Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

duk da cewa aƙauye kike zaune, amma kuma kullum ƙara kyau kike, yanayin shigarki ta kame kai tana matuƙar yi miki kyau."
Murmushi Zaleeha tayi tare da cewa.
"Uhumm kedai Aisha bakya gajiyawa da surutu, kullum ganin kyauna kike ke bakya ganin naki, dan Allah tashi muje, yau kam naƙosa muje gidanku, kodan ma na huta, da gorin da kikemin, kan cewa da kike, wai kullum ni bana zuwa gidanku, saidai ke kizo."
Miƙewa Aisha tayi tana dariya, nan suka fito daga ɗakin.
Babu kowa atsakar gidan, domin kuwa tun safe Elizabet, da kuma Solomon suka tafi church, kasancewar yau Lahadi.
Suna fita Zaleeha ta jawo ƙofar gidan ta rufe, nan suka ɗauki hanya zuwa cikin rugar su Aisha, wanda yake nan kusa bashi da nisa,

Koda suka shiga cikin rugar sosai Zaleeha taji zuciyarta tayi sanyi, sakamakon ganin yanda jama'ar rugar keta hada hadansu, wanda dukansu musulmai ne kana kuma fulani masu mutunci waɗanda hasken addini ya ratsasu, don da ka kallesu zakaga hasken musulunci agoshinsu, idanu ta lumshe, tare da sauƙe ajiyar zuciya, tabbas akullum tana ƙara godewa Allah daya yita musulma, domin kuwa tabbas duk wani addini da ba na musulunci ba, babu komai acikinsa sai ɓata,
musulunci shi kaɗaine haske.
Koda suka ƙarasa gidan nasu Aisha, cikin girmamawa ta gaishe da Innar na Aisha, haka dai suka ɗan gaggaisa da ɗan sauran jama'ar gidan. Nan suka zauna da Aisha'n, suka shiga ɗan taɓa hira.
Sun ɗan jima suna hira ganin cewa la'asar ta kusa ne, yasa Zaleehan miƙewa, nan tace zata tafi, batason yammaci ya mata awaje, Inna Maman Aishan ne, ta bata pure nono cikin wani babban gora, wanda aka zuba zuma acikinsa, Aisha kuwa da kanta ta gasawa Zaleehan naman ƙatuwar Zabuwa, duk yanda Zaleeha taso kin amsa, saida suka sata ta amsa, nan tayi musu godiya sosai, sannan Aisha ta rakota, har kusan wajen rugar, daga haka sukai sallama, inda Aishan tace da Zaleeha sai tazo.

Batayi wani tafiya mai nisa ba ta iso gida, nan ta iske har zuwa wannan lokacin su kawun nata basu dawo ba, ɗakinta ta shiga inda ta aje nama da kuma nonon da suka bata.
Fitowa tayi donyin alwalan sallan la'asar, dai-dai nan Elizabet ta shigo cikin gidan, kamar an jefota ba sallama duk tayi wujiga-wujiga da ita, ƙafarnan tata tayi futu-futu, idanunta kuwa sunyi tsuru tsuru, alamun gajiya da wahala ya bayyana ƙarara ajikinta.
Dubanta Zaleeha tayi, kana ta kau da kanta gefe, da taso yi mata sannu da dawowa, amma tunowa cewa Elizabet ɗin daga church take, hakan yasa ta fasa, zama tayi akan dakali, tare da jawo ƴar butar ta, ta soma al'wala.
Elizabet kuwa kan wani benci dake tsakar gidan ta baje, nan tashiga maida numfashi akai-akai, saikace wacce tayi wasan tsere, amatuƙar gajiye ta ɗago kai ta dubi Zaleeha, wanda ke gudanar da al'wala cikin nutsuwa, ƙura mata idanu Elizabet ɗin tayi, tana me kallon yanda take alwala'n, cikin ranta tace.
"Oo ni Elizabet kalli yanda suke gudanar da ibadansu cikin nutsuwa da kwanciyar hankali da jin daɗi, batare da wani hayaniya ba da ife-ife da raye-rayeba."
Ajiyan zuciya ta sauƙe tare da ɗan gantsarewa dan azabar ciwon da ƙugunta yakeyi sabida wuni rawan da suka wuni tiƙawa a majami'ar bautar tasu.
Duban ƙafanta wanda sukayi suntum tayi, hakan kuma ya farune sakamakon tiƙar rawa da tayi a church, don kuwa tun safe suke rawan bahutu, gaba ɗaya ta gaji.
Idon dai ta zubawa Zaleeha tana ganin yadda take gudanar da harkar ibadarta a mutunce.

