Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya hau kekensa ya wuce cikin gidan, da sauri Zaleeha ta rufa masa baya, cikin sassanyar muryarta take ƙiran sunansa, sam bai tsaya ba balle har tayi tunanin zai juyo ya kalleta, sun kawo dai-dai bedroom ɗinsa ne cikin sauri ya shige tare da jawo ƙofar ya rufe, hakanne yasa bata samu daman shiga ba, fuska ta kwaɓe tare da ɗan karyar da wuyanta gefe, a bayyane tace.
"Me yasa bazaka amsa min tambayoyina ba Hamma Saif why?." asanyaye ta juya ta fice daga cikin falon. Shikuwa yana shiga cikin ɗakin nasa ya saki wani irin murmushi, dariya ya ɗanyi me sauti, cikin tsantsar nishaɗin daya samu kansa yace. "Kina yarinya ƙarama amma bakya iya gane mutane to in kin tsufa kuma wato wata ranama cewa zakiyi ni ba mijinki bane ki sani uku".
daga haka kayan jikinsa ya ɗan rage sannan ya wuce toilet.

Zaleeha kuwa daga sashin nasa part din Ummi ta wuce, rashin ganin kowa acikin falon yasa taɗan ɗaga murya, tana ƙiran sunan Ummi'n, jin shiru babu amsa ne yasa ta nufi ɗakin Hayatuddeen kasancewar ta jiyo muryar Hayatuddeen ɗin yana ce mata.
"Ummi ta shiga wonka".
kana taga ƙofar ɗakin nasa abuɗe, ahankali ta tura ƙofar ɗakin ta shiga bakinta ɗauke da sallama.

Shi kuwa Hayatuddeen zaune yake akan sofa, yayinda ya baje hotunan Abbansu da Ya Nuruddee da Saifuddeen tun kafin ya samu matsalar tsayuwa, kasan cewar in Ummi taga hotunan tana kukane yasa suka ɓoyesu, yanzuma begen ganin mahaifinsu da babban yayansune yasa ya fito dasu.
Hotunan Saifuddeen ne agabansa yana kallo, wanda kuma yayi hotunan ne tunkafun yasamu nakashewar ƙafafunsa, hankalinsa ya ɗanyi nisa shiyasa baiji sallaman nata ba, Ahankali ta ƙaraso cikin ɗakin, tare da baza idanunta akan hotunan dake gaban Hayatuddeen ɗin, wani irin bugawa taji zuciyarta tayi, alokacin da ta sauƙe idanunta kan wani hoton Saifuddeen wanda yake tsaye akan ƙafafunsa shidasu Ahmad dasu Salisu Ishaq yana murmushi, ga fuskarnan tasa fayau ta bayyana, babu wani cikar ƙasumba asamanta, saɓanin yanzu da saje yayi mata ƙawanya, hannunta dake rawa tasa ta ɗauko hoton, gaba ɗaya jikinta ɓari yake, bakinta na rawa tace. "Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un, Hayatuddeen waye wannan?."
jin muryanta yasashi ɗago kai, murmushi yayi yana ɗan kaɗa kai yace.
"Kaman yaya waye wannan kina nufin baki ganeshi bane?." Cikin ruɗani tace. "Please Hayatuddeen kafaɗamin waye shi, karkacemin shine Hamma Saif kuma na kasa gane shine dan zan jawa kaina Allah ya isa, ka cemin wanine daban ba Hamma ba."
Cikin yanayin mamaki yaɗan shafi sumar kansa, shaye da mamaki yace.
"Ikon Allah yau kuma Hamma Saif ɗinne baki gane ba, to ki wanke idanunki wannan ba kowa bane face Hamma Saif, nasan kinyi mamakine saboda kin ganshi tsaye kan ƙafafunsa, lokacin bai samu matsalan spinal cord injury bane shiyasa." Durƙushewa tayi akan ƙafafunta, murya na rawa tace.
"Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un, wallahi shine, shine mutumin daya taimakeni Hayatuddeen Hamma Saif ne, shi ya ceceni daga hannun ƴan iskan da suka so tarwatsamin rayuwata, shine wanda ya zamemin Garkuwa alokacin da babu me iya taimakona, shi ne wanda ya zama makari kuma madubin dubawata, da ace alokacin babu shi, da yanzu rayuwata wani babin take fuskanta ba wannan ba, Wallahi Hamma Saif ne Hayatuddeen, shi nake ta nema tsawon shekaru Wlh Hamma Saif ne!!!." Ta ƙarishe mgnar da ƙarfi Baki Hayatuddeen ya buɗe yana kallonta, shikam cike yake da mamakin Zaleehan, dan kalamanta sun ɗaure masa kai.
Dai-dai lokacin Ummi ta shigo cikin ɗakin da sauri, kasancewar fitowarta falo kenan, taji tashin maganganun Zaleeha'n, Zaleeha kuwa ganin Ummi yasa ta ƙarasa gabanta cikin sauri, tuni hawaye sun kwaranyo daga cikin idanunta, hannuwan Ummin ta kamo tana jijjiga kai tace.
"Shi ne Ummi Hamma Saifuddeen ne, wallahi da gaske shi ne! Gskyan ADDA MARYAM tayi gsky."
Da mamaki Ummi ke kallonta, cikin rashin gane inda maganganun Zaleehan suka dosa tace.
"Bangane me kike faɗa ba Zaleeha, shi ne wa?". Ganin Ummin kaman bazata fahimceta ba, yasa cikin sauri ta nufi hanyar fita daga ɗakin, baki buɗe Ummi ta bita da kallon mamaki.

