Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hau, jikinsa na rawa ya nufi toilet ɗin.
Zuwa lokacin kuwa gaba ɗaya ta galabaita, dan har ta durƙushe akan ƙafafunta, dan kuwa amai ɗinta na uku kenan. Da sauri ya ƙaraso cikin toilet ɗin, hannayensa yasa duka biyu ya ɗagota jikinsa, dai-dai lokacin kuwa wani sabon amai ya sake zuwar mata, saida ta amayar da duk wani abu na cikinta, faɗawa jikinsa tayi tana me fitar da nishin wahala, dan ta jigata ƙwarai, hankalinsa ne yayi matuƙar tashi, tallafo haɓarta yayi, cikin body language ɗinsa yace.
"I'am sorry my happiness, am so sorry, sannu ko kinji, dama baki da lafiya ne? tun yaushe kika fara amai? please tell me what happened dear?." Idanunta wanda sukayi narai narai dasu ta ɗan juya, awahalce tace. "Wayyo Hamma Saif jiri nakeji, sannan inajin kaman zan amayar da ƴaƴan hanjina, please helf me."
Cikin matsanancin tausayinta in boddy language yace.
"Oh My God am sorry kinji, zaki samu sauƙi insha Allah, taso na wanke miki jikinki kinji My Love ɗina, yanzu 2am, da sasssfe zan ƙira Dr. ya dubamin ke." Kanta kawai ta iya jinjina masa, cikin kulawa kuwa ya ɗagota, inda ya wanke mata jiki da kuma bakinta, ɗagota yayi jikinsa kaman ƴar baby, haka suka fito daga bathroom ɗin tana liƙe ajikinsa, jin jikinta da zafi ya sa ya shumfuɗeta akan gado, tare da bin bayanta ya kwanta, acikin jikinsa ya sata, yana me shafa bayanta ahankali, kasancewar yaɗanji jikinta da zafi. Sake lafewa ajikinsa tayi, tare da sakar masa sassanyan kukan shagwaɓa. Jin sheshsheƙan kukan nata ya sashi hugging ɗinta tide, ahankali ya zura harshensa acikin kunnenta yana ɗan lasa. Hakanne yasa tun tan kukan ahankali, har tayi lub ajikinsa, wani wahalallen bacci ne ya ɗauketa, ganin tayi bacci ya sashi shima ɗan lumshe idanunsa.
Ai kuwa baccin nata baiyi nisa ba, wani sabon amai ya sakota gaba, da sauri ta yunƙura ta sauƙa daga kan gadon, saidai tun kafun ma ta ƙarasa toilet ta riga da ta sheƙasa akan tiles.
Hankalin Saifuddeen ne yayi masifar tashi, dan yaga yanda take kwara ama'n, gaba ɗaya babu ƙarfi ajikinta, duk tayi weak, saida ya bari ta gama, sannan ya gyara wajen, ɗaukanta yayi ya maida ita kan gado, zama yayi sannan ya ɗaura kanta akan cinyarsa, sosai yakejin wani irin matsanancin tausayinta.
Itakuwa zuwa yanzu ko ƙarfin kirki bata dashi, hakanne yasa take ta faman sauƙe ajiyar zuciya akai akai, tana kuma ɗan numfasawa awahalce.
Suna nan zaune ahaka har aka ƙira sallan asuba, da ta fara bacci amai zai taso ta gaba, dole kuma saitayi take ɗan samun relief, ganin ta soma bacci ne yasashi janye jikinsa, toilet ya shiga yayi alwala, yana fitowa kuwa jallabiya ya zura ajikinsa, saida yayi kissing ɗin goshinta, sannan ya fice daga cikin ɗakin. Kaitsaye sashin Ummi ya nufa, ba kowa afalon sai sautin A/C dake tashi, ƙarasawa jikin ƙofar Ummin yayi, tare dayi mata knocking, Ummi wanda fitowanta daga toilet kenan ta ɗauro alwala, jin ana buga ƙofar ɗakinta yasa ta ƙarasowa ta bude, ganin Saifuddeen yasa tayi mamaki ƙwarai, dan tasan baya taɓa zuwa gaisheta sai ya dawo daga masallaci, cikin yanayin mamaki tace. "Saifuddeen lafiya kuwa, naganka adai-dai wannan lokacin?." Ɗan shagwaɓe fuskansa yayi, cikin bayyana damuwarsa yace. "Ummi Zaleeha ne bata da lafiya, tun cikin dare take ta amai, gashi jikinta duk ya ɗau zafin zazzaɓi." Idanu Ummi taɗan zaro, cikin jimami tace. "Subahanallah amai kuma? dama bata da lafiya ne?."
Narke fuska yayi akasalance yace.
"A'a Ummi lafiyanta fa ƙalau har muka dawo daga wajen diner." Ɗan jim Ummi tayi tare da cewa.
"To bari nayi sallah sai naje na duba ta ko, amma kafun nan kaƙira Dr. yazo ya duba ta." Kansa ya jinjina, sannan ya juya ya koma cikin falon, wayarsa ya ciro tare da dannawa number'n Dr.Adnan ƙira, ringing biyu kacal Dr.Adnan ya ɗaga wayan. Bayan sun gaisane Saifuddeen ɗin keyi masa bayanin rashin lafiyan Zaleeha'n, cikin tausayawa kuwa Dr.Adnan ɗin yace idan ya idar da sallah zaizo saiya duba ta, da haka sukayi sallama Saifuddeen ɗin ya wuce masallaci. Koda aka idar da sallan baiwani tsaya acikin masallacin ba, dan bayaso yayi nisa da Zaleehan, koda ya koma ɗakin nasa har yanzu tana nan ayanda ya barta, har yanzu kuwa sama sama take fitar da numfashi.
Akusa da ita ya zauna, cikin lallami ya tasheta, ahankali taɗan bude idanunta, kanta ya shafa, cike da soyayyarta ya mata mgna da yarensu. "Sannu ko dear, tashi kiyi sallah kinji, ya jikin naki?."
Kai kawai ta iya gyaɗa masa alaman.