Ita kuwa Zaleeha, tana alwalanne amma gaba ɗaya kewar da begen gida da danginta da Baba Malam ne ya cika zuciyarta, sosai takejin kewar mahaifin nata, tana matuƙar son Baban nata ƙwarai da gaske, tabbas ta wani ɓangare tanajin son komawa gida, tana so da ƙaunar taga tayiwa mahaifinta biyayya tana son farin cikin shi dana Ya Ahmad koda irin al'ƙawarurrukan da ya mata, tana jin ciwo a ranta ace da aure a kanta a kuma bata gidanta ɗakinta damahaifinta ya umarceta data zauna lokuta da dama tamkar tayi zama tsuntsuwa tayi fiffige ta koma cikin iyayenta tayiwa mahaifinta biyayya, koda ko sanadin rasa masoyin nata zaisa ta rasa ranta.
To amma hakanan takeji kaman anɗaure ta da jijiyoyin jikinta, wanda takejin kamar dole akai mata zama anan Numan ɗin tanaji a ranta tana son ta koma amman duk sanda ta aiyana haka sai taji kamar a ɗaureta ne, a garin, haka dai ta kammala al'walanta kai tsaye ta wuce ɗakinta,
a nan tabar Elizabet zaune tana ta faman maida ajiyar zuciya.

Sallah tayi sannan ta jawo goran nonon, nan taɗansha kaɗan sosai kuwa taji daɗinsa, kasancewar bata wani jin yunwa yasa ta ajiye, kan cewar sai zuwa dare taci zabuwan da kuma nono'n....

Gombe State.

Kasancewar yau ya kasance litinin, kuma yaune su Adda Rahama zasu wuce Kaduna, daga nan kuwa Abuja zasu inda zasu ɗau lefen agidan Ya Ahmad, sukai zuwa gidansu Ameena.
Ƙarfe 9 dai-dai dukansu suka hallara afalon na Ummi, Adda Rahama, Goggo Dada, Ahmad da kuma Hayatuddeen, sune wanda zasu tafi, tun ƙarfe 8 Raliya ta gama musu break fast, inda sukaci suka ƙoshi, ƙarfe goma dai-dai jirgin dazai kwashesu zuwa Kaduna zai tashi, hakan yasa tuni suka kammala duk wani shirye-shiryensu, ɓangaren Saifuddeen kuwa, yana can part ɗinsa, baimasan wainar da suke toyawa ba.

Kasan cewar lokacin ana tsaka da gyara Airport ɗin Abuja shine ya basu damar samun jirgin kaduna kai tsaye.

Raliya da kuma Ummi sune sukai musu rakiya, har zuwa airport, kamar yanda yake arubuce kuwa ƙarfe 10 dai-dai jirgin nasu ya tashi.

Kwata kwata tafiyar mintuna 46 jirgin nasu yayi, ya iso cikin airport ɗin garin Kaduna, koda suka sauƙo daga cikin jirgin nan suka iske Saminu najiransu, wanda shi da kansa yazo ɗaukarsu, sunyi farin ciki sosai da ganin juna, nan ya kwashesu cikin motarsa, suka nufi gidansa.