Hayatuddeen kuwa zuwa yanzu ya fahimci abun da Zaleehan ke nufi, dan baya taɓa mantawa sun taɓa taɗin da Zakariyya, wani irin dariya yayi, tare da shafa sumar kanshi, cikin matsanancin farinciki yace.
"Yess dama ashe akan mune aketa wannan badaƙalar, wannan shine rashin sani yafi dare duhu, mu ake so kuma mu ake gudu, batare da ansani ba."
Dariya yayi sosai, hakanne yasa Ummi da Raleeya wanda ta shigo yanzu, suka zuba masa ido, cikin ƙufula Ummi tace.
"Wai kam lafiyanka, kaketa dariya?." gyara zamansa yayi, cikin zumuɗi ya labartawa su Ummi duk abun daya sani.
Ai kam su Ummi sosai suka shiga mamaki, sun kuma yi farinciki sosai, tabbas sun yarda cewa Allah Babu yanda baya abunsa.
Raleeya kuwa cewa tayi. "Lallaima Aunty Zaleeha ashe dama duk wannan guje gujen naki, akan Hamma ne batare da kinsani ba." ita kuwa Zaleeha tana fita part ɗinsa ta nufa da gudu, dai-dai ta kawo bakin ƙofar shiga falon nasa, shima ya bude zai fito.

Cikin wani irin tsananin sauri da rawan jiki da wani irin sabon shauƙi ta faɗa jikinsa, wani irin zazzafan runguma tayi masa me ratsa jiki da zuciya,
azauce ta soma sakar masa wasu irin zazzafan kisa-kisai aduk fuskarsa harma da wuyansa, lips dinsa ta kamo tana tsotsa kana hannunta na shafa tsakiyar kanshi zuwa ƙeyanshi da kuma wuyanshi, duk ta zauce ji take kaman ta maidashi cikin jikinta, wasu irin hawayen farinciki ne suke kwaranyowa daga cikin idanunta, hannayenta tasa ta kamo kumatunsa, cikin wani irin mood da ɗaga murya tace.
"I love you Hamma Saif, I really love you, I love you so so much, i can't live without you, nd I love you forever nd ever...." Amatuƙar zauce ta ƙare maganar.
Wani irin kyakkyawan murmushi ya sakar mata, tare da zuba mata kyawawan idanunsa. Harshenta tasa ta lashi lips ɗinsa, cikin wani irin sanyi tace.
"Inasonka Hamma Saif, Inasonka Sosai da sosai, meyasa baka faɗamin ba? meyasa ka ɓoyemin? tsawon lokuta da yawa ina bege da jiran zuwanka, mutane da yawa sunyi mini kallon zautacciya kuma mahaukaciya akan ka, natsumayeka, na kuma soka tamkar raina, Inasonka jiya, yau, yanzu, dama gobe, da jibi, kuma zanci gaba da sonka har gaban abada, kaine rayuwata Hamma Saif, bugun numfashi da zuciyata, tana tafiya ne da naka, kaine gaba ɗaya duniyata Hamma Saaaaaiiiiffff!!". Yanayin yanda taja sunan nashi shiyasa yaji gaba ɗaya duk gaɓɓan jikinsa sun amsa, idanunsa ya lumshe, alokacin da yaji ta kamo harshensa tana succking, ga kuma hannunta da ta ɗaura akan ƙirjinsa, tana murza kan nipples ɗinsa, kasancewar rigar jikinsa irin me aninayen nan ne, ɗayan hannun nata kuwa cusa shi tayi acikin gashin kansa, wani irin hot romantic kiss takeyi masa, wanda yasa gaba ɗaya sassan jikinsa ya amsa, bayajin zai iya jure salon da Zaleehan keyi masa, hakan yasa shi ƙara mannata da jikinsa, azafafe cikin matsanancin shauƙi suke kissing ɗin juna, sama da 20 minute suka ɗauka ajikin juna, duk sun gigita kansu, wani irin romance sukayi me tsayawa arai, ya sha mamakin yanda ta ciresa a hayyacinsa ƙwarai, saida aka ƙira sallan magriba, sannan suka iya janye jikinsu, baƙaramin dauriya yayi ba, na hana kansa kusantarta, dan kuwa ta kaisa ƙololuwa, saidai sanin cewa ba itace da shi ba, yasa baiyi yu ƙurin yin sex da ita ba, saboda hakan dai-dai yake da shiga haƙƙin Ameena.

