Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Sadda kanta ƙasa tayi, saboda bazata iya musawa Ummi'n ba, kanta Ummi ta shafa, tare da cewa.
"Ki kwantar da hankalinki kinji, Insha Allah gobe Hammanku zai kaiki kuje ku bawa Baba Malam haƙuri, kuma Insha Allah Baba Malam zai yafe miki, ki daina kukan nan kinji!."
Ummi tafaɗi maganar cikin lallashi, jin cewa Hamma Saifuddeen ɗin ya yarda zai kaita yasa taji wani irin farinciki ya lulluɓe Zuciyarta, hakanne yasa ta faɗa jikin Ummi ta saki kuka. Rarrashinta Ummin ta somayi tare da sanya hannu tana shafa bayan Zaleeha'n, cikin kukan tace.
"Nagode sosai Ummi, haƙiƙa kin zame min uwa, nagode sosai..."
saurin rufe mata baki Ummi tayi, cikin kulawa tace.
"Kamar ƴa haka na ɗaukeki Zaleeha, saboda haka bama saikin min godiya ba, duk wani burina bai wuce farincikin ku, Allah Ubangiji ya muku al'barka, ungo wannan kayan ɗazun Hayatuddeen ya sayo miki su."
Ummi ta faɗi maganar tana me miƙawa Zaleehan ƙatuwar ledan dake hannunta.

Amsar ledan tayi cikin farinciki tace.
"Nagode sosai Ummi." har cikin ranta taji daɗin kayan, saboda itama kayan jikin nata sun isheta, yau kwanansu biyu kenan ajikinta, abunda tunda take aduniyarta bata taɓayi ba kenan, dama haka rayuwa take tana juyawa da abubuwa kala-kala, wai ita Zaleeha me yawan ado da kwalliya uwa uba ƙwalisa, itace ke sanye da kaya ɗaya ajikinta har tsawon kwanaki biyu, bacin da arana ɗaya saita sanja kaya kusan kala uku, amma yau gashi komai ya juya mata, damuwa ya mata yawa, wani lokacin har takan manta wasu abubuwan da suka shafeta.
Ummi kuwa tashi tayi inda da kanta ta shiga toilet ta haɗawa Zaleehan ruwan wanka me ɗumi, cikin kulawa Ummi tace da Zaleehan ta shiga tayi wanka, babu musu kuwa ta shiga rage kayan jikinta, ganin haka yasa Ummi fita daga cikin ɗakin, tare da jawo mata ƙofa.

Jikinta aɗan sanyaye haka tayi wankan, ba laifi kuwa taɗanji damuwarta ta ragu, nan cikin kayan da Ummin ta kawo mata ta zaɓo wata doguwar abaya gown me kyau ta sanya, sam damuwar da take ciki kuwa bai hana zallan kyawunta fitowa ba, gashi rigar ta amshi jikinta tayi mata ɗas, mayafin doguwar rigar ta yafa, sannan cikin yanayin sanyi ta fito zuwa falo.
Nan ta iske Raleeya da Hayatuddeen zaune, Raleeya karatun littafin hausa take, shikuwa Hayatuddeen game ya haɗa yakeyi.
Yana ganinta ya ɗan waro idanunsa, tare da cewa.
"Wow Adda Zaleehan mu kinyi kyau, yeah ashe dai niɗin gwanine wajen iya zaɓen kaya." Murmushi tayi masa, tare da zama anan kusa da Raleeya.
Duban Raleeya tayi cikin kulawa tace.
"Sister sannu da gida." cikin sakin fuska Raleeya tace.
"Yauwa sannu my kyakkyawar Auntyn mu, halan wannan kwalliyan duk na hamma ne" Raleeya ta ƙare maganar cikin yanayi naɗan tsokana, murmushi Zaleehan tayi wanda har saida fararen haƙwaranta suka bayyana, nan ta sadda kanta ƙasa tana tunanin. Uhum Hammanku kam ko kallo ban isheshiba ba ai. Hayatuddeen kuwa tashi yayi ya wuce ɗakinsa, mintuna kaɗan sai gashi ya dawo da leda ahannunsa, nan kan cinyarta ya ajiye mata, cikin kulawa yace. "Aunty roasted fish ne da cake, please kici kinji, nasan kinaso." murmushi tayi tare da cewa.
"Nagode auta." Dukansu murmushi sukayi sannan suka shiga ɗan taɓa hira, ita dai haryanzu akwai damuwa kwance aƙasan zuciyarta, hakanne ma yasa maganarta bai wuce.
"Eh, ko A'a ba".
Suna nan azaune Ummi ta fito ta samesu, zama tayi acikinsu, itane ma take ƙoƙarin jan Zaleehan da hira.