Adda Rahama na shiga cikin gidan, Raihana ta rungumeta cikin tsananin farin ciki, itama Adda Rahaman rungume Raihanan tayi, don kuwa tayi kewarta, Hayatuddeen ne ya zumɓura baki tare da cewa.
"Wayyo Adda Raihana ni bazaki rungumeni bane, kodai bakiyi kewata bane?."
Dariya Raihana tayi tare dajan kumatunsa, cikin tsokana tace.
"Ƙato dakai ne zan rungume ka, kaikam ai saidai ma nasa maka duka, kancewa ka shigomin gida, ƙato dakai, ai da katsaya daga waje."
Dariya suka sanya su duka, Hayatuddeen kuwa, sake tunzura baki yayi, tare da faɗin.
"Ae dama batun yauba nasan Raliya tafiki sona."
Jin haka yasa Adda Raihana'n jawo hannunsa, cikin ƙaunar autan nasu, ta rungumesa, cikin son sanyaya masa zuciya tace.
"Inasonka mana autan Ummi, ai kowa ya soka bayana ne, saboda kai fa yasa na shirya lafiyayyen girki, harma fa ferfesu nayi maka naka kai kaɗai na musamman."
Jin haka yasa Hayatuddeen sakin murmushi mai ɗauke da tsananin farinciki.
Cikin jin dadi yace.
"Yesss shiyasa nake ƙara sonki Adda na, saboda koba komai kinfi su matar o'o kirki."
Yaƙare maganar yana me satan kallon Ahmad.
Dariya suka sanya don sarai sun gane dawa yake.
Ahmad kuwa ƙwafa yayi inda yace.
"Zamu koma ne yaro zakayi bayani agabanta."

Nan dai suka zazzauna inda Raihana ta cika musu gabansu da kayan ciye ciye, haɗi dasu drinks.
Saida sukaci abincin suka ƙoshi sannan, suka kimtsa don kama hanyar Abuja. Inda Ahmad ya ɗauki ɗayar motar Saminu, wanda ya ɗauki Goggo Dada da kuma Adda Rahama acikinsa, sai kuma Saminu wanda ya ɗauki, Hayatuddeen da kuma Matarsa Raihana.

Kasancewar tsakanin Abuja da kuma Kaduna babu wani nisa, hakan yasa suka isa dai-dai an idar da sallan Azahar.
Kaitsaye unguwar Wuse zone 2 suka nufa, wanda anan gidan Ya Ahmad yake.
Koda suka ƙarasa gidan sun samu tarba me kyau daga wajen Aunty Lubna, sunkuwa ji daɗi ƙwarai, nan tafito musu da kayan auren suka gani, sosai suka yaba, don ƙwarai kayan sunyi kyau.
Kimtsawa itama Aunty Lubna'n tayi, inda cikin motarta su Hayatuddeen suka loda akwatunan.
Kaitsaye suka nufi Asokoro wato gidansu Ameena.

Horn sukayi inda maigadi ya wangale musu gate ɗin gidan, suka shigar da motocinsu ciki. Tabbas gidan yayi kyau ba laifi, sannan suma masu kuɗi ne.
Wata matashiyar Mata itace ta fito zuwa compound ɗin gidan, nan tayiwa su Adda Rahama jagora zuwa cikin gidan, yayinda driver da kuma mai bawa flowers ruwa sune suka shiga jidon akwatunan suna shigarwa zuwa falon gidan.
Koda su Adda Rahama suka ƙarasa zuwa cikin gidan, sun samu tarba mai kyau, cikin karramawa matan da suka samu acikin falon suka tarbesu.
Nan dai suka zauna inda suka gaggaisa.
Take kuwa aka cika musu gaba da kayan shaye shaye.
Bayan sun ɗan nutsane.
Adda Rahama ta gabatar musu da kayan, nan suma suka yaba sosai, haka dai suka ɗan taɓa hira cikin mutunta juna.
Koda suka tashi tafiya haka aka cika musu bayan motarsu da kayan ciye ciye.
Nan dai suka rabu cike da ganin mutumcin juna.

Duk wannan wainar da ake toyawa Ameena na kwance aɗaki tayi ƙumus, zuciyarta cike take da ɗanyar farinciki, ji take kaman tafi kowa sa'a aduniya, bazata iya misalta daɗin da takeji ba, tabbas babbar nasarace samun Saifuddeen amatsayin miji.

Su Adda Rahama kuwa, gidan Aunty Lubna suka koma, nan dai suka ɗiba mata kayan ciye ciye dana shaye shayen da aka haɗosu dashi.
Basuwani jima agidannata ba suka kamo hanyar Kaduna.

Can gidan su Ameena kusa, ƙwarai sun yaba da kayan, kasancewar sanin Ameena ba budurwa bace, hakan yasa basui tunanin dangin Saifuddeen din zasuyi mata wannan karamcin ba.
Koda Momma taƙirawo ta akan cewar tazo taga kayan, koda tagani taji daɗi ƙwarai, don harta farincikinta saida ya kasa ɓoyuwa, Allah kawai take ta godewa acikin ranta.

