulawan daya dace dasu ba."
Dariya Ummi tasanya, tare da dubansa, saida tayi dariya sosai sannan taɗan soma tsagaitawa, shikuwa Saifuddeen kafeta yayi da idanunsa, tare da sanya mata fuskan tausayi.
Ɗan tsagaitawa da dariyan Ummi tayi tare da cewa.
"Ikon Allah, Yau kuma Saifuddeen kaida kanka kake ƙiran kanka da Nakasashshe? duk saboda ance ka ƙara aure shine har ka aminta cewar kai nakasashshe ne, har kuma ma kake ƙiran kanka da hakan, tsawon lokaci ban taɓa ji kaƙira kanka da wannan sunan ba, amma yau sai gashi da bakinka ka faɗa, ka kuma nanata.  hmmm lallai ma kuwa to wallahi in sha Allah auren nan babu fashi, sai anyi shi, na kuma gama yi maka zaɓi, umarni ne idan kuma kace a'a, shikenan saika ƙira surukin naka wanda ya yanke hukuncin, kace masa kai bazaka bi umarninsa ba."

Idanunsa ya lumshe, jin zuciyarsa yake tayi masa nauyi, a kasalance, cikin yanayi marar daɗi yace da Ummi, ta sanar dashi, "Wacece zaɓin nata?."
Nan Ummi tace.
"Idan yana buƙatar sani, zai iya zuwa ya tambayi Adda Rahama, zata sanar dashi koma wacece."
Jin haka yajuya yafita jiki a mace, yana mai saƙawa ransa to wacece ina take ina suka samota da zasu liƙa mishi ita, tuno babu in da zai samu amsoshin duk waɗanan-nan tambayoyin sai wurin Adda Rahma.
Ae kuwa kaman jira yake cikin sauri ya juya ya fice daga cikin ɗakin.
Kai tsaye ɓangarensa ya nufa, inda ya kimtsa kansa,  koda ya fito text message ya turawa Ahmad kan cewar yana son ganinsa.
Kasancewar Ahmad ɗin na cikin gida, hakan yasa mintuna kaɗan sai gashi ya fito.
Cikin body language Saifuddeen ɗin yace da Ahmad.
"Ya kaishi gidan Adda Rahama."
Sanin kwanan zancen yasa babu musu, Ahmad ya ɗauko musu mota, nan suka shiga, inda ya jasu zuwa gidan Adda Rahaman bayan sun biya jonapwd sun ɗauƙi ishaq wanda a zaton Saifuddeen ishaq zaibi bayanshi.

Koda Adda Rahama ta gansu batayi mamaki ba, don tun kafun zuwansu Ummi ta ƙirata ta yi mata bayanin komai.
Tray ɗin drinks masu sanyi ta dire agabansu, Ahmad ne ya ɗauki kwalin exotic ya miƙawa ishaq kana shima ya ɗauka inda yasoma kwankwaɗa, don shi fes yakejin ransa bashi da wata damuwa.
Hakama ishaq da shi yafi kowa jin haushin Zaleeha, kuma Babanshi ya mishi bayanin son ƙarawa Saifuddeen aure da Baban Zaleeya ya shiryawa.

Saifuddeen kuwa fuska ya marairaice, duban Adda Rahama yayi, tare da ɗaukan wayansa, cikin message ɗin Ummi ya shiga, nan ya nuna mata fuskar wayar, tare da yi mata alaman tambaya, kan cewa.
"Wacece? Ina take?".
Murmushi Adda Rahama tayi masa tare da cewa.
"Miye abun tada hankalinka haka ne Saifuddeen? da ka nutsu ma don amaryar taka ba ɓoyayya bace awajenka kasanta."
Cikin son ƙarin bayani ya zubawa Adda Rahama'n fararen idanunsa.
Duban tsab Adda Rahama tayi masa, kana cikin nutsuwa tace.
"Nasan kasan Ameena ae, wannan nurse ɗin da ta baka kulawa, lokacin da kake jinya a Abuja, kafun ku wuce India, to ita ce dai Ummi ta zaɓa maka, nima kuma nayi na'am don yarinyar akwai hankali, Masha Allah.
Ka tuna har gida tazo itada Mamanta suka dubaka da jiki."

