Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ɗaya taji wani irin shock ya shiga jikinta gaba ɗaya wanda hakan yasa jikinta karkarwa idanunta suka firgita woje jin sauƙar muryar da bazata manceba tsawon shekaru 20 kenan da ta daina jin amo da kuma sauti wannan muryar, tun tanasa rai da jinta har ta cire,
mafarki takeyi ne ko kuwa da gaske ne?so take ta tantance hakan yasa ta dafe kanta dake juyawa da kuma ƙirjinta dake barazanan fitowa waje, hannu tasa ta soma mutsstsuke idanunta.
Ahmad ne wanda shigowarsa cikin ɗakin kenan yajie sautin muryar Saifuddeen ɗin ya daki dodon kunnenshi muryar da bazai taɓa mancewa da itaba komin yawan shekarun da aka kwashe bai jitaba kuwa.
Ji yayi gaba ɗaya jikinsa ya soma rawa tsikar jikinsa na mimmiƙewa idanunsa ne suka ciko da wani irin ƙwalla.
Saifuddeen kuwa ganin irin kallon da Ummi keyi mashine mai ɗauke da tantama yasashi miƙo hannunshi jiki na rawa ya kamo hannunta, cikin tsananin rawan jiki da kaɗuwa Ummi tace.
"Saifuddeen!!!". Ido ya rumtse da ɗan ƙarfi yace.
"Na'am Ummi!". wani irin tsuma da karkarwa jikinsu keyi gaba ɗayansu,
Hayatuddeen kuwa samun kansa yayi cikin wani irin masifeffen tashin hankali da kuma firgici abune da wanda shi dai zaice bai taɓa zaton ko tsammanin ba asalima kuma shi zai iya cewa bai san kalan muryar Hammanshin ba tunda yana ɗan ƙarami Hamman nashi ya kuramce, bai taɓa jin yayi maganaba sai yau,
cikin wani irin razana ya fasa wani ihu na tsananin kaɗuwa da farin ciki take kuma ya tafi luuu ya faɗi a sume,
da sauri Ahmad ya tareshi ya kontar dashi bisa carpet, dan sam hankali Ummi baya kanshi, shi kuwa Saifuddeen zafin ciwo yasa bai kula da suman da Hayatuddeen yayiba shima kanshi Ahmad hankalinshi na kan Saifuddeen shiyasa kawai sai ya kontar da Autan Ummi kamar maiyin bacci.
A kiɗine Ummi ta matsoshi tare da cewa.
"Babana kana jina kana mgna, Ya Allah na in mafarki nakeyi ma ka tabbatar min dashi".
Cikin dauriyar ciwon da yake ji ɗin yace.
"Ummy a zahiri ne, ba mafarki kikeyi ba, ƙudurar ubangiji ce, dare ɗaya ya ɗauke jina da mgnata, kana bayan tsawon shekaru ashirin ya dawo min jina da mgnata a dare ɗaya".
Cikin wani irin kaɗuwa Ummi tace.
"Yaushe ka fara magana yaushe ka fara jin mgna? Saifuddeen".
Wani irin rumtse idonshi yayi dan jin kanshi kamar zai rabe gida biyar ga wani irin sarawa da ƙugunshi keyi a fizge yace.
"Ummi daren jiya na fara jin Zaleeha tana kiran sunana, tana ihu, Ummi sunana da kuka da ihun Zaleeha na fara ji tamkar zai fasa min dodon kunne Ummy kuka Zaleeha tai tamin".
Sai ya kuma saki hannun Ummi ya riƙe kanshi da hannu biyu da ƙarfi ya matse kan nashi murya na rawa yace.
"Wayyo! Allah na wayyo bayana Ummy bayana zai ɓalle inaji kamar ana haɗa jijiyoyin ana ɗinkewa Ummy bayana, kaina, wuyana, ƙuguna, cinyana, ƙafata,
Cikin tsananin kiɗima Ahmad ya matso
Saifuddeen ɗin tare da kiranshi.
