Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ɗin, wanka tayi sannan ta ɗauro al'wala'n sallan isha,  rigar da ta cire shi ta sake mayarwa, wanda dama doguwar rigar atamfa ce ajikinta.      Koda tayi sallan ta jima akan sallaya tana addu'o'i, har kusan ƙarfe tara na dare tana nan zaune akan sallaya'n, daga ƙarshe kuwa anan kan sallayan ta kwanta tare da lulluɓe jikinta da bargo, luf tayi tana sakin ajiyar zuciya, hawaye kuwa na tsiyaya daga cikin idanunta.                     
A ɓangaren Saifuddeen kuwa dawowarsa daga sallan isha kenan, kai tsaye bathroom ya nufa, wanka yayi  haka ya fito jikinsa sai tashin ƙamshin turaren wanka yake, tura wheelchair ɗinsa yayi zuwa gaban dressing mirror, cikin nutsuwa ya shafawa jikinsa mai me daɗin ƙamshi,   body spray ya fesa, sannan yaja wheelchair ɗinsa ya ƙarasa gaban drawer'nsa, wani 3 quater jeans ya sanya tare da wata blue ɗin t-shirt me kyau,  sake feshe jikinsa da turare yayi sannan ya ƙarasa inda laptop ɗinsa yake, ɗauka yayi tare da ajesa akan cinyarsa, cikin nutsuwa ya soma ɗan daddanawa.          Ahankali ta turo ƙofar ɗakin ta shigo, tasha kwalliya cikin wata sleeping dress me kama jiki, kana ta sake ɗan gashinta wanda iya kansa ya kwanto kan wuyanta,    tsaye tayi ajikin ƙofan tana kallonsa, sosai yayi mata kyau, akullum indai ta ɓangarenta ne ƙara kyau yakeyi tana masifar sonshi shiyasa take tsananin kishinsa ji take tamkar dan ita ɗaya aka halicceshi, shikuwa Saifuddeen sam ma baisan da zuwanta ba, saboda ya bawa ƙofar shigowa ɗakin baya sannan kuma gaba ɗaya hankalinsa akan laptop ɗinsa yake.           Murmushi ta ɗanyi tare da takowa ta ƙaraso inda yake, hannuwanta tasa  ta bayansa kana ta rungumesa,  ɗan lumshe idanunsa yayi,  tare da cije laɓɓansa, dama yasan  aje azo dole saitazo ta katsesa daga abun da yakeyi.     
Ameena kuwa zagayowa ta gabansa tayi ya zamana suna fuskantar juna,  wani irin annuri  ta hango akan fuskar tasa,   take taji ƙirjinta ya buga, shikuwa Saifuddeen ganin yanda ta ƙuresa da ido ya sashi ɗan sakar mata murmushi.    Itaɗinma murmushi ta mayar masa, tare da ɗan duƙowa tayi kissing ɗinsa akan forehead ɗinsa,   ɗago  kyawawan idanunsa yayi ya kalleta,  ɗan lumshe idanunsa yayi tare da miƙa mata hannunsa, kama hannun nasa tayi, shikuwa ya jawota cikin jikinsa ya ajiyeta kan cinyoyinshi ya zama suna fuskantar juna da kyau, wani sakalin murmushi yayi mata tare zaro harshensa  waje yana ɗan karkaɗa mata wani irin abu taji ya ratsa jiki da zuciyarta, ido ta zuba mishi ganin ya sanya lips ɗinsa yaɗan yiwa kumatun ta kiss,     wani irin sanyi taji acikin ranta,  hannayensa ya sanya ya tallafo haɓarta, haɗe fuskarsu waje ɗaya yayi, tare da kamo bakinta yana kissing,   cikin jin daɗi da farin cikin da ta samu kanta ciki, ta kamo tongue ɗinsa tana tsotsa,          tunaninta ne ya fara kwancewa, sakamakon irin salon da taji yanayi mata, wanda bata bai taɓa yi mata irinsa ba sai yau ɗin,  wani tunani da yazo zuciyarta ne yasa ta ɗan janye jikinta baya, idanu ta ƙura masa tana me ƙoƙarin karantar yanayin da yake ciki.   