Saifuddeen ne ke tura wheelchair ɗinsa, yana son ƙarasawa part ɗin Ummi, dai-dai lokaci Ameena wanda dawowarta daga aiki kenan ta shigo cikin gidan, ganin Saifuddeen ɗin yasa ta ƙaraso da sauri tana sakar masa murmushi, shiɗinma murmushin ya sakar mata, tare da miƙa hannu ya karɓi Adeel dake rungume akafaɗanta. Ɗan ranƙwafowa tayi tayi mishi kiss a forehead ɗinsa, cikin kulawa tace. "Nayi kewarka Mijina." murmushinsa me kyau yayi mata, tare dayi mata alaman cewa shima haka, nan ta riƙe saman wheelchair ɗin nasa, tana turasa shikuwa yana riƙe da Adeel haka suka nufi part ɗin Ummi.
Ahankali suka tura ƙofar falon suka shiga bakin Ameena ɗauke da sallama, hakanne yasa gaba ɗayansu suka ɗago kai suka kallesu, Ummi ne ta fara amsa sallaman, kafun suma suka amsa, kallo ɗaya Zaleeha tayi musu ta duƙar da kanta ƙasa, cikin kulawa Ummi tace. "Mutanen asibiti kun dawo."
Murmushi Ameena tayi, wanda ganin Zaleeha cikin shiga me kyau yasa duk taji zuciyarta ba daɗi, ɗan durƙusawa tayi tare da cewa.
"Ummi barka da gida." Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
"Yauwa Ameena ya wajen aikin naki?" tana murmushi ta amsa da lafiya lau, Raleeya da Hayatuddeen ne sukayi mata sannu da dawowa, baki awashe haka ta amsa musu, duk dama dai aranta sam bataji dadin ganin Zaleeha ba, gashi kuma Zaleehan tayi kyau sosai, Ɗago kai Zaleeha tayi tare da ɗan kallon Ameena'n, cikin sanyin murya tace.
"Ummu Adeel barka da dawowa."
Cakwai haka Ameena taji muryan Zaleehan acikin kunnuwanta, take kuwa taji kaman an watsa mata ruwan zafi ajikinta, wani irin haushin Zaleehan ne ya cika mata zuciya, amma ganin idon su Ummi yasa ta ɗanyi yaƙe tare da cewa.
"Yauwa Sannu." Ɗan ɗago kai Zaleeha tayi ta saci kallon Adeel dake kan cinyar Saifuddeen, Gani tayi Adeel ɗin na kallonta, hakan yasa ta sakar masa murmushi wanda har saida dimples ɗinta suka lotsa, shima yaron murmushi yake ta mata yana wangale mata haƙora tare da mutsu-mutsu har yana zamowa tare da miƙo mata hannu alamun ta ɗaya shi.
Cikin dariya Hayatuddeen yace.
"Aunty Zaleeha ke yakeyiwa hakafa".
murmushi Ummi tayi tare da cewa.
"Ae wannan ɗan naku saiku yaron ba dai ƙirniya ba abinda ya iya".
Murmushi sukayi baki ɗaya su.
Ita kuwa tashi tayi daga zaunen da take, gaba ɗaya ta gama mantawa cewar ma yaron akan cinyar Saifuddeen ɗin yaƙe, ƙarasawa tayi tare da ɗan ranƙwafawa tasa hannu zata ɗauki Adeel ɗin, daddaɗan ƙamshin turarensa ne ya daki hancinta, cikin tsautsayi kuwa hannunta ya gogi nasa, wani irin shock sukaji su duka biyun, ahankali ta ɗauki Adeel ɗin, sannan ta ɗagashi sama tana sakar masa murmushi,
baki ya wangale mata harda tsalle shi, Allah ya sani tana son Adeel har cikin ranta kuma shima yaro yana sonta.
Baki buɗe Ameena ke kallonsu, kishi kuwa haka takeji kaman zai fasa ƙirjinta, ƙwarai tazo iya wuya, dan kasantuwar Zaleeha akusa da Saifuddeen ɗin baƙaramin dacewarsu ta gani ba.
Ummi kuwa jin wayarta dake cikin ɗaki na ƙara yasa tatashi ta bar musu falon, Raleeya ma miƙewa tayi ta haura sama.
Nan falon ya rage daga Hayatuddeen, Zaleeha, sai su Saifuddeen ɗin, Zaleeha kuwa rungume Adeel ɗin tayi tana yi masa wasa, Saifuddeen kuwa ahankali yake ɗan satan kallon Zaleeha'n, saboda tayi masa kyau sosai, duk da kasancewar ma ya lura cewa idanunta aɗan kumbure suke kuma gaba ɗaya yanayin rayuwarta ta sauya ta zama mai sanyi, hakan yasa shi jin wani abu na tausayi acikin ransa. Ameena kuwa ganin cewa Saifuddeen ɗin na ɗan satan kallon Zaleehan ƙasa-ƙasa ne, yasa taji gaba ɗaya ranta ya ɓaci, wani irin matsanancin kishi ne ya taso mata, amma saita dake, cikin kirsa ta tashi ta dawo kusa da Saifuddeen ɗin, ɗan durƙusawa tayi tare da tallafo haɓarsa cikin son nunawa Zaleeha matsayinta tace. "Mijina Mekakeso na kawo maka kasha?" Shikuwa sanin cewa Zaleeha na falon, yasashi jawo hannun Ameenan kusa dashi, kissing ɗinta yayi, tare da nunata da hannunsa, alaman ita yake so, wani irin daɗi haɗi da farinciki ne suka cika zuciyar Ameena, wani irin fari tayi da idanunta, da ɗan ƙarfi yanda ta tabbatar cewa Zaleehan zataji tace.
"Indai nice kasameni." Saman Wheelchair ɗinsa ta kama, tare da juya akalan keken suka fice daga cikin falon, sai sakin wani shu'umin murmushi takeyi.