Ɗakinsa ya wuce dan dole saiya sake sabon wanka, dan ko tantama bayayi yanda suka murza juna yasan tuni sperm ya zo masa, ita ɗin ma Zaleeha hakanne ya kasance da ita, dan tuni ta jiƙe, saida tayi wanka sannan tayi alwala, cikin wani irin nishaɗi takejin kanta.
Koda tayi sallah godiya tayi tayiwa ugangiji, bata iya barin sai tayi sallan ishaba ta kira Aunty Lubna tana jin ta ɗaga wayar cikin tsananin farin ciki tace.
"Alhamdulillah Aunty Lubna, yau na gano wanda ya taimakeni ya ceceni a hannun ƴan iska".
Tsoro da mamaki Lubna tace.
"Innalillahi Zaleeha a ina kuma to me ruwanki dashi karfa ki mance ke matar aure ce".
Cikin zumuɗi tace.
"Mijina ne Aunty Lubna Hamma SAIF shine wanda ya taimakeni, shine naketa nema, ashe sanadin dukanshi da sukayi ya samu larurar nakasar tafiya My Aunty wlh I very very very love him, shine rayuwata".
Tana gama faɗin hakan, ta katse kiran, ta kira Ya Ahmad ɗin ta, wanda yaketa dariya dan yana kusa da Lubna yaji duk magar da sukayi, jin yana dariya yana ce mata.
"Aha ƴar uwarta na tayaki murna kice abin nema ya samu matar ɗan sanda ta haifi kulki an gano ɓoyeyyen masoyi ko".
Da sauri ta katse kiran dan kunyarshi jin yadda yaketa mata dariya.

Daga nan ta kira Rashida ta gaya mata nan itama tai ta mata tsiya harda cewa,
"Allah ya sa dai yau kece dashi ki samu ki nuna mishi soyayyarki".
Dogon tsaki tai tare da cewa.
"Ke dai bari ai wlh kishiya bata haɗu ba".
Dariyar Ishaq da tajine yasa ta katse kiran da sauri.shiko Ishaq da yake gefen Rashida akan sallaya da alama salla sukayi,
dariya yayi sosai tare da cewa.
"Masha Allah, ashe yanzu kam ana kishin aminina bare yau an gano shine masoyin da ake nema."
Dariya sukayi baki ɗayansu.

Hayatuddeen kuwa tuni ya kira Zakariyya ya shafa mishi zancen,
shima Zakariyya jiki na ɓarin gulma ya shiga falon Baba Malam ya gaya musu,
Dariya sukayi tare da sanya al'khairi.

Saifudden kuwa tunda yaje sallan Magriba bai dawo gidan ba saida akayi sallan Isha.
Yana dawowa kuwa dukansu suka haɗe a falo danyin diner, hadda Ameena dan tun kafun magriba ta dawo, saidai ta tsaya a sashin Ummi, bata ƙaraso sashin su ba.