Can Kaduna kuwa, gaba ɗayansu zaune suke afalon Raihanan, inda suke ta hiransu, Hayatuddeen ne yasaka bowl ɗin snacks agaba yanaci kana yana yagan cinyar kaza, sai wani jijjiga kansa yake, yana lashe red lips ɗinsa, wanda suke shige dana Hamma Saifuddeen ɗinsa.
Dubansa Adda Rahama tayi, cikin zolaya tace.
"Aikin ka kenan autan Ummi ci, acici kazar birni, niko da ace halittarka mai ƙiba ne, sannan ci nasa ƙiba, tabbas Hayatuddeen da yanzu girman jikinka ya cika falon nan."
Idanunsa ya zazzaro waje.
Cikin shagwaɓa yace.
"Haba Adda saikace Yaya Saminu."
Dundu Raihana takai masa tare da cewa.
"Mijin nawa?."
Dukansu suka sa dariya.
Ahmad kuwa cewa yayi "Kaɗan ma kika gani indai Hayatuddeen ne."
Shima dariyar yayi kana yace.
"Ya Wareesu fa nake nufi."
Haka dai sukaci gaba da hiransu, har aka ƙirayi sallan magriba.
Saida sukayi sallan Isha kafun suka zauna inda suka sake kafa sabon hira.
Haka dai sukaita hira har kusan goman dare, dagananne kowa ya nemi makwanci, Inda Ahmad da Hayatuddeen suka shiga cikin wani extra ɗakin dake cikin falon, Su Adda Rahama, da goggo Dada ma ɗaki guda aka basu. Domin kuwa gidan na Saminu akwai yalwatattun ɗakuna.

Washegari da safe kuwa, Raihana lafiyayyen break fast ta shirya musu, inda suka cika cikinsu, nan kuma suka soma shirye-shiryen tafiya, don yau ɗinma jirgin ƙarfe 10 zasu bi zuwa Gombe.
Saminu ne ya kaisu airport wanan karon hadda Raihana tayi musu rakiya.
Basu bar airport ɗin ba kuwa saida suka ga tashin jirginsu, sannan suka dawo gida.

Ƙarfe sha ɗayan rana acikin garin Gombe tayi musu, inda Sule driver yazo da babbar motar Saifuddeen har airport ya kwashesu zuwa gida.
Afalon Ummi suka baje, wanda nan suka samu Saifuddeen zaune akan wheellchair dinsa, yana shan yogo fruit wanda Ummi ta haɗa masa, yayinda tasashi agaba sai tarairayarsa takeyi kamar wani ƙaramin yaro, shikuwa dama aikinsa ne shagwaɓa hakan yasa ya narke mata.
Sam abun baya bawa su Adda Rahama mamaki, saboda sun san ƙaunar dake tsakanin Ummi da kuma Saifuddeen mai ƙarfi ce.
Nan dai suka shiga labartawa Ummi, irin tarban mutumcin da suka samu daga wajen dangin Amina.
Jin suna ta yaba kirkin dangin su Ameenan yasanya Saifuddeen kauda fuska, nan yamaida hankalinsa ga tv, don bama yason fahimtar mai suke faɗa.

Anan dai Adda Rahama tayi sallan La'asar kafun Dr Adnan yazo ya ɗauketa.
Goggo Dada ma ɗakin Ummi ta wuce don hutawa, shi kuwa Hayatuddeen sama ya haura, yana shiga ɗakinsa ya jawo wayarsa, data ya kunna sannan yashiga cikin Whatsapp ɗinsa. Nan ya iske saƙon Ameena. Inda tace.
"Hey ƙanina." Ganin tana online yasashi sakin murmushi, nan yayi mata reply da cewa.
"Sannu me wayo, wato kinma fara ƙirana da ƙaninki ko, saboda kinsan kinyi nasara, zaki auri handsome ɗin Hammana."
Ameena dake kwance ganin saƙon Hayatuddeen din yasa ta saki murmushi, harda dariya. Cikin kulawa tace.
"Dama na faɗa maka ae watarana insha Allah zan zama auntynka saboda haka biyayya dole."