Duk da cewa duk abun da sukeyi tana jinsu, amma gaba ɗaya hankalinta ba akansu yake ba, sam kuma bataji wani abu na ɓacin rai dangane da hakan ba, gaba ɗaya ma ita hankalinta naga wajen yiwa Adeel wasa,
sai dai tana jin zuciyarta na riƙe da abinda sukayi.
Hayatuddeen kuwa sosai hakan da Ameenan tayi yasa yaji ba daɗi, saboda ya fahimci cewa, Ameenan so take ta ƙuntatawa Zaleeha, amma ganin cewa Zaleehan bata damu ba, yasashi girgiza kansa kawai ya ci gaba da game ɗinsa.

Ameena kuwa suna isa part ɗinsu, cikin mazari tasoma ƙoƙarin rage musu kayan jikinsu, jin ranta take fari ƙal, saboda hakane ma zata gwadawa Saifuddeen ɗin soyayya kala-kala, tayanda sai tasa ya manta da wata Zaleeha.

Afalon Ummi kuwa saida aka ƙira sallan Magriba, kafun Ummi ta karɓi Adeel,
inda tace da Zaleeha taje tayi sallah.
Koda ta idar da sallan kuwa bata tashi akan sallayan ba sai da aka idar da sallan isha, daganan bata ƙara leƙa waje ba, kifi da kuma cake ɗin da Hayatuddeen ya bata shi taɗan ci, sannan ta kwanta, take kuwa bacci ya ɗauketa.

