Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuwa tana murzawa ƙofar key, da gudu ta haura kan gado tare da shigewa cikin blanket, ƙam haka ta kulle idanunta gaba ɗaya jikinta karkarwa yakeyi, sai alokacinne ma tatuna da irin shigar dake jikinta, take wani irin abu ya tokare maƙoshinta, tashi zaune tayi tare da duban kanta, ganin rabin ƙirjinta awaje, yasa ta cije baki, cikin takaici haɗi da kishin kanta tace.
"Sam baicancanci yaga surata ba, wayyo ni maiyasama nafita ne?."
Tsuka tayi tare da komawa ta kwanta, baccin tsorone ya ɗauketa batare da ta shiryawa hakan ba.

Shikuwa Saifuddeen saida yasha artabu da jikinshi da zuciyarshi sosai kafun ya iya maida bacci.

Washe gari.
Kamar yanda takeyi tun da tazo gidan haka yauma tayi, tana gama idar da sallah tatafi ɓangaren Ummi inda tagaisheta.
Yau ɗinma Ummi cikin so da ƙauna ta amsa mata gaisuwarta,
a falo ta haɗu da Saifudddeen da Hayatuddeen bisa dukkan alamu daga masallaci suke,
cikin sakin fuska Hayatuddeen yace,
"Barka da safiya Aunty Zaleeha."
ɗan tsayawa tayi fuska a sake tace.
"Barka dai autan Ummi."
murmushi yayi tare da cewa.
"Ya amarci da gajiyan biki."
hararansho taƴi cikin sanyi ta ratsa gefen Hamma Saifuddeen ɗin harara ta cillamishi, sai kuma tayi wuf ta wuceshi kamar dai tsoro take kar ya cabketa
abinma dariya ya basu kana suka bita da ido.
daga ɓangaren na Ummi kaitsaye part dinsu ta  dawo, komawa tayi tanaɗe akan gado inda tacigaba da baccinta.

Acan gidan su Zaleeha kuwa sai jiya Mama tadawo daga tafiyanta da tayi, Baba Malam dai ko sannu baice da ita ba, koda ya lura cewa Zaheera bata gidan, tana can gidan Zaleeha, sosai ransa ya ɓaci, nanfa yasa Ya Ameenu Habu akan su kwashi kayayyakinta na aure da motocinta su kai maita kana su ɗauko Zahira sannan su ƙara yiwa Zaleehan nasiha inda yaje.
Hakan kuwa akayi, tuni Ya Ameenu da Habu sukatafi dan ɗauko Zaheeran bayan duk sun lodo kayan aurenta a motocintan.
Koda sukaje gidan nasu Saifuddeen sai Ya Aminun ya bawa Habu kuɗi yacewa Habu ya hau keke napep ya koma ya ɗauko motarshi su samu wacce zasu koma da ita tunda duk motoci biyun da suka zo dasu na Zaleehan ne ɗaya na cikin kayan aurenta ɗaya kuma wacce Ya Ahmad ɗinta ya saya mata,
Ya Aminu na fitowa cikin motar ya nufi wurin maigaɗinsu akan yaje ya mishi sallama da masu gidan a nan suka haɗu da Ahmad, inda suka gaisa cikin girmamawa da mutum ta juna, Ahmad ne yayi masa jagora har cikin gidan, saida Ya Ameena yafara zuwa ɓangaren Ummi tukunna, cikin mutum tawa ya gaida ta, sannan yayi mata bayanin cewa yazo ɗaukar Zaheera ne,  sosai Ummi taji daɗin karramata da yayi, nan tasake aminta da tarbiyan gidan Baba Malam ɗin, Ahmad ne yayiwa Ya Ameenu jagora zuwa ɓangaren Zaleehan, don kuwa Saifuddeen bayanan, sun tafi meeting ɗin ƙungiyarsu na Jonapwd shida Ishaq.
Sosai Zaleeha taji daɗin ganin yayan nata, saidai kuma jin cewa Zaheera yazo ɗauka, yasanya taɗan ɓata fuska, saidai kuma bata isa cewa komai ba, sanin cewa Ya Ameenun nada zafi sosai, babu ruwansa yanzu saiya solleta soso da sabulu.
Haka Zaheera ma ranta baiso ba, don dai kawai Ya Ameenun ne yazo da kansa, amma da wanine bazata bisa ba, don ita ke gadin Zaleeha a cewarsu a yadda suka tsara kenan wai ai duk nacinsa bazai zo inda takeba in Zahira nan kuma da ita aketa plant ɗin yadda Zaleeha zata gudu,

