Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sauraranta ba, domin yariga dayasan ko awajen Allah bashi da wani laifi, tunda dai bai aikata ba dai-dai ba. Blanket ya ja ya rufa ajikinsa, tare da lumshe idanunsa. Ameena kuwa ganin yanda yayi kwanciyarsa ba tare da ya kara ce mata komai ba, yasa taji gaba ɗaya ranta ya ƙara ɓaci, can nesa dashi ta matsa tare da jawo Adeel jikinta.

Saifuddeen kuwa dama baji yake ba, kuma gashi ya bata baya, hakan yasa baimasan tanayi ba, dan baccin gajiya ne ma keneman ɗaukarsa.
Saida tayi kuka sosai kafun take maida ajiyar zuciya, jitake inama da ace Zaleeha bata dawo gidan ba, inama da ace Saifuddeen baikasance mijin Zaleeha ba, da duk hakan baifaru akanta ba, dan tanajin zata iya jure kishi da kowacce mace amma banda Zaleeha, ta jima sosai tana sheshsheƙan

Washegari da asuba kuwa antashi da ruwa, hakan yasa bai samu zuwa masallaci ba, nan cikin toilet ya shiga ya ɗauro alwala, tare da shumfuɗa darduma ya tada sallah.
Itama Ameenan miƙewa tayi, ta shige toilet ruwa ta ɗan watsa ajikinta, saboda ta tashi taji zuciyarta wasai, acikin kaso ɗari na damuwarta kaso saba'in ya ragu, hakanan taji cewar abun da tayi masa daren jiyan bata kyauta masa ba, sauda dama takanyi regreting abubuwan da takeyi mai, dan kuwa ita kanta tasan baiyi mata laifin komai ba hakama Zaleeha bata tare mata komai ba, kawai dai zafin kishi ne ke ɗawainiya da ita wanda kuma tana addu'an ALLAH ya yaye matashi tajin son Zaleeha koda al'barkacin son da takewa Adeel, nan kusa dashi ta shumfuɗa wani darduman, tare da ta da sallah, zuwa lokacin kuwa shikam ma harya idar, zaune yake akan guiwowinsa, yana gabatar da azkar, yana nan azaune harta idar da sallan itama azkar ɗin tayi, sannan ahankali ta ɗago ta kalleshi, gaba ɗaya jikinta asanyaye yake, ga kuma wani irin fitinannen ƙaunarsa da kuma sha'awarsa da takeji, hannunta takai ta dafa kafaɗansa, sarai yajita amma sai yayi kaman ma baisan tanayi ba, ganin haka yasa ta dawo gabansa suna fuskantar juna, ganin yana kallonta yasa taɗan sunkuyar da kanta, asanyaye tace.
"Ina kwana."
Kansa ya jinjina mata alaman.
"Lafiya." ƙoƙarin hawa wheelchair ɗinsa yasomayi, ganin haka yasa ta faɗa jikinsa, cikin sanyin guiwa tace.
"Dan Allah Abban Adeel kayi haƙuri, nima bansan meyasa nakejin wasu abubuwa akanku wani lokaci ba, kasan inasonka wannan dalilin yasa nakejin kishinka sosai araina, amman in sha Allah zan bari dan nacewa Mamana taita min Addu'a Allah ya yaye min kaima kaita min Addu'a kuma nima inayi." Idanunsa ya zuba mata, shi mutum ne me saurin fahimta da kuma uzuri, musamman ma ita da yasan cewa kishine ke ɗawainiya da zuciyarta. Ɗan lumshe idanunsa yayi, tare da jinjina mata kai alaman.
"Shikenan komai ya wuce."
murmushi ta sakar masa tare da sake shigewa jikinsa, bakinta har rawa yake haka ta shiga kissing ɗinsa tako ta ina, sam bai hanata ba, dan baiso ya tauye mata haƙƙi, jikinta na rawa haka ta taimaka masa ya kwanta akan gado, bin bayansa itama tayi, tare da haɗe jikinsu waje ɗaya.
Duk wani abun da takeso baiƙi yi mata ba sabida shima yana buƙatarta, haka ya bata duk wani haƙƙinta dake kansa, after 22 minute gaba ɗaya jikinsa yayi weak, gajiya ne keta damunsa, da ƙyar ya iya tashi yayi wanka, fita yayi inda yaje ya gaishe da Umminsa, yana dawo wa kuwa nan kan gadon ya kwanta yana me da numfashi, ahaka har bacci ya ɗaukesa.
Ameena kuwa jin ranta take fari ƙal, wani annushuwa takeji acikin ranta, koda ta fito daga wankan, mai kawai ta shafa sannan ta yiwa Adeel wanka, saida ta fara shirya Adeel ɗin, kafun ta shirya kanta cikin kayanta na zuwa aiki.
Ganin Saifuddeen ɗin na bacci ne yasa taɗan ranƙwafo tare da yi masa kiss agoshinsa, Adeel na ɗauke akan kafaɗanta ta fice daga cikin ɗakin, kaitsaye sashin Ummi ta nufa, anan falo ta iske su azaune, yayinda Zaleeha ke zaune anan ƙasan sofa, tasha kyau cikin simple riga da sket ɗin dake jikinta, anutse ta gaishe da Ummi sannan Zaleeha ta miƙa hannu ta amshi Adeel, yau ko breakfast ma bata tsaya tayi ba, saboda taɗan makara.
kuma tana son yau ɗin ta keɓe da ƙawarta, Samira tasan zata ƙara kwantar mata da hankali kuma zata bata shawarwarin yadda zata samu ta yaƙi wannan zazzafan kishin ta zauna da ƴar uwarta lfy.