Kyawawan idanunsa ta kalla, wanda suka kasa ɓoye abun da ke zuciyarsa, wani irin zallan farinciki ta hango acan ƙasan idanunsa,   dubansa tayi sosai shaiɗan na ingiza kishinta, har yanzu fuskarsa ɗauke take da sahirtaccen murmushi wanda ke nuni da can ƙasan zuciyarsa na danƙare da tarin farin ciki mai ratsa jiki da zuciya gashi har ya baiyana bisa fuskarsa,  take wani tunani yazo ranta, nan kuwa taji wani abu me ɗaci ya tsaya  a maƙoshinta,  tabbas tasan cewa wannan farin cikin da ta hango akan idanunsa bawai na haka kawai bane,  tasan wannan farincikin da take hangowa acikin idanunsa, bai rasa nasaba da dawowan Zaleeha abinda ranta ya saƙa mata kenan,  take taji wani ɓacin rai ya zo mata,  matsanancin kishin da tsanar Zaleehan ne ya sake rufeta,     ahankali yasake matso da fuskarsa gab da nata, ƙoƙarin sake kamo laɓɓanta yake, cikin sauri tajanye jikinta baya,   ji tayi gaba ɗaya idanunta na neman kawo ruwa, hakan yasa cikin sauri ta juya ta fice daga cikin ɗakin.                       Binta yayi da kallon mamaki, saboda yanda yaga yanayinta ya sauya lokaci ɗaya. 
     Ɗan jim yayi, yana tunanin shi dai bai mata komai ba lokaci guda kuma ya saki murmushi, maida kansa ga laptop ɗinsa yayi  ya cigaba da aikin da yakeyi.           
            Ameena kuwa tana fita daga ɗakin nasa, kai tsaye ɗakinta ta wuce, ranta nayi mata ƙuna, akan gado ta zauna, take kuma sai taji hawaye nabin gefen idanunta,  hannu tasa ta dafe kanta,       ita ta sani tabbas wannan farincikin da ta gani akan fuskarsa duk dan saboda dawowan wannan aljanar tasa ne,   tana sonsa   shiyasa take jin kishinsa sosai, bama kamar yau da ta hango soyayyar Zaleehan acikin idanunsa, bayan kuma tasan cewa Zaleeha tafita komai, kyau, sura, dama komai da komai.     Tashi tayi ta kashe hasken ɗakin nata, kana ta haye saman gado ta kwanta, gaba ɗaya ranta babu daɗi.

Sai wajajen ƙarfe 11 kafun ya kammala abun da ya keyi, harzuwa lokacin kuwa Ameena bata dawo ba, sosai abun ya basa mamaki, dan a iya saninsa baiyi mata wani abu da zai ɓata ranta ba, wayarsa ya ɗauka tare da laluɓo number'n ta ya shiga rubuta mata text message kamar haka. _"Har yanzu fa ke nake jira banyi bacci ba, kuma baki zoba, Please kiyi sauri kizo, idan zaki zo ki taho, ki ta homin da Adeel."_
yana gama rubutun ya tura mata, ƙoƙarin sauƙa daga kan wheelchair ɗinsa yayi inda ya haura saman gadon.
Dai-dai lokacin da saƙon nasa yazo mata kuwa, tana nan kwance sai-dai ba bacci takeyi ba, gaba ɗaya tsananin kishinsa ya hanata sakat, ganin wayarta ta kawo haske yasa ta ɗauka ta duba, tana gama karanta saƙon nasa ta maida wayar ta ajiye, batare da tayi masa reply ba. Saifuddeen kuwa ɗan kishingiɗa yayi, yana jiran ko zata shigo, amma shiru babu alamarta, kuma sannan babu reply, jawo wayartasa yayi ya sake tura mata wani text ɗin. Shima sama da mintuna goma aka kwashe babu amsa, ganin haka ya sashi gyara kwanciyarsa tare da jawo blanket ya rufawa jikinsa, cikin ransa yace.
