Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yana kallonta haka aka shiga da ita ɗakin theatre'n, kuka sosai Ya Ameenu yasa kaman ƙaramin yaro, Baba Malam ne ya riƙesa yana rarrashinsa.


Ameena kuwa koda taje asibitin aje Adeel tayi awajen wata ƙawarta mesuna Umaima, nan ta nufi theatre room dan ansanar da ita cewa, babban Dr ɗinsu na nemanta acan ɗin.

Takusan kaiwa theatre room ɗinne tahango Baba Malam, Ya Ameenu, da kuma Ya Habu, sai Mamy suna tsaitsaye, cikin sauri taƙarasa garesu, ganin fuskokinsu ɗauke da matsanancin damuwa yasa jikinta yin sanyi asanyaye ta gaidasu, tare dayi musu tambayan halan ko wani suka kawo bashi da lafiya, dan taga idanunsu gaba ɗaya sunyi jajur.

Hankalim Mamy amatuƙar tashe yake faɗa mata cewa.
"Maryam ne suka kawota haihuwa, ankuma ce dole sai theatre za'ayi mata, yanzu haka ma anshiga da ita ɗakin theatre'n."
Hankalin Ameena ne ya tashi sosai, take cikin sauri ta nufi ɗakin theatre'n.




Littafina na ƙuɗine in kina buƙata turo katin mtn na ɗari uku ta wannan no ɗin 09097853257 ko kimin transfer ta asusuna 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa.