"Da sauƙi." Hannunta ya kama suka wuce bathroom shi ya taimaka mata ta ɗauro alwala, shida kansa kuma ya sa mata hijab ta tada sallah, koda ta idar da sallan jingina kanta tayi ajikinsa, har yanzun dai jiri take ji, ga kanta dake ɗan sarawa, kamo hannunta yayi ya maida ita kan gadon, tare da rufa mata blanket, kallon agogon dake saƙale jikin bangon ɗakin yayi, ganin ƙarfe 5 ɗin asuba, ya sashi sauƙe ajiyar zuciya, dai-dai lokacin kuwa yajiyo knocking ɗin ƙofar falonsu, take kuma wayarsa ta kawo haske alaman shigowar saƙo, koda ya duba saƙon Dr.Adnan ne, inda ya rubuta masa cewa.
"Na iso."
ahankali yake sarrafa wheelchair ɗinsa, har ya fice daga cikin ɗakin, dakansa ya ƙarasa jikin ƙofar falon ya buɗe, ganin Dr Adnan tsaye yasashi ɗan sakin murmushi tare da bashi hannu sukayi musabaha, iso yayiwa Dr.Adnan ɗin har cikin ɗakin nasa, Ƙarasawa jikin gadon Dr.Adnan yayi, anutse ya ƙira sunanta, jin muryan Ya Adnan ɗin yasata ɗan ɗago kanta, kansa yaɗan jinjina cikin kulawa yace.
"Sannu ko, ya jikin naki?." Kanta taɗan jinjina masa alaman da sauƙi, ɗan ƙaramin jakan dake hannunsa ya ajiye, yana ƙoƙarin saka hand clobes ahannunss yace.
"Ina da ina ke miki ciwo?."
awahalce taɗan karyar da wuyanta, murya asanyaye tace.
"Amai da jiri nakeji, sai kuma tashin zuciya da zazzaɓi, gashi bakina duk ba daɗi".
Idanu yaɗan zuba mata, lokaci guda kuma sai ya ɗan saki murmushi, bargon da take rufe dashi yaɗan yaye, hannunta ya kamo tare ɗa ɗaura mata wani abu kaman igiya, ganin ya fito da allura ne yasata rumtse idanunta da ƙarfi tare dasa hannu ta riƙo hannun Hamma Saif ɗin.
Jininta yaja sannan yayi mata wata allura, wanda yasan zata ɗan taimaka mata, dai-dai lokacin Ummi da Raleeya suka shigo cikin ɗakin, amutumce suka gaisa da Dr.Adnan ɗin, nan yace musu zai koma asibiti dan yanaso ya gwada jininta daya ɗiba,
"to" sukace sannan ya fita.
Ummi ne ta ƙaraso jikin gadon, kan Zaleehan ta shafa, cikin kulawa tace. "Ayya Zaleeha sannu kinji, ya jikin naki?."
Jin muryan Ummi ya sa ta buɗe idanunta ashagwaɓe tace.
"Da sauƙi, amma Ummi jiri fa nakeji kuma har da amai".
dagajin yanayin maganan nata kasan ba iya zafin ciwo bane, harda zallan shagwaɓa ne da raki.
Sake shafa kanta Ummi tayi cikin kulawa tace. "Sannu ko, zaki samu sauƙi insha Allah." Raleeya ne tayi mata ya jiki, jinjina mata kai tayi alaman da sauƙi.
Zama sukayi awajenta suna ƙara shagwaɓata da kuma tattalinta, Saifuddeen ma kasa barin ɗakin yayi, idanunsa kawai ya zuba mata, ita kuwa kasancewar alluran da Dr.Adnan yayi mata nada ƙarfi, hakan yasa wani irin bacci me nauyi ya ɗauketa. Ba'awani ɗau lokaci sosai ba Dr.Adnan ya dawo, fuskarsa cike take da wani irin annuri haɗi da zallan farinciki, ahankali ya buɗe ƙofar ɗakin ya shigo, ganin yanda yake sakin murmushi hannunsa riƙe da wata farar takarda yasa suka zuba masa ido,
Saifuddeen ne ya fara cewa.
"Lafiya kuwa Dr. me yake damunta?." Ƙarasowa cikin ɗakin yayi tare da miƙawa Saifuddeen ɗin hannu, alaman su gaisa, da ɗan mamaki Saifuddeen ya basa hannunsa, cikin bayyana farinciki Dr Adnan yace.
"Congrats Bro, Zaleeha na ɗauke da cikinka almost 2 to 3 month." Tamkar shigar shock haka duka sukaji maganan acikin kunnensu, Jikin Saifuddeen ne ya soma ɓari, cikin matsanancin mamaki, jin abun yayi kaman al'amara, duk da yasan cewa shiɗin baida matsalan rashin haihuwa, amma hakanan yakejin batun cikin Zaleehan kaman amafarki, Allah mabuwayi me yin yadda yaso a lokacin da yaso, yau gashi Zaleeha macen da zuciyarsa ke tsananin so da muradi, tana ɗauke da cikinsa, zamewa yayi daga kan wheelchair ɗinsa yayiwa Allah sujjada, dan nuna godiya da kuma tsantsar farincikinsa. Ummi da Raleeya kuwa ba abun da suke cewa sai.
"Alhamdulillah Masha Allah."
Cike da matsanancin farinciki, Ummi ta dubi Zaleeha, wanda ita bata ma san meyake gudana ba, dan baccinta ya ɗanyi nisa, Murmushi me ɗauke da farinciki tayi, cikin jin daɗi tace.
"Allah sarki Zaleeha yarinyar kirki, Allah Ya miki albarka, ya kuma sauƙeki lafiya".
Sai alokacin Saifuddeen ya ɗago daga sujjadan da yayi, kan wheelchair ɗinsa ya hau, sannan ya ƙaraso jikin gadon, wani irin farinciki ne bayyane akan fuskarsa, rungume Ummin sa yayi ƙam, tamkar wani ƙaramin yaro, cikin kasa ɓoye farincikinsa yace. "Alhamdulillah, Ummi na kinga Allah me iko ko, yabani kyauta me mahimmanci alokacin da ba zata ba, Ummi ki taɓa zuciyata kiji, har wani tsalle take saboda tsabar farinciki." murmushin jin daɗi Ummi tayi, cikin kulawa tace.
"Nasan kana cikin farinciki Babana, kuma muɗinma hakane muna cikin farin cikin."
Ɗan janye jikinsa daga na Ummi'n yayi, inda ya ƙurawa Zaleeha mayun idanunsa, cute face ɗinta yake kallo, wanda tayi fayau da ita, lokaci ɗaya har taɗan rame. Wani sabon zazzafar soyayyarta da ƙaunarta ne ke ratsa duk jikinsa, haka yakeji kaman ya jawota ya rungumeta.