Saifuddden da Ameena kuwa, yau zagewa tayi ta nuna masa soyayya kala kala, babu laifi kuma shima ya biye mata, hakanne kuma yasa kasantuwarsu tayi mata armashi, dan bakaɗan ba takejin daɗin Saifuddeen. Haka ko da suka kwanta bacci tawani rungemesa, ranta kuwa fari ƙal, bata da wani damuwa, saboda kasantuwarsu na yau yasa tanajin kanta kamar wata sarauniya.

Washegari

Yau ya kama Lahadi, inda gobe Monday Amina zata fara zuwa aikin rana.
kuma yaune ake sadakan Uku na rasuwar Adda Maryam, Inda sukejin mutuwar ta dawo musu sabuwa, sosai suka sha kuka har suka godewa Allah, yayinda mafi yawancin mutanen da suka zo musu ta'aziyya duk kowa ya kama gabansa. Haka gidan ya rage daga, su Yaya Ahmad sai kuma Hajja Inna da Goggo maryama, sai kuma su Ziyada da kuma wasu mata guda biyu, wanda suke ƙannen.
Yaya Ameenu ne, wato Zainab da kuma Ubaida, sai wanda suma dukansu matan aure ne, sai Hajja Ma'u mahaifiyarta Ya Ameenu kenan rasuwar ne ya sasu zama anan gidan na Baba Malam, wanda suɗin ma yau zasu tafi, zuwa yanzu babu wani baƙo ko ɗaya da ya rage acikin gidan, iya su yasu ne, haka suka sha kukansu suka ƙoshi, daga ƙarshe sukayiwa Adda Maryam ɗin addu'a da fatan Allah ya raya ɗanta Ayman.

Can gidan su Saifuddeen kuwa, Yau Zaleeha da wuri ta tashi, tana idar da sallah kuwa tawuce ɗakin Ummi ta gaisheta, anan ta iske Saifuddeen ɗin, koda ta gaishesa, saida ya ɗauki kusan second 30 kafun ya jinjina mata kai alaman ya amsa, haka tatashi ta koma ɗakinta jikinta duk asanyaye, shikuwa falon Ummi ya koma ya zauna.
Wanka tayi sannan tasaka ɗaya daga cikin riga da sket ɗin da aka sayo mata, ganin kayan ya kamata yasa ta ɗaura hijab akai, murɗa handle ɗin ƙofar tayi tafita, dan tanason fara taya Raleeya aikace aikacen gidan. Tana fitowa falon kuwa anan zaune ta iskesa, sadda kanta ƙasa tayi sannan ta wuce kitchine, Sarai ya ganta amma saiyayi kaman bai ganta ba, saida ta wuce yabi bayanta da kallo, harda wani ɗan lumshe idanunsa.
Tana shiga kitchine ɗin kuwa tasamu Raleeya na firan dankali, amsa tayi ta soma tayata suna ɗan taɓa hiransu.