"Saifuddeen!." Ɗago idanunsa da suka kaɗa sukai jajazir yayi, murya na rawa yace "Na'am Ahmad." Idanu Ahmd ya zazzaro cike da shock, sai kawai ya fashe da wani irin kuka, tare da jawo Saifuddeen ɗin jikinsa ya rungumesa sosai. Dai-dai lokacin kuwa Raleeya ta shigo cikin ɗakin aguje, ganinsu ahaka yasa ta yi turus tana me ƙare musu kallo. Ganin yanda Ummi da Ahmad ke kuka yasa taji gaba ɗaya ƙafafunta sun fara rawa, ƙoƙarin buɗe baki take dan tayi magana, ta hango Hayatuddeen a yashe aƙasa baya motsi, kansa tayi agigice ta durƙusa tana jijjigasa, hankalinta amatuƙar tashe tace. "Hayatuddeen ka tashi dan Allah, me yake faruwa, Yaya Ahmad me kukayi masa? meyasa baya motsi? wayyo dan Allah Ummi kizo kiga Hayatuddeen baya motsi.."
tafaɗi maganan tana me jijjiga Hayatuddeen ɗin dan gaba ɗaya ta ruɗe. Saifuddeen ne ya ɗan janye jikinsa daga na Ahmad ɗin dan ji yake kamar gatari ake kima mishi a bayanshi komawa yayi ya konta tare da rumtse idanunsa, dan ciwo yakeji sosai acikin jikinsa.
Ummi ne ta tashi daga durƙuson da take inda ta ƙarasa kan Hayatuddeen zuwa lokacin kuwa tuni Raleeya ta ɗauko goran ruwa ta yayyafa masa, wata iriyar ƙatuwar ajiyar zuciya ya sauƙe.
Ganin haka yasa Raleeya itama sakin ajiyar zuciya. Ummi kuwa akan gadon ta zauna, har yanzu hawayene ke tsiyaya daga cikin idanunta, Hannun Saifuddeen ta kamo, cikin muryarta dake rawa tace. "Saifuddeen Babana hankali ya tashi gani nake kamar mafarki nakeyi, meya sameku ina Zaleeha."
tafaɗi maganan tana me ɗan shafa gefen fuskarsa.
Idanunsa da suke lumshe ya buɗe tare da zubawa Ummin nasa su, sake riƙe hannunsa dake cikin nata yayi, laɓɓansa yaɗan motsa ahankali yace.
"Ummi baya na zai golɓole. Allah ya bani lafiya ayanzu na zama akaman kowani meji da faɗa amman kuma baya zai tsinke."
sabon kukane da fargaba ya sake ƙwacewa Ummi, cikin zuciyarta take ambaton sunan Allah tare da neman agajin Allah. Raleeya kuwa haka ta zama kaman gunkin da aka sassaƙa, ganin abun take kaman awata duniya ta daban, jikinta ne ya ɗauki ɓari, saboda yanda taga Hamman nata na magana, abune wanda bazatace ga lokacin da ta taɓa gani yayi ba, ko adacan baya lokacin daya kurumce bata da wani isashshen wayo.
Hannu tasa ta dafa kanta dake bugawa, muryarta na rawa tace. "Hamma Saifuddeen." Jin muryan Raleeya acikin kunnensa yasashi daurewa ya kalleta, tare da sakar mata murmushi, cikin muryarsa me fidda azabar da yakeji yace. "Na'am Raleeya."
Wani irin kukane yazo mata, take ta tafi da gudu ta faɗa jikinsa, lokaci guda kuwa ta saki kuka me sauti, tare da ƙanƙamesa, cikin kukan tace.
"Alhamdulillahil lazi bini'imatihi tatimussalihat, Alhamdulillah Ya Allah, Hamma Saifuddeen kaine, kake magana, Alhamdulillah Allah." Sai kawai ta sake sakin sabon kuka.
Shi kuwa Saifuddeen ji yayi kamar anja bayanshi da ƙarfi hakanne ya sashi zubda wasu hawayen azaba.