Saifuddeen kuwa sosai yayi bacci, dan bashi ya farka ba sai wajajen ƙarfe 10, bathroom ya shiga ya sakeyin wanka sannan ya kimtsa kansa cikin, wasu haɗaɗɗun riga da wando, sai baza ƙamshi yake haka ya nufi sashin Ummi, dan yunwa yakeji sosai.
Ummi ce da Zaleeha kaɗai zaune afalon, Ummi nakan kujera, ita kuwa Zaleeha tana ta kaikoma acikin falon, sai faman jijjiga Adeel dake kuka yake,
shigowarsa cikin falonne yasa Ummi cewa.
"Yauwa gama babansa nan, Zaleeha miƙawa babansa shi ko zaiyi shiru, tun ɗazu ya cikamu da ihu, bansan meke damunsa ba, bacin kuma ƙiwa ba halinsa bane." Ɗan kallon Saifuddeen ɗin Zaleeha tayi, sai kuma ta sadda kanta ƙasa.
Shikuwa ahankali yaɗan lumshe kyawawan idanunsa da suka sauƙa akan haɗaɗɗiyar surar jikinta, hips ɗinta wanda ya cika sket ɗin jikinta, yayi masifar kyau da tsaruwa yake kallo, jiyayi tsikar jikinsa sun mimmiƙe, asanyaye Zaleeha ta karaso inda yake, ɗan sunkuyawa tayi daniyar ajiye masa Adeel ɗin akan cinyarsa, hakanne yasa beautyful breast ɗinta suka ɗan bayyana ta saman wuyan rigar, ganin kyawawan saman breast ɗin nata yasa yaji wani abu na yawo ajikinsa, wajen miƙa masa Adeel ɗin ne kuwa, hannunta ya gogi nasa, take sukaji wani irin shock, hakanne yasa cikin sauri ta zare hannunta tare da komawa gefen Ummi ta zauna,
ɗaga Adeel ɗin yayi yana yi masa wasa, take kuwa yaron yasoma sakin murmushi, harma da ɗan dariya,
Ummi ne tace.
"Kuji ja'irin yaro, wato yaga Babansa shine harda dariya, dama kenan mu kakewa ƙiwa." Murmushi kawai Saifuddeen ɗin yayi, yana riƙe da Adeel ɗin, ya ƙarasa dinning area, ganin haka yasa aɗan kunyace Zaleeha ta tashi, ta ƙarasa dinning table ɗin, cikin nutsuwa take seving ɗinsa haka nan take jin kamar ta zauna kusa dashi, shikuwa idanunsa ya zuba mata, dan sosai tayi masa kyau, yau ɗin zallan yarintarta ya bayyana sosai, gashi kayan jikin nata sunyi mata cif-cif, har gabansa ta kawo masa plate ɗin abincin, ɗan ɗagowa tayi, hakanne yasa idanunsu sarƙewa acikin na juna, rolling eyes ɗinsa yayi, take taji wani irin yaarrr yaarrr ajikinta, saboda yanda abun ya ƙarawa fuskarsa kyau, wani irin kallon shauƙin daya bita da shine yasa, takusa yin tuntuɓe wajen barin dining area'n,
wani ƙawataccen murmushi ya sake, tare da ɗauke kansa ya maida hankali kan abincinsa. Nan kusa da Ummin ta dawo ta zauna, suna ɗan taɓa hira da Ummin, har ya kammala cin abincin, koda yazo fita, akan cinyanta ya ajiye Adeel ɗin, sannan ya fice. Yana fita kuwa Adeel yasa musu kuka, haka suka dinga rarrashinsa ita da Ummi, saida yayi bacci kafun suka samu salama, Zaleeha kam tuni kukan Adeel din ya ruɗata, har tanajin ƙwalla sun cika idanunta, sam batason kukan Adeel ɗin.