          By
*GARKUWAN FULANI*

              
10/4/20, 7:04 PM - Mmn Khalid: *(heart touching)*

Sbpejy Su Baba Malam kuwa tsayuwa sukayi, gaba ɗaya jikinsu asanyaye y'ake, babu wanda yayi yunƙurin zama acikinsu, Mamy kuwa hawaye take ta sharewa, zuciyarta cike take da tausayin Maryam.
Can cikin theater room kuwa, alluran nan dake gusar da hankali, likitotin sukayiwa Adda Maryam, Doctors kusan guda huɗu ne suka duƙufa akanta, cikin ƙwarewa kuwa suka soma yi mata aiki.
Shiru ɗakin theater'n yayi bakajin motsin komai, sai na kayayyakin aikin da likitotin ke amfani dasu.
Sosai aikin nasu ya ɗauko nisa, gefe kuwa Ameena ne da wata nurse wanda sune ke taimakawa wajen miƙawa doctors ɗin kayan aiki.
Ahankali ƙwayar idanunta ke tsiyayar da wasu sassanyan hawaye, sosai kuma hawaye suka rinƙa kwaranyowa daga cikin idanunta, Ameena wanda gaba ɗaya hankalinta naga Maryam din ne, ganin idanun Maryam ɗin na zubda hawaye, yasa amatuƙar firgice ta matso kusa da ɗaya daga cikin doctors ɗin dake yi mata aiki'n, ɗan taɓasa tayi yana juyowa kuwa tayi masa nuni da fuskar Maryam, cikin yanayin tsoro haɗi da mamakin ikon Allah likitan yayiwa ƴan uwansa nuni da Maryam ɗin, wanda idanunta suke ta zubda hawaye, koda suma suka ga yanda Maryam ɗin take , sosai suka shiga shock, saboda sunsan sunyi mata alluran gusar da hankali masu ƙarfi, wanda baiyiwuwa ma ta farfaɗo koda nan da awa 2 ne, sai gashi abun mamaki ko mintuna 30 ba acika ba idanunta na zubda hawaye kamar dai kuka takeyi mamakin hakanne yakamasu ƙwarai, saboda koda jinin mutum nada ƙarfi, idan akayi masa wannan alluran yana tasiri sosai ajikinsa, ɗaya daga cikin doctors ɗinne ya sake haɗa wani alluran yayi mata, bayan ya mata alluran da kamar mintuna uku ne, suka ga idanunta sunyi lib sun dena ɗan motsawan da sukeyi saidai kuma har yanzu hawaye na fita daga cikin idanunta, yana bi ta cikin kunnenta, kana yana sauƙa akan matashin kanta.
Sosai abun ya ɗaure musu kai, dan kuwa basu taɓa samun irin haka a cikin aikin su ba, nan dai suka maida hankalinsu wajen ciro yaron dake cikin nata.
Cikin ikon Allah kuwa suka fito da santalelen yaro, saidai kuma yariga daya rasu, tun jiya shiyasa ma haihuwar ta gagara, ya zama sai an mata tiyata, ɗayar nurse ɗin da suke aiki tare da Ameena suka miƙawa yaron, sannan suka duƙufa wajen ɗinke ta, cikin mintuna kaɗan suka gama yi mata duk wani abun daya dace cikin iya da kwarewa da sanin makaman aikinsu.
Ɗaya daga cikin doctors ɗinne yayiwa su Ameena alama kan cewa su fita da ita, zuwa ɗakin hutu.
Hakan kuwa akayi, inda Ameena da wannan nurse din suka turo gadon da Adda Maryan ɗin ke kai.
Gaba ɗaya jikin Ameena yayi sanyi, tausayin maryam ɗinne ya cika zuciyarta, tana tausayin halin da Maryam din zata shiga, idan ta tashi, taji cewa yaron nata baizo da rai ba, tasan tabbas zata shiga damuwa.
Haka dai suka turo gadon, inda suka fito daga theater room ɗin, direct ɗakin da zasu kaita dan hutuwa suka nufa, wanda yazama kuma dole sai sun wuce ta gaban su Baba Malam, kasancewar su Baba Malam ɗin sunyi kusa da ɗakin theater'n.
Dab da sun kusa ƙarasowa wajen su Baba Malam ɗinne, Maryam ta bude idanunta a hankali lokaci guda kuwa hankalinta ya dawo jikinta, ahankali ta buɗe idanunta, cikin wata irin murya me sanyi, da kuma yanayin mayen jinya taƙira sunan.
"Baba Malam!!."
Al'amarin daya sanya su Baba Malam ɗago kansu kenan, dan dukansu kansu aƙasa yake, basu ma lura da fitowar su daga ɗakin theater'n ba, cikin hanzari su Baba Malam suka nufo ta, da sauri ɗayar nurse ɗin ta dakatar dasu, cikin sauri tashiga tura gadon, don ba aso kowa yaje kan wanda akaiwa theater sai bayan mutum ya huta tukun, Ameena kuwa cikin sauri haɗi da tashin hankali tanufi office ɗin babban doctor ɗinsu, hankalinta amatuƙar tashe yake, domin farfaɗowan Adda Maryam ɗin akaro na biyu, zai iya zama hatsari.
Maryam kuwa a hankali ta samu ta ɗaga ƴan yatsunta cikin wata dashashshiyar murya tace.
"Yaya Ameenu kazo, kazo kada su hanaka zuwa Yaya Ameenu mutuwa zanyi."
Dai-dai lokacin kuma nurse ɗin ta shige da ita wani ɗaki, cikin matsanancin sauri Ya Ameenu yazo dan bin bayan matarsa, wata nurse ce ta taresa dan ba'a shiga kai tsaye, sai an baka izini, cikin wani irin gigita Ya Ameenu ya daka mata tsawa, ransa amatuƙar ɓace hankali a tashe yace. "Matatace fa, tana ƙirana kuma kuce bazan je ba." Hannu yasa ya ture nurse ɗin gefe, nan ya faɗa cikin ɗakin su Baba Malam suka rufa masa baya.
Yana shiga cikin sauri ya ƙarasa jikin gadon, Adda Maryam kuwa da hawaye ke zuba daga cikin idanunta hannunsa ta kama, dai-dai lokacin su Baba Malam suka iso, ɗayan hannunta tasa ta kamo hannun Baba Malam ɗin.
Ƙam ta riƙe hannun Baba Malam, cikin wata irin murya me ɗauke da tsananin sanyi tace.