Hayatuddeen wanda farfaɗowansa kenan, janyo jikinsa yayi, inda ya raɓa jikin Hamman nasa, ya saki wani irin kuka me taɓa zuciya, wace irin ranace yau tazo me cike da al'khairi agaresu?. Saida sukayi kuka sosai kafun suka ɗan janye jikinsu daga nashi, dan jin yanda jikin nasa ya ɗauki zafi zau kaman wuta, gashi sai rawan sanyi yake, haka Raleeya ta fita daga ɗakin da gudu kaman wanda aka tsikara.
Ummi ne ta matso kusa dashi, tare da kamo hannunsa ta zuba masa ido, tanajin wani irin farinciki da fargaba na neman fasa mata zuciya. Shikuwa zuwa lokacin shikaɗai yasan me yake ji ajikinsa, ciwo sosai yakeji.
Hannun Ummin ya kuma damƙewa, cikin muryarsa dake fitar da rauninsa yace.
"Ummi ciwo nakeji acikin jikina, bayana inajinsa kaman zai ɓalle, kaina ciwo yake Ummi, zazzaɓi nakeji, ko zama bazan iyaba Ummi bayana zai ɓalle." Hawayen da suka cika idanunta ne suka samu daman gangarowa, hankalinta amatuƙar tashe tace.
"Saifuddeen me yasamu bayan naka? ,mekakeji ajikin ka? kafaɗamun ko wani irin ciwo kakeji sai na ƙira Dr Adnan yazo ya dubaka."
Duka Ummi tayi masa tambayar tana me shafa gashin kansa. Awahalce yaja numfashi, murya asanyaye yace.
"Ummy bayana." Hannu Ummi tasa ta rufe fuskarta tana sakin sheshsheƙan kuka, tare da ambaton Allah acikin ranta, tanayi masa godiya tare da rokowa ɗanta lfyar bayanshi da yaketa ce mata zai tsinke, lallai Allah ma buwayi ne gagara misali, meyin yadda yaso alokacin dayaso, ya bada alokacin da yaso, ya kuma hana alokacin da yaso, yakanyin duk yanda yaso, babu wani meyi masa shamaki, shine sarkin kowa da komai.
Ahmad ne ya kamo hannun Saifuddeen ɗin ya riƙe, jin haka yasa Saifuddeen ɗin, awahalce yace.
"Ahmad Bayana, inajin zogi da zafi sosai." Hawaye Ahmad ya share tare da cewa.
"Sannu kaji Saifuddeen, zaka daina jin hakan insha Allah, ko wani abu ya samu bayanne?." Kai ya gyaɗa alaman "Eh." dan zuwa yanzu maganan ma daƙyar yake saboda yanda yakeji. Ummi ne cikin matsanancin tausayawa. tace.
"Saifuddeen ina Zaleeha?." Dogon numfashi yaja asanyaye yace. "Zaleeha bata da lapiya Ummi, tun jiya da daddare ta suma, dan Allah Ummi kije ki taimaka mata, kada wani abu ya same ta." Idanu Ummi ta ɗan zaro cikin tashin hankali tace. "Innalillahi wa inna ilaihirraju'un, ta suma kuma?."
Kansa kawai ya iya jinjina mata alaman "Eh." cikin sauri Ummi tatashi daniyar zuwa ɗakin Zaleehan.
Hannun Ummin ya kamo hakan yasa ta juyo tare da zuba masa ido. Kansa yaɗan girgiza akasalance yace.
"Dan Allah Ummi karku faɗawa Zaleeha cewar nafara magana, banaso tasan cewar kunnuwana sun dawo, dan Allah kumin al'kawarin cewar bazaku faɗa mata ba." Ɗan jim Ummi tayi, wani tunani dayazo ranta ne yasa ta jinjina kai, tare da cewa.
"Insha Allah bazamu faɗa ba harsai ka nemi hakan."