Fahimtar hakane yasa. Ummi miƙewa,
ta fita cikin jin daɗi, hakama Raliya ta bita a baya,
suka tafi cikin tsananin jin daɗi.

A ɗakin Saifuddeen ɗin kuwa cikin kula ya Adnan ya ɗaura mata wani ɗan leden ruwa ƙarami,
dasa mata alluran cin abinci,
daurewa iya daurewa Zaleeha tayi amman duk da haka saisa ta fidda hawaye da anasa mata allurar ruwan a hannunta,
Hamma Saif kuwa cikin kula da lallama yake in boddy language yake cewa.
"So sorry Sannu ko, da zafi ko? Ya Adnan ayimata a hankali".
Dariya Ya Adnan yayi kana ya tattara kayan aikinshi yace.
"Raki da raki sun haɗu, a kula da cin abin cinta, domin bawai cikinne ya sata amai da jirinba, rashin cin abinci ne yasa yunwa yayi ta murɗanta, yunwarce kuma tasa mata jiri da kasala da duhun da take gani, so dole a kula da ita da cin abinci."
cikin gamsuwa Hamma Saif in boddy language ɗinsa yace.
"In sha Allah zan kula ya Adnan, na lura kam tunda na dawo bata son cin abinci".
ƙarishe haɗa kayanshi yayi kana ya sallamesu ya tafi.