Koda suka zauna akan dinning ɗin Zaleeha ne tayi serving ɗinsu, gaba ɗaya jinta take awata duniyar farinciki, sam takasa ɗauke idanunta akan Saifuddeen, ji take kaman ta maidashi cikin jikinta, bataƙi ace su kasance tare ajikin juna ba, daga nan har zuwa ƙarshen rayuwarsu, shikansa yau kasa ɗauke idanunsa akanta yayi, dan shima yanajin kansa acikin nishaɗi, saboda yasan kome tayi masa abaya tayi ne abisa rashin sanin, cewa shi ne muradinta, tabbas yasan Zaleeha tayi masa wani irin mahaukacin so, wanda kuma ayanzu hakan ke bayyana acikin idanunta ƙarara, su Ummi kansu yau saida suka fahimci farincikin Zaleeha'n, dan ko abincin kirki bata iya ci ba. Haka dai suka kammala diner'n cikin nutsuwa, hira suka ɗan taɓa kaɗan kafun kowa ya nufi sashinsa, shida Ameena suka wuce part ɗinsa.
Ita kuwa Zaleeha ta wuce part ɗinta, yaune karon farko da taji cewa inama da ace ita kaɗaine awajensa, tabbas da ace yau aɗakinta yake, da ta shayar dashi wata madaran soyayya wanda bai taɓa jin irinta ba, zata nuna masa tattali, da kuma soyayya me tsada da kuma tsabta, zata mantar dashi duniyar da yake ciki, da ma kuma shi kansa, lallai tashirya masa wani abu na musamman wanda ta tabbatar zaiyi alfahari da hakan, koda ta kwanta akan gado, hannu tasa ta shafi cikinta, idanunta ta lumshe saboda wani irin tsabar daɗin da taji, haƙiƙa Allah Na sonta, ya bata Hamma Saif ɗinta, ya kuma bata ɓoyayyen masoyinta, sannan ya bata ciki dashi, Baba Malam ɗin ta kuma ya yafe mata kafurai da dama sun musulta sanadinta aduniya ta gama samun komai.

Can ɓangaren Saifuddeen da Ameena kuwa, a daren yau morewansu sukayi, dan sosai ya dage wajen bata haƙƙinta, bai barta ba kuwa saida ya zautar da ita, ya sata kuka da sambatun daɗi, dan har jin kanta take kaman ba'a duniya ba, lallai ta yarda Hamma Saifuddeen gwanine wajen iya sarrafa mace, lokaci guda yake gigita tunanin mutum.

Washe gari da sassafe kuwa misalin ƙarfe 6 flight ɗinsu ya ɗaga zuwa sararin samaniya zuwa garin Lagos, har aiport kuwa su Ummi suka rakasu, haka suka rabu cike da kewar juna.

Ci gaba da luluƙawa jirgin nasu yayi asararin samaniya, ahankali taɗan zame jikinta ta kwantar da kanta akan kafaɗansa, hannayensu kuwa dama sarƙafe suke acikin na juna, jin ta kwanta ajikinsa yashi ɗan shafa kanta, ahankali ta ɗago kanta, take kuwa idanunta suka sauƙa akan wata matashiyar budurwa da ta kafesu da ido, idanu Zaleehan ta zuba mata, tanason sanin inda tasan fuskar budurwan, take sunan budurwan ya faɗo mata wato Asma'u Ahmad Matawalle, ganin yanda Asma'un ke kallon Saifuddeen kaman zata cinyesa ɗanye ne, yasa taji wani irin zazzafan kishi ya cika zuciyarta, ƙasa-ƙasa ta harari Asma'u Ahmad Matawalle'n, ahankali ta ƙara shigewa jikin Saifuddeen ɗin, tare da juyo da fuskarsa gareta. Shikuwa sarai tun ɗazu ya lura da Asma'u Ahmad Matawalle'n, amma sai ya kawar da kansa, yayi kaman bai ganta ba, Zaleeha kuwa tayi hakanne saboda ta nunawa Asma'un cewa fa yana da mata, ga kuma tanan akusa dashi. Ganin hakane yasa Asma'un ɗauke idanunta daga kansu, dan kuwa sunyi masifar dacewa da junansu.
Cikin zuciyarta tace.
"Ikon Allah, yanzu kenan matansa biyu, ni dama tunda naji ance ya kara aure, na ciresa araina saboda najima da gane cewa, me aurensa sai me sa'a, bare irin wannan matar tasa gogaggiya wayayya, ga ta kyakkyawa, dole bazai kallemu ba, dan da dukkan alama balarabiya ce, dan wannan tsantsar kyaun ba abanza ba, me irin wannan macen ai bazai taɓa kallon wata mace ta burgeshi ba, dan duk wani kyau anƙaresa ajikin matarsa." Shi kuwa Saifuddeen ganin yanda Zaleeha ta lumshe idanunta ne, ya sashi ɗaura hannunsa akan cikinta, asanyaye ya hura mata iskan bakinsa me daɗin ƙamshi.
Jin sauƙan iskan bakinsa, akan fuskarta, yasa ta buɗe idanunta, wani kyakkyawan murmushi ta sakar masa, tare da ƙara rungume sa, shiɗin ma murmushi ya mata, tare da ɗaura kansa akanta, haka suka kasance manne da juna, har jirginsu ya sauƙa a babban Airport ɗin dake Lagos DAN International Airport Lagos.
Suna riƙe da juna suka fito daga cikin jirgin, already sun samu jirgin da zai kaisu ƙasar Turkey har zuwa garin Instanbull a ready, hakan yasa basu wani ɓata lokaci ba, suka shiga,
ciken jirgin, suna shiga cikin jirgin kuwa, bai wuce da 30 minute ba jirgin ya tashi zuwa sararin samaniya.

