Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

      
Jin alaman kwanciyarta ya sashi buɗe idanunsa, don dama ba bacci yake ba. 
               Ɗan mirginowa yayi tare da juyowa, ya zama  suna fuskantar juna,  matso da jikinsa yayi kaɗan,  tare da sa hannunsa ya tallafi fuskarta,  hakanne yasa  ta buɗe idanunta.         Bakinsa ya ɗaura a dai-dai goshinta, inda ya ɗan manna mata sasanyan kiss.    
Sosai taji abun ajikinta hakan yasa ta lumshe idanunta.
A hankali yasa tafin hannunshi ya shafi fuskata,
Jawota yayi ya mannata da jikinshi, cikin yanayin zazzaɓi da yakeji ya ruggimeta. sannan yasake rufasu da blanket,  shigawa cikin jikinshi tayi da kyau tare da lafewa tana sauƙe ajiyan zuciya,
shi kuwa Saifuddeen bisa goshinta ya kuma sumbata kana ya rufesu da kyau saboda wani irin sanyi da yake ji.                 Itakuwa Ameena sosai ɗan kiss ɗin da ruggumar   da yayi mata ya jefata cikin shock, taji daɗi ƙwarai, dan kuwa koda wasa bata tsammaci kulawa daga garesa ba,  rungumeshi tayi tana murmushi.                
Shikuwa Saifuddeen yayi  hakanne, saboda yaga dacewar abun, bai kyautuwa ace yana shareta, sannan  kuma ya hanata kulawarsa, tabbas akwai haƙƙinta akansa, wanda kuwa idan bai sauƙe ba, Allah zai iya kamashi,  saboda haka dole zaiyi ƙoƙari sauƙe duk haƙƙinta daya rataya kanshi, amma badon wai yana jin sonta aransa ba sam babu ko ɗaya, ƙauna dai guda ɗaya ce, kuma tun a haɗuwar farko ya mallakawa Zaleeha gaba ɗaya ƙauna da zuciyarsa, saboda haka baijin cewa Ameena zata taɓa samun gurbi cikin zuciyarsa, saidai yayi mata kara da kawaici kawai dan darajar sonshi da takeyi tafi ƙarfin wulaƙantawa, amma bawai don yana sonta ba.

Tana rungume dashi haka bacci ya ɗauketa,  shikuwa yajima sosai kafun bacci ya ɗaukesa,  saboda zazzaɓin jikin nasa yaƙi sauƙa.
                         
Ƙiran sallan asuban fari da akayi yayi dai-dai da lokacin dayi juyi, saboda gaba ɗaya zazzaɓi ya hanashi samun isashshen bacci,   ahankali ya tashi zaune,  hannunsa ya ɗaura akan wuyansa, sosai jikin nasa yayi zafi jau.  
Cikin ɗan dauriya ya jawo wheelchair ɗinsa,   hawa yayi tare da shagwaɓe fuska, sam shi hakanan yake baida dauriyan ciwo, musamman ga  irin waƴannan ƙananun ciwukan, yafiso idan baida lafiya yayita zuba sakalci, haɗi da shagwaɓa tamkar ƙaramin yaro kuma ma dai halittarsa ce raki in yaji ciwo kaɗan zaitawa Ummyn shi da Adda Rahma Raki.      
Bathroom yashiga inda ya ɗauro alwala, koda ya fito sallaya ya shumfuɗa, sauƙa yayi daga kan wheelchair ɗin, inda ya zauna akan sallayan.              Nafila raka'a biyu yayi,  yana idarwa ya jingina jikinsa da jikin wheelchair ɗinsa, wanda ke bayansa,  ganin alamun anshiga sallan asuba ne, yasa shi ta da nasa sallan a gida, dan sam baijin cewa zai iya zuwa masallaci, bama yajin ƙarfi ajikinsa.    