Sakinta yayi, ta fice daga cikin ɗakin da sauri, Hayatuddeen ne ya matso kusa dashi,Yanzu Hammansa najin duk wani motsi, kuma yana faɗin duk abun dake rai da zuciyarsa, me yafi hakan daɗi da farinciki awajensu? farinciki, lafiya, da kuma jin daɗin Saifuddeen shine nasu baki ɗaya.
Raleeya kuwa tana fita daga ɗakin, da gudu ta haura sama, wayarta ta ɗauka hannunta har rawa yake wajen dannawa numbern Adda Rahama ƙira. Bugu biyu kuwa Adda Rahama ta ɗauka, kuka me haɗe da Dariya Raleeyan tasa, jin haka yasa Adda Rahama dake zaune miƙewa tsaye, hankalinta ne yasoma tashi jin kukan Raleeya'n, cikin ɗan tashin hankali tace. "Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un, lafiya kuwa Raleeya, meyake faruwa?."
Ɗan tsaida kukan Raleeya tayi, murya na rawa tace.
"Adda Rahama, ranan yau takasance mana rana mafi al'barka agaremu wanda bazamu taɓa mantawa da ita ba, Adda Rahama kunnuwan Hamma Saifuddeen sun buɗu, yanzu yanajin duk abun da mutum zai faɗa, haka kuma idan kaƙira sunansa zai amsa, Adda Rahama Hamma Saifuddeen ya warke daga cutan kurumta, yanzu yazama mutum me lafiya ji da magana." Wani irin shock Adda Rahama taji ajikinta, sosai maganan ya daki zuciyarta, saboda abune wanda bata taɓa zato ko tsammani ba, tasan tabbas Raleeya bazata taɓa yi mata wasa ƙo ƙarya akan irin wannan babban al'amarin ba. Samun kanta tayi itama da fashewa da kuka, kasa cewa komai tayi, haka tayi wurgi da wayan nata, da gudu ta nufi falo inda Dr Adnan ke zaune. Tana isa falon kuwa ta faɗa jikinsa, tare da sakin wani sabon kuka. Hankalin Dr.Adnan ne ya tashi, ɗagota yayi cikin kulawa yace. "Subahanallahi lafiya kuwa me ya faru?"






By
*GARKUWAR FULANI*
10/4/20, 7:04 PM - Mmn Khalid: Kanta ta shiga jinjina masa, cikin kuka me ɗauke da murmushi tace.
"Ya Adnan Kunnuwan Saifuddeen sun buɗe, Saifuddeen ya fara jin magana da yin magana." Idanu Ɗr Adnan ya ɗan zaro cikin yanayin mamaki haɗi da kaɗuwa yace.
"Kinsan me kike faɗi kuwa Rahama, Saifuddeen ya fara jin magana fa kikace?". Kanta ta jinjina masa, tare da ɗan sharce hawayen farin cikin dake kan fuskarta, cikin farinciki tace.
"Eh Ya Adnan wallahi dagaske yanzu Raleeya ta ƙirani tana kuka take faɗamin".
wani irin matsanancin farinciki ne ya lulluɓe zuciyar Dr Adan jawo Adda Rahma'n jikinsa yayi tare da rungumeta ƙam, take suka shiga yiwa Allah godiya.
miƙe Ya Adnan ɗin yayi tare da mikar da ita cikin tsantsar jin daɗi yace. "Maza tashi muje gidan Ummi'n, tashi da sauri mu tafi".
cikin farinciki kuwa ta miƙe ɗaki tashiga ta ɗauko mayafinta,
Shi kuwa Ya Adnan miƙewa yayi, zuciyarsa cike da farinciki, ya nufi ɗakinsu Faruq yana shiga ya kamo hannun Farouq da kuma Adam tare da cewa.
"Yaran kirki kuzo mu tafi gidan Ummi".
Cikin Mamaki Faruq ya kalleshi tare da cewa.
"Daddy da sassafen nan".
Kai ya gyaɗa mishi tare da cewa.
"Uncle Saifuddeen ne ya worke shi zamuje mu dubi".
Wani irin zabura sukayi a tare tare da cewa.