Saifuddeen kuwa yana fita daga part ɗin Ummi'n, kaitsaye gidan ya bari, dan suna da meeting ɗin da zasuyi.

Adeel kuwa wunin yau gaba ɗaya kuka ya dinga musu, da ƙyar suke iya rarrashinsa.

Ameena kuwa yau da wuri suka tashi, a hankali suke tafiya ita da ƙawarta Samira, har suka iso bakin harabar inda suke aje motocinsu, shiru Ameena ta ɗanyi tare dacewa Samira.
"Yau baki fito da motarki bane?".
Murmushin Samira tayi tare da cewa.
"Eh yau a napep nazo, ƴar uwatace motarta na wurin gyara, kuma sunada biki a danginta, shiyasa na bata nawan".
Cikin fidda numfashi Ameena tace.
"Uwar gidanki ko?".
Kai Samira ta gyaɗa mata alamar eh,
cikin sanyi Ameena tace.
"Kinji dadi Samira inamw ace nima Allah zai yaye min kishi in samu in saki jikinda uwar gidana, dan wlh ita dai irin kice."
Murmushi Samira tayi tare da cewa.
"Uhum Ƙawata ai abin mai sauƙine muddin kika sauƙaƙawa kanki to Allah zai sauƙaƙa miki in kuwa kika tsananta wa kanki zakisha wuya, ni da uwar gidana wlh ko ƴan uwa sai haka, bamu da matsalar komai sabida mun sawa ranmu haƙuri, bawaifa bama kishin bane, no ai kishi kumallon matane, amman kishinmu mai tsari mukeyi, ina gaya miki ki saki ranki da abokiyar zamanki zakuji daɗin zama, tunda keda kanki kin shaida min ita bata da kishinki asalami ke gani kike wai kamar bata son mijin nakune, to wlh Ameena bawai bata son mijinku bane ba mamaki ma ta fiki sonshi kawai dai ta iya takunta ne, babu mamaki ma ta fiki sonshi sai dai wata ƙil ita sonta irin son nanne da zaka so miji ka kuma so duk abinda yake so, kawai dai ta iya sarrafa kantane."
Cikin sanyin jiki Ameena tace.
"Shiga motata muje in sauƙeƙi dama ina son muyi mgna".
kai ta gyaɗa mata kana suka shiga Mota,
shiru sukayi saida Ameena ta dai-dai ta hancin motarta kan titi kana ta juyo ta ɗan kalli Samira cikin sanyin jiki tace.
"Wato ko Samira ni kaina nasan zuciyata bata min adalciba akan Ammin Adeel, na yarda na gane tana masifar son ɗana so kuma na gaskiya, kana tana kawar da kanta akan harkata da mijinta tamkar bata san me mukeyi ba, bawai ina jin na tsaneta bane a a wlh ni kaina ina sonta sai dai ina masifar kishinta,ina son Abban Adeel wani irin son da ni kaina bansa adadinshiba shiyasa nake kishinsa bana son yayi nesa dani, kinga tsabar zugar kishi wallahi yanzu sai yayi ta bina yana son haƙƙinshima sai inji to ai yanada wata matar."
Juyowa Samira tayi ta fuskanceta da kyau cikin wayewa da iya salon kishi na Musulunci tace.