Yana cikin gabatar da sallan Ameena tatashi, tasha mamakin ganinsa, dan kuwa tasan baya sallah agida,  nan dai ta wuce toilet ta ɗauro alwala, can gefe ta shumfuɗa sallayanta sannan ta tada nata sallan.             
Saifuddeen kuwa yana idarwa, addu'a kawai ya shafa,  ataƙaice yayi azkar tare da ɗan jan jikinsa ya sake hayewa saman gado,  dan zazzaɓin ƙara hawa jikinsa yake, ko ina na jikinsa ya ɗau zafi jau, kamar wanda ake hura masa wuta, sake  duƙunƙunewa yayi acikin blanket, lokaci ɗaya ya fara masassara.              
Koda Ameena ta idar da salla, cikin sanyi ta dubeshi,   tashi daga kan sallayan tayi nan taƙaraso zuwa jikin gadon.      
Cikin kulawa tasanya hannu inda taɗan taɓa forehead ɗinsa, jin jikinsa da zafi yasa taɗan waro idanunta waje.    
Cikin yanayin tausayinsa tace. 
  "Sannu baka da lafiya ne?"                        Idanunsa ya lumshe batare daya amsa mata ba, saboda sam baya son damuwa, cikin zuciyarsa kuwa cewa yayi.
"Kuji shegen iyayi, koma mene bake kika jawomin ba, ina zaman zamana kinzo kin tsotseni, jarababbiya kawai, saboda kin zuƙeni ne ae yasa duk zazzaɓin ya hau jikina,  hakanan ina matsayin saurayi, kinzo cikin mintuna kaɗan kin maidani ɗan ƙaramin bazawari."                 
Ganin yayi shiru ne yasa Ameena cikin tausayawa  ta gyara masa blanket ɗin, nan ta kashe AC'n da sanyinsa keta busawa,   asanyaye tace. 
  "Allah ya ƙara sauƙi."     
Nan tashiga kimtsa ɗakin nasa, tana kammalawa kuwa ta kunna burner, inda ta zuba turaren wuta mai daɗin ƙamshi, take kuwa ɗakin ko ina ya cika da ƙamshi.     
Fita tayi daga ɗakin nasa, kai tsaye ta koma nata ɗakin, wanka tayi  tare da kimtsa kanta cikin riga da sket na atamfa, kana ta yane jikinta da mayafi, flat shoe tasanya, kai tsaye ta nufi ɓangaren Ummi dan zuwa gaisheta, kamar yanda ta saba akowacce rana.

Saifuddeen kuwa, bacci ne ya ɗaukesa, don dama daren jiya baiwani samu isashshen bacci ba.              

Itakuwa Ameena koda ta ƙarasa ɓangaren Ummi, yau bata iske Ummin a falo ba, saidai ta taradda Raliya wanda ke ƙoƙarin kimtsa falon, kasancewar daren jiya anan Hayatuddeen ya ƙare hirarsa da ciye ciyensa, gaba ɗaya yayi fatali da filullukan kujerun falon, ya watsar su aƙasa, sannan ga ledodin sweet wanda yasha ya zubar acikin falon.
     Gaisawa sukayi da Raliyan sannan ta nufi ɗakin Ummi. 
Tsayawa tayi ajikin ƙofar tare dayin knocking,  Ummi dake zaune akan gado, jin ana buga ƙofar, yasa ta bada izinin shigowa,  ahankali Ameenan ta tura ƙofar ɗakin ta shiga.  
Ganin Ameena yasa Ummi sakin murmushi. 
Ƙarasowa cikin ɗakin Ameena tayi, anutse ta durƙusa, cikin ladabi ta gaishe da Ummi'n, nan Ummi ta amsa mata fuska asake, tana murmushi kamar kullum.   
Ganin kaya akan gadon Ummi'n, wanda da dukkan alama kayan gugane, yasa Ameenan tashi, cikin nutsuwa ta shiga jerawa Ummi kayan acikin drawer, sosai Ummi kuwa taji daɗin hakan, dan dama tana ƙoƙarin jera kayan kenan Ameenan ta shigo.   Haka Ameena ta gama jera  kayan tsab, inda suke ɗan taɓa hira kaɗan kaɗan da Ummi'n, tana kammalawa kuwa ta sharewa Ummi ɗakin nata, duk da cewa ma ɗakin fes yake, bai wani buƙatan shara, don kuwa Ummi sam batason ƙazanta, kusan awajenta ma Saifuddeen ya gaji ƙamshi da kuma yawan tsabta da ƙyanƙyami.      Koda ta gama  falo ta dawo, bayan tasamu sanya al'barka daga bakin  Ummi'n,  ganin Raliya  a kitchine yasa tayi  kitchine ɗin itama, nan  tashiga tayata aikin breakfast ɗin da takeyi, inda suke hira sosai.          
Koda suka kammala kuwa akan dinning suka jere komai, lokacin kusan ƙarfe 8 na safiya kenan, Ahmad ne ya shigo cikin falon, dai-dai lokacin kuma Ummi ta fito daga ɗakinta. 
   Cikin girmamawa Ahmad ya gaidata,  cikin kulawa, da kuma nuna ƙauna ta amsa masa.
Sosai tayi mamakin rashin ganin Saifuddeen a falon, dan kuwa tasan dayaje sallan asuba ya dawo, ita yake fara zuwa ya gaisar, amma saigashi yau bashi babu alamansa, abun dayaso ɗaga mata hankali kenan, dan tasan cewa idan Saifuddeen nada lafiya bazai taɓa kai warhaka baizo ya gaisheta ba, kuma kullum, koda yaushe, a irin wannan lokacin zaka sameshi cikin falon nata zaune.
Duban Ameena tayi cikin kulawa tace.
"Ameena waini kuwa yau ina Saifuddeen, anya kuwa yana lafiya?."
Kai Ameena ta sadda ƙasa, cikin sanyi tace.
"Yana ɗakinsa, tun safe yake kwance, zazzaɓi ke damunsa."