"Dady ya worke? yana yanaji? kuma yana magana? da tafiya?".
Cikin sauri Ya Adnan yace.
"Ku dai kuzo muje".
aifa tuni sunyi gaba, Adda Rahma kuwa tana fitowa suka ɗunguma zuwa mota.


Raleeya kuwa tana jin Adda Rahama ta katse wayan, numbern Raihana ta nema, wayar bata wani jima tana ringing ba, Raihanan ta ɗauka, kaman yanda Raleeya ta sanarwa Adda Rahma muryarta na rawa, haka ma ta sanarwa da Raihana, kusan sumewa Raihana tayi saboda tsananin mamaki da kuma shiga shock, sosai taji abun wani iri acikin kunnuwanta, saboda abune da bazasu taɓa zato ba, duba da irin yanda aka kwashe tsawon shekaru baya ji ba kuma ya magana, kuka ta fashe dashi, dan takasa jurewa bare ita dama saurin kukane da ita,
ji take kaman tayi tsuntsuwa ta ganta acikin garin Gombe, Sameenu dake zaune agefenta, wanda shima yaji komai ne ya jawota ya rungumeta ƙam acikin jikinsa, shi kansa saida idanunsa suka kawo ƙwalla, sosai shima yaji hankalinsa ya taho Gombe, take ya miƙe cikin kula ya janyeta daga jikinshi cikin tsananin farin ciki yace.
"Zauna Ummu Affan, bari yanzu inje airport inda in bincika man in akwai jirgin da zai tafi Gombe, yau ko gobe zamu taho Gombe'n.
Cikin tsananin jin dadi tace to.
Kana ta kuma jawo wayar ta kira Raliya kan zata ce mata ta haɗata da Hammansun taji muryanshi to kuma wayar Raliya sai tana sa mata line busy dole ta haƙura.

Raleeya kuwa suna gama waya da Raihana, numbern Bappa Ali ta dannawa ƙira, yana ɗagawa taji wani sabon kuka yazo mata, saboda jin Bappa Alin suke kaman Babansu mahaifi, hankalin Bappa Ali ne ya tashi sosai, jin yanda muryan Raleeyan ke rawa, cikin nuna damuwarsa yace. "Raleeya lafiyanki kuwa, me yake faruwa? Meya samu gidan?."
Ɗan jan sheshsheƙa tayi murmushi ne kuma yazo mata, cikin zumuɗi tace.
"Bappa Ali kunnuwan Hamma Saifuddeen sun buɗu, yanzu Hamma yanajin magana kuma yana iya mayarwa." amatuƙar ba zata Bappa Ali yaji sauƙar maganan Raleeyan acikin kunnensa, wani irin farinciki ne yaji ya lulluɓe zuciyarsa, irin wanda bai taɓa jiba a rayuwarsaba ko randa aka haifa mishi Dady baiji wannan farin cikinba, Idanunsa ne suka ciko da ƙwalla, jiyayi gaba ɗaya jikinsa yayi, sanyi, cikin ƙarfin guiwan da ya samu kansa aciki, yace. "Alhamdulillah,
Allah abun godiya. Tabbas dama idan da rai to tabbas da rabo, sannan ba acire rai da ni'ima haɗi da kyautar Allah, ni dama tun can bancire rai da cewar Saifuddeen bazai sake ji ko magana ba, tunda dama ciwo ne daya sameshi a sama, bawai da shi aka haifesa ba.
Alhamdulillah Raliya mun godewa Allah mai rayawa mai kashewa mai badawa mai hanawa mai cuta da waraka".
Sosai ya nuna farincikin sa akan hakan, har ma yace gashinan zuwa Gombe'n, dan idan ba zuwa Gombe'n yayi ba, kwata-kwata bazaiji zuciyarsa ta gamsu ba.

Suna gama waya da Raleeyan ya shige cikin gida dan ya faɗawa Aunty Meena, fuskarsa cike take da fari'a, kallo ɗaya zaka masa ka fahimci cewa yana cikin matsanancin farinciki.