"Meye hakan ke nufi kenan? fushi tayi ta tafi ko kuma me? To fisabilillahi ni me nayi mata da zatayi fushi dani? To ko dai tayi bacci ne?". kansa ya girgiza tare da ɗage kafaɗunsa, cikin ransa yace.
"Allah ya sani ban mata komaiba a iya sanina kuma banyi komai da nufin baƙanta mata ko cutar da itaba, domin nasan son da take min shiyasa nake ganin kimarta sam bani da nufin tozartata duk rintsi zan kasance mata adalin miji jagora mai tausayinta. maganar zuci ya kumayi banyi mata wani abun da ya kamata ace taji haushi ba, well zata ma kawo kanta da ƙafafunta kwadayayyi kawai cingom ɗin na."
sake gyara kwanciyarsa yayi, yana rufe idanunsa kuwa sai bacci, don dama agajiye yake.
Ameena kuwa da ƙyar ta iyayin bacci, saboda duk juyin da zatayi shaiɗan da zafin kishi na zuzuta mata kyawun Zaleeha, da kuma zallan farincikin da ta hango acikin ƙwayan idanun Saifuddeen su ke yi mata gizo, haka nan taji gaba ɗaya ta raina kanta, sannan kuma wata zuciyar na faɗa mata cewa, kada tayi kuskuren wuce matsayinta, saboda Zaleeha zaɓinsa ce, ita kuwa zaɓin iyayensa ne bana saba, kuma dama Maza irin su Saifuddeen rayuwarsu zai tafi ne da kyawawan mata irinsu, tasan kai tsaye baza a ce mata mummuna ba, amma kuma idan aka sanyata alayin su Zaleeha, bazata ganu ba, dan ko stage ɗin farko na kyawunsu bata taka ba, domin kuwa a kyau su nasu stage ɗin acan sama yake, musamman Zaleeha da ta haɗa komai da komai, haka kishi yasa ta yita kuncewa da saƙawa, daga ƙarshe dai haka bacci ya ɗauketa, ranta duk ba daɗi.

Ɓangaren Zaleeha kuwa ƙiran sallan farko na asuba akan kunnenta, kasancewar dama bata wani samu ishashshen bacci ba, duk yanda taso hana kanta kuka ta kasa, haka ta wayi garin yau ɗin ma da wani sabon kuka, cikin kukan haka taje ta ɗauro al'wala tare da zuwa ta gabatar da sallan Asuba, zama tayi akan sallayan, nan cikin muryarta me ɗauke da kuka take karanta Al'Ƙur'ani saboda tasan karantasa zai yaye mata damuwa.
Tajima tana karatun saida taga gari yayi haske, kafun tatashi daga kan sallayan, zuwa lokacin idanunta sun sakeyin luhu luhu, gwanin ban tausayi, kallo ɗaya zaka mata, kasan ta kwana kuka, ƙarasawa jikin ƙofar ɗakin tayi, cikin sanyi ta fice daga cikin ɗakin. Kaitsaye ɗakin Ummi ta nufa, abakin ƙofa ta tsaya, tare da yin knocking, daga ciki Ummi ta bada izinin shigowa, ahankali kuwa ta murɗa handle din ƙofar tashiga, Ganin Ummin na zaune akan gado, yasa cikin sanyi ta ƙarasa tare da durƙusawa, cikin muryarta dake rawa tace. "Ummi ina kwana." Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
"Lafiya ƙalau Zaleeha ya jikin naki dai?" Asanyaye tare da muryarta dake bayyana rauninta tace.
"Da sauki."
Kai Ummi ta jinjina cikin kulawa tace.