"Kin wahala kin ɗorawa kanki dala ba gammo, ke ƙawata in banda tsaurin ido irin namu na mata ki samu mace da mijinta kice zaki zafafa kishinki yo in dai ita bata zafafabaai ke kuma bai dace ki zafafaba me ruwanki da ita zamanki da ban nata da ban, tsakaninku babu babbancin matsayi ku duk matanshi ne, ki dena sawa ranki yafi sonta, ko ganin wani ƙira nata, ki gyara zuciyarki zakiji daɗin zama da kowa a gidan".
Shiru Ameena tayi jiki a mace dan ta ƴarda da batun Samira tasan gsky take gaya mata,
ita kuwa Samira cikin kula ta kalleta tare da cewa.
"Ni kam Ameena kiyi haƙuri ba gulma bane menene ya rabaki da mijinki na fari wanda kika cemin yayanki ne ɗan baffanki kuma a wurin iyaye shi kika girma".
Wani nannauyan ajiyan zuciya Ameena ta sauƙe tare da maida numfashi,
ganin haka yasa Samira cewa.
"Sorry bawai na matsa bane in san sirrinki,ina son in fahimci wani abune inji ko laifin ya Amir ne".
Kai ta rausayar cikin sanyi tace,
"Akwai kam, akwai laifinshi".
Cikin kula Samira tace.
"Menene laifin nashi?"
Hankalinta ta maida kan tuƙin da takeyi kana ta fara bawa Samira labarin.
"DADY Baban Ya Amir ƙanin babane uwarsu ɗaya ubansu ɗaya, babanane babba,
Allah ya azurta babana da dukiya da ilima kana da ƴara dan mu ƴaranshi mun kai goba.
Yayinda Dady kuma Allah ya bashi tarin dukiya da ilimi amman ɗanshi ɗaya ne rak a duniya wato ya Amir ɗin,
Mommo matarshi tana masifar sona tun ina ƙarama ita ta roƙi Mamana da Babana aka bata ni,
shine sanadin da yasa na girma a Abuja dan iyayena asalin ƴan Jada ne.
Ya Amir ya tashi cikin tsananin so da gata shiyasa ya zama sangartacce, kana Ya Amir irin mazananne masu azabar jaraba mace bata isarsu da wuri,
Kuma tun ina ƙarama yake sona sabida Mommonshi ma tace shi tayiwa kamu,
haka kuwa muka taso yana sona nima ina sonshi, to matsalar ya Amir ɗan bunsurune baya iya rayuwa saida mace.
Amman ni a lokacin ban saniba hakama Dady bai saniba, amman ita mommo mamanshi ta sani ganin ya tsananta bunsuranci yasa tace, kawai ayi aurenmu in ƙarisa karatuna a gudanshi, ita a nata zaton tunda jarabace kuma mace yakeso to ai in an aura mishi ni zai daina neman mata.
Kuma koda yaji batun aurenmu da iyayenmu suka tayar yaji daɗi sosai.
Madadin iyaye ke tsuma amarya tofa shi ya Amir shine ma ke seyo min abubuwan gyara ya kawomin, kuma sosai na dage ina gyara kaina
Alhamdulillah kuwa akayi aure lfy lafiya, muka tare a anan cikin gidan namu side ɗinmu nacan nesa dana Dady.