Haka dole ta haɗo kayanta, Gyara zama ya Ameenu yayi, cikin kulawa haɗi da kwantar da murya, yashigayiwa Zaleehan nasiha, dayi mata nuni akan tabi mijinta, idan ya umarceta da yinnabu matuƙar bai saɓawa shariya ba yace tayi to koda bataso tayi, domin hakan shine dai-dai domin al'jannarta na ƙarƙashin diga-diginsa .
Itadai Zaleeha jinsa kawai take, amma bata ɗauƙa, koda yazo tafiya har compound ɗin gidan ta rakosu,
nan kuma yasa Hayatuddeen da Imran dasu Zakariyya kwashe kayayyakinta kab suka shigar mata,
sannan ya bata car keys ɗinta duka biyu a hannunta, godiya tayi tare da cewa ya gaishe mata da Ƴar uwarta Maryam.
Haka Ya Ameenu yatasa Zaheera suka bar cikin gidan, shikansa ya yaba da tsarin gidan, musamman ma part ɗin Zaleeha wanda yayi matuƙar kyau, shida kansa ya ƙyasa, ya kuma yabawa Saifuddeen sosai, don bakowani namiji bane zai iya ɓarnatar da dukiyarsa wajen ƙawata gida mai kyau kamar haka ba.

Tafiyan Zaheera yasa Zaleeha duk taji gidan bayayi mata daɗi, hakanan taji komai ya tsaya mata, batasan dacewa motsin Zaheeran na ɗebe mata kewa ba, sai ayanzu da Zaheeran tatafi, haka ta koma ɗaki ta kwanta, zuciyarta cike da saƙe-saƙe kala-kala.
Tananan ƙule aɗaki har akayi sallan isha,
Nanfa wani irin tsoro yashiga diro mata, take fargaba ta cika zuciyarta, sam batajin zata iya kwana itakaɗai aɗakin batare da wani nata ba, sosai tsoron sa yashiga zuciyarta, tabbas ayanda taga cikin idanunsa jiya to idan tayi wasa komai zai iya aikata mata, abanza saiya rabata da virginty ɗinta, shikenan kuma daganan yagama cutanta, dan tasa aranta cewa bamakawa daga ranan daya yayi disvirgin ɗinta tofa shikenan itakam ta sallama rai da rayuwa, don baƙinciki ne zaiyi ajalinta tabbas.
Tashi tayi daga kan sallayan tare da kai dubanta jikin ƙofar ɗakin, ganin babu key ajikin ƙofar yasa gaba ɗaya hankalinta ya ƙara tashi,  atsorace tashiga neman key ɗin amma bata gani ba.
Ƙirjintane yatsananta bugu alokacin da taji motsin mutum a falonta.

Shikuwa Saifuddeen lokacin dawowansa kenan daga masallaci, kaitsaye ɗakinsa ya wuce, dan yanaso yaɗan watsa ruwa, kafun ya ya ɗa ci abinci.
Jin motsin buɗe kofar falonsa, dakuma rufewa yasanya taɗanji zuciyarta tayi sanyi, cikin hanzari ta ɗauki blanket da pillow, saikuma phone ɗinta, saɗab-saɗab tafito daga cikin ɗakin, ahanzarce tayi hanyar fita daga cikin falon, tana samun kanta aɗan compound ɗin shashin nata kuwa ta saki ajiyar zuciya,  kaitsaye garden ɗin dake cikin part ɗin nata ta nufa wanda yake cike da sanyi da sauraye, kan wata kujera dake ɗan cikin garden din ta kwanta, tare da jawo blanket ta rufa jikinta, ɗaura kanta tayi akan pillow tare da sauƙe ajiyar zuciya, ta dai gwammace kwana awajen da dai ta tsaya aciki ya illata mata rayuwa, zata jure komai amma bazata iya jure abinda zai iya mata ba, hakanan bata tsaya wani mugu yayi disvirgin ɗinta ba tunda ta duba ɗaya ɗakinma babu key sai tayi zaton shine ya zaresu dan karta rufe ƙofa ya samu damar shigowa ya mata fyaɗe injita da faɗi.