Yana fita Hamma Saif ya hau gadon da kyau, hannunshi yasa yana shafa gashin kanta,
ita kuwa Zaleeha tunda taji Ya Adnan ya ambaci kalmar ciki sai tayi shiru tana bin Hamma Saif ɗinta da ido,
cikin tsananin jin daɗi yayi mata rubutu a wayarshi ya miƙa mata,
"Maman Baby, maman yara Ammin Adeel, my happiness my life my Everything. Ngd Ngd Ngd matuƙa,
Alhamdulillah Zaleeha Allah ya azurtamu da samar da abu ɗaya, jinina da jininki sun kasance a sashi ɗaya, burina da fatana sun cika kina da ciki har na tsawon wata biyu da sati uku".
Sai kuma ya sunkuyo yayi kissing goshinta,
ita kuwa Zaleeha lumshe ido tayi da sauri bayan ta karanta abinda ya rubuta mata,
hannunta tasa bisa lafeffen cikinta, wani irin daɗi farin ciki salama ne suka cika mata zuciya a baiyane tace.
"Alhamdulillah. Allah na gode maka da kyautar da kayi min, ya Allah ka al'barkacin abinda ke cikina,
ka bani shi mai kama da mahaifinsa".
Sai kuma ta ɗan buɗe ido ta, Hamma Saif ɗin nata, rubutun da yayine ta kuma karantawa.
"My dear meyasa!? Meyasa!!? Meyaaa!!!? Baki sanarmin kinada cikiba, meyasa kika ɓoye min abin farin cikinmu?".
A hankali ta kalleshi cikin sanyi tace.
"Hamma Saif nima bansan ina da cikiba".
Da sauri ya rubuta mata.
"Kamar yaya baki sani, tunda bakiga al'darkiba har wata biyu har na uku, ai yaci kisan kinada ciki".
A hankali tace.
"Hamma Saif ni ba ko wanne wata nake al'adaba, ina tsallake wata, wani lokacin har wata biyu nake tsallakewa sai ana uku sai ingani, shiyasa yanzunma da ban ganiba ban damuba dama duk zatona wata ƙil ƙarshen watannan zanyi dan ban taɓa tsallake wata ukuba a tunanina nanda kwana biyar zan gani".
Da sauri yasa hannu ya zare alluran ruwan dan ganin ruwan ya ƙare,
ɗagota yayi ya ruggumeta a jikinshi tsam, yana kissing nata tako ina.