Cikin matsanancin damuwa Ummi tace.
"Subahanallah, zazzaɓi kuma, to yasha magani ne?."
Kai Ameena ta girgiza alaman.
"A'a"
Ahmad dake zaune ne yace.
"Nima nayi mamaki dan yau banganshi cikin masallaci ba, kenan ko sallan asuba bai samu yaje ba."
Kai Ameena ta jinjina alaman.  "Eh."
Cikin yanayin sanyi haɗi da tausayawa Ummi tace.
"Nidai nasan cewa hakanan Saifuddeen bazai taɓa kaiwa har iwar haka, batare da yazo ya ganni ba, rashin lafiya ce kaɗai zata ɓoyeshi, muje yanzu ki kaini sashin naku na duba shi."
Nan Ahmad da Raliya sukace suma zasu, Hayatuddeen da fitowarsa kenan, jin cewa zazzaɓi na damun hammansa yasa yaji gaba ɗaya hankalinsa ya tashi.
Nan suka bi Ameena zuwa part ɗin nasu.

Haryanzu kwance yake acikin blanket, dan kuwa zazzaɓin nasa bai ragu ba, saidai kuma ya farka daga ɗan baccin daya ɗaukesa.
Ahankali Ameena ta tura ƙofar ɗakin, kasancewar itace agaba.
Nan su Ummi suka rufa mata baya.
Ganinsa nannaɗe cikin bargo yasa Ummi ƙarasowa cikin sauri, hannu tasa taɗan ɗage blanket ɗin, hannunta takai ta taɓa goshinsa, jin an taɓa goshinsa ya sashi ɗan buɗe idanunsa kaɗan, dan duk atunaninsa mayyarsan ce Ameena. 
Ganin Ummi yasa shi ware idanunsa, tare daɗan yunƙurawa ya tashi ya zauna.
Cikin kulawa Ummi tace.
"Sannu Saifuddeen."
Kansa ya jinjina mata amatuƙar shagwaɓe, yana me kallon su Ahmad dake tsaye.
Kafaɗansa Ummi taɗan kama, cikin kulawa haɗe da tausayinsa tace.
"Sannu meke damunka ne?."
Sake shagwaɓe mata fuska yayi, cikin zuciyarsa yace.
"Bakune kuka matsa sai na auri wannan Ameenan ba, gashinan jiya duk ta tsotseni, ta rabani da samartaka na, ji yanda take wani wuƙi-wuƙi da ido, ko kunyana ma bataji." 
  a bayyane kuwa hannun Ummin nasa ya kamo, ya ɗaura akan wuyansa.
Nan Ummi taji jikin nasa zafi jau, cikin tausayawa ta dubesa, murya asanyaye tace.
"Zazzaɓine ke damunka ko, sannu, yanzu me kakeson ci, idan kaci sai kuwuce asibiti da Ahmad, dan nasan bakasha magani ba."
Kwaɓe fuska yayi tare da kamo hannun Ummin nasa ya sanya acikin nasa, idanunsa yaɗan lumshe, gane abun da yake nufi yasa Ummin riƙe hannunsa ɗaya cikin kulawa tace.
"Bayan zazzaɓin kuma saime ke damunka!."
haka take lallaɓasa kamar wani ɗan yaro.
Shikuwa kansa ya ɗaura akan kafaɗanta, inda yasa hannunsa ɗaya ya nuna mata waist ɗinsa ta baya, alaman bayan zazzaɓin nan ke masa ciwo, sannan kuma ya nuna mata jikinsa, alamun cewa gaba ɗaya jikin nasa ma ciwo yake masa.