Raliya kuwa wacce tazo rufe window'n ɗakinta dake abu ɗe ne taga kaman wulgawan mutum ya shiga cikin garden, kanta tasake zurowa ta cikin window'n, nan idanunta suka gane mata Zaleeha dake ƙoƙarin kwanciya akan wata kujeran ƙarfe.
Mamakine yakusan  kasheta awajen, sosai abun ya ɗaure mata kai, komawa cikin ɗakin nata tayi ta zauna tare dayin jigum, me hakan yake nufi kenan? tsanar da Zaleeha tayiwa ɗan uwanta har yakai wanda zataƙi haɗa shumfuɗa dashi? har ta gwammaci kwana acikin sauro da ciyawi da sanyi a kan kujerar ƙarfe akan ta kwana dashi.
Kanta ta jinjina tare da rumtse idanunta wanda suka ciko da ƙwalla, sam bahaka ta ke wa ɗan uwannata fata ba, babban burinta shine yasamu ingantaccen kulawa daga wajen matar tasa amma meyasa Zaleeha ke gudunsa?
kwaffa tayi tare da cewa.
"Ko ya zakiyi wlh in sha Allah sai dai ya raɓi jikinki in Allah ya yarda duk iskancinki kin shiga hannu kenan mutu ka raba, ato sai yaci sadakinshi."
Tana faɗin haka sai kuma ta miƙe da sauri ta nufi.....!





Littafina na kune in kin ganshi a wojema na satane, turo ɗari 300 ta wannan no 09097853276 ko ka/kiyi min transfer'n 300 ta asusuna na 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa.




Wanda ya karanta na sata Yaseeeen doguwa.

By
*GARKUWAR FULANI*
10/4/20, 7:04 PM - Mmn Khalid: Cikin bedroom ɗin ta da nufin zataje ta sanarwa Ahmad,
ko meye ta tuna kuma, oho sai ta koma ta zauna tana nazari.
Sosai abun yayiwa Raliya ciwo, koda Ahmad ya fito ganin meya tsareta,  kamar zata faɗa masa saikuma tayi shiru, shi kuwa da bai san meke faruwaba sai janta yayi suka koma bedroom ɗinta dan yana tare da begenta.

Ɓangaren Saifuddeen kuwa kwata-kwata ma bai nemi Zaleehan ba, yana fitowa daga wanka kwanciya kawai yayi,  sam bayaso yaje gareta, harma yaga abun da zai rabasa da nutsuwarsa, dan shikaɗai yasan irin azaban dayasha jiya, saboda haka baya sake fatan shan wani azaban kalan wannan, kasancewar agajiye yake hakan yasa yana kwanciya bacci ya ɗaukesa.
Zaleeha kuwa gaba ɗaya tatakura akan kujeran da take kwance, sam kujeran bata da daɗin kwanciya bare daɗin bacci, cikin mintuna ƙalilan har jikinta yasomayi mata ciwo, gawani irin masifaffen sanyi dake busawa acikin garden ɗin, mutsutstsuka jikinta kawai takeyi, sosai takejin wuyanta ya ƙage amma kuma bata da wani zaɓi, wanda ya wuce yin haƙurin kwana awajen.
Atakure haka bacci ɓarawo yasamu nasarar ɗaukarta.

Ƙiran sallan asuban fari da akeyine ya ratsa jikinshi ya bashi lokacin salla yayi, ahankali ya buɗe idanunsa,  ɗan miƙa yayi tare da haɗawa da salati a zuciyarsa, nan yatashi zaune, kekensa ya jawo tare da hawa kanta, cikin nutsuwa da ɗan sauran kasalan bacci yakai kansa banɗaki, wanka yayi tare da ɗauro alwala, kaitsaye yafice daga ɓangaren nasa.
Har yaƙarasa jikin ƙofar na Zaleehan saikuma wani tunani yazo masa, take yafasa shiga tada'ita da yayi niyya, sai ya ƙonƙasa mata ƙofar, kana ya juya ya tafi,
kai tsaye yawuce masallaci.