"Tun kwanaki nake ta ji ajikina cewa, mutuwa zanyi Baba, rayuwata tazo ƙarshe, Dan Allah Baba Malam kayafemin, sannan kaya fewa Zaleeha, nasan duk inda take tana cike da kewa, da kuma nadamar abun da ta aikata, natabbata kuma idan ta dawo zatayi maka biyayya fiye da wanda ni nayi ma, dan Allah Baba Malam ka yafewa Mama, ka barta ta dawo ɗakinta ta zauna, dan nasan itama tayi nadama, nikam nasan bazan sake zama acikin ku ba, nasan daga nan bazan koma gida da numfashi ba, lokaci na yazo, zan tafi na barku badan naso ba, zan yi nesa daku, zan tafi inda bazaku sake gani, ko jina ba."
Hannu ya Ameenu yakai ya rufe bakinta, tuni wani irin kuka ya taso masa, kansa ya shiga girgiza wa, murya na rawa yace.
"Bazaki mutuba Maryam, bazaki mutu kibarni ba Insha Allah zaki samu lfy. Rayuwata bazata taɓayin inganci ba, matuƙar babu ke acikinta, dan Allah kidaina faɗin cewa zaki tafi ki barmu, muna tsananin buƙatarki agaremu."
Hawaye ne suka tsananta zuba daga cikin idanunta, wani irin murmushi me ciwo tayi tare da girgiza kanta cikin sanyi tace.
"Dan Allah ya Ameenu idan na cika, ku maidani gidan Baba Malam kuyi mini wanka acan, sannan kusamin sutura, idan kun sallaceni, inaso kusani cikin kabarina da hannuwanku."
Shiru tayi sakamakon shaƙuwan daya taso mata, kuka Ya Ameenu ya fashe dashi, tare da soma girgiza kansa, sake damƙe hannun Yaa Ameenu da kuma Baba Malam tayi, cikin wani irin yanayi da muryarta wanda bata fita sosai tace.
"Kuyafewa Zaleeha, kada kuyi mummunan kuma dogon fushi da ita, Mamy ke da Ya Habu ku yafe mata, nikam zantafi na barku nasan da cewa zakuyimin addu'a aduk lokacin da kuka tuna dani, sannan Baba Malam zan tafi, ina me al'faharin kasancewar ka mahaifi agareni." Hawayen da suka cika idanun Baba Malam ne suka samu daman gangarowa, take wani irin kuka ya taso masa, sake damƙe hannun Maryam ɗin yayi, Mamy kuwa tuni ta koma gefe tana kuka, Ya Habu ma kukan yake sosai. Idanunta wanda sukayi farare fat ta ɗago ta zubawa Ya Ameenu dake kuka, yana ta faman girgiza mata kai, murmushi tayi masa, kana kuma tamaida dubanta ga Baban Malam, lokaci guda ta soma wani irin shaƙuwa, ganin haka yasa Baba Malam fashewa da wani irin kuka, mai tsuma zuciya, sosai ya kama hannunta yana ji yana gani ƙudirin Allah na wakana bashida iko ko da, da ace duk duniya gatan Maryam ne da masoyanta bazasu tseratar da ita koda na second ɗaya ba, cikin muryar kukan yake. faɗin kalmar.
"La'ila ha'illallah, muhammadur rasulullah, sallallahu alaihi wasallam!!!." Haka yake faɗan kalman ararrabe saboda matsanancin kukan dayaci ƙarfinsa. Cikin muryarta, dake ɗauke da shaƙuwa itama tasoma bin bakinsa, tana faɗan kalman shahada'n, duk abun daya faɗa itama sai ta faɗa, atare suka kai ƙarshen salati'n shida ita, nan take yaji jikinta yayi sanyi, komai nata ya sake, idanunta sun kafe suna kallon sama, yayinda baƙin cikin ƙwayar idanun nata ya ɓace ɓat, sai farin kawai kake gani.
Ya Ameenu kuwa dama tuni ya daina gane komai, hakanne ma yasa bai lura da cewar ta daina motsi ba, cikin wani irin yanayi Baba Malam yaja da baya tare da fashewa da wani irin kuka mai tsuma zuciya, kuka irin wanda bai taɓayi ba arayuwarsa, wannan kukan nasa shine abun dayasa Mamy da kuma Ya Ameenu da Habu, suka kai dubansu garesa, ganin irin kukan da yake, yasa Mamy da Ya Habu suka tabbatar da cewa, Maryam ɗin tarasu, kuka Mamy tasa sosai, shima Ya Habu haka, Ya Ameenu kuwa hannunta dake cikin nasa yaɗan murza, idanunsa sun cika tab da ƙwalla, hakan yasa baya ganin yanda idanunta suka juye, cikin muryar kuka yace.
"Bazaki mutu ba Maryam, in sha Allah bazaki mutu yanzu ba, saboda muna da buƙatarki acikin rayuwarmu, kidaina faɗin cewa zaki mutu, mutuwa bazata ɗaukeki yanzu ba, idan kika mutu kuma ya kikeso ni nayi da rayuwata? bazan iya zama babu ke ba, ki tashi kinji!."
ya ƙare maganar yana meɗan jijjigata, jin hannunta dake cikin nasa, jin yayi nauyi ne, yasashi matse hawayen da suka cika idanunsa, har suka hanasa gani da kyau, duban fuskarta yayi, nan yaga idanunta sunkafe, take yaji wani irin abu ya bugi kansa, dai-dai lokacin kuma, Doctor'n da Ameena ta ƙira ya shigo cikin ɗakin da sauri, ganin yanda su Baba Malam ke kuka, ya sa shi ƙarasowa jikin gadon, idanunta daya gani akakkafe yasashi girgiza kansa, nan yaja wani ɗan mayafin dake jikinta ya rufe fuskarta bayan yasa hannu ya shafe idanunta. Girgiza kai Ya Ameenu yashiga yi, cikin kiɗima yace.
"Miye haka? meyasa ka rufe mata fuska?"
Cikin tsananin tausayawa Dr. ɗin yace. "Am sorry to say Allah yayi mata rasuwa."
Tamkar sauƙan guduma haka Ya Ameenu yaji maganan doctor'n acikin kai da kunnuwansa, lokaci guda yaji gaba ɗaya lakar jikinsa ta tsinke, ƙafafunsa ne suka gaza ɗaukan nauyinsa, take yazube akan guiwowinsa, kifa kansa da jikin gadon Maryam ɗin yayi, yasaki wani irin kuka mai tada hankali, wani irin kukane, me matuƙar jijjiga zuciya, wanda hakanne yasa Ameena dake waje shigowa cikin ɗakin. kuka Ya Ameenu keyi me tsanani, irin wanda duk wanda yaji sa, dole ya tausaya masa, lokaci ɗaya jikinsa ya soma rawa, numfashinsa ne yayi wani irin fusga, take ya faɗi awajen sumamme.
Cikin sauri Ya Habu da Dr. ɗin sukayo kansa, dan Baba Malam kam kuka yake sosai da sosai.