Ameena ce tashigo cikin falon, ɗauke da Adeel akan kafaɗunta, ganin Saifuddeen zaune afalon Ummin yasa ta sakin murmushi, shima murmushin ya sakar mata, har acikin ransa yaji daɗin ganinta yanzun, dan da itane zaina buga Game ɗinsa, wanda ya tabbata wata rana kuwa zaiyi winning, ƙarasowa cikin falon tayi, tare da ajiye masa Adeel akan cinyarsa, nan ta wuce ɗakin Ummi, koda taje ɗakin na Ummi kuwa cikin ladabi ta gaisheta, fuska asake Ummi ta amsa mata, tare da tambayanta Adeel, murmushi tayi tare da cewa.
"Ummi yana falo suna tare da Abban shi."
Itama Ummin murmushi tayi tare da jinjina kanta, dan tana lazumi ne, batason magana. Miƙewa Ameena tayi ta fice daga ɗakin, Tana fitowa falo Saifuddeen ya miƙo mata hannunsa, cikin jin daɗi ta ɗauke Adeel dake kan cinyarsa tayi, ta ɗaurasa akan kujera, raɓawa kan cinyar Saifuddeen ɗin ta ɗanyi dan taga falon ba kowa kuma tasan Ummi na lazumi ba yanzu zata fitoba, ahankali ya sanya hannuwansa, ya saƙalo waist ɗinta, harshensa yasa inda ya ɗan laso lips ɗinta, idanunta ta ƙura masa bata ko ƙiftawa, ganin haka yasashi ɗan ɗaga mata gira, murmushi tayi tare da sake shigewa jikinsa, fuskarta ya ɗago ya haɗe bakinsu waje ɗaya, jin haka yasa ta kamo laɓɓansa tana tsotsa sosai.
Gaba ɗaya sun shagala, musamman ma Ameena, wanda idan tana shan laɓɓansa takejin kamar tana shan sweeet.
Adeel kuwa sai wutsil wutsil yake, yanason jawo flowern dake gefen kujera, hakanne yasa har yazo bakin kujeran batare da sun ankara ba, Zaleeha ce ta fito daga cikin kitchine ɗin hannunta riƙe da flask, da sauri taja baya sakamakon abun da idanunta suka gane mata, ƙoƙarin komawa cikin kitchine ɗin take, idanunta suka sauƙa akan Adeel wanda saura ƙiris ya faɗo daga kan kujeran, cikin sauri ta ajiye flask ɗin hannunta, da gudu ta ƙarasa inda yake, dai-dai lokacin kuma har ya faɗo daga kan kujeran, saidai kuma bata bari yakai ƙasa ba, tayi saurin zubewa akan guiwowinta ta taro sa, yafaɗa jikinta, wani irin firgitaccen ihu ya saki har kamar zai shiɗe dan yayi masifar tsorita ruggumeshi tayi a jikinta da kyau, hakan yasa ya ƙanƙameta tare da kuma cilla ihu, wanda hakanne ya fargar dasu Saifuddeen, azabure suka juyo suna kallonsu, ɗagosa Zaleeha tayi tare da mannasa aƙirjinta, tana jijjigasa, Idanu Saifuddeen ya zuba mata, ita kuwa Ameena hakanan taji wani iri aranta, kukan Adeel ɗinne yafito da Ummi, daga ɗaki, harta Raleeya ma saida tafito, cikin kulawa da tsananin son yaron Ummi tace. "Lafiya kuwa me ya sameshi."
ta ƙarasa maganar tana shafa kanshi tare da kallon Zaleeha
Cikin damuwa murya a tausashe Zaleeha kamar zatayi kuka tace.
"Faɗowa ya kusayi daga kan ƙujera, inaga shiyasa ya tsorata, gashi yana ta kuka."
ta faɗi maganar tana me ci gaba da jijjigasa, saboda sam batason kukan Adeel ɗin, tanajin yaron sosai aranta, ganin baiyi shiru bane yasa ta sanya bakinta akunnenshi tana ɗan hurawa masa isaka tare da ɗan bubbuga bayanshi kana tana jijjigashi, wanda hakanne ya bawa jikinta damar rausaya wa, take kuwa yayi shiru, tare dayin lub ajikinta, jin yayi shiru yasa ta wuce ɗakinta dashi.
Har zuwa lokacin kuwa idanun Saifuddeen akanta suke, Ameena kuwa gaba ɗaya ma takasa tantance meke damunta, tausayin ɗanta ne ko baƙin ciki da kishi takasa tantance wanne ne ɗaya, ganin lokaci na ƙurewa yasa ta juya ta fice daga falon dan batason tayi lattin zuwa wajen aiki dan yau ɗin mitin zasuyi da manyan likitoci.
Zaleeha kuwa tana shiga ɗaki, ruwa me ɗan ɗumi ta haɗa, tayiwa Adeel ɗin wanka, Hayatuddeen ne ya shigo cikin ɗakin, hakan yasa tace dashi yaje ya karɓo mata kayan Adeel tasa mai.
Part ɗin Ameenan yaje, ya amso kayan sannan ya kawo mata, tsab ta shirya Adeel ɗin cikin kayansa me kyau, sosai kuwa yaron yayi kyau, haka ta rungumesa aƙirjinta tana ta yi masa wasa.
Ganin alamun bacci yakeji yasa ta ɗauki towel ta goyeshi ai tuni yayi bacci.
Saida Ameena ta zo tafiya aiki sannan ta amshe sa, still agaban Zaleehan Saifuddeen ya sake jawo Ameenan yayi mata kiss abayan hannunta kafun ta tafi, Zaleeha kam idan ta kallesu sau ɗaya bata yarda ta sake kallonsu, zuwa yanzu ma mamaki suke bata dan ta lura basa gajiya da tsotse, saidai kuma idan ta tuna cewar rashin damuwa ne ke sasu hakan, sai taji matsanancin tausayin kanta.
Tace su kam sunji daɗi da basu da damuwar duniya.
Koda tayi break ɗaki ta komawa tayi ta kwanta, cikin zuciyarta kuwa fargaba ne, me tarin yawa, saboda batasan ta yaya zata fuskanci Baba Malam ba.