A darena na forko da Ya Amir bai ɗaga min ƙafa bai sahir taminba,
haka yayi ta caccakata kamar ba gobe,
na wahala sosai a wurinsa, washe gari da safe, Mommo da kanta ta gyarani naji dama-dama ta kula dani sosai sanadin haka na ɗanji sauƙi dan mommo da zuciya ɗaya take sona,
still a dare na biyuma haka Ya Amir yayi ta caccakata,
abu kamar wasa ya maidani kamar abinci, rana ta uku nace ni kam na gaji bazan iyaba,
mafarin matsalar kena, dan wlh ido da ido yace min.
"Tunda bazaki iyaba bari in kira Dina tazo ta taimaka min".
Wlh ni na ɗauka wasane, dina sakatariyar shi ce kuma arniya ce,
in taƙaice miki a gabana ya kirata yace su haɗu a hotel,
Shine ma farin kishina, dan ji nayi kamar zan mutu,
duk da dare yayi naje na sanarwa Mommo ranta yayi masifar ɓaci ta kirashi baya ɗagawa, koda ta gayawa Daddy yaji baƙin cikinda bazai misaltuba yayi ta faɗa yacewa Mommo.
"Wlh da nasan Amir mazinaci ne da bazan haɗashi da ƴar ɗan uwanaba, ƴarinya da ta kame kanta in haɗata da fasiƙi".
Sosai mommo taita kuka.
Ranan a side ɗinta na kwana washe gari daya dawo suka solleshi soso da sabulu,
abin ta kaici sai yayi ta kuka wai to a ƙara mishi wata matar in munyi biyu zamu iya da buƙa tunshi, niko jin zai ƙara aurene tun satin forkoma bai ƙareba nace na yarda ni zan iya dashi".
Ɗan rage gudun motarta tayi kana ta ɗan kali Samira da ta zuba mata ido cikin sanyi taci gaba da cewa.
"Yanajin haka yace to shike nan in sha Allah ya dena bin mata, ke da haka muka koma side ɗinmu dake yana hutun amarci,
ranar tare muka wuni yana ta bidirinshi dani,
tun ina jin zafi har na dena ji, kamar wasa cikin kwanaki biyar, muka zama kamar tib da taya,
dan nima na tsumu da mugunguna da yake bani kuma shiyasa nake jin daɗi in muna sex sosai Ya Amir ya liƙe min nima kuma na fahimci ina ɗaya daga cikin mata masu buƙata matsalar da aka samu, rashin sabo da kuma zafin amsar budurci yasa nake ɗan gajiya,
randa mukayi kwana biyar ɗin ne ya wuni liƙe dani koda dare yayi na gaji yayi yayi in bashi kaina na gaza nace ya bari saida safe, ina fir yaƙi, nan na gane ya Amir Harijine,
gashi dare yayi,
ganin zai matsamin yasa na gudu na koma ɗaya ɗakinmu,
ashe ya kira Dina tazo har cikin gidanmu a ɗakinmu na sunna akan gadona,
sukayi masha'arsu tun dare har asuba.
koda na dawo na samu Dina a ɗakina,
na kusan kasheta dan da keret aka kwace a hannuna, kuma ina ihu da hargowa har Dady da Mommo sukazo suka samemu a nan da keret Dady ya kwace a hannuna gudun kar inyi kisan kai.
To nan take Dady yasa Ya Amir ya sakeni.

Haka kuwa yamin daɗi dan gaba ɗaya Ya Amir ya fice min a rai na tsanesa sabida Allah ya sani ina ƙyawar zina da mazinatan.

Koda Baba na yaji yaso ya meda auren Dady yaƙi,
daga nan na koma sashin Mommo kamar da mukaci gaba da zamanmu tana sona.