"Masha Allah, Allah Ya ƙara sauƙi, sannan ki ƙara kwantar da hankalinki kinji, komai yayi farko yana da ƙarshe, haka ma kuma komai yayi tsanani zaiyi sauƙi da yardan Allah, ako yaushe kina sawa zuciyarki nutsuwa, kinga ko yawan kukan nan ma da kike bashida amfani, kiyi haƙuri kinji, ƙaddara ce babu kuma yanda bata zuwa wa bawa, saidai neman sauƙi awajen Allah kawai."

Kanta ta ɗan jinjina cikin muryarta dake rawa tace.
"To Ummi, amma kullum zuciyata ƙara karyewa take, gani nake kaman Baba Malam bazai taɓa yafe min ba, tsoro nakeji Ummi, idan na mutu Baba Malam na fushi dani, samun aljanna zaiyi min wahala, kuma kowa nace ya roƙamin Baba Malam sai yaƙi, har Daddy (Malam Adam) shima nace ya bawa Baba Malam haƙuri, amma yace shi babu ruwansa, shima fushi yake dani."
Ɗan jim tayi tare da sakin sheshsheƙa, asanyaye tace. "Zakariyya yace duk wanda na ɗauko dan yabawa Baba Malam haƙuri, bazai haƙura ba, har saidai in Hamma Saif ne ya rakani.
Dan Allah Ummi ki roƙamin Hamma Saif ya yafemin, ya rakani mu bawa Baba Malam hakuri, idan Baba Malam baiyafemin ba, nasani haske bazai taɓa ziyartan rayuwata ba ." Taƙare maganar cikin yanayin ban tausayi, ga kuma hawayen da gaba ɗaya suka gama jiƙa mata fuska.
Hannayen Zaleehan Ummi ta kamo cikin yanayin kulawa haɗi da tausayawa tace.
"To kidaina kuka, insha Allah zan faɗa masa, kuma nasan zai yafe miki, sannan kuma zai rakaki kuje ku bawa Baba Malam haƙuri, ki tsaida kukan haka kinji."
Ummi ta faɗi maganar cikin lallashi. kanta ta jinjina, saboda ta ɗanji sanyi aranta. Jan jikinta tayi ta zauna anan kusa da Ummin.

Ahankali ya turo ƙofar ɗakin ya shigo, dan alokacinne dawowarsa daga masallaci, kusan atare suka ɗago kansu suka kalleshi, hakanne yasa idanunsu faɗawa cikin na juna, lokaci guda ya kawar da duk wata annuri dake kan fuskarsa, itama asanyaye ta yi ƙasa da kanta, cikin haɗe fuska ya ƙaraso cikin ɗakin, dan ma Ummi ta riga da ta ganshi ne, da ace bata gansa ba babu abun dazai hanashi komawa inda ya fito.
Ƙarasowa kusa da Ummin nasa yayi, haɗe hannayensa biyu yayi, kana cikin body language ɗinsa ya gaida
ta.
Amsa masa gaisuwar Ummi tayi tana ɗan sakin murmushi.
Asanyaye Zaleeha ta ɗago kanta, cikin wata irin murya me ɗauke da sarƙewa, akaron farko kenan na tarihin rayuwarta da zata fara gaida shi, cikin sheshsheƙan kukan daya taso mata tace.
"Ina kwana." kasancewar yana iya kallonta ta gefen idanunsa ne,yasashi fahimtar abunda tace, amma sai ya share yayi kamar baigani ba, saima sake haɗe fuskarsa da yayi, tare da ƙoƙarin soma ciro wayarsa, daga aljihun rigarsa. Ganin hakane yasa Ummi sa hannu taɗan taɓashi, ɗago da kansa yayi ya kalli Ummi'n.
Da idanu tayi masa nuni da Zaleeha kana tace. "Bakaga Zaleeha na gaisheka bane."