Zaleeha kuwa dama gaba ɗaya batayi wani ishashshen bacci ba, dan sanyine awajen sosai, jin motsi alaman cewa yatafi masallaci yasata tashi zaune, cikin sauri ta ɗau bargon haɗi da pillow'n ta, ahanzarce tanufi ƙofar falon nata, dai-dai lokacin Ahmad yafito daga ɓangarensu dan zuwa masallaci, idanunsa ne suka gane masa Zaleeha, fuskarsa ɗauke da ɗan mamaki yabita da kallo, ganin fitowarta daga cikin garden gashi hannunta riƙe da bargo da kuma pillow alamun nan ta kwana kenan yasanyashi girgiza kansa, cikin ransa yace.
"Allah Ya shirya ki, ae dama mai hali baya taɓa fasa halinsa, saidai in ba'a zauna ba kuma dai duk tsaurin wayon amarya to wlh sai ansha manta anci sadaki an suɗe ki dai gama ɓoye-ɓoyenki."
Nan yawuce masallaci.
Itakuwa Zaleeha sam-sam ma bataga Ahmad ɗin ba, kaitsaye ɗakinta ta wuce, cikin hanzari tasoma rage kayan jikinta, ruwan ɗumi ta haɗa inda tayi wanka, tana fitowa daga wankan ta zura wata farar jallabiya mai kyau,  hijab tasanya tare da ta da sallah, koda ta idar da sallan bata tashi akan sallayan ba saida tayi azkar, nan ta ɗauko ɗan ƙaramin Qur'aninta tasoma karatu,  ba'ita ta rufe Qur'anin ba saida taga gari yaɗan somayin haske,
wasu bedroom slippers masu kyau ta zura aƙafafunta, inda tasake feshe jikinta da turare me daɗin ƙamshi.
Koda tafito daga ɓangaren nasu kai tsaye part ɗin Ummi ta  nufa, bakinta ɗauke da sallama haka ta kutsa cikin falon, wanda ke cike da jama'a, Raihana ne da Saminu waƴanda zasu koma Kaduna asafiyar ta yau, saikuma Goggo Dada da Aunty Meena wanda zasu koma Dukku, Aunty Rahama ma yau zata koma, don tunjiya Dr.Adnan keyi mata waya, kan cewar yayi kewarta gashi weekend  yana gida shiyasa yace zaizo da safen ya ɗauketa.
Cikin yin ƙasa da kai haɗi da nuna tsantsar ladabi taƙaraso cikin falon,  har ƙasa ta durƙusa inda ta gaishe da Ummi, cikin fara'a haɗi da sakin fuska Ummi ta amsa mata gaisuwan nata, tare da miƙo mata hannu ta kamo nata, cikin kulawa Ummi tace.
"Taso kizonan kusa da Umminki yarinyar kirki, kema ai ɗiyatace, tunda kika shigo cikin mu kuwa kinzama jininmu."
Tasowa tayi daga inda take tare da ƙarasowa kusa da Ummi,
Ummi ne tajawota inda ta zaunar da ita agefenta, sadda kai ƙasa Zaleeha tayi tana murmushi, hakanan itakam Allah ya samata son matan aranta, sosai take ganin ƙima da kuma darajan Ummi'n,  su Raihana ne suka gaishe da Zaleehan, amatsayinsu na ƙannen Saifuddeen,  haka ta amsa musu fuska asake, ɗan zamowa ƙasa tayi inda tagaishe da Goggo Dada dakuma Aunty Meena, sai kuma babbar yaya wato Adda Rahama, da kuma Saminu wanda ke zaune gefen Saifuddeen, da fara'a akan fuskarsu duka suka amsa gaisuwar nata,  komawa gefen Ummi tayi ta zauna a ƙasan carpet dan tana matuƙar ji da ganin darajar Ummi, shiru tayi yayinda ko kallon inda Saifuddeen yake batayi ba, shikuwa har acikin ransa mamakin irin tsantsar ladabinta ga ƴan uwansa yake, tanason kowa acikin ahalinsa tana mutuntasu da girmamasu, amma wato shine marainin wayonta sam bata ganinsa da gashin ido, murmushi yayi wanda  shi kaɗaine yasan ma'anonin murmushin ransa yace.
  tabbas kuwa zanyi maganinta ne, very soon zankashe bakin tsiwan, badai ni ta raina ba?."
hmmm yasha alwashin duk randa ya kamata kuwa zataji ajikinta.