To matsalar forko dana samu itace yawan sha'awa ina yawan shiga damuwa, in begen sex ya dawo min domin gaba ɗaya Ya Amir ya dawo dani irinsa cikin sati ɗayan nan da mukayi, ga magungunan daya ɗuɗɗura min sun kamani sosai.
Allah ya sani Samira daga nan na zama jarabebbiya, ina tajin tsoro kar naje na samu lusarin miji in boni domin a zaman da nayi dole azumi na yawaita yi shiyake rage min kaifin fitinar da Ya Amir ya raɓa min.
Randa kuma na fara ganin Abban Adeel naji tsoron wani abu da nagani, dan ya zarta ya Amir nesa ba kusaba,
koda na koma gida wlh sai naita mafarki dashi muna sex,
raina da zuciyata sun ƴardarmin shine irin mijin da zai iya magance min matsalata, na sani bazan iya jure zama da lusarin mijiba,
shiyasa kikeji ina ce miki bana son Abban Adeel yayi nesa dani, Alhamdulillah kuma shima ɗin ba tayan baya bane".
Ta ƙarishe maganar cikin jin kunya,
ita kuwa Samira dariya tayi sosoi kana tace.
"Wato ya Amir ne ya maida min ke fitinenniya".
Murmushi kawai tayi,
tare da karya konan shiga layinsu Samira.
Ita kuwa samira cikin kula tace.
"Yanzu ya Amir ɗin yayi aurene?".
Da sauri ta gyaɗa kanta tare da cewa.
"Ya musuluntar da Dina tayi istibira'i ya aureta dan itama harijace irinsa, yanzu yaransu biyu yamin takwara da yarshi ta biyun Amina sai ɗan farinsu Hisham ita kuma Dina yanzu sunanta Fatima".

Cikin jin daɗi Samira tace.
"Alhamdulillah kinga wani hanin ga Allah baiwace,
yanzu dai ni bance kada ki liƙe mijinkiba amman ki dena kishin Zaleeha dan itafa matarsa ce ba karuwarsa bace kamar Dina da ya Amir so dan Allah ki sawa ranki salama, ki fauwalawa Allah lamarinki kamar forko, shi zai ɗaga daraja da kimarki a wurin mijinki wlh Abban Adeel yana sonki".
Dai-dai lokacin suka isa ƙofar gidan Samira, cikin sanyi Ameena tace.
"In sha Allah zan kula dan wlh ni kaina nasan Abban Adeel yana son farin cikina".
Kai Samira ta jinjina tare da cewa.
"Yauwa ƙawata ki kula gudun kada ki ɓarar da damarki sai gobe in mun haɗu zamu ƙara tattaunawar zan baki shawarwarin yadda zaki samu sauƙin kishin kuma ki yarda yana sonki."
Cikin jin daɗi Ameena tace.
"To Allah ya kaimu gashi yauma itace dashi gobema itace sai ran monday zan ƙarɓeshi kuma kinga ran monday ɗin munada off zan wuni a gida kusa da Mijina da ɗana, Allah dai ya bani ƙarfin hali irin naki, amman in sha Allah bazan sake tayar da hankali naba".
Amin Amin Samira tace lokacin data fita,
Kai tsaye cikin gidanta ta wuce, ita kuma Ameena taja motarta ta koma gida.

Koda Ameena ta dawo nono ta bawa Adeeli take kuwa yayi shiru kamar ba shine ya wuni koke-koke ba.
Anan sashin Ummin tayi magriba, tana idarwa kuwa ta tattara komanta ta wuce sashinta, dan yau ba itace da girki ba Zaleeha ce, shiyasa gaba ɗaya komai keneman dawo mata sabo donma tayi dace da shawarwari Samira aminiya ta gari mai imani ta nusar da ita ta koyi kauda ido kan miji da kishiyarta kada ta tsananta binciken cewar sai ta gano waya fi so a cikinsu ta kuma cire zargi, to Alhamdulillah kuma ta gamsu da shawarwarin Samira tasirin ƙawa ta gari kenan.