Hawaye ne suka silalo daga cikin idanun Ameena, wanda ke tsaye agefe, sosai jikinta yayi sanyi da rasuwan Adda Maryam ɗin, Da taimakon Ya Habu doctor ɗin ya ɗan yayyafawa Ya Ameenu dake sume ruwa akan fuskarsa, cikin abun da baiwuce minti ɗaya ba kuwa Ya Ameenu'n ya farfaɗo da wani irin gigitaccen kuka, dukansu kuka suke anrasa wanda zai rarrashi wani acikinsu, da ƙyar Baba Malam ya iya tsaida kukansa, ganin cewa magriba ta kawo kai, tasowa yayi inda ya ƙaraso har wajen da Ya Ameenu'n ke zaune, har yanzu kuka yake me tsuma zuciya, yayinda ya jingina kansa da jikin gadon da gawar Maryam ɗin take, dafa kafaɗansa Baba Malam yayi, cikin da shashshiyar muryarsa yace.
"Kayi haƙuri Ameenu, ayanzu Maryam bata buƙatar kukan mu, tafi buƙatar addu'ar mu fiye da komai."
kai Ya Ameenu ya shiga jijjigawa cikin matsanancin kuka, yace.
"Yazanyi na daina kuka Baba, bazan iya ba, bazan iya daina kuka ba, bazan iya jure rashin Maryam ba Baba, mutuwa ta ɗauki Maryam ta barni, mutuwa ta nisanta ni da Matata, mace mafi soyuwa agareni, tayaya zan iya jure rashin Maryam, wanda koda sau ɗaya ne bata taɓa ɗaga min murya, ko ƙin abun da nakeso ba, komai nakeso shi take so, idan nace kada tayi, har abada bata taɓa yi, idan na umurceta bata taɓa tsallakewa, farinciki na shine nata, ta amince da aure na batare da tana sona ba, hakan kuma baisa taƙi min biyayya ba, Dama mutuwa ta sani da ta barmin Maryam saboda ina da buƙatarta acikin rayuwata!."
sake rushewa da wani sabon kuka mai tsuma zuciya yayi, idanu Baba Malam ya lumshe take wasu hawaye masu zafi suka gangaro daga cikin idanunsa, matuwar Maryam tayi matukar girgizasa ƙwarai, yanaji yana gani mutuwa ta ɗauki ƴarsa agaban idanunsa, mutuwa ta ɗauki ƴarsa mafi soyuwa agaresa, ina ma da ace mutuwa tana neman zaɓi, tabbas daya bata zaɓi ta ɗauke Zaleeha tabar masa Maryam, saboda Maryam takasance tamkar haske ne awajensa, takasance meyi masa biyayya, ita da Ahmad sun kasance suɗin daban suke acikin ƴaƴansa, masu tsananin biyayyya ne suɗin.