Saminu ne yace da Raihana su hanzarta sutafi, bayason tafiyar da bata safiya ba, saboda alokacinne yakejin karsashi ajikinsa, nan kowa yatashi don yi musu rakiya zuwa compound ɗin gidan, ciki kuwa harda Zaleeha wanda ta kamo hannun Daddy yaron Bappa Ali wato Junior mai sunan Abbandu Saifuddeen kenan,  kasancewar yaron kyakkyawane yasanya sosai yashiga ranta, gashi nan da wayonsa irin yaran nanne masu shiga zuciya, haka suka fito compound ɗin gidan inda yaketa zuba mata surutu, itakuwa murmushi kawai take tayi masa, har bakin mota suka rako su Raihanan, nan sukayi sallama da juna, cikin yanayi na tsokana Raihana ta dubeta, tare da cewa.
"Kikulamin da Hammana da kyau da kyau, dan ko ƙuda bama son ya taɓa manashi."
Dariya sukayi gaba ɗayansu,
itakuwa Zaleeha ɗan guntun murmushi tayi, yayinda taji wani malolon abu ya tokare maƙoshinta, cikin zuciyarta tace.
"Lallai kuwa zai mutu, indai nice zan kula dashi!.
Yo ni me haɗina dashi kunamai ma su sauƙa ajikinsa mana ba ƙuda ba ni me yadameni."

Motar su Raihana baigama fita daga gidan ba saiga Dr.Adnan nan shima yazo ɗaukar matarsa, nanfa suka gaisa, inda Zaleeha tagaishesa cikin mutuntawa,  Farouq da Adam kuwa sai tsalle suke dan sunga babansu, duk girmansu baigani ba haka yasasu ajikinsa,  babu yanda basuyi ba akan cewa Daddy yazo su tafi ba amma yaƙi,  waishi ala dole yasamu sabuwar Aunty yace shi Dukkunma bazai komaba, kusan saida yabawa kowa dariya haka suka tafi anata raha.
Daddy kuwa da ƙyar  suka iyayi masa wayo yabi iyayen nasa da karatunshi,  Ahmad ne yazo da motarsa wanda dama shine zai mayar dasu Goggo Dada gida, lokaci ɗaya fa gaba ɗaya jama'an baƙin biki  suka watse gida yayi shiru.

Ummi Raliya da kuma Zaleehan kawai aka bari, dama Saifuddeen yana part ɗin Ummi, kasancewar shi baifito rakiyan ba, shikuwa Hayatudden sarkin bacci, yanacan tun dawowansa daga sallan asuba daya koma bacci shine haryanzun baitashi ba.

Direct Zaleeha part ɗinta ta koma, inda su Ummi da Raliya suka koma wajen Saifuddeen.

Tana shiga cikin ɗakin nata ta cire hijabin dake jikinta, kan gado ta faɗa tare da ɗan lumshe idanunta, sosai takejin wani sabon bacci naƙoƙarin ɗaukarta.

Can ɓangaren Ummi kuwa, Saifuddeen naganin dawowansu, ya sakawa Ummin nasa shagwaɓa, sanin halinsa na sakalci kaman wani ƙaramin yaro yasanya Ummi da kanta tashiga kitchine inda ta haɗa masa coffee, sosai yaji daɗin haɗin coffee ɗin da Ummin tayi masa, ɗaukan mug ɗin yayi tare da bar musu falon, kai tsaye yanufi sashinsu.