Ɗan jim Ummi tayi tare da ƙuresa da ido, hakanan zuciyarta ta bata wani abu, ɓoyayyen murmushi ta sake, take wani irin daɗi ya cika zuciyarta, hannunta tasanya cikin gashin kansa, cikin yanayin kulawa tace.  
"Fine boy ɗina sannu ko, zakaji sauƙi insha Allah, sannan ciwon jikinma zai daina, yanzu faɗamin mekakeson ci, zan dafa ma da kaina."

Baki Ameena ta buɗe tana kallon Ummi da Saifuddeen ɗin, tunda take aduniya bata taɓa ganin ƙauna irin tasu ba, wannan salon ƙaunar tasu daban take, musamman idan akayi dubi da irin yanda Ummi ke shagwaɓa Saifuddeen, shikuwa indai yana gaban Umminsa jinsa yake kamar yaro ɗan shekara 3, saboda haka duk wata irin shagwaɓa ta duniya da taɓara ya iyata.
Ahmad  da Raliya kuwa murmushi kawai sukayi, dan sunsaba da ganin zallan shagwaɓan Saifuddeen da kuma yanda Ummi ke biye masa, Hayatuddeen kam waje yanema ya zauna.

Sake narkewa Ummin nasa yayi, asakalce ya kuma ƙara ɗaura kansa akan kafaɗanta, sai wani ɗan yamutsa fuska yakeyi, saikace wanda shi yayi aikin.
Kansa Ummi ke shafawa, duban Raliya tayi kana tace.
"Raliya haɗo masa tea, da kuma chips, idan yaci sai su wuce asibiti"

Hannun Ummin nasa ya kamo tare da girgiza kansa, cikin body language ɗinsa, yace.
"Fruit salad da maltina kawai yake da buƙata."
Dubansa Ummi tayi tare da sakin murmushi, nan tace da Raliya takawo masa maltina'n, idan yaso saita koma ta haɗo masa fruit salad ɗin.
Hakan kuwa akayi, maltina meɗan sanyi Raliya ta kawo masa,  Ummi dakanta ta ɓalle masa murfin maltina'n, ahankali yakai bakinsa tare daɗan lumshe idanunsa,  cikin ransa yace.
"Idan kuwa nasha naji ƙarfi ajikina, ya tabbata cewa wannan Ameenan ba sperm kaɗai ta zuga ajikina ba harda jinina."

Ɗago idon da zaiyi kuwa karab sukai ido huɗu da Ameena wanda ta ƙura masa ido, itakam sosai duk wani acting ɗin da zaiyi yake burgeta, yanzu ma haka ji take inama da ace ita yakeyiwa shagwaɓan nan ba Ummyn shiba aima itace matarsa itace ta dace da irin wannan abin da yakeyi.
Ɗauke idanunsa daga kallonta yayi, cikin ransa yace.
"Wallahi gudunki zannayi, hakanan da ƙuruciyata  bazan amince ki maidani tsoho ba, daga zuwa ɗaya har kinsani rashin lafiya, next kuwa inaga ko tashi bazan iya ba, da wani idanunki awajen ai kin san dai bani da lfy."
Yaƙare zancen zucin yana ɗan hararan gefenta.