Sanin cewa kuka bazai bawa Maryam ɗin komai ba, yasa can cikin zuciyarsa ya soma ambaton sunan Allah, yana meyi mata addu'a, cikin ransa kuwa, yanajin cewa Insha Allah, Maryam ɗin zata dace da rahamar Allah.
Duban Mamy dake kuka sosai yayi, kana ya kalli Ya Habu wanda shima kukan yake kaman ƙaramin yaro, dai-dai nan Dr Adnan ya shigo cikin ɗakin, gaba ɗaya jikinsa amace yake, dan kuwa labarin rasuwar Maryam ɗin yaje kunnensa, ganin yanda Ya Ameenu dasu Ya Habu ke kuka, yasa yaji idanunsa sun cika da ƙwalla, haƙiƙa mutuwa wata abace dake ruguza duk wani farincikin iyali, sannan kuma bata barin wani dan wani yaji daɗi.
Cikin matsanancin tausayawa Dr Adnan yayiwa Baba Malam ɗin ta'aziyyan rasuwar, Ya Habu ne ya miƙe ya fita daga cikin ɗakin, nan cikin kuka ya laluɓo wayarsa daga aljihun rigarsa, number'n Yaa Ahmad ya fara dannawa ƙira.
Ya Ahmad dake zaune afalo shida Aunty Lubna, hakanan yana ganin ƙiran Ya Habu'n yaji zuciyarsa ta tsinke, gabansa ya faɗi, Yana ɗaga wayan kuwa zuciyarsa ta soma bugawa da ƙarfi, sakamakon yanda yaji Ya Habu'n na kuka wiwi.
Cikin matsanancin tashin hankali Ya Ahmad yamiƙe tsaye akiɗime yace.
"Habu lafiya meke faruwa ina Baba Malam?". cikin muryan kuka Ya Habu yace.
"Ya Ahmad, Allah yayiwa Maryam rasuwa!."
Ɗaɓas haka Ya Ahmad ya sulale ya zauna aƙasa, cikin matsanancin tashin hankali da kuma mugun kaɗuwa, take jikinsa ya soma ɓari, inda yaji kunnensa sunyi masa wani irin luuuuuu, sake wayar tasa yayi lokaci guda kuma sai ya fashe da wani irin kuka me sauti, wanda har Ya Habu da bai katse ƙiran ba yana jiyo sautin kukan.
Cikin matsanancin tashin hankali Aunty Lubna tace.
"Lafiya kuwa wani abune ya faru agida? dan Allah meke faruwa?".
Tayi masa tambayar aruɗe.
Cikin matsanancin kukan da yakeyi, ya ɗago kansa, ya dubeta, yana kuka sosai yace.
" Lubna Allah yayiwa Maryam rasuwa."
Wani irin hajijiyane taji naneman ɗaukanta, domin maganar tazo mata abazata, durƙushewa tayi kan ƙafafunta, take wasu irin hawaye suka silalo daga cikin idanunta, sai kawai itama ta fashe da kuka, Ya Habu kuwa yana katse ƙiran, Goggo Maryama yaƙira inda ya sanar mata maganan rasuwan, amatuƙar rikice Goggo Maryama tasa masa kuka, jin tana kuka itama yasashi katse wayan, Nan ya dannawa lambar Malam Adam ƙira, bugu biyu kuwa ya ɗauka, jin abun da Ya Habun ke faɗi, yasa Malam Adam, sanya salati, hankalinsa amatuƙar tashe, yace zaizo nan asibitin ya samesu.
Lambar Hajja Inna ya kuma laluɓa, saida wayar ta kusa tsinkewa kafun ta ɗaga, tana shirin masifance sa kan cewa ya dameta da ƙira, jinsa yana kuka yasa cikin matsanancin tashin hankali tace.
"Kai Habu lafiyanka kuwa? me yake faruwa naji kana kuka?"
Cikin matsanancin kuka yace.
"Maryam ne."
Cikin sauri Hajja Inna da ƙirjinta ke bugu tace. "Maryam ne me? Meya sameta."
Zakariyya da Ziyada dake zaune nan falon, tun da Hajja Inna ta fara wayan suka tsura mata ido.
Cikin kukan da yaci ƙarfinsa yace.
"Allah yayi mata rasuwa."
Sa ke wayan Hajja Inna tayi, tare da sulalewa ƙasa.
Cikin sauri Zakariyya ya ɗauki wayar ya kara akan kunnensa, jin muryan Ya Habu na kuka, yasa aruɗe yace.
"Ya Habu, meya samu Adda Maryam ɗin."
Jin muryan Zakariyya yasa, Yaya Habu cewa.
"Maryam ta rasu Zakariyya, Allah ya karɓi rayuwarta." azabure Zakariyya yasoma girgiza kai, lokaci guda kuma wani irin kuka ya ƙwace masa, nan ya durƙushe gaban Hajja Inna dake kuka, shima kukan yasa me tsuma zuciya, fahimtar abun daya faru yasa Ziyada faɗawa jikin Zakariyyan ta rungumesa tana kuka. Hajja Inna, Zakariyya, Ziyada, duka kuka suke, an rasa mai rarrashin wani acikinsu.
Ya Habu kuwa haka ya dinga ƙiran ƴan uwa yana sanar musu da rasuwan, kowa yaji saiya girgiza, saboda Maryam macece abun soyuwa ga kowa, bata banbance kowa natane.