Saida sukayi tafiya me nisa, kafun ahankali ya ɗaura ƴan yatsunsa biyu akan wuyanta yana shafawa, akasalance taɗan ɓude idanunta, giransa ɗaya ya ɗaga mata alaman
"Ya dai?." ɗan kwaɓe fuska tayi, cikin sakalci da kuma shagwaɓan daya zame mata jiki tace.
"Na fara jin yunwa." kyawawan Idanunsa ya ɗan zaro, cikin yanayin mamaki, dan kuwa ko 30 minute ba'ayi ba, da ta gama cin su biscuits da snacks amma yanzu wai har tana maganan yunwa takeji.
Murmushin daya ƙara bayyana kyakkyawar fuskarsa yayi, ahankali yasa hannu ya ja dogon hancinta, in a body language ɗinsa yace. "To acici kazar birni, ni kam har tsoron wannan yawan cin naki nake, kodai kin zama rumbun gwamnati ne."
Ya ƙare yanayin maganan yana ɗan dariya.
Ɗan ƙaramin bakinta ta turo gaba, mintsininshi tayi tare da cewa.
"Ni ce ma acicin ko? to ai naga koma me kai ka jawo, tunda kaine kasamin yaro me ci acikin, haka kullum sai yata ƙwaƙulana, da zaran naci abinci sai ya kwashe, haka fa nakejin cikina kaman ba komai acikinsa, nidai wallahi kasan yanda zakayi dani ehe."
ta faɗi maganar tana me shafa cikin ta, yanayin yanda tayi maganan yasa gaba ɗaya alamomin yarinta suka bayyana akan fuskarta.
Jawota jikinsa yayi da kyau, tare da zuba mata ido, acikin jirgin nasu kuwa kowa harkan gabansa yake, kasancewar ba a normal sit suke zaune ba, wajen nasu na musamman ne VIP, ahankali yake ɗan goga hancinsa da nata, cikin nutsuwa ya kamo lips ɗinta masu taushi, wani irin tsotsa yake mata me kwantar da zuciya, sannu ahankali yake tura mata yawunsa abakinta tana haɗiyewa, sosai taji komai ya fara lafa mata, dan tayi imani yawunsa kaɗai sinadari ne ajikinta, kissing ɗin juna sukayi sosai sama da 25 minute, saida sukaji suna neman wuce gona da iri, sannan suka tsagaita, lub tayi ajikinsa tana sakin ajiyar zuciya.