Ahmad kuwa duk abun da Saifuddeen din keyi yana lure dashi, hakanan yasaki wani irin dariya, wanda yasa Saifuddeen ɗin watsa masa harara, cikin ransa yace.
"Ehem dole kayi dariya ae, tunda kafahimci cewa mayyar da kuka haɗani da ita, tun ba'ayi nisa ba tafara tsotseni." 
  Idanu Ahmad ya kashe masa alaman, yane?  laɓɓa SAIFUDDEEN ɗin ya ciza, tare da jinjina kai, alaman zasu haɗu ne.

Ummi kuwa murmushi take, dan tagama fahimtan komai, tabbas tasan cewa Saifuddeen baison wahala ko kaɗan, wannan dalilin shiyasa ma wata ƙila zazzaɓi ya sauƙar masa.
Yana gama shan maltina'n Raliya ta kawo masa, haɗaɗɗen fruit salad wanda yaji madara.
Balaifi ya ɗan sha, ya kuma ji daɗin bakinsa.
Dubansa Ummi tayi cikin kulawa tace.
"Kasamu kayi wanka, kuje asibiti likita ya dubaka, ko kuma ma zan ƙira Dr Adnan kawai yazo ya dubamin kai agida."
Tana gama faɗan haka ta miƙe tsaye, nan ta fice daga cikin ɗakin,  kana Raliya ma ta rufa mata baya.
Ahmad ma binsu yayi, Hayatuddeen kuwa hannun Hamman nasa ya kamo, cikin kulawa yace.
"Sannu My lovely Hamma Allah yabaka lafiya."
Kai Saifuddeen ya jinjina masa alaman "Ameen."
Nan Hayatuddeen ɗin ya miƙe yafice daga cikin ɗakin.

Ajiyar zuciya Ameena ta sauƙe, tare da takowa taƙaraso kusa dashi, zama tayi agab dashi, cikin kulawa ta kamo hannunsa,  fuskarsa ta shafa tare da cewa.
"Ya jikin naka?"
Kansa yaɗan jinjina mata, alaman.
"Dasauƙi"  tare da ɗan mako hannunta yayi kissing bayan hannun, sannan ya janye fuskarsa  baya.
Jawo wheelchair ɗinsa yayi ya hau, ahankali ya tura kansa zuwa toilet.

Ajiyar zuciya Ameena ta sauƙe, hartayi tunanin binsa cikin toilet ɗin kuma saita fasa,   nan dai tayi kwance akan gadon, lumshe idanunta tayi, tana me tuno moment dinsu na daren jiya, hannunta takai kan mararta, asanyaye tace.
"Ya Allah kasa adaren jiya nasamu rabo daga Saifuddeen, tabbas kuwa da sainafi kowa farinciki, domin samun iri daga Saifuddeen babban abun al'fahari ne,  sannan kuma zan zama kamar zara acikin taurari, dan haihuwa da Saifuddeen babban nasara ce, ya Allah kabani ɗa ko ƴa me kama dashi."
Cikin farin ciki ta amsawa kanta da "Ameen."

Saifuddeen kuwa balaifi yaɗanji dama, sake wanka yayi tare dayin brush, nan yafito jikinsa duk danshin ruwa, harzuwa lokacin Ameena na kwance, kasancewar wani ɗan bacci-bacci ne ke fusgarta.
Tsane jikinsa yayi, inda ya shirya kansa cikin wasu lafiyayyun riga da wando ƴan kanti masu tsadar gaske, sosai yayi kyau cikin kayan,  wankan turare yayiwa jikinsa,  wasu baƙaƙen toms yasanya aƙafansa, masu kamar combat, gashin kansa sai ƙyalli yake, wayansa ya ɗauka, nan yaƙaraso jikin gadon, ahankali yaɗan leƙa fuskar Ameena, gani yayi ma baccinta take cikin kwanciyar hankali.
Kansa ya jinjina tare da yin ɗan murmushi cikin zuciyarsa yace.
"Badole kiyi bacci ba, tun da dai daren jiya kinsamu ɗan bawan Allah kin gurza."  
tura kekensa yayi inda ya fice daga cikin ɗakin.