A cikin gida kuwa,
Dr Adnan na fita Ameena na shigowa.
A can falon Ummi kuwa cikin farin ciki Ummi tace.
"Ni dama na daɗe da zargin Zaleeha nada shigar ciki, dan har kamar zan gayawa Saifuddeen sai kuma nace bari dai in barsu inga zasu gane da kansune ko sai an ganar dasu, kuma da yake sabbin shigane duk basu ganeba, kai yarinta da daɗi ƙuruciya dangin hauka.
Hayatuddeen ne da Ahmad dake ta farin cikin labarin suka haɗa baki wurin cewa.
"Au Ummi itama Zaleeha bata san tana da cikinba".
Raliya ce tace.
"Ato da alama kam bata saniba, dan in ta sani ai Hamma Saif zai sani".
Dariya sukayi baki ɗayansu.
Dai-dai lokacin Ameena ta shigo.
bayan sun gaisa da sune ta kalli Hayatuddeen daketa cilla Adeel sama suna dariya tace.
"Autan Ummi yau farin ciki da sassafe babu baƙin halin tashi daga bacci mai ka samu haka?".
Cikin dariya yace.
"Yo Aunty Ameena ai dolena in girma tunda naga kun dage tuƙuru zaku cika mana gida da yara, Adeel zaiyi ƙani ai dole in daina yarinta kada ayi uban banza".
Cikin mmki da rashin fahimta ta kalli su Ummi dake dariyar mgnar Auta, a hankali tace.
" Ummi me muka samune".
Cikin kula Ummi tace.
"Ammin Adeel ne, ta kwana ba lfy, to shine da Yayanku yazo ya gwada yake cewa cikine gareta".
Wani irin sassanyan murmushi Ameena tayi cikin jin daɗi da kekyawan zuciya tace.
"A a Alhamdulillah. Adeel ya girma, ya zama babban yaya, Allah ya sauketa lfy".
Amin Amin suka amsa baki ɗayansu.
Sosai sukayi farin ciki,
Nan Ameena da Raliya suka shiga kitchin.

Ummi kuwa ɗakinta ta koma,
a waya ta sanarwa Raihana dan tasan Adda Rahma kam mijinta zai gaya mata.
ta kuma sanarwa Goggo Dada da Aunty Mina ma sosai yan uwa da abokan arziki sukayi ta murnar cikin.

A can sashin Saifuddeen kuwa,
shi da kanshi ya taimaka mata, a tare sukayi wonka,
kana suka shirya,
rigar daya cire mata ta maida,
daga nan ta nufi ɗakinta dan canza sakekkiyar riga.

Shi kuwa Saifuddeen tana fita ya fara kiran abokanshi yana sanar musu,
sosai sukayi ta farin ciki sunayiwa Zaleeha tsiya wai ai dolema ta gudu ta kuma dawo da kafarta, wai Adeel ne ya korata, cikin kuma shi ya dawo da ita.

Ishaq ne ƙarshen kira dan yasan angone kar ya takurashi da sanyin safiya.

Ishaq kuwa yana jin wayarshi na rigging amman bai samu damar ɗagawa ba,
sabida yana lallaɓa amrya Rashida da yayi mata Dalla Dalla, sabida sam ya kasa ɗaga mata kafa, kun san riƙaƙƙun tuzurai ba sauƙi.