Koda Hayatuddeen yagama karanta saƙon dariya sosai yayi, nan dai ya tsaya suka ɗan taɓa hira da Ameenan, daga ƙarshe ganin ta sauƙa online, yasashi maida hankalinsa wajen chatting da abokansa.

Yau kwana Uku kenan dakai lefen Ameena, har zuwa yau kuwa ko da sau ɗaya ne Saifuddeen bai taɓa tura mata saƙo ba, harkokin gabansa ma yake, yayinda ya watsar da batun auren acikin ransa. Inda yanzu auren ya kama saura kwana takwas kacal, domin dasa lokacin auren zuwa yanzu anci kwana shida acikin kwanakin bikin.

Adda Rahama da kanta taƙirayi Ummi inda tace ta tambayi Saifuddeen, ko yayi mgna da Ameena'n, sai alokacinne ma Ummi ta farga.
Aikuwa tana aje wayan, ta dubi Hayatuddeen dake kwance akan doguwar kujera yana chat.
Cikin kulawa tace.
"Hayatuddeen ƙiramin Hamma'n ka."
Take kuwa ya miƙe, inda ya nufi part ɗin Hamman nashi.
Koda yaje afalo ya iskesa, zaune akan wheellchair, inda yake sanye da dogon wando da kuma wata farar t shirt, laptop ɗinsa ne agabansa yana ta faman dannawa yana ta murmushin ganin amsar saƙon da ya kai kwana goma da turawa Zaleeha shi da numbarsa ta sirri in da ya nuna mata shi saurayine kuma yana sonta, to bata duba saƙonba sai shekaran jiya, bata kulashiba kuma sai yanzu da ya sake ce mata.
"Hello my love". Koda ta buɗe saƙon sai yaga ta turo mishi amsa.
"Wa iyazubillahi, kai wanne irin mutunne da zaka rasa wanda zaka so da bibiya sai matar aure, nayi block naka tun randa naga saƙonka sai kuma naga ka kuma min mgna ban san kai waye bane dake iya sarrafa na'urar da ba tasaba, na haɗaka da Allah da Manzonsa kada ka sake yimin mgna ni matar aurece, kaji tsoron Allah ka rabu dani!".
Murmushi yaketayi yana mai-maita karanta saƙonta, yasan dole tayi mmkin cewar tayi blocking nashi kuma taga ya sake mata mgna. A ranshi yake cewa.
"Baki san cewa nike sarrafa wayarki ba."
Saƙon Ummin Hayatuddeen yasanar masa, sannan ya juya ya fita.

Bai wani ɓata lokaci ba, ya nufi ɓangaren Ummin nasa bayan ya rufe system ɗin nashi.

Tana nan zaune akan kujera, tana ganinsa taɗan sanja yanayin fuskarta, sarai tasanshi dayaga murmushi akan fuskartata, to tabbas tasan zai ɗauki maganar da zata faɗa masa amazaunin wasa kuma zai samu damar shigar da ƙorafinshi.
Dubansa Ummin tayi bayan ya ƙaraso gabanta.
Cikin kulawa tace.
"Daga ranan dana baka number'n Ameena kawo yau sau nawa katura mata saƙo?."
Gane abun da ta faɗa yasashi kwaɓe fuska, tabbas yasan dama watarana za'ayi haka.
Ganin yanda ya kwaɓe fuska yasa Ummi cewa.
"Au baka tura mata saƙon ba kenan?."

Kansa ya jinjina alaman "Eh." danshi dama kwata-kwata bai iya ƙarya ba, sannan kuma koda wasa baya yiwa Umminsa ƙarya.

Duban sa Ummi tayi tare da cewa.
"To lallai katabbatar da yau katura mata saƙo, ko ka manta cewa aurenta zakayi ne?."

Fuska ya sake kwaɓewa, tare da ɗan ciza kyawawan laɓɓansa, shikam yaga takansa da wannan liƙaƙƙen auren, hakanan an tilastashi auren wata mayyar yarinya, gashi tun ma bata shigo cikin gidan nasu ba, Umminsa ta fara takura masa akanta.