Cikin nutsuwa ya nufi part ɗin Ummin nasa, koda Ummi tagansa taji daɗi sosai, duk da cewa zazzaɓin baisakesa duka ba amma dai yaɗanji sauƙi, kwanciya yayi afalon, Ahmad dake zaune afalon ne ya matso kusa dashi.
Duban Saifuddeen ɗin yayi cikin ƙasa da murya yace.
"Ango kasha mai, to yaya yakaji auren da daɗi ko?"
Cikin takaici Saifuddeen ya ɗauki pillow'n kujera ya gwaɗawa Ahmad ɗin, dariya Ahmad yayi, tare da cewa.
"Daga faɗan gaskiya kawai, ai kuwa dai wannan amarya taka jaruma ce, saboda haka ka ƙara riƙeta da kyau, kaikuma saika tsaya adubaka,  saboda dai yanzu kam kafita sahun saurayi kadawo bazawari!."
Cikin tsokana Ahmad ya ƙare maganar, sanin cewa ya hasala Saifuddeen ɗinne yasashi matsawa gefen cikin sauri, dan yasan yanzu Saifuddeen ɗin zaikai masa duka.
Saifuddeen kuwa sosai ya ƙulu, hakan yasa yadinga cije laɓɓansa, yana hararan Ahmad, Ahmad kuwa mezaiyi inba dariya ba.
Suna haka Dr Adnan ya iso, dan Ummi taƙirasa, inda tasanar dashi matsalan Saifuddeen ɗin.
Sosai Dr Adnan din yayi checking dinsa, ganin komai lafiya yasashi, rubutawa Saifuddeen ɗin magunguna, nan ya miƙawa Ahmad yace "Yaje pharmacy ya sayo."  
bakomai yasa masa zazzaɓin ba kuwa face, yanayin daya samu kansa aciki wanda bai taɓa ba, hasali kuma hakan yafarune bawai don bashida lafiya ba,  ko wasu masu lafiyan sukan samu kansu cikin irin condition ɗin da Saifuddeen yasamu kansa,  musamman idan hakan yazama shine farkon fara sex ɗinsu, sannan hakan na faruwa idan Namiji yaɗauki tsawon lokaci yanajin sha'awa, sannan kuma bai samu yayi sex ba, to aduk lokacin da yayi sex da mace, yana zubar da sperm zazzaɓi  me zafi zai iya rufesa, wanda kuma zai iya sauƙa akowani lokaci.
Nan dai Dr Adnan yayi masa fatan sauƙi daga, haka yayiwa Ummi sallama ya tafi.
Cikin mintuna kaɗan kuwa Ahmad ya kawo maganin, shida kansa ya bawa Saifuddeen din magungunan yasha.

Haka dai Saifuddeen ya ƙare, gaba ɗaya wunin yau  a part ɗin  Ummin sa, ba laifi kuma yaji sauƙin jikinnasa sosai.           