Kai tsaye makullin matarshi ya ɗauka wacce Baga daɗe da saya mishi ita kuma hannunshi bai gama faɗawa a tuƙin sosaiba. Kai tsaye unguwar Sirankiyo ya nufa gidan ƙanwarsa Goggo Dada mahaifiyar Ahmad,
koda taji wannan dadɗan labarin da sanyin safiya cewa tayi ƙafarshi ƙafarta da ita zaije.

Acan ɗakin Hayatuddeen kuwa, Ahmad ne ya ƙira Ishaq ya faɗa masa buɗuwan kunnen Saifuddeen ɗin, sosai Ishaq ya shiga shock dajin haka'n, lokaci ɗaya kuwa ya zube akan guiwowinsa inda yayi sujjada, tare da yiwa Allah godiya, sannan ya fashe da kukan farinciki, wanda shi dama yanaji ajikinsa cewa, watarana Allah zai dubi Saifuddeen ya yaye masa koda ɗaya daga cikin larurorinsa, kukan farinciki yayi sosai cikin gida ya shiga ya sanarwa Ummanshi da Babansu sosai sukayi farin cikin wannan labarin inda shima sukayi mishi addu'ar Allah ya yaye mishi tasa larurar shima ɗin.
, take kuma ya miƙe tsaye, waje ya nufa, dan so yake yaji muryan abokin nasa acikin kunnuwansa.

Shi kuwa Saifuddeen har yanzu akwance yake, sai nannauyan nishi yake saki akai akai, dan har zuwa yanzu bayan nasa bai sake ba.
Ummi na fitowa daga sashin nata, sukayi karo da su Adda Rahama, wanda zuwansu kenan. Cikin sauri Adda Rahama ta faɗa jikin Ummi tare da sakin kuka mai ɗauke da dariya.
Saboda farinciki Ummi ma rungume Adda Rahaman tayi, cikin matsanancin farinciki Adda Rahama'n tace. "Ummi ina Saifuddeen, inason naji muryarsa, ina kuma so yaji magana ta, wanda tsawon shekara 20 kenan da ya daina jinta".
Hawaye ne suka silalo daga cikin idanun Ummi, hannun Adda Rahman ta kama.
cikin sanyin murya tace. "Zakiga Saifuddeen Rahama, amma yanzu mutafi zuwa ɓangaren Zaleeha, saboda Saifuddeen yace min tariga da ta suma, muje tana buƙatar taimakon mu".
Idanu Adda Rahama taɗan zaro atsorace, bakinta na rawa tace. "Subahanalli Ummi me yake faruwa ne?".
ɗai-dai lokacin Dr Adnan ne ya ƙaraso inda suke tsayen, cikin girmamawa ya durƙusa har ƙasa inda ya gaishe da Ummi'n, amsa masa tayi tana murmushi, cikin kulawa dan Ya Adnan kamar Nuruddeen take ganinshi cikin jin daɗin zuwansu tace.
"Yauwa Adnan kaje ciki, Saifuddeen yana ta kukan cewa bayansa na riƙewa ka isa ka duba shi yana ɗakin auta".
Cikin sauri Dr.Adnan ɗin yace.
"To." take ya wuce sashin Ummi'n. Ummi kuwa hannun Adda Rahama ta kama suka nufi sashin Saifuddeen, dan dama Saifuddeen din yace mata Zaleehan nacan sashinsa.

Gaba ɗaya hankalin Ummi, da kuma na Adda Rahama atashe yake. tun daga falo suka hango ƙofar bedroom ɗin nasa a buɗe,
cikin sauri Ummi ta ƙarasa Adda Rahma na biye da ita, inda suka kutsa kansu cikin ɗakin, hango Zaleehan da sukayi nannaɗe acikin bargo ne, yasasu ƙarasawa cikin ɗakin da sauri.