Ai tunma kafun Ummi ta gama rufe bakinta, yasake maida kansa ƙasa, dan bama yaso ya fahimci abunda Ummin ke ƙoƙarin faɗa, ahankali ya tura wheelchair ɗinsa, ya nufi hanyar fita daga ɗakin, ko inda Zaleehan take bai kuma kallo ba. Baki buɗe Ummi ke kallonsa har ya fice daga cikin ɗakin, kanta kawai ta girgiza, tare da sakin ɓoyayyen murmushi, sarai tasan gano ƙasan zuciyarsa cewa wannan fushin nasa da yakeyi da Zaleehan hukunta yakeyi har cikin zuciyarsa, kuma yanayi ne dan ya gwada mata ɓacin ransa, akan abun da ta aikata, sannan kuma ya nuna mata kurenta ta kuma sani shima mutunne kamar kowa yanada zuciya kuma zai hukuntata muddin ta ɓata mishi.
sanin irin zazzafar soyayyar da Saifuddeen ɗin keyiwa Zaleeha yasa Ummi sanin cewa bazai taɓa iyayin haƙiƙanin barranta da ita ba.
Itakuwa Zaleeha asanyaye ta miƙe, cikin sanyin da ayanzu ya zama tamkar ɗabi'arta tace.
"Ummi ina Raleeya, da Hayatuddeen."
ɗan murmushi Ummi tayi tare da cewa. "Raleeya na kitchine, Hayatuddeen kuma kinsan yau weekend yanacan yana baccin nasa da baya gajiya dashi."
Kanta taɗan jinjina, sannan tace.
"To bari inje kitchin ɗin in taya Raliya aikin".
Da sauri Ummi tace.
"A a jeki kwanta". Zata kuma yin mgna Ummi tace.
"Nace kije ki konta ki huta".
ganin yadda Ummi tayi mgnar cikin bada umarnine yasata cewa.
"To Ummi bari naje na ɗan kwanta."
Kai Ummi ta jinjina mata, saboda duk wani koke koken da tayi adaren jiya, Ummin najinta, hakanne ma yasa tasan cewa Zaleehan bata wani samu ishashshen bacci ba. Tana fitowa daga ɗakin Ummin kuwa, sukai karo da Hayatuddeen wanda da dukkan alama yanzu tashinsa, dan sai hamma yake ta zubawa tare da miƙa.
Ganin Zaleehan yasashi sakin murmushi, ƙarasowa yayi tare da kamo hannunta, cikin kulawa yace.
"Good morning my beautyful Aunty, ya jikin naki?"
Kanta taɗan jinjina masa alaman da sauƙi, idanunta ne suka sauƙa akan Saifuddeen wanda ke zaune akan kekensa ya basu baya, yana ta faman aikin danna wayarsa, saurin ɗauke idanunta daga kansa tayi, tare dayin ƙasa da kanta.
Dai-dai lokacin Raleeya ta fito daga cikin kitchine, gaisawa sukayi cikin kulawa kuwa Raleeya ke tambayarta jikinta, nan tace mata da sauƙi. Hayatuddeen ne ya kamo hannun Zaleehan, tare da zaunar da ita akan ɗaya daga cikin kujerun falon, cikin kulawa yace.
"Adda Zaleeha dan Allah minti biyu, ki jirani anan ina zuwa."
kai ta jinjina masa tare da sadda idanunta ƙasa tana wasa da ƴan yatsun hannunta.
Ameena ce ta buɗe ƙofar falon ta shigo bakinta ɗauke da sallama, shirye take tsab acikin kayan aikinta, ga kuma kekyawan ɗanta Adeel da ke riƙe ahanunta, shigowarta falon kuwa yayi dai-dai da fitowan Ummi daga ɗaki.
Jin ƙamshin turaren Ameenan ne ya sashi ɗago kansa ya kalleta.
ƙarasowa cikin falon tayi, da ganin Zaleeha kuwa sai taji gaba ɗaya ranta yayi ƙunci, ɗan durƙusawa tayi, aladabce ta gaishe da Ummi', fuska ɗauke da fara'a da kulawa Ummi ta amsa tare da miƙa hannu ta karɓi Adeel dake ta yi mata dariya irin tasu ta yara.