Can cikin Gombe State University kuwa Hayatuddeen ne ke zaune acikin class, inda gaba ɗaya fiye da rabin ɗaliban ajin nasu ke waje, kasancewar sun ƙarƙare lecture ɗinsu na wannan ranan,   can ƙarshen benci yaje ya takure kansa, wayarsa ƙirar iphone 8+ ne ahanunsa, yayinda ya saƙala earpiece akunnensa,  gaba ɗaya yaba da hankali haɗi da nutsuwarsa ga wayarsa, da dukkan alama wani abu yake kallo wanda ya ɗauke masa hankali.           
Khamis dake tsaye akansa tun ɗazu batare da, Hayatuddeen din  yasan da zuwansa ba ne yasaki dariya, azabure Hayatuddeen ya ɗago kansa, ganin Khamis yasashi, sakin wata irin ajiyar zuciya me ƙarfi, aɗan hasale yace. 
"Mcheeww wallahi Khamis kai banza ne ji ka tsoratani."     
Murmushi Khamis yayi tare da zama agefen Hayatuddeen ɗin, hannu yasa ya dafa kafaɗan sa, dubansa yayi tare da cewa.   
"Kai wallahi tsoronka yayi yawa, menene to acikin BF da har ma sai ka ɓuya kake kallonsa, hmmm yaro inzakasha giya kasha ta dubu, kaine har yanzu kanka bai gama wayewa ba, har yanzu fa baka iya ko riƙe hannun mace, iya iskancinka ya ƙare a waya, daga anyi magana kace kai bazaka iya ba, mufa yanzu mune manyan gobe, yanzu ne ya kamata ace munci ƙuruciyar mu, mun shana, sannan muyi abun da mukeso." 
         
Iska Hayatuddeen ya fesar ta bakinsa,  girgiza kansa yayi tare da   cewa.                  
"Bazan iyaba Khamis, ni sam bazan taɓa iya aikata haka ba, insha Allah har duniya ta tashi bazan taɓa yarda nakusanci zina ba, kasan girman zunubin wanda ya aikata zina kuwa Khamis?  hmmm nikam dai ba ruwana, iskancina a iyaka waya ya tsaya kamar yanda ka faɗa da farko, amma taɓa jikin wata mace, wanda ba muharamma ta ba gaskiya bazan iya ba."     
Hararansa Khamis yayi tare da cewa. 
"Shiyasa nace bazaka taɓa wayewa ba, yanzu mene amfanin kallon BF matuƙar bazakanemi inda zaka gusar da sha'awan ka ba? hmmm nidai wallahi shanawa ma yanzu na fara ehe."     
Murmushi kawai Hayatuddeen yayi tare da playing vedio'n sa ya cigaba da kallo, yana mejin wani irin abu acikin jikinsa, sau dayawa yakanji kamar ya daina kallo, amma kuma zama da Khamis yasa kallon BF ya zame masa tamkar wani kallon film, yayi sabo da ganin BF sosai, saboda haka koda yace zai daina sai yaji ya kasa, duk da cewa yasan kallon BF din ba kyau, amma sosai idan yana kallo yakejin kansa cikin wani irin shauƙi, saboda  yanajin cewa shima yanzu yazama saurayi shekara 20 da yake dasu, sunsa yanajin kansa kaman ɗan 30 years.
Shida kansa yasan da taraiyar sa da su Imran tafi mishi daɗi da al'khairi to abin ta kaicin Imran F.C.E yake Sulaiman kuma da Isma'il Kashere University suke. Zakariyya kuma da yake nan cikin G.S.U ɗin sai kuma ya kasance Department ɗinsu ba ɗayaba, tofa wannan dalilin ne ya rabashi da tsoffin abokansa a makaranta ya haɗashi da wannan ɗan banzan khamis ɗin mai ƙafafu kamar faskaren wawa.

Wannan yana ɗaya daga cikin illar abokai, dole iyaye mu lura da abokan yaranmu muddin sun fara tasawa.
Zakiyi shekara 14 kina bawa ɗanki/ƴarki tarbiya mai inƙanci to. Tofa daga shekara 15 zuwa 18 akai ashirin zaki fara yaƙi da gasa da abokanshi da zasu fara bashi tasu tarbiyar da in kinyi sakaci da addu'a dasa ido cikin awa ɗaya zasu kore taki tarbiyar nan su ɗaura tasu, shike nan sunyi nasara a kanki sun cuci rayuwar yaronki damake kanki, hattara garemu iyaye mu kula...!

Tashi tsaye Khamis yayi tare da cewa. 
  "Saika tayi ae, kazauna nan a haka kada ka nemi ƙarin wayewa akan wanda kake dashi, ni kaga ma tafiyata, saboda yau ƙarfe 7 dai-dai muna da wani show me zafi a night club, nasan ma idan nace kazo ba zuwa zakayi ba."                  
Kai Hayatuddeen ya jinjina tare da cewa.       
"Saimun haɗe gobe, danni ma nasan driver ya kusa zuwa ɗauka na,  aje night club lafiya amman banda ni kam, bazanci amanar hamma da Ummynmu ba."       
Dukan wasa Khamis ya kai masa, sannan ya juya ya fice daga cikin class ɗin.                 
Bawani jimawa shima Hayatuddeen ɗin, sule driver yazo ya ɗaukeshi.                           