Saifuddeen kuwa sanin cewa yau ne zaikai Zaleehan ta bawa Baba Malam haƙuri, yasa shi barin gidan ma gaba ɗaya, bashi ya dawo ba kuwa sai wajajen sallan azahar. Kaitsaye ɓangaren sa ya wuce, wanka yayi sannan ya shirya kansa cikin wata ɗanyar getzner me masifar kyau da tsada, kasancewar getzner ɗin na sa nada kalan coffee, shi yasa ya matuƙar amsar farar fatar jikinsa, yayinda akayiwa getzner ɗin dinkin half jumper da kuma wandon pencil, wata murzazziyar hula mai kalan light coffee ya ɗaura akansa, hatta takalmin dake ƙafansa me kalan dark coffee ya sanya, yayi kyau matuƙa ga kuma apple touch watch ɗinsa dake ta faman ɗauke ido, tabbas Saifuddeen yayi kyau ƙwarai, dan bazaka kallesa sau ɗaya ka ɗauke idanunka ba, haɗaɗɗiyar sajen dake kwance akan fuskarsa kuwa ta kwanta tayi lub lub, jajayen laɓɓansa kuwa sai sheƙi suke, ga wanda baisansa ba zaice wani abun ya shafa musu, amma ko ɗaya haka yake, sirrin kyau ajininsa yake. Wayoyinsa ya zura acikin aljihun rigarsa, sannan kai tsaye ya danna madannin wheelchair ɗinsa ya fita daga cikin ɗakin, sai baza ƙamshi yake.
Anan compound ɗin gidan kuwa, sanin cewa zasu fita yasa Sule driver tuni ya gama tsabtace motar da zasu fita da ita ɗin, wata haɗaɗɗiyar mercedes benz ce me kyau, sabuwa dal sai sheƙi take tana ɗauke ido, fitowarsa compound ɗin gidan ne, ya hango Sule driver, hakanne ya sashi ƙarasawa wajen Sule driver'n, cikin kulawa Sule driver'n, yayi masa barka da fitowa, da kai ya amsa masa kamar koda yaushe. Buɗe murfin motar yayi, nan ɓangaren gidan baya ya shiga, dan dama shi baicika zama agaba ba, akomansa yafison sirri, musamman ma yanzu da yake mazaunin jami'in sirri, yana shiga ya jawo murfin motar ya rufe, wayarsa ya laluɓo daga cikin aljihunsa, cikin text message ya shiga, ataƙaice ya rubuta cewa. _"Ummi kice mata tayi sauri, dan tana ɓatamin lokaci."_
yana gama rubutun yayi sending, tare da maida wayan ya ajiye, laptop ɗinsa ya ɗauko yana dannawa.
Ummin kuwa dama tuntuni tasa Zaleehan ta shirya, tsab cikin ɗaya daga cikin sabin rigunan da tasa aka sayo mata, duk da cewa akwai yanayin damuwa mai yawa akan fuskarta, amma hakan baihana kayan yi mata kyau ba, saboda doguwar rigace irin abaya ɗinnan ta larabawa me kyau, yayinda ta yane kanta da ɗan kwalin kayan, wanda ya sauƙo har zuwa ƙirjinta.
Tunda ta gama shiryawan take zaune abakin gado, gaba ɗaya ta rasa mekeyi mata daɗi, tsoro da fargaba ne suka cika zuciyarta, ga kuma yawan faɗuwar gaba da takeji, ƙirjinta ne ke wani irin duka, gaba ɗaya atsorace take, koda tayi ƙoƙarin bawa kanta ƙarfin guiwa kuwa hakan baya yiwuwa, saboda fargaban daya cika zuciyarta.