"Kajini dae kam ko?."
Ummi ta katse masa tunanin da yake.
Kansa ya jinjina mata alaman yaji.
Daga haka Ummi batace dashi komai ba, ta juya inda ta wuce ɗakinta, idanunsa yaɗan lumshe tare da buɗesu alokaci guda, kallonsa ya mayar ga Hayatuddeen wanda gaba ɗaya hankalinsa nakan wayarsa, sai murmushi yake yi, da'alama wani abun yake.
Ƙura masa idanu yna ƴan wasu mintuna Saifuddeen yayi, kana ya girgiza kansa, cikin nutsuwa ya tura kekensa inda yabar falon.

Bayan yadawo Sallan Isha ne, yaje part ɗin Ummin coffee ya amso tare da dawowa part ɗinsa, wayarsa ya ɗauka inda ya shiga cikin Whatsapp chat ɗinsa.
Contact ɗinsa yabi inda ya laluɓo numbern Ameenan, da yayi seven ɗinta da sunan *Ta'annabi* a cewarsa wai sadaka za'a kawo misho ita shiyasa ya raɗa mata sunan Ta'annabi.
ido ya ɗan zuwa no tata wanda hoton ta nema akan profile picture ɗinta. View ɗin hoton yayi, inda ya ƙurawa hoton ido.
Sosai tayi kyau a hoton don tasha adone cikin wani jan lace, sannan fuskartan nan tayi fayau, don tana murmushi ne aka ɗauketa hoton, taɓe baki yayi tare da maganar zuci, mayya ko me ya tuno kuma sai yayi murmushi sannan ya rubuta mata saƙo kamar haka.
"Slm".
Ameena wanda kusan always tana online, kwance take akan gado, kamar da wasa kuwa taga numbern Saifuddeen ɗin yayi mata magana, azabure tatashi ta zauna, cikin zumuɗi tace.
"Wayyo Allah ni daɗi kasheni, nakarɓi numbern ka wajen Hayatuddeen inason yi maka magana, sai gashi kai ka rigani."
Cikin sauri ta amsa masa da.
"Wslm".
harma da ƙarin tambayarsa.
"Ya gida."

Yana karanta saƙon nata, yaƙara taɓe laɓɓansa, cikin zuciyarsa yace.
"Su mazari, daga magana sai amsa babu ɗan jan aji kamar ba maceba."
Ɗan jim yayi, cikin rashin sabo ya rubuta.
"Ykk." Sannan ya tura mata.
Lumshe idanu Ameena tayi tsabar daɗi, cikin mamaki tace.
"Wai yau ni Ameena Saifuddeen ke tambaya ya nake?."
Cikin sauri tayi typing.... "Lafiya ƙalau ya aiki, yasu Ummi?."

Saida yayi kusan 3 minute bai buɗe saƙon ba, kafun daga bisani ya buɗe.
Koda ya karanta ataƙaice yace.
"Lfy." Ya amsa ataƙaice.
Sanan ya kuma rubuta.
"Meyasa kika amincewa Aurena, bayan kinsan da cewa, ni kurma ne, sannan kuma bana iya tafiya?."

Ganin tambayar tasa yasa Ameena sakin murmushi, abayyane tace.
"Kaiɗin nakeso Saifudeen ina matuƙar sonka, inasonka fiye ma da yanda nakeson komai."
Arubuce kuwa cewa tayi.
"Nakasa Ba Kasawa Bace, inasonka aduk yanda kake, sannan kuma zan zauna dakai ahaka, aurenka kuma ba kasawa bace."

Koda ya karanta saƙon idanunsa ya lumshe tare dayin shiru, kamar zaice wani abu kuma, ataƙaice ya rubuta.
"Okay saida safe jekiyi bacci."
Daga haka ya kashe data'n sa, tare da aje wayan gaba ɗaya.
Inda ya haurawa saman gado ya kwanta.
A ranshi yake cewa.
"Hmmmm kina dai da abin da kikeso a jikina, fitinanniya kawai mai idon cin maza."

Ameena kuwa ganin ya sauƙa online yasa ta lumshe idanunta, daɗi da farin ciki su suka cika zuciyarta, haka tayita juyi akan gadon, wani irin shauƙinsa ne ke damunta, da haka tayi bacci.