Idanunsa ya zazzaro waje tare da jujjuya kai da ƙarfi sosai yashiga mamaki, lokaci ɗaya yaji kaman an watsa masa ruwan zafi, amamakance ya ɗan ƙanƙance idanunsa, cikin yanayin maganarsa wanda ya saba, wato body language yace.
"Allah ya sauwaƙe ni dai na auri wannan Ameenan, mezanyi da ita bazawara ce fa!."
Cikin tsananin mamaki Adda Rahama ta dubeshi,  kallonsa tayi da kyau tare da faɗin.
"Kai Saifuddeen banda sharri bazawara kuma? wa ya faɗa maka cewar bazawara ce?".
Murmushin gefen baki yayi, tare da jijjiga kansa, in a body language ɗinsa yace.
"Impossible!, nine zan auri bazawara? chab hmmm Allah ma ya sauwaƙe, sam banason sauran wani wlh Allah ya kiyasheni suɗe ƙashin da wani ya rigani tsotsa."
Baki Adda Rahama ta buɗe fuska cike da tarin mamaki sauƙe a jiyan zuciya tayi tare da cewa.
"Wai nikam wayace dakai itaɗin bazawara ce?."
A shagwaɓe ya rubutawa Addan nasa.
"Ae basai an faɗa min ba, duk ckekken Namiji in dai ya nitsu idan mace bazawara ce zai gane ta ido, kuma nayi imani cewa Ameena bazawara ce, saboda haka ni dai bana sonta wlh bazan iyaba, ba kuma zan aure ta ba."
Ahmad da Ishaq kam dariya sukeyi sosai fahimtar abinda yake faɗin.
Baki Adda Rahama ta taɓe, inda ta gyara zamanta, dubansa tayi da kyau,ido cikin ido tace.
"Naji koma dai bazawara ce, ita Ummi ta zaɓa maka a matsayin mata, sannan da kake ta maganar cewa, ita bazawara ce, kai ɗin dakake magana saurayi ne kai? inace kaima bazawarinne tunda dai kayi aure."
Bakinsa ya turo gaba, a shagwaɓe ya narke fuska, cikin body language yace.
"Wallahi ni banason Ameena, yarinyar da idanunta abuɗe suke, ta fa riga da tasan Namiji, sannan kuma har yanzu ni matashin saurayi ne, tayaya ma zan yarda na auri Ameena."
Duban Adda Rahaman yayi tare da kamo hannunta, cikin yanayin daya saba musu alaman magana yace.
"Kin sanni tun ina ƙaramin yarona ma ko ta yaya bana amfani da tsohon abu, hatta kaya idan ya kasance gwanjo ne bana sawa, sannan idan yakasance wani ya taɓa amfani da abu, bana kuma amfani da abun, a iyaka tsawon rayuwata nafison komai sabo, koda wajen zama ne nafison sabo, banason wanda wani ya taɓa amfani dashi, harta mota ko wayar hannu, ban taɓa sayan second ba, komai na nafison yakasance sabo, ko lokacin da nake makaranta, ko yaushe ni nake zuwa first a acikin aji, bana taɓa yarda nazo second akomai na, to me yasa yanzu zan yarda na auri mace second hand? sauran wani, wanda wani ya cakalkala ya bari, ragowar wani fa Adda tunda nake gidannane kawai nataɓa sayan abu second hand kuma kin san shima saida na sabunta mana shi, bazan iya auren sauran waniba kinfa san inada kishi."
Kansa ya girgiza tare da cije laɓɓansa.
Baki buɗe Adda Rahama ke kallonsa, sosai take mamakin ƙarfin hali irin na Saifuddeen ɗin.
Shikuwa Ahmad da shaq dake gefe sai ƙyalƙyala dariya suke tayi, don sosai show ɗin na Saifuddeen keyi musu daɗi.
Ajiyar zuciya Adda Rahama ta sauƙe tare da cewa.
"Koma menene dai Ummi ta gama magana, kuma ta yanke hukunci, wanda mu dukan mu mun gamsu, ta kuma ce zata sanar wa Bappa Ali, don asamu ayi bikin cikin gajeren lokaci, kaman yanda Baba Malam ya buƙata, kai da za'ayi maka auren gata ma, miye na damun kanka, sadaki, kayan aure, komai da komai, duk fa Baban Zaleeha yace ya ɗauke ma, wannan kaɗai bai isa saka farinciki ba, auren huce haushi fa zaiyi maka."
Jan kujeransa baya yayi, inda ya kwaɓe fuska, nan ya dubi Ahmad yace dashi.
"Su tafi." kana ya ja hannun ishaq
Shidai Ahmad dariya kawai yake, har hakan yaso ƙular da Saifuddeen.
Haka dai suka dawo gida, bayan sun sauƙe ishaq ko amota Saifuddeen fuskar nan tasa aɗaure take tamau.
Suna isowa gida, kai tsaye part ɗin Ummi ya sake komawa.
Ganinsa yasa Ummi kafesa da ido, cikin sanya fuskar tausayi, yayiwa Ummi alaman cewa.
"Shi bayason Ameena, saboda bazawara ce, sannan kuma shi tsoronta ma ya keji, gata da kallon tsiya, sai kace mayya, gaba ɗaya idanunta abuɗe suke."