Yana tafe yana kuma gwada kiran Ishaq, yana shiga falonshi Ishaq na amsa kiran cikin tsokana yace.
"Ango kasha mai".
Dariya Ishaq yayi tare da cewa.
"Caɓa-caɓa ma kuwa mai kam harda lagwada, ai da nasan haka abin yake da ɗan karen daɗi da tuntini nayi aure".
Dariya sukayi baki ɗayansu,
Rashida dake manne jikin Ishaq ɗinne ta ɗan sune kanta a jikinshi.
shi kuwa Saifuddeen cikin happy yace.
"Al'bishirinka".
Da sauri Ishaq yace goro".
dariyarsa mai sanyi yayi cikin jin daɗi yace.
"Ka kusa samun ƙanin Adeel, jiya tunda muka dawo Baby keta amai ashe, cikine ni bamu saniba sai ɗazu ya Adnan ke sanar min."
Cikin tsananin jin daɗi Ishaq yace.
"Alhamdulillah, kai nayi farin ciki, kai mutumina ba sauƙi kai ko yaushe bugu ɗaya kake jefa ƙollo a raga".
Dariyar keta Saifuddeen yayi tare da cewa.
"Sune zalamammu daga na basu sai su ƙarɓa, kuma dama Zaleeha kam addu'ar da nayi tayi kenan, har a kaba na roƙi Allah ya azirtamin samun haihuwa da ita akai-akai kafinma ta ankara, gidana ya zame mata farin cikin duniyar ta, ta haifo min yara dozin-dozin".
Dariya sosai Ishaq yayi kana yace.
"Mugu, to Allah ya sanya al'khairi ya sauƙeta lfy".
Amin Amin yace kana sukayi sallama".
Daga nan ya shiga falon Zaleeha a falon suka haɗu cikin kula ya miƙo mata hannu, kana suka nufi falon Ummi.

Suna shiga, duk suka gaggaisa, hannu Zaleeha tasa ta karɓi Adeel dake hannun Hayatuddeen,
cikin kula sukayi mata sannu da jiki.
Ameena da Rayila ne da suka gama shirya breakfast a dinning table suka iso falon cikin sakin fuska Ameena ta kalli Saifuddeen fuska a sake tace.
"Congrats Abban Adeel, Allah ya sauƙeta lfy".
Amin Amin sukace baki ɗayansu,
Ita kuwa Zaleeha sunkuyar da kanta tayi ƙasa cikin tsananin jin kunya.
Shi kuwa Saifuddeen wani irin fitinenne kallo yakewa Ameena kallo mai cike da mutun taka, ji yake tamkar ya kamota ya ruggumeta, amman ba dama, ita kuwa ganin kallon da yake matane yasa ta meda kanta kan Zaleeha sabida taga Saifuddeen kallon farin cikin tayashi murnar da tayi yake mata ta hango wani baiyanenne farin ciki a fuskarshi cikin kula tace.
"Ammin Adeel ya jikin?".
A hankali tace.
"Na worke fa Ummu Adeel".
Dariya Raliya tayi tare da cewa.
"In kinci abinci ne zamu yarda kin worke".
Da sauri Saifuddeen ya jinjina mata kai alamar da kyau.

Ahmad kuwa dariyar ƙeta yayi tare da cewa.
"Allah ya fito mana da _Sodangi_ mu lfy, dan dai shine ya somu yasa aka gudu aka kuma dawo,
Jingudo haka sunan yake ko macece ko na mijine".
Dariya sukayi dukansu, Ameena kuwa shiru tayi.
Kalmar Jingudo da Ahmad ya kira ta amsa mata tarin tambayoyin dake ranta na cewa ina Zaleeha taje
Dan duk cikekken bafulatani in yaji an kira yaro da Jingudo ko Sodangi to yasan auren dole akawa mace, ta haifeshi a gidan wanda aka aura mata dolen, to shi ake cewa Jingudo."
A ranta ta tuno kalmar Adda Rahma inda take cewa mata.
"Kan Abu ɗaya ya taɓa nuna ƙulafashinsa a duniya a kanta ne kaɗai,
Sai ta kuma nazarci kalmar Ahmad na cewa Allah ya fito mana da Sodanginmu lfy don dai shine ya somu an gujemu an dawo".
Kai ta rausayar jin Ummi na cewa suje suci abinci.
kan dinnin table ɗin suka nufa, tana mai magar zuciya.
"Uhumm Ahmad kenan da kenan ka sani yanzu son Abban Adeel da nake hangowa cikin idonta ya wuce zaton mai zato, Allah sarki wato auren dole akayi mata, da alama kuma guduwa tayi lokacin da Adda Maryam ta rasune ta dawo ikon Allah to meyasa Zaleeha zataƙi Abba Adeel duk da tarin kyanshi da dukuyarshi basu ruɗeta ba."
Jin Saifuddeen ya murza hannunta alamun taci abinci ne yasa tasa hannu ta fara ci.
Zaleeha kuwa sanadin alluran da akayi mata to ta samu taci abinci sosai,
shiyasa duk jiri da murɗa da duhun suka tafi sai ɗan kasalar da ba'a rasaba.