Tabbas akullum kwanaki ƙarewa suke, haka kuma lokaci na shuɗewa, akwana atashi asaran me rai, yau dai ya kama saura kwana uku kacal bikin Ameena da Saifuddeen.
Inda daga ɓangare biyu na gidajen duk shirye shiryen bikin suke.
Babu ma kamar gidansu Ameena, inda Ameena'n ke karɓan gyara na musamman, sosai ake mata gyaran jiki, hakan yasa fatarta tayi fresh.

Ɓangaren gidansu Saifuddeen kuwa, su Ummi ne kaɗai ke kiɗa da rawansu, Saifuddeen iyakacinsa ido, tunkuwa ranan da yayiwa Ameenan magana ta Whatsapp baisake bi ta kanta ba.

Zaune suke su dukansu Afalon Ummi, nan Ahmad ya shigo inda yake ƙara sanar dasu batun tashinsu don dama ya kammala gidansa tuntuni, Nan fa Saifuddeen ya kafe kan cewar Ahmad ɗin babu inda zaije, ae tunda ya saka baki ake ƙoƙarin yi masa auren dole dolensa kuwa ya zauna agidan.
Duk kuwa yanda Ahmad yaso Saifuddeen da Ummi su barshi ya koma gidansa sun ƙiya.
Nandai Saifuddeen yace Hayatuddeen ya dawo ƙasa, su kuma Ahmad ɗin su koma sama.
Hakan kuwa akayi, inda aka gyara duka ɓangare biyun, Raliya ta tattaro kayanta suka dawo sama.
Hayatuddeen kuwa ƙasa ya dawo.

Can ɓangaren su Ahmad ɗin kuwa aka gyarawa Amarya Ameena.

Sannu-sannu bata hana zuwa saide adaɗe ba'a je ba.
Rana kuwa bata ƙarya.
Yau yakasance Alhamis, inda gobe Jumma'a ɗaurin auren Saifuddeen da Ameena.
Acan Abuja yau Ameena ta gudanar da walima, inda aka yi wa'azi mai ratsa jiki, sosai kuwa waliman ya ƙawatar, don Ahmad dakansa ya tura mata kuɗi a account ɗinta, inda yace tayi duk wani hidima da takeso. Kana kuma yaune akaiwa Amarya jere, domin kuwa Babanta da kansa yayiwa kamfanin masu saida furnitures magana, ta online suka sai kayan, wanda Ameenan da kanta ta zaɓi kalan da takeso.
Ma'aikatan kamfanin kuwa suda kansu suka zo har gidan su Saifuddeen ɗin suka jera mata kayanta, sosai kuma yayi kyau.

Washegari.
Jumma'a.

Ranan yau takasance jumma'a, wanda kuma ayau ɗinne za'a ɗaura Auren Saifuddeen da kuma Ameena.
Tun safe kuwa Saifuddeen yaƙi fitowa, inda ya ce bashi da lafiya, sanin cewa Ameenan ba budurwa bace, kana kuma ba agari za'ai ɗaurin auren ba, yasa sam su Bappa Ali basu matsa masa ba.

Ƙarfe tara dai-dai jirginsu zai tashi.
Baba Malam, Bappa Ali, Dirankadi, Malam Adam, Baba Bello, Ishaq, Ahmad, Wareesu, Saleesu, Hayatuddeen, sune waƴanda zasuje ɗaurin auren, sai kuma Adda Rahama da Aunty Meena, wanda sune zasu ɗauko amarya.
Ƙarfe tara acikin jirgi tayi musu, inda suka ɗaga zuwa garin na Abuja.

Sun isa Abuja ƙarfe goma dai-dai, inda kuma za'a ɗaura auren ƙarfe 11 na rana dai-dai.
Ya Ahmad ne yazo ɗaukansu kai tsaye Asokoro gidansu Amarya suka nufa.
Nan suka tarar da ƙofar gidan ɗinke da jama'a, ƴan ɗaurin aure.
Alhaji Naseer da kuma mahaifin Ameena Alhaji Sadam su suka tarbesu cikin mutum tawa, inda su Adda Rahama kuwa suka wuce cikin gidan.