Dubansa Ummi tayi, tare dayin dariyar zuci batayi mamakin jin cewa Ameenan bazawara bace, saboda kafun isowarsu Adda Rahama ta kirata tasanar mata.
gyara tsayuwa tayi tare da cewa.
"Allah mai iko, yau kuma Saifuddeen  kai ne me tsoron mace? uhmm saboda bakason auren ta  shiyasa kake tsoronta ko?"

Sake shagwaɓe fuska yayi, duk yanda yaso Ummi ta fahimce sa, ƙiyawa tayi, daga ƙarshe ma juyawa tayi ta koma cikin ɗaki.
Ganin haka yasashi komawa part ɗinsa, ransa duk ba daɗi, wani haushin Ameenan nema duk ya cika masa zuciya, wannan rana haka dai yayi bacci zuciyarsa duk ba dadi.

Washegari.

Yana gamayin break fast ya shirya kansa, inda ya ɗauki Sule driver suka nufi gidan su Ishaq, don tun adaren jiya ya tsara cewa zai je yasamu Dirankaɗi da maganar, wato Baban Ishaq kenan."
Koda yaje Ishaq ne yayi masa jagora zuwa falon mahaifin nasa,  bayan sun gaisane Saifuddeen yayi masa bayanin duk wani abun daya kawosa, ta hanyar yi masa rubutu a laptop ɗinsa.
Koda Dirankaɗi ya karanta murmushi yayi tare da duban Saifuddeen ɗin.
Cikin son basa ƙarfin guiwa yace.
"Tayaya kake tunanin cewa, bazaka iya auran mata biyu ba? Kai jarumi ne Saifuddeen, saboda haka kada kasa wani damuwa aranka zaka iya."
Nan fa Saifuddeen ya tubure masa kan cewar lallai shi bazai iya ba, ganin haka yasa Dirankaɗi ɗaukar wayarsa, inda ya ƙira Bappa Ali, shi kuma Ishaq dariyan Saifuddeen ɗin kawai yake.
Gaba ɗaya abun da Saifuddeen ɗin ya faɗa, shi Dirankaɗi ya maidawa Bappa Ali, nan Bappa Ali yace da Dirankaɗi, ya faɗawa Saifuddeen ɗin, aure babu fashi, tunda Baba Malam da kansa ya yanke hukunci.
Koda Dirankaɗi ya faɗawa Saifuddeen ɗin, take yace.
"To Baba nifa banida kuɗin auren ma in da ba sadakanta iyayenta zasuyi ba".
Nan Dirankaɗi da Ishaq suka saka dariya, dubansa Dirankaɗi yayi tare da cewa.
"Ae dama ba kaine zaka sayi komai na auren ba, auren gata za'ayi maka ae."
Haka duk yanda Saifuddeen yaso ya kaucewa auren, Dirankaɗi da Bappa Ali sunƙi basa dama, dama shi Baba Malam baisan wainar da ake toyawa ba.
Dole haka Saifuddeen ya dawo gida, zuciyarsa cike da tunani kala-kala.