Tafiya suka sha asararin samaniya kafun jirginsu ya sauƙa airport ɗin, dake babban birnin Turkey wato _*Sahabi Gokcen International airport Instanbull*_ Yana riƙe da hannunta suka soma sauƙowa daga kan matattakalan jirgin, wani irin daddaɗan iska da kuma matsanancin sanyi ne ya soma ratsa duk ilahirin jikinta, haka ma Saifuddeen ɗin, saidai baza'a haɗa jin sanyinsa da nata ba, because ita me lafiya ce, shikuwa lafiyar tasa har yanzu da ɗan saura, saidai shima kuma yanajin sanyin. maƙalewa tayi ajikinsa ƙam, tana me ƙarewa yanayin garin kallo, Gari ne wanda ya haɗu sosai komai nasa atsare yake gwanin burgewa ko ina korayen itatuwa ga ruwan dake malale a lugguna da soƙoƙin garin, duk da cewa dare ya ɗan soma yi, hakan baisa mutanen cikin garin sun tsaida hada hadan da sukeyi ba, kowa rayuwarsa yake babu ruwan wani da wani, ganin yanda take ta kakkame jikinta alaman sanyin na shiga jikinta ya sashi tsaida musu me taxi wanda duk na cikin airport ɗin ne, me taxi ɗin da kansa ya sa musu kayansu abayan motan, sannan suka shiga suka zauna, wata ƴar farar takarda ya ciro daga aljihunsa, rubutu yayiwa akan paper'n sannan ya mikawa mai taxi ɗin, karɓan takardan yayi ya karanta, sunan hotel ɗin. _*Swissotel The Bosphorus Luxury Instanbull Hotel*_ ya rubuta masa, hakan kuma na nufin cewa, wannan hotel ɗinne yake so ya kaisu, take kuwa babu ɓata lokaci suka kama hanyar hotel ɗin.
Basu wani jima suna tafiya ba suka iso bakin tangameme kuma haɗaɗɗen hotel ɗin, hotel ne da akayi masa tsari me kyau, komai gwanin burgewa kana a saman ruwa yake. Biyan me taxi ɗin, yayi sannan suka shiga cikin hotel ɗin, daga gefe Zaleeha ta zauna, inda shi kuma ya ƙarasa yayi musu duk wani abun daya dace.
Wani haɗaɗɗen ɗaki ya kama musu, me shegen tsada da kyau, dan ko anan wajensu VIP ne sukafi kama ɗakunan dake area'n, wato Very Important People, hannunta ya kama suka nufi ɗakin nasu.
Key yasa ya bude ƙofar ɗakin, da addu'a acikin zuciyarsa ya kutsa kansa cikin ɗakin, kana itama ta rufa masa baya, yayin da suka samu kansu acikin haɗaɗɗɗen falo, wani irin sassanyan ƙamshi ne ya daki hancinsu. Cikin mamakin haɗuwan falon Zaleeha tace. "Wow, gaskiya wajen nan ya haɗu, can you imagine seriously ban taɓa tunanin haka wajen nan ya haɗu ba."
yanayin yanda tayi maganan tana ɗan yawo acikin katafaren falon, shi ya sashi sakin murmushi, yasan Zaleeha tanason abubuwan ƙyale-ƙyale, da kuma duk wani abu daya shafi shaƙatawa, shiyasa yayi amfani da hakan, wajen kama musu ɗakin da yasan zai gamsar da ita, burinsa akullum shine ya faranta mata, saboda bayan so da ƙaunarta dake kwance acikin zuciyarsa, akwai tarin tausayinta, shi me rauni ne akanta ƙwarai.

Zaleeha dake ta santin falon nasu, wanda yake ɗauke da two bedrooms acikinsa, sai gefe kaɗan kuma wani haɗaɗɗen dinning area ne, idan ka ƙara gaba kuwa, wani haɗaɗɗen decoration akayi, sannan aka kewaye wajen da wani haɗaɗɗen cottings me shara shara, daka yaye cotting ɗin kuwa, wani haɗaɗɗen swimming pool ne wanda aka masa tsari me kyau, ruwan cikinsa sky blue me masifar ƙamshi. Juyowa tayi ta kalli Saifuddeen ɗin, wanda tun shigowansu idanunsa akanta suke, murmushi tayi masa tare da masa waving fingers ɗinta, cikin son tsokanansa tace.
"Hey Bravo, wannan kallon fa duk na miyene? wato kaga big girl, big ajibo, shine kake neman haukacewa akaina ko, well kacigaba da kallo na, maybe anjima na iya kula ka."
Dariya irin marar sautin nan yayi sosai, dan yasan zallan tsokana ce kawai ke damunta, ƙwafa yayi tare dayi mata alaman cewa.
"Hmmm zan kamaki ne ƴan mata."
Tagefenta ya raɓa ya nufi ɗaya daga cikin bedroom ɗin falon, ita kuwa Zaleeha tsayawa tayi tana ƙarewa kowani kusurwa dake falon kallo kujerune ɗika-ɗikane suka zagaye da falon sai wani tattausan carpet dake malale a tsakiyar falon da akayiwa daɓe da katakon ƙasashen wajen,
ga wani ɗimemen tv a manne wanda kana zaune a gefe ma zakiyi control ɗinshi da wayarka,
sai wani ɗan danda mali da akayi aka zagayeshi irin ɗan abun nan

Please Login or Register in order to submit comment