Ranar dai Saifuddeen wuni yayi yana jinya,
shida kanshi kuwa ya kira Ya Ameenu da ya Ahmad ya sanar musu batun cikin Zaleeha,
sosai Ya Ahmad yai tawa Zaleeha wasa wai ashe yanzu kam girma yazo zata bar guje-guje.


A can gidan ya Ameenu kuwa suna gama yin mgnar ya kalli Ziyada dake zaune gefenshi hannunta ya rike a hankali yace.
"Kinji Adda Zaleehan takima bata da lfy, tanata aman laulayi ciki gashi kema har yanzu tafiyarki bata gama gyaruwa ba,
kiyi haƙuri sai kin ƙara samun sauƙi sai in kaiki ku wuni kinjiko Mar'tus saliha na tuba".
Kai ta jinjina cikin sanyinta irin na adda Maryam tace.
"To Ya Ameenu".
Jawota yayi ya ruggumeta domin biyeyyarta sak Maryam yake gani sam basu da gardama.

Bayan sati ɗaya lokacin cikin Zaleeha ya cika watanni uku cib-cib kuma Alhamdulillah ba laulayi sosai yanzu sai yawan cin abinci.
Da dare Ameena ce ke zaune gefen Saifuddeen wanda yake waya da Dr Acash prasat,
nan yake gaya mishi. "Lokacin dawowarka fa ya kusa".
Kanshi ya gyaɗa dan video call sukeyi cikin nitsuwa yace.
"Eh inata shirin zuwa ai".
Da sauri Dr Acash prasat yace.
"No karka taho India, ƙarshen watan nan zamuyi taron ƙarawa juna sani na duniya baki ɗaya, zamuyi taron ne kuma a Istanbul na kasar Turkey.
So kayi ƙoƙari mu haɗu a can, zan haɗaka da wani babban Dr da zai dubaka wanda duk ya fimu sanin matakan warakar ciwon insha Allah zaka samu dace".
Cikin gamsuwa da wani sahirtaccen jin daɗi Saifuddeen yace.
"To ba matsala".
Daga nan suka katsa wayar,
cikin kula Ameena tace.
"Kai ƙasa mai daɗi kena Instabul weather su akwai masifar daɗi."
Murmushi yayi tare da cewa.
"Sanyi su ne keda yawa, tsarin ƙasar is Gud, a dai irinmu masu larurar spinal cord injury jikinmu irin garin yakeso".
miƙewa tayi tare da cewa.
"Eh sosai ma kuwa".
A hankali yace.
"Ina zakije kuma kika tashi."
Hannu tasa ta tallaɓe ƙirjinta tare da cewa.
"Zan ɗauko Adeel ne naji mamanshi nata tsastsafo alamun ya tashi a bacci kenan".
Dariya yayi tare da cewa.
"Tsakanin uwa da ɗanta sai Allah".
Murmushi tayi kana ta fita.
Shi kuwa text message ya turawa Zaleeha.
"Salam, Baby maman baby kinyi bacci ne?".
da sauri ta maida mishi amsa.
"A a banyi ba, ina cin abin daɗin ne Ummi na ta dafa min."
murmushi yayi tare da rubuta mata.
"Abin daɗin kam ai yana wurina".
Murmushi tayi.
da sauri ta duba sakon daya kuma tura mata.
"Kinada E Passport ne"?".
a hankali ta rubuta mishi "Eh to gsky nawa ya daɗe bazaiyi aikiba yanzu".
"To ki shirya gobe da safe zamuje imagireshon Office, aiyi miki E Passport ɗin".
ido ta lumshe cikin tsananin farin ciki dan dai tasan ƙasar za'a bari da ita kenan tunda taji ana neman E Passport a zahiri kuma sai cewa tayi to.

Washe gari kuwa da safe sukaje akayi mata E Passport ɗin ta,
daga nan airport suka wuce,
ya fara nema musu damar barin ƙasar,
sai azahar suka dawo gida.


Alhamdulillah yanzu tana cin abinci ba laulayi, kamar yadda Ameena ta raini cikinta a sauƙaƙe,
to haka itama ko dan jinin

Please Login or Register in order to submit comment