Saifuddeen nafita, Ummi tayi murmushi cikin jin daɗi tace.
"Allah kenan maiyin yadda yaso a lokacin da yaso, kafun auren nan kowa yasan cewa yarinyar nan bason auren nan take ba, amma yanzu cikin ƙuduran Allah gashi suna zaune lafiya, kinga ta saki ranta."

Murmushin gefen baki Raliya tayi tare daɗan muskutowa, cikin jimamin abun dake damun zuciyarta tun daren jiya tace.
"Hmmmm hakane kam Ummi, amma nikuwa jiya naga abun daya ɗauremin kai ya bani mmki, dan nima da fari da naga ta saki ranta naji daɗi."
Dubanta Ummi tayi tare da cewa.
"Mene kuma yafaru?."
Gyara zama Raliya tayi tare da cewa.
"Ummi kinsan kuwa cewa jiya awaje cikin garden ta kwana? wallahi Ummi abun yabani mamaki sosai, inata tunanin dalilin da zaisa ta kwana cikin garden, idan har zatana gudunsa haka, meyasa ta amince da aurensa?."
Cikin matsananci mamakin jin maganan da Raliyan ta faɗa Ummi ta sauƙe wani irin ajiyar zuciya, jiki amace tace.
"Raliya kin tabbatar da abun da kike faɗa kuwa?."

Kai Raliya tajinjina tare da cewa.
"Wallahi Ummi da idanuna naganta jiya a garden ta kwana, kuma koda natashi sallan asuba dana leƙa naganta, alokacin tana ƙoƙarin barin wajen, kuma tabbas nasan babu makawa itace dan Abban Farida ma ya ganta dayazo tafiya masallaci."
Ɗan jim Ummi tayi tare dajinjina kanta, take taji zuciyarta tayi mata wani irin ba daɗi, hankali ya tashi fargaba ya cika mata zuciya wato har ƙiyayyar ta kai haka, jiki a mace tace.
"To Allah dai ya kyauta."
Amin Amin Raliya ta amsa jiki a mace.

Haka dai zaman yaci gaba da gudana har tsawon kwanaki, Kullum  in gari ya waye Zaleeha na idar da salla zataje ta gaida Ummi a mutunce, lokuta da dam takan samu Saifuddeen a wurin Ummi, amman tsakaninta dashi sai harara da murguɗa baki,
tana son kowa na gidan yayinda suma duk suke matuƙar sonta musamman Raliya da takanje har ɗakin Zaleeha su ɗanyi hira,
dan itacema ta tayata shirya tarin akwatunan kayan aurenta da kimtsa mata duk abinda zata buƙata a durowa, sauran akwatunan suka kaisu ɗaya ɗakin,
Hayatuddeen kuwa dama akwai sabo a tsakaninta haushinta da yaji kan cewa da tayi bata son Hammanshi yanzu babushi tunda yanaga har ta yarda da auren ta zauna lafiya dashi.
tana matuƙar girmama Ummi wanda hakan yasama mata soyayya a idanunsu,
tana mutunta Ahmad a cewanta mai sunan yayanta ne dan Yaya ma take kiranshi tun tana gaidashi yana amsawa a yatsine har dai ya fara ɗan sasaautawa.