Nan take labarin rasuwar ya kewaya gaba ɗaya cikin danginsu yan uwa da maƙoto, lokaci ɗaya kuwa iyalan familyn suka ruɗe da koke koke.
Saida Ya Habu yagama sanarwa kowa, kafun yake dannawa number'n Mama ƙira, wayar bata wani jima tana ringing ba Mama ta ɗaga, Kukan da taji Habun nayi ne yasa hankalin ta matuƙar tashi, cikin ruɗewa tace.
"Tun safe nakejin gabana na faɗuwa, Habu faɗamin wani abune ya samu Zaleeha ko?".
Jin abun da ta faɗa yasa Ya Habu sake fashewa da kuka, cikin matsanancin kuka yace. "Mama Maryam ne, Maryam tatafi ta barmu, Maryam tayi nesa damu ta yanda har abada bazamu sake ganinta ba, Mama Allah ya karɓi rayuwar Maryam ɗazun nan, shikenan Mama Maryam tatafi inda bazamu sake ganinta ba...."
Tunda Mama taji yace Maryam ta rasu, shikenan ta daina fahimtan sauran maganganun da yake faɗi, har wayar hannunta ta faɗi kasa batare da ta sani ba, akiɗime ta shiga jujjuya kanta, maganan rasuwan ƴarta ta Maryam ne ke yawo acikin kunnuwanta, ƙafafunta ne sukai mata nauyi, hannu ta ɗaura aka ta saki wani irin fitinannen kuka, wanda yasa Zahira fitowa daga cikin ɗaki da sauri, ganin Maman zaune daɓas aƙasa tana kuka, yasa Zahiran ƙarasowa cikin tashin hankali tace.
"Mama meya faru?." Cikin kuka Mama tace.
"Tarasu Zahira, Maryam ta rasu, tabar mana duniyar."
Wani irin ƙara Zahira tayi take kuma ta faɗi awajen tana kuka.