Kamar yanda aka sanya lokaci, ƙarfe sha ɗaya dai-dai jama'an dake wajen suka shaida ɗaurin auren Saifuddeen da Ameena, akan sadaki naira dubu hamsin.
Nan fa jama'a suka dinga sanya alkahiri, da nema musu zaman lafiya.

Acan cikin gida kuwa, amarya Ameena tayi kyau don an tsantsara mata meckup dai-dai misali, inda ta suturce jikinta da shiga ta al'farma, balaifi tayi kyau don kuwa sam bata da muni, saidai kuma bata da azababben kyau.

Jirgin ƙarfe ɗaya zasu biyo don dawowa Gombe, hakan yasa Dady wato Alhaji Naseer da kuma mahaifinta suka jata gefe inda sukayi mata nasiha sosai mai ratsa jiki.
Harma da ɗan guntun ƙwallanta.
Daga haka su Adda Rahama suka kamata, inda aka sanyata a mota, ƴan uwanta biyu ne zasuyi mata rakiya.
Akwai auntynta wanda ake ƙira da Aunty Zubaida, sai kuma ƙanwar mamanta, Aunty Zainab, nan dai suka ɗunguma dukansu zuwa airport.
Ƙarfe ɗaya kuwa dai-dai jirginsu ya tashi, zuciyar Ameena cike da kewar gida.

Sun iso cikin garin Gombe lafiya, inda lafiyayyun motoci har guda shida suka zo ɗaukarsu, Baba Malam dai kaitsaye gidansa aka wuce dashi shida Malam Adam, sai kuma Dirankadi da Ishaq, wanda suma kaitsaye gida suka wuce.

Koda suka ƙaraso, sosai ƴan uwan Ameenan suka yaba da kyaun gidan nasu Saifuddeen, nan dai kaitsaye part ɗin Ummi aka wuce da ita.
Tarba mai kyau Ummi tayi musu, tare da nuna musu ƙauna, haka ta jawo Ameenan jikinta cikin kulawa tayi musu addu'an samun zaman lafiya, da kuma zuri'a ta gari.

Daga nan kuma Adda Rahama tayi musu jagora zuwa ɓangaren Ameenan.
Nan ma sun yaba da tsaruwan part ɗin nata.

Kasancewar waƴanda sukai mata rakiyan ba kwana zasuyi ba, ƙarfe 5 na yammaci dai-dai sukabi jirgi inda suka koma Abuja.

Nan fa akabar Amarya Ameena ita kaɗai aɗakinta.

Yayinda ƴan tsirarun mutanen da sukazo bikin, tuni suma sun koma, domin dama Ummi batayi wani gayya ba, Aunty Mina ma tabi Bappa Ali sun koma dukku.
Haka gidan ya rage, daga Ummi, Adda Rahama, sai Raliya da kuma Hayatuddeen.
Shikuwa Saifuddeen tuni dama yana ƙule acikin ɗakinsa.


Koda akayi sallan Isha kuwa, saiga su Ahmad da Ishaq wai sunzo yi masa rakiya zuwa ɗakin amarya, abun ma dariya ya basa, nan dai ya haɗe gabar da yamma, inda yace.
"Baya buƙatar rakiyan nasu."
Duk yanda sukaso rakasa wajen Amaryar ƙiyawa yayi.
Haka suka tafi suna masa dariya.

Part ɗin Ummi ya nufa inda yasamesu zaune su dukansu afalo.
Cikin salon shagwaɓansa, ya dubi Ummin, gane abun dayake nufi yasa tace da Raliya ta ɗauko masa flask ɗin coffe ɗinsa, don dama tuni ta haɗa masa.
Yana amsa kuwa ya juya inda ya nufi part ɗinsa.
Ta ɓangaren Zaleeha yabi inda yashiga falonsa, kai tsaye ɗaki ya wuce, kayan jikinsa yaɗan rage sannan yasha coffee ɗin, kan gadonsa ya haye tare da rufawa kansa blanket, sam babuma maganar zuwa wajen Ameena acikin ransa, don kuwa ko Zaleeha dayake mutuwar so, ranan farko baije ɗakinta ba balle wata Ameena da yasan jira take ta ganshi ta mishi fyaɗe dan ya dai san abinda take so.

Can ɓangare Ameena

Please Login or Register in order to submit comment