Ƙarfe takwas na dare dai-dai  yadawo daga masallaci, kaitsaye part ɗinsa ya wuce, kasancewar akwai wani aikin sirri wanda zai gabatar, domin ansashi binciken wani riƙaƙƙen ɗan fashi, wanda ya addabi mutane, sannan kuma har zuwa yau ankasa gano inda yake, saboda hakane ma aka danƙawa Saifuddeen ɗin ragamar case ɗin ahanunnsa, kasancewar sun san ya ƙware wajen iya computer, da computer kaɗai zai iya gano musu inda mutumin yake.          
Yana  shiga ɗaki kayan jikinsa ya soma ragewa, inda ya zauna daga shi sai 3 guater da kuma farar singlet, laptop ɗinsa ya jawo tare da sanyata  gaba, nan ya maida gaba ɗaya hankalinsa ga aikin da yakeyi.             

Da misalin ƙarfe 9 kuwa Ameena tashigo cikin ɗakin.    ganin cewa yana gudanar da aiki me mahimmanci,  yasa batayi ƙoƙarin damunsa ba, kan gado kawai ta ɗale tare da kwanciya, sama-sama taɗan latsa wayarta daga haka bacci ya ɗauketa, ko data'n ta dake akunne bata kashe ba.    
Shikuwa Saifuddeen har wajen 12 na dare yakai yana aikin bincike, cikin sa'a kuwa yagama haɗa duk wani information da yake so, dan kuwa ya gano inda mutumin yake, saida ya turawa ogansu komai kafun yake rufe laptop  ɗinsa, nan ya ɗauro alwala sannan yazo ya kwanta, ganinta haka bata rufe jikinta ba, yasashi rufa mata blanket, tare da gyara mata konciyarta, cikin mintuna kaɗan bacci ya ɗauke sa.      

Washegari kuwa ya tashi da ayyuka masu yawa akansa,  hakan yasa tunda ya fita daga gidan bai dawo ba sai wajajen 3pm,  nan ma dai part ɗin Ummi ya zauna.   Koda dare yayi ya tafi zuwa ɓangaren su, nan yasamu Ameena har tayi bacci, yaji daɗin hakan kuwa, don dama baiso ya isketa idanunta biyu, gudun kada ta ce zata ƙara neman wani abu daga garesa.              
Aikinsa ya ɗan taɓa kafun bacci ya ɗaukesa.       

Yauɗin ma dai baitashi da niyan zaman gidan ba, dan yanzu aikin nasa yaɗau zafi wani abun dole sai ya fita da kansa yaje ofishin sirri na DSS.  
Cikin nutsuwa yagama kimtsa wa, cikin wani lallausan yadi me kyau da tsada, yayi kyau matuƙa, Ameena dake tsaye tana kallonsa ne tasaki murmushi, tare da ƙarasowa kusa dashi,ido ya ɗan zuba mata ganin ta sunkuyo kanshi a hankali ta dai-daita fuskarsa da nata, batare da yayi  aune ba sai kawai jin bakinta yayi, acikin nasa tanayi masa tsosan sweet,  sam bai hanata ba saboda haƙƙin tane, saidai kuma baiwani biye mata ba, cikin mayen soyayyarsa ta ɗago idanunta ta kallesa, kallo ɗaya yayi mata yaɗan ɗauke kansa, murmushin yasakar mata tare da shafa gefen fuskarta, cikin body language ɗinsa yayi mata alama kan cewa.
"Saiya dawo."
Fatan al'khairi tayi masa, yana fita tafaɗa kan gado, tare da sakin ajiyar zuciya.       
Shikuwa  Saifuddeen saida ya biya ta wajen

Please Login or Register in order to submit comment