Can cikin asibiti kuwa Dr. Adnan ne ya nemo ambulance inda aka sanya gawar Maryam aciki.
Da ƙyar Baba Malam ya iya rarrashin Ya Ameenu, sai-dai kuma har yanzu bai-daina kuka ba,
Cikin minti kaɗan saiga Malam Adam yazo, zuwan Malam Adam ɗin shiya taimaka wajen rarrashin Baba Malam da kuma su Ya Habu da Mamy, suka bar kuka, amma Ya Ameenu kam hawaye sun kasa daina zuba, daga cikin idanunsa.
Malam Adam ne yayi duk wani abun da ya dace, shine ma yasanya Ya Ameenu amota, sannan dukansu suka nufo gida.

Nan gidan nasu kuwa tunkan isowan su tuni ya cika da ƴan uwansu na kusa, nan fa kuka ya dawo sabo, kaitsaye falon Baba Malam aka wuce da gawan, nan kan tiles ɗin falon aka kwantar da ita kudu da arewa tana fuskantar gabas Ya Ameenu ne ya zauna inda yasa gawan agaba ya fashe da wani irin kuka, wanda saida yasa kowa kuka awajen, ganin kukan yayi yawane yasa, Malam Adam ya tara gaba ɗaya jama'an gidan, nan ya bawa kowa alƙur'ani, yace sufara karatu, sannan ayanzu Maryam addu'a take buƙata, bawai kuka ba, nan aka fara karanta mata al'ƙur'ani, Baba Malam ne yasa gawan agaba, yana mata karatun al'ƙur'ani hawaye na tsiyaya daga idanunsa, Ya Ameenu kuwa muryarsa kwata kwata ta daina fita saboda tsabar kuka.

Ɓangaren Ameena kuwa, koda taga tafiyan su Baba Malam gida tare da gawan Adda Maryam ɗin, excuse ta ɗauka, dan batajin zata iya zama, mutuwar Adda Maryam ɗin yasa gaba ɗaya jikinta yayi sanyi, koda ta fito daga asibitin, adai-dai-ta sahu ta hau, dan bawani iya mota tayi ba, shiyasa bata fitowa da motar da Saifuddeen ɗin ya saya mata wajen aiki, sannan kuma tasani sarai, duk wani abu na ƙarfe ba karɓanta yake yi ba, da ta fara amfani dashi zai lalace, shiyasa ma kawai ta ajiye motar, gudun kada Motar ta mutu da wuri.

Zaune suke dukansu afalon Ummi suna hira, lokacin dawowar su Saifuddeen da Ahmad kenan daga sallan magriba.
Bakinta ɗauke da sallama ta shigo ɗakin, jikinta amatuƙar sanyaye.
Da mamaki Ummi ke kallonta, dan kuwa tasan bayanzu ne lokacin dawowanta ba, kasancewar duty'n dare takeyi sai nanda kwana uku zata koma na rana, cikin kulawa Ummi tace. "Ameena lafiya kuwa naganki haka asanyaye."
Hawaye ne suka zubo daga cikin idanunta, hakanne yasa hankalin su Ummi tashi, hannu Raliya tasa ta amshi Adeel dake riƙe ahannunta, cikin

Please Login or Register in order to submit comment