Ɗago kai Zaleeha tayi, karab kuwa suka haɗa idanu da Ameena'n, kasancewar dama idanun Ameena'n akanta suke, ta tsareta da idanu kamar ta samu tv. Cikin sanyi Zaleehan ta janye idanunta, tare da cewa Ameena'n'.
"Ina kwana." zazzaƙan muryar Zaleehan da Ameena taji shiya sanya bugun zuciyarta tsananta, wanda har yasa ta kusa daburcewa, cikin in ina ta amsa da "La fi..ya." dan zata iya rantsewa cewa bata taɓa jin murya me daɗin a zahiri irin ta Zaleehan ba.
Kallon Adeel dake hannun Ummi Zaleeha tayi, cikin sa'a kuwa yaron shima kallonta yake, murmushi tayi masa sai kawai ya buɗe baki yana mata dariya, wani irin kyau yaron yayi mata, musamman ma yanda dimples ɗinsa suka lotsa da yana dariyan, lokaci guda taji ya shiga ranta, hakan yasa ta miƙa hannu dan ta ɗaukeshi, babu ƙiwa kuwa yazo wajenta, karɓansa tayi tana sakin sassanyan murmushi. Ummi ne itama tayi murmushi cikin kulawa tace.
"Lallai Adeel yaga ɗiyarsa, tunda dai baiyi mata ƙiwa ba." Kallonta Zaleehan tayi da ɗan mamaki, kai Ummi ta jinjina tare da cewa.
"Ai me sunan Baba Malam ne."
Wani irin farinciki ne ya cika zuciyar Zaleehan, sai kawai ta rungume yaron ajikinta tanajin sonsa sosai aranta haka nan sai takeji kamar itace ta haifeshi in ba gizo idonta ke mata sai takega kamar yaron yana kama da ita, musamman dimples ɗinsa irin nata ne sak.
Dai-dai nan Hayatuddeen ya fito daga kitchine hannunsa ɗauke da cup, wanda aka zuba yoghurt acikinsa, akusa da Zaleehan ya zauna tare da miƙa mata yoghurt ɗin, cikin kulawa yace.
"Adda Zaleeha amsa kisha, al'ƙawari nayiwa Zakariyya cewar yau sai nasa kinci abinci, saboda haka dan Allah kisha kafun agama break fast." ɗan marairaice fuska tayi, sai dai kuma ita kanta tasan cewa tana matsanancin jin yunwa, hakanne ma yasa ta amsa, tare da ɗan sha kaɗan, kan Adeel da har yanzu ke kan cinyarta take shafawa, sosai yaron ya shiga ranta tana jin sonshi da ƙaunarshi har cikin ranta.
Duk wannan wainar da ake toyawa Ameena idanu kawai ta zuba musu, itakam Allah yasani bata gajiya da kallon Zaleeha, to itama da take mace, bata gajiya da kallonta, inaga kuma Namiji haka yasa kishinta kuma ninkuwa a ranta.
Hayatuddeen ne ya ɗago kansa ya dubi Ameena'n, murmushi yaɗan saki cikin kulawa da girmamawa ya fuskanceta tare da cewa. "Aunty Ameena ina kwana."
itama murmushi'n ta mayar masa tare da cewa.
"Lafiya Auntan Ummi, ya rigima." murmushi kawai yayi, batare da yace mata komai ba, ya maida hankalinsa wajen Zaleeha tare da kissing goshin Adeel dake kan cinyar Zaleeha, wanda da dane kuma ta tabbatar tsayawa zaiyi yayita mata rigima, amma yanzu gaba ɗaya hankalinsa naga Zaleeha.