Har yau kuma a woje take kwana cikin gardin,
wannan abun shine yasa Ahmad yake matuƙar jin baƙin cikinta,
shi kuwa Saifuddeen  da fari baisan bata kwana a ɗakintaba dan baya shiga kuma da safe yana ganinta a wurin Umminshi,
To tun shekaran jiya daya dare ya ankara da bata ɗakin, ya dudduba ko ina na cikin part ɗin nata babu ita ba dalilinta, falonshi ya koma wayarshi ya ɗauka tare da yin mgnar zuciya,
"To ina take zuwa ta kwana yau kwana biyu kenan bata kwana a nan."
Kanshi ya ɗan jingina da jikin kujerarsa tare daci gaba da mgnar zuci.
"To waya sanima ko ta daɗe da barin kwana a nan."
sai kuma yayi ajiyan zuciya tare da cewa.
"ko dai part ɗin Ummi take kwana? kai Anya kuwa Ummi zata barta ta kwana a side ɗinta,
to ko dai part ɗin Raliya take kwana."
Text ya rubutawa Ahmad,
"Kayi bacci ne?."
Ahmad da ke zaune a falo shida Raliyya suna mgnar Zaleeha dan hango wucewarta da sukayi,
murya a sanyaye Raliya tace.
"To wai ko dai Hamma Saifuddeen bai san bata kwana a ɗakinba?."
Ajiyan zuciya Ahmad ya sauƙe tare da cewa,
"Ina zaton bai saniba, kinfa san shi da miskilanci, in kuwa yasan bata kwana a cikin to yasan inda take kwanan shiyasa bai kulataba ai jiki magayi."
da sauri ya ɗago wayarshi ganin saƙon Saifuddeen ne ya sashi cewa.
"To ina ga dai bai san bata kwana cikiba sai yanzu dan ga text ɗinshi wai nayi bacci ne."
ido Raliya ta zuba fuskar wayarshi tana ganin amsar da yake rubuta mishi.
"A a banyi bacci ba, lfy dai ko?."
jim kaɗan sai ga wani saƙon.
"To lafiya dai zance,amman Zaleeha na wurinku ne?."
murmushi Ahmad yayi tare da cewa Raliya,
"Hmmm zanyi mgnin yarinyar nan."
sai kuma ya rubuta mishi amsa.
"A a Zaleeha kuwa, bata nan."
a take sai ga wani saƙon.
"Kasa Raliya ta dudduba nan wurinku, taje Side ɗin Ummi ma ta duba ko tana can."
yana gama karan tawa yace.
"Lafiya dai kam ko?."
tsaki Saifuddeen ya ɗan ja kana ya rubuta mishi,
"Nima ban saniba lafiya ko ba lfy ba, ina dai zargin yarinyar bata kwana a gidan nan, dan tun shekaran jiya na lura babu motsinta, sannan yanzu na dudduba ko ina bata ciki side ɗin."
cikin nuna fargaba Ahmad yace.
"Innalillahi, to ina take zuwa ta kwana, gani nan fitowa."
sai ya kuma miƙe ya kalli Raliya tare da cewa,
"Maza kije side ɗin Ummi ki gaya mata, ana neman Zaleeha ki kuma ce karta nuna tasan inda take kwana zanyi mgninta."
to tace tare da juyawa ta nufi side ɗin Ummi,
kana shi kuma Ahmad ya nufi ƙofar falon Zaleehan nan yayi kicibis da Saifuddeen daya fito,
"To wai ina ta shigane, mufa mun dudduba wurinmu babu ita."
kai ya jujjuya mishi alamun shimafa ya dudduba wurinsu babu ita.
dai-dai lokacin kuma Ummi da Raliya suka iso, nan fa suka haɗu suka nuna basu san inda takeba.
ita kuwa Zaleeha tun fitowan su Ahmad ta buɗe ido,
jin ita ake nema yasa ta zame a hankali ta konta a ƙasan kujerar fulawi ke zagaye da ita.
Ahmad kuwa yana hangota hakan ya sashi cewa.
"Hmmmm zaki gane kurenki."
wayarshi ya zaro lallatsata yayi ya nemo number Ya Aminu,
ya kirashi kana ya kara wayar a kunnenshi.