Haka akayi ta kai ruwa rana da Saifuddeen inda yaketa cemusu wai aifa Dr yace bazai iya zama da mata biyuba, Ya Adnan kuma yace a a ba wani Dr daya faɗi hakan.

Ɓangaren Baba Malam kuwa, tuni ya turawa Yaya Ahmad kuɗi, kan cewar ya bawa Aunty Lubna ta shiga cikin shoprite na Abuja, tayi musu sayayyan kayan lefe,  wanda za'aiwa Saifuddeen sabon aure dashi.
Yaya Ahmad  ne yace da Baba Malam ya amshi kuɗinsa,  shi zai haɗa lefen da kansa,  nan Baba Malam yace "a'a so yake komai na auren yayi da guminsa, da kuma haƙƙinsa, don ya ƙudurta aransa cewa, auren huce haushi da kuma gata zai yiwa Saifuddeen ɗin."

Can ɓangaren Zaleeha kuwa, rayuwarta mai sauƙi take gudanarwa acan garin na Numan, zuwa yanzu bata da wani abinci sai kayan fruits,  dangin su apples da kuma ayaba, goiba dabina sai su water meloon, acikin ƴan kwanki kaɗan ɗin, tuni abubuwa da yawa sun sau ya mata, zuwa yanzu abu biyu ne ke damunta, wato tana jin can ƙasan zuciyarta bata son gudowan da tayi tana kewan kowa hatta su Ummi tana kewansu, ji take kamar ta koma amman da zaran ta tuna ta koma ɗin sai taji kanta yana juyawa sai taji ta gigice lokaci ɗaya taji kamar an ɗaure mata zuciyarta.

Sai kuma nata soyayyar mutumin da har yanzu takasa sake sanyashi acikin idanunta, sosai soyayyarsa ke ƙara ninkuwa acikin zuciyarta, dashi take kwana kana dashi kuma take tashi, yayi mata tsaye acikin rai.

Yanzu ma zaune take akan katifarta, laptop ɗinta ne agabanta, inda ta saka earpiece akunnenta, wani series film take kallo acikin laptop ɗin nata, don tahakane take samun rage kewa, wayarta dake gefe ne ta soma ƙara alamar shigowar ƙira, sunan Balkeesu ne ke yawo akan screen ɗin wayar, saida ta kusa katsewa ta ɗauka tare da kara wayar akan kunnenta.
Daga can ɓangaren Balkeesu tace.
"Mutanen ƙauye."
Baki Zaleeha ta taɓe tare da faɗin.
"Ya akayi ne."
Balkeesu kuwa dariyar dake cinta arai ta danne tare da faɗin.
"Lafiya lau, ya kike kwana biyu ina ƙiran number ki baya tafiya."
Ajiyar zuciya Zaleeha ta sauƙe, cikin halin rashin kulawa tace.
"Maybe matsalan network ne."
Dariya Balkeesu tayi inda cikin zuciyarta tace.
"Ko kuma matsalan wuta ba." Afili kuwa cewa tayi.
"Dama Rabeel ne yace nayi miki magana, yana ta ƙiran wayarki amma bakya ɗauka, sannan yayi miki text duk babu reply, meyasa bazaki ɗauki wayarsa ba, ko kin manta cewar abokin aikin ki ne?."
Baki Zaleeha ta taɓe tare da cewa.
"Tayaya kike tunanin zan ɗaga ƙiransa, halan ya manta cewar ina da aure ne? igiyoyin auren wani

Please Login or Register in order to submit comment