Hakanne yasa asanyaye ta juyar da kanta ɓangaren Saifuddeen, ai kuwa idanunsu ne ya haɗe, dan dama kallonta ya keyi, murmushi ta sakar masa, domin tuni haushin nasa da takeji ya gushe, ayanda take matsanancin sonsa batajin zata iya dogon fushi dashi bare ta ɓata rawanta da tsalle, shiɗin ma murmushi yayi mata tare da miƙa mata hannunsa, ganin Idanun su Ummi baya kansu yasa ta kama hannun nasa, gamamakinta sai gani tayi yajawota dab dashi, har jikinsu na gogan na juna, kasancewar jiyan ba'a ɗaki ɗaya suka kwana ba, hakan yasa bata gaishesa ba sai yanzun, ahankali tace.
"Ina kwana." Kansa ya jinjina mata alaman lafiya, sannan ya tallafo haɓarta, kiss ya ɗaura mata akan kumatunta da kuma bakinta, baruwansa da wani jin kunya wai dan su Ummi na falon bare yasan idon Ummi baya kansu.
Gaba ɗayansu sunga abun da Saifuddeen din yayiwa Ameena hakan ne yasa suka janye idanunsu gefe, Zaleeha ma da tsautsayi yasa ta ɗago, idanunta sun gane mata abun da ya faru, kawar da kanta gefe tayi, tare da ƙara manne Adeel ajikinta, ko ajikinta itakam, bata ma ji wani abu adangane dasu ba, saidai zuciyarta ta tsegunta mata cewa. "Halan Ameenan matarsa ce kenan." Ummi kuwa, tashi tayi gaba ɗaya ma tabar falon, dan ta gano cewa wannan sabuwar kulawan da Saifuddeen ɗin ya fara bawa Ameena agabansu wani salone, kawai yayi ne saboda wata manufarsa ta daban. Ameena kuwa da gangan ta kamo lips ɗinsa itama ta tsotsa, cikin sanyin murya tace. " I will miss you dear" sake manna masa wani kiss ɗin tayi, sannan ta ɗan janye daga jikinsa, Hayatuddeen kuwa baki ya sake yana kallon ikon Allah,
Zaleeha kuwa sam bata ƙara ɗago kanta bama sai wasa takeyiwa Adeel wanda da ka gani kasan tana jin son yaron har cikin ranta.
Ƙarasowa inda suke Ameenan tayi, tare da sanya hannu ta ɗauki Adeel, tana sakin murmushi me ɗauke da ma'anoni kala kala, haka ta saɓa Adeel akafaɗanta ta fice daga cikin falon, wani irin farinciki takeji acikin ranta, wannan kiss ɗin da Saifuddeen yayi mata agaban Zaleeha ji take kaman kyautar zuciyarsa ya bata a gaban Zaleeha ji takeyi ya gama mata komai dan ko ba komai ya nunawa Zaleeha itama matarsa ce kuma yana sonta murmushi kawai take tayi.

Tashi Zaleeha tayi ta wuce ɗakinta, kusan rabin cup tasha yoghurt ɗin sannan ta kwanta. Acan falo kuwa Raleeya ce ta gama shirya musu abinci akan dinning area, Ummi ne tace da Hayatuddeen yaje ya ƙira Zaleeha tazo suyi beak, koda yaje ɗakin nan ya isketa tana bacci. Dawowa yayi ya faɗawa Ummi'n, hakan yasa Ummi tasa Raleeya ta ɗeba mata nata break fast ɗin daban.

Saida suka kusa kammala break fast ɗin, Ummi ta ɗago kanta ta dubi Saifuddeen wanda yake tsakalan chips yana kaiwa bakinsa, ahankali yake tauna abincin, yanayin komai nasa cikin nutsuwa.
Gyara zama Ummi tayi tare da ɗan muskutawa ta kamo hannunsa, ɗago kansa yayi, tare da sakarwa Ummin nasa murmushi.
Itama Ummin murmushi tayi masa, cikin kulawa tace.
"Ka bani

Please Login or Register in order to submit comment