"Me zata tarar agidan Baba Malam? wata ƙila ma yaƙi yafe mata ya kuma sake koranta." Wannan abun shine abun daya tsaya mata arai, duk yanda taso jin sauƙi azuciyarta abun yaci tura, hakanne yasa kawai ta fashe da kuka, dai-dai lokacin Ummi ta turo ƙofar ɗakin ta shigo, ganin Zaleehan na kuka yasa ta ɗan dafe kanta, sam batason yawan kukan na Zaleeha, jin an shigo ɗakin ne yasata ɗago kanta, ganin Ummi yasa cikin hanzari ta tashi tare da ƙarasa gareta, cikin muryarta dake rawa tace.
"Wallahi Ummi tsoro nakeji , idan mukaje Baba Malam ya koreni sannan yaƙi yafemin ya zanyi? shikenan nikam rayuwata tana cikin garari." taƙare maganar hawaye na silalowa daga cikin idanunta, Ɗan bubbuga bayanta Ummi tayi, cikin son kwantar mata da hankali tace. "Kada ki faɗi haka Zaleeha, share hawayenki, insha Allah Baba Malam zai yafe miki, nasan nanda ƴan wasu awanni zaki kasance cikin farincikin yafiyar Baba Malam, yanzu taho muje Hammanku nacan mota yana jiranki."
Idanunta ta ɗan lumshe, ahankali taɗan gƴaɗa kanta kamar wata ƙaramar yarinya, haka hawaye ke tsiyaya daga cikin cikin idanunta, hannunta Ummi ta kama suka fice daga cikin ɗakin, anan falo suka samu Raleeya tsaye. Ummi na riƙe da hannunta, yayinda Raleeya ka biye dasu abaya, haka suka fito zuwa compound ɗin gidan, har jikin motar tasa suka ƙarasa, still hawaye Zaleeha take, Ummi kuwa na riƙe da hannunta, murfin motar Ummi ta buɗe tare da sanya Zaleehan aciki, ganin ankawo masa ita kusa dashi ne, ya sashi ɗago kansa ya dubi Ummi, amatuƙar shagwaɓe ya ɓata fuska, cikin body language ɗinsa yace wa Ummi da ke kallonsa,
"Ni Ummi me yasa zaki kawomin ita kusa dani, baganan gidan gaba ba, dan Allah Ummi kisata agaba, ni banason ta zauna akusa dani." Daƙuwa Ummi tayi masa, tare da kama haɓanta, sosai take mamakinsa itakam, musamman ma yanzu da ya ari halin da ba nasa ba ya yafa. Sake ƙara shagwaɓe fuska yayi, cikin ransa yake ta ƙunƙuni, wanda ko bakin zuciyarsa bai je ba, dan duk abun da yakeyi pretending ne kawai, sam baisa azuciyar sa ba.
Allah ya kiyaye Ummi tayi musu sannan Sule driver yaja motar suka fita daga gidan. Saida su Ummi suka ga, fitansu kafun suke komawa cikin gida.

Koda tafiyan nasu tayi nisa, ƙanƙame jikinta waje ɗaya tayi, saboda sanyin AC'n dake tashi acikin motar yaso ya yiwa jikinta yawa, gaba ɗaya bata wani cikin nutsuwarta, domin suna fita daga cikin gidan na Ummi taji gaba ɗaya zuciyarta ya karye, haka hawaye keta fita daga cikin idanunta, yana sauƙa akan fuskarta, daga gefe guda kuwa daddaɗan ƙamshin turarensa ne ya gauraye numfashinta, haka take ta sakin sheshsheƙan

Please Login or Register in order to submit comment