Can cikin bacci Ya Ameenu yaji wayarshi nata suwa,
a hankali ya ɗan zare Maryam daga jikinshi,
hannu yasa ya ɗauki wayar time ya duba ƙarfe ɗaya na dare.
"Ahmad kuma a daren nan lfy kuwa?."
sosai yaji fargaba ,kar dai Zaleeha nacan na tarfa musu rashin ɗa'a, jiki na rawa ya amsa kiran cikin sauri yace.
"Salamu alaikum ,Ahmad lfy kuwa?."
cikin nuna tashin hankali yace.
"Ya Ameenu Zaleeha ce bamu ganiba mun nemata ko ina a gidan babu ita ba dalilinta,
kuma Saifuddeen yace tun shekaran jiya bata kwana a side ɗinsu,
to sai yayi tunanin wai ko side ɗinmu take shigowa ta ɓuya ko na Ummi,
to shine yanzu ya sanarmana zatonsho tana wurinmu,mun duba kab gidan bata, nan shine nace bari in kiraka ko ta dawo gidane?."
cikin kaɗuwa Ya Ameenu ya miƙe tare da cewa.
"Zaleehan to ina take zuwa?."
a taƙaice Ahmad yace.
"To ko tana gida ne?." rai a ɓace Ameenu yace.
"Kai anya kuwa sam bata gida, to ina take zuwa ta kwana, yi haƙuri bari in kira Baba malam."
to Ahmad yace kana ya katse kiran sannan ya gaya.musu yadda sukayi da Yayanta Ameenu,
kana yace su shiga ciki kafin Ameenun ya kirashi.

Shi kuwa Ya Ameenu wani irin tashin hankali ne da ɓacin raine mai tsanani ya rufeshi to ina Zaleeha take zuwa ta kwana ina take tafiya ta bar ɗakin mijinta me haka yake nufi?
kiran Baba Malam yayi bawan Allah yana zaune bisa sallaya yana karatun qur'an kiran Ameenu ya shigo wayarshi,
har wayar ta katse bai ɗaukaba duk da yaga Aminune so yake yaje ƙarshen surar Arrahaman da yake karantawa,
yayinda wani fargaba ya rufeshi lfy kuwa kira da tsakiyar daren nan.
Yana zuwa ƙarshen surar kira na uku na shiga wayar, da hamzari ya amsa kiran,
"Barka da dare Baba Malam kayi haƙuri na tada kai daga bacci."
Ameenu ya faɗa a ladabce,
murya a ɗan harɗe Baba Malam yace.
"Ameenu lfy kuwa meke faruwa?."
cikin sanyi Ya Ameenu yayi mishi bayanin da Ahmaɗ yayi mishi, ya ƙara da cewa.
"Ko dai ta taho gida ne?."
lumshe ido Baba Malam yayi yana jin wani irin suya da zuciyarshi keyi me Zaleeha ke nufi zubda mishi mutunci da kima  a idanun mutane ko?
a hankali ya cewa Ameenu.
"Ameenu bana zaton tana cikin gidana ,bazata zo nanba, amman dai bari in bincika."
to Aminun yace kana y katse kiran.
shi kuwa Baba Malam fitowa yayi da kanshi yayi tabin luggu da saƙo na gidan ya duba ko ina kab babu ita, koda ya titse Mama da tambayar ina Zaleeha ke zuwa ta kwana,
rantse-rantse tayi ta mishi akan ita bata san ina Zaleeha ke zuwa ta kwanaba.
a daren Ameenu ya kira goggonsu Maryama da duk inda suke zaton zataje ko ina sai ace musu bata zoba.

Wannan abu yayi matuƙar tada hankalin Baba Malam ya Ameenu kuwa ji yake in yaga Zaleeha zai kusan karta,
dole ya kira Ahmad yace,
wlh bata wurinsu amman tunda da safe tana dawowa zai zo ya sameta, har ɗakinta.

Da  wannan kowa ya koma ɗakinshi, Ahmad kuwa ranshi ƙal yasan Zaleeha zata gane kurenta.

Washe gari kamar yadda ta saba, suna tafiya masallaci ta koma ɗakinta wonka tayi da ruwan ɗumi wai ko tsamin cizon sauro da  jikinta keyi zai ragu, wanka da al'wala tayi,
kana ta fito tazo tayi salla koda ta idar  azkar tayi sanan ta miƙe ta kimtsa jikinta cikin wata doguwar rigar mai ɗan karen.kyau wanda duk na kayan aurene, da mayafinshi ta yane kanta ,kana ta nufi sashin Ummi.
a falo ta samesu, dukansu, cikin nitsuwa ta isa gaban Ummi dake mata murmushi tare da cewa.
"Gari ya waye ko ɗiyata?."
murmushi tayi tare da rusunawa gaban Ummi cikin ladabi da sanyin

Please Login or Register in order to submit comment