Zaleeha kuwa koda ta idar da sallan isha, wani haɗaɗɗen riga da wando me taushin gaske tasa, rigan irin mai hannun vest ɗinnan ne, tabi gaba ɗaya surar jikinta ta lafe, har takai ga ana iya hango shatin nipples ɗinta, dan batasa bra ba, wandon kuwa meɗan faɗi ne, amma duk da haka bai hana mayataccen hips ɗinta bayyana ba, dogon gashinta ta tubke sannan ta feshe gaba ɗaya jikinta da turare, wani irin kasala haɗi da bacci takeji, saboda hakane ma yasa batajin zata koma sashin Ummi, hayewa saman gadonta tayi, tare da jawo hand bag ɗinta, diary milk ta ɗauko, tare da ɓarewa, kwanciya tayi tana ɗan gutsuransa kaɗan kaɗan, wayarta ce ahannunta tana ɗan kallon hotuna a IG wanda duk hotunan Hamma Saif ne take gani wanda Hayatuddeen ke sakasu kamar ba gobe ta rasa me take ji a kanshi a haka ko mintuna 15 batayi ahaka ba, bacci ya ɗauketa, da diary milk riƙe ahannunta, takarasa akusa da bakinta, wayarta kuwa tabar data akunne saƙonni sai shigowa suke. Ɓangaren Saifuddeen kuwa saida akayi sallan isha kafun yake shigowa cikin gidan, sashin Umminsa yaje suka ɗan taɓa hira dasu Ahmad, sai wajen ƙarfe 9 ya nufo part ɗin nasu, kaitsaye ɗakinsa ya wuce, wanka yayi tare da shirya kansa cikin wasu kayan bacci masu taushi, sun kuwa yi masa kyau sosai, turarensa maidaɗin ƙamshi ya fesa, sannan ya nufi ɓangaren Ameena. Ahankali ya murɗa ƙofar ɗakin ya shiga, tana nan zaune akan gado, ko kayan bacci bata saba, ta zuba uban tagumi, ga kuma idanunta da suka cika da ƙwalla, gaba ɗaya komai bayayi mata daɗi, sam arayuwarta bata ƙaunar taga ranan girkin Zaleeha ya zagayo, saboda batason abun dazai nesanta ta da Saifuddeen ko kaɗan. Ganin yanda tayi tagumi ne yasashi ƙarasowa cikin ɗakin, hannun da tayi tagumin dashi ya sauƙe ƙasa tare da ɗan shafa gefen fuskarta, cikin body language ɗinsa ya dubeta, tare dayi mata alaman cewa. "Meke damunta?" Kallo ɗaya tayi masa ta kawar da kanta gefe, zuciyarta duk ba daɗi, sanin cewa idan ya matsa mata da tambaya, zata sake bayyana kishinta ƙarara, yasashi ɗan ƙarasawa ya sakarwa Adeel kiss agoshinsa, hannunta ya kamo, tare da ɗan lumshe idanunsa, alama yayi mata kan cewar saida safe, sannan ya juya akalan kekensa, tana kallonsa ya fice daga cikin ɗakin.

Samun kanta tayi da danne kishinta, kan gado ta faɗa tare da jawo pillow ta rungume tana fidda zazzafan numfashi.

Shikuwa Saifuddeen yayi hakanne dan shine abun da yafi dacewa, saboda yasan tsayuwarsa awajen nata, tamkar ƙara mata wutar kishi ne acikin ranta.
Ta cikin falonsa yabi, inda ya shiga sashin Zaleehan, dama baiyi tunanin ganinta acikin falo ba, hakan yasashi wucewa ɗakinta, ahankali ya tura ƙofar ɗakin ya shiga, sassanyan ƙamshin turare da kuma sanyin AC ne ke tashi acikin ɗakin, ɗan lumshe idanunsa yayi, tare da buɗewa, hangota da yayi akan gado ne yasashi ɗan ƙarasawa. Idanunsa ya zuba mata, tundaga kan ƴar yatsar ƙafarta yake kallonta, har ya gangaro zuwa ƙirjinta, wanda rabin breast ɗinta suka fito ta saman rigar, ga kuma shatin nipples ɗinta da suka bayyana kansu, ta cikin rigar, wani irin zubawa yaji tsikar jikinsa nayi, take yaji jijiyar jikinsa na neman miƙewa tsaye, saboda sexy dress ɗin dake jikin Zaleehan ya isa hautsuna tunanin duk wani ɗa

Please Login or Register in order to submit comment