Hankalin Adda Rahman a tashe ta ɗan yaye bargon, tare da ɗago hannun Zaleeha'n, luuu haka taji hannun ya sake, idanu taɗan zaro, tare da kai hannunta saitin hancin Zaleeha'n, jin har yanzu bata numfashi yasa hankalinta sake tashi cikin kiɗima ta kalli Ummi data ɗan kauda kanta dan surkunta. Atsorace Adda Rahman tace.
"Ummi Zaleeha fa bata numfashi, meya sameta ne?".
Cikin fargaba Ummi ta janye blanket ɗin da Zaleehan ke lulluɓe dashi dan ganin akwai sutura a jikinta, idanunta ne suka sauƙa akan jinin da ya ɓata farin zanin gadon, wanda har aƙafan Zaleehan, akwai ɗigo ɗigon jini da ya bushe ajikin fatarta.
Wani irin matsanancin tausayin Zaleehan ne ya daki zuciyar Ummi, har saida taji ƙwalla sun cika mata ido.
Adda Rahama ma da idanunta suka sauƙa akan jinin dake jikin zanin gadon, ji tayi gaba ɗaya jikinta yayi sanyi, tausayin Zaleehan ne ya kamata, cikin sanyi hawaye na tsastsafo mata cikin ƙwayar idonta ta zauna abakin gadon tare da tallafo kan Zaleehan ta ɗaura akan cinyarta, dan dukkansu sun fahimci me ya faru da Zaleeha'n.
Cikin sauri cikin kiɗima Ummi ta wuce toilet, da kanta ta haɗa wa Zaleehan ruwan wanka me zafi acikin bathtube, wanda tasan idan ta shiga zata ɗanji dama dama, saida ta haɗa komai daya dace, sannan ta fito daga cikin toilet ɗin dan tama mance a samu ta farfaɗo yafi dacewa. Haryanzu kuwa Adda Rahama na riƙe da Zaleehan,
ɗan ƙaramin fridgen dake ɗakin, Ummi ta buɗe, tare da ɗauko goran ruwa, dawowa kan gadon tayi ta zauna, hannu tasa taɗan ɗago kan Zaleeha dake cinyar Adda Rahama, buɗe murfin goran tayi, tare da ɗan tsiyayan ruwan ahannunta, ɗan yayyafa ruwan tayi akan fuskar Zaleeha, waiko zata farfaɗo amma shiru, hakanne yasa zuciyar Adda Rahama soma bugu da sauri sauri, saboda tsoro.
Ummi ma kanta ta tsorata da hakan, sai-dai batayi ƙasa a guiwa ba, saida tayi hakan kusan sau uku, kafun taji Zaleehan ta saki wani irin numfashi, tare da sauƙe nannauyan ajiyar zuciya. Ganin ta farfaɗo yasa su Ummi sauƙe ajiyar zuciya.
Ahankali ta shiga ɗan jujjuya kanta, batare da ta buɗe idanunta wanda sukayi nauyi haɗi da kumburi, cikin muryarta da ta dashe wanda ko fita da kyau batayi, amatuƙar wahalce batare da ta dawo cikin hayyacinta ba tace.
"Dan Allah Hamma Saif kayi haƙuri, zafi nakeji zan mutu, wayyo Allah na Hamma Saif kayi haƙuri dan Allah zafi....".
Wani irin kuka ta fashe dashi me tsuma zuciya, still bata buɗe idanunta ba.
Matsanancin tausayinta ne ya cika zuciyar Ummi, ahankali cikin sassanyar murya tace.
"Zaleeha, buɗe idanunki kinji, ba Hamma Saif ɗinki bane nice Umminkune, buɗe idanunki kinji."
Jin muryan Ummi acikin kunnuwanta, yasa ahankali taɗan soma bude idanunta wanda sukayi dishi-dishi, suka kuma kumbura kaman wanda ta yi sati guda tana kuka.
Ganin Ummi yasa ta faɗa jikinta tare da ƙanƙameta ƙam, sosai ta fashe da wani irin kuka mai taɓa zuciya dan gani take kamar zai sake zuwa ya danneta. Bayanta Ummi ta soma

Please Login or Register in order to submit comment